Kenza eBookz

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 50

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 50

L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 50: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 50. "Haisam" Ta fadi sunan a hankali,saidai.kaman ana jiran…

3,370 words

"Haisam" Ta fadi sunan a hankali,saidai.kaman ana jiran ta furta sunan ne taji an buda qofar a hankali da wani irin yanayi da ba lallai ka lura ba idan ba hankalinka yana gurin ba.

Bata tsorata ba......amma rashin zaton shigowar kowa cikin dakin a wannan lokacin yadan bata mamakin da yasa ta wara idanunta sosai ta qasan abun rufar tanason gane waye ya shigo?.

Kwanyarta bata wahala ba.....tambayarta batayi nisan kiwo tana shawagi ba qamshin nan nasa ya gaya mata MUHAMMAD HAISAM NE.

Wani abu ya buga tsakiyar zuciyarta,wani irin yanayi ya saukar mata a hankali,wani irin sanyi yana ratsata tun daga tafin qafarta zuwa saman kanta.

Tunda ya tako qafafunsa cikin dakin,idanunsa suka sauka a kanta yakejin kamar wani magent ne yake jansa. Numfashinsa ya sauya da wani irin yanayi na bugun zuciya a sanda taga daya zuciyar 'yar uwarta. Ya shaqi qamshinta sosai,sabon qamshin da yakeji tattare da ita tun a wancan ranar data shigo hannun nanay dinsa zuwa yanzu.

Idanunsa a kanta,ya sanya hannu yana balle dan maballan gaban rigarsa a kasalce

Tana iya ganin motsinsa a tsaye,batasan me yakeyi ba,saidai koma meye din yakeyi ba abinda yake sanyawa zuciyarta sai wani matsanancin bugu da takeyi.

Tsoro ke saukar mata a hankali,ya akayi cikin sauqi haka ya iya riskar dakin?. Baya tsoron wani ya shigo ya ganshi?,me ma ya kawoshi?" Ta yiwa kanta dukka wadannan tambayoyin. Tayi.shuru ne kawai ta dauke numfashinta,tana sanya ran ya koma inda ya fito yayi zaton bacci takeyi.

A kasalance yake zare rigar jikinsa. Wani irin kwadayinta yakeyi,kwadayin wannan lallausar fatar me sulbi qamshi da taushi. Mahaukaciyar kewarta ce take taso masa,kamar tsohon zakin daya jima baiga abinci ba yaga nama.

Har lumshewa idanuwansa sukeyi da kansu,ya kammala zare rigar sannan a hankali ya nufi gadon ya soma haurawa.

"Me yake shirin yi haka?" Ta tambayi kanta zuciyarta tana bugawa,saidai duk da haka bata shirya fallasa masa kanta idanunta biyu ba,don haka ta maida idanunta ta lumshe. Tana fatan idan ya hawo saman gadon yaji bacci takeyi ya koma,saidai fatanta baici ba,don a hankali taji yana daga duvet din da take ciki,sannan ya fara zura jikinsa cikin duvet din yana hade tazarar dake tsakaninsu a hankali.

A hankali ya mata kyakkyawan masauki cikin jikinsa,wata sassanyar runguma ta baya wadda faffadan qirjinsa ya laqume fadin bayanta gaba daya.

Wani irin sauti zuciyarta ke bayarwa,tanaso ta miqe ta zare jikinta,ta masa magana ko ta hanashi,amma ta gaza aiwatar da ko daya daga ciki,sai zuwa sanda ta aza hannunsa saman ruwan cikinta ya jawota sosai cikin jikinsa yana sanya qafarsa daya tsakanin cinyoyinta yana rabasu.

"Hah......hais......" Ta fadi a rarrabe ba tare data iya fadin cikakken sunan ba saboda yadda taji dumin cinyoyinsa cikin nata suna ratsata.

