L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 30
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 30: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 30. Munyi wata irin shaquwa taban mamaki,irin shaquwar da…
3,268 words
Munyi wata irin shaquwa taban mamaki,irin shaquwar da idan ka kallemu zaka dauka mahaifa daya muka kwanta,ko bacci baya iya rabamu,komai namu daya,hatta da abinci cikin kwano daya mukeci. Daidai da dan kunne idan wannan ta canza sai wannan ta canza nata,wata iri shaquwa taban mamaki da ba zaka taba ganin d'aya bakaga daya ba,komai tsanani komai runtsi. A haka muka taso da wata mugun qaunar juna,ko ciwo daya keyi to hankalin sauran ya tashu,tare ake ciwon nan,dame ciwon dame lafiyar gaba daya...." Sai nanay ta sauke numfashi tana sakin wani murmushi me sanyi,wanda ya tabbatarwa haisam ta tuna da quruciya ne.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"A haka muka girma,muka zama yammata sosai.....abun burgewar kowanne namiji,kowa kuma qoqarin mallakarmu yakeyi,saidai wani ikon Allah nice naketa samun manema a sannan,amma naqi yarda da kowa,saboda alqawari muka yiwa junanmu babu wadda zatayi aure tabar 'yar uwarta. To amma da yake shirin Allah daban yake dana mutum,ba zato Allah ya kawo sarkin jimma kakanka kenan,ya kuma ganni,ya yiwa d'ansa yarima me jiran gado kamu,take mahaifina ya bashi ni,ban ganshi ba,bai ganni ba,amma saina samu kaina da qin musawa umarnin motii" Ta sake kai gabar maganar tana murmushi,murmushin da ya tabbatar ya boye abubuwa masu yawa data tuna. Samun kansa yayi shima da murmusawa kadan,kwanyarsa tana dauko masa banbamcin tarbiyyar yaran yanzu da na daa......tunaninsa yana kawo masa dauki ba dadin da aka dinga yi watanni kadan tsakanin akhnan da mahaifinta,sai ya zame tunanin ya watsar yana maida hankalinsa ga nanay.
"Na haifi yayanka bai jima ba ya rasu,ina da cikinka kuma rigima ta barke tsakanin mummu falmata da mahaifin SAFEENA ta" Ta dakata kadan tana shan numfashi,dakatawar daya tabbatar akwai wani abu cikin qirjinta da take hadiya da bai wuce mata ba har yau.
"Wannan rigimar ita ta zama sanadi na biyu da har yau ban sake ganin safeenata ba......ban sake ganin usainata ba safiyya ba,ban kuma sake kwana na tashi da farinciki cikakke ba saboda rashinsu cikin rayuwata ba tare dana shirya ba......ya dage sai an bashi safeena ya mata miji,motii ya bashi haquri akan ya bari ta zabi mijin da takeso,da yaga ya dage yace ya bashi dama yayi bincike,motii ya bincika yaga cewar akwai matsala shigar safeena wannan gidan,matansa biyu,saidai matarsa ta biyu gagararriya ce,banda uwargidan tsayayya ce da tuni itama ta fitar da ita,motii yayi qoqarin fahimtar dashi amma ya rufe idanu,duk da motii yana qarfin ikon da zai hanashi ko ya tursasa janye auren amma baiyi haka ba,yace mahaifi mahaifi ne,ya bashi safeena ta,aka aurar da ita ga mutumin da har yanzu bansan waye ba,shekara daya da auren ya saketa,a ranar da motii ya cika kwana bakwai da rasuwa.
