Kenza eBookz

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 40

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 40

L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 40: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 40. *zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta…

3,360 words

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 71* __________________________

*_Amintaccen gurin siyayya_*

*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*

*_BONONZA DA PROMO akai akai_*

*dukka sai a HUGUMA CLOSET*

*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*

*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*

*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*

*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX __________________________

Kallonsa tayi sannan tayi qasa da kanta,batasan yadda zata gaya masa ba,batasan yadda zatace masa bata sallah ba. Kunya da nauyi takeji,idan tana period dinta ba wanda ya sani,batasan ta inda zata fara masa bayani ba sam.

Baiko motsa ba,shi da yace lokacin sallah yayi amma yana tsaye hannayensa harde a qirjinsa yana qare mata kallo. Alamar jiranta yakeyi kenan?. Kamar yasan tunanin da take ya motsa labbansa a hankali muryarsa can qasa.

"Bani da lafiya....kuma kin sani,amma kin barni a tsaye ina jiranki,muje muyi sallah" Ya fada idanunsa suna lumshe kansu gami da budewa lokaci guda.

Dole ta juya a hankali ta fara takawa,ya bita da idanu a nutse yana jin kamar tana tafiya da wani sashe na zuciyarsa.

Kamar me gadi da ubangidansa haka yake biye da ita,yana sauke kowacce qafarsa a inda ta dauke tata. Takunta......wani irin yanayine a cikinsa me tafiyar da hankali,wani irin taku da yakeji kamar ya banbanta da sauran dukka wani taku daya sani.

Kowanne sashe na jikinta yana motsawa a sanda ta daga qafarta ta kuma sauke da wani irin yanayi me janye hankali.

"Ya salam" Ya fada idanunsa suna sake lumshe kansu gami da budewa bayan da zuciyarsa ta d'arsa masa.

"Maza nawa sukaga wannan takun nata?,maza nawa suka kalleta?,qasashen duniya nawa taje suka kalli wannan jikin?".

" Ba haka bane" Zuciyarsa ta sake fadi masa bayan data shiga masa tariyar halinta. Adadin mazan da ta hanawa damar kallonta kadai......adadin mutum nawa ma suka samu damar ganinta ido da ido,sassanyar ajiyar zuciya ta subuce masa daidai sanda idanunsa suka sauka akan saamee.

Da wani irin sauri ta dauke idanunta daga kansu zuciyarta na wani irin bugawa. Bugun da takejin kamar zai hadu ya tarwatse da zuciyartata gaba daya.

Yadda suka jero,yadda yake biye da ita kamar salon karin maganar nan da ake kira da raqumi da akala. Fes idanunta sukaga yadda yake qarewa komai nata kallo ta baya. Wani abu ya tsaya mata a wuyanta ta dinga jin kamar zatayi amai.

"Barka da fitowa" Kalmar ta fadeta ne saboda taja hankalinsa ko yaya,amma haka kawai yaji Kalmar tazo tayi masa karen tsaye. A yadda yakejinsa dinnan,bayason kusanci daga kowa sai daga gareta,baya buqatar motsin kowa a duniyarsa sai nata. Baya marmarin numfashin kowa kusa dashi sai nata sassanyan numfashinnan da yake fita da wata irin kalar nutsuwa. Kai kawai ya daga a nutse yana ci gaba da binta a baya.

Ta danji mamaki kadan sanda taga shima ya tura qofar dakin data shiga din ya shiga. Ta waiwayo tana dubansa da shagwababbun idanun nan nata. A zahiri zakace shagwaba takeji......amma a bad'ini shi yake narka mata zuciya gaba daya,wani irin MAHAUKACIYAR SOYAYYA takeji tana huda fatarta tana ratsawa zuwa ga jinin da zuciyarta ke aikewa zuwa kowanne sashe na jikinta don samun rayuwa yadda ya dace.

"Ki fara yin alwalar" Ya fada a mugun kasalance yana jin yadda mararsa ke sake daurewa kaman bazai iya sake taka qafarsa ba daga gurin,saidai duk da hakan hannun rigarsa yake nannadewa zuwa gwiwar hannunsa.

