L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 19
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 19: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 19. " Zaki ganshi biftu dole.....dole zaki ganshi,ko kinaso…
3,361 words
" Zaki ganshi biftu dole.....dole zaki ganshi,ko kinaso duniya ta karanci cewa almaz zabina ne ba zabinki ba?" Ta fadi da 'yar fusata a muryarta,fusatar data sanya akhnan maida hankalinta jikinta.
"Na soma gajiya da musunki biftu......na fara tunanin nan gaba kadan zaki daina yarda duk wata shawarata" Ta fada cikin bacin rai tana gwada miqewa,saidai akhnan din ta kamota abinda ya sake maidata ya zaunar da ita kenan.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Kiyi haquri" Taji muryar akhnan din ta fita da wani irin sanyi. Wani farinciki ya saukar mata,don kuwa wannan kalmar wata kalma ca da bata tunanin ko sultane yana yawan jinta a bakin akhnan din. Kalma ce da tafi kowacce kalma wuyar furtawa a bakinta baya ga kalmar INA SONKA/KI.
Muryarta ta sasasauta,saidai har yanzu bata saki fuskarta ba.
"Aure zakiyi a idanun duniya irin auren da kowacce yarinya 'yar gata takeyi,aure zakiyi da dole idan kinaso ya saje da auren gaske sai anyi dukkan wani abu da aka saba gani......indai kinaso a barki da sa'ido dabin qwaqwqwafi......a barki kiyi rayuwarki kalar wadda kika tsara kike muradi.......koma lalacewar auren 'yar sultane a zuciyarki sunansa dai BIKIN AURE,dole a komai baki akwai GIRMA a komai naki akwai MARTABA a komai naki akwai DARAJA akwai MULKI. Koda bikin binne gawa ne dole naki yasha banbam dana kowa. Biki nakeso muyi da zaya bar tarihin da bazai gogu ba,biki nakeso ayi irin wanda ba'a taba yin kwatankwacinsa ba tunda aka kafa qasar agadez......biki nakeso ayi da labarinsa zai zagaye nahiyar africa gaba daya......bikin da za'a jima ana labarinsa.......bikin da bazai goge a bakuna da zukatan al'umma ba komai tsahon zamani". Saita dakata tana gwargwada adadin yadda maganan ya shigi akhnan din.
Numfashi take saukewa a hankali,tana jin wannan girman izzar da martabar suna saukar mata. Izzar da tuntuni ina ta qara qarfinta cikin jininta da dukka fitar numfashinta.
Wadannan kyawawan blue eyes din nata ta daga tana duban mammina dasu,tana jin dukka yarda da aminci da abinda ta gaya mata.
"Me ya kamata ayi?" Murmushi mammina ta sake,tana gyara zamanta cikin jin dadi tana dubanta.
*HAISAM*
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 33*
MACE TA GARI aljannar duniyar namiji ce,tasan wannan,shi yasa koda yaushe bata gajiya da yiwa yaranta maza da mata addu'ar dacewa da aboka rayuwa,shi yasa kuma kullum hankalinta yake karkata kan saamee. Tana ganin tasan komai kan haisam,tana ganin kamar zata iya jure komai,yanayinsa attitude nasa da komai ma,to amma sai bata bari zuciyarta tayi mata zabi ba,ta barwa Allah yayi wannan zabin da duk wadda ya dace a sanda ya dace koda saamee dince.
*NOTE~Qalubale gareki uwa,kinga tun a zamanin nan,samun miji na gari,da mace ta gari yana wahala,ina ga zamanin 'ya'yanki?,tun yanzu da basu da hankali ya dace ki tsaya musu da wannan addu'ar,suma ki koya musu yinta tun basusan tsadar abinda suke roqa a gurin Allah ba. Bayan miji na gari da zai sauke mata kowanne haqqi da Allah ya dora masa,ki roqa mata personally mijin da zaiyi tarayya da ita cikin damuwarta,walwalarta da baqincikinta,samunta da rashinta,wanda Allah zai jarabceshi da tsaftatacciyar soyayyarta,soyayyar da zata sanya ya zama ABOKIN RAYUWA na gaske,MIJIBANCIN na gaske,ba wanda zai sauke iya haqqoqinsa din kawai ba kuma shikenan,can cikin rayuwarta tana jinta empty......tana jin loneliness,Alla ya datar mana dasu.*
"Ina buqatar qarin sani akan iyalin ajani" Ya furta da yaren oromo. Shuru ya ratsa tsakaninsu sannan nanay ta gyara zamanta.
