Kenza eBookz

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 41

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 41

L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 41: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 41. "Itace mace me daraja...mai qarfin kudi dana…

3,364 words

"Itace mace me daraja...mai qarfin kudi dana iko.....'yar kasuwa irinta ta farko a tarihin musulunci....amma bata daga kanta ga soyayya ba...." Ya furta a nutse kamar me maida numfashi.

".....lokacin da taga abinda takeso" Sai ya sake dakatawa.

"......ta zabeshi cikin nutsuwa.....ba hayaniya......ba matsawa"

"Kuma bai manta da ita ba ko bayan ta rasu......ya qare rayuwarsa yana ambatonta har a gaban macen da yace yafiso wato nana aisha RA.....ya maimaita mata yana son khadeeja.....ya sake maimaita mata Allah bai musanya masa da wadda ta fita ba......kinsan duk dalilin me yasa ta samu wannan darajar?". Kai ta girgiza a hankali,kwadayinta da son jin cikakken labarin yana ratsata.

Idanunsa ya bude sosai a kanta yana dubanta,

"Ta soshi sanda kowa ya qishi,ta sadaukar masa sanda kowa ya hanashi......ta rungumeshi sanda kowa ya juya masa baya......ta gasgatashi a sanda kowa ya qaryatashi......ta zabeshi a sanda ta fishi dukiya......ta fishi shekaru......itace kuma uwar 'ya'yansa gaba daya banda guda daya tal a ciki". Sai yayi shuru yana duban cikin idanunta. Shuru ya biyo amma yana iya ganin yadda ta kalleshi har sau biyu.

Tanaso tace ya bata cikakken tarihin.....amma kamar mejin nauyin hakan. Murmushi ya saki

"In baki tarihin......ke kuma me zaki bani?" Ya tambaya da wani irin coolness idanunsa kamar namejin bacci. Batasan sanda murmushi ya subuce mata ba,.....a karo na biyu ba tare data kawo komai a ranta ba tace.

"Komai.....komai da kakeso" Kai ya jinjina sosai,sannan ya gyara kwanciyarsa cikin jikinta. A nutse kuma ya fara warware mata tarihin tun daga farkonsa har qarshe.

Tarihin yazo qarshe da kiran sallar magariba dake kwararowa daga babban masallaci zuwa cikin gidan. Sai shuru ya ratsa dakin sai sautin kira sallar. Zuciyarta tayi wani irin sanyi.......wani irin yanayi takeji yana saukar mata.

"Khadeeja da muhammad S A W" Ta lumshe idanunta tarihin yana qawatar da ita. Sunan kuma yana sake mata yawo cikin kanta.

"Kamar sunana da nasa?" Ta tsinci kanta da tambayar kanta da kanta,saita ware idanunta wani murmushi yana subuce mata.

Tunda take kallace kallecenta......tunda take karance karancenta bata taba cin karo da tarihin soyayya me qayatarwa irin wannan ba.

Ya miqe a hankali yana jin yadda zazzabinsa yake sake yawa da kadan da kadan.

"Zanyi tattaki inje masallaci".

" A dawo lafiya" Ta samu kanta da furtawa a nutse.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 73*

Da wani irin yanayi ya tafi ya barta,wani irin sanyi takeji a zuciyarta. Wani wasai takejin zuciyarta,kamar wadda aka bawa kyautar wani abu.

Haka kawai takejin wata walwala ta musamman tattare da ita. Tayi sallah saita shiga wanka. Tunda ta shiga toilet din kansa burgeta yakeyi,wani irin gini da har yanzu idan ta kalleshi,ta kuma hadashi da ginin gidan data baro na koyon al'adu mamaki takeyi. Wadanne irin qwararrun engineers ne dasu haka?. Masu wata irin fasaha?.

Wanne irin iko ne haka masarautar suke dashi?. Ko ina idan ta waiwaya ba abinda take gani sai luxury. Wasu abubuwan da yawa saita dinga hangen yadda aka narka gold muraran akayi abun ado na cikin parlor da dakin gaba daya.

Riga ta saka mara nauyi,tayi magariba tayi isha'i. Har zuwa sannan bataji alamun shigowarsa ba. Taga tex dinsa bayan sallar isha'in.

