L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 38
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 38: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 38. Tambayar ta yiwa saamee daidai,sai taji noorah ta…
3,334 words
Tambayar ta yiwa saamee daidai,sai taji noorah ta matuqar bugeta da tayi tambayar. Tambayar da take ranta kenan noorah din ta wakilceta,tambayar da tasan ba zata iya yiwa nanay ita kanta tsaye ba,don tana kula da duk wani abu da zatayi da nanay zata iya gani kai tsaye wanda zai tuna mata da zarginta na Kamar tana son muhamamd haisam din,har komai da zatayi ma ya dasa tunanin kishi takeyi da akhnan.
Da nanay ta daga idanunta ta kalli su rumaisa sai taga kusan dukkaninsu kamar tambayar da noorah tayi mata itace a bakunansu,kawai noorah din ta wakilcesu ne. Murmushi ta saki kadan,wani irin qauna suke gwada mata data juye zuwa wani irin sabo da shaquwa. Sabon daya shiga tsakaninsu zaka dauka dukkaninsu ita ta haifesu,duk da kasancewar akhnan din ba ma'abociyar surutu ba,tana zama kawai a cikinsu tana jin hirarrakinsu da harshen oromo da a yanzun ta iya kaso ashirin da biyar cikin dari. Zata yi murmushi sau tari idan sukayi wani abun,maganarta qalilance,bame yawa ba amma me tarin ma'ana.
"Tana girin obbo dinku.....na barta ta kula dashi" Ta amsawa noorah tana amsar wayarta daga hannun jakadiyarta zuhura.
Wani irin duka kalmar tayi mata tana jin kamar ana girgizar qasa saman kanta. Spoon din abincin data debo ta maidashi a hankali tana ajiyeshi,tana jin wani irin abu yana tsaga zuciyarta da qirjinta kamar iskar dake kai kawo a gurin ta mata kadan.
Ji tayi kaman nanay tana sane ta fadi maganan kai tsaye.....cikin wani irin yanayi take magana na nishadi kuma kanta tsaye. Ta yaya zata bari wannan alaqar ta qullu haka da sauri?. Saita miqe a nutse ba tare data bari kowa ya ankara da ita ba ta soma nufar kitchen tana maida farantin abincin.
"Ta tafi kenan Nanay?" Noorah ta tambaya tana kwabe fuska,sai nanay tabar danna wayar da takeyi ta maida dubanta kan fuskar noorah din.
"Dama batazo don ta zauna damu ba noorah,tana qarasa kwanakinta da saura kwana uku suka rage zata wuce gidanta ita da obbo din naku" Idanu noorah ta fidda.
"Nanay......harda obbo shima?"
"Eh mana....." Ta amsa mata tana tsare noorah din da ido. Shuru ta danyi sai kuma ya furta
"K'nnnn" Tana maida wayarta ta rataya a wuyanta. Tana jin Aanani na mata dariya.
"Autancin nan ya cuceki noorah.....kin dauka obbon zai dawwama ne a nan?". Daga kanta rumaisa tayi daga assignment din da takeyi ta kalli Anaani.
"Ke kowa ma saikin tsokana ne Anaani?" Dariya abinta Anaani tayi.
"Allah banga kyau a autanci ba" Sake jifanta da harara rumaisa tayi.
"Ai baiwa ce,tunda Allah bai baki ba saiki zauna a matsayin da kike kai ki haqura hakanan". Murmushi kawai nanay tayi tana miqewa daga gurin. Irin wannan 'yan qananun fadace fadacen nasu ta riga ta saba dashi tun ba yau ba. Kawai abu daya take tunani,duk randa ta aurar dasu shikenan?,shikenan haka gidan zai mata shuru?,shikenan haka zata daina gilmawarsu ta daina jin muryoyinsu?.
"Nanay" Taji an kirata a tausashr daga bayanta. A nutse ta waiwaya don bataji alamun akwai wani cikinsu daya biyota ba.
