Kenza eBookz

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 52

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 52

L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 52: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 52. A hankali ta lura da wata kalar girmamawa daga dukkan…

3,352 words

A hankali ta lura da wata kalar girmamawa daga dukkan wanda yake gurin. Duk wanda haisam ya isa gabansa sai taga ya sunkuyar da kansa kadan kafin ya bawa haisam hannunsa suyi musabaha. Cikin ladabi dukkansu suke kiransa.

"Welcome back mr aba jifar" Sunan daya tsayawa akhnan sosai a ranta. Ba wai don yau ta fara jinsa ba.....aah,sai don yadda take ganin dacewar sunan dame shi.

"Thank you" Yake amsa musu dashi,saidai saman fuskarsa akwai murmushin daya rage miskilancin saman fuskarsa.

Kaman yasan ta shiga wani tunani na daban,ya matsa yatsunta a hankali kamar yana tuna mata cewa yana tare da ita ne.

"Don't look so startled.....they're only being polite" Ya fada calmly.

"Only being polite?" Ta maimaita kalmar a cikin kanta. Wasa yakeso ya mata da hankali kenan kamar yadda ya saba?. Ta sake maimaita kalmar.....alhali mutanen suna kallonsa da irin girmamawar da akewa sarakuna. Yarima ne shi ta sani....ba wani sauran abinda zai boye mata.....sai sauran abinda bata sani ba.

Wani daga cikin mutanen ne ya matso,hannunsa dauke da tablet

"The palace district has been informed of your arrival sir" Kadan taji numfashinta ya tsaya

"Palace district?" Ta sake maimaitawa qasan zuciyarta.

"And everything has been prepared..." Ya qarasa maganan yana miqa masa tablet din.

"Good" Haisam yace kawai yana riqe tablet din cikin hannunsa,mutumin ya gyada kai kamar wanda aka bawa lambar yabo yana matsawa a gurin.

Sake riqeta yayi a hankali tana daga bayanshi suna takawa. Idanunta na cikin airport din zuwa motocin da suke dosa,amma kunnuwanta suna jiye mata sautin haisam. Sautinsa ne.....saidai a yau din da wani yare da wani harshe da bata taba ji yayi magana dashi ba. Harshen larabci....mafificin harshen da a duniya shine yare na daya da take matuqar son taga ta iya.

Yana mata wani irin dadi.......tana jin wata nutsuwa a duk sanda ake yaren,koda kuwa bata fahimtar komai a cikinsa.

Duk da tarin mutanen dake neman yabawarsu wajen girmamashi......amma hakan bai hanashi barinsu ba,ya matsa a nutse ya bude mata qofar Royce rolls din yana duban idanunta da girmamawa.

Takawa tayi a nutse zuwa cikin motar,saidai idanunta a kansa. Kowacce rana sake bata mamaki yake,kowacce rana bayyana mata kanshi yakeyi ba tare da yayi magana da bakinsa ba.

Dangerous calm smile dinsa ya sakar mata,sannan ya zagaya a nutse daya daga cikin guards dinsa suna bude masa tasa qofar.

"Wane irin mutum ne wannan?,And how much of him have I yet to discover?" Ta yiwa kanta tambayar sanda convoy din motocin ke motsawa a hankali suna barin harabar airport din.

Bata sake sanin cewa ta shiga duniyar mutumin da take tunanin kawai ta sanshi bane.....bata sake sanin a yanzun bane zata fara sanin.....zata kuma fara ganinsa da gaske ba sai sanda suka isa harabar hotel din.

"Ya salam ya Allah" Ta fada can qasan maqoshinta lokacin da motocinsu ke qoqarin sanya kansu farfajiyar hotel din.

*_Turqashi!!!.....haisam ne akhnan......akwai saura.....baki gama shan mamakinsa.....ki adana mamakin nan kada ya qare.....ba akhnan ba.....ko ni da naga hotel din an gama tashin kaina 🧐🧐,mu hade gobe in sha Allah with scene view na hotel din in sha Allah kaman yadda muka saba_*

*_INA FATA BAKU MANTA BA....WANNAN WEEK DIN NA DABANNE NACE KO IN SHA ALLAH_*

*HUGUMANKU CE*🙌🏽🙌🏽🙌🏽

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 92* __________________________ https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0

*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*

*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*

*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*

*_Assalamu alaikum my loyal people_*

*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*

*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*

*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*

*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*

*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*

*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*

*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*

*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*

*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee* _________________________

*_ATLANTISTHEROYAL_*

.......Hotel mafi tsada a dukka hotels na duniya. Hotel din da bata taba kawowa a kanta zata shigeshi ba. Dream hotel dinta.....ba ita kadai ba,hatta da aisa shehnaz dama duk wanda ta sani suna tafiye tafiyen yawon bude idanu.