Bamusan me ya faru ba,ranar da motii ya cika kwana arba'in,muka wayi gari ba mummu falmata ba safeenata ba usaina safiyya......ba irin neman da ba'ayi musu ba har yau har kwanan gobe bamu sake jinsu ko ganinsu ba.....duk da daga baya malamai da yawa suna fadin kurciya akayi musu. Hankalin momma balkes ya tashi,mahaifiyata a sannan ta dorama kanta karan tsana.....ta dinga ganin kamar kowa zaiga ita ta kora falmata da yaranta saboda gado,amma saboda kusan kowa yasan zaman da sukayi masu zato da zargin kadanne,don dama shi dan adam baka amintar da kowa da kowa lokaci guda. Bayanai daga baya sunyita fita da rade radin kishiyarta ta biyu da tayi silar fitarta a gidan ita ta jefeta da mummunan asirin......qabilar data fito a ciki qabila ce mafi hatsari a nan qasar,ana aurensu ne kawai saboda an camfa aurensu yana zuwama mutum da arziqi,shi yasa mijinta ya kasa rabuwa da ita. Ban sakeji ta bangarensu ba haisam.....ban sake gani da jin komai daya shafesu ba tsahon wannan shekarun,suna raye?,ko dukkansu sun mutu?,ban sani ba muhammad" Nanay ta qarasa fadi muryarta a karye sosai.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 51*
Sosai yaja wani irin numfashi yana lumshe idanunsa da kyau. Adadin bugawar da kansa keyi yana qara gudu. Wani irin birkicewa yakejin tunaninsa yanayi tare da hade tunanikan nasa guri guda.
Tabbas wannan matar me suna safeena,kuma obboleettii lamaan din nanay dinsa(twin sister din nanay dinsa).
A zahiri Kawann ne yake gani masu tarin yawa kwance saman fuskar wadda take kamanni da fuskar Akhnan din adan qanqanin ganin da yake mata,sannan ga wani kamannin ta wani bangaren kuma da suke bayyana kansu da wannan kamilar dattijuwar......matar da koda yaushe kamalarta ke mata kama data nanay dinsa wato MORSA SAFIYYA. Duk da haduwarsa da ita cikin gidan idan har yayi yawa bazai wuce sau biyar ba,ba ma'abocin iya kallon fuskokin matan al'umma bane saboda kalar nashi kishin da yake dashi,amma duk da hakan yasan akwai kamanni na gasken gaske cikin wannan labarin.
Idan har hasashensa ya tabbata kenan,morsa safiyya ita dinma 'yar Ethiopia ce?,jinin sarautar GUMMA?. Amma hakan sai bai nuna a al'adunta da yanayinta ba,ko don hakan yana da nasaba da barin qasar da tayi shekaru masu yawa?,shi yasa ta juye gaba daya ta koma 'yar agadez ba'abzina ta gaske?.
Dukka wadannan tunanin nasa hasashe ne.......bashi da tabbaci ko daya,ballantana ya lasawa nanay xuma a baki. Bayason ya bata tabbacin abinda ba haka yake ba.
"Idan na zama silar haduwarki da obboleettii lamaan dinki nanay......wane kyauta zakimin?" Ya furta da wani sassanyan murmushi akan fuskarsa,yana jin yaqini da imanin wannan karon zai sauka daga kan layi......wannan karon zai sauka kadan daga layin aikinsa don bawa nanay farinciki.
Wani irin kallo take masa,wani irin kallo dake dauke da wani kwantaccen farinciki,wani irin kallo daya bayyana adadin ruwan hawaye me yawa cikin qwayar idanunta.
"Na gode Muhammad......koda baka hadani da obboleettii dina ba na gode maka,dama can kai din yaro ne daya zama sanyin idaniya ga iyayensa,kai din me share hawayen iyayensa ne da sanya farinciki a zukatansu,ba shakka rayuwarka zataci gaba da albarka......amma saidai inaji a jikina zai wahala ace safiyya ko safeena suna raye......zai wahala ace suna raye zasu kai wannan lokacin basu nemeni ba,koda asiri ne zai sakesu zuwa yanzu tabbas" Ta qarasa maganar tana qoqarin maida hawayen don kada ta raunata masa zuciya.
Idanu kawai ya zubawa nanay din yana karantar zurfin ciwon dake cikin zuciyarta,can qasan ransa ya cikashi da addu'a da fatan ubangiji ya taqaita masa jarrabawa game da soyayya da qauna akan komai ma.