Saamee ce,sanye cikin doguwar rigar dake zuwa hade da hijab dinta. Da wannan innocent face din nata me cike da alamun haquri,kamannin da sukayi sak da sak dana mahaifiyarta,babbar hadimarta data zamewa nanay kamar 'yar uwa saboda dadewa da kuma sabo da amana irin ta mahaifiyarta.
"Saamee.....ya akayi?,akwai wani abunne?" Nanay ta fadi tana duban saamee da wannan idanun nata na uwa,da wannan yanayin da take iya karantar kowacce buqata ta d'anta.
Murmushi kadan saamee tayi,tana jin yadda zuciyarta ke tsalle cikin qirjinta. Tanaso ta roqi wani abune da babu shi cikin al'ada.....amma tana jin karamcin nanay zai sanya tayi mata. Zata roqi wani abune da yake cikin manya manyan tsari da schedule dinta na tsanin cimma nasararta.....tana addu'a da fatan wannan zaren da zata qulla ya dauru a daidai.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 68*
"Cewa nayi....me zai hana wani na cikin gida ya kasance da giiftii safiyya a sashen obbo?.....duk da ya saba da al'ada da tsarin masarauta,amma saboda jagoranci da nuni akan yadda komai yake na sauran abubuwan da bata sani ba ko bata fahimta ba na masarauta. Dole ana buqatar makusanci na captain don muna buqatar sirri akan baqin al'ada dake jikinta su kammala ficewa tas ba wani tabu ko aibu da wani zai kalleta dashi,tana buqatar me mata nuni don kula da captain sosai da samar da qarin kusanci a tsakaninsu.....a duba mata cikin amintattun hadimai.nanay,hakan kamar zai sanya komai yafi zuwa mata da sauqi....amintaccen da zai zama me sirri,ina neman afuwa idan maganata tazo a wata gaba da bai dace ba,ina fatan kuma za'a gafarceni da shishshigin da nayi" Ta fada tana maida kanta qasa sosai ba tare data iya hada idanu da nanay ba.
Shuru nanay din tayi,a hankali tana nazartar saamee din.
"Wa kike ganin za'a hadata da ita?".
"Amintattummu nanay.....zatafi samun sauqi akan abubuwan da bata sani ba batare data tambayi kowa ba".
"Zaki iya riqewa da dauke wannan amanar?" Duk da buqatarta kenan,kusantar duk wata mu'amala ta haisam din da akhnan.....duk da burinta kenan amma sai taji kalmar nanay din ta mata nauyi.
"Idan akwai wadda ta fini cancanta nanay......ina ganin ita zatafi dacewa da wannan matsayin".
"Babu saamee,saboda ke kadai kikayi wannan tunanin,saboda bakyason diyata ta wahala ko ta nemi tallafi daga waje akan abinda ya shafi tsari da al'adarmu,....ke zakije,tare kuma da amanar tsayawa iyakar iyakokinki". Har cikin ranta taji wani sanyi yana saukar mata,KUSANCI shi kadai take buqata a tsakaninsu a yanxu. Tanaso ta qarewa mu'amalarsu kallo ta nazarceta,tasan raunin akhnan,ta soka nata qudurin ta qarqashin wannan raunin.
"Na gode da yarda aminta da kikayi dani,in sha Allah......zan kare duk wani muradai da martabarki data obbo dama masarautarmu gaba daya". Kai nanay ta jinjina,tanason gamsar da kanta hukuncin baiyi rashin tsari ba.....kuma ba kuskure a cikinsa.
Takawa taci gaba dayi har ta isa daya daga cikin kebantattun dakunan hutawarta,ta lalubi number wayar kai tsaye ta kira,tayi shuru tana jin yadda wayar ke bugawa ta cikin kunnuwanta a hankali.
*A K H N A N*
Wayarta ce tayi qara a hankali cikin qaramin sound din duka ringing haka suke da wani irin sanyi,ta koma ta zauna a hankali tana duba me kiran.
"NANAY" data gani jikin wayar da take amfani da ita tun a wancan ranar da hasnaaa ta bata ya sanyata daidaita zamanta tana shirin daga wayar.
