L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 54
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 54: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 54. Cikin bathroom din tayi alwala ta tayar da sallar…
3,370 words
Cikin bathroom din tayi alwala ta tayar da sallar magariba a musallah din dake dakin. Data idar kiran falaak ya shigo mata. Nan ta zauna tana sake cikata da surutu kafin kuma tace.
"Maleekqalb ya kusa dawowa.....zanje na shirya yaa biftuu"
"Yayi kyau" Ta amsa mata a taqaice. Wayar ta ajiye tunaninta yana tafiya wani guri.
"Kenan kwalliya zata masa sanda yake dawowa daga wani guri?" Sai taji kaman saqo ne falaak ta aike mata,ta miqe a nutse tana tayar da ishai bayan da wayarta ta sake bugawa.
Samun kanta tayi da zare kayan jikinta ta daura towel. Wani ra'ayi taji yana saukar mata......ta gwada wani abu itama,ko sau daya ne ta gani ko zata burge?.
Bathroom ta wuce ta bata lokaci tana wanka,bawai don akwai buqatar yin wankan tare da ita ba. Ta fito steam din bathroom din yana yawo a hankali.
Ta tsaya a gaban babbar luxury closet din dake cike da kayan da suka bata mamaki. Tun asali suke zube a jere a tsare haka a ciki?,ko kuma dama yasan ya shirya tahowa ne da ita?.
Abinda yaf bata mamaki,komai ta taba cikin kayan sai taga favourite dinta ne,tun daga color zuwa design gaba daya.
"Ya akayi ya sani?" Ta tambayi kanta,sai taji can qasan ranta tana ganin baike da aibun kanta. Ta kasa riqe abu daya da nanay ta gaya mata tattare dashi,duk wani leakage a kanshi ta gaza haddaceshi.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Me yasa ya damu dani da komai da nakeso?" Ta kuma fadi sanda take sake qarewa kayan kallo.
Silk abayas,soft fabric....elegant sleepwear......ga wasu luxury perfume masu yawan da batasan adadinsu ba,kamar kwasosu kawai akeyi ana zubawa(batasan gidan turaren ta tarar ba).
"Wanne ne zaisa ya kasa dauke idonsa daga kaina?" Karo na farko da taji tanason yin abu don ta burge wani,wanin ma wai d'a namiji da basa cikin lissafinta. Dariya ta yiwa kanta,kafin ta saka hannu ya ciro wata soft royal silk abaya.
Soft champagne gold color me wani irin taushin kallo a idanu. Lokaci ta bata sosai ta shirya kanta da wanin irin yanayi da taga birra na mata. Hannunta dukka taji sun gaji ko kafin ta gama gyara gashinta,saidai ko ita kanta data gama styling nasa sai data sake kalla cike da mamakin ita tayi wannan gyaran?. Ya kwanta ta gaban goshinta kadan,ga wani soft waves kadan.
Haka kawai tayi sha'awar sauya turare yau saboda tarin turarukan data gani a gabanta. Kowanne idan ta dauko sai ta bude idanunta waje saboda tsadar duk kwalba daya.
Abinda yafi daure mata kai shine.....duk favorite brand dinta ne
"Bai manta ba a wancan ranar dana gaya masa?" Ta fada qasan ranta. Murmushi ya subuce mata,a karon farko da taji wani aminci da yarda da son da yake mata,duk da bata taba kokwanto ba.....amma na yau din na dabanne.
Vanilla oud and rose musk tayi amfani dashi,qamshin da ita kanta taji ya tafi sosai da ita. Sanda ta kalli agogo sai taga lokacin ya mata tsayi qwarai daga sanda ya fita zuwa yanzun.
Wayarta ta dauka ta juya tana fita saita yanke wucewa inda zata iya ganin panoramic views na dubai.
Tana tsaye gaban panoramic glass window din. Sosai take ganin dubai skyline din tana qyalli da haske a gabanta kamar taurari masu rai.
"Beautiful but lonely" Ta fada a hankali tana jin yadda gurin yayi mata. Su shehnaz ta tuna a irin wannan lokutan sukan kasance tare. Suyi hotuna da videos su ajiye a matsayin memories kafin dawowa ta gaba.