"You can call my name my healer......amma bata irin wannan hanyar ba..... Qorafi......i hate complain akhnan pleeeeaaaaseee" Ya fada yana dan jan sunan sanda yake nutsar da fuskarsa tsakanin dogon wuyanta da gashinta dake a barbaje a gadon bayanta yana bada wani tattausan qamshin hair mist na kamfanin shuwa incense and more.

"Barka da warhaka my princess......." Ya sake fada cikin wani irin maye kamar wanda yasha giya ya bugu.

"I'm sorry biftu.....really sorry,for making you feel like i disappeared....i don't like how quite i left your day.......kiyimin afuwa" Shuru ya ratsa sai fitar numfashinsa kafin ya sake cewa.

"......na karbi abu mafi girma da daraja da kowacce 'ya mace ke taqama da tutiya dashi......ya kamata na zama a kusa dake for the whole day....i'm so sorry my princess......" Ya qarashe da qyar saboda yadda numfashinsa yake nauyi a qirjinsa.

"......next time i leave,you will know where i am and when I'll be back".

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Shuru kawai tayi accent dinsa na kasheta.....shuru ta masa tana sauke numfashinta a hankali......shuru tayi tana jin yadda bugun zuciyarsa ke sauka a gadon bayanta.....shuru tayi tana jin yadda ya zura hannuwansa ta qasan rigarta ya soma yawo dasu a sassan jikinta.

"I.......i......i know you didn’t mean it" Ta maida masa da French kaman yadda yayi mata muryarta tana rawa.

"Thanks" Ya furta can qasan maqoshinsa.

A hankali bugun numfashinsu ya sauya shi da ita gaba daya......a hankali wani abu ya soma yawo cikin jininta dama sassan jikinta,wani abu me nauyi da wani irin qarfi dake ratsa zuciyarta da kowanne sashe na jikinta. Saidai duk da haka.....duk da haka jiya bata fita a kanta ba.....wannan azabar......wannan wahalar.....wannan tsoron yana kwance cikin rai da zuciyarta. Bata manta ba......bata manta komai ba.....bata manta kowanne wucewar daqiqa minti da second ba.....bata manta yadda ya cillata wata nahiya me cike da azaba da radadi ba,don haka a yanzu jikinta yana kakkarwa ta sanya hannu ta damqe hannunsa da taji ya fara tafiya zuwa qirjinta kai tsaye da wani irin zafin nama da jikinsa yake gwada mata.

"Babyyy" Ya furta a karon farko a hargitse.

"Ba abinda zan miki.....just want to feel them......nayi missing......mayi missing nasu,bazan iya bacci bane ni kadai......don Allah......karki hanani,zan miki kuka" Yadda muryarsa ta narke.....yadda muryarsa ke rawa sai taji kaman kukan yake shirin sakar mata,abinda ya sake gigitata kenan. Tsoro takeji,sosai takejin tsoro biyu yana hade mata.

".....idan nanay ta shigo fa?" Ta fada itama tata muryar tana rawa.

"Babe......Ki daina saka ni jin kamar zan ji tsoron mamana a gaban matata......" Ya fada yana qanqameta cikin jikinsa,bai kuma bata second chance da zatayi tunanin komai ba ya birkitota suka koma fuskantar juna.

Yatsansa ya dora daga saman goshinta yana saukowa dashi zuwa karan hancinta,sannan ya wuce saman labbanta dake daukan hankalinsa,fuskarta ya kama ya saka tasa sosai a ciki,sannan ya zame fuskar tasa zuwa kan kafadarta,ya lalubi kunnenta,cikin wani narkakken yanayi ya rada mata.

"Let me have this moment with my wife in peace.....no nanay tonight......only khadeeja and muhammad" Ya qarasa fada yana sake bata muhalli me kyau cikin faffadan qirjinsa.