Wani kima da kwarjini matar ke mata,wani girmanta da nauyinta take gani cikin idanunta. Bata sani ba,ko wannan hirarrakin da takanji anayi akan surukai normally anajin nauyinsu ne?. To amma ba wannan ba......cikin zuciyarta tana jin wani irin kusanci tsakaninta da nanay,bawai kawai iya kunya bane. Tanajinta da wani irin kusanci da yayi kwatankwaci da kusancin da D'A yakeji tsakaninsa da MAHAIFIYARSA.
Da cikakkiyar sallamar da a yanzun ta fara zamewa akhnan dabi'a ta amsa wayar nanay din,cikin sanyi da nutsuwar da takanji ta mamayeta a duk sanda zasuyi magana da nanay.
"Giiftii safiyya" Ta kira a nutse. Sunan yana yiwa akhnan wani irin girma da nauyi idan nanay ta kirata dashi,yana tuna mata da abubuwa masu yawan gaske,yana kuma tuna mata da ita wacece.
"Na'am nanay" Ta amsa mata a nutsen itama.
"Nafito?" Akhnan ta tambaya a hankali,tana fatan Nanay tace eh. Wani irin abu takeji a kowanne sashe na zuciyarta yana danneta da wani irin nauyi da bataso. Wani irin abu da sannu a hankali ta fara zargin SO ne....wannan son dataketa avoiding......wannan son da take qaryatawa.....sannan soyayyar da takejin kunyar tabar zuciyarta tayi amanta. Ta yaya tana mace ita zata fara?. Duka ma wai yaushe tayi saken da wannan abinda takeji din ya juye zuwa soyayya?.
Wannan malamin.....malamin nan dai nasu falaaq.....malamin nan dai da takewa kallon bagidaje.....wannan malamin daya shayar da ita mamakin da har yanzu bata gama kwankwadeshi ba.
Magajin sarauta a wata duniyar da kullum ta daga kai,....kullum ta daga kai taga irin girma da matsayin daya siya mata.....kullum ta daga kai taga tarin qauna da soyayyar daya siya mata ya jawosu zuwa cikin rayuwarta......kullum ta juya tunaninta tana duban yadda ya kawo wata mace cikin rayuwarta wadda ruhin mahaifiyarta ya koma ga ubangijinsa yana mararinsa......saita rasa ME YA DACE TA BASHI?....ME YA DACE TA SAKA MASA DASHI?.
"Ki soshi" Amsar da zuciyarta ke bata kenan aduk sanda ta xurfafa cikin irin wannan tunanin,amma saita juya kan nata a hankali,saita dinga ganin kamar ba a wannan muhallin bane kyautar zuciya.....ba'a daidai wannan lokacin ba.....ba'a wannan yanayin ba sam sam.
"Mun wuce ai,dani da motii" Amsar nanay ta shiga kunnuwanta a hankali suka bata wani sauti na faduwar gaba. Sai data qara yawan numfashin da take zuqa zuwa ga hunhunta tana jin wata siririyar fargaba. Zamanta na duk minti daya a nan gurin hatsari ne.....hatsari ne ga zuciyarta gaba daya. Komai da zata kalla nasa.....komai daya shafeshi idan ta kalla sai taji kamar zuciyarta kamar tana sake nutsewa a cikin wani sassanyan ruwa a hankali da wani irin nisan nutsewa.
"Giiftii" Nanay ta kirata da sautin da yaja hankalinta sosai.
"Na'am nanay".
" Na bashi aronki......ki zama kusa da inda yake,ki kula dashi,na kwana uku kawai". Ta fada a nutse amma kaman itama tanason fahimtar wani abu cikin kalamanta data fada din.
Wani nauyi taji kaman nanay ta aza mata. Sun tafi sun barta.....sun tafi sun barta a muhallin daba kowa,daga ita saishi. Sun tafi sun barta da wannan sheikh din....wannan malamin dai da yake mata tsananin kwarjini.....sun tafi sun barta da wannan mutumin da a kullum....daga ita sai zuciyarta tasan yadda take gudun fanfalaqi.....yaqi da fadi tashin qaryatawa dama boyewa gami da binne abinda ke cikin ranta da zuciyarta gaba daya.
