Kenza eBookz

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 34

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 34

L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 34: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 34. "Ina safeenar......Allah yasa tana tare dani" Maganar…

3,335 words

"Ina safeenar......Allah yasa tana tare dani" Maganar data sanya komai tsaye musu cak. Wani kewa.....wata qauna ta mahaifiyarta ta taso mata,kawai saita kife kanta sosai saman hannunta dake cikin na nanay qwalla tana zuba.

Hakan da tayi ya sanyayar da jikin nanay sosai,cikin mutuwar jiki ta aza hannunta saman kan akhnan tana jin zuciyarta na wani irin bugawa

"Ya Allah......ya Allah" Ta fada a hankali,tana neman agaji ya bata juriyar abinda zataji.

Gabanta ya zagayo,ya kuma tsugunna saman qafafunsa a nutse. Nutsa hannunsa yayi tsakiyar nata hannun dake cikin na akhnan,sannan cikin softness yace

"Allah ya karbi kayarsa shekarun baya da suka wuce,amm....." Daga masa hannu tayi da sauri.

"Safiyya fa?"

"Tana nan,tana raye,tana agadez cikin qoshin lafiya" Wata iri nannauyan ajiyar zuciya ta sauke,hawaye suna son sake zubo mata amma ta sanya dukka jarumtarta tauhidinta da imaninta da Allah ta danneshi tare da fadin.

"Alhamdulillahi ala kulli haall.....Alhamdulillahi sirran wa jahran,Allah na gode maka,daka dauki safeena saika bamu copy dinta.....sannan ka barmin safiyyahta a raye,Allah ka gafarta mata cikin yalwatacciyar rahamarka" Duk da cikin wani yanayi take,amma sai taji amsa addu'ar ya zame mata dole,ta amsa a hankali labbanta suna motsawa.

Matso da akhnan tayi zuwa jikinta sosai,wata qauna dukka da takewa safeena tana jin tana tashi tana komawa kan akhnan din. Ta rumgumeta sosai cikin jikinta.

"Koda raina ne zan iya bawa safeena.......kisa a ranki safeenanki data mutu gata ta dawo......ni nanay,zan zamemiki sama da uwa idan akwai,duk dana sani.....kin samu komai daga safiyya" Idanunta ta lumshe a hankali,wata nutsuwa tana shigarta,yayin da rayuwarta da momma safiyya ta gilma ta idanunta.

"Me ya kawo haka?" Ta tambayi kanta,me yasa haka ya dinga faruwa tsakaninta da momma,me yasa sai daga qarshe take jinta kusa da zuciyarta kaman yadda takejin nanaya a yanzu?

"Ya sunanta.....sunanta na gaskiya"

"Khadeeja nanay.....sunanki aka mayar" Ya fadi sunan da wani irin yanayin da zai tabbatar maka yasan asalin sunan yadda yake,yadda ya fada ya qarawa sunan dadi da daraja,ya lumshe idanunsa yana budewa akan akhnan wadda tayi suman zaune.

"Ya akayi yasan every details haka a kanta?,yaushe yasan sunan Nanay aka saka mata?,da gaske sunan nanay dinne?,wanne irin aminci ne haka a tsakaninsu?,zataso taji......zataso ta samu wannan cikakken labarin.

"Allah sarki....Allah sarki" Kawai nanay ke maimaitawa tana tuna girman qaunar dake tsakani.

"Nanay.....kun manta damu?"muryar noorah wadda tayi magana a shagwabe da Aanani ta turota ya ratsa kunnnensu. Bata shigo parlor din ba,tana daga bayan qofar tayi maganar.

Yanayin maganarta ya bawa haisam da nanay dariya,akhnan batace komai ba,don da harshen oromo tayi magana bata gane me tace ba,bayan siririyar muryar dake nuna mata qaramar yarinya ce take magana.

"Zamu qarasa magana nanay" Ya fada yana miqewa a hankali yaja baya.