Numfashinsu.....shauqinsu......dama zuciyoyinsu gaba daya sukayi wani irin cakudewa guri daya cikin daren. Wani irin hot romance......zafafan saqonni daya birkita mata kwanya dasu......wani irin yanayi daya sanyata ta yarda cikakkiyar maqaryaciya ce ita data dauka zata iya bacci me dadi da ma'ana alhalin baya gefanta......alhalin baya tare da ita.

Ya tarawa zucuyarta da gangar jikinta gaba daya gajiya. Ya aike da ita can wata qololuwar duniya da zata iya fadi kai tsaye a yau karon farko takai can din a yanayin da take cikin hankalinta. Saidai ya kauda mata kowanne tsoro ta hanyar cika mata alqawari. Yayi controlling din kansa,yayi namijin qoqarin dakatawa baikai har can headquarter din ba,ya jata a jikinsa cikin taushi da nutsuwa,wanda sai saukar numfashinsa taji a hankali kansa na kwace cikin qirjinta,yayi pillow dash yadda yakeso.

Wannan tsoron ta dauka zai haneta sakewa......sai gashi ta manta da komai,wani daddadan bacci ya sureta yayi awon gaba da ita.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 89* __________________________ https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0

*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*

*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*

*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*

*_Assalamu alaikum my loyal people_*

*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*

*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*

*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*

*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*

*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*

*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*

*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*

*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*

*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee* _______________________

*A S U B A H*

Sanye da fararen kayan sallah take takowa zuwa dakin a nutse don tayar da akhnan salla,kaman yadda ya zame mata al'ada tayar da kowa tsakanin Aareef rumaisa Aanani noorah da saamee.

A nutse ta murda qofar dakin ta kuma turata a hankali tana shiga,saidai abu na farko data fara ji shine,wannan scent din da mutum daya ta sani ya mallakeshi.

Ta bude hancinta a hankali tana sake shaqar qamshin don ta tabbatar. Shi dinne dai,ta miqa hannu tana kunna qwan dakin bakinta dauke da sallama gami da kiran sunan akhnan din da GIIFTII.

Ba kowa saman gadon,tabi shimfidar gadon da kallo a hankali. Komai a yamutse yake,wasu pillows din sun fado qasa sun zube daga gefe. Idanunta ta dauke a hankali,wannan gadon bai kama da mutum daya bane kawai ya kwanta,yanayinsa kamar anyi dambe ko yara ne sukayi bacci akai suka tashi.

Idanunta ta maida qofar bandaki sanda take budewa. Akhnan ce,sanye da doguwar riga cotton me laushi sosai data saukar mata har qasa. Ta sani,bada rigar ta kwanta bacci ba,kaman yadda gashinta ke a hargitse ba kaman yadda ta ganshi dazu data shigo ta kashe mata wuta ba.

Qasa akhnan tayi da idanunta,haka kawai tana jin wani faduwar gaba dakunya suna saukar mata. Gani take kaman nanay tana ganin komai,yadda ya kwana tsakanin qirjinta,yadda ta farka fuskarya saman lallausan gashin kansa,yadda ta sake bude idanu ta tarara yana tsaye yana qare mata kallo,sumarsa na digar da ruwan da take da tabbacin wankan ibada yayi. Ya yarfa mata ragowar ruwan hannun nasa a tausashe yana sakin lallausan murmushi.

Ta bashi wani abu da ake kira da suna NUTSUWA wato peace inji bature. A yau yasan yayi wani irin bacci daya amsa sunansa,kalar baccin da bai taba irinsa ba kaf rayuwarsa.

"Gate up......ko kina so nanay tazo ta sameki a haka?" Duvet din data boye fuskarta ta janye kadan,tanason dubansa amma ta kasa,ta ganta a haka kaman yaya?.

Daga ido tayi karo na biyu,caraf ya riqe idanun cikin nasa,ya mata nuni kuma da jikinta,takai hannunta a hankali tana tabawa. Ya rabata da komai sai a sannan ta tuna,ta cure guri daya tana duba lokaci,shirye shiryen sallar asuba akeyi.