"Matansa biyu ne......duk da ana rad'e rad'in ya auri wata matar a boye,wanda ba kowa ne ya santa ba,sa'annan ma ba'a kai ga tarewa ba ajalinsa ya riskeshi,so ba wanda zaice ga fuskarta ko gata,saidai wataqila cikin makusantan abokansa na qut da qut. Shahararren dan kasuwa ne na duka duniya gaba daya,harqallar kasuwancinsa tafi tsakanin sarakuna na qasashe da attajirai,don yana kawo duk wasu kaya na alfarma da zai sanya gidan sarauta ya amsa sunanshi. Matarsa ta farko yaranta biyar,hudu mata namiji guda daya ka sanshi basai na gaya maka ba,tunda shike tsaye tsahon shekarun bayan daya mallaki hankalinsa don binciko wadanda sukayi kisan gilla wa mahaifinsa. Matarsa ta biyu kuma wadda ya aureta ne shekara guda kafin a kasheshi bata haihu dashi ba kwata kwata......."
"Meye sunanta?" Haisam ya samu kansa da katse nanay,don binciken kusan yana jin dole zai biyo ta kanta itama.
"Zeenatu.......zeenatu sunanta,mahaifinta ba wani sananne bane,don baida sana'ar data wuce saida nau'ikan gahwa a qaramin shagon unguwa,saidai tana da kyau daya sanya take da tarin manema,wannan akace shine dalilin daya hanata zaman aure,don tana aure take fitowa,a qalla sai data auri maza biyar ajani ne na shida. Duk da kowa yasan ajani bai mata ba,bata kuma sonshi,amma haka ta aureshi,wannan dalilin ya sanya bayan an kasheshi uwargidansa da yaranta mata don sannan namijin bai wani girma ba tunda shine qarami sukace basu yarda da ita ba.
Anyita tafka shari'a dasu,amma daga bisani kotu ta wanketa,don bata da hannu ko masaniya. Andai samu shatin hannu da sauran abubuwa kan wanda yayi kisan,saidai duk irin nema da bincike na jami'ai sun gaza samoshi".
"Kina da masaniyar inda zan iya ganinta ita zeenatu din?". Kai nanay ta girgiza.
"Ba wanda zaice maka ga inda zeenatu take,don ana rade radin ma ta bata,shekara da shekaru ko gilmawarta ba'a sake gani ba cikin qasar nan,wasu ma na zargin uwar gidanta ki dangin ajani daketa zargin qiyayya tasa ta kashe musu dan uwa sune suka batar da ita" .
Shuru haisam yayi,yana kuma juya labarin cikin kansa. Haka kawai dan adam bazai bata ba kaman kudi.......ace rana tsaka an nemeshi an rasa?. Dan adam dinma mace me cikakken hankali wadda ta samu kaso na gado me yawa ace ta bace?.
"Amma meye haka me nauyi na ajani dake hannun motii da aka yita attempting kai masa hari?" Ajiyar zuciya me nauyi nanay ta sauke.