"My doctor....ina tare da baqi 'yan dubiya" Kalmar ta dinga maimaitawa. Yaushe har ta zama likitanshi? Wanne kulawa ma ta bashi?. Ajiye wayar tana sakin ajiyar zuciya,siririn murmushi yana subuce mata. Sai taji tanason bashi kulawa din sama da yadda ya zata daga gareta.

"Don ramuwa ga kyautatawarsa.....don godiya ga soyayyar nanay a gareni" Ta fadawa kanta da kanta murmushi yana sake wanzuwa akan fuskarta.

Rabonta da abinci tunda rana,wannan ya sanya ta zauna ta debi kadan daga cikin abinda zata iya ci.

Sake duba agogo tayi,bata gaji da zama ba.....amma sai takejin kamar tana cikin kewa....kamar akwai wani abu daba daidai ba tattare da ita,sannan kamar akwai abinda zuciyarta take buqata.

Ta sauke qafafunta kenan da zummar miqewa don ta wuce daki ta sauya kaya kira ya shigo wayarta. Tadam fidda ido tana mamaki,shehnaz ce.....a wannan lokacin?,saita sauke murmushi ta koma ta zauna tana daga wayar.

"Matar nan,nan gaba sai mun fara cika foam Allah sheikh zai bari mu kiraki bama ganinki ba" Idanu akhnan ta fidda kadan,kewar 'yar uwarta yana kamata. Tayi missing rigimar shehnaz......da komai nata. Fadansu da aisa kawai ke iya rabawa.

"Ni matsalata dake ko.....sharrinki baya sallah" Dariya sosai shehnaz ta sauke.

"Da gaske nake miki......ba kowa ke iya kiran wayarki ya samu ba,kin zama wata ta daban......irin matar eh....." Bata qarasa ba ta sanyasu dariya gaba daya ita akhnan din,irin dariyar data kwana biyu batayi ba.

Zama.tayi sosai tana tambayar masarauta dama kowa da kowa,duk da zai wahala rana ta fito ta fadi momma bata kirata ba.

Wani lokacin takanji kamar ta yiwa morsa safiyya tambaya akan nanay,amma saita tuna alqawarin data yiwa nanay din,ba zatayi maganarta da morsa din ba har sai lokaci yayi.

Hira suke sosai,irin wadda suka jima basuyi irinta ba.

"Ina fushi da aisa da gaske shehnaz".

"Ki yiwa aisa uzuri......ta shiga wani aiki ne,amma komai idan ya kammala na tabbatar da kanta zata nemeki,ko waya bata riqewa yanzun". Mamaki ya kama akhnan,duk qaunar aisa da waya?,

" Wanne irin aiki ne wannan?"

"Banace ba....ni kaina batamin cikakken bayani ba". Shuru alkhnan tayi na wasu daqiqu sannan a hankali ta furta.

" Allah ya taimaka" Can qasan ranta tana tuna case din sahel couture,abu daya data sani sultane ya gaya mata ta nutsu ta kwantar da hankalinta,shi zai kula da komai,shi yasa bata sake maganarsa ba.

"Ya ake ciki mutuniyar?" Shehnaz ta fadi da salon tsokana.

"Shehnaz......zaki fara ko?" Ta fada a narke,don ta sani indai shehnaz ta fara magana da irin wannan yanayin,ba shakka saita tuburaka da tsokana.

"Na shigesu.....akhnan wacce irin murya ce wannan?.....sak muryar mutumin daya fara soyayya" Ta fadi tana dariya. Karon farko dariya ta qwacewa akhnan,shehnaz nada tsokana da sharri kala kala......amma sau tari tana da saurin dago abubuwa a zahirin ma'anarsu.

"Banason iskanci shehnaz"

"Tsaya....to me ya faru?don Allah ki gayamin,tsakanina dake akwai Amana fa" Yadda ta marairaice mata ya bawa akhnan dariya wannan karon sosai.

