Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 4 PAGE 17

Post

KIDA A RUWA BOOK 4 PAGE 17

.....he took one bath and did not do it since he came out at night. However, no matter how much he wanted to go out for the Fajr prayer, it was impossible for him. He has to do it in a room and he is holding his head. He had a terrible headache and felt as if he might lose his life. So he went back to bed and hardly slept. Around 7:30 Imran called. When he slept with it on his mind, he could hardly pick up the phone. Even when he responded to Imran's salutation, he started provoking him and his face fell. Confused, he started asking him questions. He told him that he was just not feeling well, he had a headache yesterday. Daddy Imran's mind was very upset, so he just cut the call. They are now entering the house with Dadahn's trusted doctor who is taking care of his poising case here at home. They sat in his living room and Imran called his phone. Now, because of one sleep, he started carrying it and he could hardly lift it. Dan did not wake up to see Nabeeha in the room. He knew that she was angry because he came to pray and called her by the name of Nimrah, and to God, there was a problem because he had been very close to the girl for the past two weeks. But he did not humiliate

Standalone post2,107 words

*_Typing📲_*

*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_Masu fama da matsalar idanu kuma naku ya fara sauka a AREWAPEN faka-faka AUDIO da zafinsa. Book 1 zaku sameshi a cikin book 1. Book 2 na tare da book 2 shima. 💃💃😘😘😀_*

*_GENERAL FICTION_*

_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._

*_BOOK 4_* _Chapter 17_

__________________ __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........Anan ɓangaren Dada kam baida lafiya. Abinda ya sha a ruwan da Rayhana ta ajiye da abinda ya shiga tsakaninsa da Nabeeha ya saka shi a wani hali. Da asuba da ƙyar ya iya yin wanka daya kasa yi tun dare ya fito. Sai dai duk yanda yaso fita sallar asuba hakan ya gagare shi. Dole ya yita a ɗaki yana layi da riƙe kai. Wani irin azababben ciwon kai yake ji tamkar zai iya rasa ranshi. A haka ya sake komawa gadon da ƙyar ya kwanta. Wajen 7:30 sai ga kiran Imran. Da ya kwana da shi a zuciya, da ƙyar ya iya ɗaga wayar. Koda ya amsa sallamar Imran ɗin daya fara tsokanarsa sai gabansa ya faɗi. A rikice ya shiga jera masa tambaya. Shine yace masa kawai baya jin daɗi, ciwon kan jiya ne bai sake shi ba. Sosai hankalin Daddy Imran ya sake tashi, dan haka ya yanke kiran kawai. Shine yanzu suke shigowa gidan tare da amintaccen likitan Dadahn dake kulawa da case ɗinsa na poising anan gida. A falon shi suka zauna Imran ya kira wayarsa. Yanzun ma saboda barci daya fara ɗaukarsa da ƙyar ya iya ɗagawa. Dan bai tashi yaga Nabeeha a ɗakin ba. Yasan fushi tayi saboda yazo tashinta salla kawai ya kirata da sunan Nimrah, shi kuma har ga ALLAH an samu matsala ne saboda kwanakin nan na sati biyu da ya samu kusanci da yarinyar sosai. Amma badan ya wulaƙanta ta yayi ba. “Muna falonka, zaka iya fitowa?”. Daddy Imran ya katse masa tunani. Ban san amsar da Dadan ya bashi ba daga can. Yadai miƙe yana faɗin, “Bari kawai mu shigo ciki idan ba damuwa.” Amsar daya sake bashi ce ta sashi yanke kiran yana cema Doctor, “Ina zuwa”. Daga haka ya wuce bedroom ɗin na shi..

★=========★

Nimrah sarkin nauyin barci da ƙyar ALLAH ya taimaketa alarm ɗin data saita ya tashe ta. A hakan ma sai da ta makara. Tana idar da salla ta zauna shiru zuciyarta na kai-kawo. Yayinda yanayinsu da Dadah a kowacce safiya kamar haka ya fara zuwa mata. Turashi tai da tsiya-tsiya, ta ɗauki Alkur'ani ta hau karatu. Tayi nisa kamar abin almara taji ringing ɗin waya a ɗakin. Wayar ma irin ƙaramar rakani kashin nan. Mamaki ne ya kamata. Dan tasan ita dai bata da irin wayar. Cikin waige-waigen da take ta fahimci inda wayar take. Alkur'anin ta rufe, tare da miƙewa ta je inda wayar take ta yaye labulen. A jikin window ne aka saƙalata. Ƙirjinta ya ƙara bugawa. Cikin rawar hannu da karato addu'ar da duk tazo mata a baki ta ɗakkota. Dai-dai nan kiran ya sake shigowa. Ta sake tsirama number ido. Dan number ce da har abada bazata manta da ita ba. Zuciyarta ta shiga raba mata hankali akan ta ɗaga ko ta barshi. Ɓangaren da yafi ƙarfafata tabi, ta dangwarar da wayar ta koma inda take karatun ta ƙarasa. Duk a cikin son ƙarfafa kanta ta sake komawa gadon tai kwanciyarta tana addu'a da fatan barci ya ɗauketa.....

