Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 18

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 18

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 18: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 18. "Akwai wani abu ne daya haifar da rashin aminci ko wani…

3,357 words

"Akwai wani abu ne daya haifar da rashin aminci ko wani motsi da ba'a amince masa ba?". Shuru tamim yayi,kafin ya girgiza kai a hankali.

"Banga komai ba......saidai wannan kwarjinin nasa daya cika gurin gaba......"

"Tamim.......akwai wani me kwarjini ne sama da nawa?"

"Babu" Ya amsa mata cikin qanqan da murya

"Yaushe idanunka suka fara ganin hakan?"

"Ayimin aikin gafara" Ya fada yana rusunawa,abinda ya haifar da shuru kenan.

"Zaka iya wucewa,ka tuntubi bulama ko akwai wani sabuwar alama ko sabuwar masaniya?". Ta fadi tana jin ranta yayi jagulewar da bazata iya ganin bulama bama.

"An gama Allah ya baki nasara" Ya fada yana miqewa,ya sake kai gaisuwar ban girma sannan ya juya yana fita.

Iska ta fesar,tana son ta riski akhnan don auna gwargwadon matsayar tunaninta,tanason kuma ta samu layin tafisu,don tana son shirya komai na auren akhnan ta fanni biyu. Bangaren akhnan din da almaz da takeso kowanne motsi ya tafi da babban motsin da zai ajiye alamun GIRMA cikin dukiyar aure shigarsa da cikar kamalar da zata masa jagorancin samun KARBUWA a zukatan kowa da kowa.

*MORSA SAFIYYA*

A nutse ta amsa sallamar nanny tana ajiye carbin dake hannunta a gefanta saman lallausan kujerar da take zaune a kai.

Daya daga cikin palukanta na alfarma dake sassanta,wanda ke dauke da wani irin sassanya kuma nutsatstsen yanayi. Iya nutsuwa da tsarin sassanta kawai zai gaya maka adadin tata nutsuwar data wanzu har saman fuskarta,duk da tarin ciwuka da firgici tsoro da take boyewa cikin fitowar kowacce rana zuwa faduwarta,amma qarfin riqonta da addu'a ya sanya nutsuwa takan mamaye dukkan wani fargaba da tsoronta.

Cikin girmamawa ta marabci nanny kaman yadda suka saba. Ta zauna suna maganar su Aeera data samu daga falon farko sun gwagwgwafe ana musu lalle.

"Haka kawai don rigima falaak ta tashi kira da neman a kira mata me jan lalle.......wai sun karanta cewa sunnah ce me qarfi......tanaso lallai tayi koyi da abinda annabi ya umarci mata su dinga yi". Kai nanny ta gyada tana murmushi.

"Sosai sheikh yake da qoqari.......ban taba ganin matashin da nutsuwa tayi masa hijabi ba irin malamin nan nasu,ko yanzu bamu dade da gama maganarshi da babansa ba sultane" Ta fada tana murmushi,murmushin daya sanya morsa itama sakin nata murmushin.

"Komai na falaak ya canza,nutsuwarta ta sake yawa,abubuwa da dama sun sauya tattare da ita,duk wansa ya sameshi a matsayin d'a ko suruki dole yayi alfahari da hakan". Morsa safiyya ta fadi tana sakin murmushi,har cikin zuciyarta tana jin dadin sauyin falaak din. Hakan yana sake tabbatar mata da girman tasirantuwa da mutanen kirki da mutanen arziqi. Daidai nan hadiman morsa safiyya suka gama cika gaban nanny da kayan ciye ciye sannan suka janye.

"Ai dama sun jira......basuyi wannan lallen ba,bata hannuwansu zasuyi,su dake da biki a nan kusa" Nanny ta fada tana murmushi. Maganan ya danja hankalin morsa safiyya,ta daga idaunta tana duban nanny din ba tare data tambaya komai ba.

"Daga qarshe dai akhnan ta fidda miji.......in sha Allah kuma sultane ya sanya daurin aurenta sati na sama". Nanny ta fadi alamun farinciki yana wanzuwa saman fuskarta.

