Kenza eBookz

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 49

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 49

L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 49: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 49. "Akwai jet da zai iya tashi dakai qarfe takwas na daren…

3,369 words

"Akwai jet da zai iya tashi dakai qarfe takwas na daren gobe zuwa dubai din......na gama magana da ma'aikatanmu na can,sun kammala shirin tarbarka"

"Good job abbool......ka yiwa hussam magana ya saka maka dollar dubu biyu a account dinka ladan aikin da kayimin cikin sauri" Wani farinciki ya ballewa abbool din,har yana nunawa a muryarsa.

Aiki da mai gidan nasu komai qanqantarsa riba ne dashi,ballantana shi din,mutum ne da yake very serious akan komai nasa,shi yasa muddin zaka zama serious akan kowanne aiki naka taku zata yita zuwa daya. Ya rusuna duk da baya ganinsa ya fara masa godiya....godiyar da bai tsaya ya qarasa saurarenta ba ya datse kiran ya ajiye wayar yana wucewa gurin motii.

Sassanyar iska ce take kadawa a kowanne sashe na gidan. Iskar dake sake kashe masa jiki da saukar masa da wata sabuwar kasala. Dukkan hadimai kowa yana kan aikinsa da wani irin tsari da qwarewa da cikakken horon da suka riga suka samu kuma suka saba dashi daga gurinsa.

Duk inda ya gifta hadimai ne suke zubewa suna gaidashi cikin girmamawa,shi kuma yana amsasu cikin nutsuwarnan tasa da zai wahala ka rasata a tare dashi.

Iska ya zuqa sosai ya fesar daga bakinsa yana duban gidan yadda ya soma yin fayau saboda shigowar dare. Ta yaya zai iya kwana shi kadai yanzun?.

Ta yaya zai fara fuskantar wannan yanayin?. Bazai iya ba,bayajin zai iya karbar wannan sabon yanayin.....wannan kadaicin. Ta yaya zai iya shiga dakin ya kwanta shi kadai,me yasa nanay ba zata fahimceshi ba?.

Kai tsaye yake takawa cikin babban bangaren motii dake da wani tsaro da tsari. Tsaron da komai aka tsarashi akan na'ura dake kula da motsin kowa da isowar baqi. Wani irin katafaren gini me matuqar tsari da daukan hankali,shuru sashen yake a hankali har ya qarasa qofar madaidaicin dakin da aka qawata da wasu irin manyan filalluka masu fibers dake dauke da tamburan da zane na gidan sarauta.

Yana zaune saman lallausar daddumar ruwan madara,hannunsa riqe da carbi. Ya sukuya a hankali yana zare takalmin qafarsa bakinsa dauke da sallama yana takawa zuwa saman abun sallar.

*_to nanay dai uhmmmm......da alama qara za'a kaiki kenan😂😂_*

*_Satin nan da zamu shiga Monday kenan in sha Allah,kowa ya shirya,satin saukar alkhairai ne in sha Allah💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽_*

*_Abubuwa kala kala......sai kowa ya zama cikin shiri_*🙏🏽🙏🏽😄

Asha weekend lafiya Huguma na muku fatan alkhairi

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 87* _________________________ https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0

*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*

*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*

*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*

*_Assalamu alaikum my loyal people_*

*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*

*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*

*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*

*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*

*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*

*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*

*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*

*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*

*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee* _________________________

A nutse ya zauna cikin nutsuwa da girmamawa,idanunsa a rusune gaban moti aba jifar.

Cikakken dattijo,tun daga halayya zuwa kammni da dabi'unsa gaba daya. Adalin sarki kuma jagora da al'ummar qasar jimma ke ji dashi. Zabgege dashi me zubi da surar qabilar oromo ta anihi.

Yana da wani irin kyau wanda akasan yawa yawan qabilun qasar habasha dashi,akwai wasu kammanni kadan nashi da wasu daga cikinsu Anaani da suke debo.

Tare suka shafa addu'ar da ya kammala shi da haisam din. Idanunsa akan haisam,fuskarsa dauke da murmushin da zallar sabo yake nunawa muraran.

"Barka da warhaka abuu" Ya furta cikin girmamawa da rusunawa yana kiranshi da sunan da su kadai ke kiranshi dashi.

"Barka kade muhammad......sannu da qoqari" Motii din ya fadi. Yasan aikin daya tafi yi addis ababa,don ba inda zaije ya boyewa motii din bai sani ba. Kusan duk wani gwagwarmaya da zai shiga yana iya boyewa nanay,saboda ita din uwa ce,tana da tarin rauni da abubuwan da ba zata iya jurar taji ko ta gani tattare da yaronta ba.

