L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 47
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 47: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 47. *_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don…
3,366 words
*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*
*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*
*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*
*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*
*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*
*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee* __________________________
Wani iri nauyi taji yana mamayarta,wani irin abu yana taba zuciyarta.
"Ya aikata kenan" Abinda ta fadi a zuciyarta jikinta yana wani irin sanyi. Hannu tasa ta maida duvet din tana rufe gurin. Kawai sai taji a yau ita ke kunyar akhnan,ba akhnan kawai ba,hatta da jinin kunyarsa taji tana ji. Shi yasa wannan uban zazzabin ya rufeta?,bai kuma kira kowa ko ya yiwa kowa magana azo a taimaka mata ba?.
"Bazaiso ki gani ba....bake ba,kowa ma bazaiso ya gani ba,qilan yanaso ya dawo ya gyara abinsa da kansa ne" Wata zuciyar ta gaya mata saboda sanin haqiqanin halinsa.
Ta sani,tabbas inda yasan zata shigo har dakin taga abun bazai taba fita ko nan da can ba. Ta miqe a hankali jikinta yana wani irin sanyi,tausayin akhnan yana saukar mata. Tasan irin yadda yanayin yake da girma da wahala a gurin kowacce d'iya mace......tasan yanayi ne me radadi qwarai.
Amma kuma ta wani Fannin wani irin sanyi ne yake ratsata,qauna girma da soyayya mara misali ta akhnan tana ratsata.
"Alhamdulillah" Ta fadi can qasan ranta,tabbas safeena tayi haihuwa me kyau.....morsa safiyya tayi halin qwarai da suka iya tsaiwa kan tarbiyyar d'iyarsu har takai budurcinta inda ya kamata a karbeshi.
Batasan me ta nanay ta gani ba,saidai kawai taji kalaman bakinta sun yanke,idanunta ta maida ta lumshe,sai kuma taji muryar nanay din a tausashe tana fadin.
"Sannu giiftii" Sake bude idanun nata tayi tana dubanta,haka kawai sai taji gabanta ya karye da irin kallon da ta gani cikin idanun nanay din. Kallo ne na jin nauyi hade da tausayi,ba irin kallon data gani dazu bane.
"Zaki iya tashi?" Ta tambayeta a tausashe. Da sauri ta daga mata kai gabanta yana faduwa. Ko da ba zata iya ba to tabbas zata tattara dukkan qarfinta ta miqe din don kada nanay din ta gano komai.
"To bismillah" Nanay din ta fada tana ja baya kadan ta bata guri. Ta qyaleta ne saboda tanaso ta miqe din taga iya adadin b'arnar da yaro nata yayi.
Ta tattakura kuwa cikin gwaninta da jarumta ta tashi daga kwancen,sannan ta fara yunqurin miqewa,saidai tuni ta koma ta zauna tana cije lebe gami da riqe "Wayyo Allah" Da taso fada.
"A hankali mana.....karki qarawa kanki ciwo" Nanay data zaburo cikin zafin nama ta fada tana qarasowa gami da riqe akhnan.
"Bakiga yadda jikinki yake bane?" Nanay ta sake fadi tana janye duvet din da zai iya hardeta.
Tayi qasa da idanunta,tana jin kamar nanay din tana fahimtar komai,saidai kafin takai ga sauke idanunta gaba daya,idanun suka fara haska mata yadda gurare da yawa suka baci jikin farin zanin gadon.
Wata irin faduwar gaba ta saukar mata,taji kamar tana daga zaunen jiri zai kayar da ita.
"Meye wannan?" Ta fadi cikin sakalci da rashin sanin komai,saidai tana dire tambayar kwanyarta ta dauko mata falaak a wancan ranar.
"Innalillahi......na shiga uku" Ta fara maimaitawa a ranta tana curewa guri daya.
Itama saida yayi mata irin na falaak din?,tana yabonsa salla ashe alwala ma ya kasa yinta?. Wanne irin babban tashin hankali ne wannan?,Me yasa zai mata haka?,me yasa zai kira mata nanay?,wanne irin tonon silili yayi mata haka?.
Ya tsallake hasnaaa ya tsallake rumaisa ya tsallake dukkan hadimai ya kira mata nanay?. Batasan me yasa bayajin nauyin wasu abubuwa ba.