Yanzun kam kai tsaye take kallon haisam. Tana ganin ta gama saninsa,tunda tasan cewa shi din yarima ne,dan sarkin jimma. Tana tunanin ta gama saninsa tunda tasan family dinsa......amma saidai a yanzun ta fara qaryata wannan.

Bai kula da kallon da take masa bane.....ko basarwar daya saba ne cikin jininsa oho,bai waiwaya ba har zuwa sanda motar ta gsayata qawatacce kuma tsararren gurin adana motoci,ya sanya hannunsa ya bude side dinsa. Ta glass din tana iya kallon yadda yake sallama da mutananen da suka masa rakiya. Da wannan yanayin da zai gaya maka tabbas an haifeshi ne a cikin IKO.....ba kuma shike neman ikon da girma ba,sune suke bibiyarsa.

Takunsa a nutse.....wannan royal walking din ya qaraso gaban motar,ya sanya hannu ya bude mata hana dubanta a tausashe.

"Bismillah.....my princess" Idanunta ta lumshe a kansu,sannan ta budesu lokaci daya.

"Bazan iya saukowa ba......alhalin har yanzu ban gama sanin waye kai ba" Idanu ya zaro gaba daya mamaki yana bayyana saman fuskarsa,kafin kuma a hankali ya maye gurbin mamakin da murmushi.

Matsowa yayi gaba kadan zai riqe hannunta amma ta janye

"Is okay....." Ya fadi shima yana maida hannunsa ya hade tafukan hannayen nasa yana murzasu guri daya.

"Kiyi haquri....."

"Nayi.....kuma zanyi,bazan matsa maka ka gayamin komai ba,har sai sanda ka shirya......amma zuwa yanzu.....duk abinda na gani na tambayeka lallai zaka bani amsarsa.....wannan shine sharadin shigata ciki" Ta fada tana dan bin ginin hotel din da kallo.

Shuru ya danyi,kamar yana nazarin wani abu,sai kuma a hankali ya gyada kansa yana lanqwasar da kansa cikin yanayi na girmamawa.

"Accepted your royal highness" Ya furta yana saka tafin hannunsa a qirjinsa.

Cikin jikinsa ya riqeta sosai,yana jin kamar zata bace masa ne. Idanunta a hankali suke qarewa hotel din kallo,zuwanta na farko kenan saidai gani a hoto da videos. Wasu irin palm trees masu haske da qyalli da suka qawata shi a jere gefe da gefensa. A zahirinsa yafi mata kyau,yafi kama da modern palace.

Qofar main entrance na hotel din,doormen din suka matsa cikin girmamawa,matsawar tasu ya bashi daman ganin wadanda ke tsaye suna jiransa.

Security da managers ne na hotel din,wani irin fountain light. Crystal reflection tako ina,ga wani irin fresh oud scents dake yawo a cikin iskar gurin.

"Welcome back sir" Managers din ke fada cikin girmamawa.

"Welcome back" Ta sake maimaitawa. Hakan na nufin ya saba.....ya riga ya saba da zama kenan a gurin?..

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Larabcinsa dasu yaci gaba da shiga kanta,ta sake lumshe idanunta tana jin tarin tambayoyi a kansa suna cika mata kwanya. Yanayin accent dinsa ya fita daban da nasu,ta kasa tantance a cikinsu waye yaren yafi zama da dadi akan harshensa?. Zata iya cewa SHI duk da hakan zai zama kamar wani son kai ne tayi,saidai kam zata zabeshi ta sake zabinsa saboda. Husky voice dinsa da take zama very calm da wani irin soft tone yadda take fita yasha banban da nasu,ta saba jin hakan,muryarsa daban....da wani irin banbanci da muryar kowanne d'a namiji a duniya.

"Your penthouse was ready" Muryar daya daga cikin staff din ta fada. Godiya ya masa kaman yadda ta lura dabi'arsa ce ga duk wanda ya masa hidima,sannan kowa ya qyaleshi da ma'aikatan hotel din biyu da security din data kasa ganewa nasa ne tun asali ko a nan yayi hiring nasu?.

Penthouse kawai ke yawo cikin kanta,idanunta kuma suna son gane mata zahirin abinda kunnuwanta sukaji mata.

