L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 48
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 48: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 48. A yanzun bayajin akwai wani yanayi duk girmansa da zai…
3,367 words
A yanzun bayajin akwai wani yanayi duk girmansa da zai iya jurewa ya raba tsakaninsa da ita. Bazai iya ba ya sani,bazaiwa kansa qarya bama. Ko a yanzun yanajin kamar ya sanya nisan tazara me tarin yawa ne a tsakaninsu.
"Hello obbo" Abdii ya fadi jin shurun yayi yawa.
"Tu yaushe abdii?".
"Kusan awa uku" Amsar abdii ta gama haska masa komai. Idan ta fita ne don gaida nanay zuwa yanzu ya kamata ta koma. Sai a sannan ya tuna,yau din sukayi da nanay zai maidata,tazo ta dauketa kenan.
"Shikenan.....zan sake kiranka idan akwai buqatar hakan."
"To a dawo lafiya" Abdii din ya fada.
Komawa yayi da baya ya sake zama,ya kamata ya zama cikin shiri kawai. Nanay tayi nata shirin shima yayi nasa,da ranshi da lafiyarsa dai bazai bari nanay ya dauke masa mata har sai bayan wasu kwanaki ba.
Wayar ya sake budewa,ya shiga contact,yatsansa ya tsaya daidai kan wata number dake dauke da sunan abbool.
Bugu biyu ya dauka cikin girmamawa yayi masa sallama. Da sassanyar muryar nan tasa ya amsa masa.
"Ina hussam ya shiga?" Ya tambayeshi kai tsaye.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 85* __________________________ https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0
*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*
*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*
*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*
*_Assalamu alaikum my loyal people_*
*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*
*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*
*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*
*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*
*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*
*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*
*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*
*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*
*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee* _________________________
"Yabar wayarsa ya tafi raka wasu baqi da suka kawo sample na turare sukeso kamfani ya fitar musu" Kansa ya gyada a hankali,yasan da zuwan baqin,kuma shine yace su samu hussam su gama maganar.
"Kace masa ya duba wayarsa yanzun.......inaso a dubamin available ticket zuwa dubai tsakanin kwanakin ukunnan,ka gayamin na yaushe da yaushe aka samu saina fada maka wanda zaka yankamin"..
"An gama obbo" Ya fada da tarin girmamawar da ita kadai ta isa ta gaya maka adadin girman da yake dashi.
Kwata kwata sai yaji zaman addis ababa din ya gundureshi,bayajin koda ya zauna zai iya ayin aikin yadda ya dace,don haka ya soma takawa qafarsa babu ko takalmi yana komawa office din nasa ta qofar dake maqale da resting room din.
Yaja kujera saidai bai zauna ba,ya qara laluben wata number ya kira. Shima dai bugu biyun ya dauka da sallama.
"Ka dubamin wanne private jet ne available kayimin booking zuwa jimma.....if possible kada ya haura awa daya"
"Yanzu in sha Allah" Ya amsa masa,sai ya kife wayar yaja kujerar zuwa gaban system din gabansa ya fara tattara bayanan daya fara aiki a kansu yana maidasu documents.
Ya shiryasu don ya turawa bobbo muhammad dawud ne. Sai yanzun ya gane ma'anar hutun da ake bawa angwaye. Shi baima sani ba sam,ya dauka a ranshi hutun na lalaci ne kawai,sai yanzu ya fahimci muhimmancinsa.
Ya karbi hutunsa yanzu kam hannu bibbiyu,zai cinyeshi harda qari ma,saboda yanaso ko sanda zai dawo sosai cikin office dinsa ya kammala da duk wani issue daya shafi agadez.
Yana cikin aika bayanan wayar tasa ta sake qara,ya daga ya barta a hand free.
"An samu jirgin,amma sai nan da awa biyu zai tashi" Ya fada a ladabce. A hankali ya lumshe idanunsa,yana liasafa awa biyun nan cikin kansa. Jinta yake kaman adadin tsahon shekara biyu. A yanzu a yadda yakejin kansa.....inda yana da iko ya kulle idanunsa kawai ya ganshi a gabanta.
"Alright" Kawai ya amsa masa a taqaice,kuma wannan amsar ta isarwa abbool cewa a shirya jirgin kenan.
Iska me zafi ya furzar daga bakinsa sanda ya kammala aike duka documents din,sannan ya rubuta gajeriyar wasiqa ya aikewa bobbo muhammad dawud ta e-mail dinsa,ya kashe dukkan wata na'ura ya daura alwalar sallar la'asar ya fita zuwa masallacin cikin hukumar.