Zata iya damuwa ko ta saka damuwa cikin ranta,amma motii kuwa jajirtaccen uba ne da kusan qashin bayan nasararsa shine. A komai yana iya riqe masa hannu. A komai yana dafa masa da dukkan iyawarsa.

"Yauwa motii......fatan na sameku lafiya"

"Alhamdulillah......amma......wanne irin sauqi aikin yazo dashi haka naga harka dawo qasa da lokacin da kace?" Motii ya fada yana kallon agogo gami da jawo wani irin mazubi da akayi mixing gargajiya da zamani wajen qerashi.

Wani irin mazubi ne dake nuna zallar iko da daukan hankali,kamar an sassaqashi ko kuma qerashi akayi.

Qasa ya danyi da kansa yana rasa abinda zaice masa. Wani sashe na zuciyarsa na shawartarsa yakai qorafinsa kawai. Idan ance anfi sabawa da shaquwa da uwa......shikam zaice tsakanin motii da nanay bazai iya zaban daya yabar daya ba. Kowanne a cikinsu akwai kalar sabo da shaquwar dake tsakaninsu,kowanne akwai kalar wani sirri da yake tsakaninsa ne kawai dashi,kowanne akwai kalar maganganun da suke iya tsakaninsu ne.

"Na barwa bobbo ragowan zai qarasa.......tafiyata dubai ne ya taso motii" Yayi maganan yana yin qasa da kanshi.

"Ma sha Allah.....ma sha Allah" Ya fadi da murmushi bayan ya bude mazubin gabansa. Lafiyayyen nono ne da aka zuba masa wani abu me kama da fura sannan aka bishi da sauran kayan itatuwa irin inibi da sauransu. Ya saka ludayin masu kyau na wata irin tasa dake kama da azurfa daya a gabansa daya a gaban haisam din.

"Lokacin yayi ne?.....kamar nine banyi lissafin daidai ba kenan?" Murmushi kadan haisam yayi yana girgiza kai,bayan ya saka hannu ya dauki ludayin. Bawai don yana da niyyar sha ba,....don tun sanda ya tabbatar ba akhnan a sassansa komai ya daina masa d'an d'ano.

"Ya Allah.....kada ka sanya jarrabawata makauniyar soyayya ce" Abu na farko daya fara roqon Allah kenan.

Ya sani,tun ba yau ba,yana da wani irin hali na so me matuqar girma da qarfi ga duk abinda yakeso. Koda dabba ce yake kiwonta,to zai mata so na gaske,wannan ya sanya bai bata saida dokinsa ko raqumi ba,saidai ciwo da ajali ya rabasu dashi. Yadda yakeji yanzu a kanta,awanni kadan da bata gefansa sai yakejinsa wani uncompleted.

"Baka lissafa ba daidai ba motii......kawai inaso nan da gobe ko jibi na fara yin gaba saboda ragowar shirye shirye. Zan shiga masarautar dubai din......sarki mohammad bin rasheed Almakhtoum,akwai wasu royal distribution rights da zan karba daga gurin prince Hamdan bin muhammad Almakhtoum.....still akwai wasu papers da zan kammala concerning na kamfanin......bayan haka mun samu mutane da yawa da sukeso su saka hannun jarinsu a ciki,akwai buqatar mu tattauna dasu. Ba dubai emirate kawai ba......akwai Emirates da kusan hudu da sukeson turarukan da zamu fara fitarwa saboda masarautunsu da royal events nasu" Kai kawai motii yake jinjinawa. Shi kansa ya sani,wata baiwa ce Allah S W T ya sallada shi zai haifeta. Wata irin tarin baiwa ce da Allah ya qaddara ta jininsa zata fito.

Muhammad haisam.....shi ya haifeshi,amma shi kansa yasan cewa wata ajiyar Allah ce yaron. Nasararsa ta girmi shekarunsa. Baiwarsa da hikimarsa ta d'ara shekarun da yayi a duniya.

Dashi da nanay dukka abu guda suke roqa masa MACE TA GARI,sunsani ita daya ce zata sama silar ci gaba da wanzuwarsa a yadda yake,ita daya ce zata tallafeshi ta bashi kafadunta a duk sanda yake buqatar hakan,ita daya ce zata bashi hannuwanta ya kama yaci gaba da tafiya a sanda ya laluba hannunsa cikin fadin duniya yaji WAYAM babu su a raye.....zai karye.....zai fadi qasa warwas.....zai rasa dukkan nasararsa a duk sanda ya rasa MACE TA GARI.

