
Post
KIDA A RUWA BOOK 4 PAGE 18
..... son, you don't have to let me go". "You don't owe me anything, but you have something important to me, Nimrah. Then I owe you a lot. I have been looking for a way to find you for a long time but I have lost. I just recently heard that you got married. You married your enemy, who tried to kill your mother. Nimrah did not think there was any mistake in doing that. But I apologize to you, I understand that you still don't know who Zak-Shadow is. That's one person's ability to walk and walk. He is a complete mess who does not understand his front nor his back...” You distract me a lot. Because of the things you told me about him in the past, I don't see that from him now. But I will give you one chance, if you fail, you will be surprised. "Mr Specter quickly gave Dagger a sign that he agreed. So Dagger calmed down again and said, "I agree to all your conditions, Nimrah. And this time I promised you that I will confirm the hidden face of Zak-Shadow that you do not know. Then I revealed to you his bad deeds. Then I will connect you with your mother who is hiding herself because of him".
*_Typing📲_*
*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_Masu fama da matsalar idanu kuma naku ya fara sauka a AREWAPEN faka-faka AUDIO da zafinsa. Book 1 zaku sameshi a cikin book 1. Book 2 na tare da book 2 shima. 💃💃😘😘😀_*
*_GENERAL FICTION_*
_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._
*_BOOK 4_* _Chapter 18_
_________________ _________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
..........Cike da tsiwa Nimrah ta ɗaga wayar. Dama gashi zuciyarta a kusa take. “Nikam wai ko kana bina bashi ne malam? Ka takurama rayuwata fa. Tunda ka faɗi abinda kake son faɗa a baya ba sai ka ƙyale ni ba”. “Ba kici bashi na ba, amma kina da abu mai muhimmanci a wajena Nimrah. Sannan ni da alkairi nake binki. Na jima ina neman hanyar dazan sameki amma na rasa. Sai a kwanan nan nake samun labarin kinyi aure. Auren ma wai maƙiyinki kika aura, wanda yay yunƙurin kashe mahaifiyarki. Anya kuwa Nimrah baƙya ganin akwai kuskure a yin hakan. Amma na miki uziri, dan na fahimci har yanzu baki gama sanin waye Zak-Shadow ba. Makirin mutum daya iya taku da bada ƙafa kenan. Shi ɗin ƙuli-ƙuli ne da ba'a gane masa gaba balle baya.....” “Nifa gaskiya kana sakani a ruɗani. Kana raba min hankali da yawa. Saboda ko abubuwan daka gaya min a kansa a baya ni ba haka nake gani daga garesa ba a yanzu. Amma zan baka dama guda ɗaya tak, idan har ka gaza zaka sha mamaki na. ” Da sauri Mr Specter yay ma Dagger alamar yace ya yarda. Dan haka Dagger ya sake kwantar da murya ya ce, “Na yarda da duk sharaɗin ki Nimrah. Sannan a wannan karon na miki alƙawarin sai na tabbatar miki da ɓoyayyar fuskar Zak-Shadow da baki sani ba. Sai na bankaɗo miki munanan ayyukansa. Sannan zan haɗaki da mahaifiyarki dake ɓoye kanta saboda shi”. Nimrah ta ɗanyi shiru kamar mai nazari. Sai kuma a hankali ajiyar zuciya mai nauyi ta suɓuce mata. Ta kai zaune a bakin gadon karo na farko. Tabbas tana son ganin Ummanta, tana kwaɗayin hakan kodan ta tabbatar da gaskiyar nan akan Dadah... “Kin amince?”. Dagger ya katse mata tunani. Kamar tana a gabansa ta jinjina kanta a hankali. “Na amince. Sai dai ina sake tabbatar maka idan naga daɓanin abinda ka faɗa zan baka mamaki. Dan kai ma baka san wacece ZAKANYAR KAWU TANIMU ba. Nimrah kawai ka sani”. Dagger yay ƙaramar dariya. “Niko nasan Zakanyar Kawu Tanimu. Amma bazaki san na sani ba sai nan gaba idan kika gama sanin wanen ni. Na barki lafiya. Sai dai nan da kwana kaɗan saƙona zai riske ki. Idan kin aiwatar yanda ya kamata ki fara shirin haɗuwa da Ummanki. Kije ga mijinki dan yau kaɗan ya rage kishiyarki ta halaka shi da ƙwaya...” Ɗiff wayar ta katse. Ƙirjin Nimrah ya buga, sakamakon kalaman ƙarshe. “Kwaya?”. Ta maimaita kalmar da tafi tsaya mata a ƙofar zuciya. Ai ba shiri ta watsar da wayar ta miƙe jiki na ɓari ta fita....