Private elevator suka shiga,iya shi da ita kadai,sauran suka shiga wata don su tarar dasu a building din da zasu sauka.

Ya matsa ya bawa elevator din number building din,tayi tsaye a bayansa tana kallon yadda yake tsaye. Cikin nutsuwa da kamewa,da wani kalan hali da dabi'ar da bazaka taba zaton ya taka irin wannan matsayin ba a rayuwarsa.

*_Mr aba jifar hallway_*

Abinda ta gani kenan a rubuce jikin wani arrow na silver bayan fitarsu daga elevator din. Mamaki yana sake kasheta,private floor?,dama akwai private floor a hotel?. Residence guda take gani a rubuce,bawai suit da suka saba sauka ba?.

"Mallakinsa ne kenan wannan ginin?" Tambayar da taji ta mata girma akai.

A hotel irin wannan.....wanda kwana daya tal a cikinsa girma ne.....nasara ce......daraja ce da alfarma,amma a ciki har ace wani dan adam ya mallaki sashe guda nasa na qashin kansa..

"Who is muhammad haisam aba jifar?" Tabbas akwai wani.mutum still a boye a bayan wannan sunan.....a bayan wannan fuskar.....a bayan duka abinda ta sani. Ba basarake kawai malami ba.....tana hangen zai iya zama wani billionaire ne?...... Tambayar tayi tsawa cikin kanta ta kuma sake daga kai still tana kallonsa ta gefan fuskarsa.

Ta sake daga idanunta,a entrance na private hallway din akwai engraved silver plate dake dauke da sunan PRINCE HAISAM ABA JIFAR RESIDENCE.....ba room number bane kaman yadda aka saba a dakunan hotel.

"Residence?" Ta tambaya tana duban fuskarsa sanda yake scanning key card dinsa. Yanaso yayi kaman baiji ba,amma sai.ya tuna,alqawari ya mata,duk da bai da tabbacin zai amsa kowacce tambaya tata.

Yanaso LOKACI yayi.....LOKACI yake jira da zata gama sanin koshi waye.....zata san dukka tambayoyin dake kansa a zuciyarta,amma ya sani.....a abinda yake gani a idanunta tattare dashi,ba lallai ta iya kaiwa wannan lokacin haka ba.

ZUCIYARTA yake fafutukar mallaka a yanzu.....dole ya cire duk wani burbushin rashin yarda da sake sakewa tsakaninsu.

"Eh....residence.....It stays closed unless I’m in Dubai.” ya fada softly yana miqa mata hannunsa. Taku biyu ta qaraso,ta miqa masa nata hannun ya jata a hankali zuwa ciki.

Zata iya kiran ginin da cikakken gida madaidaici wanda ha hada komai da komai. Madaidaicin gidan da idan kana ciki ba zaka dauka rayuwa kake cikin hotel ba.

Private infinity pool,personal butler team,private dining area,ga panoramic dubai skyline view daya tafi da ita tun a kallo daya wata duniya ta daban.

Ta gama sarewa.....ta gama sallamawa......a take kuma ta gayawa kanta

"DA GASKE BAKISAN WAYESHI BA AKHNAN.....WUTSIYAR RAQUMI TAYI NESA DA QASA".

Ta sake daga idanunta,komai na gurin yana gaya mata tabbas gurin mallakinsa ne. Kowacce iska da qamshin turarensa data sani take kadawa. Favourite coffee brand dinsa yana gurin,dakin ajiyar suturun da tana kalla tasan tabbas nasa ne....ga gurin sallarsa.....yana shirye da tsarinsa kamar wanda suka baro a gida,kaman yadda tsarin nasa na gida yake.

"Ya Allah" Ta fadi jikinta yana wata irin mutuwa,saita koma gefe ta zauna a hankali tana jiyo motsin ruwasa daga toilet.

Wannan sama da abinda tayi buri ne.....wannan sama da abinda ta roqa ne.....bama wannan ba kwata kwata. Batayi burin me dukiya ba......saboda tana ganin ta gada. Batayi burin me tarin dukiya irin wannan ba. Wayayye ta nema.....shi ta dinga lalube wanda zai tayata ta qara gina kanta. Wanda zai bata dukkan 'yanci. Amma a yanzun wani mutum a daban take gani,wani LU'U LU'U take hange wanda ya shiga cikin farin qarfe na azurfa yake rayuwarsa.

"Anya bankai kaina inda akafi qarfina ba?" Ta tambayi kanta tana jin kamar tana narkewa tana zama qasqantacciya.

