L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 22
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 22: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 22. "An gama ranki ya dade......amma ki sani.....kallon…
3,347 words
"An gama ranki ya dade......amma ki sani.....kallon kallo yana da hadari a wadansu lokutan,sai gwani shike iya satar kallo ya kuma fusgi abinda ganin ya bashi a sanda na kewayensa basu ankare da haka ba" Shuru ya ratsa tana fahimtar saqon da tamim ke aike mata da karkataccen harshe,saidai a yanzu zuciyarta bata aminta da shawarar tamim ba.
"Tafiyar hawainiyarmu bata kawomin alfanun komai ba bayaga MAFAKA,mafakar fa wani lokaci nake Allah wadai da ita...,hanzari nake buqatar gwadawa wannan karon,koda bayani ya motsa wasu sassa da zasu farka daga dogon baccin da suke......akwai wani taku na musamman.......dama ya kamaya susan KIFI NA GANINKA ME JAR KOMA!" Tayi maganan a wannan karon tana jin itama ta shirya ta kowanne bangare!!!.
_Uhmmmm.....me karatu,tafiyar fa zazzafa ce......abubuwa da yawa na shirin qulluwa agaba ba'a bigiren da aka shirya qulluwarsu ba,FADUWA DA NASARA......YIWUWAR FARA AFKUWAR SABON WASA TSAKANIN MAMMINA DA HAISAM......SHIN WASAN WAYE ZAIWA DADI?......WAZAI AFKA CIKI?.....KU BIYONI MUJE......._
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 39*
*AKHNAN*
Idanu kawai takebin mammina dashi,wanda ta zauna tana bude kyautan da suka kusa cinye kaso daya cikin uku na dakin hutawar nata daya bayan daya kowanne tana ajiyeshi a gefe bayan ta bude.
"Ba zaki takura ba da rayuwa dashi.....nasanshi nasan mamanshi tsahon shekaru,bayason takura wannan shi ya hanashi aure tuntuni,yana neman matar da zatayi rayuwarta ne kawai ba tare data dameshi ba.....zaki samu dukkan wata izza daga sunan family dinsu kawai....zaki samu kalar sakakkiyar rayuwar da kikeso......kalli a iya yau kawai kyautukan alfarmar daya sauke miki" Mammina ta fadi tana ci gaba da bude kyautukan,wanda kusan kowanne box dake gurin tasan meye a ciki,amma yadda take nuna zumudinta zaka dauka karon farko data fara ganin kayan alatu na rayuwa irin haka.
Baki kadan akhnan din ta tabe,don sam bataji wata burgewa tattare da almaz ko daya a ranta ba. Eh ta karanci abinda mammina ta fada a kansa,da gaske bayason damuwa,ganinsa na farko ta tabbatar da hakan,ta sauke numfashi kadan tana sake tabe baki tare da tuna awannin baya da suka wuce.
Cikin qasaita dake cakude da fargaba ta yiwa kanta matsugunni saman daya daga cikin lafiyayyun kujerun da aka qawata gurin dasu. Wani irin ado da wani irin yanayi da tunda take ganawa da dukka mazajen da siltane yake mata ba'a taba tsara gurin irin haka ba.
Juyawa birra tayi da nufin fita daga gurin ta basu sarari,saidai a nutse da salon kalar umarnin data saba basu ta tsaida birran,sai birra din ta koma gefe daga bayanta ta tsaya tana sauke kanta a qasa.
Da dukka manyan kyawawan idanunta ta qure mutumin da kallo,wanda ke sanye da wata qawatacciyar alkyabba,bayan takalmin da aka yiwa wani irin qawataccen ado daya zame ya ajiyeshi a gefansa.
Kansa yana duqe a qasa,wanda bazai bata dama da ikon gane fuskarsa da kyau ba,saidai mamaki ya soma ratsata a hankali na rashin tantance bacci yake ko gyangadi?,don sam bataga alamun waya a hannunsa ba ballantana tayi tunanin waya yake dannawa.
