Kenza eBookz

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 53

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 53

L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 53: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 53. Wannan tunanin ta watsar,don ta tabbatar bata da riba a…

3,374 words

Wannan tunanin ta watsar,don ta tabbatar bata da riba a ciki sai sake dilmiya cikin qaunarsa,sannan ba abinda zai amfanar da ita face ta zama baqauyiya zam kamar yadda hotel din yake shirin maidata cikin qasa da minti arba'in kawai. Komai na musamman ne....komai na dabanne,komai kuma da nasa tsarin cikin hotel din. Especially mr aba jifar residence din. Karon farko kenan data gani da idanunta,bawai a labari ba. Residence guda cikin hotel din da yafi kowanne hotel tsada a duniya?.

"Wanne irin arxiqi ya mallaka?,me yasa baya qoqarin nunawa duniya kanshi?,me yasa silently power dinsa take magana?" Ta yiwa kanta dukka tambayar yana qoqarin lalubar number shehnaz ta kira kota WhatsApp,duk wadda ta samu.

Shuru dakin ya dauka,sai qarar zubar ruwa a hankali daga bathroom din.

"Akhnaaaannn" Kalmar ta fito da wani irin sauti tana sauka a kunnenta ta gauraya da shurun da dakin yayi. Haisam ne.....sautin ya fito can qasa amma ya mata wani irin tasiri a gangar jikinta.

Kanta ta daga a hankali tana duban qofar bathroom din. Bashi ya bayyana ba,muryarsa ce kawai.

"Hmmmm?" Ta fada a hankali.

"Can you bring me the towel?" Ya fada da tattausan French dinsa dake dake tsumata. A duk sanda zai magana dashi sai taji wani abu cikin zuciyarta da kanta ya motsa. Girarta tadan tsuke kadan,me ya hada da bashi towel indai ba neman tsokana ba?. Idanunta ya sauka cikin nasa sanda yadan leqo da idanun nasa,wataqila yanason yaga yanayinta ne.

"Mantawa kayi baka dauka ba?" Ta fadi a shagwabe,tana son dauke idanunta daga lallausan gashinsa dake digar ruwa,ya kuma kwanta sosai a gefan fuskarsa,hakan sai ya zama kamar wani ado na musamman ga kyawunsa.

"Apparently" Ya fada idanunsa suna lumshewa suna bude kansu kusan lokaci guda,akwai wani siririn abu cikin muryar tasa,kaman yana amsa mata ne da nishadi,irin nishadin da mutum keji a duk sanda zai tsokani wani.

"this French man....."

".......and his endless tricks" Ta fada can qasan maqoshinta tana kyabe fuska a shagwabe. Idanunsa ya sake lumshewa,ta masa kyau.....wani irin kyau da shagwabar tayi mata,yana jin kamar ya hadiyeta ya huta.....ko ya zauna ya lashe kayarsa tas.....saidai yanzun ba irin wanna kusancin yake nema ba. SABO yakeso.....sabon da zata nemeshi cikin kowanne motsi na rayuwarta. Kusanci zukata first kafin na gangar jiki.

Miqewa tayi a hankali ta dauki towel din dake ajiye hannun kujerar daya cire kayan nasa. Da alama ya daukoshi dinne ya manta,sai wannan ya bata nutsuwa kadan,ta kuma sakejin nutsuwa sanda ta isa bakin toilet din taga kanshi baya nan kamar dazun.

"Ga towel din" Ta fada tana dan daga murya kadan.

Hannunsa taga ya zuro,tabi fararen dogayen yatsunsa da kallo wadanda ke digar da ruwa. Miqa masa towel din tayi saitin hannunsa,sai ya matsar da hannun gefe.

"Gashi fa a ta nan" Ta fada tana sake cuna masa,saidai ya sake kaucewa gefe,kawai saita yanke shawarar kama hannun nasa ta saka cikin towel din.

Wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi,sanda ta kama hannun,sai yayi amfani da wannan damar ya damqe yatsunta cikin nasa,ya kuma hade da ita da towel din ya jawosu cikin softly gaba daya ya maida qofar ya b'ameta b'am da lock.

