L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 35
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 35: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 35. Da wani irin tsari motocin suka jera kansu,suka kuma…
3,370 words
Da wani irin tsari motocin suka jera kansu,suka kuma fara shiga ta babbar qofar,jerawar bawai don gudun matsewa ba....aah,hasalima sama da mota ashirin na iya shiga ta qofar idan an budeta a lokaci guda. Jerawar na nuna irin tarbiyyar ta tsaro da suka samu wanda ba tsoro sam a cikinta.
Daka kalli qofar zakasan itama mix ne na zinare da lu'u lu'u da aka yafasu jikin sassaqaqqen dutsen da yake wani irin qyalli,a jikin qofar zane ne na sarauta dawakai da kuma rubuce na nasarorin masarautar da yaruka har guda uku,hakan sai ya sake zama wani ado me daukan hankali matuqa da gaske.
Masu tsaron cikin gidan sun banbanta dana farko da suka tarar. Wadannan tufafin jikinsu silk ne,suna tsaye cikin tsari da wata cikakkiyar nutsuwa kamar masu tsaron wani rufaffen sirri,su suka sanya hannu suka bude qofar gaba daya da sassarfa bayan da suka fahimci sheikh muhammad haisam aba jifar da mama oromo ne ke shigowa masarautar da kansu.
"Barka da dawowa ya me daraja" Abinda ta iya fahimta suna fada kenan a duk sanda motor haisam dake bayansu zata gifta daya daga cikinsu,cikin wani kalan rusunawa da girmamawa.
Idanu ta janye zuciya da hankalinta gaba daya a jagule,wani tashin hankali yana sauko mata. Abinda take gani a yanzu ya girmi hankalinta,abinda take gani a yanzu yafi gaban tsoro shakka ko kokwanto,yafi mata kama da ALMARA irin wadda hankali bai taba kawowa ba.
"Wacce irin masarauta ce wannan?" Ta tambayi kanta tana jin dukka wani qoqarinta yana zagwanyewa. Ta gama sallamawa,wannan mutumin,ta gama miqa wuya wannan shiekh din ba shine sheikh din da suka taso dashi daga agadez ba. Kwanyarta ta gaji da tambaya da tuhuma,ta gama saddaqarwa ba zata taba sanin wayeshi ba sai sanda yaga daman gaya mata da kansa,ko Allah yasa taji.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Amma wanne girman matsayi yake dashi a nan din?,wacce irin masarauta ce me girman iko haka?" Ta fadi daidai sanda motocin suke sake kutsa kai cikin gidan,tana kuma ci gaba da ganin abubuwan almara.....yadda alatu yake magana da kansa......yadda MULKI DA IKO suke aiki ba tare da anyi magana ko an bada umarni ba.
"Kin shirya muna iya fita?" Nanay ta fadi a nutse,kalmar data jawo hankalinta daga duniyar tunanin data tafi. Kanta a qasa,jikinta a mugun sanyaye ta gyadawa nanay kai,kaman ana jiran hakanne aka buda mata murfin motar,sannan aka buda ta bangaren nanay din.
"Barka da shigowa masarautar oromo.....barka da shigowa ahalin oromia.....jini mafi girma da daraja jinin aba jifar" Wata mata data zube a gabanta kaman yadda sauran matan suka zube ta fadi kanta a qasa sai kace bishiyar da aka dasata bata da niyyar motsawa.
"Muna farinciki da kasancewarki macen da yarimanmu me jiran gado ya mallaka.....muna alfahari da wannan d'iyar sarkin agadez". Wani irin tsalle zuciyarta tayi cikin qirjinta sannan ta samu guri ta dire. Maganan matar ta qarshe tana maimaita kanta cikin kunnuwanta,
"Matar yarima me jiran gado?,wanne yariman?,an sauya mata wani da haisam ne?,ko kuwa shi dinne?,idan shi dinne ta yaya hakan zai buya a gareta tsahon zamansu?,tsahon wannan lokaci?,tsahon kasancewarta da 'yan uwansa?.