Yadan kashe wasu mintuna talatin a masallacin wai don ya rage lokaci kafin ya dawo office din. Bayason hayaniya wani lokaci ko dogon magana,yau kuma akwai qananun ma'aikata da yawa cikin hukumar da suka sanya masallacin ya zama noisy. Daidai da office dinsa yana da wani irin tsarin gini ne da idan ka shiga ciki ba zakasan abinda ke faruwa koda a bangon office din nasa ba na hayaniyar mutane.
Ya tsaya qofar ta kammala scanning nasa zai wuce,daya daga cikin messengers dinsa ya qaraso dauke da wani kwando.
"Ranka ya dade......saqo ne aka kawo,yanzun nan dan saqo ya juya ya tafi ganin baka dawo ba" Yayi maganan yana matso da basket din gaban haisam.
Idanu ya zubawa basket din sosai,sannan ya maida dubansa ga messenger din.
"Waye ya kawo?".
" Ban sanshi ba ranka ya dade.....amma dai yace idan aka baka katinnan zaka gane waye" Ya nuna dan card din dake ajiye saman kwandon.
Sunkuyawa yayi ya dauki katin a nutse yana budewa. Cikakken sunanta dana mahaifinta daya gani ya fahimtar dashi daga inda saqon yake.
Da yace bazai samu daban kaiwa sama da awa uku ba,bazai zauna cin abincin ba shine aka biyoshi dashi har nan?. Katin ya maida saman kwandon ya ajiyeshi kaman yadda yake da farko.
"Joseph" Ya kirashi da nutsatsiyar muryarsa me zurfi data sanya mr Joseph shiga hankalinsa.
"Na'am yallabai"
"Ka manta dokokina?" Ya tambayeshi a gajarce.
"Ban manta ba ayimin afuwa ranka ya dade"
"Baka manta ba.....amma ka karya.....me yasa?" Ya tuhumeshi hadi da bashi daman kare kansa duka lokaci daya kamar yadda dabi'arsa take.
"Bayanin da yayi da cewa kasan wanda ya aiko da saqonne yasa na karba,amma ayimin afuwa,in sha Allah bazan sake bari wani abu makamancin wannan ya sake faruwa ba" Baice komai dashi ba ya fara wucewa ciki,yanaso ya tambayeshi ya za'ayi da abincin amma kwarjininsa ya hanashi,sai dab da zai rufe qofar ya jishi yana fadin.
"Ka daukesu daga nan,duk yadda zakuyi kuje kuyi dashi" Ya maida qofarsa ya kulle.
Saman table dinsa ya koma ya zauna da tunanin ko zai duba wani abun ya sake ragewa amma sai ya kasa komai. Tsakanin bakin glass view na office din dake haska masa harabar hukumar sosai,zuwa zama saman table sofa da shan coffee baisan wanne yafi yi da yawan adadi ba,baisan ya shanye shayinsa duka ba sai da yaje zai qara ya danna coffee maker din yaji shuru maqatau.
A hankali ya shafa sumar kanshi yana sakin wani wahalallen murmushi. Shi kansa mamakin kansa yake. Abun kamar asiri?,ya zama wani very depressed haka?,duka duka har yanzu baikai awa shida da rabuwa da ita ba.
Can qasan ransa ya lalubi abinda yafi daga masa hankali NANAY ce. Ya sani kunya ba zata bar ta ta iya fita kai tsaye har gurin nanay ba,hakan yana nufin da kanta nanay taje ta sameta kenan.
Taga wannan yamutsatsen gadon?,taka d'iyarta duka a yamutse?.
"Ya salammm" Ya fada yana jin nauyin nanay din tun kafin ya hada idanu da ita.
Saidai yana ji a ransa muddin ta dauke masa mata ne,hakanan zai runtse idanunsa ya tunkareta ya kuma dauke matarsa,koda ta wata hanyar daban ce.
Agogo ya sake kalla,awa daya ya rage masa,yaja siririn tsaki,lokacinma kamar baya gudu,sai ya bulla dressing room dinsa kawai ya soma sauya kayansa zuwa trouser da wata tattausar long sleeve shirt.