"Allah yayi albarka Muhammad.....ga iyali ka fara ajiyewa......wadannan hidimomin....karka yarda su hanata lokacinka" Murmushi ya saki me sanyi,wannan kalar murmushin da ko yaushe yake cakude da nutsuwarsa. Yana jin motii ya soma sosa masa inda yake masa qaiqayi.

"In sha Allah abu" Ya fada da girmamawa.

"Amma da iyalinka zaka tafi ko?,kasan ba wani abu da zai gagari mutum.....ba wata gajiya da zata da yiwa d'a namiji tasiri me yawa idan akwai mace a gefansa" .

Wani irin sanyi da dadi yaji yana ratsashi.

"Barakallahu fi umrik" Kawai yake maimaitawa a ransa yana yiwa motii addu'a da fatan alkhairi.

"Zanso hakan motii" Ya fada da murya can qasa yana saukar da kanshi qasa. Dakatawa kadan motii yayi yana duban fuskarsa,daga yadda yaga yayin yasan akwai magana ne cikin ransa,fada ne baiyi ba,kaman yadda yake da kara da yakana a lokuta da dama.

"Tunda kanaso.....me zai hanaka tafiya da matarka?" Maganan ya masa nauyin daya sake shafa sumarsa. Ta ina zai fara?,yace nanay ta dauketa saboda ya raya sunnah da matarsa?,ko kuma meye?.

"Tana gurin nanay" Ya furta a hankali kansa a qasa.

Shuru motii kawai yayi yana kafe haisamd din da kallo.

"Tama gurin ta?,bata barta tayi jinyartaka ba kenan?" Motii ya masa tambayar da haisam din yaji kaman yana nutsewa a gurin.

"Tayi" Ya amsa masa kawai a taqaice. Bayaso ya qara komai,bayaso ya sake cewa komai,gani yake komai da zai sake fada kaman zai tona asirinsa ne.

Shuru da wani irin idanun nazari motii ya zubawa haisam din,yanason nazartar komai Koda yaron nasa bai gaya masa ba.

Na wasu sakanni kawai wani boyayyen murmushi ya subucewa motii din. Can qasan ransa yaji kaman ya karanto komai a sunkuyayyen kan haisam daya kasa dagashi.

Shi bai taba ganin rigima irin ta nanay ba,hasalima baisan matarsa rigimammiya bace sai yanzu. Baisan wanne irin so takewa surukartata ba,har idanunta suka rufe tana son illata d'anta?.

"Motii yana kiranki,idan zai yuwu kada yayi sama da minti goma" Abinda kunnuwan haisam suka jiye masa kenan,sai ya daga kansa a hankali yana saukewa akan motii daya ajiye wayar a gefansa. Sai a sannan ya fahimci nanay ya kira,ya danyi rau rau da idanunsa,da wannan yanayin da yakanyi a gaban iyayensa.....wannan yanayin da a gaban mutum biyu kawai yake bayyanashi RAUNINSA. Sai a yanzun da Akhnan ta zama ta uku.....ta ukun da a yanzun tayi wani juyi zuwa ta farkon da tasan rauninsa sama da kowa.

"Abu.....karfa taga kaman na kawo qararta ne". Daga kansa motii yayi yana dubansa sosai. Murmushi ya saki yana juya nonon

"Lallaba maka ita zanyi,ni kaina bani da qarfin fada da khadeeja ai". Murmushi yaso qwacewa haisam,wannan soyayyar,....wannan qaunar na daya daga cikin abubuwan da idanunsa suke kalla suke kuma matuqar burgeshi.

Dukkan power da ikon fada aji motii nada shi saman nanay. Ba wani umarni da take tsantsan bi irin na motii,ba wani umarni da take gaza tsallakeshi irin na motii. Amma motii din ya bata wani irin 'yanci dama da kuma sakewa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Wannan sakewar sabanin ta matan yanzu ce. Wannan sakewar bata sanya nanay tanayin abubuwa marasa kyau ba ko abubuwan da taga dama ba. Ta riqeta ta hanya me kyau da yin komai daya dace,wannan ya sanya motii din ya sake sakar mata sosai. (Qalubale ga matan da Allah ya bawa dama a gidan miji,kiyi abinda ya dace a sanda ya dace da damar da miji ya sakar miki,kada kisa son ranki ko rashin tsoron Allah a wannan damar da kika samu,idan kika sanya hakan sai Allah ya qwace abarsa).