" Yau masarauta zata kwana cikin farinciki mara misaltuwa,zukatanmu cike suke da fatan alkhairi a gareku,tare da fatan samun zuriya me albarka tsakaninki da yarimanmu.....yarima sheikh muhammad haisam,jinin oromiyawa" Matar dake duqe har yanzu a gaban akhnan ta fadi,sannan ta yaye wani farantin silver da yafi kama da farantin azurfa
Komai da yake kan farantin na zinare ne,sai abu guda daya da haskensa ya dara na komai da yake kai. Qafar akhnan daya ta riqe a hankali ta dora saman cinyarta,a yadda take tsugunnen,ta saka hannu ta ciro wata sarqar qafa me bala'in qyalli da daukan idanu,ta bude marufin sarqar,ta soma sakata a tsintsiyar qafar akhnan din.
Wani irin numfashi me tauri samee dake can gefe ta shaqa ta kuma furzar. Wannan sarqar me daraja ce,tsananin daraja kuwa a fadin tarihin qabilar oromo,ba kowanne gida bane.....ba kowacce masarauta bace,ba kuma kowacce suruka bace ake iya mallaka mata ita. LU'U LU'U ne wato zallar diamond,ta dade tana bincike akan tarihinta da asalinta,kasancewarta mutum me yawan bincike akan abinda ya shige mata duhu. Darajar sarqa tana ganin tafi gaban a mallakawa akhnan din ita,amma saidai kuma,ana azata saman qafartata kyanta da darajarta ya sake fitowa,tamkar don saboda akhnan din kawai aka qerata.
"Kina cikinmu yanzu,cikin qauna da aminci" Ta fada matar da harshen girmamawa.
Miqewa matar tayi da farantin azurfar a hannunta,saidai bata iya tsaiwa gaba daya a gaban akhnan din ba,wata irin tsaiwa ce ta nuna girmamawa.
Ta bude wani turare,ta zuba a wani qaramin abu tana miqawa akhnan din. Ta fahimci me take nufi,don haka ta bata dukka tafukan hannayenta ta zuba mata shi. Tun batakaishi jikinta ba ta gane turaren,da sauri ta maida dubanta ga kwalbar. Turaren nan ne dai.....turaren da ya riga ya zame mata jarrabi....turaren nan da tayi nemansa harta gaji.....turaren data dinga nema kamar tayi hauka?,ya akayi suka sameshi?.
A sannan ji take kaman ta miqa hannu ta daukeshi,a sannan tanajin ko nawa zata iya bayarwa a batashi.
"Mun tsarkake miki guri,mun karbeki da hannu bibbiyu tamkar dama daga cikinmu kika fito" Ta sake fada da murmushi akan fuskarta.
Maganar ta sake dokawa cikin kunnuwan saamee,maganganun matar kamar gugar zana sukeyi mata,maganganunta kamar suna fadin cewa.....akhnan ta cinye gurin.....ba zasu sake karbar wata matar daban bayan ita wa sheikh haisam din ba.
Wani qaramin kofin azurfa ta sake dagawa ta miqawa akhnan din wanda yake dauke da sassanyan ruwan zamzam,hannunta ta miqa ta karba,amma saita gaza sha.
"Sha diyata.....addu'o'in tsari ne daga dukkan abunqi da mugun ido" Nanay tace da akhnan qasa qasa,saidai duk yadda tayi qasa da muryarta hakan bai hana saamee jin abinda nanay din ta fada ba.
A nutse idanunta suka fada kanshi,yana tsaye nesa kadan dasu,nesa kadan din da take jin ita kadai take iya ganinsa.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 63*
Kamar an sauyashi daga bakin qofar gidan zuwa shigowarsu ta yanzun da tsaiwarsu. Wani mutum daban take sake gani.....cikin suturar oromo data maidashi wani kamilin matashi. Zaki take gani wanda qananun namun daji sukewa hidima,don ko a yanzun tana hangen yadda hadimansa ke gyara masa zaman rigarsa cikin tsananin kulawa da girmamawa
Fuskarsa a tsuke,da wani irin qarancin fara'a daya sanya gabanta tsananta faduwa,qarancin fara'ar kuma daya qara adadin yawan kwarjinin dake shimfise akan fuskartasa. Sannan ya sake kawo wani kwantaccen kyau ya zube a fuskarsa gaba daya. Kaman an ninka kyansa....kamar an ninka kwarjininsa.......hakanan kamar an ninka haiba da kamalarsa.