"Ruwan wanka yana ciki yana jiranki".

" Ni bazanyi wanka ba" Ta fada tana tura baki kunya kaman ta kasheta. Karon farko ra yuwarta da taji sautin siririyar dariyarsa,ya tako a nutse yana isowa dab da kanta ya sunkuya kadan.

"Ba zaki wanka ba.....amma awannin dazu kike fadin....." Sai ya sassauta muryarsa yana maimaita mata maganganun da ko daya a ciki ba wanda tasan tayi.

"Wayyo Allah na bappi.....zai lalatamin kunnuwa na" Ta fada da siririyar muryar nan tata dake kasheshi,musamman duk sanda tayi magana da sautin shagwaba.

Baya yaja a hankali sautin siririyar dariyarsa yana fita,wani abu daya zowa akhnan da wani sabon yanayi.

"Ba sharri na miki ba,pillows din dake nan da suna magana zasu fada"

"Nidai ka fita" Ta fada hawaye na tarar mata a idanu. Ya akayi ta bari ya yaudareta har haka yaji wadannan kalaman a bakinta?. Banda tasan baya qarya zata iya tsinewa kanta ita ba ita ta fada ba.

Yana sakin qasaitaccen murmushin nan nasa dake gaya mata,ba abinda ta furta kawai ba......tuna komai daya shude cikin awannin dadi yake masa,ya koma private musallah din,ya shimfida tattausar daddauma ya tayar da salla abinsa hankali kwance,kaman baya duban lokaci,kaman baya tsoron wani ya shigo ya ganshi.

Tayar da sallarsa ya bata cikakken daman wucewa bathroom din kai tsaye a gurguje,ta samu ya hada mata komai,hatta da towel da zatayi amfani dashi,kaman yadda birra ke mata. Sanda ta fito taga dakin wayam,batasan sanda ya fita ba,sai ta sauya kayanta kawai wanda tana kammalawa ta koma bandakin don daura alwala,fitowarta ne a yanzun sukayi kacibus da nanay.

Idanunta kawai ta janye nanay din,jikinta yana bata akwai wani abu da yake ba daidai ba,saidai bata nunawa akhnan din komai ba tace

"Alhamdulillah,kin tashi kenan".

"Eh na tashi" Ta amsawa nanay wadda har takai bakin qofa a sannan.

"Zenebe zata shigo zata ganki" Abinda tace kawai kenan tana fita daga dakin.

Kawai juya abun take cikin ranta,tana tafe tana amsa gaisuwar hadimai da ma'aikatanta cikin girmamawa kaman yadda ta saba. Can qasan ranta take maido da yanayin dakin da qamshin haisam da taji,kadafa su bata kunya.....karfa ya sake maimaita wani abun kamar yadda motii ke fada mata.

"Bayan na kwanta,akwai wanda aka sake budewa sassan nan ne?" Ta tambayi saamiyaa wadda keda alhakin kula da shige da fice na cikin dare.

Qasa kadan tayi da kanta,tana jin nauyin fade,duk da ya wuce abinsa ne kai tsaye bayan ya tambayeta nanay din ta kwanta?,ba tare da yace mata komai ba.

"Saamiya" Ta kira sunanta tana juya daffaffiyar madarar hannunta.

"Eh......yarima haisam ne ranki ya dade" Shuru nanay tayi,ta gyada kai a hankali,kawai sai taji dariya nason qwace mata.

Karo na farko......karo na farko kenan data taba shata iyaka da layi akan abu amma haisam ya tsallake. Ta yarda da maganan motii,ta kuma yarda duk wanda ya rigaka kwana zai rigaka tashi. Namiji baida amana akan mace da gaske ne,kota yaya ne zai samawa kansa ita. Ta sake gyada kai tana godewa Allah da tunda asuba aka gaya mata isowar saqon,kuma duka a yau zata iya yiwa akhnan amfani dasu,iyaka dai kawai ta barta subi jikinta na kwana uku kawai shikenan ta miqa masa matarsa.