Wani irin duba na mamaki morsa safiyya takebin nanny dashi,maganar tayi mata mugun zuwa a bazata. Idanunsu ya hadu guri daya,abubuwa da yawa nanny din ta fuskanta tattare da morsa din.

"Ta fidda miji?,a yaushe?,a 'yan tsukakkun kwanakin nan?,kuma har ta iya gabatarwa sultane?" Tayi tambayar dukka ga nanny wata irin shakka tana ratsata. Kai nanny ta gyada

"Nima nayi mamakin juyewa da sauyawar ra'ayinta haka cikin qanqanin lokaci......saidai shi Allah ba yadda baya iya sauya al'amuransa a yanayin da yaso,a kuma lokacin da yaso" Shuru morsa safiyya tayi,tana jin wuta tana dauke mata. Kowanne sashe na jikinta yana gaya mata wannan ba ra'ayin biftu bane......ba ra'ayin akhnan bane. Fuskar mammina ta gilma ta cikin idanuwanta,ta lumshe idanuwanta a hankali ba tare data iya furta komai ba.

Cikin kunnenta ake mata busa da kamar kalaman.

"Tayi nasara a kanki" Wani sashen na zuciyarta kuma yana kokawa da hakan......yana kuma qaryata abinda takeji daga qasan ranta.

"Safiyya" Nanny ta kira sunanta tana karantar yanayinta. Bata amsa ba illa bude idanunta da tayi tana duban nanny.

"Na roqeki don Allah......karki zargi komai,kada kisa komai cikin qasan ranki,komai Allah yana shiryashi ne daidai da tsarinsa,ki bita da fatan alkhairi da dukka gudunmawar da zaki iya bata don samun ingantaccen aure me dorewa......sultane kansa ya rufe maganar,yace dukkan wanda zai dawo masa da hannun agogo baya zai iya fuskantar fushi da kuma bacin rai......banason ranki ya baci safiyya.....banason wani abu mara dadi.ya gilma tsakaninki da sultane dalilin kishi". Idanu ta zubawa nanny shuru yana dan ratsa gurin,sai kuma ta saki wani siririn murmushi.

"Kishi?" Morsa safiyya ta maimaita kalmar,saita jinjina kanta a hankali

"Koda nace miki toh.....koda nace miki ba komai to tabbas kema kin sani qarya nakeyi. Na rasa idanuwa irin nawa cikin agadez da zasu dinga ganin kalar abinda ni nake gani......na rasa hankula da zuciyoyi irin nawa SAK!. Akwai tarin duffai daya kamata ace sun yaye.....ban sani ba,ko lokacin yayewarsu ne baiyi ba?,amma a cikin jikina zuciyata da gangar jikina suna bani lokacin yana dab da yi......koda bani da abinda zan yiwa khadeeja......amma akwai kyakkyawar alaqa tsakanina da ubangijina.......akwai sauran fili me yawan gaske da zan gurfana gaban ubangijina,ya kuma saurareni da dukkan rahamarsa da jin qansa,komai tarin buqatu da qorafe qorafe na.......bazan iya hana kowa aikata komai akan akhnan ba......amma kuma nima ban manta ba......addu'a tana sauya qaddara mara kyau izuwa me kyau......addu'a tana sauya tarin qaddarori...." Takai qarshen maganar tana jinjina kanta cike da tarin yaqini da tabbaci da wani irin gamsuwa da takeji har cikin qasan ranta da zuciyarta.

*MAMMINA*

sai data gama shiryawa tsaf cikin wani silk material na hareer me tsadan gaske sannan ta koma saman stool ta zauna tana sake gwada kiran tafisu.

Ajiyar zuciya me sanyi ta sauke sanda tafisun ke mata sallama cikin qasqantar da murya.

"Daga yanzu......zaki tafiya ta qarshe wadda ta haura zagayen agadez.......zaki kasance a kurkusa kuma a duk sanda ba buqaceki".

"Duk yadda kikeso shine abinda zai faru.....duk yadda kikeso kuma haka za'a yishi.....fansar lokacina raina da lafiyata a gareki". Wani qasaitaccen murmushi ta saki,tana jin ta gama samun dukkan wata dama ta duniya......an gama hore mata sarrafa dukkan wani mutum dake kewaye da ita,burika qwaya biyu kadai sune abinda suis rage mata cikarsu.