"Babu komai magulmaciya"

"Na sanki ciki da bai.....nafi tsoronki idan kikace ba komai,har gwara kicemin akwai kuma kiqi cewa komai din.....inaso ko yaya naji wani abu game da sheikh......wannan zuciyar......yayi nasarar sace mana ita?" Har tsakiyar ranta taji maganar shehnaz,wani sirri ne dake danqare a zuciyarta,ko yaya kuma tana buqatar wanda zata fitarwa dashi....ko yaya tanason wanda zasu tattuna tare.

"Nace miki fa ba komai......shi baida lafiya ma.....nanay ta bani jinya" Dariya sosai shehnaz takeso tayi,tana sake yarda da maganar nannie da tace dukkaninsu sun girmi akhnan din. Quruciyarta ta dabance a cikinsu.

"Aah.....kice kin zama likita kenan,ko kuma dai zuciyarsa kike gyarawa?" Ta fadi tana dariya. Murmushi tayi itama,tana tuna kalmar daya kirata da ita kenan dazu. Kenan likitar daya kirata......tana iya daukar ma'anar LIKITAR ZUCIYA?.

Kai ta girgiza da sauri,ta yaya?......bai taba gwada furta mata komai da yayi kamaceceniya da wannan ba,bataga komai da yake alamta mata wannan ma'anar yake nufi ba. Tabbas kulawa......dukkan wani nau'i na kulawa ta sameshi. Kalar kulawar data sanyata ta fara jin kanta daban.....kalan kulawar data sanya ta fara gane girmanta yana sama da yadda ta zata yake a baya.

"Bansan me yake nufi ba shehnaz" Ta furta da wani sauti daya tabbatarwa shehnaz har cikin zuciyarta abinda ta fada. Tashi shehnaz tayi ta zauna sosai tana maida yanayinta na nutsuwa.

"Bani labari biftuuu.....ba wani abu daya sauya?,bakya jin komai har yanxu game dashi?......kinsan kalar mijin da kike aure akhnan?.....prince ne.....yariman da yake cikin jerin sahun yarima guda goma da sukafi kowanne yarima gata ilimi kyau da qarfin iko na sarauta a duniya......baki taba googling ba?" Mamaki sosai ya kama akhnan,tadan fidda idanu waje kadan. Dama shehnaz ta sani?,tasan wayeshi amma bata taba gaya mata ba?.

"Ya akayi kika sani?,me yasa baki gayamin ba?". Kai shehnaz ta girgiza.

" Ba lokacin gaya miki wannan bane akhnan,a sannan ba zaki fahimta ba.....amma a yanzu gani ai ya kori ji ko?,mu gyara wannan issue din akhnan please,ki gayamin....." Shuru tayi kawai tana sauraren zuciyarta,zuciyar dake tsalle a qirjinta cikin bugawar kowacce daqiqa.....muddin zata ganshi....muddin yana kusa da ita......muddin zatayi tunaninsa.

"Ya gayamin da kansa....yacemin kamar zuciyata tana gayamin wani abu.......amma naqi saurarenta". Wani numfashi shehnaz ta sauke me nauyi. Tana tsananin son kasantuwar akhnan da haisam,wani irin hadi ne da ita akhnan din batasan adadin dacewar da sukayi da juna ba ita dashi. Batasan yadda labarinsu a yanzu haka ya fara trending bane a duniya ba,da wani irin tittle na HADIN AURE MAFI TSADA DA DACEWA DA JUNA A DUNIYA NA WANNAN SHEKARAR.

"Kina qin jin me?"

"Ban sani ba" Ta amsa da sauri,dariya sosai ta qwacewa shehnaz.

"Kin sani kawai kina tsoron fada ne"

"Ba haka bane shehnaz ki fahimta mana"

"To meye?" Tambayar data tsaidawa akhnan dukkan wani hanzarinta. Bata katse mata shurun ba,har zuwa sanda ta motsa labbanta a hankali.

"Idan na yarda......komai zai canza fa kenan shehnaz?".

"Me kike jira ne akhnan?,me kike jira?,ki gwada wannan canjin mana.....ina me baki tabbacin alkhairi ne.....ina me baki tabbacin canji ne da zaki gode masa......me kike jira akhnan?"

"Nima ban sani ba......amma na sani.....shi bai taba furta komai ba" Wata irin mahaukaciyar dariya shehnaz ta saki har sai da akhnan ta daga wayar tana dubanta.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Lafiya kike shehnaz?"

