Kenza eBookz

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 37

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 37

L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 37: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 37. *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

3,330 words

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA๐Ÿ‘‘*

*HUGUMANKU CE*โœ๐Ÿฝ๐Ÿ’Ž *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*๐Ÿ’Ž

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 66*

Sanye yake da short sleeve leaf green t.shirt,sai dogon trouser nude color daya dan ciza kadan. Wannan sassalkan gashin nasa yana warwatse saman kansa da wani irin yanayi da zai tabbatar maka baiyi tajeshi ya kuma kwantar dashi yadda ya saba ba.

Manyan idanun nan nasa sun rusuna kadan da wani irin yanayi daya canza launinsu,rusunawar da sukayi ta qara musu wani irin kyau,ta kuma sake kusantar da eyelashes dinsa na qasa dana sama da suke da tsaho sosai kaman zasu hade. Kallo ne na sakanni,saidai ya tafi da wani irin yanayi da saqo da batasan ya fita a idanunta ba. Wani irin kyau.....kwantaccen kyan nan me sanyi da wani irin sassanyar nutsuwa take hanga a tattare da fuskar nan ma'abociyar haiba.

Fuskar data kwashe darare tana kawo mata farmaki cikin mafarkinta, fuskar data kwashe kwanaki tana juyi saman tattausan gadonta tana gilmawa ta cikin duhun dakinta....fuskar da sannu a hankali kewarta ta fara illatata ba tare da ta farga ba. Wani sassanyan aniyar zuciya ta qwace mata,taimakonta daya ta sauka ne a hankali daga zuciyarta zuwa hunhunta ta fidda siririyar iskar ta hancinta.

Idan har taga daidai.....wani abu taga ya hadiya a hankali,ya kuma motsa bakinsa kadan kaman zaiyi magana,sai kuma taga ya zare idanunsa daga kanta.

Kan motii ya maida dubansa,wanda yake zaune dab dashi saman wani ottoman lallausan offwhite. Kallo daya tak yayi mata wani abu ya tsarga masa,tun daga tsakiyar kansa zuwa tafin qafarsa yaji kaman yana neman loosing control nasa,baya buqatar hakan kuma,a yanzun da yake gaban motii da kuma nanay.

Baisan abun zai zame masa jarrabawa ba sai daya gaza samun ganinta na wadannan kwanaki. A duk inda zai sanya hannunsa sai yaji bai ajesu daidai ba. Kaf pillows dinsa na saman gado ba wanda baisha matsa ba.....amma still baya samun sassaucikoda na daqiqa daya. Ya sauya pillows ya sake qara wasu amma still ba wani taimako da yake samu. Baisan daga inda matsalar take ba.....

Hirar su ta shekaran jiya yake tunawa. Shi da maleek da suke turkey yanzu haka shida falaaq din,sai naseeb. Hirar ta ranar iya su uku ne,don naseeb yace iya hirar masu iyali ce kawai,saidai shi dimma daga qarshe shuru ya musu tsakanin naseeb da maleek suketa shaqiyancinsu.

Ya sani,wani abun idan maleek ya fada dashi yake,maganan maleek ta qarshe ta sanyashi yanke kiran ba tare da yace musu komai ba,sukayita qoqari sake kiransa amma yaqi basu wannan damar.

A daren idanunsa ya maida ya lumshe yana jin yadda ciwon ke sake masa qarfi. Baisan dalili ba,amma har bayason dare yayi cikin kwanakin nan. Tun yana irga kwana daya biyu uku har zuwa sati guda.

Yayita zuwa gurin nanay dukka satin,zuwan dashi karan kansa baisan dalilin yinsa ba. Yakan jima zaune yana jiran nanay,yakan jima zaune suna hira dashi.

A satin ya dauka zaiga koda gilmawarta,a satin ya dauka ko sau daya zasu hadu gurin cin abinci a gurin nanay amma ba koda alamunta,sai saamee dake neman kusanci dashi.

Basai an gaya masa ba.....a matsayinsa da matakin karatunsa.....tabbas akwai wani gagarumim sauyi dake neman zuciyarsa idanu rufe,saidai ya gaza samun qwaqwarar hujja ko shaida da zai gasgata hakan.

