Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 20

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 20

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 20: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 20. Saidai kuma tazo a gabar da 'yan miskilancin nasa suka…

3,265 words

Saidai kuma tazo a gabar da 'yan miskilancin nasa suka motsa,real version dinsa na introvert ya soma aikinsa a jikinsa,don haka ya maida bayansa jikin kujera yayi relax yana amsa masa.

"Naji,na kuma karbi kiranta,zan kuma isketa,amma ba yanzu yanzu ba,akwai qananun abubuwa da nakeso na kammala". Cikin matsanancin mamaki da kuma tsoro sadam ya daga kansa yana duban haisam din. Karon farko!.....a karon farko giwa ta kira wani yana sanar mata bazai samu daman amsa kiranta ba har sai a sanda shi hakan yayi masa?. Harara kawai abdii yake zabgawa sadam ganin yadda ya qame a gurin,da alama amsar haisam din ke tabashi,inda yasan girman wanda ke a gaban nasa wannan sai yafi girgiza hankalinsa akan amsar da aka bawa uwar dakin gidan gaba daya.

Shurun da haisam yaji ya sanya ya zare littafin daga fuskarsa ya zube idanunsa akan sadam yana kuma tambayar lafiya?,da idanunsa kawai ba tare da ya buda bakinsa ba.

Wani abu me tauri sadam ya hadiye maimakon tuni da yakeso ya yiwa haisam akan wace giwa? Da kuma irin girman matsayinta a agadez dama nijer gaba daya. Wani mugun kwarjini haisam din yayi masa,har kwarjinin dake cikin idanunsa suka danne girman mamaki da kuma girman matsayin zaituna dake gilmawa cikin zuciyarsa,sai ya miqe a hankali yana juyawa,cikin ransa dauke da zulumin yadda zaya isar da saqon ga sarkin gida daya tabbatar zai gayawa yalwa ne ba tare da shi ya kasance mai laifi ba.

"Obbo" Abdii ya kira sunan haisam a hankali.

"Ya akayi?" Kawai yace dashi ba tare daya dauke idanunsa daga kan littafin ba.

"Baikai lokacin da zasusan naka matsayin ba da kuma waye kai?" Shuru haisam din yayi,har abdii ya fidda ran amsawarsa,sai kuma ya zame littafin yana duban abdii da dukka idanun nan nasa masu tsananin kwarjini.

"Banzo nan na zauna na rayu dasu don nuna musu girman matsayina koni waye ba......nazo ne don cimma nasara.....nasarata nake nema bawai jaddada matsayi ba". Shuru abdii yayi,yana duban sanda haisam din ya miqe yana ajiye littafin

" Ka shiga dashi ciki......lokacin sallah saura mintuna kadan,kayi alwala zamu wuce masallaci,sannan ka shaidawa salaana,gobe da dare yazo ya daukeni a hanya.....zanje gida" Dan dubansa kadan abdii yayi sanda yake tattare litattafan,daga yadda yayi maganar kamar ya gaji da komai ma,sai ya amsa masa yana dauke sauran takardun ya fara wucewa ciki.

Parlor din farko ta dawo ta zauna,muhallin da hadimanta suka fiya kai kawo a cikinsa. Tanaso a yau ta sauke masa wani kaso mafi girma cikin izza da girman da yake tunani ya samu,tanason ta rage masa kaifin abinda yakeji a kansa idan ma har wannan ya soma tasiri a kansa. Ta zabi tayi hakanne gaban hadimanta mata don yafijin kunya,yasan kuma shi din ba kowan kowa bane,ba kuma komai bane.

Wayarta ta ajiye gefe tana duban yalwa sanda take shigowa Parlour din,daidai sanda hadimanta uku ke aikin shirya mata gabanta da kayan marmari dana motsa baki duk da bata buqaci hakan ba,amma ta maida musu shi al'ada saboda nuna cikar izzarta.