"A rabon gadon da aka yi ba'a taba komai na taskokin ajani ba guda biyu,mahaifinku shine amintaccensa guda daya,kuma shi daya yasan inda za'a samesu da yadda za'a sarrafa danyar dukiyar dake ciki,kama daga gold da Diamond,wasu tarin abubuwa masu darajar gaske,maganan da sukayi ta qarshe da ajani,kaman yasan ana fakon kasheshi,ya gaya masa muddin yaga ya mutu to kasheshi akayi,wadanann sirrikan dukiyar kuma yanaso ya masa alqawari bazai bayyanasu ba......zai adanasu saboda iyalinsa da d'ansa,har sai sanda komai ya bayyana kan wa da ya kasheshi,idan har ba haka ba,idan har ya damqa dukiyar ga iyalinsa,to tabbas za'a qarar dasu ne daga doron duniya,za'a yita binsu ana kashesu daya bayan daya saboda wannan dukiyar......a daren munyi magana da motii hankalinsa a tashe,ya bawa ajani shawarar ya qara yawan masu tsaronsa,ya kuna nema hukumar tsaro ta shiga cikin sahun masu bashi kariya,amma sai ya yiwa motii murmushi kawai
"Idan ajali yazo ba wata kariya da zata iya kareka......saidai fatan cikawa da imani" A safiyar ranar ne zuwa azahar kuma labarin kisan gillar da akayi masa a gidan gonarsa ya karade qasar nan dama maqwaftan qasashe" Nanay ta dakata tana tuna girman tashin hankalin da qasar ta fuskanta a lokacin,saboda ajani Ahmed kamar amintacce ne daga wata qasar da Ethiopia ta maida dan qasarta halak malak saboda alfanu na kudaden shiga da take samu ta sanadin kasuwancinsa.
Shuru haisam din yayi shima,kafin ya sake daga kanshi yana dubanta.
"Sanda aka fara kaiwa motii farmakin farko......zenatu tana Ethiopia?". Kai Nanay ta girgiza.
" Takai shekara biyu ko uku a sannan bata nan". Lumshe idanunsa yayi,wani dan qaramin murmushi yana subuce masa,tunaninsa yana hada wasu abubuwa kafin ya bude idonsa.
"Inaji a jikina zeenatu tana raye......inaji kuma a jikina akwai mafakar data samu take shirya abubuwa wa qasarmu cikin kwanciyar hankali da nutsuwa" Yayi furucin da nutsuwarsa.
"Me kake cewa muhammad?" Nanay ta tambaya da mamaki.
"Ba komai nanay,kici gaba da yimin addu'a,amma inaso na sanya motii alfahari me yawa dani,zan kare masa qasarsa da rayukan al'ummarsa in sha Allah" Kai ta gyada a hankali.
"Allah ya baka nasara,ya doraka akan kowa da komai".
"Ameen nanay" Dan shuru tayi sai kuma tace.
"Kana kiran saamee koda bayan lokaci ne kuwa kuna gaisawa?". Idanu yadan zubawa Nanay kadan yana karantarta kafin yace.
" Wani abu ya faru ne?" Kai nanay ta girgiza,tana jin sai yaushe hankalinsa zaikai kai ne?.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Kawai naga ta damu da rashin wanzuwarka a gida,harma fiye da 'yan uwanka" Dan qaramin murmushi ya sauke
"Idan haka kike buqata nanay zan dinga kira in sha Allah". Kai ta girgiza itama tana murmushi.
"Banda matsawa kai,a duk sanda dama ta bayar da hakan,kaji kuma zaka iya kiran"
"Na gode" Ya fada da girmamawa da kuma tarin qauna.
"Omari zaizo,zai kawo miki wani saqo ki duba ko zaki iya tuna wani abu akai" Kai ta jinjina a nutse
"Allahumma bareek" Ta fada tana dafa kanta wanda hakan yana nufin tanajin kamar ta dafa kan haisam dinne direct,kansa ya qansqantar yana amsa mata,tamkar yadda yakeyi a gabanta.
Ko bayan gama wayar tasu wayarshi ya dauka yana bude hotunan da yasa abdii ya tura masa. Da kwanukan abincin ya fara,komai da komai irin na yaren oromo,best dishes da Oromian people suke dashi,komai kamar a qasar. Ajiyar zuciya ya saki yana sake jin lallai AKWAI WATA A QASA,sannan ya koma ga hoton frame din da abdii din dai ya turo masa.
A idanun me kallonsa,da kuma idanun wadanda suka dauki shekaru suna rayuwa tare da ita. Tura hoton yayi cikin sirrintacciyar system dinsa,sannan ya aikashi zuwa ga sashen bincike na can qasar yayi dan gajeran bayani a qasan hoton.