Izzarta ta hanata magana,a haka suka shafe a qalla mintina biyar kafin ya motsa a hankali yana daga kansa gami da jinginar da bayansa a kujera.
Idanunsa ne ya soma sauka akan fuskarta,kaman yadda nata idanun suka sauka a kanshi,kallon kallo kuma ya sarqafe tsakaninsu na wasu sakanni kafin ta fara janye idanunta mamaki yana sauka a hankali saman zuciyarta.
"Shin me mammina ta gani tattare dashi data hangi dacewarsu?" Tambayar data soma yawo kenan saman kanta,wadda ta tilasta mata maida idanunta a karo na biyu kansa.
Still shima ita yake kallo,saidai a wannan karon yayi qoqarin sakin murmushin daya dan fidda kyansa ya kuma haska wani abu cikin idanunta. Sake zare dubanta tayi daga kansa tana rasa kowanne feelings a kansa. Soyayya dai dama tasan bata da lokacinta,bama kuma batunta akeyi ba,saidai wannan tarin baqincikin da bacin rai da tsananin tunzura da takeji a zuciyarta a duk sanda wani namiji ya tsaya a gabanta da sunan neman aure a yanzun bata jin ko guda daya.....
Me yasa dukka sharuddan data tsara gindaya masa?.....me yasa duk wani doka data tsara shimfida masa don yasan cewa bawai zai amsa sunan mijinta da gasken gaske ba suke sulalewa?.
"Na sani.....kada ki wani damu......zaki rayu yadda kikaga dama.....kaman yadda zan rayu yadda naga dama" Ya furta da wani izza ciki muryarsa da yadan ja hankalinta sosai ta sake daga kai tana dubansa.
Wannan karon tsakiyar idanunsa kawai ta kalla kai tsaye,sai takeji a ranta kamar ta taba ganinsa a wani guri kafin nan,kamar ta taba saninsa kafin yanzu,saidai dukka tunaninta ya gutsire a sanda yayi wani motsi nan take tarin hadiman data fahimci tare dashi suke suka fara shigowa gurin,shi kuma ya miqe tsam yana takawa da wani kamata irin yanayi data kasa tantance ne meye.....izza ce?.....ko nasa yanayinne a haka?.
Ko sanda zata dawo daga tunaninta tuni sun kammala jere takin kyaututukan data dinga binsu kawai da kallo ba tare da tasan ainihin meye da meye a ciki ba sun kuma juya suna take masa baya.
Bataji kalmar DACEWA ko BURGEWA tattare dashi ba.....saidai sam bata damu ba,don dama ba auren wadannan dukka zatayi ba.
"Gobe in sha Allahu zasu gabatar da sadakinsu" Mammina ta fadi tana tattara hankalinta akan akhnan bayan ta gaji da bude kyaututukan. Sanin dukka abinda ke ciki ne ya gajiyar da ita,tanaso kuma tayi saving lokacinta.
Sosai akhnan din ta tsuke idanunta tana duban mammina. Abu na farki daya fara zuwa mata kai shine SHIEKH HAISAM shine zai yanke adadin dukiyar da za'a bayar shi kuma ya basu ita?.
Idanunta ta dauke daga kan mammina,wani sabon bacin ran yana shimfida saman fuskarta. A hankali da wani irin coolness ta motsa labbanta.
"Me yasa saishi mammina?.....me yasa sultane zaiyimin haka?" Ta tambaya tana sake maido dubanta ga mammina.
"Wannan izzar.....wannan kimar,wannan dangantakar kwanann nan zata fara zama tarihi cikin agadez.....kwanan nan qyamata da ala wadai zata maye gurbin komai" Wannan shine abinda yake yawo saman zuciyar mammina din,saidai kuma a fili murmushi ta saki.
Har a ranta takejin matsalolin da take dasu guda biyu ne......tana kan hanyar kauda daya ta fuskanci dayar.......saboda haka dukkan wani uzuri da akhnan zata bayar tana daukarshi a matsayin wani bata lokaci ne kawai.