Inde a abinda take gani ne ya tabbata...lallai babu ko shakka MUHAMMAD HAISAM yafi qarfinta ita AKHNAN MUHAMMAD HAMMUD fin qarfi na har abada. Anya kowa da kowa ma ya gama sanin wayeshi?,ko!yana binne kowa ne kaman yadda yaketa binneta?.

"Are you okay?" Taji ya fada a hankali. Idanunta ta daga tana sake kallonsa,ya cire thobe dinsa ta sama,amma farar jallabiyyarsa na sake nuna kwarjininsa da haibarsa.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 93* __________________________ *_Amintaccen gurin siyayya_*

*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*

*_BONONZA DA PROMO akai akai_*

*dukka sai a HUGUMA CLOSET*

*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*

*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*

*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*

*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX __________________________

Duk wani abu da takeji ko take qissimawa zata masa.....ko zata aikata da zarar ta kalli wadannan narkakkun idanun nasa saita kasa. Da zarar ta kalli qwayar idanunsa sai taji komai yana kwance mata. Batasan wanne irin baiwa ce dashi haka ba......batasan har yanzu a wanne aji zata sakashi ba.

Abu daya ta sani,kowacce rana yana kan yiwa zuciyarta mummunae b'arna. Kowacce rana yana sake lalata tunaninta,yana sake sanya mata buri da kuma son kasancewa dashi.

Hannun rigarsa da yake warwarewa ya saki yana takowa a hankali,ya iso gabanta,sannan ya tsugunna kamar wanda yake neman gafara. Kyawawan idanun nan nasa cikin blue eyes dinta,tafin hannunsa ya dora a nutse saman cinyarta,dumin hannunsa ya ratsa fatarta,ya kuma isa ga qasusuwanta ya ratsa jini da jijiya.

"My healer?" Ya fadi yana karkatar da kansa gefe kaman wanda yakeson sake ganin fuskarta da kyau sama da yadda yake kalla yanzu. Da wannan salon na iya sarrafa harshe,cikin harshen French ya soma magana da ita da accent dinsa ke kai mata ko ina cikin jikinta.

"Na sani,....na saka shakku da yawa a kaina cikin zuciyarki....amma ina me tabbatar miki ban boye komai wallahi don na cutar dake ba. Bansan ta yaya zan fahimtar dake komai ba.....bansan ta yaya zan miki bayani duka a dunqule lokaci daya ba,amma ina roqonki....." Sai ya dakata kadan,kamar yadda ta fahimci rarrabe magana a dabi'arsa yake,kuma duka yana cikin abubuwan dake sanyawa kaji idan ya maka magana,maganar tashi takai maka ko ina.

"......ina neman alfarma......ki barwa lokaci ya miki bayanin waye ni. Abu daya zan iya gaya miki da kaina,ni muhammad ba macuci bane....ba kuma mugu bane......." Ya sake dakatawa yana kallonta

"......zaki wannan alfarmar?,ni kuma zan amsa miki duk abinda kika tambayeni da haqiqanin gaskiyata" Ya qarasa fada muryarsa can qasan maqoshinsa.

"La haula wala quwwata illa billa" Ta fada a hankali tana lumshe idanunta. Ita daya tasan yadda yake nasarar rugurguza zuciyarta. Ita daya tasan yadda maganansa ke samun nasarar narka mata zuciya. Ita daya tasan tasirin da komai nasa yake mata. Maganarsa.....kallonsa....kai daidai da wanzuwarsa kadai a guri yana ruguza mata dukkan lissafi.

"Kinyimin?" Ya sake fada a hankali yana dora kuncinsa saman cinyarta yana leqen fuskarta. Kai ta daga masa a hankali yana kaucewa kallon fuskarsa,don da qyar take hadiye yawu saboda yadda gaba daya kwarjininsa ya cika mata guri.

"Na gode" Ya fada a tausashe yana miqewa,ya dora lips dinsa saman goshinta yayi kissing sannan ya janye baya a hankali. Agogonsa ya kalla kadan sannan ya sake maida dubansa kanta.

"Xakimin haquri na kwanaki uku zuwa sanda zanje gayyatar da akamin.....zan zama busy na kwanakin kadan.......Allah yasa hakan bazai bata miki rai ba" Kai ta kada a hankali,tunaninta ma Allah yasa shehnaz su iso da wuri,idan sun iso ma bata da matsala da yawa,suna da gurin zuwa sosai da zai debe mata kewa na kwanakin.

"Na gode" Ya sake maimaitawa,daidai sanda na'ura ke shaida masa ga saqo daga kitchen.