"Ko mu shiga tare?" Ya fadi da wani yanayi na kaman neman izini yana narka idanunsa cikin nata.

Idanun nata ta dauke,harshenta yayi nauyi,period ta gama dazun da safe,tana kuma sanya ran ganin tsarki daga kowanne lokaci daga yanzu,saidai batasan sanda zatayi wankan ba bare tayi sallah,don bata sake dubawa ba bare ta tabbatar da jufuf ko qassatul baidaah,wanda ita nata qassatul baidaah dinne(kamar yadda yazo a musulunci alamun tsarki guda biyu ne,yana da kyau kowacce mace ta kula da wannan lokaciin,a wannan yanayin wasu suna barin sallolinsu da yawa,akwai ramuwar sallah game jinin al'ada,mata da yawa kuma basu sani ba,sai a kula da kyau).

"Biftuuu" Ya kira sunanta da wani accent daya sanya taji dukka wata tsiga ta jikinta ta miqe,kafin tace komai kuma ta tsinceshi dab da ita. Zullewa taso tayi saboda tana jin kamar cikin wucewar kowacce daqiqa kasheta yakeyi........kasheta yakeyi da idanunsan nan.....sautin muryarsa......qamshin turarensa......da wani irin kusanci da kaf duniyarta bata taba tunanin akwaishi ba.

Nuna mata banbacin dake tsakaninsu yayi,da wani irin zafin nama ya riqo hannunta cikin nasa sannan ya jawota gaba daya,sai gata tayi kyakkyawan masauki cikin qirjinsa.

Wani irin shuru me dauke da wani irin yanayi ya gilma a tsakaninsu. Jikinta takeson zamewa saboda wani irin nannauyan yanayi da yake bata,wani yanayi daya aza mata wani irin tsoro saboda yadda takejin jikinsa sosai cikin nata,amma yadda taji bugun zuciyarsa da numfashinsa suna fita sai tsoro ya kamata. Ta daga idanunta da sauri tana dubansa,sai ta sake daburcewa ganin yadda wadanan manyan fararen idanun nasa suka sauya launi sannan suka rusuna girmansu yana raguwa sosai.

"Jikin naka ne?" Ta tambayeshi tana dan rudewa,rudewar data nuna har cikin wadannan blue eyes din nata masu daukan hankali.

"Bani da lafiya biftuuu......bani da lafiya" Ya fada muryarsa tana rarrabewa saboda yadda yakejin numfashinsa yana neman masa kadan. Qoqarin zamewa tayi tana fadin.

"Sannu.....bari na dauko maganin da nanay tace....." Maidata jikinsa yayi yana fadin.

"Wannan maganin ba?.....wannan maganin bazaiyimin komai ba biftuu" Yayi maganar kamar qaramin yaron daya rasa uwa a sanda yake tsananin buqatarta yana kwantar da kansa saman kafadarta.

"Sai wanne?,saina yiwa nanay magana a kawo"

"Kece......kece maganin akhnaann!" Ya fadi da wani irin harshe muryarsa tana komawa can qasan maqoshinsa yana sake matseta a jikinsa kamar zai ballata.

Wani irin shuru tayi zuciyarta na bugawa da matsanancin guda da taji kamar zata fasa qirjinta ta fito. Qwaqwalwarta da tunaninta suka hade guri daya suka damule gaba daya.

"Itace maganin?.....ta yaya ta zama magani?" Tambayar data sanyata yin shuru kenan tana Jin yadda jikinsa yayi wani irin dumi kaman wanda zazzabi.ke shirin saukar masa.

Gaba daya ya dagula mata lisaafi ya kuma dagula mata tunani,ta gaza gane wanne irin lalura ne haka?.

"Ta yaya?" Ta fadi a hankali da gasken gaske tana son sani.

Kaman jira yake ta fadi,ya sassauta riqon da yayi mata din,yadan janyeta daga jikin nasa a hankali sannan ya sanya dukka tafukan hannayensa guda biyu ya daga fuskartata yana kallon cikin idanunta.