"Iya wannan lokaci,iya yanzu ne kawai yake da dama a kanki biftu,ki kwantar da hankalinki,daga wannan lokaci na miki alqawarin bazai sake shiga gonarki ba.....zan nesantashi da dukka iyakokinki,keda igiyar aure ma zata baki dukkan wata power?,kin manta wannan igiyar auren zata dawo da dukka wata kyakkyawar alaqa da dangantaka tsakaninki da sultane?,duk wani kusanci da kika rasa zaya dawo miki,meye abun damuwa?,ba abinda ya rage miki sai ki nutsu komai ya tafi daidai da hankulan masu nazari" Kai ta girgiza a hankali,hakan taketa qoqarin yi,amma sai takejin abun kamar yayi mata wahala.
"Niamy nakeso na koma mammina" Ta furta da wani irin sarewa,tana jin komai bayayi mata daidai.
Murmushin dake kwantar da zuciya ta saki tana maida hankalinta a kanta.
"Gaggawar me kike?,zaki zauna a shiryaki kaman kowacce amarya me gata,ko randa aka daura aure ne zaki iya wucewa niamy keda mijinki,wanda hakan shi zai sake bawa sultane nutsuwa da aminci a kanki......" Kai ta girgiza a hankali,a yanzu ba abinda take buqata irin ta samu 'yancinta,ta kuma koma rayuwarta kamar yadda take a baya,mara tarin matsaloli,rayuwa me cike da 'yanci da zartarswa akan dukkan abinda takeso.
"Sahel couture......ya miki nisan da bazai dawo hannunki kamar yadda yake a baya ba.....har gaban abada......zan tabbatar ya sake zamewa daga hannunki ta hannun amintacciyar taki" Ta furta qasan ranta tana sakin murmushi a bayyane,murmushin da akhnan ke kallonsa a matsayin wata hanya guda daya da mammina ke amfani da ita don samar mata da nutsuwa.
★A nutse suke takawa cikin farfajiyar kebantattun sassan haisam din da sultane ya mallaka masa,zuwa doguwar veranda da zata sadashi da qofar da zasu isa kai tsaye ga sassan nasa.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Yarima haisam tare da yarima maleek,wanda dukkaninsu suka narke cikin masarautar agadez da wani irin yanayi da bazai baka daman fahimtar sarautar dake jinin kowannensu ba. Saidai kuma kowannensun akwai wani irin kwantaccen kwarjini a tattare dashi,irin kwarjinin da jinin sarauta yake gaadarwa kowanne ahali nashi.
Dukkaninsu suna sanye ne da fararen tufafin da aka saqasu daga lallausar auduga me darajar gaske,saidai ba kowa bane zai fahimci hakan,saboda sassuqar sutura ce a jikin kowannensu. Maleek yana sanye da kurta pyjamas ne riga da wando,saman kansa kuwa Indonesian cap ce sassauqa data dace da suturar jikinsa,yayin da haisam ke sanye da jallabiyya fara sol me wani irin sulbi data dace da zatin tsahonsa da kyakkyawar fatarsa ta asalin qabilar oromia da suka sabawa ainihin kalarsu ta hanyar yin haske kadan daga ainihin skin color dinsu.
Komai na adon zaren jikin rigar fari ne qal,hakanan hiram din daya yiwa wani irin nadi na asalin samarin larabawa shima fari ne sol daya fidda kyan fuskarsa da dogon hancinsa dake zauna sosai saman fuskarsa ya sake bayyana tsananin kwarjinin idanunsa guda biyu. Half shoe ne a qafarsa shi dinma fari ne sol,lallausa kuma sassauqan da zai wahala ka fahimci yana yanayi da takalmin basarake.
Da azahar maleek ya sauka,ya kuma soma sanyawa an saukeshi a personal gidansa dake wajen masarautar,ya fara zuwa suka gana sannan suka tattauna akan yadda zai baqunceshi cikin masarautar,saboda tsarin shiga da fitar baqi daya sauya yanzu,dole ana buqatar bayanansa da kuma asalin yarensa wanda tuni haisam ya shirya kowanne bayani da zai bayar.