"Shuru ba shine yake alamta mutum babu shi ba nanay,ki yarda dani kuma kimin fatan alkhairi,na miki alqawari indai suna raye zan kawo miki su......amma kafin sannan qoqari daya zakiyimin" Ya fada adam apple dinsa yanayin sama da qasa alamu ya hadiye wani abu. Yayi bala'in qin jinin zalunci,baya qaunar zalunci ko kadan a rayuwarsa,da wanna dabi'ar yayi sabo tun haihuwarsa,wannan dalilin.....wannan dabi'ar ta sanya ya tashi da KISHIN QASARSA da kuma cikakken qwarin gwiwar shiga NATIONAL INTELLIGENCE SECURITY SERVICE da yake ciki a yanxu.
"Ina jinks muhammad" Ta fadi yana dauke hawayen daga fuskarta. Hawayen da haisam din yake jinsa kamar d'igar dalmar wuta saman ruhinsa. Duk wani hawaye na d'iya mace ciwo yake masa a rai,koda na wadda bai sani bane.....yana kallon kukan 'ya mace a matsayin qarshen rauninta......qarshen lafazin dake danqare a zuciyarta wanda baki bazai iya fadinsa ba......yana kuma kallonsa a abu mafi girma daya kamata aduba ga diya mace.....ballantana kuma nanay dinsa.....nanay dinsa da yakejin wani sashe ne na rayuwarsa gaba daya.
"Sunan mijin da safeena ta aura kawai nakeso na samu......sai sunan da kuke kyautata zaton shine sunan qasar mumma falmata". Ya qarasa maganar yana damqr haqoransa guri guda cikin dabara,saboda yadda yakejin kamar yana shirin fita daga hayyacinsa zuwa lokacin har idanunsa suna dan lumshewa kadan.
"Kana lafiya muhammad?" Nanay ta tambayeshi cikin tsananin kulawa. Murmushin qarfin hali da yabawa da tarin qauna da tsananin kulawar nanay. Duk yadda yaso ya boye mata abinda yakeji a jikinsa amma sai da yayi noticing wani abu?.
"Lafiya lau nanay" Ya fadi yana sake qarfafa mata zuciya. Shuru tayi na wasu mintuna sannan ta furta.
"Alhamdulillah...."
"Muhammad shekarun sunja sunyi kuma nisa da yawa,amma zan gwada neman zenabu......aminiya ga mahaifanmu,ban sani ba ko falmata ta taba gaya mata sunan mijin,duk da tsufa ya risketa,amma kyautata zaton zayayi wahala ta iya tunawa"
"Zata tuna nanay......zata tuna in sha Allah,ki gwada"
"Zan gwada muhammad......yankin da falmata ta fito muna kiransa da birnin Aiir". Ta qarasa fada tana xube idanunta kan haisam din. Haka kawai a karon farko bayan rasa dukkan wani fata da buri a yau ya sanyata tana jin fatanta da burinta yana dawowa.
"Na miki alqawari nanay" Ya fada yana yanke kiran saboda yadda yakejin komai nasa yana masa nauyi,yanke kiran kuma da yayi saiga saqo daga headquarter dinsu daga amintaccen me bincikensu.
"Almaz......gudajjen yaron da har yanzu YATAAMAA ORPHANAGE HOME ya kasa tsinto inda yake,bayan sun raineshi na shekaru ta hannun wata mata data kawoshi". Daga qasa tarin nau'ikan hotunan almaz dinne daban daban.
Wani irin nauyi yaji yana sake danneshi,yana shirin bude sauran hotunan da basu budu ba da hanzari video na sultane ya fado masa,sai ya canza akala ya bude hannunsa yana dan rawa kadan.
Yana zaune cikin haram na makka daura da ka'aba yake bashi saqon,cikin kamalar nan tasa da dattakonsa. Godiya sosai yake masa da wani irin yanayi da yasa zuciyar haisam ta qara nauyi.
