Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 31

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 31

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 31: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 31. "Muhammad.....lallai Allah ne kadai yakeson Ethiopia da…

3,349 words

"Muhammad.....lallai Allah ne kadai yakeson Ethiopia da rahama ba qabilar oromo ba ba jimma da yankunanta ba.....ba iyayenka kadai ba da Allah yasa aka haifeka a cikinmu,sannan yayi ma intelligence security service baiwa daya sanya ka daya daga cikinmu......muhammad binciken daka tursasa ayi akan tsohuwar matar AJANI ya fito,ya kuma bada sakamakon bacewar da akace tayi ba bata tayi ba,da qafafunta ta fita daga Ethiopia ta barauniyar hanya......ta wani sashen kuma sai wani binciken namu ya nuna mana TA MUTU a wani asibiti dake daura da YATAAMA ORPHANAGE HOME. Ga certificate dinta nan na mutuwa,bayanan binneta dama kabarinta,haka 'yan uwanta dukka kowa yayi amanna da mutuwarta,don har zaman makoki anyi mata......kaga kawai ayar tambaya kenan akan matar ita kanta?". Tunda muhammad dawud ya fara magana jinjina kai kawai haisam yakeyi,tako ta ina ta share dukkan wata shaida ko alama da zata bayyana itace ta qulla kisan......

"Bobbo"

"Muhammad" Ya kira haisam yana sauke gauron numfashi.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Mutumin da muke fadi tashin nema......ba bisa radin kansa ya kashe ajani ba.....daukarsa haya akayi.....sakashi akayi,matar ajani kuma da gaske ita ta saka ayi kisan....kuma tana raye,tabbas tana raye" Haisam din ya fadi kai tsaye.

"Me yasa kace haka?".

" Lokaci.....lokaci nakeso ka bani.....zan tabbatar maka da hakan,wacce qasa ake hasashen zata iya tsallakawa?" Haisam ya tambaya kai tsaye yana komawa ya zauna sosai saman Rocky chair din.

"Qasashe biyar ne muke da iyaka dasu,Eritrea,Djibouti,Somalia,kenya,south sudan,sudan......"

"Wannan shine zai sanya ta tsallakesu gaba daya,taqi fadawa ko daya daga cikinsu saboda bincike zai iya cimmata.....zata wuce kai tsaye ne daga east Africa zuwa South africa wato NIGER......Tabbas ita da duk wanda ya jibanci lamarin SUNA NIGER AGADEZ bobbo" Dif muhammad dawud yayi,yana sake jinjina girman baiwar da Allah ya yiwa muhammad haisam din. Gaba daya ya zube lissafinsa fes .....sai a yanzun da haisam yayi magana yaga tabbas maganar haisam dince akan layi.

"Ma sha Allah,ma sha Allah,Rabbiin si haa eebbisu(ina fatan Allah ya albarkaceka)" Ya fadi da harshen oromo,jikinsa yana sake sanyaya da tarin baiwar haisam din.....wani farinciki yana sake lullubeshi.

"Tabbas zanyi alfahari kafin na sauka daga shugabancin NISS ace a zamanina qasata ta kubuta daga wannan tuhumar.....qasata ta binciko wannan me laifin.....qasata ta hukuntasu"

"Zan saka kayi wannan alfaharin tabbas bobbo" Ya furta a nutse yana zare wayar gami da miqawa omar.

"Ka daukomin wayoyina" Ya bawa omar umarni nakai tsaye idanunsa cikin nasa don kada ma ya masa musu,saidai duk da haka saida omar ya kauda kansa kadan sannan yace.

"Ka fara maganin abinda yake damunka mana haisam kafin ka magance matsalar qasarka." Yakai qarshen maganar sanda maleek ke qarasowa dauke da tray. Yau din duk tari sarautarsa da mulkinsa.....amma abota ta gaskiya ta sanya da kansa yake hidimawa haisam. Shi kansa haisam da kallo ya bishi yana mamakin yadda ya zubda duk qasaitarsa da mulkinsa saboda abota ta gaskiya,gefe daya kuma maganar omar tana daure masa kai.