"Ina fata kin sanar dashi saqona.....don bani da lokacin zaman jira,ina da abubuwan yi da yawa a gabana" Ta fada cikin zaquwa da son isowar tasa,saidai tana qoqarin binne hakan da izzarta.

"Kiyimin aikin gafara,amma yace bazai samu isowa yanzu ba......akwai qananun abubuwa da yakeso ya kammala". Ba hadiman dake kai kawo da masu shirya mata kayan maqulashe a gabanta kadai bane suka kadu da maganan ba......hatta da wadanda ke nesa kadan da gurin saida hakan ya nuna jikkuna da fuskokinsu,don daya daga cikinsu saida apple din da take qoqarin yankawa ta subuce a hannunta.

Mammina tabi apple din dake gangarawa gefe da kallo tamkar tana kallon faduwarta da kuma gangarewar mutuncinta da tsiyayewarsa a idanun duk wani wanda ke qasanta.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 35*

Mammina tabi apple din dake gangarawa gefe da kallo tamkar tana kallon faduwarta da kuma gangarewar mutuncinta da tsiyayewarsa a idanun duk wani wanda ke qasanta.

Ta tabbatar apple din ta fadi ne bawai don abun yazo bane a al'adance yadda aka saba......ta tsinkayi dalilin faruwar hakan da kallon data yiwa idanun kowaccensu. Wani irin abu me ciwo yana sukar mata zuciya ta maida dubanta ga fuskar yalwa.

"Hukunci ya shafeki.......ta yadda nan gaba zaki san yadda zaki dinga isar da saqonnin magana kunnuwan zaituna.....dole ki koyi ladabin isar da saqo yalwa.......ki tashi ki nemi tamim kice ya tabbatar ya kawomin sheikh gaba nan da mintuna talatin.......a gaya masa bijirewa kirana bazai haifar masa da d'a me ido ba,bijirewa kirana kuma yana daidai da qarewar kwanakin zamansa cikin masarautar nan". Gaba daya jikin yalwa kama rawa yayi,tsananin tashin hankali yana saukar mata,abinda taketa tsoro kenan,wannan ya sanya ta dauki kusan mintuna goma tana juya da sigar da zata isar mata da saqon,don amsarsa ta gigitata fiye da yadda zaitunan ta gigita. Dole ta tashi,don bata bata damar yin magana ba,idan kuwa har ta sake tayi tayi imanin qaruwar laifi da kuma hukunci ne a kanta,saita juya ta sauka tana fita a gurin da sassarfa.

A nutse ya kammala alwalarsa,ya kuma yi taku biyu yana bari muhallin da aka gewaye a farfajiyar tasa saboda alwala irin haka. Tattausan handkerchief ya zaro daga aljihunsa yana rage lemar hannuwansa dake dauke da gargasa,wanda hannun jubah din jikinsa yana tattare ne har saman gwiwar hannunsa dab da dantsensa.

Ba alamun takun takalma saboda gurin shimfide yake da lafiyayyar grass carpet.......amma cikin jikinsa yakejin kamar akwai wanda idanunsa ke kansa,kamar akwai wanda ke tahowa nan inda yake.

A nutse ya cira idanunsa yana duban shiyyar da yakejin motsin takun na tunkarosa,sai ya zube idanun nasa gaba daya akan tamim dake takowa da wani irin karsashi da cikakken kuzarin dake nuna da dukka lafiyarsa yake isowa gareshi.

Tun daga saman kansa zuwa qafafunsa wani irin abu me qarfin gaske ya ratsashi,wanda ya fito kai tsaye daga idanun haisam zuwa nashi idanun. Samun qafafunsa yayi da yin laushi,kuzarin daya shigo dashi gurin da zummar tasa haisam din a gaba har zuwa gaban mammina sai ya nemeshi ya rasa. Sai haisam din ya zare idanun nasa cikin nutsuwar nan tasa yana sake hannun rigarsa a hankali. Ya karanci komai dake cikin idanunsa,ya kuma karanci da yanayin da ya tunkaroshi,saidai ya sani.....koda wanda yafi tamim hadari ne.....koda wanda yafi tamim jin power ne ba abinda zai iyayi a kansa. (Akwai addu'o'in da muddin suka ratsa jikinka ba wani abu dake karyaka sai qarfin ikon Allah.....tsananin ambaton Allah yana bada wannan kariyar,ba sihiri bane,ba kuma tsafi bane).

