Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 4 PAGE 8

Post

KIDA A RUWA BOOK 4 PAGE 8

..... yes, this is all her work, and she is a gold you can look at her as a key holder too. It's a disaster if you keep shooting with it or it doesn't do anything. You can shoot a person with it while you are sitting next to each other and you don't know. Dadah pulled off his face mask. He directly explained to her in his confused face of ZAK-SHADOW. In an open voice similar to the roar of a LION he uttered. "I don't keep my promises to those who are careless. I haven't even made a promise to them, let them think that I will keep it. You have come into the trap of ZAK-SHADOW with the brain of a PIG". Jush's uncontrollable screams let go of his body and showed Dadan. But there is no opportunity to speak. Dadah put a piece of gum in his mouth. So once it is opened, the mouth goes away like a gum when you put it on something and pull it. Torment was part of him, he put his hand on his mouth and his body was in a state of collapse as if he was looking for a dirge. Dadah didn't even look at him, he knew he was done with him. Desperate and wanting to show her to him, it was Jush's girlfriend, Jush, who pulled out a small gun in her hair and showed it to him. Saying, "Are you going to DIE

Standalone post2,010 words

*_Typing📲_*

*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_Masu fama da matsalar idanu kuma naku ya fara sauka a AREWAPEN faka-faka AUDIO da zafinsa. Book 1 zaku sameshi a cikin book 1. Book 2 na tare da book 2 shima. 💃💃😘😘😀_*