"Nayi amanna da dukka kulawarka da jagorancinka,na tabbatar ban damqa amanar mutanena da iyalina hannun da zai gaza kula dasu ba,ina da labarin komai ya gudana daidai alhamdulillah,bansan da wanne abu zan gode maka ba,na yaba sosai muhammad na yaba........abinda kawai ya rage saqo na qarshe shine......kayi qoqarin damqa akhnan hannun mijinta bisa amana.....banaso ta wuce kwanaki uku a gidana kowanne kalar biki zasuyi......" Dishi dishi ya soma gani,a hankali yaji numfashinsa yana quntata a qirjinsa,tamkar qofofin fitar numfashinsa aka tsuke ko aka rage yawansu.
Hannunsa ya miqa yana b'alle button din wuyan rigarsa,a hankali ya kifa kansa saman table din yana jin yadda ganinsa ke sake dishi dishi.
Da sallama maleek ya shigo,amma yanayin da yaga haisam din ya daga hankalinsa. Da hanzari ya qaraso yana qoqarin daga fuskarshi.
"Na fada baka da lafiya....amma ka musa hakan......" Maleek din ya fadi hankalinsa yana tashi. Da manyan idanunsa da suka lumshe a hankali ya dubi maleek,sai ya miqawa maleek hannu,ya bashi nasa hannun ya dagashi daga gurin,yana riqe dashi suke takawa a hankali suna fita a dakin.
Bai fahimci likita ya kira masa ba sai bayan ya kaishi daya daga cikin bedrooms dinsa,likitan ya shigo da kayan aikinsa yana ajewa a gefe idonsa akan haisam din. Ruwa kawai ya fara qoqarin saka masa saboda yana zaton mugun zazzabin dake jikinsa ya qone ruwan jikinsa,sai daya kammala sannan ya dauki jininsa yace zaije yayi gwaji ya dawo don ganin maganin daya dace yasha.
Komawa gefe maleek kawai yayi ya zauna yana duban fuskar haisam wanda bacci ya daukeshi. Mamaki can qasan zuciyarsa da wasu lissafe lissafe,akwai abubuwa da yawa dake kai kawo cikin zuciyarsa. Baisan lokutan daya dauka ba yana gadin haisam din har zuwa sanda likitan ya shigo wannan karon shida omar ne.
"Banga wani matsala cikin gwajinsa ba gaskiya,nayi tunanin malaria ne ko wani abu na daban,amma ba ita a cikin jininsa......abinda kawai nafi tunani shine stress ne yayi masa yawa,so yana buqatar ya huta sosai,yayi isashen bacci,idan zai yuwu kada ya sake wani aiki me wahala ko dogon tunani da zai kawo masa damuwa ko jigata.....Allah ya bashi lafiya" Likitan ya fadi yana hada kayayyakinsa.
"Mun gode" Maleek ya fadi yana bashi hannu,sannan ya ciro wayarsa ya kira su beeno yace su sallameshi su maidashi asibitin daya daukoshi.
"Wai garin yaya?" Omari ya tambayi maleek damuwa fal a fuskarsa yana zama saman bedside drawers din dake gefan gadon haisam din.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Bana ce ba omar......kasan halinsa wani lokacin da zurfin ciki sosai......kusan kwana biyar kenan nake ganin bashi da lafiya,baice komai ba har sai dana gaji da ganin canzawar yanayinsa na tambayeshi,sai lokacin yake fadimin wai baya jin dadi ne.....to kuma dazun na barshi a study room dinsa mun fita dasu beeno neman likita ya dubashi,tunda nasan halinsa tun a school,muna dawowa na sameshi yana duba saqo kaman zaiyi loosing conscious nasa..."
"Saqo kuma?" Omar ya tambaya cikin mamaki. Kai maleek ya jinjina
"Yes.....don ban tsaya ma rufe masa system din ba......coz nasan aikin naku da tsari,kada naje naga sunana cikin suspect" Ya fada yana dan murmushi. Shima omar murmushin ya maida masa,sai ya miqe yana fadin.