Anya?,tana da qwarin gwiwar jure wannan kusancin?,anya tana da wannan jarumtar?,ta kula dashi?......zata iya?.
"Giiftii" Ta sake kiranta.
"Amma ba kulawa dashi kadai ba......" Ta fadi tana yanke maganar,ta bawa iska dama a tsakani sannan ta sake cewa.
"Ki kula da kanki ma...." Sake jin wani nauyi tayi yana sake daureta sosai. Kunya kuma tana samun kyakkyawan muhalli tana cakudewa da fargaba cikin ranta.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Ki kula dashi da dukka nau'in kulawar data dace......irin kulawar da mace ke bawa mijinta. Karki bari yaga gazawarki duk qanqantarta.....saidai kowacce kulawa tana da iyaka" Ta tsagaita da magana kamar tanason ji ta bangaren akhnan din.
"Yana da hali me kyau,bawai don yana yarona bane......kuma idan bashi da lafiya,yana komamin kamar qanqanin yaro ne,wannan din dabi'arsa ce.....tun daga quruciya har zuwa yanzu daya girma bai sauya ba" Wannan kalmar ta nanay ta qarshe tana jin yadda ta furtata,da wani sassanyan murmushi a cikinta......wani kalan murmushi da koda akhnan bata ganshi ba tasan yana tuna mata da wani bangare ne na quruciyarsa,sai taji kaman Nanay taci gaba,kaman nanay tayita bata labari akan abinda ya shafi quruciyarsa.
"Giiftii" Ta sake kiran akhnan din a tausashe,kiran daya ratsa har zuciyar akhnan din. Sautin ya isa kunnuwanta da wata irin nutsuwa,tana sake ji kamar tana magana da mamminta ne.
"Ko tsakanin harshe da haqori ana sabawa......a kwanaki ukun nan,koda zakiga alamun yana fushi dake....." Saita sake dakatawa,sannan ta dora a hankali.
"Ba fushi bane.....kulawace da baya iya boyeta". Wani siririn murmushi ya kubcewa akhnan......murmushin da batasan yadda akayi ta samar dashi a saman fuskarta ba.
Maganan nanay ta yanzu.....kalmarta data fada a yanzu,hakan yana nufin......ba fushi yakeyi da ita ba dazu?....hakan yana nufin kulawa ce?. Kenan itama tana cikin jerin sahun mutane masu muhimmanci a gurinsa da zasu iya samun kulawa?.
"Idan namiji irinsa yayi shuru......kiji tsoron shurunsa....musamman a inda akayi rashin kyautawa......amma idan yayi magana,wata qofa ce ya bude miki" A hankali ta gyada kanta tamkar tana gaban nanay. A hankali duk wata kalma dake fita daga bakin Nanay ke burgeta......a nutse takejin kowacce kalma daga bakin nanay din tana samun wani kyakkyawan gurbi da matsugunni a ranta. Kamar tana buda mata wani babi ne.....kamar wani kundi me matuqar daraja da muhimmanci take buda mata.
"Yana da wata zuciya da take MAKAHON SO...qila shi yasa Allah ya damqa masa 'yar uwarsa a matsayin matarsa......a jininki da nashi kawai nakejin zaku fahimci juna koda baku magantu wa junanku ba....." Maganan tata ta sake kaiwa qarshe da wani irin taushi.
"Ki zauna dashi..."
"Ki kula dashi......Allah ya tsareku".
"To nanay.....na gode" Ta fadi da wani harshe data fara koyon ladabin magana dashi. Wani harshe da yake mata dadi matuqa....wani yanayi da ita kanta idan tayi magana da mutane dashi yake burgeta.
Idanunta ta lumshe sosai tana relaxing bayanta jikin makarin kujera. Taja iska sosai cikin hunhunta sannan ta fiddata a hankali. Tunaninta gaba daya yana komawa kan nanay ne. Tana jin ta aza mata wani nauyi me girma amma kuma sai takejin kamar dolenta ne.