"Akwai wata matsala ne da nace maka ina da ita?" Ya jefawa omar tambayar yana tsareshi da ido,saidai sam.omar yaqi kallonsa don yasan zurfin gubar kallonsa idan yaso. Ga mamakinsa sai amsa ta fito a bakin maleek daya samu nashi gurin zaman daura da haisam din.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 53*

"Damuwar da za'a barta cikin qwaqwalwa tafi kowacce kalar damuwa cutarwa,kasan da haka.........me yasa ka gaza fahimtar ka fara jin qaunarta cikin zuciyarka?......me yasa kayi fatali da komai?". Sosai maganan maleek yazo masa a bazata,ya kuma zo masa da wani irin yanayi da kai tsaye zuciyarsa ta qaryatashi.

"Wace kenan?" Yayi tambayar da alamun rashin fahimtar maganar maleek din na gasken gaske.

Idanu maleek ya janye,yana mamakin yadda haisam keta yin komai kaman baisan komai ba.

"Ka daina pretending mana haisam.....akhnan nake maka magana" Maleek ya fadi kansa tsaye yana dubansa.

Manyan idanunsa ya qanqance ciki kadan,yana ci gaba da duban maleek din.

"Maleek?.....matar aure?....matar wani?,kasan inda matatace aka kama wannan hirar a kanta kowa zai iya rasa wani sashe na jikinsa?" Yayi maganar dake nuna da gaske ne abinda yake furtawa akan harshensa shine har cikin zuciyarsa. Murmushi kadan maleek ya saki yana sake karantarsa da dukka ilimin karantar halayyar dan adam din da yake dashi.

"Matarka ce.....amma kayi sake kaje ka aurawa wani.....type dinka ce haisam.....itace kalar matar da kake nem......"

"Stop it mana maleek!" Haisam din ya fadi da husky voice dinsa,sannan yayi shuru yana jin wani abu me kama da rai a jikinsa yana motsi.

"Bakaji me na fada ba maleek?......matar wani ce.....matar aure ce,sannan a yanzun bakaga kalar aikin da yake gaba na ba?.......rayuka ake dab da rasawa amma zancan soyayya kake maleek?,soyayya fa?,a irin wannan yanayin?,a irin wannan lokacin?" Ya qarashe maganan muryarsa tana sanyi ba kaman dazu ba.

Idanu maleek ya janye yana lumshesu sannan ya girgiza kai sosai.

"Is okay.....shikenan......amma bayan hankula sun kwanta naka bazai taba kwanciya ba.....bayan ka kammala wannan aikin a sannan ne zakasan girman aikin dake gabanka,sabon babi zaka bude captain" Maleek yakai qarshen maganar yana miqewa tsam,ya dauki mug daya na coffee kawai ya soma takawa yana barin gurin.

Wani abu yakeji yana yamutsawa a kansa da qirjinsa......yana kuma qaryata maleek karon farko a dukkanin wani hasashensa......yanaji cewa abinda ke gabansa ya danne abinda maleek din yake magana akai. Ta yaya zaiso yarinyar da bai ganta sau goma ba a rayuwarsa?,yarinya da tako ina dabi'unta basuyi masa ba?,yarinyar data shigo ne kawai cikin aikinsa da tsarinsa?,uwa uba kuma MATAR WANI?,Duk da yana qoqarin ganin WAYE WANIN nan kafin takai ga zuwa gidansa?. Yana gudun isarta ga hannun mutumin da nan gaba dashi sultane zaiyi kuka......yana gudun shiga cikin tsarikan mammina da yayi imanin ta gama hada dukkan wani target dinta. Ya tabbatar da cewa wannan auren SHIRYASHI AKAI akwai tsararru kuma shiryayyun manufofi a qarqashinsa......ta yaya zai bari daidai da taqi daya ya zamana yana da gudunmawa wajen tabbatuwar tsarinta masu rushe rayuwa?.

"Bishi" Yace da omar kansa tsaye yana hade dukkanin girar sama data qasa tasa.

"Yes sir" Omar ya fadi kawai yana yunqurawa gami da miqewa yana danne wani abu me kama da dariya can qasan ransa. Yana tare da maleek a wannan hasashen,daga inda yake yana ganin zurfin nazarin da haisam din ya fada,zurfin nazari kuma yana faruwa ne ga haisam a bisa dukkan abinda ya bawa muhimmanci ne kadai.