A hankali ta sake komawa tunaninsa,muryarsa nakai kawo cikin kwnayarta. Royal suit din yayi shuru amma muryarsa ta gaza tsaiwa a cikin kanta.
"Yaushe na fara jin rashin wani mutum haka a kusa dani?" Ta tambayi kanta a hankali tana bude idanuwanta gaba daya gami da saukesu can qasa wadda keda nisa da inda take tsaye,saidai hakan baya hanaka ganin movement na ababen hawa.
Tana shirin dauke idanunta wani convoy na black luxury SUVs ya shigo hotel entrance din.
A nutse take bin tsarin motocin nasa da kallo wanda ke motsawa zuwa ciki da wata irin nutsuwa.
"Haisam" Harshenta zuciyarta dama gangar jikinta gaba daya suka furta a lokaci guda.
Kasa motsawa tayi a gurin,zuciyarta na qarfafarta ta fita ta tarbeshi kaman yadda nanay ta koya mata.....wata zuciyar kuma najin kunya da nauyin hada idanu dashi suna danneta.
"Zan iya....zanyi" Ta gayawa kanta ta soma takawa a hankali tana fita zuwa bakin qofar farko ta suit din nasu.
Ba gajiya kawai yakeji a jikinsa ba.....harda wata irin kewa da matuqar buqatar kasancewarsa a gefanta.
Daga bakin residence din suka dakata,yaci gaba da takawa a hankali da waya a kunnensa yana sauraren bayanan balaraben daketa son saka hannun jari me yawa cikin sabon kamfanin turaren. A yau yaso su hadu dashi su gana shima,amma yawan ayyukansa na yau din bai bashi wannan damar ba.
Sanda ya murda handle din yaji kaman bashi kadai ya murdashi ba,amma saboda hankalinsa yana takan wayar bai kawo komai a ransa ba ballantana ya kawo cewa itace.
Daskarewa yayi gaba daya sanda qofar ta yaye,qofar data zama hijabi qwaya daya tsakaninsa da akhnan din
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 96* _________________________ *_SHUWA INCENSE AND MORE_*
😊 *_kai daga jin sunan basai an gaya maka ba_*
*_kai daga jin sunan basai ka tambaya ko tsaya tunanin maganar me ake ba_*
*_MAGANA CE TA GIDAN QAMSHI_*
*BAFA GAMA GARIN QAMSHIN DA KIKA SABA JI BA HAJJAJU*
*KINA QONA TURARE YANA QAURI*
*KINA SAKA KHUMRA TANA BIN SHANUN SARKI*
*WANNAN DIN TURARE NE DAKE DAWWAMA A DAKI DA JIKI.....DA SALON QAMSHIN DAKE MANTAR DA ZUCIYA DUK WANI B'ACIN RAI*
*TASTED AND TRUSTED👌👌👌100% HAJJAJU*
*NA DABANNE A CIKIN NA DABAN*🙌🏽🙌🏽
*idan akazo kan SHUWA INCENSE an tashi magana*
*idan ma kinsan baki shirya jan magana ba a duniyar qamshi to kisha zamanki hajajju*
*_zaku iya magana da ita kai tsaye ta wannan number wayar_* +234 704 229 3387 __________________________
Wayar hannunsa ya sauke a hankali kamar wanda hannun nasa yake masa ciwo....kamar kuma tana shirin zamewa ta fadi daga hannunsa,idanunsa suka tsaya kyam a kanta. Wani irin kallo yake binta dashi kamar mayunwacin zakin da yaga danyen nama. From head to toe,irin kallon nan da ake kira da kallon qurilla,kallon da babu wani sashe daya bari na jikinta ba tare daya sauke Idanunsa a kanta ba. Silk kayan jikinta da sukabi jikinta suka lafe suna sake fidda calm aura dinta.