Dab da magariba maleek ya shigo gidan,daidai lokacin da haisam din ya kammala ganawa da dattawan da sukazo karbar auren akhnan a hannunsa kaman yadda sultane ya buqata. Sunzo da tarin sadakin da ya sanyashi mamaki......ba kuma mamakin yawan sadakin ba.....saidai ya riski wani yanayi daya sanyashi zuzzurfan tunanin da har yanzu bai gama sakinsa ba.
Hannun wanda ya miqo sadakin shine abu na farko daya fara kalla......daga yanayin hannun.....yanayi na ainihin zubin halitta,bai hangi wani alamu da ake iya ganewa daga qafa zuwa hannu dake tabbatar da nasaba ba,wanda wani ilimi ne da ba kowa yake dashi ba. Abu na biyu yaga gilmawar almaz......fuska da kamanninsa suka dinga masa yawo a ido,saidai yawan busy din da yayi a yau din ya cunkushe masa duk wani haske da zai iya tuna masa INA YASAN ALMAZ?........A INA YA TABA GANIN FUSKARSA?.
Ya yita maimaita ma'anar sunan dama sunan cikin kansa. Almaz yana nufin DIAMOND (lu'u lu'u cikin yaren oromo). Kai ya jinjina a hankali,yana jin dukkan gamsuwar cewa zaituna ita ta fiddawa akhnan miji kamar yadda a ranar data gabatar da hakan ya zargi an shirya mata komai ne,an kuma karanta mata komai,nata zartarwa ba tare da wani sauran zabi daya rage mata ba.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 40*
"Albarkar auren itace abinda mukafi buqata,ba tarin sadaki ba,iya wannan adadin sune abinda muka yanke muku" Ya fadi cike da dattako yana sake karantar yanayin kowannensu. Cikin qasa da minti daya kacal ya karanci kallon kallon da sukewa junansu. Kamar wani kallo ne na rashin tabbas......kallo ne na rashin sukuni da rashin sakewa da hukuncin daya zartar din. Bai sake basu daman magana ta biyu ba ya miqe wazeer kuma ya dafa masa baya cikin gamsuwa da abinda haisam din yayi.
Ya shaidawa sultane komai,wani irin farinciki ya ratsa sultane din yana aje numfashi a hankali. Gefe daya kuma yana baqincikin subucewar wani abu me daraja daga cikin ahalinsa.....wani abu da yayi tsananin sanya rai a kansa
"Komai kaga ya dace ka zartar muhammad.....wuqa da nama duka suna hannunka" Abinda ya amsashi dashi kenan a taqaice.
Ko yanzun da suke tattaki zuwa sassan nasa don maleek ya fara kewar coffee yana so yasha kafin ya wuce masaukinsa dake personal gidan haisam din tunani ne fal kansa. Fuskar mutumin da aka bashi tabbaci shine wanda aka karbawa auren ya gaza barin idanu da tunaninsa.
Bawai yana mamaki bane.....ba kuma yana raina matsayi dacewa ko cancanta ba,duk akwai abubuwa masu tarin yawa daya kamata ya tsaya tsakanin kotunan sultane ya amsasu inda yana da hurumi akan abinda ya shafi rayuwarta......saidai aah......yana jin kamar akwai wani abu da yakeso ya sani......yana jin kamar akwai wani al'amari dake da alaqa da bincikensa.
"Karon farko da omar ya zauna gidan sarauta zama me dan tsaho kamar haka......shi yasa komai yake sake burgeshi,kasan kowacce rana sai ya bani labarin agadez?.....wannna yaja ra'ayina zuwa ga agadez din" Maleek ya fada yana murmushi yana kuma jin yanayin qasar da garin duka ya masa.
Kadan haisam ya jingine tunanin dake ransa,ya danja fasali kadan sannna ya magantu.