"Idan na fada miki......zaki zamarmin maganin?,kinyi alqawari?,zaki taimakeni?" Ya fada a jere idanunsa suna narkewa cikin nata.

Yanayin data gani tattare dashi taji ya mata nauyi da yawa. Ya mata abubuwa masu kyau da yawa cikin rayuwarta,duk da har yanzu bata gama sanin wani bangare nasa ba......amma abinda ta sani shi alkhairi,ko yaya akayi maka shi kayi qoqari ka saka daidai gwargwado,ka zama dan halak daidai da abinda zaka iya.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Zanyi......in sha Allah" Wani sanyi yaji yana ratsashi,a hankali yaji ta haura zuwa mataki na biyu cikin zuciyarsa da rayuwarsa,ya lumshe ido yana jin girmanta da kimarta ya dadu.

Ya sani......batasan wanne magani yake nema ba......batasan wanne taimako yake buqata ba.....amma kai tsaye ta aminci ta tsaya a gefansa......ta tsaya cikin rayuwarsa.

"Muyi sallah.....saina fada miki".

" Ka fadamin naga abinda zan iyayi kafin muyi sallar" Amsar data sanya ya bude idanunsa dukka a kanta,yana sake jinta cikin wata qololuwa ta zuciyarsa.

Irin wannan attitude yake nema daga mace idanu rufe.....macen da zata aminta zata sadaukar maka komai girman wannan sadaukarwar.....macen da zata aminta ta tsaya kusa da kai......macen da buqatarka zata fara zuwa farko kafin tata....duk da girman buqatar,duk da rashin sanin taqamaimai rawar da zata taka a rayuwarka......irin wannan dabi'un yake nema.....shi kuma ya sadaukar da rayuwarsa da komai daya mallaka,ya qarar da sakanninsa.....mintunansa......awanninsa......watanninsa.......dama shekarunsa na rayuwa gaba daya a kanta.

Wani lallausan murmushi ya kubce masa,murmushin daya sake sanya idanunsa suka lumshe.

"Idan an kira sallah.....komai ajjiyeshi akeyi har sai anyi sallar....."

".....ina fashin sallah" Ta fadi tana katse maganarsa gami da juyar da fuskarta gefe daya,don a yanzun ta bashi wannan taimakon da yace itace zata iya shine kawai a gabanta ba tare da tasan ainihin abinda yake buqata daga garetan ba.

Dif yayi.....kamar kawowa wuta da daukewarta. A hankali yaji jikinsa yana sanyi......komai kuma ya soma narkewa yana fita daga kansa.....ya barshi da wannan daurewar marar da kuma wani zazzabi da yaji yana fara kamashi. Hannunsa ya sanya ya kamo fuskarta a hankali yana dawowa da ita saitin inda yake tsaye.

"Har kwana nawa kikeyi?"

"Mene haka?" Ta tuhumeshi can qasan ranta ba tare data iya furtawa ba. Zai titsiyeta ta gaya masa abinda ita kadai ya shafa?.

"A addinance......ya kamata na sani" Ya fadi yana aza tafin hannunsa gefan fuskarta yana sake tsareta da ido.

"Gobe" Ta samu kanta da fadin hakan bawai don ta shirya fadar haka din bane. Ba yau ba ba gobe.....kwanaki da yawa takeso ta cika masa......amma batasan meye a cikin idanunnnan nasa da bata iya masa qarya ba.

Zare hannun nasa yayi a hankali yana sauke sassanyar ajiyar zuciya.

"Zaki bani magananin?,ba gurin na nanay ba" Ya sake fada a hankali yana takawa da baya da baya zuwa toilet din yana jin gaba daya duniyarsa ta tattara cikin tafin hannunta.

"Nayi alqawari.....na yiwa nanay alqawarin zan kula dakai,bada magani bazai zame min abu me wahala ba......idan na dauki alqawari,inaso naga na cika.....kaman yadda idan aka daukarmin nakeso naga an cikamin" Ta fadi a nutse tana bayyanar da wani sashe na dabi'arta da ta taba furta masa karon farko.