Hawaye kawai ya balle mata sabo,ita yanzu da wanne ido zata kalli nanay?,ba zata sake yarda da ita ba.....zataga kaman duka laifinta ne. Don idan bata manta ba ai tace mata ta kula da kanta,ashe abinda take nufi kenan?.
Kallo daya kawai tayi mata ta fahimci yanayin data shiga. Ta sani,ko wacece dole a irin wannan yanayin kunya ta dabaibayeta. Ta kasa koda motsa yatsanta,ta wani cure guri daya tana hawaye kamar ta kashe dan mutum.
Tausayinta da qaunarta suna sake narkar da zuciyarta,sai kuma murmushi ya subucewa nanay din mara sauti. Murmushin alfahari da ita.....murmushin nasarar samun suruka irinta. Ba shakka kunya wani abu ne.....kunya adon diya mace ne.....kunya tana burgeta idan ta ganta tattare da d'iya mace.
Hannu tasa ta cire cliff din da aka riqe zanin gadon dashi na gefe guda,ta sanya hannun ta tattareshi can bata iya inda akhnan din bata zaune a kai.
A tausashe ta kamo hannunta ta riqe cikin nata,abinda ya sake yawaita kukan akhnan din harda dan sauti.
Shuru ya ratsa tsakani,har yanzu dariya akhnan din ke bata,murmushi take me gauraye da tausayinta.
"Ai kukan ya isa haka ummm takwara?" Ta furta a tausashe.
"Karki kuka da yawa,kanki zaiyi ciwo......kiyi haquri a madadina a madadin muhammad haisam.....muna nema masa afuwa" Wannan maganar data fada ta qarasa sanya akhnan ta narke gaba daya,wani sabon kukan ya sake zuwar mata.
Shikenan.....ya fadawa nanay din ma,bashi da kunya ta rantse baida kunya,a yanzu ta sake yarda da haka ta kuma sake tabbatarwa.
A nutse nanay ta janyota cikin jikinta ta rungumeta sosai,kuma bata sake cewa komai da ita ba ta barta sai dataji sautin kukan ya sassauta sannan ta fara magana cike da dattako da nutsuwa,har a sannan tana rungume da ita.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Wajibi ne akan dukkan macen data kawo mutuncinta gidan mijinta ta fuskanci irin wannan wahalar daga farko.....duk da tana wucewa ne a hankali kamar bai taba faruwa ba......akwai wahala,amma alfarmarki kenan......alfarmar diya mace kenan da bata da kamarshi har abada. Alfarmar da ba wadda zata sameta......martabar da babu wadda zata sameta sai wadda ta kaiwa mijinta halalinta wannan budurcin. Wani alfahari guda daya da koda bayan shekara dubu ne zaki iya kallon qwayar idanun mijinki ki goranta masa.......kiyi wannan alfaharin ki sake maimaitawa. Koda ya musa komai daga gareki,koda ya musa dukkan alfarma a nan bashi da abun cewa. Ki godewa Allah daya sanyaki cikin matan da suka rabauta da wannan DARAJAR da ALFARMAR......" Sai tayi shuru tana sauke numfashi.
"Alhamdulillah" Ta samu kanta da fada can qasan zuciyarta.
Wani irin kwantar mata da hankali maganganun nanay sukayi,wannan shine yake bata tabbacin abinda ya fada a jiya. Kowanne miji da mata da gaske sunayi kamar yadda yace da ita a jiya. Kenan kowa boyewa yakeyi yana shuru?,kuma haka kowacce takeshan wannan wahalar amma taga sunci gaba da zama shekara da shekaru da mazan?. Kamar nanay din tasan abinda take tambaya a kai tace.
"Wannan wahalar.... Wannan tsananin na dan lokacine,kada ki damu,zaki daina jin komai.....kinsan me nakeso dake?" Ta fada tana dago akhnan din daga jikinta tana duban fuskarta.
Kanta ta girgiza a hankali ba tare data iya yarda ta kalli idanun nanay ba.
"Ki dauka a ranki safeena da safiyya ne dukka a nan" Ta furta tana nuna qirjinta.
"Duk da ban rayu dake ba,amma nima kamar uwa nake a wajenki.....da wannan idon nakeso ki kalleni,da wannan zuciyar nakeso ki saki jiki dani. Zan miki abinda zanwa su rumaisa da Aanani,don baki da maraba dasu a gurina. Ni ba surukarki bace daga yau.....ni mahaifiyarki ce......uwa nake a gareki" Kanta ta gyada a hankali,tana jin wani irin nutsuwa da gamsuwa suna mamayarta.