"Yayi kyau......inaso a gobe ki kasance cikin masarauta.......ina buqatar kowanne shiri ya fara gudana na bayyanar almaz a matsayin surukin masarauta.......sannan ina buqatar kowanne shiri ya zama a tsare,irin shirin da akewa bikin kowacce d'iya ta gata. Inaso a shirya dukiyar aure mai gigita hankali da tunani,inaso a gabatar da gaisuwar aure kalar wadda ba'a taba gani ba......inaso girma da izza su nuna kansu,inaso a siyawa almaz mutunci martaba da kwarjinin da ba'a taba ganinsa tattare da dukkan wanda ya taba zuwa neman auren akhnan ba.......komai inaso ya wanzu bayan tafiyar me martaba umara kafin kuma dawowarshi".

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 31* __________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________

"An gama......ki qaddara komai ya wanzu kamar hakan". Kai mammina ta jinjina cikin izza sannan ta katse wayar.

Idanunta ta maida saman fuskarta tana sake sakin wani murmushin,a nutse takai hannunta saman fuskarta tana shafawa,wani murmushin yana sake yanke mata.

Tana matuqar kula da kanta da fatarta gami da jikinta gaba daya,wannan ya sanya zai wahala ka iya qididdige shekarunta kai tsaye. Dukkanin duniyarta a yau wani dadi take mata,komai ya hau saiti,komai kuma yana tafiya a hannunta yadda takeso.

DAUKAN FANSA yana mata matuqar dadin da yake wanzar da zuciyarta cikin wani irin nishadi da aminci........ballantana fansa irin wannan,fansar da take da tabbacin ba'a taba wani abu a tarihin rayuwarta da take buqatar fansa a kansa ba irin FANSAR SAFEENA.

A nutse ta miqe,ta dora alkyabba mara nauyi saman rigar jikinta daidai sanda idanunta ya sauka akan jewelry organizer dinta. Haka kawai ta samu kanta da zubawa gurin idanu tana jin sauyin bugun zuciyarta,shakka da kuma kokwanto suna ratsata a hankali,taji kamar wani abu yana fincikar hankalinta a kansa,sai ta miqa hannu ta danna wani madanni,take ya bude ya kuma ware dukka fadinsa dake dauke da sassa sassa.

Akan abun hannun idanunta suka fara sauka,kallon daya saukar mata da wasu yani mabanbamta da har sai daya kaita ga miqa hannu ta daukeshi tana juyashi cikin hannunta.

Abune me matuqar tsada da daraja a gurinta,bawai kuma don daga gurin wanda ya fito ba tun asalinsa,sannan bawai don tsadar da yake dashi ba kasancewarsa d'anyan narkakken gold ba......aah,saidai kasancewarsa me dauki da wani tarihi me nauyi a gurinta.

Iska taja me yawa a hunhunta,zuciyarta na jin qin aminta da zamansa a gurin haka kawai,zamansa a wajen takejin baiyi mata ba a daidai wannan lokacin da take da tarin zarge zarge da ayoyin tambayoyi akan kusan kowa da kowa ma,sai ta taka kawai a hankali tana wucewa zuwa ainihin kebantaccen closet dinta,ta wuce kai tsaye ga ajiyayyen safe dinta,ta jawoshi ta saka abun a ciki ta rufe tana jin ya samu amintaccen gurin zama sama da dressing table dinta,sannan ta fara takawa tana ficewa a daga walk-in closet din.

Dab da zata fita a gurin jikinta ya saukar mata da wani irin yanayi. Saita tsaya cak,ta waiwaya tana sake qarewa gurin kallo. Mintuna aqalla uku ta shafe a haka tana duban gurin. Batasan me yasa takeji a jikinta kamar akwai wani abu daya taba gun,kamar akwai wani daya kusanci gurin?,amma ko daya bataga wani abu daya sauya gurin ba,daidai da qananun alamomi data sanya da ba wanda zai gane alama ce ajiyayya da zata iya fahimtar da ita an taba mata wani abun,an shiga gonarta ko an wuce iyakarta,dukka suna nan a muhallinsu,ba ko daya daya fadi ko ya canza yanayi.