*_GENERAL FICTION_*

_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._

*_BOOK 4_* _Chapter 8_

__________________ __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Maimakon bata amsa kawai Dadah ya saka mata wata ƴar mitsilar bindiga mai kama da ta wasan yara, ta wasan yaran mai irin ta cacar balo ɗin nan da ba'a iya sarrafawa. Sai dai fa wannan komai nata na aiki, sannan Ta zinari ce da zaka iya mata kallon wani key holder ma. Tsabar masifa idan akai harbi da ita ko ƙara bata yi. Dan za'a iya harbin mutum da ita kuna zaune ƙugu da ƙugu batare da ka sani ba. Dadah ya janye mask ɗin fuskarsa. Kai tsaye ya bayyana mata a rikitacciyar fuskarsa ta ZAK-SHADOW. Cikin buɗaɗɗiyyar murya mai kamanceceniya da gurnanin ZAKI ya furta. “Ni bamai cika alƙawari bane ga gafalallu. Dan tun fil azal ma ban ɗauka musu ba balle suyi tunanin zan cika. Kin shigo tarkon ZAK-SHADOW ne mai kwakwalwar ALADU”. Ihun da baya fita Jush ya saki jikinsa na rawa yake nuna Dadan. Sai dai babu damar magana. Dadah ya tatse masa wani ruwan gum ne a baki. Dan haka daya buɗe sai bakin ya tafi yammm kamar yanda gum keyi idan an saka shi a abu ana ja. Azaba ta sashi saka hannu ya dafe bakin yana wani burburwa da jiki kamar mai neman wajen dirga. Ko kallonsa Dadah baiyi ba, dan yasan ya gama da shi kuma ai. Cikin ɓacin rai da son nuna masa ita a dole tantiriya ce budurwar ta Jush tai wani kalar salo tana zaro itama ƙaramar bindiga a cikin gashinta ta nuna masa. Tare da furta, “Ashe kuwa zaka MUTU”. “Tabbas zan mutu. Amma in sha ALLAHU ba a hannun irinki ba”. Ya bata amsa da tsawa mai firgitarwa. “Ƙarya kake, dan ko'a zamanin da kuka ce ku masu jarumta ne BAYI kuka koma mana. Idan kana da jahilcin sanin DUNIYA jeka binciki TARIHI. Kaf African ƙasƙantattu ne a gabanmu”. Dadah ya gama kaiwa wuya. Cikin kwarewa da salo na musamman irin na horarren Barde ya sakar mata harbi a hannun da take riƙe da bindigar. Sai dai abin mamaki wani kalar sauti ta bada (tsuttt) kawai kamar an saki ƙaramin tsaki. Bindigar hannunta ta faɗi ƙasa. Ta riƙe hannunta tana ƙoƙarin ɗauka ya kwasheta da ƙafa sai gata a ƙasa. Hannun ya take dai-dai wajen harbin. Tako saki wahallen ƙara jikinta na rawa. Amma abinka da masu jan kunne, sai ta shiga tattaro yawu zata tofa masa cike da ƙarfin hali. Bata san ZAKIN ZAKI bane. Har ya gama karance manufarta. Ya wani kalar saka ɗayar ƙafarsa ya daki bakin da mugun takalmin Boot ɗin ƙafarsa mai kama da kofatan doki. Kamar yanda suke magana da harshen turanci ya ce. “Ƙarya kike ƙaramar kunama. Ko'a jiya MAZAN KWARAI basu kwanta kun taka su ba sai da kuka haɗa da makirici. Wawayen cikinmu suka kasance SAI BANGO YA TSAGE a gare mu. Da wannan ne kuka ci nasarar sarrafamu da sunan BAYI. A yanzu ko KU ne bayin mu. Dan dole ku ƘERA, ku SAMAR, ku JIRA muzo mu saya. Ku shigo jikinmu da ZAMBA CIKIN AMINCI ku sata daga arziƙin mu. Kuna murnar mamayewa daga GAREMU ku ɓata lokaci ayin gine-gine na ƙawa. MU ZO CIKI mu huta. Domin mu mun yarda abinda MUKA TARA shine NI'IMAR MU ta hanyar KASHEWA koda sune last kobbo ɗin mu. Da ace kina da sauran dama dana baki saƙo. Sai dai kash yau ce RANAR TAFIYA. Ranar da zaki san ALLAH ALLAH ne. Ranar KAICO, ranar DANA SANI. Jeki ki amsa KIRAN MAMALLAKIN DUNIYA DA KAYAN CIKINTA Gafalalliya.” Tsutt. Ya sake sakar mata harbi a saitin zuciyarta. Wani gurnani ta saki dai-dai da wanda Jush yayi cikin magun-magun. Dadah ya miƙe idanun nan a juye. Inda Jush yake ya koma. Zafin da zuciyarsa keyi bai ma san ya fara sauke masa naushi a fuska ba. Ai da gudu su Imran suka iso. Dan sun tabbatar idan zuciyar tasa ta gama haurawa maƙoshi kashe shi zai yi. Duk da bai mutu ba kafin su shigo ya jigata. Har ya fara haɓon jini. Da ƙyar suka iya kwatar sa a hannun Dadah. Sai wani irin nishin wahala yake ga baki ya zama roba. Har muƙamiƙin sun fara kumbura saboda yanda in yaja bakin gum ɗin ke jan kansa shima ya kuma maida lips ɗin ya ɓame.... “Haysam cool down please. Muna buƙatar mutumin nan a raye kaima ka sani. Sannan muna buƙatar barin ƙasar da shi cikin aminci duk da damar da muke da ita. Amma zamu iya samun matsala tunda kasan a yaya lamarin yake. Da sunan wani zamu kama shi ba shi ba”. “Bani ruwa”. Dadah ya faɗa kawai yana huci. Da sauri Daddy Imran ya fiddo kwalbar ruwa a jikinsa ya miƙa masa. Sanin halinsa dama yasa shi tanadarta, dan yasan yanda yay masifar tsanar mutum nan da wahala su kamashi salin alin bai jijjiga masa jini ba. Tass ya shanye ruwan. Ya wullama Imran kwalbar. Cafeta yayi kawai. Shi kuma ya riƙe kansa. Tsahon mintuna su Faro nacan na gyarama Jush jiki. Tare da zirkuɗa masa allurar kashe jiki gaba ɗaya ya sassanƙame kamar matacce. Kamashi sukai suka fita da shi. Babu jimawa sosai suka shigo da wani kuma dake a sandare shima. A yanayin jiki sai ka rantse Jush ne. Shinfiɗe shi sukai kusa da yarinyar. Kusan mintina biyar kafin Dadah ya ɗago yana kallonsu. “Bama buƙatar kansa, hanunsa da ƙafafunsa.” Da mamaki T-Dalha ya juyo yana kallon sa. Haka ma Imran da Faro. Da ƙyar Imran ya ce, “aboda mi?”