Wayarta taga ta dauka,tayi kira hadi da yin waya na duka duka mintinan da basufi biyu ba sannan ta ajiye. Riqeta tayi ta sauka daga kan gadon,ta maidata saman sofa ta zaunar da ita a hankali tana bibiyar yadda taka taku a hankali,abinda ya sake ninka tausayinta cikin ranta kenan.
Tana zaune daga saman sofa din kanta a qasa tana kallon yadda ta tattara zanin gadon da kanta,ta bincika ta samo wani cover me zip me kama dana bedsheets din ta turashi a ciki tayi zipping nasa sannan ta dauko wani sabo.
Batakai ga shimfidawa akayi ba akayi knocking qofar. Kai tsaye ta bada damar shigowa.
Dattijuwar macace sosai,wadda tana dan yawan ganinta a sassan nanay sosai. A shekaru zata bawa nanay din shekara kusan biyar,saidai duk da yanayin tsufanta jikinta ya nuna qaqqarfa ce,irin tsufan nan me kyau da yake nuna lallai mutum yana gyara kanshi da jikinsa.
"Qaraso mama" Nanay ta fadi tana buda mata qofar,ta shigo da sallama.
Koda nanay bata gaya mata ba tasan akwai aminci da kusanci sosai tsakaninsu da matar. Daga gidan sarauta ta fito,ta san duk wanda zaa budewa qololuwar daki irin haka ya shigo tabbas amincin yakai qarshe.
Wata leda ta karba daga hannun mamar wadda take ta yiwa akhnan sannu lokaci lokaci,sannun data sanya take sake jin nauyi kamar ta narke a gurin.
Nanay bathroom din ta koma,ita kuma maman ta soma gyara gadon,nan da nan ya koma yadda yake. Daidai sanda nanay ta fito,ta dauki jakar zanin gadon ta bawa maman suna magana da yaren oromo,sai.maman ta juya ta fita.
Ita ta riqe akhnan,ta shiga da ita bathroom din. Cikin bathtub din dake cike da wani ruwa me wani irin launin kala ta taimaka mata ta shiga,sai tayi tsaye daga gefe sanda akhnan din ke nutsewa cikin ruwan idanunta a rufe.
Duk daya gasata sosai dazu,amma a yanzu sai taji ruwan yana shiga jikinta da wani irin yanayi,wadannan cinyoyin nata da takejin qashi ne kawai ya riqesu dumin ruwan dana abinda ke cikin ruwan yana ratsasu har wani lumshe idanu take.
Sau uku ana canza ruwan da wasu kalolin abubuwa,sannan daga qarshe ta tara mata ruwa me dumi sosai.
"Ki sakeyin wanka don kiji qwarin jikinki sosai,ina jiranki" Ta fadi tana ja mata qofar bayan ta fice daga bandakin. Koda ta miqe tana wanke jikinta sai taji jikinta gaba daya ya saki,ciwon da takeji
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 84* ______________________________ https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0
*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*
*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*
*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*
*_Assalamu alaikum my loyal people_*
*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*
*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*
*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*
*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*
*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*
*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*
*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*
*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*
*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee* _________________________
Sanda ta kammala saita kasa fita,ta nade jikinta da towel kawai tana tsaye tana duban madubi. Ji take kamar ba zata iya kallon idanun nanay ba,duk da qwarin gwiwar data bata,amma kunyarta takeji kaman tayi yaya.
Sau biyu nanay na mata knocking.
"Da matsala ne?,ko na shigo?" Sannan ta murda handle din ta fito kanta a qasa.
Tsaf nanay ta taimaka mata ta shirya cikin wata riga me matuqar daukan hankali. Daga yadda nanay ta fiddata daga wani akwati na musamman ta tabbatar ta musamman ce. Gaban madubi nanay ta jata,ta kuma zaunar da ita gaban madubin bayan ta ja mata kujera ta zauna. Tsaiwa tayi daga bayanta tana duban fuskarta.
"Wannan rigar.....motii ya mallakamin ita ne a ranar dana kai nawa mutuncin gidansa kamar yadda kika kawo naki. Na kuma yi alqawarin zan damqata ne kyauta halak malak ga matar d'ana na farko wadda tayi kwatankwacin abinda nayi,saidai shidin Allah baiyi me dogon kwana bane.....na sake ci gaba da ajiyarta da wannan burin,ashe zata zama.mallakin diyata ce. Allah yayi miki albarka,ya baku zuriyya dayyiba.....Allah ya jiqan safeena ya kyauta makwancinta. Allah ya hademin kanku.......ya baku dawwamammen zaman lafiya" Takai qarshe tana buda tafin hannun akhnan din ta saka wani abu da akhnan din bata fahimci meye ba.