Siririn tsaki ta saki,ta juya tana qarasa ficewa,cikin ranta da kanta tana tuhumar kanta da kanta. Me yasa haka kawai,a sanda take buqatar nutsuwa irin wannan tunanin da shakka suke saukar mata?. Bayan tayi imanin ba mutum ba,ko aljani zai masa matuqar wahalar tsallake dukka matakan tsaron data sanyawa sassanta ya isa ga wannan closet din,kome girman tsafi asiri ko siddabarun da yake taqama dashi.

"Nutsuwa kike buqata zaituna" Ta gayawa kanta da kanta,sai taja iskar ta kuma fesar a waje,abinda ya bata qanqanuwar nutsuwar da take da buqata.

Da dukkan izzarta take takawa d'ai d'ai cikin gidan,tari bayi da hadimai suna darewa suna bata hanya gami da miqa gaisuwa,gaisuwar da hadimanta ne ke amsata,saidai takan bisu da murmushi kadan kadan don tabbatar da yabon KIRKI da sukeyi mata. Duk da Kai tsaye hankalinta yana ga isa sassan akhnan,amma kuma hakan bai hanata ganin wasu tsirarun sauye sauye ba a farfajiyar gidan,abinda yadan janye hankalinta kadan,amma ta cillashi sashen qwaqwalwarta na abubuwan da zata nazarta a nan gaba.

Ba wanda ya dakatar da ita daga wucewa kai tsaye zuwa ga main bedroom na akhnan din,yayin da hadimanta suka yiwa kansu matsaya a waiting room suna jiran dawowar uwargijiyar tasu.

*HAISAM*

Yana tsaye ne tsakiyar beeno omari salawi da abdii,hannunsa zube cikin aljihun jubah dinsa bayan ya zare rawanin kansa ya ajiyeshi gefe tun bayan shigowarsu gurin.

Idanunsa dukka ya zuba ga qunshin abun hannun dake gabansa,yana sauraren bayanin qarshe da omari yakeyi har zuwa sanda ya kammala.

"Tamam" Ya fadi a nutse yana fidda hannayensa daga aljihun jubah din nasa,sannan ya fara tattaki a nutse yana samun daya daga cikin kujerun dake kewaye da parlor din ya zauna.

"Beeno da salaana.......inason ku shirya shiga sahun masu tsaron qofofin sultane palace.......omari zaka fita a qasar nan yau da abun hannun nan.........inaso ka damqashi kai tsaye ga buba......kafin sannan ina buqatar nanay ta ganshi iya na mintina biyar kacal". Ya qarasa maganan yana fiddo takardar da abdii ya hado masa da ita wadda ya sameta yashe cikin kwandon shara na dakin.

Warwareta yayi da kyau yana duba takardar,shuru ya sake ratsa dakin,kafin a hankali wani murmushi mara zurfi ya kubce masa.

"Oromia handwriting.......definitely matar nan 'yar qasarmu ce......yarenmu ce.....kuma qabilarmu ce......."

"Amma obbo me zai hana ka bari ta fahimci kasan yaren?,ka kuma iya yaren?,hakan zai baka damar ganin reaction na fuskarta,reaction dinta kuma shine zai bayyana gaskiyarta ko akasin haka". Baisan ya miqa hannu ya ranqwashi saman kan abdii ba saboda takaici.

"Sai kayi abun arziqi saika dawo kayi na tsiya,na rasa a wanne mataki ko gurbi ya kamata na ajjiyeka......har yanzu banaji a raina zan baka gurbi a national intelligence......bansan ko matsayin me goge goge da shara ba" Ya fada yana zubewa abdii idanun nan nasa masu tsananin kwarjini girma kyau da haske.

Dariya suka dan saki,dukkaninsu suna hangen wautar abdii a wasu lokutan,amma Kai tsaye idan kace yayi gadon baiwar fikira da basira bakayi kuskure ba.