*TAMIM*

*_MABUDI/MAFARI_*

_YANZU QADDARAR ZATA FARA_

A dukkan wani gaba ta jikinsa da jini yake iya wanzuwa a gurin....a dukkan wani tsoka dake da alhakin ji(feeling) yana jin wani gagarumin tashin hankali yana saukar masa.

Ya bude yatsun hannunsa......yayi qididdigen shekarun daya dauka yana bauta mata har sau ba adadi......yayi lissafi har baisan sau nawa ba......ya sake maimaita lissafin har yana bacewa daga qa'idarsa.

Yayi YAKANA yayi JURIYA ya kuma KAUDA KAI daga kan yarinyar a dukkan shekarun. Ya adana ya kuma tattala dukkan wani KWADAYINSA duk da irin tarin damarmakin da ya samu,yake dashi akan tabbas ZAITUNA zata fahimceshi tun bai furta abinda ke ransa ba......zaituna zata fahimci yaren cikin idanunsa da zuciyarsa ta kuma tattala masa TUKUCINSA a sanda zai buqaci haka. Yayi zaton shiga tsakanin burin TUKUICINSA mutuwa ce kawai,wadda yayita addu'ar kada ta daukeshi ba tare daya cika wannan burin nasa ba.

Yayiya qoqarin sake tunzura wutar nesantata da kowanne d'a namiji,a fili da bayyane,ya samu nasarori masu yawa,ya kwanta duk wata qura da tashin hankali sun biyo ta kansa,sai yanzu kuma ya zamana cikin HASARARRU?.

Qafarsa ya buga,yana jin wani qarfin zuciyar tunkarar duk wani abu da zai masa silar rasata ko nesantata dashi komai girmansa......ballantana almaz din da ta kowacce hanya yana da qarfin ikon ruguzashi ya kuma ruguza komai cikin sauqi.

"Giwa na kiranka shugaba" Yaji an furta daga bayansa cikin girmamawa. Waiwayowa yayi ya zuba idanu akan bawan. Bawan da akayi domin ya zama photocopy dinsa,bawan daya dauka ya mallaka masa irin sunansa.

"Yaushe ta buqaci ganina?".

"Tace yanzun nan,don tana da baqin da take sallama". Siririn tsaki yaja,yana jin kamar yabi shawarar da daya sashen na zuciyarsa suke bashi,saidai yaka tuna da wani abu wanda shi kadai ne yake masa shamaki.

Kewaye yaron yayi ya fara takawa ta gabansa,shi kuma ya rufa masa baya cikin matuqar biyayya.

*MAMMINA*

Idan kaga yadda take hidima cikin jama'arta,gami da kai kawo a cikinsu,ci gaba da rabon kyautututtuka masu nauyi da girman gaske ga duk wanda Allah ya tsaga yana da rabo. Ta bude qofa sosai ga.masu son ganinta da masu son gaisheta saboda yanayin farincikin da take ciki,tana so kuma ta sake jaddadawa kowa,kowa kuma ya shaida cewa da gasken gaske tana auren diyar da tafiso duk duniya ne sama da kowaaka.

Daga yanayin giftawar yalwa ta tabbatar da isowar tamim,don haka ta miqe tana bada umarnin dakatar da ganinta har sai zuwa gobe.

A yau akwai abubuwa da yawa da takeso ta dasa harsashinsu,harsashin da zai zama wani tushe kuma sanadin da zai qarasa tarwatsa rayuwar dukkan wani mutum daya kasance ahali ko tsatson diory hamani......zai qarasa sanya giyar takaici baqinciki da bacin rai cikin ruhi da gangar jikin duk wani ahalin safeena......giyar bacin ran da zata yita bugar da kowannensu har izuwa numfashinsa na qarshe.

Yana tsaye saman qafafunsa,yana kuma goye da hannuwansa a qirjinsa,saidai takun shigowarta ya sanyashi daidaita nutsuwa da yanayinsa zuwa yanayin da suka saba.

