L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 11
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 11: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 11. "Dole al'ummar agadez dana nijer gaba daya su dinga…
3,351 words
"Dole al'ummar agadez dana nijer gaba daya su dinga alfahari da wanzuwarki a cikinsu. To amma kuma idan ba damuwa,ko zamu iya sanin asalin salsalar tushenki?" Yayi maganar da sautin daya buga amsa kuwwa cikin dakin taron.
Wani irin dummmm taji cikin kanta,zuciyarta ta wani irin mahaukacin bugawa da har taji kaman tana neman amayota ta wuyanta,sai kuma tayi saurin controlling din kanta sanda ta tuna adadin cameras din dake gabanta ta saki murmushi.
"Ina zaton baka dade da shigowa agadez ba.....ko kuma kai din baqo ne ko?" Idanu yadan zuba mata,sannan ya saki murmushi yana cewa.
"Allah ya taimakeki.......cikkaken haifaffen nijer nake......tun daga kakana na goma zuwa yau.....kawai dai munaso muji daga bakinki ne" Kai ta jinjina tana qoqarin boye fushinta akan yaron,don a ranta sai takejin kamar baqar magana ya gaya mata.
"Ni dinma kamar kai,haifaffiyar nan ce kaka da kakanni.....bansan wata qasar ba bayan wannan......basan wasu al'ummar ba bayan al'ummar qasata ta nijer.......wannan ya sanya nake tsananin kishin mutane na" Ta qarashe da murmushi.
Tafi kuwa suka dauka gaba daya,abinda ya bata relief sosai taci gaba da binsu da murmushi tana addu'ar tambayar ta tsaya iya nan,saidai fatanta da addu'arta basu cilla ko ina ba wata tambayar ta sake shigowa.
"Naji dadin wannan amsar taki,saboda a guraren hira daban daban,wasu na yad'a qarairayin kamar ke din baquwar haure ce iyaye ko kakanni suka shigo" Kai ta gyada cikin nutsuwa.
"Tom....naji dadin haduwarku da adadi me yawa haka......yau zan tabbatarwa da duk me kokwanto qasata da asalina" Saita waiwaya tana duban tafisu,tayi magana da ita qasa qasa,tafisu ta tashi ta wuce,ita kuma ta maido hankalinta kansu.
"Ku jira lokaci kadan,zan baku takardun da zaku yada don kauda wannan zargin daga zuciyar kowa" Ta qarasa fada tana murmushi,duk da zuciyarta cunkushe take da haushin yaron daya tsiro da tambayar,kuma wani irin zargin me qarfi taji ya d'arsu a ranta game dashi,gwara ta nuna musu cikakkun takardunta don kashe wannan rade radin da bataso yayi nisa ko kadan.
Ci gaba tayi da amsa tambayoyinsu na daban,har zuwa sanda tafisu ta qaraso gurin.
"Miqa musu su shaidawa duniya" Mammina ta fada tana murmushi.
Kai tsaye kuwa tafisu harda tuntuben da mammina ta yaba dashi,ta kuma fassarashi dukka cikin saurin isar da saqonta ne ya kawo hakan ta miqawa dandanzon 'yan jarida takardun.
Sannu a hankali suka bude takardun,cikin qasa da mintuna uku suka fara zagayawa a tsakaninsu,wannan ya duba ya miqawa wannan,sai wasu daga cikin su suka fara daukan hotunansu suna miqawa 'yan uwansu.
Ko kusa ko alama bata kula ba,saboda sauran tambayoyin da take amsawa wani d'an jarida daban daya karbi ragamar tambayoyin,har sai da taji kamar sautin maganganu qasa qasa ya fara tashi a gurin.
Idanunta ta aza a kansu,takardun sun fara nisa daga mutanen dake gaba gaba zuwa baya.
"Bakusan a inda kuke bane,bada hujja zai zama kuna yawo da takardu masu muhimmanci haka a tsakaninku?" Tafisu ta fada cikin tsare gida,ta kuma fadi abinda mammina keson fada musu kenan.
"Kiyi haquri.....wani abune yadan rikitar damu,banbancin bayanai ne,bayanan da uwargida ke fada yasha banban matuqa da bayanan jikin takardar" Ya fada bayan ya karbo takardun yana sake kallonsu a hannunsa.