"Bakasa yare sirri bane?......a duk sanda ka tsinci kanka cikin yaren da basusan ka iyashi ba.....karka kuskura ka nuna musu ka iya wannan yaren,hakan zai baka information da security wanda qwarewarka a aiki bazai baka ba.......a cikinku akwai wanda yasan na fara jin yaren mutanen agadez?,buzaye?" Sak dukkaninsu sukayi,cike da tsananin mamakinsa.

Komai nasa na musamman ne yadda ya kasance na musamman,yana sanya aikinsa gaba da komai,yana sanya aikinsa sama da komai,yana iya koyar komai saboda aikinsa,kamar yadda yake iya barin komai din saboda aikinsa. Murmushi ya saki a nutse ganin yadda mamaki ya bayyana saman fuskarsu.

"Wanne irin aljananci ne wannan?" Omari ya fadi kai tsaye,wanda ba wanda zai iya fadin hakan dama idan ba omari din ba. Kai ya jinjina masa a nutse,sannna ya miqe yana maida cloak robe dinsa kafin ya amsa masa.

"Ka sanya tunaninka gaba da komai kafin ka fara gwada aikata komai......har yanzu inajin ban kammala cika ba,tunda ji kawai nakeyi ban iya maidawa" Ya furta maganan yana soke takardar cikin aljihunsa.

"Sanda zaka fara maidawar ma dukkaninmu bamu da labarin indai kaine.....zamu wayi gari kawai muji kana yarawa ne" Omari ya fadi cikin tuhuma,yanayin daya sanya haisam kauda kai da guntun murmushin nan saman fuskarsa,ya aza idanunsa akan salawi.

"A darennan nakeso takardun sabbin dokoki su isa hannun me wada......zuwa safiya nakeso ta game masarautar gaba daya....na riga na samu sahalewar sultane,zasu fara aiki ne nan take,kuma kowa zai hau kan saitin aikinsa a goben.......inaso ku maida hankulanku jikinku,kusa a ranku sati hudu kawai ya rage mana mubar qasar nan,kwana talatin kawai muke dashi don kammala aikinmu" Ya qarasa maganar da wannan seriousness din nasa dake qara musu qaimi.

Tare suka fita da omari a daya daga cikin motocinsa da salaana yake jansu,suka kuma ajiyeshi a sabon gurin da yake sauka a yanzu,don akwai abinda yake buqatar zuwa gida ya kebe kansa ya duba a nutse.

*MAMMINA*

Idanu ta zubawa dakin tana dubanshi ganin yadda yake a hargitse kafin ta maida dubanta kan fuskar akhnan dake tsaye tana danne danne a wayarta. Shimfidadden yanayin dake nuna kwantaccen fushi ne can qasan zuciyarta da ya bayyana sosai har saman fuskarta.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Cikin girmamawa birra ta amsa sallamar mammina din,ta ajiye bathset din data dauko da zummar sakawa cikin luggage tana zubewa qasa don kai gaisuwa ga giwar sultane din.

A taqaice ta amsawa birra,sannan ta dora da tambayar.

"Shirin meye kukeyi haka?". Qasa tayi da kanta,kafin ta bata amsa akhnan da tayi cilli da wayarta saman gado ta amsa.

" Nasa an siyamin ticket yanzu......Niamey nakeso na koma a yau......inajin komai ai ya kammala ko?,duk wani me lissafi ya cika lissafinsa a kaina" Tayi maganar dake nuna zallar fushinta cikin kalamanta.

Kadan gaban mammina taji ya fadi,don maganarta a wannan lokacin sai taji kamar da ita akhnan din take. Ta gefe daya fargabar bacin tsarinta ne ya saukar mata,bata shirya komawar akhnan Niamey yanzu ba......don komawarta Niamey yana daidai da komawarta bakin aikinta ne,wanda sam a yanzu ba wannan tsarin. Tana buqatar space koda na sati uku ne zuwa hudu......sanda aisa ta soma nisa cikin riqon qwaryar da take saka ran zata farashi cikin satin nan. Ta jima tana zurfafa hasashenta akan aisa......tana da wani quduri na daban a kanta,akwai kuma wani tunani da zuzzurfan hange da tayi a kanta.