"Kamar ba aiki ne me girma a gabanmu ba.....ka yawaita maimaita masa ko zaifi fahimtar abinda nake nufi......kowanne gidan sarauta lullube yake da tarin abubuwa da idanu basa iya ganinsa......rayuwa ko tsoma kai a cikinsa sai jajirtaccen namiji". Kai maleek ya kada,don ya fahimci maganan haisam sama ma da yadda yakeso ya fahimta din.
"Gimbiya akhnan" Maleek ya fada a hankali da qaramin murmushi,sannan ya dan juya kadan yana kallon haisam.
"Ko kasan ina da labarinta kadan kadan,bada wata masaniya me yawa can can ba tun kafin omari ya fara gayamin komai akan abinda ya shafeta?" Maleek yayi maganan yana maida dubansa gabansa.
"Akwai nazzirou dan qasar nan ne,yankin diffa,amma yana rayuwa a agadez....."
"Na karbi sadakinta dazun.....daurin aurenta rana ita yau,idan kana sha'awar zama daya daga cikin shaidun daurin aurenta kana iya kaiwa har rana ita yau a agadez" Haisam ya Fadi da yanayin daya bayyanawa hakeem sam sam baya da wani interest akan hirarta ma.
Murmushi me dan sauti maleek ya sauke.
"Wannan bayani haka da wurwuri?"
"Saboda bana buqatar dogon hira akan sha'aninta......inajin kamar shigarta cikin bincikena tana sake dagulamin shine kawai tare da shiga qofofin da bai kamata ta tsaya a nan ba".
"Dalili?" Maleek ya buqata still yana boye murmushin sa bai kuma kalli haisam ba ya bada dukkan hankalisa ne kawai a kansa.
"Wanzuwarta akan wasu hanyoyi da qofofi sune silar bata lokaci na da dadewata cikin wannan masarautar da 'ya'yan cikinta ke rayuwa cikin dimuwa da rashin sanin birnannun sirrikan dake shirin binne musu rayuwa da ransu......ciki harda tata rayuwar data dauketa da wani irin kima da tsananin girman da batasan cewa batakai can ba" Ya sauke maganan da wani irin zafi kadan cikin muryarsa,saidai can qasan ransa yana jin wani mutuwar jiki yana sauka masa.
"Kasan da haka captain......me zai hana kayi ceton daka saba?" Maleek ya tambaya kai tsaye yana duban haisam gami da rage saurin tafiyarsa kadan.
Duk da cewa dare ne amma hakan bai hana maleek ganin yadda haisam ya waiwayo yana zuba manyan fararen idanunsa ba,kafin ya janyesu a hankali. Yan miskilancin suka biyo baya,sai daga bisani daya tuna maleek ne sannan ya motsa bakinsa a nutse.
"Ban gaji da kare mutuncina da martabata ba........inda ace namiji ne.......zan iya qundunbalar aikata hakan........ta yadda koda ya qalubalanceni ina iya zage qwanjina na nuna masa munin abinda yacemin.......amma d'iya mace?......" Sai ya tsaya bai dakata ba yana girgiza kansa.
"Diya mace irinta......data yiwa kanta ado da qawa da rashin iya magana......data yiwa kanta ado da qawa da tarin rashin kunya,nakanji a raina inama ace ta fito daga jini da tsatson oromia....." Sai yayi shuru bai qarasa ba.
Duk da bai qarasa din ba maleek ya fahimci me yake nufi. Tabbas qabilarsu qabila ce da girmama manya ya zama daya daga cikin dokokinsu,ya zama wani abu da ake rainon kowanne d'a nata,tun daga haihuwa har zuwa girma.
"Akwai wasu dabi'u da qualities a tare da ita.......akwai wasu halaye da ba zaka sake samun irinsu sak ga kowacce mace ba a nan kusa.....qila sai bayan shekaru masu yawan da qila zuwa sannan furfura ta gama zama abar ado a kanka da fuskarka" Maleek yayi maganar kai tsaye tana kuma sauka saman zuciyar haisam.
A hankali ya soma maido maganan daga farkonta zuwa baya,yana qoqarin mata mazauni me kyau.......saidai isowarsu dab da gurin,da kuma hango omar da yayi tsaye a gurin da nashi cup din gahwar ya sanya ya maida maganan da yakeson maidawa malee din.