A yanzun da idanunsa suka sauka a kanta.....a yanzun da take takowa zuwa cikin parlor din.....idanunsa basa kanta.....amma cikin jininsa da jikinsa yakejin takunta....cikin jininsa da jikinsa yakejin wannan kusancin. Yana jin kamar wani abu daya rasa ne yake takowa zuwa gareshi,yana jin kamar wani sashe na jikinsa da aka cire aka wurgar ne yake dawowa zuwa anihin jikinsa.

Nauyi da kunyar mootii takeji,wani irin nauyi da ko sultane batajin nauyinsa haka. Ta wani sashen sai take ganin wasu kamaceceniyar yanayi da dabi'u a tsakaninsu.

Cikin girmamawa ta isa gabansa,ta zube a hankali tana gaidashi da harshen oromo data fara kama kalmomi da yawa na kurkusa,kaman gaisuwa da sauransu.

Da murmushin nan me cike da dattako da kulawa ya amsa mata

"Anya khadeejatu?.....har yanzu baku gama bidi'o'in naku ba?" Mootii ya fadi sanda Akhnan ke isa gaban gadon haisam din,sai kuma ta samu Nanay ta ja mata kujerar dake dab dashi din.

Wani abu guda daya data lura dashi,komai na nanay ya ta'allaqa ne akan yadda zata bawa haisam kulawa.....kamar yadda tata kulawar kuma a yanzun dukka ta tattareta a kanta.

A kunyace ta zauna,saidai abinda ya bata relief janyewar nanay a nutse ta koma kusa da mootii daya koma kujerar can kusa da qofa yana riqe da wasu takardu a hannunsa,wannan ya haifar da tazara a tsakaninsu,don parlor ne me girma qwarai.

Idanunta ta daga zuwa kan fusarsa,saidai gaba daya kalaman bakinta sun maqale saboda samun lumsassun idanunsa da tayi a kanta. A hankali ta maida bakinta ta rufe,ya riga ya saukar mata da wannan dafin.....ya riga ya luguiguita zuciyarta da wadannan narkakkun idanun nasa da suka sake narkewa.

"Kwananki nawa da sanin bani da lafiya?" Ya furta softly saidai tana jin wani abu can cikin sautinsa.

Samun kanta tayi dayin qasa da kanta,tana jin wani kimarsa tana tabata sosai. A yanzun wani kallo na daban take masa.....ba don dukiyarsa ko.matsayinsa ba.....aah,sai don yadda ta samu ahalinsa da sanin ma'anar GIRMA da MUTUNTAWA.

"Kwana uku" Ta furta a hankali da siraran labbansa da yaji kaman ya miqa yatsunsa a shafesu a hankali.

Kai ya jinjina a hankali,yana jin yadda gaba daya jijiyoyin jikinsa suke narkewa. Qamshinta.......shigarta da yanayinta gaba daya. Kwana sha hudun yake sake maimaitawa cikin kansa. A kwanakin ya dinga jin wani abune yana masa yawo a kai,a kwanakin ya tuna duk wani memories nashi da ita tas.....ba abinda ya manta tun daga zamansu a agadez zuwa ganinsa da ita na qarshe. A kwanakin ya dinga jin wani abu yana yawo da zuciyarsa cikin wani irin yanayi.

Duk debe kewa da library da litattafansa ke masa a wannan lokacin su gaza dauke masa komai.

"Kwana uku?" Ya maimaita a hankali kaman wanda kwanakin sukayiwa zuciyarsa nauyi.

Fuskarta ta narke a hankali,tana jin kamar bata kyauta ba......tana jin kamar abun bai dace ba.

"Bahaushe yace gaida me gaidaka ko?" Can wani sashe na zuciyarta ya tunasar da ita. Ta tuna yadda yake kula da ita duk sanda wani ciwo ko rauni ya sameta.....a saudiyya....a festival d'l'Aรฎr. Baiyi bacci ba... Bai samu sukuni ba sai data samu......amma ita yanzu?.....sau daya tak ta kasa gwada masa halaccinta?.