Yadda ta kasa daga qafa haka ya kasa qara taku ko daya ne don ya isa gareta. Idanun nan nasa dafi suke zame mata,wanda zaita jagwalgwala zuciyarta cikin dare,yana sake lallasa naman zuciyarta da zallar soyayyarsa. A duk wunin daya mata irin wannan kallon......tana rasa baccinta a wannan daren gaba daya. Sanda dukka idanuwa ke bacci....ita nata idanun sukan kasance a bude ne cikin bege da ganin gilmawar kowanne motsi da irin kallon daya dinga binta dashi
"What?" Ta tambaya a hankali tana motsa siraran labbanta dake glowing din lip gloss din data shafa dan kadan.
Shuru yayi na wasu sakanni,kamar ya manta yadda ake magana,kafin a hankali muryarsa can cikin maqoshinsa yace.
"......You cannot wear something like this and expect me to think normally khadeejaah." Ya qare da furta sunanta da wannan muryar da sautin dake tafiya da ita.
Kunya taji ta rufeta,kunyar data bayyana sosai ta kuma zame mata wani irin ado daya sake burgeshi yaji kaman yana narkewa a gurin.
"Its just an abaya fa?" Ta fada tana juya idanunta,ba don tayi calling attention nashi ba,kawai yanayin maganan ne yazo mata a haka.
"No" Ya fada da sauri jin wani abu yana fusgarsa zuwa gareta
"On you......its a problem" Ya cire qafafunsa yana matsowa inda take.
Burinsa shine kawai ya isa gareta,burinsa shine kawai yaji duminta cikin jikinsa.....burinsa kawai yaji fatarta cikin tasa.
Matso da ita yayi cikin jikinsa sosai,yana mata kyakkyawar tarba. Kyakkyawar rungumar data sanyata sakin ajiyar zuciya ba tare data shirya ba.
Tana jin hannunsa yana yawo tsakanin kafadarta zuwa yatsunta yana murza silk din rigar cikin hannunsa tare da fatar jikinta. Sannu a hankali ya cusa kansa tsakanin wuyanta da kafadarta yana shaqar daddadan qamshin vanilla oud din da take fitarwa,muryarsa a rikice yace.
"And.....this scent" Sai ya dakata yana sake zuqe qamshin sosai dake aike saqo cikin kwanyarsa.
"......you're trying to destroy my peace tonight" Ya qarasa maganan yana dagata daga jikinsa yana kuma sarqe qwayar idanunsu guri daya.
Kunya sosai.....kunyar data sanyata ta zabi kwantar da fuskarta cikin qirjinsa,tayi kuma kyakkyawan gamo da wannan qamshin nasa. Na musamman ne tabbas wannan qamshin. Duk yinin da zaiyi a jikinsa......bata taba ji wani abu ya jirkita qamshin ba,saidai ya sakeyin wani irin sanyi me kwantar da zuciya.
Tana jikinsa suka qarasa ciki,har a sannan tana satar kallonsa. Har yanzu wannan kyan da suite din suka masa kafin ya fita shine dai. Nauyin aiki kujiba kujiba duka basu jirkitashi ba. Yanayinsa wani abune da ba komai bane ke saurin jirkitashi. Sai ta tuna........yadda yake magana calmly......yadda baya nuna dukiyarsa......yadda yake zama kamar ordinary mutum a gabanta......alhali......mutum ne da manyan mutane ke miqewa saboda shi.
Batasan kallonshu take ba sai da yace da ita.
"You waited awake......thank you" Ya fada yana cire agogon hannunsa idanunsa a kanta.
Kasa amsawa tayi,don har yanzu zuciyarta tana processing komai a kansa. Taku biyu ya qara ya matso kusa da ita.
"What's it?" Ya furta yana shafa gefan fuskarta da lallausan tafin hannunsa.
"Wadanne mutane ne wadancan na daxun?" Wani faint smile ya taba lips dinsa. Kamar ya fahimci inda tunaninta ya dosa
"Business associates" Ya amsa mata a hankali.
"No" Ta fada har cikin ranta,haka kawai taji bata gamsu da amsarsa ba.
"....people don’t look at ordinary businessmen like that.”. Magananta ya sauka kunnensa a hankali,shuru ya ratsa na wasu sakanni,sai ya sake takowa yana sake riga tazarar dake tsakaninsu sosai da wani irin kusanci,don har yanzu bai shirya bata license na sanin waye haisam in full details ba. Da wani irin low voice ya kalleta.