. “Saboda da su za'a fi saurin gane bashi bane a bincike. Ko a tunaninku zuba ma gawar poising ɗin zai hana waɗan nan mayun bincike a kanta. Musamman daya kasance yana da amfani a cikinsu. Ba narkewa ba komi jikinsa yayi sai sun yi bincike. Sai dai bazasu taɓa gane wace kalar guba bace...” Imran yayi murmurshi. Da gaske da Zakinsa na bashi tsoro a wasu lokutan. Kamar yanda ya faɗa tabbas duk iya bincike su, zasu iya gane guba ce kawai. Amma ina aka yi ta? Waye yayi ta? Wace irin guba ce. Ina ake cinikin ta? ƙaryar su tasha ƙarya. Dan Dadah ne ya haɗata da kansa. Da kansa ɗin ma da abubuwan da ake iya samu ne daga gida. Daga gidan ma ba irin na kai tsaye da za'a iya ganewa cikin sauƙi bane. Imma an gane baka isa faɗin sirrin wace ƙasa bane dan kowane ƙasa nada irin abubuwan. Wannan tana cikin manyan baiwar Zak-Shadow. Duk da baya amfani da ita sai ta kai maƙurar ƙurewa ga azzalumai. Komai daya dace suyi shi suka gudanar. An cire ƙafafu, hannaye da kai na gawar da suka kawo. Kafin su bita da poising ɗin. Tamkar wata almara cikin ƙanƙanin lokaci gawar ta shiga zaganyewa. Namanta da ƙashin na wani kalar narkewa tamkar an saka zinari ko azurfa a wuta. Abinda poising ɗin ke ciki suka maida hannun budurwar ta Jush, tare da saka mata duk wani ayar tambaya alamar itace tai komai. Daga haka suka kimtsa duk abinda basa buƙatar zame musu damuwa sannan suka sake bincike gidan domin tabbatar da babu wata ɓoyayyar cemara. Dan hatta makeken compound ɗin gidan basu barshi ba a wannan dare... Kuce da ni ina securitys?. Securitys dai kaf ɗinsu goma cus nasu Dadah ne. Ainahin na gidan budurwar Jush da ta hau zuga da keken ɓerar da Dadah ya ɗorata ta tattare su ta zuba a wani ɗaki dake gidan bayan ta makar da su da wasu kalar kayan maye masu haɗari. Haka su Dadah suka tsara dama su kasance ba su mutu ba. Dan sai da sune shaidar budurwar Jush ta aikata komai zai fito ma duniya. Abinda zai sake baka mamaki bayan kammala aikin koda suka fito motar dake jiransu a yanzu bana ɗazun bane. Tuni waɗan can an fita da su an kawo wasu sabbi an ajiye. Jush kuma na cikinsu an wuce da shi asibitin da aka ɗakko gawar. Dadah ya kalla Agogon hannunsa sannan ya kalla su Imran. “Yanzu zaku je masaukin ku ku kasance cikin shiri. Shi kuma nanda awa huɗu za'a kammala shirya shi a wuce da shi airport. Dole ku kasance kun riga isa airport ɗin dan jirgin ku na saura mintuna zai tashi zasu baku shi.” Kai suka jinjina masa. Ya sake bin gidan da kallo, tare da faɗin. Da mun fita da awa ɗaya a saki cemaras ɗin gidan. Nan ma suka amsa masa. Motar ya buɗe ya shiga baya. Baƙon fuskar nan ya shiga mazaunin driver. Su kuma su Imran suka shiga ɗayar motar. Yanzu ma Faro ne yay driving ɗin dan yana da lasis ɗin ƙasar. Motocin na fitowa kowacce ta kama tsaginta. Akai gabas da Dadah, su kuma sukai yamma. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso bakin teku. Gadai garin dare ne amma duk harkoki ba'a fasa ba. Dadah bai fita ba har sai da wancan ya fito ya buɗe masa. Cikin risinawa. Koda ya fito ɗin ma sai ya miƙa masa wani ƙaramin bag. Amsa Dadah yay kawai. Batare da yin magana ba ya ɗaga masa hannu ya wuce abinsa. Yana isowa gaban ruwan wani jami'in ruwan ya jefa masa key. Cafewa yay da hannu ɗaya batare daya kallesa ba ya haye mashin ɗinsa na ɗazun daya tsallako. Sakar masa shi akai daga kafen da yake. Kawai ya burga shi yana saka ruwan wani yin fiyyyaaaa ya wuce..........✍️

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*

*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*

*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*

*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*

*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*

*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*

_(2k)_

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (2k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.

_(1,500 CFA)_ *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_AREWAPEN (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*