"Barka da yammaci" Tamim ya samu bakinsa da furtawa

"Kana lafiya?" Kawai ya amsa masa gaisuwar da tambaya

"Lafiya qalau alhamdulillah......" Sai ya danyi shuru sannan ya tattara dukka jarumtarsa.

"Saqo ne daga uwar gida giwa......tace na shaida maka,mafi girman kuskuren da zaka aikata a rayuwarka shine ka bijirewa kiranta........yin hakan daidai yake da kawo qarshen zamanka cikin gidan nan dama yankin agadez gaba daya.......ta umarceni dana shaida maka cewa,kayi gaggawar amsa kiranta,ka ajiye dukkan abinda kakeyi ka sameta a inda ta buqata cikin mintunan da basu haura biyar ba". Yakai qarshen zancan yana zubawa haisam idanu don ganin iya adadin tasirin da maganar tayi masa. Saidai baiga komai tattare da haisam din ba,baiga sauyin nutsuwa ko kadan a tare dashi ba,hasalima wani tattausan murmushi yaga ya saki,sannan a nutse ya daga idanun nan dakewa tamim wani irin tasiri ya dubeshi.

"Ka shaida mata ka gayamin,kuma naji......zan amsa kiranta idan na kammala uzurin gabana kaman yadda na fadi da farko" Abinda ya fadiwa tamim kenan a nutse,sannan ya fara zura takalmansa a dogayen fararen qafafunsa ya soma takawa a nutse yana barin gurin.

Da kallo kawai tamim ya bishi yana jin wani irin madaukakin mamaki yana ratsashi. A karon farko,a kuma tarihin mammina......a tarihin rayuwarta kaf cikin agadez an samu wanda ya tsaya ja in ja da umarnin mammina giwar agadez.

Har wani irin tashi tsigar jikin tamim takeyi,don yana auna irin girman hukuncin da mammina din zata sanya ayi masa. Yana hangen irin baqar azaba da baqin hukuncin da zai fuskanta daga gurinta,yana tausayin yadda daukakar da sultane yayi masa ya rudeshi.....shi kansa a yanzun da yake takawa don isarwa da mammina saqon abinda ya fada cike yake da fargabar yadda zata karbi bayanin.

"Fadi abinda ya gaya maka kai tsaye,ban kuma lamunce ko boye ko ka sauya koda harafi daya cikin zantukansa ba" Ta fada tana jin jikinta yana tsuma saboda tsananin mamaki da bacin ran daya shayar da ita.

Ajiyar zuciyar samun sassauci tamim ya saki. Wannan damar data bashin sai ya zamana kamar sassauci a tare dashi,don haka bai boye din ba,ya fadi ya kuma dora da fadin.

"Ya cancanci ya fuskanci kalar hukuncin da wani a yankin nan da gidan nan bai taba ganin irinsa ba......saboda me sha'awar gwada koda irin hakan ya kiyaye" Tamim din ya fadi zuciyarsa cike da hassada da kishin haisam. Guraben da ya samu a gurin sultane da morsa.....gurabe ne da matsayin daya jima ya shafe lokaci me tsaho yana nemansu bai samu ba. Wasu matsayine da suka kasance qarshen mafarkinsa a kowacce rana,amma rana tsaka an samu wanda ya samu wannan gurbin a taqaitaccen lokacin da idan aka kwatanta da nasa shekarun daya kwashe daidai suke da qiftawar idanu.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Shi yake da ikon zabar lokacin amsa kiran masarauta?"