Ya sani,ya kuma karanci hakan cikin dabi'arta yake.....ko bata fada ba......amma a yau data fada da kanta da bakinta......sai yaji abun ya sake zama cikin kansa.

"Dabi'a ce me kyau.....haline me kyau,domin Allah ya fada......alqawari abun tambaya ne" Ya qarashe maganar yana isa bakin toilet din,sai ya juya yana karanta addu'ar shiga bandaki ya saka qafarsa a nutse.

Tana da wasu qualities.......tana da wasu dabi'u da ita kanta batasan tana dasu ba. Komai zaiyi baya yinsa kansa tsaye,....komai zaiyi yana binciken ingancinsa. Cikin dabi'unta akwai CIKA ALQAWARI. Bata iya qarya ba,kaman yadda bata iya boye abinda yake cikin ranta ba. Tana bayyana zuciyarta ne saman fuskarta koda hakan baiyi daidai da abinda mutum yakeso yaji ko ya gani ba.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 72* ____________________________ *_Amintaccen gurin siyayya_*

*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*

*_BONONZA DA PROMO akai akai_*

*dukka sai a HUGUMA CLOSET*

*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*

*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*

*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*

*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX __________________________

Izzarta.....wani abu da yayi masa dari bisa dari. Mace me izza a gurin 'ya'ya maza DUNIYA CE. Zai wahala a yaudareta ko a cutar mata ta wasu hanyoyi da basu kamata ba. Zata kamewa miji kanta.....ba namijin daya isa sai MIJINTA KAWAI mallakinta. Zata bashi dukkan soyayyarta saboda shi daya ne ya cancanta ya mallaketa ba tare da wani ba.........uwa uba.........bayan izzarta,ya karanci abinda ya sake fusgarsa shine.......BA'A SAMUN ZUCIYARTA......BA'A SAMUN SOYAYYARTA.....BA'A SAMUN YARDARTA TA SAUQI.

Ya tsarawa kansa zama namijin da zai qwace daga hannun Tarin mazaje.....ba wanda za'a kawo masa ko ya samu yana daga kwance ba.... Ya zabi yayi farautar zuciya,....bawai zuciyar tazo ta sameshi a inda yake ba. A nan maganganun omar suka dawo masa.

Da gaske ne.....itace kalar macen da yakeso......ba'a halitta kawai ba ko zallar ilimin addini.....aah dabi'u. Wasu kebantattun dabi'u da ba jikin kowacce d'iya mace zaka sameshi ba.

Ya kasa son Menelik......ya kasa son saamee duk da tarin qualities da suka hada da kusanci da alaqa dake tsakani.....baisan dalilin hakan ba sai a yanxu. Saboda ya samesu ta sassauqar hanya,qila inda bayan gwagwarmaya ne kamar akhnan.....daya fada masarautarsu cikin tsakiyar yaqi ya zaqulota a tsakiyar sarqaqiyar da batasan tana ciki ba.....a hakan ma tana taurin kai da qi fadin yarda ta zama mallakinsa har sai daya cita da yaqi.....qila ya sosu suma.

Da tarin saqe saqe ya daura alwala ya baro toilet din. Tana zaune tana murza yatsun hannunta,tarin saqe saqe ne fal cikin zuciyarta. Ganin fitowarsa ya sanya ta miqe,bai kalleta ba saboda tattalin alwalarsa yakeyi yace da wata dakakkiyar murya.

"Karkije ko ina....nanay tace ki kula dani,kin manta?" Komawa kawai tayi ta zauna,shi kuma ya taka zuwa wannan corner din data gani ya sauke hannun rigarsa,ya jawo wata qaramar drawer sai taga ya fidda wata kyakkyawar farar hula irin ta larabawa ya dora saman kansa,ya tattara dukkan nutsuwarsa kamar yana fita daga wannan duniyar zuwa wata sannan ya kabbara sallar.