"Kome zan baki bazan biya farashin kyautar da kika yiwa d'a na ba......na gode....na gode" Sunkuyar da kanta tayi tana jin kamar zata nutse a gurin,sai nanay din ta sanya hannunta dukka biyun ta dagata.
"Zan wuce dake sashena,don ki samu ki huta sosai" Har qasan ranta taji dadin hakan da nanay tace,amma sai kuma takejin wani iri sanda suke takawa cikin nutsuwa da rakiyar hadimai suke barin sashen haisam din zuwa sassan nanay.
Wani kebantaccen bangare aka bata cikin sassan nanay,don dakin da parlor din qwaya biyu ne tak amma sunfi qarfin a kirasu daki ciki da parlor kawai.
Dab yake da dakunan nanay,saidai akwai lubby daya rabasu kadan,nata yana daga hannun hagu,na nanay yana daga hannun dama.
Ta lura tun kafin su qarasa hadimai da yawa suka kammala gyaran gurin tsaf,nanay da kanta ta shigar da ita,sai a sannan birra da zenebe suka qaraso.
"Ki kula da ita.....ku barta ta huta sosai" Umarni na qarshe da nanay ta bayar kenan.
Hakan kuwa sukayi,sun samar mata da wani yanayi me dadi daya sanyata kwanciya bacci cikin nutsuwa,bayan nanay tasa an kawo mata wani irin farfesun naman da batasan ne meye ba,da wani abu sha me yaji yaji kadan da yafi mata kama da tsumi ko mad'i. Sai wani babban abun rufa me wani irin dumi daya dade a jikinta,wada tana cireshi taji kowacce gajiya ta jikinta tana sauka,sannan zazzabin jikinta yana yin nasa guri,ba jimawa kuwa wani irin bacci me dadi yayi awon gaba da ita.
*_HAISAM_*
A yau ya kalli agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa har baisan adadin sau nawa ba.
Aikin da yake ganin zai kammalashi cikin awa uku ko hudu,sai gashi yana dosar awa biyu ba tare dayakai inda ya kamata ace yakai cikin awannin ba.
Yana cika awa biyu dole ya dauki hutu,ya wuce resting room da yake manne da katafaren office dinsa dake cikin hukumarsu dake addis ababa..
A nutse ya zauna saman tausassar sofa din dake dakin,ya zare socks dinsa yana daukan wayarsa wadda duka hankalinsa yana kai.
Duk bayan mintuna sai wannan cute face din nata ya dawo masa,yadda take jage jage da hawaye.
Ya lumshe idanunsa yana budewa. Daren jiya ne ke dawo masa fes cikin kansa. Moments din gaba daya,wani irin yanayi daya gaza barin kansa,ya kuma rushe tarihin kowanne dare daya taba kashewa a tare da ita.
Banda babban dalili baiga abinda zai sanyashi biyo jirgi tun sassafe,ya baro gefanta ya taho addis ababa da safiyar daya kamata ace tana kwance cikin jikinsa tana hutawa ba.
Kiranta yakeso yayi direct,amma yana tunanin kada yaje bacci takeyi ya tasheta,don haka ya zauna a nutse ya rubuta saqo yana tura mata.
_"I hope the tears are gone now._ _I did not like leaving you that way this morning."_
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Wayar ya ajiye a gefa bayan ya cireta daga silent. Yana sanya ran jin amsa ko yaya daga gareta,ya miqe yana isa dan dining area din dake cikin setting room din riqe da wayar a hannunsa.
Black tea ya samu kamar ko yaushe,kamar yadda me kula da cimarsu yake tsananin kula da tsrin cin abincinsa da yanayin da yafiso. Black tea ne da aka noma ganyan da komai ma daga yankin oromo,wani abu da baya nisa dashi,shi yasa yasha wahala sosai a agadez kafin ya saba da kalan nasu shayin,inda daga qarshe dole yasa aka shigo masa da nasu ganyen a boye.
Abun mamaki a yau sam baya gane test din shayin,duk da yasan irin qwarewar cook din wajen iya sarrafa shayin.