Tuni birra ta fice don basu guri da kuma cika umarnin kaucewa daga dukkan ganawar da mammina zatayi da akhnan,wannan ya bawa mammina damar qarasawa cikin dakin tana kama hannun akhnan ta zaunar da ita.

"Me yasa wasu lokuta bakya tunani.....bakya kuma zurfafa hasashenki?" Mammina tayi maganan alamun fushi kadan yana bayyana a sautin muryarta.

"Har yanzu zuciyar sultane a tunzure take,kinaso kici gaba da abinda zaki tunzura zuciyarsa maimakon yin abinda zaki amintar dashi?" Mammina ta sake fadi wannan karon tana sassautowa da muryarta.

"Me ya rage mammina?.....me ya rage kuma?......wannan qaunar wannan kulawar sultane dukka ya tuntsirar da ita......tun daga sanda ya yaye dukka wani hijabin sirri dake tsakanina dashi gaban bagidajen malamin can.....tun daga sanda ya nunawa wancan bagidajen malamin da baisan komai ba illa allo da tawwada sirrina,ya dauki matsayina ya bashi,ya kusanta kansa dashi fiye da yadda yake kusanta kansa dani.....ya maye gurbina dana malamin can,daga qarshe ya dauki ragamar daurin aurena ya damqa a hannun mutumin da baida asali,tsintacciyar magen da bamusan daga wanne datti da daudar ya fito ba!" Tayi maganar da fushi sosai cikin idanunta fuskarta dama muryarta,don rawa muryar tata takeyi kaman yadda idanunta suke tara ruwan hawayen da zasu iya sauka kowanne lokaci.

Sosai mammina ta nutsu,ta kuma zuba mata ido tana karantar yadda abun yayi mata zafi.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 32* _________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________

"Naji zafi fiye da wannan zafin da kikaji sanda safeena ta qwace min sultane a hannuna.....sultane din da ba shine abu na farko data fara qwata a hannuna ba......naji zafi fiye da wannan zafin da kikaji sanda na samu labarin haihuwarki......naji zafi sama da wannan a sanda nake iya kallon safeena a matsayin matar sultane a sanda nake gefe cikin tarin baqinciki da qunci kuma ba abinda zan iya aikatawa a sannan......ina kanjin zafi a duk sanda na daga ido na kalleki a matsayin DIYA ga sultane,ba kuma nina haifeki ba.....inakan jin zafi a duk sanda na tsinceku keda sultane kuna sirrin da ba wanda yake iya bayyanawa saike kadai. Ya kamata ne na barki kiji wannan zafin.......ya kamata na qyaleki,amma kuma zan tayaki mu tunkudeshi saboda tanadin dana miki a gaba. Kin cancani kiji zafi sama da wannan zafin da kikeji a yanzu,kin cancani hukuncin da yafi wannan tsanani keda zuri'ar diory hamani gaba daya.

Idanunta ta janye tana maida hankalinta ga akhnan da tsananin kafiyarta da taurin kanta ya taimaka mata taketa qoqarin maida hawayen daya rantse sai ya zubo.

"Wani lokaci ina raina wayonki biftu,bakisan ba kowanne lokaci bane akecin nasara da aiwatar da komai cikin zafi ba?. A wasu lokutan saika kwanta an tattakaka anbi ta kanka kafin nasara take zuwar maka......kin sani,bazanbar komai ya tafi a haka ba,amma ya zama dole a yanzu ki siffantu da siffar macen dake shirin zama AMARYA da mijin daya zama ZABINTA" Tayi maganan tana sake zube mata duba na tsanaki.

"Kamar yaya?" Akhnan din ta tambayi mammina kai tsaye,tana kuma fatan bawai zata sanyata yin duk abubuwan al'ada da sukeyi ga amare ba har zuwa ranar aurensu.

"Da farko dole zan gargadi sheikh haisam don yasan iya matsayin da yake tunanin ya taka kada ya rudeshi......na biyu zaki gana da angonki almaz......."

"Babu buqatar hakan mammina......bana buqatar ganinsa,ya zauna a inda yake,na zauna a inda nake".

Readers Also Read

More by Huguma