Yinin ranar ta sani za'a iya samun yaiwatar zirga zirga da jama'a. Saboda walimar da hussam ya shirya zaiyiwa haisam din. Nanay din tana jinsa yanata mita.

"Karma kaje kayi abinda ba zai burgeshi ba.....shigar jubah zamuyi,kowa ya saka thobe kawai" Ya fada yana ya mutsa fuska,tana jinsa ya bada kalan shigan da za'a yi na jallabiyya,color kowa ya zabi favourite colour nasa.

Breakfast kawai akhnan din tayi,zenebe da wata mata da ba zata iya tantance qabilarta ba,sukazo suka dauketa saboda gyaran jiki na qarshe da zasuyi mata,suka zagaya da ita baya inda nanay tasa aka kebance wani guri na musamman don suyi komai acan.

*H A I S A M*

Ya kammala shirinsa gaba daya na tafiya a yau din,wuni guda yana kai kawo bai zauna ba na hada sauran takardu da komai da zaya buqata,saidai ko sau daya bata bar tunaninsa ya huta ba.

Baisan me yasa baya samun wayarta ba,saidai abinda bai sani ba nanay ta karba ta kashe. Can qasan ranta tanaso yayi missing akhnan dinne,tanaso yaji ya matsu da ita da gasken gaske,sannan kuma tana tsoron abinda ta gani a idanun akhnan din. Rauni da wata irin QAUNA data fara hange ta bata tsoro,kada ya hure mata kunne ya bata shirinsu na kwanakin data tsara.

Zuwa yammaci aka soma gudanar da walimar. Cikin wani irin ba zata da bai zata ba saiga team dinsa dukkaninsu. Naseeb.....mutallab.....amjad......khadeem sai omar. Maleek kam yana can ya maqale,yace har yanzu honeymoon yakeci.

Yayi mamakin ganinsu,saboda dukkaninsu zasuje bikin bude company a dubai nan da kwana biyar din daya rage,saidai kuma mamakinsa baiyi yawa can ba,don dukkaninsu suna dasawa da hussam. Baisan me yasa sukeyin hussam din ba,ko don zubin vibes dinsu yana zuwa daya dasu wani lokaci,saidai dukkaninsu a ranar kowa zai koma bakin aikinsa,tunda tafiya ce ta jirgi.

Daga cikin gidan ma still wani walimar ne da Aanani da rumaisa suka shirya,harda noorah. Ita kanta nanay batasan sun shirya kayarsu ba. Daya daga cikin dakunan taro na gidan suma sukasa aka shirya musu shi da sauran qawayensu,dukkaninsu kuma shiga ce sukayi ta gargajiya,ta aninihin tufafin yaren oromo da suturarsu da yake zuwa kaloli biyu (Zan saka a status dina na watsapp in sha Allah,kusan tafiyar namu gani da jine😄).

Ranar sai gidan ya zama hidima kawai akeyi,hakan ya yiwa nanay daidai,itama taga kawai gwara a kammala komai ta bashi matarsa kafin yakai ga fada mata gaba da gaba. Saidai nanay din batasan kalan tsiyan da yake qullawa ba.

Da yammacin dab da faduwar rana kayan da suke nuna girmamawar ango zuwa ga amaryarsa a qabilar oromo suka iso. Koda ba'a gayawa kowa ba zakasan kayan mene tunda an riga an saba. Ya sameta a cikakkiyar mace da takai budurcinta.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

(A kowanne yare.....a kowacce al'ada,a kowacce qasa.....a kowanne gari BUDURCI abune me muhimmanci....kada ki yarda.....karki kuskuren da zaki rasa baki a banza a wofi,ki tabbatar duk runtsi duk wuya duk gwagwarmaya kin kai naki dakin mijinki,mijin nan da yasan darajarki,yabi dukkan matakai ya biya sadakinki,wallahi ba wani abu.....ba wani gyara da za'a miki a rudeki ace budurcinki zai dawo,qarya ce wallahi wallahi tallahi,ko waye ya gaya miki ya yaudareki,hajiya kayan kamfani daban daban dana shago,ba wanda ya isa ya halicci wani abu da yayi daidai da wanda ubangiji ya halitta tun asali tun haihuwa,Allah ya bamu ikon kai zukatanmu nesa ameen summa ameen).