"Ina zuwa" Ya taka yana fita a nutse.
Mintina biyar omar ya shigo da system din a hannunsa,ba personal system dinsa bane dake dauke da muhimmam bayanai sosai bane,wannan din itace ta biyu,akwai bayanai a cikinta amma baikai ta farko ba.
Da idanu maleek ya bishi sanda ya dora system din saman sofa bed,yayi playing video din sultane. Dakin ya dauki shuru har suka kammala gani kafin su janye idanunsu suna kallon juna lokaci guda.
Shuru ya ratsa dakin ba wasu mintuna,kafin qaramar dariya ta subuce musu lokaci daya.
"Me kakewa dariya?" Omar ya tambayi maleek still da murmushi kan fuskarsa.
"Kai me kakewa dariya?" Shima maleek ya tambayi omar da wannan salon na tsohuwar abota da aminci dake tsakaninsu,wanda sukan zama cikin zolaya da sakewa a junansu a duk sanda suke tare.
A hankali fuskar maleek ta koma daidai,ya koma prince maleek dinsa,wannan ya sanya omar shima tattara nutsuwarsa guri daya. Numfashi maleek ya sauke,a nutse ya fara magana.
"Farin shiga ne captain.......baisan daga yadda komai yake iya farawa ba......ba dole bane soyayya ta fara daga jin soyayya a zuciya ba......takan iya farawa daga fada.....rashin jituwa,tausayi da sauransu.....wani lokaci ma daga qiyayya take farawa,daga sanda na fara ganinta ido da ido.....bayan labarai na dabi'unta da naji na tabbatar itace kalar matar da haisam yake lalube a wata duniyar......gata a wannan duniyar tana rayuwa koda shi baisan hakan bane......amma baqo ne shi ta wannan feeling din dake samun zuciya,shi yasa ya kasa banbamcewa,dabi'unta da yake ganin basuyi masa ba sune su saamee suka rasa a tare dasu,wannan shi ya sanya suka gaza samun bude koda qofar farko ta zuciyarsa......inda ace irin dabi'un su saamee kawai sun wadatar dashi daga zabar matar aure......da tuntuni ya zama mijin saamee tunda dadewa.....ko ita ko......"
"Menelik" Omar ya qarasa masa da hanzari,don ya hango yadda kalaman maleek suka hau kan saiti sosai,yaji kuma yana gamsuwa dasu d'ari bisa d'ari.
"Yes....menelik.......so yanzun kuma,bai fahimta ba......zai mutu saboda ance a kaita gidan mijinta,bari ya farfado kaji bayaninsa bazai taba bari yayi daidai da harsashena ba". Murmushi Omar ya saki yana maida dubansa ga fuskar haisam din dake bacci peaceful,saidai yana jin wani rashin dadi da komai yazo a baibai,yana kuma jin wani iri daya kasance haisam din bai fahimci komai ba.
"Yanzu meye abunyi?" Omar ya tambayi maleek yana dubansa.
"Babu" Ya bawa omar din amsa kai tsaye,abinda yasa omar din xuba masa ido yana dubansa.
"Eh,matar wani ce ita yanzun,kuma shine ma ya daura auren" Maganar maleek ta fita da wani sauti na daban,sautin daya haifar da shuru a cikin dakin,dukkaninsu kamar an kwashe sauran kalaman bakinsu.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 52*
★★Zaune yake saman rocking chair wadda ke ajiye cikin qawatacciyar harabar dake gurin da aka qawata da nau'in shuke shuke daidai da yadda nature dinsa yake nason tsirrai.
Gefansa dan mini table din dake dauke da tarkacen kayan coffee kamar yadda yake a cikin jini da al'adar duk wani dan qabilar oromo tsananin qaunar coffee kamar rai da rayuwa.
Shima nasa hannun riqe yake da mug dake tururi,yana sipping coffee din a hankali yana motsa rocking chair din zuwa gaba da baya tana dan lilo kadan kadan dashi.