"And yet....." Ya fada yana kulle idanunta cikin nasa.
"…you still look at me like I’m only Haisam.” kasa magana tayi,yana sake dora mata kunyarsa. Batasan adadin yadda take kallonsa ba,ita kanta kamar idanunta sun rasa control haka takeji.
Murmushi ya sake mata dan kadan,saidai zurfinsa a zuciyarta yana da yawan gaske. Yakai hannunsa yana dan janye mata gashin kanta daya sauko kaman zari rufe mata ido.
"I think that’s my favorite thing about you.”
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Tanaso ta tsaida kallonsa haka,amma abubuwan mamaki yake bata episode episode. Tayi tsam da ranta tana duban inuwarsa ta gefe kamar tana qoqarin hada mutum biyu guri guda.
Haisam din dake mata magana cikin laushi......karyar da kai da karya matsayinsa. Haisam din dake iya roqonta.....haisam din dake iya bata haquri.....haisam din dake koma mata tamkar qaramin yaro. Da kuma mutumin da manyan mutane ke rusunawa.....mutumin da manyan mutane ke biye dashi a baya.......mutumin da manyan mutanen ke rakashi har bakin mota cikin girmamawa.
Baya ya janye mata kadan,ya saka hannu yana cire cufflinks dinsa a nutse yana ajiyewa saman table.
"Ban sanka sani na haqiqa ba" Ta fada a sanyaye,tana tsoron fadawa inda aka girmi matsayinta da Nisan tazarar da zata wafce dukka kimarta
"Really?" Ya furta yana dage dukka girarsa gaba daya idanunsa suna rusunawa sosai kaman wanda yasha wani abun maye. Idanunta ta sake zarewa a hankali,da gaske takeso ya dauki abinda take gaya masa.
"Kullum saina gano sabon abu game dakai....." Saita dakata.
".....me girma" Ta dora da fadi numfashinta yana sauyawa. Yadda numfashinta ya canza hakan yaji ya tabashi sosai. Ta yaya zai iya jurewa ci gaba da jinyarta ne?,tana juyewa da wani salo da baisanta dashi a baya ba. Sai shima yaja da baya yana jingina da table din dake kusa dashi don ya bashi support. Idanunsa baibar fuskarta ba
"And does that scare you?". Ta fahimci wasa da kuma tsokana kawai yakeson maida zancan. Amma gaskiya ne.....kadan kadan abubuwan suna bata tsoro.
"......A little" Ta yanke shawarar fadin gaskiyar abinda yake ranta.
Wani siririn murmushi ya taba lips dinsa,murmushin fahimtar gaskiyarta da take fada,murmushin fahimtar bata iya boye abinda yake ranta sosai ba.
"Na fahimta......zaizo ya wuce,kema zaki fahimci komai...amma" Ya fadi yana dakatawa.
"You missed me after only a few hours right?" Idanu ta waro sosai tana sake jin mamakinsa da tsoronsa.
"Bance haka ba" Ta fadi da yanayin son karya hasashensa. Can qasa yayi dariya irin wacce ba kasafai yake yinta ba.
Idanunsa sun sake rusunawa sosai sanda yake takowa yana dawowa gabanta.
"You waited by the window" Ya fada calmly yana sake riqe qugunta da duka hannayensa,kaman wanda ake busawa siririyar sarewa take shiga kunnuwansu a hankali.
"You watched for my cars...." Ya sake fada muryarsa tana sakeyin qasa.
"......And your heartbeat changed the second I walked in.” ya fadi da muryar rada wadda ta raunata dukkan jinta da gangar jikinta.
Kunya.....wata irin kunya ta sake lullubeta
"Haisam....." Ta furta da wata kalan kasalalliyar murya. Sai ya sake matseta sosai a jikinsa,yasa yatsansa yana daga habarta a hankali.
"Say it" Ya fada cikin rad'a
"Me....." Ta fada muryarta tana sake zuqewa itama
"That you missed me...." Ya qarasa maganansa ta farko. Da sauri ta girgiza kai,sai ya saki wani kasalallen murmushi......wannan dangerous calm smile din.