...★ Anan kam kusan tare members na ƙungiyar duhu suka sauke ajiyar zuciya. Domin kuwa wannan kira nasu ne bana Dagger ba. A daren jiya duk wani mai alaƙa da ƙungiyar ya dawo gida. Cike da matsanancin ruɗanin abinda ya faru da Oga Jush. Tun a jiyan suke meeting. Sai faman ƙullawa da kwancewa suke tare da hasashe-hasashe. Daga ƙarshe dai suka yanke komawa yin amfani da Nimrah kamar yanda Oga Jush ya tsara kafin mutuwarsa. Shine suka saka Dagger ya kirata tunda dama shine ya fara aikin. “Woow aiki mai ƙyau Dagger”. Viper ya faɗa cikin katse shiru da tunin da ɗakin meeting ɗin ya ɗauka. Murmurshi Dagger ɗin yayi, zuciyarsa na ayyana masa (Kaina nake ma wannan aikin ba ku ba. Tunda Oga Jush ya tafi gara na ɗauke Nimrah ta mu kama gabanmu muma) a zahiri kuwa godiya yay ma Viper dama sauran shugabanin dake nuna yabawa. Mr Specter ya miƙe, cikin gyaran murya ya fara magana da isar daya saba.. “Yanzu dai mun samu bakin zare na farko da zamu tabbatar da zarginmu da ya karkata akan Zak-Shadow sakamakon binciken da muka yi a kansa. Inda muka samu tabbacin tafiyar da yayi kwanaki ƙasar Dubai yaje. Wannan yasa bazamu taɓa cire zarginmu a kansa ba game da kisan shugaba. Duk da a yau sabon bayani ya sake fitowa game da budurwarsa. Ba zamu ƙi amsarsa zancen su ba. Tunda iya tunaninmu mun rasa makamar riƙewa dangane da abinda ya faru da shi. A labarin sirri dana samu daga majiya mai ƙarfi game da rasa Oga daren jiya shine budurwarsa ce ta kashe sa. Dan bincike ya nuna sunyi faɗa a watannin baya da shi, inda har ta nema suyi aure shi kuma yaƙi, ita kuma tace dolene fa wannan aure nasu ayi, idan ba haka ba zata bashi mamaki. Dan zata kai shi kotu tare da bayyana ma duniya ɗan da suka haifa tare tun shekarun baya da shi kansa bai san da shi ba na nan. Da farko ya ɗauki maganarta ƙarya da wawanci, sukai faɗa sosai suka rabu. Sai dai ya kasa samun nutsuwa ya shiga binciken ta batare data sani ba tsahon watanni. Kwatsam a watan daya gabata ya gano maganarta gaskiya ce. Ta haifi yaro tun a farko fara mu'amular su, amma ta kai yaron gidan marayu ta ɓoye. Yabi wasu hanyoyi domin ɗauke yaron dan yana masifar tsananin kama da shi amma ya samu duk ta toshe, daga ƙarshe ma data gane yana bibiyarta sai ta ɗauke yaron ta sake ɓoye shi. Wannan shine dalilin da yasa muka kasa gane kanshi kwanaki da yin sakaci da komai na ƙungiya, shine kuma dalilin koma mata ya bata haƙuri ya kuma ce ya amince, sannan ya buƙaci ta bashi yaron ko ganinsa yayi. Ta amince zata bashi, sai dai da sharaɗin dukkan dukiyarsa zai maida da sunan ɗan nasu ko ya yarda dai ayi aure. Anan ne ya gane manufarta a kansa, wato ta ajiye yaron matsayin makami dan ta mallaki abinda ya tara shiyyasa take son suyi aure. A zahiri baiƙi ba, ya amince mata, sai dai ya shirya mata shima da shiri na musamman, dan haka ya yaudareta suje Dubai su huta daga nan suyi baiko sai ya shigo ya gana da mu ya kuma ƙaddamar da sabon tsare-tsare na ƙungiya. sai ya sake komawa wajenta suje suga yaro ya kuma mallaka komai gareshi na dukiya. Ita kuma suyi aure. Batai ko musu ba duk ta amince, sai dai itama da nata shirin take. Shirin nata ne kuma ta aiwatar, duk da masu fashin baƙi sun shiga rikicin tunani akan miyasa zatai haka batare da samun damar mallakar dukiyar ba? Wasu kuma na kallon lamarin da Oga Jush ɗin ne ya fara kai mata hari kota gano manufarsa shiyyasa... To gaskiya dai ta gagara