"Kamar yaya?" Mammina ta samu kanta da yin tambayar kai tsaye ba tare data jira tafisu tayi mata tambayar ba.
"Kiyi haquri ki sake dubawa ranki ya dade......takardu ne na qasar Ethiopia,cikakkiyar shaida.....shekarun haihuwa takardar haihuwa ta asibiti original ba jabu ba,harda sanya hannun shugaban qasar dake tabbatar da takardun na asali ne daga tushe ma". Batasan ta miqe ba,batasan kuma ta isa gaban tarin cameras din dake zagaye da ita ba ta, saka hannu ta fusgi takardun cikin fushi.
Gani take qarya kawai yake mata,gani take kawai ya fada ne saboda ya rikitar da ita,ya fada ne saboda alamunsa sun nuna akwai mummunan quduri a tattare dashi.
A birkice take kallon takardar kamar wadda bata taba karatun boko ba. A gigice take bin rubutun daki daki tana karantawa. Takardar zama haifaffiya kuma mallakin qasar Ethiopia ce tabbas a hannunta,kamar dai yadda dan jaridan ya fada da farko.
Idanunta ta daga tana duban tarin tulin 'yan press din da kowannensu shima ita yake kalla. Ta bisu daya bayan daya da idanu. A qalla sunkai mutum ashirin,daga mabanbantan gidajen tv dana radio. A cikinsu batasan adadij mutanen da suke da hoton takardar ba. Batasan adadin mutanen da suka watsa hotunan a take daga daukarsu ba,don ta tabbatar,babu ta yadda za'ayi labari me dumin gaske irin wannan ya shiga hannun d'an jarida ya kwana lafiya.
"Ranki ya dade......nace kodai akasi aka samu?,zaki iya mana cikakken bayanin ya akayi haka ta faru?" Ya sake cusa mata tambayar yana saita camera dinsa.
Idanu ta zuba masa da wani irin wulaqantaccen kallo. Ta sani.....taba d'an jarida abune me hadarin gaske,bashi kadai bama harda iyalinsa gaba daya,koda shi daya ne a guri ballantana gurin cike yake da abokan aikinsa?.
"Ayimin afuwa.....wataqila takardun sun cakuda da wasu,zan nemeku idan komai ya daidaita" Abinda ta fadi kenan,bata kuma tsaya jira ba,bata tsaya jin tarin tambayoyinsu ba ta juya a gaggauce tana wucewa. Tana iya jin muryoyinsu suna jefa tarin tambayoyi mabanbanta,to amma ko tsaiwa qafafunta ba zasu iya ba ballantana ta fuskancesu.
"Tabbas..... Akwai wanda yayimin kutse dakin ma'ajiyar sirrina......tamim!!!!.....zaka mutu,tabbas zaka mutu idan baka bincikomin abinda ke faruwa ba,bayan komai a hannunka yake?!" Ta fada cikin qaraji kaman wata tababbiya. Cikin kanta da ranta takejin tabbas idan har an taba wannan dakin......to bata da wani sauran qwarin gwiwa. Ta jima tana saka ranar da zata shiga ta kwashe wasu kaya a ciki ta qonesu amma sai ta manta.....don ta tabbatar wanzuwarsu a tare da ita mugun hadari ne,duk da tasan tayi kafuwar da babu me banbareta cikin agadez. Ko bayaga haka,idan an matsanta banbareta,to bomabomai ne zasu dinga fashewa daya bayan daya da sunan sarkinsu dama diyar da yafi qauna duk duniya.
Hannunta har rawa yake sanda ta karbi takardar da tamim ke miqo mata sanda yake shigowa dakin da wani irin kwantaccen tsoro saman fuskarsa. Jikinsa dukka rawa yake,kaman yadda haqoransa ke haduwa kaf kaf kaf saboda tsananin tsoro kaika dauka wanka aka masa da ruwan qanqara.
*_Bismillahir Rahmanir rahim_*
*_Wamay yihinullahu fama lahu mimmukrim_*
*_Alaisallahu bi khafin abdah?_*
*_SHEIKH MUHAMMAD HAISAM MOTI ABA JIFAR IBRAHEEM the silent one_*
Duk da cewa sakin layin qarshe na takardar kawai ta fahimta.......wani irin girgiza zuciyarta tayi. Sunan IBRAHEEM kadai wata babbar barazana ce ga zaman lafiyarta......ballantana ta ganshi hade da sunan da dazu dazu ta gama bankwana dashi cike da farincikin ya tafi babbar dama ta samu a gareta.