".....ko sau daya...." Ya sake fadi a hankali da wani irin coolness idanunsa cikin nata.....yana jin wani abu me qarfi yana fusgarsa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

".....baki nemeni ba?" Ya qarashe da sigar tambayar data sanyata lumshe ido tana jan wani numfashi. Shigar kalmar data gauraya da sautinsa cikin kunnenta.....wani irin lallausan sauti da takejin kamar ba muryarsa ba....kamar ya manta waye da waye a gurin.

"An hanani....."

"Na sani....." Ya tari numfashinta ba tare daya bari ta qarasa ba.

"Nanay ko?" Ya sake fadi da wani nauyi cikin muryarsa. Sai ya maida bayansa ya jingina sosai da fuskar kujerar.

"Me yasa rashin zuwana ya masa ciwo?" Ta tambayi kanta da kanta cikin jikinta har yanzu da idanunsa a kanta. Da zai taimaketa....da zaiyuwu daya debe wadannan tsimammun idanun nasa daga kanta,rikitata yake.....sosai yake sanyata jin tana rikicewa.

"Ko sau daya....ko da tambaya?...koda saqo?.....koda daga bakin qofa ne?" Ya sake fadi da wani lallausan sauti me cike da tuhuma.

Kaman zata shide taji,don sai taji muryar tasa tayi wani mugun kusa dashi,kuma koda data motsa saita fahimci ya rage distance din dake tsakaninsu ne.

"Don Allah......kayi haquri" Ta fada a rarrabe tana jin wani kunya da nauyin kusancin daya samar a tsakaninsu. Kamar idanunsa baya tuna masa nanay da motii dake gurin?.

"Ba komai" Ya fada a hankali yana sake relaxing sosai cikin kujerar karo na biyu,sannan ya maida idanunsa ya lumshe.

Har cikin zuciyarta takejin bata kyauta ba.....amma da wanne harshe.....da wannw yanayi zata cewa nanay GANINSA NAKESON YI?. Da wanne idanu zata cewa nanay KEWARSA NAKE?.

Tayi imanin baisan abinda takeji cikin zuciyarta ba.....inda ya sani bazai tuhumeta da komai ba.

"Da nine.....da sai a kiramin bappi ko?".

" Kayi haquri naceeeee" Ta furta da sauri a wani mugun narke da wata irin shagwaba da bata yita da kowacce manufa ba....illa manufar yabar zancan haka.

Yanayin ya sanyashi cije lips dinsa na qasa a hankali yana lumshe idanunsa. A hankali bakinsa ya furta!

"Ya salam" A hankali yana jin yadda juriyarsa take zagwanyewa....a hankali yana jin yadda dauriyarsa take raguwa. Anya zai iya?....zai iya ci gaba a haka?,alhalin tana gefansa?......zai.iya ci gaba da qaryata kansa?......alhalin komai yana bayyana gaskiyar abinda yakeji?.

Cikin cikakkiyar nutsuwa mutumin yayi sallama. Dogo ne baqi me murjajjen jiki,wanda asalin fatarsa ta nuna qabilar Ethiopia ne na gaske shi din.

"Allah ya taimakeka....na kammala"

"Madalla Dr jamaal.....ina saurarenka" Motii ya fadi,bayan ya baiwa Dr jamaal hankalinsa.

Takardar hannunsa ya bude yana sake kallonta,sannan ya rufeta a hankali,ya maida dubansa ga haisam dake zaune,da Akhnan dake gefansa,sannan ya maida dubansa ga motii.

"Ranka ya dade.....kaman yallabai yayi aure ko?" Ya fada cikin girmamawa da d'ari d'ari,kasancewar sarai yasan halin haisam.

Tambayar kuwa ta sauka saman zuciyar haisam din,sai yaji kaman duk duniya Akhnan din yake kalla tun daga shigowarsa. A nutse ya matsa yatsunsa,muryarsa can qasa taji ya furta.

"Tashi ki shiga ciki" Daga kanta tayi a nutse,cikin yanayi na rashin fahimta,saidai ba tare daya kalleta ba ya sake maimaitawa.

"Jeki giiftii" Nanay ta furta a nutse.

Miqewa tayi a hankali,tana jin wata kunya na dabaibayeta. Mene zaice ta wuce ciki?,bedroom dinsa fa kenan?,a gabansu?,bayajin nauyi ne?,ita bataga dr din ya kalleta ba kwata kwata,yaushe ma yaga hakan shi?.