"Yarimanmu me jiran gado" Kalmar ta sake dawo mata cikin kunnenta,saita sake aza idanunta a hankali akan fuskarsa. Tantama take......komai nasa ya sake canzawa daga taku daya tak da tayi zuwa cikin gidan?,komai yanayinsa ya sauya?,anya shine?,shine kuwa?.
Firgigit tayi saboda magana da yayi mata,bada bakinsa ba don ko motsawa wani sashe na jikinsa baiyi ba. Da idanu da kuma girarsa kawai,kaman yana cewa.
"Kisha abinda suka baki,mutane ne kewaye dake suna jiranki" Sai ta sauke idanunta da suka raunana sosai,suna jinta ta koma wata maqasqanciya,ba kuma don an tozartata ba ko an durqusar da matsayinta ba,aah......sabda cin karo da tata izzar da tayi da IKO da yafi nata tsananin qarfi.
Tayi bismillah ta kurba,ta daga kanta a hankali sanda take ajiye cup din saman tray din tana maida idanunta inda yake dazun,saidai a yanzun bata da damar ganinsa.....a yanzu baibaye yake da dogaransa ma'abota fararen kaya,zagayeshin kuma da sukayi ya hana mata daman koda ganin wadannan idanun nasa masu qyalli.
Wani bracelet ta miqa mata,na azurfa wanda akayi dukkanin adon jikinsa da qananun duwatsun lu'u lu'u.
"Wannan girmamawa ce daga yarima muhammad haisam....." Ta fadi tana miqata ga akhnan. Sake kallon gurin tayi,still bata iya ganinsa,tasa hannu ta karba bracelet din daketa sheqi yana daukan mata idanu,sai jakadiyar ta janye farantin baya,sannan ta soma komawa da baya da baya ba tare data juya ba. Ta fahimci al'adarsu ce haka,sanda duk zasubar gaban me iko basa juya masa baya,saidai suyi qasa da kansu,su kuma janye da baya da baya har su bacewa ganinsa.
Wanne irin iko ne wannan.....wannan hanya ce ta shiga cikin iyali ba tare da kalma ba?. Tambayar datawa kanta kenan wadda ba wanda zata iya yiwa bare ya amsata,hasalima miqaqqiyar hanya suka fara bi ita da nanay,jama'ar dake tare dasu suna rarraguwa da kadan da kadan,har suka bulla wani kyakkyawan guri.
Shi ba parlor ba.....shi ba hanya ba,amma yana da wani irin girma da aka cikashi da alatun da ya sake sanyayar da jikinta. Komai da ake adanashi a boyeshi domin ado me tsada da daraja......su dashi suke amfani suke shimfidewa a bango da inda qafafu zasu taka?.
"Zan tsaya a nan.....muhammad da kansa zai miki jagora,ki kwanta ki huta sosai,zuwa gobe in sha Allah,zamu tattauna sosai,Allah yayi miki albarka diyata"
"Ameen na gode" Ta fada tana matse abun hannun cikin tsakiyar tafukan hannayenta. Batasan wanne kalar tunani zatayi ba sam,batasan ma wanne yanayi zatace tana ciki ba?.
Nanay ta janye a hankali,idanun akhnan a kanta har tabi ta wata qofa,ta dauke idon a hankali tana dawo dasu inda take tsaye,sai kuwa suka sauka kai tsaye a kanshi.
Yana daga gefanta,amma ba ita yake kalla ba. Dab da ita yake a yanzun,sai kuma yanzu ta gane ashe kallon data masa daga nesa maqaryacin kallo.ne. mamaki yana sake mamayarta......yaushe ya sauya sutura?. Shigar dake jikinsa a yanzun tasha banban da wadda suka taho da ita daga palace learning residence.
Wata shiga ce ta qasaita a jikinsa a yanzu.....wata shigar girma data fidda kamanninsa sak.....ya koma YARIMA CIKAKKE da wata suffa da bata taba ganinta ba.....da wata kamala ta cikakkiyar SARAUTA da bata taba ganinta ba sai yau cikakkiya a tattare dashi.