"Tabbas.....yace zaizo idan ya samu sararin hakan bayan kammala uzurorinsa". Kai take sake jinjinawa cike da wani tarin mamakin.

"Zaizo a wani lokaci?,idan ya samu sarari" Ta sake maimaita maganar cikin jin wani abu yana girgiza girmanta. Kai ta jijjiga da qarfi sannan ta,waiwaya ga tamin "Tashi kaje.......ka qarasa aikinka......inaso almaz a gobe ya fito a cikakken mutum......inaso almaz a gobe ya fito da fitar da yanayin da zai sace zuciyar akhnan lokaci daya,banaso mu rasa wannan damar......." Ta fadi tana kauda tattauna zancan haisam a tsakaninta da tamim,duk da ita daya ce tasan abinda takeji,amma batason abinda zai dauke hankalin tamim daga shirin zuwan almaz a gobe.

Kai tamim din ya girgiza a hankali,yana jin zallae rashin adalcin da ake shirin gwada masa. Ya kwantanta buda abinda ke cikin baki da zuciyarsa,amma a duk sanda ya zauna gaban zaituna da zummar fadin irin tukuicin da yake buqata daga hannunta na bautar shekara da shekaru sai yaji ya kasa,sai yaji ya gaza.......amma a yanzun da ake shirin sanya almaz gaba dashi......ake shirin sanya almaz gaban buqatarsa,sai yakejin kamar wani abune da zuciyarsa ba zata iya jura ba.

A nutse yayi sallarsa ya gama,ya kuma yi addu'o'insa,wanda yana shafasu kira ya shigo wayarsa. Baikai ga ciro wayar ba,wadda ba ringing take bayarwa ba ba kuma vibration ba,wata alama ce da shi daya yake gane shigowar kira ya fahimci waye yake kiran. Sanda ya daga wayar muma qaramin murmushi ya subuce masa. Maleek ne,sai ya taba na'urar kunnensa ya maida wayar aljihunsa ya miqe yana yiwa maleek cikakkiyar sallama,baya amsa waya a masallaci saboda girmama muhallin da kuma girmama wanda ake bautawa a gurin.

Yana amsa wayar a nutse yana bin hanyar da zata sadashi da sassan mammina. Ya shirya tunkararta ne dama bayan yayi sallah,bai shirya zuwa gareta ba a kiranta na farko.

Hankalinsa yana ga yanayin yadda gidan ya fara daukan saiti da sabbin dokokin da tuni suka karade gidan,suka kuma ratsa kowanne bangare na gidan,suka isa hannun kowanne hadimi bawa da wanda keda alhakin tsaro na gidan.

Duk inda ya gilma ko ya taka qafarsa gaisuwar girmamawa ce take biyo baya,saboda kowa na cikin gidan yana qoqarin ganin ya cika umarni da burin sultane na daukar haisam tamkar dan cikinsa.

____kyakkyawar fuskarta shimfide take da wani irin yanayi dake cike da miskilanci,rashin walwala da kuma takurar da takeji tun daga zuciyarta harma da ilahirin rayuwarta gaba daya. Saidai duk da hakan ba zaka rasa hangen wannan sassanyan kyan a tattare da ita ba sanda take saukowa daga cikin motar data kasance mallakinta,bayan ta raka aisa ta tashi zuwa Niamey ta filin sauka da tashin jiragen sama dake agadez din.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 36*

Kamar kowanne lokaci hadimanta guda biyar din dukka suka kasance tare da ita cikin hidimarta,birra na cire sauran diguwar rigarta data rage a cikin mota,buhaina na gyara mata lullubin matsakaicin mayafin dake jikinta,bushira na qoqarin rufe murfin motar,yayin da barratu ke clearing mata hanya. Wani abu guda da a kullum yasa take sake jin jinin sarauta da izza cikin kanta da jikinta,yake kuma qara mata nishadi da jin dadin irin tsatson data fito.