Yadda yake sallar a nutse haka take qare masa kallo a nutse. Karon farko data ganshi cikin qananun kaya,amma sai takeji a duniya ba wani d'a namiji data taba ganin qananun kaya sunwa kyau kamarsa. Ta rasa tsakanin jubah da cloak thobe dinsa da qananun kayansa wanne ne yafi masa kyau?.

Abu na biyu yadda yake sallarsa. Yadda yake sallarsa yana sanyata tana jin kamar tata sallar bata karbuwa.....kamar ba daidai take sallar ba,kamar akwai tarin kurakurai a cikin sallartata da abubuwan da ba'a kan daidai take yinsu ba.

Ta dauke idanunta tana sauke ajiyar zuciya sanda ya kammala sallar. Tana kallonsa,ya jima saman abun sallar yana azkar da addu'o'i. Karon farko da taji ya sake burgeta,wani iri haske da kwarjini ke fita saman fuskar tasa.

Da wannan damar tayi amfani don tasan ba lallai yayi magana ta miqe a hankali zuwa parlor.

Tana zaune ita daya daga gefe guda tana lissafin mintunan da suka kwashe cikin dakin ba motsin ko daya a cikinsu. Fitowartata ya sanyata zabura saboda wani abune da bata zata ba.

Kallo daya tak tayi mata ta dauke kai tana ci gaba da takawa zuwa saman dining. Kamar itama ta shareta.....kamar kada tace mata komai amma saita tuna bata haka ya cancanci ita ta bullo ba.

"Akwai abinda ake buqata?" Ta fadi a taqaice sanda akhnan ke buda warmers din.

Cikin ginshira da jan aji irin wanda ya zame mata jiki ta amsa mata bayan shudewar daqiqu kamar ba zata amsa din ba.

"Ba aikinki bane wannan" Ta fadi itama a taqaice ba tare data kalleta ba. Tadan jinjina kai,kamar zata sake magana amma ta kasa,saboda yadda ta amsata din da wani yanayi ne na kedin baki da muhimmanci.

"Ki danyi nesa kadan da nan,idan da buqatar za'a kiraki......." Maganar akhnan ta biyu ta saukar mata da wani irin nauyi da saida ta waiwaya ta kalleta sannan ta amsa da to. Kalmar to din data fita da qyar daga qasan maqoshinta.

Tayi matuqar qoqari wajen zuba komai a qananun bowl,cikin takatsantsan ta zuba a wani qaramin kwando,ta debi magungunan ta zuba akai sannan ta fara takawa tana komawa dakin.

Mamaki.......shine abinda ya saukar masa sanda take tura qofar dakin da kwandon a hannunta. Ya miqe a tausashe yana takawa zuwa gareta idanunsa a kanta. Wani irin kimarta tana ninkuwa a ransa.

A nan kusa,......bai taba zaton zatayi hidima haka dashi ba. Ya sani bata komai.....komai saidai ayi mata,daidai da zuba abincin,kaiwa bakinta kawai ta sani,amma a yau ta zabi ta kwatanta dafa masa shayi,sannan ta kusanto da abincinsa har daki.

"Me zata zama a nan gaba idan ta samu rainon daya dace?" Maganan data sauka a kansa kenan sanda ya isa dab da ita. Hannu yasa ya amshi kwandon idanunsa cikin nata.

"Na gode" Ya furta kalmar da wata zababbiyar murya da kuma zababbbun haruffa.

Har cikin jininta taji kalmar.

"Na gode" To me tayi masa?. Bata manta yadda yake hidima da kai kawon duba lafiyarta ba a duk sanda bata da lafiyar.

Idanunsa lumshewa kawai suke suna budewa sanda tayi zaune a gabansa tana zuba masa abincin. Daga yadda yake komai zakasan bawai ta iya bane.....amma ta burgeshi yadda bata sare ba,bata kuma gayawa kanta bata iyaba bazatayi ba. Komai tana qoqarin zubashi yadda taga nayi,tanayi kuma tana gyarawa.