*_Shin ubangiji bai isarwa bawansa ba?_*
*_Dukkan wanda Allah ya wulaqanta lallai bashi da wani wanda zai girmamashi_* wannan sune fassarar abinda ke rubuce a tarin tulin takardun nan" Tafisu ta fada tana sake nutsa hannunta cikin takardun da dukkaninsu rubutu daya ne a ciki,kuma sune suka maye gurbin duk wani file da a cikinsa a baya can muhimman takardunta ne a ciki.
"Innalillahi......na shiga uku!" Ta samu kanta da furtawa,a karon farko da rauninta ya bayyana muraran,ta sulale tana zama dabas a gurin a gaban tamim da tafisu tana manta meye ma matsayinta!!!.
★★ Karo na farko a rayuwarta da takejin wani namiji haka dan da dab kusa da ita. Karon farko kenan da takejin wani irin kariya da tsaro suna bibiye da ita. Dukkan wani taku nata qwaya daya da zata sauke zaya sauke nashi a tare da ita,hakanan koda wani sashe na mayafi ko abayarta ya tattare tana iya jin yadda hannunsa ke kaiwa gurin ya gyara zamansa sosai a jikinta.
A duk sanda yayi hakan......wani abu daban yake saukarw a jikinta da ruhinta.....wani yanayi takeji na izzar da bata tana jin makamanciyarta ba.
Tun daga faarfajiyar airport na agadez bata sake saka falaaq da maleek a idanunta ba,bawai don ta damu ko akwai sabo da shaquwa me yawa ba.....aah,haka kawai lokaci lokaci sai zuciyarta ta gaya mata a yanzun bata da wani sama da falaaq din.
Blue eyes dinta ta daga a nutse ganin ba wani cikowa ko mutane.......karo na biyu wani mamakin ya kasheta bayan wanda ta shiga a airport na agadez ganin private jet din da daga ita saishi ya daukosu ya kuma ajiyesu a nan Niamey din.
"Private terminal?" Ta fadi a hankali idanunta akan private jet na biyu da suke tunkara wanda yasha banban da wanda ya kawo su Niamey din.
"Me yake faruwa?" Ta furta can qasan ranta.
"Alfarma ce dashi haka?" Ta sake tambayar kanta da kanta daidai sanda sauran ma'aikatan dake gurin suke gaidashi cikin tarba ta musamman da kuma girmamawa,saidai duk maganan da suke kaman a agadez da wani yare ne da bata jinsa bata kuma ganewa,amma yanayin girman da suke bashi sai abun yake sake jefata cikin duhu.
_yanzu kika fara shiga duhu akhnan?,ko baki fara shiga bama?_
*_yan uwana masoyana assalamu alaikum warahmatullah_*
*_gaisuwa da fatan alkhairi,biki gareni na sisters dina har biyu,ina neman uzuri da afuwa idan har kuka jini shuru laraba alhamis da juma'a,duk da zanyi dukkan qoqari tuquru naga ban tsallake muku kwanakin ba in sha Allah,saboda halin rayuwa da yanayin biki,amma koda page bibbiyu ko daya daya ne ya samu zan qoqarta kada na barku haka_
_na gode muku qwarai da gaske,in sha Allah huguma ba zata baku kunya ba_🙏🏽🙏🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 20*
*_Assalamu alaikum warahmatullah_*
*_welcome back diaries,na gode sosai da tarin addu'o'inku ga amare,mun kammala lafiya alhmdlh,Allah ya qara zumunci ya sassaka muku da alkhairi_*
Har cikin qasusuwanta wani irin mamaki yake ratsawa,mamakin da ya sanya takejin wani irin yanayi na rashin sakewa a tare da ita.
"Bonsoir, Madame. Soyez la bienvenue. Permettez-moi de prendre votre bagage(barka da yamma madame,muna miki barka da zuwa,ki bani dama na karbi jakarki)". Taji an fada cikin girmamawa.