"Ke za'a tambayar biftuuu......ashe?,jira kike sheikh muhammad yace ina sonki akhnan?,sau nawa kikeso ya maimaita fadi?". Kanta yadan daure kadan,yaushe ya fadi?,indai ya fadi ne ita bataji ba......ko sau daya bata ji ba.

" Ina sonki akhnan ko?" Shehnaz ta sake fadi.

"Ki daina fada please mana shehnaz"

"Oh.....kalmar ta fara miki tasiri kenan......tabbacin ya fada sau ba adadi ganewa bakiyi.......mu ajiye wasa akhnan......sirrine wannan tsakanina dake......ki fadamin.....abu mafi muhimmanci ke ki soshi.....ki fadamin......kina sonshi?".

Sosai tambayar tayi mata nauyi,sosai tambayar ta ninka adadin tsoro da fargabar dake ranta,ta lumshe idanunta a hankali sannan ta miqe tana tattaki cikin dakin.

"Shehnaz....."

"Akhnan....." Ta kirata itama da yanayin data kirata dashi.

"HAISAM........ina sonshi shehnaz......INA SONSHI......" Kalmar da sunan gaba dayansu suka shige kunnensa sanda ya dora hannunsa kan handle din qofar.

Zare hannun nasa yayi a hankali,ya maida qofar data bude ya bameta cikin wata irin nutsuwa da bazata bata daman sanin ankai ga bude qofar ba. Hannunsa da qafafunsa dukka yaji suna rawa,saiya koma da baya da baya a hankali yana zama kan daya daga cikin sofas din da aka qawata hallway din dasu.

Bugawar zuciyarsa keyi sosai,wani irin lallausan murmushi ya subuce masa duk da zazzabin da yakeji yana saukar masa,wanda dajin wannan kalmar sai yaji kaman ya ninku.

Wacce irin sa'a haka gareshi?,dawa take waya data aminta ta sanar masa da abinda ya gani cikin qwayar idanunta tanata boyonsa?,abinda ta share wata da watanni tana fada da zuciyarta a kansa don kada ta fallasata kota tona mata asiri. Ya fahimci tana kiyaye alfaharinta ne......tana kiyaye alfarmarta ne.....bataso ta zube.

"Ba zata zube ba.....wannan alfarmar.....wannan jin kan,wannan alfaharin na diya mace dake cikin jininki bazan bari ya zube ba" Ya fadawa kansa da kansa yana takawa a hankali don kada ta ankara da mutum a gurin yana barin gurin.

Da maganganun shehnaz.....doguwar hirarsu da musayen ra'ayin da suka jima sunayi ta shiga ta sake watsa ruwa. Tana tsaye tana brush tana kallon fuskarta a madubi. A yau a karon farko ta fallasa asirin zuciyarta. Gani take kaman ba ita ba,dole a yau ta yarda ta amince ta fara sonshi.....wannan malamin.....matashin yariman nan dake da abubuwan ban mamaki masu yawan gaske. Yana cikin ranta duk gilmawar daqiqa,ya kamata zuwa yanzu ya shigo ya kwanta ko don yanayin jikinsa......amma gashi har sha daya da rabi shuru?. Tayi iya qoqarinta ta hada kayan abincin adan qaramin parlor din dake maqale da bedroom din kafin ta shiga wankan da take fitowa a yanzu.

Da karsashinta ta bude suitcase dinta tana laluben kayan Bacci,saidai abinda ta gani ya tsaida mata komai. Wasu irin rigunan Bacci ne da basu da maraba da babu,ajiyayyun breast curves ne dasu bayan silk material din da aka ciwa mutunci aka zabgeshi wajen yiwa gown gown wani irin gata da ado na dinkin alfarma daga babban brand dinnan masu samar da kayan bacci na qasar French.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 74*

Ta jima da burin siyan kayan bacci na brand din,amma koda ta taba dubawa duka saita tarar na amare ne dole ta haqura. A yanzun ma haka ta qaraci dube dubenta,kusan komai ma birra bata saka ba. Ba brush sai a bandakin ta dauki wani,skincare dinta turarukanta duka batasa komai ba. Gantalallun kayan baccinnan da batajin zata iya duban koda idanun morsa dasu bare shi da yake ajnabin halittarta.