★★Tsaye take cikin qawataccen lambun nata da takan wanzu a cikine a duk sanda take cikin nishadi da walwala.irin wannan. Yanayin yana taimaka mata qwarai,yana sake inganta mata nishadinta.
Tun bayan da sultane ya fita zuwa filin tashi da saukar jiragen sama na agadez,zama kadan tayi taga mabuqata sannan ta kebe kanta cikin qasaitaccen lambun nata.
Tun tsakanin jiya zuwa yau din bata bawa kanta sukuni ba,shirye shirye kawai takeyi na irin uwar dukiyar da za'a narkar wajen tsarawa akhnan din komai na aure a zahiri,yayin da a badini aikin ya zame mata biyu,shirya almaz da kuma shirya dukiyar auren da take sanya ran za'a gabatar da ita bayan almaz yazo sun gana da akhnan kamar yadda al'ada ta tanadar. Lefen auren da za'a kawo da kuma yadda bikin zai kasance,wanda ta tsara gudanar da komai bayan daurin aure gudun wanzuwa ko gilmawar wata matsala,kuma ta tsara komai ya kasance a haka ne don kashe bakin tsanya.
Duk da wadannan damarmakin data samu tana jin wani susa cikin ranta idan ta tuna yadda sultane yake sake jaddadawa haisam kula da nauye nauyen da yake ganin da haisam din kawai suka dace,saidai wani sashe na zuciyarta yana bata tabbacin bai isa ya hana faruwar komai ba,bai kuma isa ya sanya komai ya faru ba. Ta gani sun kebe da sultane a gurin,sunyi maganganun da har yanzu suke gilmamata da tsananin kwadayin son jin meye da meye sultane ya gayawa haisam din a kebe?.
A yanzun da take gurin,tana waya da amintacciyarta ne dake mata siyayya da order na duka wasu kayan qyale qyalen alfarma na buqatar rayuwa,daidai lokacin data hangi tahowar yalwa da sassarfa hannunta dauke da wata takarda fara.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 34*
Idanunta akan yalwa,amma hankalinta yana kan wayar da takeyi,saidai zuwan yalwan bai hanata yin wayarta ba,har zuwa sanda ta kammala wayar da cewa.
"Ki lissafa dukka adadin da kudin ya kama,zan tura miki,a tsara komai yadda ya dace,yadda kuma zai qayatar".
"An gama ranki ya dade" Ta amsa mata cikin girmamawa sannan ta yanke wayar tana jiyeta saman doguwar takardar daje gabanta data sanya sabeera tayi list din komai.
"Ya ake ciki?" Ta tambayi yalwa tana dubanta a tsanake. Kasa magana yalwa din tayi,sai miqa mata doguwar takardar tayi tana komawa mazauninta ta zauna. Kamar ba zata karba ba,sai ta sanya hannu a qasaice ta karba,ta bude takardar tana dubawa cikin tattara hankalinta guri daya.
saidai tun batayi nisa ba hankalin nata ya dagu sosai,ta tsuke girarta tana duban jerin sabbin dokokin masarautar AGADEZ.
Tarin mamaki ne ya soma yankowa yana lullubeta,wasu irin tsare tsare da dokokin da tunda aka kafa masarautar bata taba ganin shigensu ba. A fusace ta dangwarar da takardar,ta daga idanunta cikin wani irin yanayi na fusata tana duban yalwa.
"Uban waye ya zartar da sabbin dokoki da hukunce hukunce irin wannan,ba masaniyata?,ba yarjewata?,ba kuma neman ta baki na kaman yadda aka saba?". Qasa yalwa tayi da kanta,tana iya hango kwantaccen fushi saman fuskar mammina din,wani irin wutar fushi data jima bataga kamarta ba.
"Allah ya huci zuciyarki,ya baki yawan rai.....sheikh muhammad haisam ne" Yalwa ta fadi cikin kwantar da murya.