"Zauna" Tace da tamim bayan ta zauna. Zama yayi kaman yadda ta buqata,saidai kuma zuciyarsa tana gaya masa a irin wannan lokacin kamata yayi ace darajarsa ya d'aga daga wadda yake kai yanzu zuwa mataki na gaba.....matakin daya tabbatar banda tayi masa shigo shigo ba zurfi da qudundune shine yanzu akai,ba wancan tsintaccen magen ba almaz.

"Ina fatan gidan ango ya kammala ko?" A nutse tamim ya jinjina kansa,yana jin wani abu me ciwo yana tsaye masa a wuya

"An kammala komai"

"Yayi kyau.....inajin dadin aikinka tamim qwarai da gaske......a bisa al'ada yau zataje ta kwana a gidan,gobe da asuba ya rakota da kanshi.....to amma nasan abune me wahalan gaske ta yarda da hakan,don haka na yanke shawarar fara qulla kusanci a tsakaninsu....." Saita dan dakata tana sanin murmushin dake nuna zallar farinciki.

"Zai bita Niamey a satin nan kamar yadda ta tsara zata tafi,duk da har yanzu ban yarda zai iya karbarmin ragowar kamfanin sahel ba......amma tafiyarsu tare nada tarin alfanu masu yawan gaske......a yau zan tilasta mata ganawa dashi koda ba zata shiga gidanta ta kwana ba......akwai maganganun da nakeso yayi da ita,na sanya an rubucesu a killace....duka hirar da zaiyi da ita yau a killace take a rubuce,banason ya dara daga abinda na tsara. Yana da kwanya fiye da yadda kake tunani,tabbas nasan zai haddaceta kamar yadda nakeso,kaje masa da ita,da yammaci ina buqatar a rakoshi cikin ayari.......ya zamana cikin shigar alfarma ta gasken gaske......ka tunasar dashi,kada ya nuna zalama ko rawar kai.....kada ya nuna mata damuwa ko kulawa me yawa.......a jininta ta tsani wadannan dabi'un.....amma a halittarta tanason namijin dake dasu". Mammina takai qarshe tana bashi takardar dake ajiye a gefe tuntuni.

"An gama....cikar umarninki shine muradinmu" Ya fada da zallar girmamawa yana hade hannuwansa guri guda. Murmushin farinciki ta saki tana gyada kai.

"Saura kadan na mallaka maka shugabancin gidannan tamim......yadda kayimin rana da alfanu masu yawan gaske,dole kaima ka amfana daga falalata me fadin gaske" Ta fadi da gasken gaske saboda jin dadin yadda ko sau daya bai taba jawo mata asara faduwa ko musanta umarninta ba.

Kai ya jinjina mata yana jaddada godiyarsa,saidai kuma abinda ke kaikawo a zuciyarsa yasha bambam da tazara me tarin yawa da abinda ke bayyane a zahiri.

Iska ta zuqa me yawa tana fesar da ita,har yanzu murmushi yaqi gushewa daga kan fuskarta,saita kira yalwa da dama ba nisa tayi ba.

"Ki daukomin alkyabbata,zani gurin akhnan".

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"An gama" Ta amsa mata tana fita da sassarfa.

D'ai d'ai take takawa tana kallon gidan,da yadda ko ina dokar haisam ke aiki duk da yana kwance baida lafiya. A baya qona mata rai abun yake,amma a yanzun saita saki dariya hankali kwance. Tana wassafa yadda aikinta zai sauka a kansa hankali kwance bayan ta ga tabbatuwar dinkewar alaqa me danqo tsakanin akhnan da almaz. Taci alwashi ta kumayi rantsuwa tabbas saita sanyashi ya kwashe kayansa cikin dare yabar agadez,don ko guduwar tasa bazaya iya bari kowa ya sani ba saboda munin abinda zata sanyashi ya aikata. Da wannan hasashen ta isa sassan akhnan din hankali kwance cikin tarin girmamawa da dukkan hadiman sassan suka zube suna bata.