Idanunsa ya sauke a kanta,sai taji kamar zata narke,sai taji.kwarjininsa ya ninka na baya......sai ta gaza musawa ko cewa komai sanda ya miqa mata hannunsa. Nata hannun ta bashi,tamkar kurame sukaci gaba da takwa suna dosar wata hanya.
Duk inda zata sanya idanunta sai taga wani abu daban take takawa,ba tiles bane,ba marbles bane irin na masarautarsu.....ba slate bane.....ba terrazzo bane. Sai da tayi tafiya me tsaho sannan ta fahimci wani irin lafiyayyen granite floor ne me tsananin sheqi sulbi da daukan hankali,wanda da alama duwatsun da aka sarrafashi dashi na musamman ne kuma na dabanne.
Wata duniyar take gani a matsayin dakin,duniyar da idan ta daga kanta saman roofing na dakin sai taga cike yake da wasu qananu qananun taurari fal dake bada haske. Tsoro ya kamata taji,ta kuma ji din,saidai data tuna itama daga inda ta fito sai izzarta ta ceceta.
Sakinta yayi ya koma baya yana zube hannayensa cikin aljihun wandonsa. Idonsa.ya wani narke yana mata wani kallo da take hangen wasu abubuwa masu tarin yawa cikin idanun nasa,amma ba zata iya ci gaba da kallonsa ba,don narkar da ita yakeyi,saita sadda kanta qasa tana wasa da wannan bracelet din na azurfa da aka bata.
"Irinsa ne a hannunki.....na mammi safeena.....yadda aka baki wannan a ranarki ta farko cikin ahalin mijinki haka aka bata......amma mugunta da zallar rashin imani ta sanya mam......" Kasa qarasawa yayi,sai yayi shuru yana hadiyar wani abu. Har yanzu idan ya tuna matar shi kadai yasan yadda yakeji ana yankar zuciyarsa a kanta. Banda akwai wani plan akwai wani wa'adi a kanta ba abinda zai hanashi qarasa hukuntata.
Sai daya gama qare mata kallo me isarsa,yana lumshe idanunsa a hankali yana jin yadda mararsa ke dake damqewa
Ya sani.....idan ya fita a wannan dakin dawowarsa zai zama wani abu me wahala. Wataqila nanay ta killaceta da tsaro sosai.....wataqila ta hanashi ganinta.....wataqila ta hanashi zuwa kusa da ita.....duk da bai sani ba....zai iya jurewa?,don haka ya fara takawa a hankali,dogayen yatsunsa suna nutsewa cikin lallausan carpet din,suna hana sautin takunsa fita.
Batasan ya iso gareta ba,sai da taji an riqe qugunta sosai,idanunta ta daga a nutse tana saukewa cikin nasa. Haka kawai takejin matsayinta gaba daya ya zabtare ya fadi a qasa.....cikin mintunan da basu rufa awanni ba wani sashe can dake cikin zuciyarta taji yana gaya mata.
"Wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa" Kamar a yanzun da yake tsaye dab da ita,qamshinsa na alfarma daya hade da qamshin da dakin ke bayarwa ya daki zuciyarta sosai,ta farajin kamar da gaske ne,kamar ya tsere matan,kamar akwai wata tazara me girma a tsananinsu.
Numfashinta ya tsaya cak sanda taji tattausan labbansa masu sulbin nan saman dokin wuyanta. Wani abu ya fusgeshi sosai da kalar qamshin dake fata daga cikin rigarta. Ya damqe qugunta sosai jikinsa yana shaking,wani irin numfashi me nauyi yana sauka saman wuyan nata.
Me yake faruwa ne dashi haka?,me yasa take fusgar hankalinsa haka?,meye dalilin da duk sanda zasu kebe shi da ita yakejin yana da burin rab'ar jikinta?. Me yasa jikinta gaba daya yake burgeshi?,me yasa yakejin wani gushewar nutsuwa a duk sanda ya kusanceta?.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Janye jikinsa yayi a hankali yana jan hanci kamar wanda yake mura,ya daga idanunsa a hankali ya sauke a kanta.