Sumarsa ya sake gyarawa sosai,ya canza takalmi da agogo duka. Cikin qasa da minti hudu saiga giant sheikh dinnan ya sauya kamar hawainiya. Sau tari mutane sukan rasa banbamcewa tsakanin manyan kaya da qananu wanne yafi masa kyau,duk da yawan shigarsa ta manyan kaya ce,musamman idan yana jimma. Amma idan yazo addis ababa yana sauyawa da duk kalar shigar da yakeso.
Already drivensa yana jiransa. Ya bude masa murfin motar yana masa barka da fitowa. Hankali kwance ya shiga,don ba wanda ya bari yasan ya fito da yanzun suna biye dashi kafin su barshi ya fita haka salin alin saiya sake bata wasu lokutan,shi yasa kawai ya fita ta qofar baya.
"Gida zamu wuce?" Ya tambaya da girmamawa.
"Airport" Ya amsa masa a taqaice yana duban hanyoyin da wani screen a motar ya nuna masa ba cunkoso da adadin tsaron da yake kai da adadin mintunan da zasu cimma airport din.
*J I M M A*
K'arfe takwas na dare da mintuna ashirin motar masarautar ta shigo dashi katafaren harabar masarautar aba jifar din dake dauke da haske tarwai......da tarin security da wani irin tsaro da yasha banban da kowacce masarauta dake kusa da yankinsu.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
A daidai lokacin da ita kuma take tare da nanay. Can cikin bedroom din nanay din da wannan shine karon farko data taba tako qafafunta.
Wani irin tsarin dakin bacci da qiris ya kusa maidata 'yar qauye......ya maidata tunaninta baya tamkar ba daga masarautar agadez ta fito ba.
Cikin wasu lausasan kayan bacci take,farare qal masu wani irin gashi gashi me tsananin laushi dukka jikinsu.
Da farko ta dauka zasuyi nauyi ko zasu dameta,amma data sanyasu sai takejin kamar bata taba saka wasu kayan bacci data matuqar jin dadinsu irin haka ba.
Hira suke wata irin hira da take sake sakawa akhnan nutsuwa da nanay. Tarin qaunar matar da kimarta da martabarta dukka cikin idanunta.
Labari take bata akan mamminta.....mammi safeena. Komai da take gaya mata a yanzu sai takejin kamar sanda yake faruwa tana gurinne. Quruciyarsu......rayuwarsu da yadda suka taso,saidai jikinta kuma ya fara sanyi da yadda nanay ta gangaro kan nau'ikan qalubalen da mamminta ta taba fuskanta a rayuwarta.
Aurenta da ajani.....gallazawar kishiyar da sunanta yayi tsaye cak cikin zuciyar akhnan. ZEENATU take wata qaqqarfar tsanar sunan kanta ya shigeta. Dan uwanta dako suna bashi dashi da aka rasa cikin asibiti......barazana daga wancan matar me suna zeenatu din,take taji hadin fruit din da nanay din ta bata tace tasha ya fita duka a kanta.
Murmushi kadan nanay tayi tana goge qwallarta.
"Komai ya riga daya wuce kada ya dameki,kuma ni da duk wanda ya rayu da ita muna kyautata mata rahamar Allah. Macace me wani irin nagarta......kiyi qoqari kawai kiyi koyi da nagartarta".
Kawai sai taji tana kunyar kanta da kanta. Dukka wadannan abubuwan mahaifiyarta ta fuskanta?,harda auren mutumin da bata shiryawa ba?daga mahaifin da baisan wata wahalarta da girmanta ba,auren mai mata har biyu itace ta uku?,ta karba bata musa ba......amma ita fa?.
Ta nemi bijirewa sultane.....sultane din daya sadaukar da komai saboda farincikinta. Sultane din da komai zaiyi yana duba maslaharta,ta hambarar da dukka zabukansa.....sannan ta tattare qafar wandonta dana hannu zata tankwabar da zabinsa na qarshe.....zabin da a yanzu zuciyarta a kowacce rana take gaya mata BAKI GAMA SANIN WAYE BA. Zabin da ko a yanzun komai ya qare.....komai ya datse tayi imanin da gaske sultane masoyine da babu irinsa a duniya.....zabin da a yanzun zata iya daga hannu ta gayawa duniya NAGARTACCEN ZABI NE. Zabi ne mafi sanin ciwon diya mace....mafi iya tausayawa da tausasawa cikin mu'amalarsa.
Bai ko waiwayi sashensa ba,ya wuce kai tsaye zuwa ga sassan nanay. Da confidence dinsa,ya saba tun a baya,duk inda yaje ya dawo sassan nanay shine guri na farko da yake fara saka qafarsa don tasan da dawowarsa,to yau dinma sai yakejin bashi da wani haufi ko fassara da nanay zata masa,don ba baqon abu bane zaiyi.