bayyana. A yanzu haka jami'an ƙasar su dana ƙasar Dubai abinda suka duƙufa nema kenan wannan gaskiyar da dalilin kisan da sukaima junan. Dan an gano bullet ɗin da aka harbi budurwar har sau biyu na Oga Jush ne. Shine yake amfani da shi a bindigar daya saka aka ƙera masa ta musamman daga zinari. An kuma samu bindigar a ɗakin itama.. kunga kenan basu kaɗai ba harmu muna buƙatar sanin wannan gaskiyar, sannan zarginmu nada ƙarfi akan Zak-Shadow”. “Tabbas haka ne. Dan ko zamu yarda da wancan labarin dole mu fara tabbatar da babu hannun matsiyatan can guda uku. Janar, Zak-Shadow, Imran. Dan ni kaina bawai wancan labarin bai kama hankalina bane. Zuciyata ta kasa gamsuwa ne. Musamman idan mukai dubi da tafiyar Zak-Shadow ɗin ta sirri a kwanakin nan. Mutumin nan makiri ne, zai iyama haɗa hannu da yarinyar ai...” “Wlhy komai zai iya faruwa indai matsiyacin yaron can ne. Dan haka dole ne barci ya ƙare mana daga yanzu. Dan in har da hannunsa to mu tabbatar ya mana duka ne a ƙashin baya. Idan mukai sakaci zamu koma rayuwa ne a wheelchair kamar masu ciwon laka....” “Tabbas indai da hannunsa wannan shine target ɗin sa a kammu. Amma idan yasan wata ai bai san wata ba. Idan ya dake mu a baya ta hanyar kashe Oga Jush, mu kuma zamu dake sa a zuciya ta hanyar yin amfani da matan aurensa guda biyu. Dan a yanzu haka wasan mu ya fara, yana can a buge kuma zai iya ɗaukar sati guda a haka, zamuyi amfani da wannan damar domin kafa sabon tsarin ƙungiya, bazamu bari yaci nasarar shirinsa ba. Rikita mu, sace mana gwiwa, da hargitsa mu. Zamu haɗa zaman makokin Oga Jush da samar da sabon shugaba a tare, hakan ne zai bamu damar shimfiɗa sabbin ayyukanmu kafin ya dawo hayyacinsa. Zamu fara da zaɓen candidate guda biyu a yau ɗin nan, amma sai zuwa dare muje mu fara nazari..” Kowa ya gamsu da tsarin. Dan haka aka buga table. Sannan akai shiru na mintuna biyar. Ma'anar shirun shine zaman makoki....
<%><%><%><%>
Duk da a hargitse ta fito, koda tazo ƙofar shiga sashen sai ta nutsu ta saita kanta sannan ya shiga. Da Daddy Imran ya fara cin karo a falon. Wanda tunda ya mata kallo ɗaya shima sai ya kauda kansa. Inda yake ta ƙarasa, cike da girmamawa ta durƙusa tare da faɗin, “Dadday ina kwana”. “Lafiya lau Nimrah, kin tashi lafiya”. Maimakon amsa saita ɓata fuska zatai masa shagwaɓa. Murmushi yayi kawai, cikin katseta ya ce, “Dadan ku ne baida lafiya. Yana bedroom an saka masa drip. Shiga ki zauna da shi zanje wani waje yanzu na dawo na samu kiran gaggawa”. Sosai ta nuna tashin hankalinta. Dan da ƙyar ma ta saurare shi yay mata bayanin idan ruwan ya ƙare zata iya cirewa?. Tace eh zata iya. Yace to taje, amma karta fita ko ina ga abinci nan ya kira za'a kawo daga sashen Mammah. Kai ta jinjina masa cike da girmamawa tana miƙewa..........✍️
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*
*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*
*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*
*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*
*_Akwai VIP Telegram 💃_*
*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*
*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*
_(2k)_
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (2k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.
_(1,500 CFA)_ *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_AREWAPEN (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*