<%><%><%>

Ba ƙaramin tashi hankalin Daddy Imran yayi da ganin halin da Dada ke ciki ba. A rikice ya shiga jera masa tambayoyi. Sai dai bai samu amsa ko ɗaya ba dan hannunsa ma na riƙe da kansa ne. Imran da yaga babu wani abun kaico da Doctor zai iya gani sai kawai ya koma ya masa iso cikin ɗakin.. Shima kansa doctor yanayin Dadan ya bashi tsoro. Musamman daya san halinsa na jarumta akan ciwo. Babu zancen ɓata lokaci kawai ya shiga dubashi yanda ya dace da jera masa tambayoyi. Ganin bashi da niyyar kula doctor ɗin Imran ya shiga roƙonsa da magiya. Dole ya daure ya amsa masa a dunƙule kuma a takaice. Cikin zargi doctor ya sake masa sabon bincike bayan na ainahin matsalar da yake shan magani a kanta. Sai dai abinda ya gano ɗin ya rikitashi, bai daiyi magana ba. Treating ɗinsa ya fara yi yanda ya kamata. Dan wasu allurai ya haɗa a cikin drip ya saka masa. Sai da ya tabbatar komai yana tafiya yanda ya kamata sannan suka fito shi da Imran ɗin saboda Dada ya fara barci mai nauyi.... “Doctor akwai wani matsala ne?”. “Tabbas akwai matsala Sir, amma in sha ALLAHU komai zai zo da sauƙi. Sai dai a sanin da naima Yallaɓai baya shan komai na maye, ban san yaya akai haka ba”. “Maye kuma? Ai ko sigari zan iya rantsewa Haysam bai taɓa kwatanta sha ba balle ma shan”. “Shiyyasa na shiga ruɗani ai. Dan gaskiya matsala biyu ce ta haɗe masa shi ya kawo masa wannan matsanancin ciwon kan da badan anyi gaggawa ba komai zai iya faruwa. Kuma ko yanzu na san da wahala in baiyi jiyyar kwana biyu ba. Damma yana da jini mai ƙarfin gaske, dan wannan kwayoyin zasu iya sakashi barcin sati guda wlhy koma su masa illa a brain”. “Doctor kanata min magana a juye fa...” “I'm sorry Sir. Yallaɓai yasha ƙwayoyi ne masu ƙarfin gaske. Sai kuma matsalar da kasan yana shan magani a kanta. Sai kuma ƴar gajiyar jiki data kawo ciwon kan tun fil azal...” “Kwaya kuma?”. “Tabbas kwaya ta shaye-shaye ma”. “No! No! Ba Haysam ɗina ba. Akwai dai abinda yake ɓoye daya kamata mu sani. Yanzu komai daya dace ka masa?”. “In sha ALLAHU. Sai dai zai iya tashi da zazzaɓi mai zafi. Idan hakan ya kasance za'a iya masa amfani da ruwan sanyi a jiki. Bayan kamar awa ɗaya idan bai sauka ba dole zan dawo na sake masa sabon treatment. Sai kuma ciwon ciki, duk da na masa allurar saurin daƙile hakan amma bamu san abinda ALLAH zai yi ba, dan wannan daga waccan matsalar ne”. Godiya Imran yay masa, tare da rakashi har compound. Hakan yay dai-dai da fitowar Mole daga bayi. Ai da uban gudu ya koma ciki zuciyarsa na duka da sauri-sauri. Tabbas yau ALLAH ya kiyaye da shida Imran dole ai kiciɓus na zahirance.....