Cikin girmamawa dukkan hadiman ke zubewa suna gaidashi,har ya iso babban parlor din dake dab da sassan dakunanta.
Babbar jakadiyarta ce ta iso,ta zube tana miqa gaisuwa.
"Allah yaja da ran yarima.....yarima mazan fama.....zaki kuma dodon masu laifi" Murmushi ya danyi,matar tana cikin amintattu mafi dadewa cikin masarautar da suka jima tare da nanay.
"Barkanki.....nanay fa?" Ya tambaya yana duban lokaci.
"Tana ciki...ayi maka iso ne?" Kai ya gyada a hankali. Bayason shiga kai tsaye nanay din ta masa wata fassarar,don haka yayi zaune yana jiran dawowarta.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 86* ____________________________ *_Amintaccen gurin siyayya_*
*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*
*_BONONZA DA PROMO akai akai_*
*dukka sai a HUGUMA CLOSET*
*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*
*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*
*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*
*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________
Kafin kowa a cikinsu ya sake cewa komai bayan shurun,jakadiyar ta nema iznin shigowa.
"Qaraso hawwa" Nanay ta fadi tana gyara zamanta.
"Yarima haisam ne ya qaraso......yana zaman jiran ganinki" Dubanta sosai nanay tayi,kafin a hankali tace
"Kina ganin ya cancanci ganina yanzu?....kice ina masa barka da dawowa.......zai iya tafiya saida safe,bazam samu fitowa ba,ina da mara lafiya" Ta fadi sannan ta dauke kanta tana maidawa ga akhnan.
Taji komai,amma tayi kamar bata jiba,taci gaba da juya fruit din cikin bowl din. Miqewa jakadiya hawwa tayi tana ficewa a nutse.
Idanunsa ya lumshe sanda take isar masa da saqon har ta kammala,ta kumaci gaba da zama tana jiran jin abinda zaice.
Kamar bazai magantu ba saboda wani matsewa da zuciyarsa takeyi,ya tabbata dai ta dauke masa akhnan ne,kuma tunda ta hanashi ganinta yasan tabbas wannan horon da wannan hukuncin takeson masa.
"Ki shaida mata,alfarma daya ta gaisuwa kawai" Ya fada a hankali. Qasa da kanta jakadiya hawwa tayi,sannan ta miqe da girmamawa tana komawa.
Shuru nanay tayi tana saurarenta har ta kammala.
"Baki gaya masa ina da mara lafiya ba?"
"Na shaida masa ranki ya dade"
"To ki sake jaddada masa hakan.....bana buqatar qarin aike kuma"
"In sha Allah" Ta fada tana miqewa.
Waiwayowar da nanay tayi shi ya sanyata saurin sadda kanta qasa tana latsa wayarta da noorah ta miqo mata tace ana kiranta. Zuciyarta na bugawa a hankali a hankali,fatanta kada nanay ta karanci komai cikin idanunta,fatanta nanay bataga komai ba.
Murmushi ne kawai ya qwacewa nanay can qasan zuciyarta,irin wanda ko a saman fuska baya nunawa. Zata barta akan bata ganta ba.....amma yanayin ya mata dadi sosai.
"Allah yasa su zamewa junansu sanyin idaniya" Abinda ta furta kenan sannan ta miqe a nutse.
"Zansa a tura miki Aanani,kamar akwai abinda kikace kinason tambayarta ko?" Kai ta gyada a hankali ba tare data iya dagowa ta dubeta ba,don sosai gabanta yake faduwa na hada idanun da sukayi da nanay.
A nutse nanay ta juya ta fita,ba taqi zuwa ganinsa bane saboda wani laifi ba,aah....idan akwai laifin ma daya ne,na kasa daga qafa yayi haquri da kwanaki ukun da suka rage. Ta kasa zuwa ne saboda ita kanta kunyarsa takeji. Wannan yaron data haifa ta riqeshi tsakanin hannuwanta ta raina a yau har yasan wata diya mace?. Idan ta tuna ita kanta kunyar hakan takeji.
Siririyar ajiyar zuciya ta sauke sanda taji fitar nanay. Tana jin maganan noorah sama sama dake bata labarin walimar da hussam zaiyi a gobe ta bikin aurensu da walimar nanay dinma da za'ayi washegari.