"Tabbas......ya kamata takwarata tasan wace mamanta....kama matarka ta tashi" Nanay ta fada tana zame hannunta daga cikin na akhnan,saidai har yanzu ta gagara daina kallonta,da wani irin murmushin qauna da soyayya shimfide kan fuskar nanay din,saita soma takawa tana nufar qofa ganin akhnan din taqi motsawa,alamu kunya dukka suna bayyana a tattare da ita

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 61*

Idanu sosai ya zuba mata bayan fitar nanay din,a hankali ya tako zuwa gabanta. Da gaske tausayinta yakeji sosai yana ratsa cikin zuciyarsa,irin tausayin da bai taba jin irinsa akan kowa ba. Ya lura akwai wani nauyi na nanay dake tsakiyar qwayar idanunta,to amma baisan meye ya kawoshi ba.

Bai tsaya miqa mata hannu ko yin magana da ita akan ta tashi ba. Kawai ya sanya dukka hannuwansa biyu ne ya dagota. Ya dagota ne a bazata,wannan ya kassara kowanne karsashi nata ya sanya ta fada jikinsa hankali kwance. Wannan faffadan qirjin da qamshinsa ya zame mata JARRABI....qamshi na biyu kenan a duk duniya da take jin yana fiddata daga duniyar da take bayan qamshinsa na anihi da wannan turaren da na shuwa incense and more.

Hannunta tasa da niyyar tureshi,saboda irin wannan rungumar da yayi mata ya sanya dukka qarfinsa ya riqeta da kyau,don haka ko motsawa kafadunsa basuyi ba ballantana ta saka ran zai matsa daga kusancin da yake tsakaninsu.

Batason wannan kallon.....wannan kallon na tsakiyar idanu da yake mata,yana qara yawaita rauninta,yana sake sanyawa ta jita wani iri,yana kuma sake haukata yanayin da takeji cikin jikinta.

Sosai yake kallon cikin idanunta,wanda hawaye ya jiqe mata eye lashes dinta ya sake sanyawa suka zama zara zara. Yatsansa ya miqa a hankali ya dora saman eyelashes din,taja wani irin numfashi tana lumshe idanun nata. Hakan sai ya qara mata kyau sosai a idanunsa,hawayen suka zama kamar wata rumfa tsakanin qwayar idanuwan nata.

Yatsu uku ya sanya yana goge mata hawayen a hankali yana sake kallon fuskarta. Komai nata na zaune akan tsari.....komai nata kaman ta zaba....komai yayi daidai da yanayinta da sigarta. Cikakkiyar girarta data dace da hancinta me tsaho da tudu.....dan qaramin bakinta me dauke da siraran labba.....

A duk sanda yatsunsa suka sauka saman fuskarta sai taji wani abu yana ratsa sassan jikinta,wani abu me kama da yawon kiyashi a jikinta. Can qasan ranta kuma tana sake juya komai a kansa,zuwa yanzu al'amarinsa ya fara bata tsoro.......al'amarinsa ya zarta dukka inda take zato.

"Yaushe?,ya akayi?,ya akayi yasan komai daya danganceta?,komai daya shafeta?,harda tsohon tarihin da ba ita kadai ya shafa ba?,mahaifiyarta ya shafa kai tsaye?"

"Waye kai?" Ta sake fadi idanunta a lumshe,amma wanna karon cikin wata karyayyiyar murya. A wannan karon cikin wani irin yanayi dake nuna tsananin buqatar son sanin WAYESHI din.

Shuru yayi yana qarewa lips dinta kallo,ba magananta ne ya dameshi ba,lips dinta ke burgeshi,burgeshi sukeyi har yana jin jikinsa ya fara amsawa,mararsa ta sake motsawa tana dan daurewa da wani irin yanayi daya tabbatar mode dinsa yana dab da canzawa. Yana jin kamar ya kamo lips din,yayita tsotsa da wannan sulbin da suke dashi wanda tunasu kawai yana iya birkita lissafinsa.

"Ka fara bani tsoro" Ta fada tana bude blue eyes dinta a kansa. Yarrrr yaji tsigar jikinsa ta zuba,ta bude idanun nata ne da wani irin yanayi da ya sanya ya kasa jurewa,sai ya sake sakata a jikinsa sanda take yunqurin zamewa,ya mannata sosai da jikinsa yana aza dukka tafukan hannayensa akan mazaunanta.