Madaukakin mamaki da kuma fargaba ne suka hadu gaba daya suka cakude mata,tayi ciki ciki da idanunta tana duban yalwa da wani irin tsini da kaifi cikin idanunta.
"Sheikh muhammad haisam?" Ta maimaita sunan kamar yau ne rana ta farko data taba jin sunan. Kai ta girgiza sosai
"Qwarai kuwa.... Don dama a taron da aka gabatar jiya an bada sanarwar samun sabbin dokoki cikin gidan nan saboda yanayi na tsaro,da kuma qarin sabbin masu tsaron cikin gida da kuma kowacce qofa" .
Wani irin zazzafan gumi taji yana karyo mata tashin farko. Kokwanto da kuma zargi me girma yana samun sabon mazauni a ranta game dashi. Ta yaya zai halicci wani tarnaqi a daidai sanda take ganin akwai space me girma da komai zai faru ya qare kafin dawowar sultane?. Sati biyun da sultane zai fara yi a france,da wata daya da zaiyi a madeena tana ganin sun isa ta aiwatar da komai. Tana sanya ran a sanda zaya dawo ma ya samu akhnan din da tsarabar jikansa.
Wanne irin mutum ne shi da hankalinsa zaikai ga shiryawa da tsara abubuwa irin wadannan a daidai wannan lokacin?. Hannu ta sanya ta sake dauko takardar tana sake dubata daga farkonta zuwa qarshe,saidai still ta kasa samun nutsuwa jira takai ga rubutun qarshe dake qasan takardar,saboda tunaninta dake yamutsewa.
Jikin kowacce doka akwai qalubale me tarin yawa.......a jikin kowacce doka akwai tasgaro da matsaloli da zasu iya cin karo da kowanne muradi nata.
"Me kike tsoro?,me kuma kike jira da zaki zauna yaro qarami irin wannan ya fara wasa da hankalinki?.......WAYESHI?". Tambayar da tayi mata tsaiwar mashi kenan cikin tsakiyar zuciyarta,yayin da zuciyarta ta kasu sassa daban daban akan haisam.
Tun daga sanda ta fara ganinsa zuwa yau takeji wani abu na daban a kansa wanda bata taba jin irinsa akan kowanne mutum ba........wani yanayi hali da dabi'u take hanga tattare dashi da suka sha banban dana kowacce baqo dake zaune yana rayuwa cikin gidan......me yasa lokaci daya wani baqo zata dinga jinsa na daban cikin gidan?,me yasa zai samu wani irin power da koda wadanda suka shekara ashirin basu da ita?.
"Ki tura saqona izuwa sashensa......a shaida masa kome yakeyi yazo inason ganinsa!.....sannan a nemomin tamim..... Amma zan ganshi ne bayan na gama ganawa da wancan yaron"
"An gama.....cikar muradanki sune farincikinmu" Ta fada tana miqewa da dukka karsashinta don cika umarninta.
"Yalwa" Ta kirata a qasaice ba tare data kalleta ba,saita amsa mata a ladabce.
"Raina yana tsananin bace,banason in zauna jira,don banaso yazo ya ruskeni a sanda zuciyata ta fara sassauta......sa'annan daga yau zuwa wayewar garin gobe.....kowa dake cikin gidannan inaso yaji a jikinsa,yasan kuma MIJIN GIMBIYA AKHNAN zaizo don ganawa da ita,inaso ayi gagarumin shirin da ba'a taba yiwa mazajen baya ba a kanta"
"An gama......an aiwatar kamar yadda kika ce ranki ya dade" Saita juya da sassarfa tana barin shiyyar.
Idanunta ta runtse tana jin zafi a ranta,zuciyarta na cika da d'ar d'ar......gabanta na wani irin bahaguwar faduwa a duk sanda zuciyarta ta raya mata. KADA KOWANNE GIRMAN IKO YA KOMA HANNUNSA.
Duk da bata fita cikin mutane ba taba kebance a nan ita kadai,amma wani irin kunya ce take saukar mata. Tana ji kamar ma kowa ya soma fahimtar abubuwa sun fara fita daga ikonta. Abubuwa da yawa cikin tsukin nan suna fara barin da'irarta......saboda wani malami da baisan kan duniya ba ballanta girma da qarfin iko na gidan sarauta ba?.