Ta kula dashi.....ta kula dashi.....idan baida lafiya yana koma mata kamar qanqanin yaro ne.....ta yaya?,ta ina zata fara da wannan aikin me girma da nanay ta aza mata?.
"Zaki iya akhnan.....zaki iya......darajarki....martabarki da mutuncinki a idanun nanay....... Zaki iya akhnan......ki tuna,ya sadaukar......da sadaukar da yawa a kanki......ki tuna akhnan,ya baki kariya ya kula da ciwonki mabanbantan lokuta.....a lokutan da bakisan daraja da girman kulawar ba" Maganar data fara mata yawo kenan a kanta,ta bata wani qwarin gwiwa,ta kuma sanyata bude idanunta a hankali ta maida dubanta kan wayarta.
Number birra ta laluba,bugu daya kamar kullum birran ta daga.
"Kada ku damu da rashin dawowata birra....." Saita gaza qarasa mata tana jin kamar yayi nauyi ta gaya musu tana gurin sheikh haisam....
"Karki damu uwar gijiyata,nanay ta yimin bayani,yanzun haka ina kan hada miki kayayyakin da zaki iya buqata zuwa sassan"
"Na gode" Kawai tace da birran tana yanke kiran.
Iska ta furzar daga bakinta,qwaqwalwarta tana mata bita da tilawar wasu daga cikin qa'idojin masarautar data karanta.
Zata zama daga ita sai haisam cikin sashen kenan iya adadin kwanakin,baqi hadimai ko bayi sai idan su suka lamunce musu shigowa. Duk wani guri da yayi kusa da falukan dake kewaye da dakunan baccin sashen ba wanda yake da ikon zuwa sai bisa sahalewarsu. Zuciyarta tadan buga kadan,ta ware tafukan hannunta tana kalla kamar wadda take neman shawara daga gurin wani.
Koda ta kira shehnaz a yanzun tana jin ita da shehnaz din suna rayuwa ne a mabanbantan duniyoyi. Babu lallai ta fahimci komai daga cikin abinda zata gaya mata. Falaak ce....kuma tana jin nauyin magana data shafi haisam da ita. Ita din gaba take da ita,kamar yadda dukkaninsu haisam din yake gaba dasu.
Qarar wayartata shine ya sake dawo mata da tunaninta daga inda ya tafi,birra ce,ta daga kiran tana sakawa a kunnenta ba tare data ce komai ba.
"An kawo komai da komai ranki ya dade"
"Na gode birra" Ta fada a nutse. Bin wayar da kallo birran tayi,a yanzun data koyi godiya abun mamaki yake baiwa birran,mamakin me yake sauya dabi'arta ne sannu a hankali a hankali?.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 69*
Kayan jikinta ta kalla,suna da dan nauyi kadan,bata iya zama da kaya masu nauyi harta wuni dasu,me ya kamata tayi yanzu?,ta ina zata fara abinda ya dace?. Miqewa tayi tsam ta soma takawa zuwa hanyar fita ko zata samu kayan da birran tace an shigo dasu,saidai tana bude qofar ta tsinci suitcase dinta tsaye a qofar dakin. Ta danji mamaki kadan,don tasan ba lallai birra ta iso gurin,to waye ya iso da ita?.
Bata tsawaita tunaninta ba ta jawota zuwa dakin da kanta,wani abu da cikin rayuwarta ba zata iya tuna sau nawa kwata kwata ta taba yinsa ba.
Ta kwantar da ita tana budeta saqo ya fado cikin wayarta. Hannu ta sanya ta dauki wayar,ganin sunan nanay ya sanyata komawa ta zauna sosai tana kallon wayar.
A nutse take bin rubutun,wani irin tsararren menu ne nanay ta shirya mata. Yadda zata kula dashi step by step,kowanne minti zuwa awa daga safiya zuwa dare.