Jikinta yana tururi da wani sample na ruwan wanka da turare da aka bata a daren tayi wanka dasu bayan an tashi walimar ta fito daga bandakin,saidai qarar shigowar saqo wayar da yanzu yanzu aka kawo mata ita ya sanyata dakatawa daga tsane jikinta da tayi ta dauki wayar tana dubawa.

_"Wear something comfortable_ tomorrow morning _And don’t ask questions yet_

_Haisam_

Juya wayar ta dinga yi kawai ba tare data fahimci komai ba. Shigowar Aanani da murmushi tana ajiye mata sauran gifts din da suka kusan cike rabin dakin ya sanyata sauke wayar

"Na gaji giifii.....ko na sanya su obsa su qarasa shigo dasu da safe?". Idanu waje kadan akhnan ta fidda.

"Wai baki gama ba?"

"Da ragowa" Ta amsa mata tana daidaita zaman wani kwali.

"Ki huta sistern captain obbo.....sai goben" Dariya sosai Anaani tayi.

"Da zaijiki kuwa zaice....wannan me kunnen qashin?,noorah ce tawa" Da murmushi ta bita da kallo harta fice,sai taji inama itace su,gasu cikin rayuwar da suka tashi tsakanin qannensu da yayyensu. Akwai wani irin so qauna da respect da suke bawa junansu,musamman haisam din. Ta karanci wani irin so kowa cikin 'yan uwanshi yake masa,saita ture komai ta soma shafa mai tana jiran birra ta qaraso ta bata rigan bacci.

Tabi tarin kyaututtukan da kallo,qawayensu da abokan hussam ne kawai suka hada mata uban kaya haka. Mamaki takeyi na yadda suke da kyakkyawar mu'amala da mutane da yawa. Kaman girma da qarfin iko na masarautarsu bai daukesu ya d'ad'asu da qasa ba. Suna wani rayuwa simple,izzar ke magana da kanta basu ke qoqarin gwada ikonsu ko nunata ba.

Sanda dare ya fara nisa sai bacci ya gagareta. Daren jiya take tunawa,kowanne moment daya shude,kowanne second minti da awa da suka qarar ita dashi,sai ta kuma samun kanta da jin kamar motsinsa,kamar takunsa da tafiyarsa,ta runtse idanunta sannan ta sake budesu a hankali,bashi ba alamunsa. Duka baccin sai taji yana neman qaurace mata,ta samu kanta da tuhumarsa.....me yasa baizo kaman jiya ba?,sai kuma dariya ta subuce mata sanda zuciyarta kece mata.

"Kece bakiso....kin manta?,amma yanzun kike nemansa?" Murmushi ta saki tana cusa kanta cikin pillow din da har yanzu bar mata qamshinsa.

★Farar cotton din riga ce a jikinta me zuwa hade da hijab saqar qasar Malaysia,wadda aka yita musamman saboda gudanar da ibadar sallah.

Kallon wayarta ta sakeyi a karo na biyu da saqonsa ya shigo mata,tsoro da mamaki cakude akan fuskarta,tuni ne dai yake sake mata.

"Minti goma sun shude.....mintuna biyar suka rage idan baki fito ba.....zan shigo har ciki,zan kuma daukeki ko a gaban waye" A jikinta takejin zai iya,a jikinta takejin zai aikata,saita sauke wayar a hankali zuciyarta tana wani bugawa.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

Readers Also Read

More by Huguma