Tudunsu ya cika masa hannu,ya lumshe idonsa yana hadiye yawu da qyar. Saukar hannun a gurin ya sanyata wani irin zabura,ta sake yunquri ta zame hannuwan amma sam bata da wannan qarfin,sai ta maida idanunta kansa.

"Please" Ta fada da wata narkakkiyar murya,ga zatonta yanayin zai taimaka mata ya saketa,saidai ba abinda hakan ya haifar sai sake kunnashi da tayi,don kai tsaye ya kwantar da kansa saman kafadarta,take taji yadda yake kokawa da numfashinsa.

"Please" Ya sake maimaita kalmar data fada din a rarrabe saboda yadda zuciyarsa ke bugawa.

"Na shiga uku" Ta fada can qasan ranta idanunta suna tara ruwan qwalla. Me yasa?,me yasa yakeson mannewa jikinta haka?.

"Obbooooooo" Muryar noorah ta cika masa kunne wadda still tana daga bayan qofar ba tare data shigo ba.

"Ya salammmm" Ya fada yana janyewa daga jikinta.

"Noorah" Ya amsa mata da birkitacciyar muryarsa.

"Muna jira obbo please" Ta fada da yaren oromo.

"Alright" Ya amsa a kasalance. A nutse ya warware hannayensa daga inda ya dorasu,ya janye baya a hankali yana Ciro tissue ya miqa mata.

"Ki goge hawayen fuskarki,ni a yanzun bani da mafita na sani sai a gurin Allah" Hannu ta miqa tana karbar tissue din tana zube idanunta cikin nasa,yaga tambayar dake yawo cikin idanuwan don haka yayi taku biyu sannan ya dora da fadin.

"Mamminki na daya daga cikin mutane mafi soyuwa a zuciyar nanay......mun tashi mun sameta cikin kewa qauna da soyayyarta,ta yaya zata bari wani abu ya taba jinin wannan halittar?" Tissue din ta dora saman fuskarta tana goge hawayen da yayi saura a hankali,tana jin wata soyayya da qaunar matar tana saukar mata,tana kuma jin tamkar mahaifiyar data rasa dinne ta dawo kaman yadda ta buqaci taji hakan.

"To amma meya banbanta ta.....me ya banbanta wannna yanayin da abinda takeji akan morsa safiyya?,me ya hana taji wannan yanayin da wuri akan morsa safiyya?".

"Mammina......kusanci da mammina" Zuciyarta ta bata amsa kai tsaye,amsar data tsaya cak cikin kanta tare da riqo hannunta da haisam din yayi cikin nasa yana fadin.

"Muje" Tadan kalleshi kadan,suka hada idanu sai ta basar. Ta fahimci kamar ya soma sabawa kansa da wasu abubuwa game da ita,kaman riqe hannunta,yana nema yayi normalizing din abu gaba daya.

Kanta ta daga cike da wani hargitsi sanda nanay ke fitowa,ta dauka zata gansu su ukune,shi nanay din da matar tashi,saidai ganin nanay ita kadai ya sanyata kafe nanay da idanu,maimakon tarin tambayoyin da su noorah suka baibayeta dashi,

Murmushi ta sakar musu tana zama tsakiyarsu.

"Ba iya surukata kawai haisam ya kawomin ba......harda tsohon mafarkina.....tsohon burina dukka ya tattara ya kawomin,diyata haisam ya shiga duniya ya nemo min.....bazan gaya muku wace ba,zanga waye zai iya gane me nake nufi bayan ta fito" Ta fada tana murmushi.

Cecekuce suka fara a tsakaninsu,kowa yana son canka,kowa yana son fadin albarkacin bakinsa,saidai ga saamee kuwa,wani qarin firgicin ta sake shiga,

Wacce diya ce ta nanay bayan su dinnan dake gabanta?,wacce diyace haka data samarwa nanay wani irin launin farinciki daga shigarta gurinta wanda ta dade ita bata gani ba a tare da ita?.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Kacamewar da sukayi da magana sai ya hadu da tunanin qwaqwalwarta kwanyarta ta soma nauyi,nauyin da bata fahimci me girma bane sai sanda idanunta suka sauka kan farar qafar haisam data fara shigowa wanda ke sa ye cikin lallausan baqin takalmi na fata.