Koda ta gama karantawa murmushinne ya sake subuce mata
"Ya Allah,na gode daka ceceni" Ta motsa labbanta a hankali tana furtawa. Sosai taji dadi.....taji dadin menu din,kamar tasan abinda take saqawa kenan a ranta,yaya zatayi?.
Menu din ya zame mata kamar wani d'an jagora a sanda take cikin tsananin duhu.
Ajiye wayar tayi ta miqe tana sake bude jakar. Ga mamakinta atamfofi a ciki dinkakku,lafiyayyun super Holland vlisco masu asalin kyau da taushi,marasa nauyi wadanda zasu baka daman sakewa cikin dinkunansu.
Mamaki kadan ya kamata,yaushe yanayin tsarin jaka da suturarta ya sauya?. Duk da bata da masaniyar komai akan suturarta amma wannan sauyin yadan bata mamaki.
Hakanan ta cire doguwar riga a ciki,wadda aka mata wani budadden dinki daga qasa,ya bude sosai,ya kuma zauna das a qirjinta,ya fitar da dogon wuyanta da kafadunta dake tsaye kyam wadanda suka dace da qirar jikinta. Tsaiwa tayi tana kallon kanta sosai,Dinkin ya taimaka wajen fitar da shape din qugunta daya baje sosai tare da budewar da rigar tayi ta qasanta. Cikin ranta karo na farko da taji atmfa ta shiga ranta,ta kwanta mata a rai. Tayi qoqarin ta daura dankwali amma ta kasa,duka hannuwa suka gaji,sai kawai ta wurgar dashi a nan,ta matsa ta dauki wani mayafi data gani cikin kayan ta yafa saman sassalkar sumarta.
Takawa tayi a nutse tana fita daga dakin,sannu a hankali sai hankalinta ya rarrabu wajen neman qofar fita. Kamar wadda aka juyarwa da kai,kaman bada qafanta ta qaraso dakin ba,kaman bayan shigowarta an canza tsarin ginin gurin,saita kasa tantance qofar fita,dole ta dinga bi hanya bayan hanya tana dubawa.
Qofa ta qarshe taga tayi mata kama da qofar data shigo din a dazun,tadan lumshe idonta ta aza hannunta akan handle din tana addu'ar Allah yasa ta dace can dince.
Yadda ta soma tura qofar cikin nutsuwa haka yake daga kanshi cikin nutsuwa yana sauke nakakkun idanunsa dinnan a kanta gaba dayanta.
Zaune yake kan wata irin sofa da zata bashi daman hutawa dama miqewa qafafuwansa sosai. Yana jingine da wani tattausan massage pillow a gadon bayansa yana amsa wayar da tsabar nutsuwa irin tasa bakajin abinda yake fadi,sai wadannan labban nasa masu sulbi dake motsawa a nutse.
A hankali ya soma tafiyar da idanunsa yana sauke mata wani irin kallo,tun daga saman kanta da mayafin data yafa ya zame zuwa rabin kanta saboda haduwa da yayi da sassalkan gashin kanta,har zuwa zara zaran yatsun qafarta da suke nutse cikin tattausan carpet din dake malale a parlor din.
Wannan kallon yaji bai masa ba......sam bai masa ba,bai isheshi ba bai gamsu ba,sai ya sake maida idanun nasa daga qafarsa yana aikensu zuwa ga jikinta a karo na biyu. Tsaiwa ta farko ya dakata daidai qugunta dake juyawa a hankali sakamakon takowa da takeyi zuwa ciki,sannan qwayar idanun nasa suka sake tsaida birki akan cikakkun qirjinta da suka cika rigar jikinta.
"Hutun sati biyu suka bayar.....sunce kayi haquri ka karba a haka,akwai sauran qananun case......" Maganan da omar yake fadi masa kenan ta cikin wayar da yaji ta fara nisa da kunnuwansa ainun,saboda zare wayar da yayi daga kunnen nasa ya ajiyeta kawai a gefansa ba tare daya damu da kasheta ba.
"Subhanallazi khaaliqunaa" Ya fada can qasan maqoshinsa adam apples dinsa yana kai kawo tsakanin maqogoransa daga farko zuwa qarshe.