*AKHNAN*

Kwanaki ukun nan da suka shude gaba daya bata da aiki sai kwanciya,bata da wani aiki sai kebe kanta ita kadai. Bata qaunar wata hayaniya,bata son doguwar magana ko dogon surutu. Kusan salla ce kadai ke tayar da ita,sai wani lokaci da takan bude wani sashe na balcony dinta. Shima ba kasafai ba,don bata son ganin kowa kamar yadda batason kowa ya ganta. An shaida mata saqon morsa safiyya harma da Nannie dakeson ganinta,amma tayi biris da aiken kowa,kamar yadda taqi yarda kowa ya ganta. A yadda take jinta ma gaba daya ko mammina ke son ganinta saidai tayi haquri,kawai tana qoqarin digesting din komai ne,tana qoqarin haqurqurtar da zuciyarta nema tayi accepting wai an daura mata aure......wai ta zama matar aure....mafarkin da take hangoshi da nisan gaske gashi ya cimmata a lokaci qalilan.

Tayi juyi tayi juyi,tayi tsaki har batasan adadinsa ba. Yanzun meye ribar wannan abun da sultane ya tursasa tayi?. Wannan aure da suka dage a kansa meye ne ribarsa?. Ita bata hangen komai a cikinsa sai wata irin rayuwa maras 'yanci,sai wata zallar takura da kashe dukkan burin rayuwa da yake cikin ruhi da gangar jiki. Saita maida idanunta ta lumshe tana qoqarin tsara yadda zata maida rayuwarta daidai kaman yadda take a baya.

Kai tsaye taji an murza qofar dakin nata a hankali,bata wani damu da bude idanun nata ba,saboda tasan koma waye da zai taks dokarta,ya tsallake mata doka to bazai wuce MAMMINA ba.

Bata motsa ba har zuwa sanda mammina ke takowa inda take a kwance. Can qasar zuciyarta tana mamaki,tasan da gaske taji motsinta,ta kuma ji shigowarta,amma bata motsa da nufin tarbarta ba kaman yadda ta saba?. Wani shu'umin murmushi ta saki kawai tana danne zuciyarta.

"Saura qiris ki rasa wannan gatan......saura qiris ki rasa wannan izzar.....saura kadan ki fahimci ke wulaqantacciya ce abar qyama,zaki biya dukkan wani farashi da safeena ta tafi bata biyashi ba". Ta fadi qasan ranta a fili kuma tana zama daidai qafafunta.

"Biftu?" Mammina ta kirata a tausashe. Kamar ba zata amsa ba,sai kuma ta tuna MAMMINA ce fa.....mammina dinta,wadda ke tsaiwa kaida fata wajen farincikinta,sai ta motsa labbanta a hankali.

"Na'am" Ta amsa a hankali.

"Tashi biftu" Shuru ya ratsa kadan,sannan a hankali ta juya tana miqewa,ta zauna sosai hadi da sanya hannunta tana tattare sassalkar gashinta da ya ware ribbon din yayi nasa gurin daban.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 54*

Idanu mammina ta lumshe tana kuma budesu idon nata akan akhnan din. Duk da yanayin da take ciki ba abinda ya gusar da wannan sassanyan kyan......wannan kyan irin na safeena......wannan kyan da ya zamewa rayuwarta dukka qalubale da baqincikin da har kawo yau ba wani abu daya sassauta a ranta. Wannan kyan tana fatan lokacin gushewarsa ya zama a kurkusa.......a shafe tarihinsa cikin qasar agadez. Shi ta yaya ma wai zata bari AKHNAN ta fita daga tasarrufinta?. Ta yaya zata yarda tabar ruhin safeena ya kwanta lafiya cikin kusewarsa?. Yadda ta sanya darare da yawa na rayuwarta suka gagara zuwan mata da dadi,haka takeso tayita rasa nata dararen a qasan kushewa cikin baqinciki da takaici.

A zahiri hannuwan akhnan din ta kamo a tausashe,har yadda tayi din ya sanya akhnan duban idanunta,tashin farko kuma ta hangi wannan tsantsar qaunar da kulawar data saba gani a tare da mammina din.

"Ina cikin tsananin farinciki yau biftu,kinsan saboda me?" Kai ta girgixa a hankali.