Tun shekaran jiya yana ciki sai yau ya fito don ya samu fresh air da yakeso ta sake buda tunaninsa da kyau,ya kwanta ne kawai saboda ya faranta ran omar da maleek daketa dawainiya dashi,amma yana kwance ne yana jin tarin matsaloli danne da kansa da kafadunsa.
Yanaji a jikinsa aski yazo gaba goshi wanda hausawa ke cewa yafi zafi,yana ji a ransa komai yana kan gabar warwarewa. Ba yadda baiyi su bashi system dinsa ba da sauran wayoyinsa amma sunce sai ya gama warwarewa,shi yasa dole a yanzu ya tako ya fito,bawai don Jikinsa ya gama qwari ba. Hasalima duk da magungunan da yakesha dare yanayi yake jinsa cikin wani quntacewa da zazzabi me zafi,sassaucin abun ma'abocin tsaiwar dare ne,da zarar kuma ya fara sallarsa yake jin sassauci yana zuwa masa a hankali.
Wani abu yakeji ya qulle a qirjinsa a duk sanda ya tuna fuskar almaz a wancan ranar......sannan ya hasko fuskarsa saman takardun gidan marayu,gidan marayun da suka bada tabbacin an fita dashi baa sake ganinsa ba,ba'a kuma san inda yake ba har yanxu.
Abu daya zuciyarsa ke maimaita masa tun daga wancan ranar ZAITUNA ce ita shigo dashi agadez.....ita ta kawoshi ta kuma aurawa AKHNAN shi.
Bayajin auren akhnan shine damuwarsa,damuwarsa shine yadda ya qulla auren da ya tabbatar AKWAI ZARGE CIKIN NADI. Da wacce fuska zai kalli sultane yace ya cika amanar daya bashi?,da wacce fuska zai.kalli sultane yace ya kare amanarsa?,da wanne harshe zaiwa sultane bayani a lokacin da GASKIYA ZATAYI HALINTA?.
Ta yaya zai kare rayuwarta daga wannan baqin duhun daya tabbatar nata idanun sun makance ba tare da ita tayi zaton yana da wani interest na shiga rayuwarta ba?......ta yaya zai fahimtar da ita zuzzurfan ramin da take dab da fadawa ba tare data dauka cewa yayi ne don ITA ba?.
Tafiyar da yaji a bayansa ya sakashi ajiye mug din sannan ya waiwaya a hankali. Omar ne a gaggauce maqale da waya a hannunsa.
"Yes bobbo.....gashinan" Ya furta yana qarasowa gaban haisam ya miqa masa wayar,sannan yaja kujerar dake facing dinsa ya zauna. Yadda yaga omar a gaggauce yasan bobbo muhammad dawud ne,tun baice komai ba kuma yasan kiran gaggawa ne,sai ya saka wayar a kunnensa cikin cikakkiyar nutsuwarnan tasa yayi masa sallama.
"Wa'alaikumussalam muhammad" Ya amsashi,har qasan ransa yana jin haisam din na daban ne,daidai da yanayin maganarsa kadai zai tabbatar maka da tambarin nutsuwar dake tare dashi.
"Barka da warhaka obbo"
"Barka kade captain muhammad.....ya jikin naka?"
"Alhamdulillah bobbo,ba wani ciwo bane sosai". Murmushi kadan muhammad dawud ya saki.
" Na jaddadawa omar su kula dakai sosai,don bansan da wanne baki zan gayawa motii gudan jininsa bashi da lafiya ba".
"Na warke bobbo" Ya amsa masa murmushi can qasan zuciyarsa yana subuce masa,duk da hakan bai bayyana a fuskarsa ba.
"Ma sha Allah......Allah ya qara lafiya.....naje umara muhammad,inata addu'akan aikinmu.....amma yanayin yadda naga abubuwa suna sake budewa da fitowa jikina yana ban komai yana zuwa gangara ne,komai yana zuwa qarshe,sati daya kacal zanyi na dawo gida......"
"Allah ya dawo dakai lafiya" Ya Fadi a nutse.