"Are you okay?" Ya tambayeta da faransanci. Ya saba yadda take matse masa jikinta.....ya saba da gardamarta.....da yadda take nuna lallai bataso ya tabata,duk da wasu sassa na jikinsa sun qaryatata,sun gaya masa qarya yakeyi.
Blue eyes dinta ta daga tana dubansa,zuciyarta a yau din a mugun karye take. Donme zai rufeta?,don me zai dade yana yaudararta ita da sultane?,don me zai rufe shi waye?,ma yake nufi?,meye manufarsa a kansu?. Ta tabbata tayi imanin duk wanda zai aikata haka akwai wata manufarsa daban a qasan zuciyarsa,kawai saita kasa controlling kanta da kanta,ta fashe da kuka mara sauti.
"Ya salam.....ya Allah" Ya fada da wata kasalalliyar muryarsa yana takowa inda take tsaye,saidai dab da zai iso taja baya tana dubansa.
"Me yasa?.....me yasa kayi haka?,me yasa ka rufe waye kai?" Idonsa ya maida ya lumshe na wasu mintuna,yana jin yadda fushi yake tasiri cikin muryarta,sai kuma ya budesu dukka a kanta,
"Ban rufe ba....kaman yadda ban bayyana ba,ba zaki fahimci komai ba.....ba kuma zaki fahimceni ba ko a yanxun ma......" Ya fada yana soma takawa da baya da baya ba tare daya juya mata baya ba kamar yadda hadiman masarautar ke mata
"ki kwanta......kiyi bacci......ki huta sosai......don Allah" Ya qarashe kalmarsa ta qarshe da wani irin sanyi da taushi sosai kaman wanda keson rada mata maganar sannan ya sake taku uku yana ficewa,saidai har ya fice din idanunsa suna zube a kanta.
Fushi takeji nasa a ranta,amma sanda yake fita din sai takejin kamar tace masa TSAYA karka fita....kamar tace ya zauna suyita fada.....ya zauna tayita fada masa abinda yake ranta.....ya zauna ta kalleshi da kyau cikin shigar sarauta.
Samun kanta tayi da zama dirshan gefan gado tana hawaye,sai kawai ta sanya tafukan hannayenta biyu saman fuskarta. Ba zatace ga dalilin kukanta ba......amma haka kawai tana jin zuciyarta a wani matuqar karye.
*_AGADEZ PALACE_*
Cikin dukkanin tsari da umarni yake tafi da motsin komai na masarautar. Ya yadda ya kuma amince d'ari bisa dari mulki ba abu bane na wasa.....wani babban aikine daya sanya a kwanakin ya sake sarawa sultane. Ba wasu matsaloli bane masu yawa,amma aikin kulawa da masarautar ya zame masa na dabanne saboda ZAITUNA.
Akwai tarin tsare tsare da dokoki da aka sanya wajen shiga sassan sultane gaba daya. Kowa da kowa....don dokokin sun shafi harda matansa.
Tun daga abincinsa.....maganinsa dama komai daya shafi lafiyarsa ta hannun ahmad kawai aka yarda ya fito,zai kuma katse komai da yake a duk lokutan wadannan ayyukan duk da hidimar tafiyar da masarauta yaje yayi masa sannan ya koma bakin aikinsa.
Kamar yanzu a wannan daren da suka kammala zama da tattunawa da manyan members na fada. Sha daya ne na dare,kuma lokacine da yawancinsa sultane bacci yakeyi,baya kuma farkawa sai dab da sallar asuba. Wani iko na Allah,baya taba gota lokacin salloli komai tafiyar da yayi,lokaci yanayi zai farka,a taimaka masa yayi sallolinsa ya koma.
Shima a wannan lokacin yake zuwa sassansa yadan runtsa,zuwa cikin dare ya dawo gareshi har zuwa asuba.
Sassan nasa sunyi shuru,sai amintattun masu tsaro da aka cika bangaren dasu. Ba kasafai ya fiya karbar gaisuwarsu ba a irin wannan lokacin,don ba lokaci bane na gaisuwa,lokaci ne kawai.na kulawa da motsi da lafiyar sultane,a haka har ya isa ciki.