Shuru parlor din ya dauka har zuwa sanda Akhnan ta bace cikin dogon corridor din da zai sadata da lafiyayyun royal master bedrooms dinsa guda hudu.

"Me ya faru.......muna jinka" Motii ya fada yana duban Dr jamaal.

Dan shafa kansa kadan Dr jamaal yayi,akwai wani kwarjini da motii din yake masa,duk da kasancewarsa kusan uba a gurinsa,saboda shi din yayan mahaifiyarsa ne.

"Irin dai wancan ciwon da yakeyi lokaci bayan lokaci.....so zuwa yanzu ya kamata ace ya rabu dashi,tunda akwai aure a......" Kasa qarasawa Dr jamaal din yayi,saboda wani kallo da haisam ya watsa masa.

Sosai yake qunshe dariyarsa ta yadda motii bazai gaji ba,da idanu kuma yakewa haisam din maganar

"Taimakonka nayi". Shuru ya wanzu a falon yana hadewa da sauran maganae Dr jamaal data maqale bai iya qarasata ba.

" Na fahimta.....na fahimta " Motii kawai ya maimaita har sau biyu yana gyada kai. Ba shiri Dr jamaal ya miqe yana shafa kansa.

"Ga magungunan da zaiyi amfani dasu nan,saidai su din relief kawai zasu bashi......Allah ya qara lafiya" Ya fadi yana karkatawa inda haisam ke zaune,nauyin motii da nanay yana narkar da shi. Bai amsawa jamaal din ba,sai tsarabar harara daya sake aike masa,yana boye da dariyarsa ya fara takawa yana fita motii da nanay na masa ya gaida gida.

Kaman jira motii yake jamaal din ya fita,sai shima ya miqe tsam yana fadin.

"Kinga yanzun ai sai ki bashi matarsa ko?"

"Zatayi jinyarsa ne yasha magungunansa motii,kwana hudu ya rage mu kammala a rakata gidanta.......ko zuwa da safe kaji qwarin jikinka......zan karbeta mu qarasa aikinmu" Ta fada tana dan duban haisam din. Saidai itama ta kasa duban cikin idanunsa.....ta daure fuska kawai tana rattaba bayani.

Murmushi kawai motii yayi yana takawa zuwa bakin qofar da zata fiddashi daga parlor din ba tare daya sake cewa komai ba. Ita dinma saita zabura tabi bayan mijinta,saidai tana sake jaddadawa haisam aron Akhnan din ta bashi.

Can qasan ran motii dariya kawai yayi,

"wanne irin qarfin hali ne wannan khadeeja?,mutum da matarsa sannan ace aro aka bashi?"

"Eh.....shi akewa gatan ai,kuma me yaci kwana uku?,kwana kin al'ada basu cika ba"

"K'nnnnn,to Allah ya taimaka" Abinda motii ya fadi kawai kenan,can qasan ransa yana sake jinjinawa halin mata,lallai halin mata daban yake dana maza,amma zaibar nanay din ta gani ganin idanunta,shidai zaiga ta yadda zata saka shinge tsakanin lafiyayyen yaronsa da halalinsa.

Yaron da kallon mata ma bai iya ba ballantana doguwar magana.....yanzun ga maganinsa ta saka dokar sai bayan kwana uku?.

*_to masu karatu.....nima dai nacw maji ma gani wai an binne tsohuwa da ranta๐Ÿ˜‚,dama ana bawa kura ajiyar nama?,to qila sheikh dinmu na mutunci dai yasan darajar abun aro,zai kuma riqeshi da kyau.....mu hadu daku a ranar litinin in sha Allah_*

*_har kullum_* *_Hugumanku ce_*๐Ÿ™Œ๐Ÿฝ

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA๐Ÿ‘‘*

*HUGUMANKU CE*โœ๐Ÿฝ๐Ÿ’Ž *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*๐Ÿ’Ž

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 67*

A hankali take daga qafafuwanta tana sauke qafafunta saman tattausan carpet din dake malale cikin dakin. Idanunta take watsawa a hankali zuwa ga kowanne sashe dake dakin wanda yake fidda wani irin tattausan qamshi da wani sanyi da yanayinsa yasha banban dana parlor din data fito. A hankali zuciyarta ke bugawa a qirjinta qamshin da nutsatsen yanayin da dakin yake fiddawa yana ratsa zuciyarta da gangar jikinta gaba daya.