Daren jiya kaf ya dauke taste din a harshensa,tunaninta da gilmawar fuskarta cikin idanunsa gaba daya ya dauke nutsuwarsa.
Yana dire mug din ya sake jawo wayar kusa dashi,daidai sanda kira ya shigo wayar tasa da wata baquwar number.
Kaman bazai daga ba,amma sai ya tuna koma waye ya iya samunsa yana da alaqa sosai dashi. Don haka ya danna koren alama sannan ya sakata a hands free,yayi relaxing sosai cikin kujerar da wannan nutsuwar tasa yana jin wata kasala tana saukar masa daga tuna iya daren jiya kawai.
Muryar macace,mamaki yadan nuna kadan saman fuskarsa sanda take gaidashi.
"Abbi ya gayamin ka shigo addis ababa ko?" Tambayar tadan daure masa kai,ya motsa labbansa a hankali.
"Wacece?" Yayi tambayar kai tsaye. Shuru ta danyi na wasu sakanni,kaman alamunta suna nuna tambayar batayi mata dadi ba.
"Menelik ce" Ta fada a sanyaye. Sunan ya maimaita sau daya sau biyu a kansa kafin mamallakiya sunan ta harba cikin kansa.
"Ayyah...." Ya fada a nutse yana jin tun bata sake cewa komai ba muryar ta ta gundureshi.
"Ya familynki"
"Alhamdulillah.....abbi yace na maka magana ko zakaci abincin dare tare damu?". Zamansa ya gyara a hankali,yana jin yadda zuciyarsa ke sake azalzalarsa da son jin muryar akhnan.
" I'm sorry.....ba dadewa zanyi ba.....banajin zan sake awa uku a addis ababa,na gode qwarai,ki gaida abbi din,idan na sake shigowa zamiyi magana dashi" Ya fadi a kalmominsa a jajjere nutsuwar dake sake zurfafa soyayyarsa a zuciyar menelik din.
"Nima na gode....." Ta fadi duk da zuciyarta ta quntata da kalar amsar daya bata. Ba haka taso taji daga bakinsa ba,yadda ta iya jurewa rashin ganinsa na wadannan watannin bata dauka zai tankwabe cin abinci dare tare dasu ba idan tayi masa tayi. Ta sauke ajiyar zuciya da alama tafiya ce miqaqqiya a gabanta.
Ko digon nasara guda daya bata hanga tattare dashi ba.......amma a yanzun tana jin ta shirya bayyana masa kanta kawai a wuce gurin.
Shi ya yanke kiran ba tare daya tsaya ya qarasa jin kalmominta na qarshe ba. Ya sake duba bangaren massages,ba wani sabon saqo daga gareta,kawai sai ya yanke ya kirata yana kashingida sosai ciki sofa din.
Tun a kiran farko computer ta gaya masa wayar a kashe take. Yana daga kashingide amma sai ya miqe sosai ya zauna yana sake maimaita kiran,kamar bai yarda da abinda na'urar take gaya masa ba.
Karon farko a rayuwarsa daya maimaita kiran wata number kusan sau biyar duka lokaci daya. Kawai sai ya miqe a hankali yana takawa sannan yana laluben wayar hussam. Tuna yanayin daya barta yayi,wani zargi ne ya d'arsu a ransa,ya lumshe ido yana fatan ba haka bane sanda wayar hussam ta fara ringing.
Kira biyu ya masa amma bai dauka ba,a sannan yanajin kamar yaje ya jawo hussam ya lakada masa duka haka yakeji.
Maida akalar kiran nasa yayi ga abdii,kira biyu tal ya dauka yana gaidashi. A nutse ya amsa Kamar a cikin nutsuwar tasa yake.
"Ka dubamin giiftii ta sassan nanay mana".
"Tana sassan nanay tare da ita" Ya bashi amsa a taqaice yana gajarta masa wahalar da yaketa yi da tunaninsa.
"Ya salam" Ya fada cikin ransa,yaushe ta fita zuwa sassan nanay?,ya tambayi kansa. Yana gujewa wani abu,ya sani nanay tana da doka da qa'ida na son cika al'adu,baiso haka ba,yaso tayi zamanta ta jirashi ya dawo koda zataga nanay. Yayi imanin indai nanay ta fahimci wani abu cikin daya biyu. Kota qara kwanakin bashi ita.....ko kuma ta dauketa har sai ta cika wadannan kwanakin,shi kuma abinda bazai iya jurewa ba kenan.