Ta zauna rai bace ta kira birra amma bata sameta ba,ta gwada kiran dukkan wanda zata kira,amma tamkar hadin baki duk wanda ta kira wayarsa a kashe

"Zan hadu dake" Ta fada cikin bacin rai tana tuna haka tayi mata tafiyarsu saudiyya.

Dole ta dauki wine color a cikinsu wadda tadan fisu mutunci,duk da gefe da gefanta a tsage suke har gurin cinyoyin.

Hakanan ta sakata tana jan tsaki a jajjere,ta qarasa gaban madubi tana kallon kanta.

Ta mata kyau iya kyau,wani irin kyau me daukan hankali,wani irin kyau da ita kanta ta gani cikin idanunta,amna ta koma kamar ahlul kitabi,don dukiyar fulaninta kamar zasuyi tsalle su fito ta qirjin nata. Ribbon din kanta ta zare ta soma taje sumarta bayan ta tattarota ta dawo da ita gaba daya kafadar hagunta. Da kallo tabi duka cosmetics din dake kan madubin,komai na tsadajjen kamfanin creed aventus ne. Ta miqa hannu ta dauka tana qarewa cream din kallo. Wani abu na burgewa yana ratsa zuciyarta game dashi

"you carry yourself quietly… but it says a lot.” ta fada murmushi yana kubce mata. Komai nasa cikin wani irin sanyi yake bayyana,baya nuna koshi waye.....amma komai yana nuna wayeshi.

Tana shafa mayukan zuwa hair da body mist din nasa tana zuqar qamshin,wani yanayi na shauqi yana bin dukka sassan jikinta yana saukar mata da kasala. Ta fesa beard mist dinsa yabi iska ya kuma sauka a hancinta sosai da wani irin yanayi. Murmushi ya qwace mata tana tuna mabanbantan lokuta da take tsintar fuskarta gaba daya cikin lallausan qasumbarsa. Wannan qamshinne.....qamshin da yake hade mata dana jikinsa gaba daya ya maida zuciyarta wasa susutacciya. Duk iya qoqarinta kuwa na kame kanta da danne abubuwa masu tarin yawa,amma hakan yana son yafi qarfinta. Amma zata iya?.....aiki da shawarar shehnaz?.

Rigar tafe take da band color dinta da wani siririn pants da igiyace kawai take riqe dashi,ta ajiye band din gefe,ta daga pant din tana kalla sannan ta saki tsaki tana jifa dashi,daidai sanda ya bude qofar dakin sanye da wasu cotton pyjamas wine color,pant din ya sauka gaba daya a fuskarsa.

Qamshin creed aventus dinsa da tayi amfani dashi ya fara zuqa a jiki,sannan ya saka hannu yana zare pant din. Sama ya dagashi yana son tantance mene?,daidai lokacin da idanunta suka sauka akan pant din itama sannan suka zarce cikin nasa idanun.

A sannan....ji tayi inama qasa tana iya tsagewa biyu ta shige ciki?. Pant dinta a hannunsa?,ya dagashi yana qare masa kallo?. Sai kuma a hankali tunaninta yabar kan nan......tunaninta ya fara komawa kan jikinta sanda taga yana sauke pant din yana aza dukkan dubasa akan gangar jikinta. Da wannan narkakkun idanuwan

"This is not ordinary....." Ya fada can qasan ransa,yana jin wani abu da yafi magnet qarfi da girma yana fusgarsa da wani yanayi me tsananin tasiri.

Karo na farko a duniya da idanunsa suka taba ganin wani abu mafi daga hankali cikin tarin wannan nutsuwar tasa da kamewa.....qirjinta muraran......bajajjen qugunta.....santala santalan cinyoyinta dake showing kansu ta gefe da gefen tsagar da aka yiwa rigar a duk sanda rigar tadan kad'a.

“…you shouldn’t look like that.” ya furta da yaren faransanci da wannan accent din da a yau ya sake fita tartar da wani sauti me kama da mutumin dake gulma bayaso koda na kusa dashi ya jishi. Yayi maganan birkitattun idanunsa a kanta.....saidai nutsuwarsa bata kauce ba.....bata kuma fasa bayyana a tattare dashi ba.