Da qyar ta yiwa kanta saiti ta koma ta zauna tana jiran isowarsa,bataso yazo ya same ta a tsaye ballantana har ya fahimci daga mata hankali lamarin yayi,ta fesar da iska daga bakinta tana duban hanyar cike da qaguwa.
_____Tun daga nesa kana iya hangen yadda farar jubah din jikinsa ta zame masa wani irin ado me daukan hankali,hular daya sanya saman kansa ga rufe tsakiyar kanne kawai saboda laushi da santsin sumarsa.
Qafarsa daya kan daya ya dorata,hannunsa dauke da littafin fataawan nisaaa yana dubawa a hankali. Zaman ya masa dadi,duk da cewa ya zauna dinne don yayi charge din kansa da shurunsa. Ba kasafai ya fiya son hayaniya ba,yana ji tana hawan masa kaine a yawancin lokuta. Ko a yanzu abdii na zaune a gefansa,kuma tun dazun abdii din ke satar kallonsa. Yasan magana ce a bakinsa,amma shurunsa da tsumewarsa suka sanya abdii jan baki yayi gum.
Duka duka bai rufe awa daya da kammala zama tsakaninsa da wazirin sultane ba,wanda a yanzu yake a mazaunin mataimakinsa cikin fadar. Ya fahimci akwai abubuwa masu yawa,ya kuma karanci matsaloli ne masu yawa lullube da masarautar sama da katangun da masarautar ke dasu.
A nutse ya qaraso cikin girmamawa. Yaron gidansa da aka sake bashi saddam ya qaraso cikin girmamawa yana rusunawa.
"Barka da warhaka" Saddam din ya furta yana rusunawa cikin girmamawa tamkar zaikai har qasa,saidai bai qarasa kaiwa qasan ba saboda tuni haisam din ya hanasu yi masa haka.
A nutse ya sauke qafarsa daya qasa yana rufe littafin hannunsa,gami da sanya yatsa daya a tsakiya. Da kai ya amsawa sadam yana lumshe idanu gami da budesu,can cikin kansa yana jin hayaniya ta soma masa yawa. Yana shawarar qarshen satin ya wuce personal gidansa koda kwana daya ne yayi,ya gaji da yadda kwanyarsa take tattaro dukka matsalolin masarautar tana shirin dora masa,duk da yadda yake qoqarin barranta kansa da dukkan wata damuwa da ba ta aikinsa ba.
"Sarkin gida ne ya iso da saqon kira daga giwa mammina.......tana buqatar ganinka yanzu yanzu" Kadan ya zubawa saddam idanu,yayin da abdii ya saki abinda yakeyi ya zubawa saddam din idanu shima.
Har cikin rai da zuciyarsa yana mamakin yadda suke ma haisam din karan tsaye,yadda suke isar masa da umarni?,amma wani lokaci idan ya tuna HAR YANZU BASUSAN WAYESHI BA sai yaji zuciyarsa ta sassauta,ba kuma hakan yana hanashi jin haushi ba gami da jin kamar ya sanar musu waye haisam din da suke rayuwa dashi?,saidai koda yaushe idanun haisam din dama kallonsa a kansa na gargadi ne da tuna masa doka da qa'idar da yake kai.
Wani lokaci yakan cilla tunaninsa baya,yakan tuna irin girma da nauyin matsayin haisam din cikin Ethiopia,amma gashi yau cikin qasar agadez ya zabi yayi rayuwa a matsayin wani gama garin malami ba tare da kowa yasan nasa girman matsayin ba.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Idanunsa ya sauke daga kan fuskar sadam yana dan sakin boyayyen murmushi. Hasashensa da dukka zarge zargensa sun tabbata,tarko ne ya d'ana kuma ya kamata,wannan kiran ko wani motsi daga gareta yake jira gashi kuma ta motsa din,iya haka kawai ya bashi tabbaci.