A hautsine tayi gaba kadan da idanunnata,suka sauketa kan qafafun akhnan din dake dauke da zara zaran yatsunta da suke da alamun ragowar lalle a rabin kowanne farce.

Da wata nutsuwa data tilastawa kanta,da wani matsanancin bugun zuciya take daga idanunta don isa ga fuskar akhnan da take bala'in dokin son ganinta. Wacece ita?,me zata gwada mata?,dame ta fita?.

Daidai sanda idanunta suka kai kan fuskartata,daidai sanda akhnan din ke daga kanta a hankali tana laluben fuskar noorah. Ta riqe muryar yarinyar da tayi kiransu har sau biyu a dazu,shi yasa a yanzun data sake jin muryarta dab da ita ta daga kanta don ganinta.

Wani sashe ne na zuciyarta taji ya zaftare daga qirjinta yana neman hanyar da zai fado. Wani tsoro shock da wani irin razani ya mamaye ruhinta zuciyarta gangar jikinta dama b'argonta gaba daya.

"Ya Allahu.....ya Allahu" Ta fada can qasan zuciyarta bakinta yana rawa,kaman yadda hannuwanta da qafafunta dukka suke rawa.

Takawa takeyi a hankali,idanunta har yanzu a qasa kadan,hannuwan noorah cikin nata ta riqesu da kyau cikin siraran yatsunta.

Ta dauka zata ganta macace kamar kowacce mace,amma sai take ganin wata TAFISU....wata mace da sunan macen kawai tayi tarayya dashi da sauran mata.....amma komai nata na dabanne. Komai nata yana nuna ainihin ma'anar kalmar KYAU.....yanayinta zubinta gaba daya yana nuna asalin abinda IZZA da qasaita ke nufi. Bata zauna da ita koda na minti.uku ba,amma daga nan inda take zaune abubuwa take hanga tattare da ita masu nauyi. Idanunta yakai kan blue eyes dinnan nata,wani nau'in kalar blue eyes da bata taba ganin irinshi ba. Wata irin fuska da aka azurtata da sassanyan kyan da ko ita ta sani KYAKKYAWA ce,duk yadda takeji a lokacin bata isa ta qaryata wannan ba.....hasalima yana daya daga cikin abu mafi daga hankali da birkitata a yanyanzun

Wata irin tafiya take majestically,natural grace,blue eyes dinta ta sake kalla,ba irin wanda ta sani bane,ba kuma irin wanda ta saba gani bane. Wannan kalan blue din me wani irin kyau ne da wani haske me daukan hankali a cikinsa.

"Ta yaya zai iya tsallake idanuwansa daga kan wannan halittar?" Wata zuciyar ta rada mata a hankali,saita maida idanunta ta lumshe tana jin haushin gaskiyar da zuciyartata ta gaya mata,tana jin yadda bugun zuciyartata ke sake ninkuwa,yana kuma sake tsananta da wani irin mahaukacin kishi.

"Ta fini.....ta fini tako ina na yarda.....amma na fita kusanci dashi,na fita kusanci da nanay,na fita kusanci da sanin komai da yakeso,don haka ina da nawa quality din,ina da sauran quality din da zan karbeshi" Ta fadawa kanta a hautsine tana sake bude idanunta tarwai a kansu.

Wannan karon daya hannun nata dake cikin na haisam idanunta suka sauka. Yatsunsa cikin nata ya sarqafesu sosai kaman wanda ke tsoron zata subuce masa. Karo na farko.....lokaci na farko a rayuwarta da taga hannunsa cikin na wata d'iya mace. Wadannan zara zaran yatsun nasa da suka jima suna burgeta,wannan yatsun nasa da takan jima tana kallonsu musamman idan yana rubutu da wani irin salon burgewa dake jan hankalinta. Wani abu ne zafi ya sake matse zuciyarta.