A hankali ta daga kanta zuwa fuskar wadda ke maganan. Daya daga cikin ma'aikatan jirgin ce,matashiya fara sol da ita,wadda koda ba'a gaya maka ba zakasan cewa bata hada komai da qasara niger ba. Saidai tana da wani irin kyau da kuma zubi na BUZAYE. Yana shigarta riga da skirt ne da kana kallonsu kasan uniform ne,saidai sun fidda shape dinta,sun mata kuma wani irin mugun kyau. Qaramin hijab ne a jikinta da bai kammala rufe qugunta ba,sannan bai hana idanu su gane irin shape da kyan da take dashi.
Idanunta akhnan ta dauke a hankali,da salon izzar nan tata daya zame mata al'ada kuma dabi'a ta miqa mata jakar ba tare da tace mata komai ba. Kadan ta rusuna,sannan ta saka hannu biyu ta karbi jakar,saidai kafin ta juya gaba daya saita waiwaya sashen da haisam yake.
"BonBonsoir, Monsieur.” Ta furta a ladabce tana rusunawa tana duban haisam din. A nutse akhnan ta daga idanunta tana satar kallonsa ta gefan idanunta da wani yanayi,yanayin da batasan me yaja hankalinta zuwa gareshi ba sanda crew din ke gaidashi ba......batasan me takeson gani ba,amma tanaso taga fuskarsa ne haka kurum,tana so taga idanunsa.
Murmushi kadan yayi,cikin nutsuwa da kamewarsa dinnan. Har kayi zaton kamar bazai amsa ba sai kuma muryarsa me cike da tarin nutsuwar nan ta motsa.
"Bonsoir" Wani irin numfashi taja,numfashi me nauyi,a karon farko tana juya
"Da gaske numfashi yana nauyi a qirjin mutum" Wani abu yana matse zuciyarta . Murmushinsa......wani abu da ba zata iya tunawa ta taba gani ba a tattare dashi. Zata iya cewa ma bata taba ganin ba kai tsaye,tafi ganin izzarsa......tafi ganin qasaitarsa.....tafi kuma ganin girman kansa a fili sama da komai.
"Ya kalleta bayan ta kalleshi" Wata zuciyar ta gaya mata a hankali. Saita tuna,sau nawa tana satar kallonsa ita amma sai taga ba ita yake kalla ba?,sau nawa tana saka ran ganin idanunshi a kanta amma sai ta tarar ba ita yake kalla ba. Me yasa?,me yasa ya daga idanun nan nasa masu girma ya sauke akan crew din.....me yasa itama take kallonsa haka?.
"Me yasa kika damu?" Tambayar da zuciyarta tayi mata kenan,tambayar kuma data sanyata saurin dauke hankalinta daga gurin kamar ba komai,saidai har yanzu matsewar nan da qirjinta yayi bataji ya saki ba,musamman data hangi murmushi shimfide saman fuskar crew din data fara takawa a hankali.
"Zan iya riqe jakata" Ta furta da hausa a wannan karon tanason lissafi wanne yare ce matar?.
Tsayawa tayi cak crew din,yaji saukar maganar a kunnensa......amma yayi kamar baiji ba
"Bien sûr madame" Ta fadi da girmamawa tana miqa mata jakar da hannu biyu cikin girmamawa.
Fuskarta a dinke tsaf take takawa tana biye dashi,saidai kuma a hankali ta fahimci ya sassauta yanayin qasaitacciyar tafiyar nan tasa,a hankali ta riskeshi......a hankali kuma ta daidaita dashi,sai a sannan kuma ta fahimci jerawa yake nufin suyi.
Idanunta zube a gabansu,tana hangen wasu mutane dab da private jet din tsaye cikin sahu da wani yanayi na girmamawa. Idan ta lura da kyau,dukkaninsu sanye suke da kalan kala guda daya. Baqaqen suit da farar shirt daga ciki.
A hankali takejin iska tana shigar da qamshin nan nasa sosai cikin hancinta,qamshin daya tabbatar mata ya sake matsowa dab da ita ne,kafin kuma tayi kowanne motsi ta tsinci lallausan tafin hannunsa cikin nata.
Wani abu ya tsarga mata tun daga kanta zuwa tafin qafafunta,wani abu me kama da magnet daya tilastata lumshe blue eyes dinta tana kuma sauraron wani irin bugu da zuciyarta keyi. A hankali taji ya zame jakar hannunta data karba daga hannun crew din,ya maidata daya hannun nasa,sannan ya sake dawowa da hannun nasa yana sake cusashi cikin tsakiyar tafin hannunta.