Ba duka hankalinta ke kan yarinayar ba,hankalinta yana can......can parlor din da haisam yayi aike har sau biyu wa nanay taqi kula da buqatarsa.
Haka kawai taji tausayinsa ya sauka a zuciyarta. Indai batun gaskiya zata fada.....ba shakka yana da haqurin da a gurare qalilan ta taba ganin fushinsa da fadansa. Yana da kawaicin da ba'a kan komai yake daga idanu ya kalleka ba bare ya nuna yasan abunda kayi masa.
Saita sauke ajiyar zuciya tana jawo daya wayartata ta kunnata,don bata lura tun safe a kashe take ba,daidai sannan saqonshi na dazu ya fado. Na farkon ta fara dubawa,sannan ta tafi na biyu da yake cewa.
*_I have been in meetings for hours… and somehow you are still distracting my mind._* *Did you rest?*
Wani murmushi ya subuce mata a hankali,kyawawan labbanta suka motsa. A hankali taji kalaman suna melting zuciyarta,wani tausayinsa ya taso yana danneta. Sai taji kaman taje ta roqi nanay ta ganshi.....sai taji kaman ta tashi taje ta bashi haquri,sai taji kuma tana hucewa daga jin haushi da tunanin shine ya turo mata nanay.
Saidai me?,tana bude idanunta saita tsinci nanay a tsaye a kanta,da alama tayita sallama ne bataji ba.
"Tunanin me kike haka?" Ta fada tana sunkuya ta dauki muqullin data bari a gefanta. Da sauri ta kifa fuskar wayar,ta kuma kasa cewa nanay komai harta dauki keys din ta fice.
Tana sake daga fuskar wayar saqo ya shigo mata ta WhatsApp. Bata fiya hawanshi ba,amma yanzun sunan shehnaz ta gani,don haka tayi clicking da sauri tana budewa.
Wani faffadar banner ne me matuqar girma da kyau,wanda ke dauke da sunan MAISON AKHNAN.
Basai tayi tambaya ba,don daga gefe akwai qananun rubutun dake gaya mata. Wannan kamfanin da tafi amfani tafi kuma qaunar turarensa sama da kowanne turare.....sune zasu bude sabon kamfaninsu a dubai.
A qasan banner din rubutu shehnaz ta aiko mata da harshen French.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Da alama wannan grand opening din saidai mu gane miki shi.....saura kwana biyar kawai....zai barki?" Idanunta ta lumshe tana jinta tana dan rikicewa.
Taci burin zuwa dubai....taci burin zuwa wannan taron,taci burin zuwa kamfanin ko zata samu ta gana da shugaban,ko zai mata alfarmar siyar mata da wannan qamshin. Qamshin da a yanxi takejin ya zama ruhi da zuciyarta sama da yadda take jinsa a baya.
Tanaso ta bashi mamaki ta mallaki qamshin ba tare da yasan a inda ta samoshi ba.
"Zanyi addu'a shehnaz.....idan ina da rabo,ko ba yanzu ba....ko bayan taron zanje". Voice note shehnaz ta aike mata dashi,wanda dariya ce zalla ciki da tsokana har tana cewa.
"Me yasa wannan princess din tamu ta zama me laushi haka cikin qanqanin lokaci?" Murmushi kawai tayi,saima ta kashe data ta sauka,don ba zata biyewa shehnaz ba. Abu daya ta sani,komai a rayuwa yana da lokacinsa,komai kuma ba zaka taba gane anihinsa ba idan baizo kanka ba.
Ya tafin kamar yadda nanay ta aiko masa. Saidai tun kafin ya qarasa sashensa yayi aiken neman izinin ganin motii a daren.
A ransa yakejin saidai nanay ta masa haquri kawai wannan karon. Toilet ya shiga yayi wanka,sannan ya fito ya shirya cikin Moroccan thobe baqa data haska fatarsa ta sake fidda kwarjini da wani kwantaccen kyau da yawa yawan qabilar Ethiopian oromo suke dashi.
Ya zura flip flops dinsa masu taushi yana kurbar tea din da yau gaba daya shi da dabino kawai ya iya ci. Yana jin kamar za'a rabashi da wani.mafi girma da kimar abinda ya taba mallaka a rayuwarsa ne.
Qarar wayarsa ya dakatar dashi daga shirin fitar da yake. Ya koma ya dauka yana ganin sunan abbool yana yawo.
"Uhmmm" Yace masa yana maqale wayar a kunnensa.