"Haisam!" Ta kira sunansa a rude tana ware blue eyes dinta a kanshi.

"Oh my god.....say it again?!" Ya furta yana cusa yatsunsa cikin jiqaqqen sumarsa yana maidata baya saboda hana mishi kallonta sosai da takeyi.

Idanunta ta janye da sauri tana duban qofar yadda ta rufe,gaba daya bathroom din ya cika da warm steam da qamshin turarensa. Bugawa zuciyarta kawai takeyi,ta kasa kallonsa.....ta kasa daga idanunta ta kalleshi,baida maraba da mutumin daba komai a jikinsa.

Da wani irin shauqi dake fusgarsa ya tsaya a gabanta idanunsa a kanta,sanye cikin relaxed black swim pant da gurare kadan ya lullube a jikinsa,gashinsa dukka a jiqe yake daga na jikinsa har na kansa,yana digar ruwa a hankali.

"You were leaving too quickly" Ya fada da wata kasalalliyar murya yana sake samun kusanci da ita,

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 94* _________________________ DEA’S MODEST ARTISTRY ✨ Aminataccen wajen samun ✔️ Abaya masu kyau ✔️ Lifaya & Veils masu tsari ✔️ Handmade paint work ✔️ Shadda designs ✔️ Elegant modest wears ✔️ Accessories masu kyau da inganci Muna kawo muku kaya masu kyau, tsafta da araha domin kowane irin event 💫 Ko na daily wear, outing, wedding ko special occasions — DEA’S MODEST ARTISTRY na tare da ke 🖤 📍Quality first 📍Affordable prices 📍Neat finishing 📍Classy & Modest styles Ki kasance cikin kyau da nutsuwa ba tare da tsada ba ✨

https://chat.whatsapp.com/IZGMwJXP8Oa5qUc4sDSKZv?s=cl&p=a&mlu=3 __________________________

Hararsa tayi wannan karon,hararar data dauki hankalinsa matuqa. Bai taba sanin harara na yiwa idanu kyau ba.....mugun kyau me fusgar hankali ba sai yanzu.

"Ka yimin wayo ne kawai....dama ka shirya hakan" Ta qarasa maganan a shagwabe tana narke masa.

Dan tattausan murmushi ya saki yana duban wadannan unique blue eyes din nata.

"Yes" Ya furta kansa tsaye

"And I’d probably do it again.”

Kanta ta girgiza,saita rabashi tana niyyar wucewa zuwa bakin qofar fita. Softly ya tare hanyar,bada qarfi ko nuna iko ba,sai wani irin teasing closeness yana lalubar qwayar idanunta

"One minute mana" Ya furta yana karyar da kanshi.

"Haisam" Ta sake fadi cikin subutar baki ganin ya fara narke mata irin yadda ya saba. Wannan narkewar da take tuna mata amanar nanay ce shi a hannunta.....wannan narkewar da take sanyata jin kamar ta gaza kula dashi yadda nanay tace tayi.

Sunkuyawa yayi kanta kadan,ya lalubi kunnenta,sannan a hankali kamar me rad'a yace.

"You called me a gymnastic guy earlier" Dam zuciyarta ta buga,ta zaro dukka idanuwanta waje,wata irin kunya tana qoqarin narkar da ita.

"Ban fada a gabanka ba!" Tayi furucin cikin mamakin yadda akayi yaji. Dariya taso qwace masa,a komai yarintarta ke bayyana. Maimakon ta qaryata ko tayi qoqarin kare kanta...amma sai ta bashi wani hint daya tabbatar masa ta fada din. Sautin dariyarsa kadan ya bayyana,still muryarsa cool yace.

"Your face did" Bata da sauran zabi,sai kawai ta saka tafukan hannunta ta rufe fuskarta cikin wani nauyi da kunya.

Da murmushi yake kallonta tana dada burgeshi,sai ya sanya hannunsa ya cire hannayen nata daga fuskarta gently

"Relax" Ya fadi a nutse.