"Yadda naji sultane yana jero miki addu'o'i na sanya albarka cikin masallacin haram. Yadda sultane ya nunamin duk wani fushi da yakeyi da ke ya kau,yadda sultane ya nunamin ya.yafe miki,kuma a yanzun kin koma akhnan dinsa ta tun tale tale" Wata nannauyar ajiyar zuciya ta saki tana jin wani nauyi dake kwance a qirjinta yana raguwa. Wani sanyi taji gami da sassauci yana sauka saman zuciyarta,sai takejin wani girma da qaunar mammina suna saukar mata. Duk wani kyakkyawan albishir na alkhairi daga bakin mammina take fara jinsa,ita daya ce take dauke da dukkan wani albishir me dadi da zai faranta rayuwarta da duniyarta.

"Amma kinsan wasu lokutan nakanji nadama tana saukarmin na hadaki da almaz?" Ta furta muryarta can qasa tana kuma sadda kanta qasa jikinta yana nuna wani irin mugun laushi da yayi.

"Mammina......nadama wacce iri?" Ta tambayeta tana jin wani fargaba kadan. Kai ta daga tana sake kallonta.

"Nayi wannan abunne don na samar miki da 'yancinki,ki sake cikin rayuwarki kamar yadda kikeso,amma abun mamaki shine.....sai walwalarki take raguwa,takura take maye gurbin sakewa,me yayi zafi biftu?,bayan a yanzunne kike da 'yancin yin kowacce rayuwa da kike so?" Kai ta girgixa a hankali,tana jin wannan raunin nata da bata bari kowa ya gani yana taso mata.

"Ban saba bane mammina.....a hankali zan saba zan saki jikina".

" Amma ko kinsan wannan rashin sabon naki yana aje ayar tambaya me yawa saman zuciyar mutane a kaina da kanki?......kinsan yau ne ranar da za'a rakaki kwanan gida?" Kai ta daga da sauri ta zubewa mammina wadannan blue eyes din. Karon farko da mammina taji kalar kallon akhnan din ya mata nauyi gami da haifar da wata jaririyar faduwar gaba.

"Mammina.....kwanan gida?.....ni da almaz?" Ta furta da sigar tambaya me wani irin nauyi.

Kai ta jinjina mata cikin bata tabbaci,sannan tace.

"Haka yake a al'adar buzaye......haka yake tun kaka da kakanni,indai baso kike ki fadawa duniya cewa almaz ba zabinki bane". Shuru akhnan tayi,wai tana qoqarin daidaita kanta tana kuma qoqarin daidaita abinda takeji a qirjinta. Wani kwana ne da amarya zatayi guda daya tal a gidanta da ango,sannan washegari ya rakota ta dawo gidansu,sannan a sake shiryata a maidata.

Kai ta shiga girgzawa don ta kasa tausar zuciyarta ta karbi maganar. Sam ba zata iya ba......ba zata iya bin kowacce al'ada da akazo da ita ba wai akan aure,to a wanne dalili ma?,auren da dole ce ta kaita ga yinsa,dolen amintar da sultane da maido kyakkyawan alaqansu ta baya.

"Bazan iya ba mammina.....ba,bazanje ba,ko sama da qasa zata hadu bazanje kwana da almaz gida daya ba a yanzun,qarshen satinnan zan wuce Niamey,bana buqatar wani tsari da zai sanya yace zai bini,ko ke kice saimun tafi tare". Numfashi mammina ta sauke a hankali,dama ta sani,tasan za'a rina,kuma dama itama bata shirya tilastata kwana gida tare da almaz ba,to amma kuma tafiya Niamey bata hangen wani abu da zai sanya ta rushe tsarin tafiyarsu a tare.

"Bazan tilasta miki ba biftu......zan sauya tsarin,saboda ya kasance dole a al'ada kuyi zaman fahimtar juna a yau,zaizo ku gana ke dashi din koda cikin gidan nan ne" Shuru akhnan tayi tana jujjuya abun. Shin meye abun damuwar cika komai da al'ada tazo dashi ne?,meye abun damuwar saita gana da mijin da HOTO ne kawai da TAKE na suna a bayan sunanta?.

Readers Also Read

More by Huguma