"Zo nan d'iyata" Kalmar nanay ta sanya kowa ya koma cikin nutsuwarsa,ta fada ne saboda tayi saving akhnan kan yadda rumaisa Aanani da noorah suka baibayeta kowa yanason ta fara bashi kulawarta.

Da idanun nan nata take kallonsu.....wani irin kallo daya motsa asalin farinciki daga zuciyarta. Murmushi ne kwance saman fuskarta ba tare data sani ba,dukkaninsu burgeta sukeyi,burgeta sukeyi da wani irin yanayi da bata taba sanin akwaishi ba. Family guda....ahali guda.....iyali guda,wasu na kama da wasu a cikinsu,nutsuwa da tarin kamewa da qaunar da take gani tasu a idanunta. Me ta musu data cancanci wannan soyayyar da kulawar?.

Kama hannunta nanay tayi,ta zaunar da ita saman kujerar data tashi. Idanu saamee ta lumshe nauyin qirjinta yana neman rinjayarta. Wata kalar girmamawa take gani daga gurin mama oromo.....mama oromo me tarin girma da kuma matsayin da ita kanta tasan ba qarami bane. Ita take tashi daga muhalli sannan ta zaunar da wata?,wani babban alama na qarshen girmamawa a al'adarsu.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 62*

"Waye zai iya gayamin.....diyata ta wanne bangarene?....ni kuma na bashi kyautar da bazai manta da ita ba" Ta fada tana murmushi tana kuma rarraba dubanta tsakanin fuskokinsu gaba daya.

Murmushin dole saamee ta qirqiro sanda idanun nanay ya sauka akan fuskarta. Ta motsa bakinta kadan,saidai wani abu daya dunqule mata a wuya ya hanata cewa komai.

"Ina ganin kamanni nanay,saidai banason fada na daga miki hankali" Balqess ta furta a hankali idanunta akan akhnan wadda kanta yake qasa har yanxu,hannuwan noorah kuma suna cikin nata.

Yarinyar taqi yarda sam ta matsa daga kusa da itama,tana jinta a yau a yanzu kamar tana cikin family dinta,kamar tana cikin ahalinta,wani irin sakewa da wani farinciki dake huda zuciyarta. Daga sanda ta biyoshi kawai ta dauka ta rasa komai nata......amma a yanzu da take ganin abubuwa tamkar musanye akayi mata zuwa mataki na gaba.

Daga shehnaz da aisa kawai take samun irin wannan abun da sakewar,amma a yanzun saiga ninkinsu a gabanta kowa na qoqarin nuna mata kulawa.

"Safeena nanay.....momma safeena idan zan iya tunawa daidai" Balqess ta fadi tana kasa jiran amsar nanay to umarninta na fadin abinda ke zuciyarta.

Sunan ya daki zuciyar saamee,ba ita kadai ba,indai zaka zauna da nanay na kwanaki uku saika san da wadannan mutanen guda biyu. Safiyya da safeena,tana jin bugun zuciyarta har cikin kunnenta,ta daga idanunta a hankali tana saukewa kan fuskar akhnan kafin ta janye,kunnuwanta na jiye mata sanda nanay ke bada tabbaci.

"Itace.......jinin safeena ce ta dawo,saidai mun rasa safeena.....amma alhamdulillah,safiyya tana raye". Ko na second daya ba zata iya sake zama a gurin ba haka taji,saita motsa qafafunta da takejin kamar sun mace,ko kuma basa iya amfani a jikinta,ta miqe tana sulalewa gami da nufar qofar fita a parlour din. Kawai tana jin tata ta qare......tana bata da wani sauran hope akan wai soyayyar nanay zata buda mata.hanya a zuciyar haisam,don koda wasa ba zata hada soyayyar safeena da tata soyayyar a zuciyarta ba.

Yadda kowacce ke sake mamakin abun ya ajiye wani abu me girma game da mutanen a zuciyar akhnan. Sai taji ta matsu ta sake samun cikakken haske.....da cikakken tarihin alaqar mamminta da wadannan ahalin.

"Ya akayi yasan da wannan alaqar wai?" Ta fadi tana satar kallonsa ta can qasan idanunta sanda yake tsaye hannayensa goye a qirjinsa,lokacin da aka gama shirya kyautukan mama oromo hajiya khadeeja yunnus jallata a gabanta.