Wani abu ya ratsa tsakaninsu,tun daga tafukan hannuwansu zuwa sassan jikinsu,wani irin dumi wani irin yanayi daya sake sanyawa tafiyar tasu ta sake zama very slow.
Yana ji a ransa kamar ya murza tafin hannunsa sosai cikin nata,yana ji kamar ya manna tafin hannun sama da yadda ya manna a yanzu. Wani abu yakeji da bai taba jin irinsa ba......wani irin yanayi.....wani irin dumi tsakiyar tafin hannun nata da yake da dan damshi na gumi kadan. Yanayi ne da bai taba jinsa a tafin hannun kowa bama. To ta yaya ma zaiji?,bayan shi din koda huldar data shafi mata baya ciki ballantana yakai ga riqe hannun diyar kowa?. Idan da tafin hannun daya sani na 'yan uwansa ne maza yayin musabaha. Sukam ba wani wan yayi koda shige da irin wannan tafin hannun ballantana kamanni.
Cak ya dakata da tafiyar,abinda ya tilastata tsaiwa kenan,yayi taku biyu ya matsa gabanta kadan,dukka hannuwansa ya sanya ya jawo veil din kanta sosai yana rufe fuskarta kafadarta da qirjinta.
Idonta ta lumshe......tana jin wannan kusancin dake tsakaninsu......tana jin wannan qamshin wanda a yanzu yake cakude da dumin numfashinsa yana sauka daga saman goshinta ya gangaro zuwa hancinta saboda tsaho daya d'arata dashi. Sau tari tana raina tsahonta a duk sanda take tsaye haka a gabansa. Bata gane tsahonsa saita tsaya a gabansa taga yadda ya kere mata. Ta lura dashi.....giant ne.....wani irin giant dake da wahalar samu.....wani irin giant da tsahonsa ya dace da murjewar jikinsa,harma ba zakaga tsahon ba sai sanda kayi gigin hada kafada dashi.
Wani rawa taji qwayar idanunta sunayi sanda taji hannuwansa saman kafadarta,idanunta kan tsakiyar qirjinsa wadda data matsanta zubawa idanu taga yadda qirjin nasa yake motsawa da yanayin bugun lafiyayyar zuciyarsa.
"Boundaries please" Ya fada a hankali idanunsa suna lumshewa a cikin nata. Baisan wanne irin kishi Allah yayi masa ba,baisan wacce irin zuciya ce dashi haka ba......baisan me yasa ba,ko yaya yaga zashi doshi wani guri da ita,wani guri da yake cakude da maza sai yaji zuciyarsa tana matsewa.
Yadda yayi mata magana idanunsa cikin nata......yadda ya furta haruffan da wani irin sanyi da taushi......ta fahimceshi,ta fahimci me yake fada,duk da ba turanci ne yarenta ba,amma tana gane da yawa daga cikin maganan da za'ayi mata dashi sama da yadda zata maida.
Kasheta kawai takeji yanayi da idanunsa.......wani irin abu takeji yana saukar mata,abin daya soma narkar da wannan zafin da taji ya tsaya mata a wuya sanda crew din ke magana dashi. Still bai zare idanunsa daga nata ba.....ya sake miqa tattausan hannunsan nan da baya rabo ko yaushe da qamshin wani tsadajjen misk,dalilin da yasa komai ya riqe,kuma komai zai riqe koda na second daya ne qamshinsa daban yake.
"Muje" Ya sake fadi da wata murya da a yau takejin ta mata ta daban.
"Welcome sir" Kalman farko data fara ji dukkaninsu suna fadi kenan da girmamawa suna rusunawa.
"Sir?" Ta sake fadi can qasan ranta tana kuma maimaita kalmar,kamar dai yau ne karon farko da tasan kalmar a rayuwarta.
Tun daga isowarsu bakin jirgin......takawarsu zuwa ciki da shigarsu sai komai ya sake tsinke mata.
Wani irin luxury sofas jet din yake dashi......wani irin tsari da sam bai mata kama da tsarin jirgi ba,sai qananun gidaje na alfarma da aka tsara saboda hutawar gangar jiki da ruhi.
Cikin wani yanayi dake nuna zallar girmamawa,girmamawar data tilastawa akhnan satar kallon duk wani motsinsa pilot dama crew din da zasu kasance dasu cikin jirgin saboda hidima garesu suka gabatar masa da kansu gami da sake gaidashi.