Yadda yake dosota kai tsaye ya qarasa karya duk wani kuzarinta. Tsoro ne yakeson mamayeta kuma tanason takawa koda towel dake kusa da ita ta dauka ta rage tsiraicinta daya bayyana......amma sai taji kaman an riqe qafafunta.

Takawa yakeyi zuwa gareta,amma yana jin kamar an qara nisan tazarar dake tsakaninsu. Wani narkewa yakejin yanayi tsakanin blue eyes dinta da wine colour din gown din suka cakuda suka bada wani kala na daban.

Ya isa gareta,idanunta cikin nasa....idanun dake cakude da tsoro,tana son karantar kowanne motsinsa ba tare daya kufce mata ba. Wata siririyar tazara ya bayar a tsakaninsu,tazarar da taku daya yayi yawa sosai ya cikasheta. Qamshin creed aventus din dake jikkunansu dukka su biyun ya hadu ya cakude dana juna. Bugun zuciyoyinsu dana numfashinsu suka soma qara adadin gudunsu. Wani irin yanayi.....me kashe jiki.....me narkar da zukatan masoya ke dawaniya dasu.

Akwai shimfidadden tsoro.....wani nau'in kunya me girman gaske dake lullube da ita,amma hakan bai hanata ganin zallar kyan da yayi cikin wine color din pyjamas dinsa masu silki da taushi ba. Kamar ita ko shi wani yasan kalan kayan da dan uwansa zai sanya a wannan daren.....wannan daren da yazo musu da wani irin yanayi tamkar an wanke qwaqwalensu an kuma jefasu wata sabuwar duniya. Duniyar da bawata halitta me rai DAGA ITA SAI SHI.

A hankali taji ya zare siririn band din dake tsakanin yatsunta.....ya kama kafadarta yana juyata tana fuskantar madubin,ya mannata sosai da qugunsa......wani irin abu ya ratsa ta fatarta yana bin kowanne sashe na jikinta yana barin saqo me tsananin nauyi,sannan ya zare kowanne kuzari nata ya watsar gefe.

Hannunsa dukka biyun ya sanya,ya tattaro gashin ta gefe da gefen kunnuwanta yana maidashi gadon bayanta kamar yadda ake kame gashin yaro da ribbon,saidai maimakon ya saka band din ya daure mata,sai ya bazashi saman tafukan hannuwan nasa ya kuma nutsa fuskarsa a cikinsu yana shaqar daddadan qamshinsa. Bugun zuciyarsa ya sake canzawa.....fitar numfashinsa ta qara gudu da wani irin adadi kamar wanda yayi wasan tsere da qafafunsa na tsahon kilomitoci.

Tunda ya taso ya sani.....kusan dukka qabilarsu suna da tsahon gashi,bama iya 'yan gidansu kawai ba,.....saidai bai taba ganin suma irin tata ba. Bai kuma taba sanin yana qaunar dogon gashi ga mace ba sai ranar daya fara ganin nata karo na farko a rayuwarsa. A ranar ya shiga da sumar cikin list na abubuwan da yake qauna daga matar aurensa.

"Bbiif......ttuuu" Ya kira sunanta muryarsa tana wani shaking bayan ya saki dukka sumar ta zuba a gadon bayanta,ya saka hannunsa ta wuyanta ya manneta da qirjinsa yana boye kansa tsakanin kafadunta da wuyan nasa.

"Naammmm" Ta amsa a birkice itama,abinda takeji daga jikinsa zuwa nata wani baqon abune da bata taba sanin akwaishi kaf rayuwarta. Uwa uba wani irin zafin zazzabi da jikin nasa taji yana fiddawa.

"You make silence......difficult....." Ya fadi a rarrabe yana jin kamar zai iya controlling kansa a yau dinma kamar baya......amma jikinsa qwaqwalwarsa da komai nasa suna gaya masa SUNZO IYAKA.

Ido ta lumshe tana jin yadda zuciyarta ke qarasa narkewa,yadda zuciyarta ke qoqarin fita daga mallakinta zuwa tasa ta har abada.

Readers Also Read

More by Huguma