Abinda ya sake bata mamaki,yadda kowa a cikin su ya shiga bada umarni ana shigowa da tasa kyautar.....kowa ciki harda auta noorah.

Wani abu da taji ya burgeta,wani abu daya alamta mata tabbas akwai qauna da shaquwa me girma a tsakaninsu,tasa hannu ta tallafi akwatin da noorah ta bata na tata kyautar. Ta kasa budeshi tana juyashi kawai a kunyace.

"Kyautar maraba daga iyalin motii aba jifar ne wannan" Zenebu ta fadi tana rusunawa a gaban akhnan.

"Na gode.....na gode qwarai" Ta fada da harshen turanci wanda kusan dashi suketa magana,don har yanzu ba cikakken communication a tsakaninsu. Kadan kadan take tsintar yaren oromo din,wanda shima bai wuce gaisuwa ba irinsu akkam jirta da sauransu,hakanan suma basu iya French ba hakanan basu iya yaren Tuareg ba,hausarsu da qyar take fita,abinda zai alamta maka basa mu'amala da masu yaren.

"Bazan tafi nabar diyata ba......tuntuni na aike masarauta anyi shela,qafata qafarta,wannan rainon.....wannan tarbiyyar nice da kaina zan qarasa dasata" Nanay ta fadi tana kallon agogo wanda yake nuna yammaci na gabatowa.

Kadan ya murmusa,yana zare hannuwansa daga aljihun wandonsa,yadan saci kallon akhnan din sannan ya dauke kanshi.

"Duk yadda kikace haka za'ayi in sha Allah".

Awa daya tak tasa a dauke duk wani abu daya shafi akhnan daga gidan,tasa aka qara motoci aka kuma shirya komai bisa tsari,suka fara gaba,sannan sukayi sallah tare da cin abincin dare,sa'annan suka wuce zuwa aba jifar palace.

Duk wannan abun tana qarqashin kulawa da soyayya ta 'yan uwan haisam,kowa kaffa kaffa yake da motsinta da bata wani irin kulawa. Noorah kuwa tana maqale da ita,kamar wannan matsayin na haisam dukka ta tattara ta maidashi ga akhnan din.

Labari take mata kala kala,saidai,muryarta qasa qasa sannan cikin nutsuwa. Ko a tafiya motarsu daya da noorah da nanay da akhnan din. Aanani tayita mita zatabi motarsu,amma dole haka ta haqura kaman yadda sauran suka haqura,kowacce ta shiga asalin nata motocin suka harba zuwa masarautar.

Wata DUNIYA take hange daga nesa bawai masarauta ba,manyan katangun da sune suke fara marabtar dukkanin mutumin dake tahowa zuwa ga masarautar. Kafin kuma ya iso dab da ita hasken wadansu irin fitilu su cika idanunsa. Fitilun da duk me kallo cikin nazari da fahimta zai gane cewa ba fitilu bane kawai na ado,ba fitilu bane na banza,fitilu ne dake gaya maka cewa ka kusanto wata duniya dake cike da IKO da QASAITA.

Wasu irin hasumiyoyi ne dake nuna tsananin qarfin tsaro na soji da dakarun da masarautar ke dashi,suna nesa da juna amma kuma abun mamakin cikin tsari suke.

Yadda jerarrun alatun fitilu suka cika hanyar masarautar,hanyar data miqe dodar har zuwa bakin babbar qofar da tafi kama da qofar shiga wata duniyar.....haka dakaru da masu tsaro kowa ke tsaye akan tsari,a muhallinsa cikin uniform launi da dinki iri daya.

Fitilu iyakar ganinka da asalinsu na tagulla ne da zinare,wanda aka sarrafasu da wani irin yanayi me daukan hankalin me kallo. Ba don haske kawai ba,don su nuna alatu gado ne ma masarautar aba jifar......don su nuna girman arziqin da qabilar oromo dukka ke taqama dashi.....sannan su nuna girma da daukakar masarautar ibraheem aba jifar.

Readers Also Read

More by Huguma