"Na gode......ina fatan zakuji dadin tafiya dani" Ya fada da wani lallausan yanayi dake nuna zallar sanin kima da darajar dan adam.
Murmushi wasu sukayi da 'yar dariya,sannan daya daga cikin pilot din ya amsa masa.
"Karramawa ce a garemu yin tafiya tare dakai ranka ya dade" Ya fada yana rusunawa,sannan a hankali suka fara jayewa suna basu guri.
"Ranka ya dade" Ta sake nanatawa a hankali cikin kanta. Ta sake lumshe idanunta tana jin yadda wannan lallausan qamshin nasa......wannan turaren nasa yake sake cika jirgin,yake kuma sake cika inda suke zaunen,wanda banda window din da take iya hangen farfajiyar airport din ba zaka taba yarda cikin jirgi kake ba,don yafi mata kama da wani qawataccen parlor na alfarma.
Ta runtse idanunta a hankali sanda jirgin ya soma motsawa. A hankali zuciyarta ta danyi wani nauyi tana jin yanayin bugunta yana sauyawa. A yau itace zata bar agadez?......sannan kuma tabar Niamey gaba daya?. Yau zata bar sultane?.....zatabar company dinta......zatabar masarauta.....zatabar mahaifarta inda cibiyarta take. Zata bar kowa......zata bar komai,ba tare kuma da cikakken bayanin yaushe?......a wanne lokaci zata sake dawowa cikinta ba?.
Suwa zata samu a can inda zataje?,wacce rayuwa zatayi dasu?,dukka bata da wannan amsar kwata kwata.
A nutse ya kammala saka seatbelt dinsa,ya daidaita zamansa sanda jirgin yake ci gaba da saita gudu saman kwalta na adadin mintunan daya saba gabanin cirawarsa zuwa sama. Ya juya a nutse yana sauke idanunsa a kanta. Idanunta a lumshe suke,ta rufesu ruf,kaman yadda ta karkatar da fuskarta kadan zuwa window,saidai hakan bai hanashi ganin fuskar dama abinda ke shimfide akai ba.
Wani abu yaji ya sauka saman zuciyarsa a hankali,wani abu daya tuna masa da kalaman sultane. Amana......ya damqa amanarta a hannunsa.....eh koda sultane bai fada ba ya sani,mata amanace a hannun mazajensu,duk wanda ya cutatar ko ya quntata akwai mummunar makoma da sakamako akansa. Basu da qarfin komai.....basu da qarfin ikon yin jayayya ko challenge naka......amma suna da me qarfin masu qarfi daya tsaya musu.
A nutse ya miqa dogon hannunsa yana zagaye qugunta dashi don ya ciro seatbelt din da baiga tayi koda alamun sakawa ba. Yanayin daya haifar da wani irin kusanci me girma a tsakaninsu,yanayin kuma daya qara gudun zuciyarta dake lullube a qirjinta saboda hucin duminsa da taji dake gauraye da turaren nasa.
Ta bude idanunta ne da sauri don tantance me yake faruwa. Kai tsaye idanun nata suka sauka cikin nasa.......wadannan idanun da suka zama idanu na farko da suka fara yi mata nauyi cikin kanta. Idanu na farko da suka fara sakata abu ko su hanata ba tare da mamallakin idanun yace komai da ita ba. Idanun da sukayi wata ajiya me girma cikin kwanyarta dama zuciyarta.
Har yanzu still,ba wani abu daya canza.....har yanzu suna da wannan nauyin da ba zata iya jurewa kallonsu ba......dole ta maida nata idanun ta sake lumshesu a hankali kamar wadda kejin bacci,yanayin daya bashi daman dora qwayar idanunsa saman qirjinta,kallonsa ya sauka a kansu da wani irin sassanyan yanayin daya harba wani abu me tsananin qarfi zuwa ga sassan jikinsa.
Wani irin girrr hannayensa sukayi kaman wanda wutar lantarki taja sanda ya zagaya daya hannun nasa zuwa gefan qugunta yana soke belt din,abinda ya sanya jikinsa ya shafi tudun qirjinta kenan,tudun daya narkar da wani abu guda dake tsaye kyam a zuciyarsa wato JARUMTA.