"Kasha muhammad" Ya fada yana sake tura kwanon gabansu.

Yasha daya biyu motsin nanay ya tunkarosu,sassanyan qamshin nan nata na dindindin na turarukan shuwa incense and more,wani qamshi da ya zama signature dinta musamman da dare irin haka idan zata kasance da motii din (Shuwa incense and more +234 704 229 3387).

Yana ganin yadda ta bata fuska sanda ta sanya idanunta akan haisam din. Sai ya sunkuyar da kansa dukka nauyin duniya yana saukar masa.

Sai a lokacin ya sake tuna yadda yabar gadon,kamar ya nuna akwai staining na jini guri guri,kuma duk ta gani?,ya tambayi kansa.

Sama sama ta amsa yadda yake gaidata,ta kuma zarce zuwa gefan motii tana zama kusa dashi da wani zama me nuna tsantsar ladabi. Wannan zaman ya jima yana ganin tana yinsa.....a gaban motii kawai,banda gabansa baiga tana yinsa gaban kowa ba. Zaman yana burgesbi,a tarin shekarun da sukayi dashi bata sauya zama a gabansa ko daya

"Gani ranka ya dade" Ta fada tana sake tsuke girarta,sai haisam ya miqe cak zai tashi.

"Koma ka zauna" Motii ya fada yana boye dariyarsa.

Komawa yayi d'an nesa dasu kadan ya zauna yana cusa yatsunsa cikin lallausar sumarsa kafin ya zaresu yana yin qasa da kansa.

"Cewa nayi.....bari na nemawa yarona aron matarsa...." Yayi maganan yana duban tsakiyar idanun nanay din.

"Aron matarsa" Taji kalmar ta mata banbarakwai a kunnuwa.

Tasan motii,ba sanin jiya ko yau ba,ya fadi.maganan a haka ne saboda dama taji banbarakwai din. Ya fadeta a haka ne saboda ta gane abinda tayi bai hau kan tsari ba,ta yadda salin alin maganarsa zatayi tasiri ba tare daya fito ya fada ba.

Bata dauke Akhnan haka kawai ba sai don saboda shi,amma kuma shi din bazai gane ba. Akwai abinda take jira daga Senegal,kuma sai gobe zai iso,da dare koda safe. Ba kuma zata bashi ita ba sai abun nan ya iso ta mata amfani dashi.

Yadda take fatan ya mallake zuciyar matarsa......haka take fatan matarsa ta mallake zuciyarsa. Tanaso taga gidansa ya kasance ALJANNAR DUNIYA sama da gidan kowanne magidanci data sani. Akhnan da haisam tuwona maina ne,a cikin su batasan wa zataso ba.....wa zata bari?.

"Qarata ya kawo maka kenan?" Ta fada cikin iya rigima irin tata da motii ne kawai ke fahimtar hakan. Murmushi ya maye gurbinsa da dariyar dakeson qwace masa.

"Aah....ko kadan,yazo shaidamin zai wuce gurin bude kamfaninsa ne.....sai naga a yanzun ai ya zama magidanci,bai kamata ya tafi warin takalmi ba......wai wanne irin al'adace haka khadeeja da taqi qarewa?" Fuska ta dauke tana tsuke idanunta.

"Laifi yayi"

"Laifi?" Motii ya fada yana qin duban sashen da haisam dinma yake.

"Eh" Ta fada tana sake tura fuskarta gefe daya ba tare data bari motii ya kalla ba.

Murmushi ya qwacewa motii din bayan ya gama raba idanu tsakaninta da haisam din,sai ya saki murmushi yana sauke kansa qasa.

"A duba mana to muna roqon alfarma"

"Sai nayi shawara" Ta fada hankali kwance. Mamaki ya sake kama motii,ya waiwaya ga haisam yana cewa.

"Jeka muhammad.....jeka abinka" Tsam haisam ya miqe. Satar kallon nanay yakeyi. Shi gani yake kaman nanay din ta sauya masa gaba daya,ta rage ji dashi,kwata kwata kaman ba ita ba.

"Khadeeja......ki bashi matarsa......" Motii ya fada calmly yana duban fuskarta da sauran murmushi akan tasa fuskar.

"Zan duba na gani" Ta sake fadi. Da gaske batason bashi akhnan yanxun,so samu ta gama sabon gyaran daya ballo mata. So take a duk sanda zai sake koma mata yaji kaman a ranar yake sake saninta a karo na farko a rayuwarsa,kaman yadda takeso akhnan din ta samu salama itama ta fara sanin dadi da ma'anar abun bawai wahalar kawai ba.