Saidai a yau din wannan zuciyar tasha banban da ko yaushe,wannan walwalar da nishadin da take samu can qasan zuciyarta a yanzun babu shi ko kadan a tare da ita,zuciyar cike take da rudani,tana jinta a quntace tamkar wanda aka sanya a wani saqo daban aka killaceta.

Shehnaz na daga bayanta tana amsa wayar jamaal a nutse,ba wani daga murya ko hayaniya,wannan zai sanya daqyar ka iya jin abinda take fada.

A yanayi irin wannan baushin shehnaz da aisa ke kamata. Sunayi kaman basusan ciwo da dadin rayuwarsu ba?. Namiji ne kawai halittar da zai iya daga hankalin mace,ya sanyata cikin tsananin damuwar da zata iya qare rayuwarta a ciki,amma a hakan dukka sun runtse idanunsu daga ganin kowanne aibu nasu?.

Misali me sauqi a kanta,bata shimfida hannayenta ta karbi kowanne namiji ba......bata marabci kowanne d'a namiji cikin rayuwarta ba.....amma duk da hakan gigita rayuwarta suke shirin yi?.

Ranar gobe tana lissafata cikin mafiya munin ranaku a rayuwarta da bata taba zuwa mata ba. Wata rana da bata taba lissafinta cikin kwanakinta ba na duniya kaf,koda kuwa zatazo bata lissafa zuwanta a nan kurkusa har haka,ta yaya zata manta da MORSA SAFIYYA cikin rayuwarta ne?.

Wani nauyi takeji a qirjinta sosai idan ta tuna qalubale ne yake tunkarota ta kowacce fuska. Mammina ce kawai qarfinta......banda tana da mammina bata da tabbacin ina rayuwa zata kaita.

Wani siririn iska ta fitar daga bakinta.......ba abunda ke sanyata cikin jin qasqanci idan ta tuna waliccin aurenta a hannun waye ya rataya a yanzu?...... MALAMI......BAQON MALAMI.......TSINTACCIYAR MAGE!. Duk da irin tarin darajar da take dashi......tarin dangi da ahalin da zasu iya aurar da ita?......amma sultane ya zabi horar da ita ta hanyar damqa waliccinta a hannun wanda ko cikakken asali bayi dashi?.

Idanunta ta daga a hankali sanda tunaninta ya kawo wannan gabar don yanke hukuncin sassanta zata nufa ko zata shiga daya daga cikin guraren dake bats relief cikin gidan a duk sanda ta shiga rudani irin wannan?. A daidai lokacin ne kuma idanunta suka sauka a kansa,wanda da saukar nata idanun shima ya daga manyan fararen idanunsa suka sauka saman fuskarta dake da wani irin kwantaccen kyau......kyan daya bayyana tarwai cikin dan qaramin hasken ranar daya haske farfajiyar ya kuma nuna ainihin kalar qwayar idanunta.

Idanunsa ya zare a hankali sannan tattausan murmushi ya kubce masa wanda labbansa da suka motsa ne kawai suka bayyana murmushi yayi saboda maganan da maleek ya gaya masa ta cikin wayar.

Idanunta ta janye itama da wani irin hanzari tana jin wata irin faduwar gaba data saukar mata. Wani irin kwantaccen kwarjini da wata ajiyayyar izza ta hanga tattare dashi,abubuwan biyu suka ciccibi tunaninta suna jefashi wani sashe na daban dake cike da zallar mamakin "MALAMI DA IZZA?....MALAMI DA KWARJINI?" Ta tambayi kanta da kanta wani abu yana mata tsaye qasan ranta.

Me yasa a kowacce siffa data kebanta dasu?,a kowacce siffa da tafi dacewa dasu?,a kowacce siffa data kasance mallakinsu ce sai ya cusa kansa yayi tarayya dasu?.