Idan tace iyakar rayuwarta.....iyara adadin yadda ta rayu a duniyarta bata ganin daki me tsari da daukan hankali irin wannan ba batayi qarya ba.

Cak ta tsaya tana tsoron wani abu,tsoron qauyanci......tana ji a hankali kaman tana neman daburcewa da rasa dukkan wayewar da take da ita.

Uwa uba wani baqunta takeji sosai a jikinta,ta sake zuqar iska sosai zuwa hunhunta wadda ta kasance wata irin sassanyar iska dake cakude da qamshin turarennan nasa da batajin har abada zata daina sonshi......turaren data shafe a mayafinta tun ranar da aka shigo da ita cikin gidan,ya kuma zame mata wani abu daban na debe kewa..

Bayan wannan qamshin,wani launin qamshi ne daban da bazata iya banbanceshi ba suka cakuda suka bada wani kalar launin qamshi me saukar da wani irin yanayi daban ga zuciya da gangar jiki.

"Komai nasa.....komai nasa me sanyi ne....komai nasa na dabanne.....komai nasa yana fadin cewa shi din......" Saita kasa qarasawa tana bude idanunta a hankali,wani nau'in tuhuma yana fitowa daga qasan zuciyarta.

"Me yasa yake tsayemin har haka a zuciyata?,me yasa komai nasa yake burgeni?.....me yasa komai nasa yakemin nauyi da kuma kwarjini?" Ta tambayi kanta tana komawa da baya a hankali ta zauna saman lafiyayyar sofa din dake ajiye wani sashe daban na dakin,wadda tayi matuqar dacewa da launin dakin da tsarinsa.

Idanunta suka sauka a hankali akwan wani sashe dake dakin. Akwai wani dan ado da qawata gurin,darduma qur'ani carbi da wasu launikan fitilu masu kyau maqale agurin,wasu kuma a ajjiye a qasa,sai litattafai 'yan tsiraru da basu da yawa.

Tattausan murmushi ya subuce mata,batasan wacce irin soyayya bace tsakaninsa da karance karance na addini ba. Zai wahala ya wanzu a guri bakaga tasirin wani abu daya shafi addini a tare dashi ko litattafan addinin ba.

Tayi kaman zata miqe don isa ga litattafan ta duba wanne iri ne,don tun daga sanda ta karanta tarihin manzan Allah take nutsawa da kadan kadan cikin litattafan addini na tarihin annabi da sahabbansa,saboda wani irin nishadi take samu qarin ilimi da dawo mata da wata rayuwa ta shekaru dubunnai da bata wanze a doron duniya zuwa gabanta.

*N A N A Y*

Cikin wani irin yanayi,wani irin tattaki da dama sun riga sun saba lokaci lokaci sukanyi tsakaninta da motii cikin masarautar suke takawa zuwa ga sashen nanay din dake manne dana motii din. Shuru Nanay ta samu kanta dayi,ba kuma don tsokanarta da motii kawai yakeyi ba.....aah,hankalinta ne taji a hankali yana kaiwa kan maganganun motii din.

"Zanga yadda wannan rigimar zata qare khadeeja,haka akeyi tsakani da Allah?,yaro da matarsa?,mema kuke jira?". Can qasan ranta tana jin akhnan din tamkar daya daga cikinsu balqees ko hasnaaa ce. Akwai wani irin narkakken tausayin yarinyar da takeji yana danqare qasan ranta. Duk da har yanzu basu samu zama haisam ya fede mata meye da meye ya faru da safiyya da safeena ba......amma tana ji a jikinta akwai abubuwa masu tsananin nauyi.....akwai abubuwa masu tarin yawa da sukazo suka dinga faruwa suna shudewa.

Akwai abubuwa da yawa.....da dama masu tarin gaske da take karanta tattare da akhnan din. Har cikin jininta take qaunarta,irin qaunar nan dai da takewa safiyya da safeena. Tana tsananin son safeena......tana tsananin son safiyya,hakanan a yanzu take shauqin son ganin safiyyan data rage mata,saidai batasan dalilin da yasa haisam din daya kawo mata su ya debi wani lokaci da zai sadata da safiyyan ba.