Ta ballo magungunan ta miqa masa hade da cup din ruwa. Yafi fari qal din tafin hannunta da kallon wanda har kwanciyar jini sukayi saboda tsananin haske da hutu,sannan ya kalli maganin daya tabbatar ance mata yasha ne kafin abinci.

"Bazan sha ba.....banason magani" Ya fadi harda maqale kafada daya.

Karon farko da murmushi ya qwace mata,fararen jerarrun haqoranta qal qal kamar qanqara suka bayyana,abinda ya sake jan hankalinsa kenan.

Kaman shi?,da girmansa amma yace bayason magani?,kai tana tantama ma.

Murmushin daya burgeshi,ya kuma daukeshi ya kaishi wata duniya ta daban. Sai yaji kamar zazzabinsa yana sake ninkuwa,wani abu yana sake kwance masa.

Tafin hannun ta maida ta kulle batace komai ba,ta jawo wayarta tahau kiran da baisan wa ta kira ba,har sai da muryar rumaisa ta bayyana.

"Da gaske ne......bayason magani?" Iya abinda tace kenan,rumaisa kuma ta gane inda zancan ya dosa. Dariya sosai rumaisa ta saki.

"Giiftii.....sai kinyi haquri da obbo.....jinjiri yake komawa nanay idan baida lafiya......bayason magani,gwara a masa allura ko nawa ne da ki bashi tablet yasha. A kan cinyar nanay yake bacci......a nan kusa da ita,itama haka take jinyarsa kamar wata noorah......shagwababben nanay ne".

"Na gode" Akhnan ta fada gudun kada rumaisa ta b'aro wani maganan,don tana kallonsa sanda ya sauko ya dawo dab da ita ya zauna,zai kuma iyajin komai da rumaisa din zata fada.

Tana kashe wayar suna hada ido.

"Tunda an tona miki asiri na.....dole ki zama copy din nanany" Ta fada a tausashe,kafin kuma tayi kowanne yunquri yayi male male saman cinyarta.

Kwanciya yayi rigingine,idanunsa akan fuskarta,tadan shagwabe fuska

"Idan ba zakasha magani ba....."

".....kece maganin.....na fada miki" Ta katse maganna nata yana lumshe mata idanunsa hannunsa harde a qirjinsa,kamar yadda yake kwance a miqe sambal daga can qasa kuma ya harde qafafunsa suma.

".....kasha wannan din....zan baka wancan maganin duk inda yake za'a nemoshi nayi alqawari" Wani sanyi yaji yana ratsashi,ya sake bude idanunsa sosai a kanta.

"Indai zaki bani wancan maganin......zansha wannan......amma ba yanzu ba......sai anjima".

Kai ta jinjina a hankali,don ta gagara magana,ya gama kashe mata jiki gaba daya. Wannan kusancin ita kadai tasan me takeji a cikinsa..

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Shuru ya ratsa dakin na wasu mintuna,ta dauka bacci yakeyi,sai kuma taji muryarsa a hankali da wata irin nutsuwa.

"Khadeeja bint kuwailid" Ya furta da wasu nutsatstsun kalmomi. Bai sake bata daman yin magana ta biyu ba ya sake furta.

"Kin taba jin tarihin me sunanki?....khadeeja bint kuwailid,matar manzo ta farko?" Ya qarasa fada yana bude idanunsa fes a kanta.

"Aah" Ta amsa masa a nutse,can qasan ranta wani abu yana motsa mata game da son jin tarihin.

Numfashi ya sauke a hankali,ya koma ya kwanta saman cinyarta kaman dazun,yana jin wata irin nutsuwa da bai taba samun makamanciyarta koda zai kwanta akan katifar da tafi kowacce katifa tsada a duniya.

"Soyayyar da bata da makamanciya har yanzu a tarihin duniya......soyayyar khadeeja bint kuwailid da manzon Allah S A W" Ta kama masa kalmar qarshe suka maimaita tare,wanda bata sake bari ta kubce mata ba tun daga randa ta karanta a tarihinsa falalar yin salati a gareshi a duk sanda aka ambaci sunansa.

Readers Also Read

More by Huguma