Meye hadinsa da wannan izzar?,meye hadinsa da wannan kwarjinin da yake nunawa saman fuskarsa?. Abu mafi qona mata rai shine......ta lura a duk sanda idanunsu zasu hadu guri daya faduwar gaba itace abu na farko dake fara ziyartarta......a duk sanda zasu hada idanu da ita shine yake fara janye idanunsa kafin ita. Baisan ma zunubi bane kallonta haka kai tsaye ido cikin ido?. Koma meye sultane ne ya janyo mata,ya bashi dama da yawa,damar kuma har takai ya bashi wuqa da naman zartarwa cikin rayuwarta.

Yadda ta lumshe idanunta haka ta dauke numfashinta a sanda yake shirin giftata. Zuwa yanzu tana tsoron shaqar wannan qamshin.....qamshin da ta soma zargin akwai wani sihiri a cikinsa. Ba wani rana.....ba wani lokaci da zata shaqi wannan qamshin bai maqale mata a hanci da tunaninta ba a yinin ranar gaba daya. Kowanne qamshi a duniya yana da asali da kuma inda aka samoshi,amma wannan mayen qamshin ya rasa asali da dukka wani bin diddigi da tayi masa.

"Barka da warhaka sheikh" Ta tsinci muryar shehnaz a bayanta tana gaidashi cikin tarin girmamawa.

"Barkanki" Amsar daya bata kenan yana maida wayar maleek kunnensa yana ci gaba da takawa.

Idanunta akhnan ta qanqance tana jin wani abu me nauyi yana sauka qasan zuciyarta. Wani irin bacin rai sabo ya soma tasiri cikin ranta tana kuma iya sauraren yadda shehnaz ta qaro sauri tana qoqarin jera kafadarta da tata.

"Me yasa kike qoqarin zubda girma da kimarki shehnaz?.....me yasa kike qoqarin nunawa duniya ke din ba kowan kowa bace?" Dubanta shehnaz takeyi cikin zallar mamaki.

"Kamar yaya biftu?" Ta tamabaya maganan tana warwarewa shehnaz kai. A nutse ta waiwayo tana ajewa shehnaz wani kallo kafin ta dauke kanta,a hankali cikin izzarnan ta fara magana.

"'Yar asali kike.....jinin sarauta cikakka daga agadez.....me yasa zaki zubda kanki akan wancan tsintacciyar magen da ba wanda yasan asalinshi?,ke ya kamata ya fara gaidawa......yakai har qasa gurin matuqar baki girma,amma kuma baiyi hakan ba saboda sultane ya bashi dukkan wata dama,tsananin girman kai yana sanyashi jin cewa wai shin wani ne......bayan ba kowa bane face wulaqantaccen......"

"Biftu mana!" Shehnaz ta fada tana duban akhnan da mamaki,yadda take maganan da wani birkitaccen fushi.

"Kina manta darajar da Allah ya yiwa malamai ne?" Hannu akhnan ta dagawa shehnaz ba tare data waiwayo ta kalleta ba,idanunta na bayyanar da zallar bacin ranta

"Bana buqatar naji komai.......ya isheni" Ta fadi har cikin zuciyarta tana jin takai geji,a yanzun bata buqatar maganan kowa akan komai.

Ta Jima shehnaz tana dubanta kafin ta dauke idanunta a hankali ta maida gabanta. Mamakin yadda kullum akhnan ke qara birkicewa yana kamata,tuna maganganun da sukayi da aisa kafin ta wuce ne kadai ya hanata cewa komai,saitaci gaba da lissafe lissafenta a ranta,tana kuma nema mata shiriya gurin ubangiji.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

A nutse ya zare device din daga kunnensa bayan ya yiwa maleek sallama,dab da zai shiga sassan mammina ya hada sabon connection da omari ya maida device din kunnensa a nutse yana sake takawa zuwa ciki.

Wani abune ya gilma cikin idanunsa daya tilasta masa sanya yatsansa babban da manuni yadan shafi idanunsa yana furta

Readers Also Read

More by Huguma