"Ina guje miki halin d'an yau......haka na gaya miki wancan ranar baki yarda ba.....me ya biyo bayan nan?" Baki ta tura sosai tana duban motii.

"Ni kam abuu.....kai kake goyon bayan yaron nan.....b'arna yayi kuma dole a gyarata. Yayi tafiyarsa shi kadai mana,idan yaje ya dawo ai dole na bashi abarsa ko?".

" Allah ya bada sa'a" Ya fada kawai yana maida kwanonsa gabansa. Shi namiji ne,kuma ya fita sanin dawar garin. A yadda yake ganin idanuwan haisam ya tabbatar zai wahala bai sake shayar da ita mamaki ba,idan da rabon hakan kuma to shi mene nasa?.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 88* ________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________

*H A I S A M*

A hankali ya rufe bangon littafin D'AUQUL HAMMAMAH(ring of the dove) da yake dubawa,littafin daya tattare dukkan wasu sirrika na sanin halayya da dabi'un mace na ainihi. Cikakken ma'anar soyayya,alamunta da yadda shi kansa son yake.

Ba wannan bane karo na farko daya karanta littafin ba,zai iya cewa tun yana da shekara ashirin da daya a duniya ya karanta littafin,ya kuma maimaitashi shi da ire irensa da dama,wannan ya sanya ya tara wani irin sani da ilimi akan halayyar diya mace me yawan gaske.

Yanason littafin,don kullum ya karantashi sabo yake jinsa,amma a yau sai yaji gaba daya littafin bai masa dadi yadda ya saba.

Hasalima yaji yaji idanunsa ke masa,gajiyace kuma fal idanunsa,tunda ya dawo daga gurin motii ya shiga sassansa sai ya kasa zama,dole ya bulla ya koma library dinsa,saboda sanin da yayi cewa shine guri qwaya daya tal dake debe masa kewa komai yawanta. Amma a wannan daren......a wannan lokacin su kansu tarin litattafan sun gaza dauke masa komai.

Ya riga ya tsara,ya kuma sanya a ransa a yau zaiyi bacci me yawa rungume da ita a jikinsa,amma cikin qanqanin lokaci nanay ya rushe wannan tsarin gaba daya.

Ya sake murza idanunsa,baccin yakeji da gaske,amma babu ta yadda wannan baccin zai yuwu ya tabbatar.

"I can't" Ya furta a hankali yana motsa labbansa,kawai sai ya ajiye littafin ba tare daya maidashi muhallinsa ba,ya zura flip-flops dinsa ya bude qofar da zata sadashi da sassansa.

Kayan jikinsa ya zare,ya sauyasu zuwa wasu kalan cotton pajamas masu hasken launi. Ya matsa gaban dressing table dinsa ya sake feshe jikinsa da sassanyan turaren nan nasa,ya gyara sumarsa da comb ya fesa hair mist,bayan ya saka Beard perfume dinsa,na chest hair perfume sannan ya feshe bakinsa da wannan mouth fresh din nasa na mint dan amana. Wayoyinsa ya kashe yana ajiyesu nan,ya taka ya fara fita a dakin a nutse.

*A K H N A N*

Shurunta ya sanya dukkan wadanda ke dakin suka dauka bacci tayi suka fice,saidai kuma idanunta biyu,tana jin sanda nanay da kanta ta shigo ta dubata,ta kashe mata dukka fitilun dakin,ta rage mata Ac sannan ya maida hasken ceiling din zuwa dim light sannan ta fice.

Numfashi taja sosai tana fesarwa. A wuninta daya tak a sashen,ta samu wata irin kulawa data kusa ninkin kulawar da take samu a agadez ta wata da watanni,amma kuma can cikin ranta....cikin cikin ruhinta da gangar jikinta tana jin wani irin emptiness. Can cikin zuciyarta da ruhinta tana jin wani abu kamar bai cika ba......can cikin naman zuciyarta takeji akwai wani abu da take KEWA.

Tayi juyi da mutsu mutsu har batasan iya adadi ba,duka a qoqarin gyara kwanciyarta wai ko zata jita comfortable,kaman wannan yanayin da takeji kwanciyarce batayi daidai ba. At last ta gane muhallin ne baiyi daidai da gurin ba......a qarshe ta gane ba nan ne gurin da gangar jikinta yake buqata ba.

Readers Also Read

More by Huguma