Bai jima da fita ba ya dawo,idanunsa a kanta.

"An kawo abinci da komai da zaki iya buqata......" Kai ta girgiza a hankali.

"Ba yanzu ba" Ta fada tana motsa labbanta a nutse. Idanunsa ya janye daga kanta ya fara cire cufflinks dinsa. Wani abu daya daya lura da ita,ba kowanne abinci takeci ba,ba kuma a kowanne lokaci ba. In fact ma gaba daya abinci kamar bai dameta ba.

Idanunta ta lumshe a hankali sanda yake zare jubah din jikinsa. Zuciyarta na bugawa d'il d'il d'il cikin qirjinta.

Wannan ginannen jikin nasa.....wada yake zagaye da muscles da aka ginu saboda daga qarfe shi ya bayyana. Qafafuwa hannaye dama qirjinsa gaba daya cike yake da gargasa dake da duhu da santsi.

"Zanyi wanka" Ya fada softly yana dubanta hannayensa harde cikin faffadan qirjinsa.

"A.....afito lafiya" Ta fada sautinta yana rarrabewa. Sanda ya bude daki daya cikin residence din bata kawo komai a ranta ba. Bata tuna zasuyi cudayya a komai ba...zasuyi tarayya a komai ba......kuma zasuyi mu'amala da komai a tare ba sai a yanzu. Sai a yanzu daya yaye mata wannan gangar jikin nasa dake matuqar mata kwarjini,wannan gangar jikin nasa da ba zaka dauka haka yake da cika idanu da ban tsoro ba idan bai budesu haka ba.

"Care to keep me company in the bath?" Ya fada a nutse da french. Ba shiri ta bude blue eyes dinta tana waresu a kansa,saidai kuma a rude ta maidasu ta kulle tana kauda kanta.

"Aah......" Ta fadi tana qarawa da girgiza kai. Dariya tazo masa a nutse,ya fiddata a boye. Da gaske yarinyace,komai nata sabo ne. Sai yayi raino da gaske.....sai ya mata wani karatu da yakeso daga macen aurensa.

Rayuwar aure yakeso abar kwatance.....irin rayuwar da soyayya ba zata mutu ko tayi bacci ba. Rayuwar aure yakeso me kama da ALJANNAR DUNIYA ba rayuwar kidahumanci ba. Rayuwar aure yakeso da litattafan soyayya zasu gaza wajen rubutata daidai.....ba kalan rayuwar akeyi a kowanne gida ba.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Juyata da dorata akan wannan bigiren bazai masa wahala ba......amma dole yabi a nutse kuma a hankali. Ya taho da ita nan ne saboda ya daidaita zuciyarta daidai da yadda yakeso ta kasance. Ya daukota nan don ya bata hutu,ta huta sosai,irin hutun daya tabbatar ba lallai ta samu a gurin nanay ba. Ya daukota nan saboda su samu shaquwa da kusancin da ko lokaci bai isa ya shiga tsakaninsu ba. Ya yiwa kansa alqawarin bazai taba koda yatsarta da sunan neman wani abu daga gareta har sai da yardarta,amma hakan bazai hanashi yada manufarsa da sake dasa kansa a zuciyarta ba.

"Is okay" Ya fada yana daga kafadunsa. Kai tsaye ya wuce bathroom din,wanda yake da wata irin qawatacciyar qofa da kuma toilet daban a ciki.

Numfashinta da take riqe dashi ta saka a hankali tana juya idanunta. Bugawar da zuciyarta keyi take saurara. Dariya kadan ta qwace mata. Ita kanta dariya ta bawa kanta,yadda ta rude dukka sai a yanzu komai yake dawo mata

"Kinga gymnastic guy ko?" Ta fadiwa kanta da kanta can qasan maqoshinta. Dariya kadan ta subuce mata,ta juya idanunta a hankali tana qarewa dakin kallo.

Wani irin tsari da yanayi da dakin ke dashi,kamar kafin a ginashi sun shiga zuciyarta sunga tsarinta da zabinta a kaloli da tsarin daki. Ta fidda iska me sanyi a bakinta,abubuwa da yawa suna mata yawo akai.

Duk inda wayewarta.....ilimi da yawan dukiyarta yakai,a yanzun tana jinta wata maqasqanciya kuma baqauyiya idan har tana tsaye a gabansa,idan har tana cikin duniyarsa......idan har tana cikin da'irarsa sai taji komai nata yana zagwanyewa.

Readers Also Read

More by Huguma