"I just wanted a little more time with you". Ya fadi kaman yana bata daman zabi.

Wani irin shuru ya sake ratsa tsakaninsu,tana iya jin yadda zuciyarta ke zillo a qirjinta,kamar tana gaya mata cewa.

"Please.....stay with himmmm" . Shurun yaci gaba da wanzuwa,bai sakar mata hannuwa ba suna cikin nasa softly,hakanan steam din bathroom din yaci gaba da zagayasu yana ratsasu dukkaninsu.

Bayaso tace NO don haka ya mata riga malam masallaci,towel din ya miqa mata sannan yace.

"Before Nanay somehow appears in my imagination again and ruins the moment.” sai ya hade da hannunta ya dagata sama cak yana nufar bathtub da ita. Duk da a dan tsorace take amma magananshi na qarshe ya bawa akhnan dariya.

"Ka tsorata da mommy na ne?"

"I’m simply protecting my peace" Ya fada sanda dukkaninsu suka tsunduma cikin bathtub din ba tare daya damu da kayan dake jikinta ba.

Minti goma sha biyar ashirin talatin har arba'in kafin yakai zuciyarsa nesa su fito daga wankan. Bai mata komai ba......amma yayi warming up nata sosai,har bata iya hada idanu dashi. Yaja mata stool ta zauna,tana jin towel din da take daure dashi yayi qanqanta da yawa,sai mutsu mutsu take tana qoqarin rufe cinyoyinta. Inda Allah ya taimaketa towel din daya dora mata saman kanta don goge danshin gashinta dashi ta rufe kafadunta zuwa saman qirjinta,duk da bai rufu ba gaba daya amma yafi babu.

Ta dauka zai maza ya shirya ne,amma sai taga ya jawo daya stool din ya dasa a gabanta,ya kuma hau kai ya zauna da nasa towel din da iya gwiwarsa kawai ya tsaya.

Ya zuba mata wadannan shanyayyun idanun nasa da suka sake tsumuwa,cike fal da shauqin soyayyarta da sha'awar kasancewa da ita.

Kasa jurewa tayi,kashe mata jiki itama yakeyi,ga wani warm light da dakin yake bayarwa yana sauka a jikinsu softly. Ko blinking idanunsa bayayi sosai,kaman ya manta da komai dake cikin duniya. Ta motsa kadan tana tattara kalaman bakinta.

"Me kake kalla haka?." Shuru kaman bazai amsata ba,sai idanunsa still dake biye da ita da wata irin nutsuwa me nauyi.

"You"ya furta softly. Zuciyarta taji ta harba,saita dauke idanunta da sauri yanayin yana mata nauyi,ta kasa jurewa still,yana sake narkata tare da kaita wani gejin da bata zata zatakai akan kowanne dan adam ba

"Karkamin irin wannan kallon...." Tattausan murmushi ya subuce masa,ya sake rage tazarar dake tsakaninsu ta hanyar qara matsowa.

"Wanne irin kallo?" Ya tambaya kaman baisan komai akai ba. Kanta ta girgiza a tausashe.

"Kamar zaka karanta duk abinda ke raina" Ta furta masa tsoronta.....tsoron daya dade da karantarsa ta cikin qwayar idanunta.

"Maybe I'm trying to" Ya motsa lips dinnan nasa masu sulbi yana furta kowacce kalma a nutse kaman mai lissafa adadinsu. Da tsoronsa kadan da mamaki ta waiwayo,suka hada idanu,murmushin da bata shiryawa ba ya kufce mata a tausashe,abinda yasa ya qara jin kallonta kawai shine abinda yafi buqata a duk duniya a yanzu.

Hannunta ta daga tayi waving gaban fuskarsa.

"Haisaammm....."da murmushin kunya akan fuskarta.

".....blink manaaa" Ta qarasa fada tana jan kalmar qarshe din. Murmushi ya saki yana kama yatsunta.