Daya bayan daya yake buda qofofin,an killace ko ina an rufe da tsaro,don ba lokaci bane na shigowar kowa,lokaci ne kawai da yake kwanciya bacci sai kuma asuba.
Idanunsa ya kafe daya daga cikin dakunan baccin sultane,wanda ya saka aka maidashi dazu da safe saboda ya samu canjin muhalli.
Qofar yake gani kamar an budeta,kamar bata rufu sosai ba,wannan abun ya sanyashi qara hanzarinsa cikin salo na sand'a da kuma sassarfa,saidai dab da zai isa gurin qofar ta bude,gangar jikinta ya fara fitowa sannan kanta wanda ta juya tana waiwayen cikin dakin.
Dawo da ganinta da tayi gabanta ya sanya suka hada idanu da ahmad,yana tsaye qyam ya zuba mata wadannan rinannun idanun nata da tun yana dan qwaya suke mata wani iri.
A hankali ya sauke idanunsa kan gorar ruwan C'bone dake hannunta,sai itama tabi robar da kallo,sannan idanunsu suka hade guri daya lokaci guda.
*_Tooooo......su zaituna dai ba za'a canza hali ba......da alama tana wasa da wannan talalar me kama da SAKE_*
*_Muje zuwa....akwai kallo fa jama'a_*
*_Saamee dai ta rantse.....taci alwashi......A INA NASARAR TAKE NE?_*
*_Me MAMMINA TA SHIGA YI DAKIN SULTANE?,...._*
*_WAISHIN wanne irin plan ne da SHEIKH MUHAMMAD HAISAM ABA JIFAR AKA AL_SAAMIT(THE SILENCE ONE)_*
*_ME YAKE DAMUN SULTANE NE?_*
_KU MAQALQALE HUGUMA😂😂,ITA KE DA AMSOSHIN TAMBAYOYINKU IN SHA ALLAH_
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 64*
Wani irin kallon kallo suke yiwa junansu shi da ita,wani irin zuzzurfan kallo dake nuni da zallar abinda ke cikin zukata sukewa junansu.
Kowa kawai qoqarin mallakar kansa yakeyi,musamman ahmad daya samu wani irin training daga gurin haisam na dan zaman da sukayi tare. Kallon dake cikin idanun ahmad din sun mata nauyi,saidai ko daya taqi yarda ta bari yaga haka cikin idanuwanta.
Ya motsa zuwa gaba kadan,cikin wata kakkaifar murya yace.
"Bansan me kikeyi a nan a daidai wannan lokacin ba" Idanu ta sake zuba masa,sannan ta saki wani shu'umin murmushi tana gyara tsaiwarta.
"Yaro man kaza......" Ta furta da wani yanayi,sannan ta mamaye maganar tata da fadin.
"A daidai wannan lokacin,yanayin lafiyarsa yana iya sauyawa.....kai bakaga kamata gurin zuwa dubashi akai akai ba?". Idanunsa ya qanqance sosai a kanta.
" Anyi masa komai daya kamata....baya buqatar wata qarin kulawa ta daban tunda ba lokacin tashinsa bane.....bayan duka wannan kin sani......doka ce an hana kowa shigowa gurinsa irin haka"
"Kowa?....kowa?" Ta maimaita sau biyu tana kallon ahmad din. Can qasan ranta tana jin wani b'acin rai yana ratsata. Wai sai yaushe komai zai saitu?,yaushe lalacewarta yakai haka?.
Yaron data raineshi da hannayenta,yaron data bashi rayuwa irin wadda takeso,yaron daya zama tamkar bawa a gareta yau shike da iko da fada a ji cikin rayuwarta data masarauta gaba daya?.
Ba shakka da tasan zai zama haka.....zai mulketa koda na rana d'aya ne tabbas data kasheshi bata bari taga zuwan wannan ranar ba.
"Ni ba kowa bace.....bana cikin sahun jam'in KOWA da doka zata hau kansa" Tayi maganan a hanzarce tana takowa don wuceshi. Alwai wani abu dangane da yaron,akwai wani abu da bata so da yake qyalli cikin idanunsa,kamar shige shigen abinda yake fita daga idanun sheikh haisam.