Ya tabbatar idan omar yaji maganan bazai qare ba......ba kuma zai mutu ba,amma indai ta maleek ne shi kadai zai wahala ya sake tayar da maganar,saidai ko bayan wani lokaci ba wannan ba.
Hand shaking suka bawa junansu da wani irin yanayin musabaha da Huggin da zai nuna maka tsantsar qauna dake tsakaninsu.
"Ka shiga kasha ka fito mu wuce.....akwai hira me tsaho yau kam" Omari ya fadi yana dan duban haisam kafin ya maida hankalinsa ga agogonsa. Baiko kalleshi ba haisam din,don har yanzu kwanyarsa cike take da tarin tunaninnika.
A nutse maleek ya wuce ya barsu a nan,shuru ya ratsa gurin na wasu daqiqu,omar na sipping coffee dinsa,haisam kuma yana tsaye da wannan tsaho da murjewar jikin dake nuna asalin halittarsa ta GIANT MAN.
*AKHNAN*
Batasan adadin hadimai nawa ta sanya su kula mata da shigowar haisam ba tun daga sanda adadin abinda ya karba a matsayin sadakinta ya isa kunnuwanta.
Batasan adadin sau nawa ta tsaya gaban mirror tana sake qarewa kanta da kanta kallo ba. Ta sanya hannu ta baje lallausar sumar nan tata me daukan hankali ta ainihin buzuwa kuma ba'abzina.
Wanne irin muni ko lalacewa ya hango a jikinta......wanne irin naqasu ko kasawa ke tattare da ita da zai karbi mafi qasqancin sadaki da sunan sadakinta?. Sadakin da koda manyan hadiman da suka jima cikin gidan.....manyan hadiman da sarauta takewa ALFARMA su shiga rigarta sunfi qarfin wannan sadakin ballanta ita AKHNAN MUHAMMAD HAMMUD diyar SULTANE guda.
Haifaffiyar diyar da har yanzu ba'a samu wata yarinya data kamo rabin qafarta a daraja da kuma gata ba kaf masarautun da qasar niger keda ita. Yarinyar da izzarta da cikar gatanta ya sanya take ganin bata da SA'A cikin yaran sarakuna ballanta har ta qulla aminci ko qawance da daya daga cikinsu.
Kai ta girgiza a zafafe tana jin wani sashe na qwaqwalwarta na tafasa da wani irin matsanancin bacin rai. SULTANE NE SILA......ta yaya zai hada mu'amalarsa da bagidajen da baisan komai ba face tarin litatttafai da tawwada?. Me yasa duk gatanta.....duk shahara da family din mahaifiyarta sukayi idanma bata da gefan uba ya gaza wakilta mutum daya da zai zama jagora wajen aurar da ita?. Sai wannan mutumin da takejin TSANARSA ta fita daban data sauran dukkan malaman data sani. Wannan mutumin da takejin yafi dukkan sauran malaman da suka rayua fadar baqar aniya da baqin sihiri.
Dukkan malamai na baya da suka rayu cikin masarautar girmamata suke.......mutuntata suke da tsananin mutuntata ra'ayinta.....bata da wata hujja ta tsanarsu face tsana data musu tun ta asali.....amma kuma wannan fa?.....shi kuma fa?.
Ya karbe ya kuma ture dukkan wani matsayi da take gani da kusanci tana dashi.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Tana jin wata fusata da ba zata barta ta fara magana da mammina ba......tanajin ya mata nisa ta tsaya shawara da mammina. Shi ya aikata,shi ya kamata ya fara ganin fushinta. Ya dace zuwa yanzu yasan iya matsayinsa.......ya kamata ya fahimci ya zurfafa da yawa,ya kamata ta farkar dashi idan ya soma shaqar iskar 'yanci da yawa harta bugar dashi ya manta matsayinsa......ya kamata old version na AKHNAN BIFTU ya motsa.