"Ki qyaleni na kalli halal dina.....kinsan darare nawa na kashe ina kasa bacci saboda wannnan?" Ya fada yana nunata daga saman kanta har zuwa qafafunta.

"Ban taba kalla a wajen wata 'ya mace ba.....so please....let me....." Sai ya kasa qarasawa yana hadiye wani abu da taga wucewarsa ta adams apple dinsa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Idanunta take sake shirin daukewa,sai maganansa ya dakatar da ita.

"You look beautiful when you're trying not to look at me" Ya sake jefata cikin wata kunyar,kawai saita rufe fuskarta da hannunta data samu ta zame daga cikin nasa. Abinda yakeso ya fara samu,don haka ya sake matsawa dab da kunnuwanta,har fatar jikinsa tana gogar tata,cikin kwantaccen sautin nan.....da sound dinnan.....da muryar nan data zama sirri a tsakaninsu

"And that makes it difficult to stop staring.”

"Wayyo Allah momma na" Ta fadi tana jin wani abu yana narke mata,saita tafi kawai ta kifa fuskarta saman dressing table.

"The beginning" Ya fada can qasan zuciyarsa,wannan dangerous smile din yana fita daga kan fuskarsa,ya cije lips dinsa na qasa kadan,sannan ya miqe a nutse daga saman stool din,ba tare daya sake matsa mata ba ya wuce don shiryawa ya barta a gurin tana narkewa kaman ruwa.

Tunda ta shirya tana zaune ta kasa daga kanta ballantana ta kalleshi. Tana iya ganin gilmawarsa da motsinsa har ya kammala nasa shirin

"Na gama.....zan fita" Ya fada idanunsa a kanta,

Maganar tasa ta sakata daga kanta,saidai tayi nadamar kallon data masa.

Wani irin kyau me sunan kyau yayi. Ya narke da wani sassanyan kyau cikin shigar suit din da wannan shine karo na biyu data taba ganinsa da ita.

Wannan sumar.....wannan sajen da yafi zubi da tsarrariyar qasumbar da aka aske aka yiwa wani style din shape daga kuncinsa zuwa habarsa......wadannanmanyan fararen idanun gaba daya sun hadu sun haska cikin kalar suit din jikinsa.

"Ina zakaje?" Ta zaqulo tambayar da qyar saboda bataso ya fahimci wannan kallon qurillar da tayi masa a yanzun.

Hannunsa ya miqa mata,ta riga ta soma sabawa da irin wannan abun nasa,saita dora nata akai. Ya kuwa tasheta tsaye yana qare mata kallo,duk da ba wani kayan jan hankali ta sanya ba,amma yana jin kamar ya cinyeta ya huta.

"You look beautiful so ma sha Allah" Ya fada softly yana kissing forehead dinta.

Qugunta ya riqo yana janta cikin jikinsa.

"Muje ki rakani,ko.iya bakin reception ne......"

"Baka ban amsa ba" Ta fada tana jin wani irin nutsuwa da wani garkuwa da take samu a duk sanda dumin jikinsa ya ratsa nata.

"Zanyi concerning wasu papers wa me gidana ne" Ya fada yana hana idanunta haduwa da nasa.

Dubansa take da zara zaran eyelashes dinsa,ya saki murmushi kadan yana miqa yatsansa ya tabasu,saita dauke kanta gefe. Wani yanayi ne daya karanci tanaso tace masa bata yarda ba amma ta kasa fadin hakan.

"I won't be long......" Ya fadi yana sake mata murmushi sanda driver ya bude masa qofar Rolls Royce din data masifar daukar hankalinta.

"Try not to miss me too much" Maganan data sauka da nauyi da kima a cikin ranta,ta mata kuma rakiya sanda take komawa ciki da wani irin yanayi me tattare da shauqi.

"Too much" Ta maimaita a cikin kanta. Ya sani ma kenan..... Yana san dole tayi missing nasa?,abu daya kawai ya roqa.....kada tayi missing din nasa da yawa.