Amma koma meye ta sani,haisam din wani irin nutsatsen yaro ne me tsari,kyauta daga Allah daya zame mata abun alfahari,ba'a gareta kawai ba,har a gurin danginsa na uwa da uba dama 'yan uwansa gaba daya,ta tabbatar akwai babban dalilin daya sanyashi haka.

Can qasan ranta takejin wani abu me kama da tausayin akhnan,haisam d'anta ne....d'a mafi soyuwa a gareta,zataso ya samu dukkan nutsuwa daga gurin mace ta gari,zataso ya samu dukkan kwanciyar hankali irin wanda kowanne d'a namiji daya dace yake samu,wannan shine babban dalilin daya sanya takarkatar da dukka wadannan kwanakin gurin koyawa akhnan din basic abubuwa da zata kula da mijinta da kanta.

Ta lura akwai abubuwa da yawa da bata iya ba,baata saba ba,batasan ma yadda zata yiwa kanta ba ballantana waninta. Ta sani su irin wadannan abubuwan mace ko ke wace,duk gatanki....duk matsayinki inde zaman aure zakiyi baki da wata daraja idan baki sansu ba,baki da wata daraja idan baki koyesu ba,baki da wata daraja idan baki iyasu ba.

A yanayi rayuwar akhnan din,ta karanci akwai gibi da yawa. Ita karan kanta taimaka mata ake gurin kula da kanta,batasan yadda zata yiwa kanta hidima ba bare waninta. Ta kwashe dukkan lokacinta,ta bata wuninta da dararenta wajen mata wasu karatuttuka,tana kuma fata ko yaya su amfaneta.

Ta sauke ajiyar zuciya tausayinta yana sake ratsata. Indai har haisam ya gaza jurewa ya taba akhnan din,ta sani ba zataji da dadi ba. Tayi imanin zataji a jikinta ainun. Tafi kowa sanin waye yaronta.....tafi kuma kowa sanin yaqin data shiga shima ya shiga gurin kare kansa da mutuncinsa.

Da gaske ne....kuma gaskiya motii ya fada a yanzun. A yanayin haisam din zai wahala a irin wannan yanayin na kadaicewa tsakaninsa da halalinsa ace Akhnan din takai labari,amma kuma sai ta tuna wani abu guda daya bata relief. Akhnan din period takeyi,duk da batasan yaushe ta fara ba,kuma yaushe zata gama ba,amma tabbas tasan bata da tsarki,ko wannan zai taimaka ta tsallake wannan tarkon?.

Abinka da uwa,haka nan kuma sai taji tausayin haisam ya maye gurbin zulluminta da fargabarta. Abune mai wahala namiji lafiyayye irin haisam din.....ya iya sanya idanunsa akan halittar akhnan baiji komai ba. Abune me wahala namiji cikakke ya iya kallon akhnan ya dauke idanunsa a kanta cikin sauqi. Ba namiji kawai ba.....ita kanta data kasance d'iya a gurinta idan ta kalleta tana maimaita kallonta a kanta ne. Sau tari takan furta.

"Subhanallah" Ko kuma

"Fatabarakallahu ahsanul khaliqeen". Wani irin zubin halitta me kyau da tsari Allah yayi mata,wani lokaci sai ta dinga hangen wani bangaren kyau da ake wassafa matan aljanna dashi,kaman dogon wuya,tsayayyun breast kuma masu yalwa da tudu da sauransu. Ta sani sam bata isa ta hada kanta da matan aljanna ba......amma wasu siffofi na kyay ta san ta hadasu,koda ba dari bisa dari ba,to casa'in da tara ne bisa dari.

"Nanay.....ina giiftii" Noorah data shigo riqe da camera dinta da itace cikakkiyar abokiya kuma qawarta ta fada tana duban nanay dake shigowa a lokacin sassan nata,bayan ta yiwa motii tattaki zuwa inda motocinsa suke jiransa zai wuce wani taron saukar qur'ani.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Readers Also Read

More by Huguma