(★)-(★)-(★)-(★)-(★)

Cikin sa'a kuwa barcin ya ɗauki Nimrah. Sai dai gaba ɗayansa mafarkin kiran wannan waya da bata ɗaga ba ya kasance. Sai kusan tara da wasu mintina ta tashi da ƙyar. Sam bata wani ji daɗin barcin ba. Sai ma ji take kanta ya mata nauyi kamar zai yi ciwo. Ga yanda jikinta yay mata nauyi wanka kawai take buƙata. Dan haka ta gyara gadon kamar ba'a kwanta ba sannan ta nufi bayi. Can ma sai da ta gyara sannan tayo wankan. Ta fito kenan kira ke shigowa wayarta. Sai da gabanta ya faɗi, sai kuma fahimtar wayarta ce bata ɗazun ba ya sa ta sauke a jiyar zuciya. Sai ta share wayar kawai ta shiga shiryawa. Sai da ta kammala tsaff cikin doguwar rigar abaya baƙa datai mata ƙyau sannan ta ɗauki wayar tana shafa ciki dan yunwa take ji. Sosai ta waro idanu waje ganin Daddy Imran ne ashe ya kirata. Da sauri ta kira shi back. Daga can Imran ya amsa sallamarta da gaisuwa da tai masa a tare. Daga ƙarshe yace tazo yanzu ta same shi a sashen Dadan su yana jiranta. Bata kawo komai a ranta ba tace to. Kamar jira ake ta yanke wayar waccan ta fara ringing itama. Ji tai wani kalar takaici ya kamata. A fusace ta nufi wayar dan ɗazun a saman sofar ɗin ɗakin ta wullar da ita. Ɗauka tai a zafafe ta ɗaga kiran....

{==}{===}{===}{==}

“Lafiya kuwa gidan nan yake Aunty?”. Shiru Nabeeha bata motsa ba, balle Amima tasan taji maganar tata. Cikin mamaki ta ƙaraso inda take jikin mirror tsaye da waya a hannu. Itama zama tai a stool ɗin mirrorn sannan ta taɓata. Firgigit Nabeeha ta dawo hayyacinta. Dan ita ko motsin shigowarta ma bata ji ba, ranta a ɓace yake sosai da abinda take ganin Dadah ya mata da gangan. “Aunty kina lafiya kuwa?. Inata magana amma shiru kamar wadda ta suma a tsaye”. Gajeren tsaki Nabeeha taja, sai kuma ta sauke numfashi tana ajiye wayar a kan mirror ɗin. “Bamma san kin shigo ba sam wlhy. Hankalina ya tafi wani tunani can daban”. “Hummm Aunty kenan. Ya kamata dai ki kwantar da hankalinki, idan ma har yanzu waccan banzar yarinyar lamarinta ke damunki. Ba gashi har sun dawo sun sameki ba cikin ƙoshin lafiya. Miya gwaguyeki? Ita kuma mi ta fiki da shi? Tana tafiya kamar zata tsinke duk da nasan ba finta nai ba. Shiru Nabeeha batace komai ba, sai dai tayi ɗan murmurshin takaici da jan tsaki. Sakin zancen itama Amimah tayi, ta koma na farko data shigo da shi. “Uhm dama fa naga wannan Imran yake ko mi a gidan da wani baƙo sun nufi sashen Yaya Haysam, shine nace lafiya kuwa?”. Sosai ƙirjin Nabeeha ya buga, tadai yi ƙarfin halin dannewa. Abinda ya faru ne daren jiya ya shiga dawo mata, duk da da safen nan abinda yay mata yasa bata tsaya tambayarsa yaya kan nashi ba. Duk da kuwa a gaban idonta tana gani da ƙyar ya iya kai kansa banɗaki tamkar wanda ke cikin maye, da alama ma akwai sabo na jiki da ya sashi farkawar. Haushin kiranta da wannan suna yasa ta baro masa ɗakin masa ɗakin batare data jira shi ba. Anan ɗakinta tai wanka tai sallar asuba. Ba kuma ta sake bi takansa ba tai zaman yin waya da Momyn su da taga tai mata kira har kusan biyar da daddar..... “Aunty baki bani amsa ba kin sake tafiya tunanin”. “Mtsoww! Ƙyale ni Amimah kinji. Idan na gama abinda nake zan fito” “Amma Aunty dakin duba ko wani abu ne dai...” “Nace ki barni. Zuwan Imran ɗin ne baƙonki a nan gidan ko mi? Kin san dai yanda kullum yake nane da shi ko matar aurensa sai haka. Mtsoww ba zuwa da sassafe ba yama dawo nan gidan shima a bashi ɗaki, kinga mu zama matansa uku ke nan”. Fahimtar ranta a ɓace yake yasa Amimah bata sake magana ba ta fito.........✍️

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*

*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*

*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*

*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*

*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*

*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*

_(2k)_

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (2k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.

_(1,500 CFA)_ *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_AREWAPEN (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*