A hankali ta waiwaya,sai idanunta suka hange mata wasu motoci daban suna rufawa tasa baya. Kenan ya zabi ya nuna mata iya rolls Royce ne kawai?. Idan ta lura da kyau royal escort ne suke biye dashi.

"Wanne irin rayuwa yakeyi ne a bayan ido na?" Ta tambayi kanta tana ci gaba da wucewa ciki a hankali. Idan baya gabanta......sai taji tarin tambayoyi da takeson masa......amma da zarar ya wanzu a gabanta sai taji kanta yayi blank......sai taji ba wata tambaya data rage mata.

Residence din nasu yayi tsit sosai,sai ma'aikata dake sake gyaran gurin da take hanga d'aya d'aya,kaman sunzo ne don su dawwama cikin hotel din.

Ta bude qofar dakin a hankali tana cire takalmanta. Takalmin da tunda ta sanyashi a qafarta take sake qare masa kallo saboda sanin ainihin kudinsa.

Idanunta ta maida cikin dakin,komai na dakin yana dauke da wanzuwarsa. Turarensa.....agogonsa daya bari....cufflinks dinsa dake saman table.....ga half finished coffee din daya fara sha ya bari bai qarasa ba.

A hankali ta zauna gefan sofa din,inda ya zauna a dazun kafin ya tashi,ta miqa hannunta ta dauki cup din coffee din. A bakinta ta sanya a hankali,hancinta ya zuqo mata qamshin coffee din da qamshinsa wanda komai ya taba koda sau daya ne tak sai yabar masa wannan tambarin na ya taba mu'amalantarsa.

"Yabar dumi a komai" Ta fada a hankali tana murmushi tare da cire cup din ta ajiyeshi,tana jin yadda gangar jikinta ta fara canzawa.

"Shin da gaske ina missing dinsa?" Ta tambayi kanta da kanta. Kanta ta girgiza da sauri tana musanta zuciyarta.

"Ridiculous" Ta fada tana yatsina fuskarta.

Telephone dake ajiye a parlor ce tayi qara,ta miqe a nutse taje ta dauka. Daga ma'aikatan sashen ne. Suna tambayarta ko akwai wani abu da take buqata?. Tace musu ba komai ta maida wayar ta ajiye.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 95* _________________________ *_Amintaccen gurin siyayya_*

*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*

*_BONONZA DA PROMO akai akai_*

*dukka sai a HUGUMA CLOSET*

*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*

*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*

*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*

*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________

Cikin mintuna taji kadaici yana neman kayar da ita,sai kawai ta sake laluban shehnaz. Bugu biyu ta dauka,saidai karadinta shine abu na farko daya fara cika mata kunne.

"Kee!!!!!...wai mu zakiwa surprise ki rigamu isa dubai?" Dariya kadan akhnan tayi amma mamaki yana cikata.

"Ya akayi kika gane?"

"Latsani......bakiga line dinki bane?,kinsan me yake rubutawa kuwa?" Idanu tadan waro waje.

"Ban gane ba.....me yake rubutawa shehnaz,banason sharri".

"Ba sharri take ba....ni kaina nasan yanzun saimun lallaba zamu dinga samun ganinki" Muryar aisa ta maye gurbin muryar. Tashi tayi ta zauna sosai tana fidda blue eyes dinta. Tayi kewar aisa ba kadan ba,har batasan adadi ba,ta jawo pillow din da sai dayazo jikinta ta tuna pillow din da haisam ya rungume ne a dazun,qamshinsa ya cika mata hanci.

"Nayi fushi....nayi fushi"

"Na yarda....kome zakice.....amma ki jira gobe mu iso,sha biyu na rana agogon dubai in sha Allah". Qaramin ihu ta saki,har tana jin kamar tayi tsalle ta kamosu.

Hira sosai ta barke a tsakaninsu. A cikin haka suka gaisa da ahmad,ahmad din da duk bayan kwanaki biyu rakkin saiya kirata. Suka gaisa da Nannie,sannan morsa safiyya da haka kawai takejin wani nauyinta da respect yana ratsata. Taso ta danyi mamakin abinda ya hadasu haka guri daya amma sai bata tambaya ba.

Ta nema sultane,kaman yadda suka saba akace mata yasha magani ya kwanta,

"Ya ahmad......seven days ba tare da naji muryar sultane ba.....haka aure yake?" Ta fada a karye. Wani dariya yasaki mata.

"An ture gwamnatinki ne wasu sunhau yarinya" Ya fada da tsokana a muryar sa. Raurau tayi da idanu,kafin tace komai taji muryar morsa safiyya,da alama wayar ta karba.

"Kada ki biye masa biftuu,ko dasu sultane yace zai kiraki,magani yasha,wani magani yake sha wanda yake yawan sakashi bacci,amma yau dinnan zan tabbatar kunyi magana" Ta fada tana qoqarin boye hawayenta da kalar raunin da zuciyarta tayi.

"Na gode momma.....na gode".

Sunyi hira sosai har ta wasu awanni kafin suyi sallama. Duk sai taji zumudin zuwan nasu yana cikata. Ta soma dawo da wasu memories,zuwansu dubai a sanda bata da aure. Suna matuqar son zuwa,saboda qasar na musu dadi da cikakken tsaro da 'yanci.

Falaak ta shiga nema,wanda ba jimawa ta shiga ta daga. Muryarta kamar alamun bacci take,amma koda taji muryar akhnan din sai gata ta wartsake.

"Yaa biftuu.....kin daina fushin dani?" Falaak ta fada a narke. Wani murmushin kunya akhnan tayi. Ta tuna wancan ranar.....wancan lokacin,amma a yanzun sai taji zuciyarta ba wannan haushin na falaak. To haushin me ma zataji nata?,bayan abinda tayi itama ya biyo ta kanta?.

"Ni ba haushinki nakeji ba falaak,tausaya miki nayi kuma baki gane ba" Dariya tayi kadan tana cewa

"Inaso na kiraki.....amma tsoro nake"

"Ni gashi yanzu na kiraki ai". Hira sosai tsakaninsu,irin hirar ma da bata dauka zasuyita ba.

A cikin hirarta da falaak ta dinga tsintar abubuwa da yawa. Da alama yarinyar ta iya abubuwa masu yawa,a hankali daga waya sai gashi sun koma chart da ita ta watsapp.

Awa daya da rabi suka shafe kafin su rabu ya chart din. A awa dayan ta d'arsa mata son koyon abubuwa da yawa,a awa dayan ta dauki wasu lesson da tayita tunanin ya akayi falaak din ta fita fuskantar rayuwa haka?.

"Momma ce ta raineta.....mammina ce ta raineki" Amsar da zuciyarta ta bata kenan. Amsar data zauna ta yita jujjuyata,ta dinga kawo abubuwa da yawa a ranta.

"Anya?" Karo na farko zuciyarta taji ta dasa wata qatotuwar ayar tambaya akan mammina din.....karon farko da taji tana sake nisa da ita a zuciyarta nisa me tarin yawa.

Batasan adadin mis calls nata guda nawa ke a wayarta ba,daga sanda tabar agadez har zuwa wancan satikan. Wasu kiran a gaban idanunta suke shigowa su kuma yanke su koma mis call,amma ko sau daya bata taba sha'awar dagawa ba ko kuma tabi kiran.

A hankali hankalinta ya soma karkata yana komawa kansa. Ta soma lissafin wucewar kowacce daqiqa da mintuna zuwa awanni. Rana ta fara karkata zata fadi,sai ta yanke fara alwala saboda kiran sallar daya fara daga cikin wayarta.

Idanunta ta lumshe tana jin wani dadi da nutsuwa yana ratsata. Bata saka kiran sallar ba,amma ta sani shine ya sanya. Yana da qoqarin kiyaye lokutan ibada matuqa,daya daga cikin abinda ke qara masa kwarjini a idanunta kenan. Da yawa sallarta da wasu zaman addu'o'i ta fara daukar yanayin nasa ba tare data sani ba.

Readers Also Read

More by Huguma