"Liar" Ya furta a hankali. Zame fuskarta tayi saboda yadda taji dukka jikinta yana amsawa.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 97* _________________________ https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0
*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*
*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*
*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*
*_Assalamu alaikum my loyal people_*
*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*
*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*
*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*
*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*
*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*
*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*
*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*
*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*
*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee* __________________________
Maganansa ya sanya ta kasa hana qaramin murmushin dake fuskarta fitowa. Sai ta juya zata wuce,still ya kamo yatsuntsa a hankali
"Relax mana....." Ya ha fada yana kashe mata idanunsa.
"I'm teasing you...."sai ya sakar mata hannun a hankali yana sassauta tie din wuyansa idanunsa a kanta still.
" Na gaji" Ta sakejin ya fada sanda shuru ke shirin musu kutse. Daga kai tayi a hankali ta kalleshi. Yadda ya fadi kalmar ne ya sanya ta lura da gajiyar dake boye a muryarsa.
"Duk da wannam composure din......ashe ya gaji sosai" Ta furta can qasa ranta.
"Sannu" Ta furta kalmar da tarin kulawa cikin sautinta da kuma idanunta,abinda yaji ya masa dadi sosai,musamman sanda ta dora da fadin.
"Da alama yau me wahala ce" Idanunsa ya lumshe har kamar bazai bude ba. 'Yar qaramar kulawarta tana nufin abubuwa da dama cikin ranshi dama darensa na yau. Sai kuma ya saki numfashi a hankali yana warware cuff din hannunsa
"Meetings.....investors....royal approval......" Ya sake lumshe idanunsa yana dorawa
".....and too many people talking at once....." fada a hankali duk da ba amsar da yayi niyyar bata ba kenan,amma sai yaga ko yaya.....ko yaya ta cancanci taji wani abu koda kadanne da zai kwantar mata da hankali.
Maganarsa ta qarshe ta kusa sanyata tuntsurewa da dariua,ta kuma shafe abinda ya kamata ace hankalinta yakai kai. Wato kaman itane.....a duk sanda tayi calling for meeting a sahel couture ba'a cika lokacin ake tashi. Batason hayaniya da dogon magana,amma shi da alama ya fita.
Ta murmusa cike da burgewa sannan tace.
"Amma ka iya handling komai calmly" Maganan ya qwace daga bakinta,don ba'a zahiri taso furta hakan ba,zuciyarta taso barwa.
Idanunsa ya sake dai lumshewar yana budesu dukka a kanta kaman ya qara musu girma yanason ganinta sosai.
"Wannan calmness din.....yana disappearing sometimes around you my princess" Bugawa zuciyarta tayi a hankali,ta buga da wani yanayi daya isa har kunnenta ya kuma sanya numfashinta nauyi cikin qirjinta.
Suits dinsa na saman ya zare a nutse,kai tsaye kuma ya miqa mata,kamar wanda ya saba yin hakan tunda dadewa.
"Zanje nayi wanka na dawo before you start over thinking life again". Rusunawa tayi tana karbar rigar daga hannunsa,wani yanayi daya tilasta masa binta da kallo sanda take juyawa tana wucewa daki da rigar.
A hankali idanunsa suka sauka akan qugunta,yadda yake juyawa kaman wanda ke karbar umarni daga wani guri,sai ya samu kansa da miqa hannu kaman zai kamota,sai kuma a hankali ya maida hannun nasa ya dunqule,murmushi yana qwace masa,ya taka a nutse yana bin bayanta.
Haka kurum tunaninta yayi nisa sanda takejin motsin saukar ruwa a bathroom din. Me ya kamata tayi?,yace ya gaji.
Samun kanta tayi da duba menu dinnan da nanay ta aiko mata a gida a wancan lokacin,ta kammala dubawa tas,sai ta saki qaramin murmushi tana cije lips dinta,ta ajiye wayar tana miqewa,a hankali kuma ta furta
"Suruka ta gari".
Mintuna kusan arba'in ya dauka,sannan ya fito parlor din sanye da black silk trouser da farar t-shirt me laushi. Sassalkar sumar nan me santsi da ragowar damshi a cikinta. Qamshin fresh oud da sandalwood na biye dashi qafa da qafa. Yau wani qamshi na daban takeji a tare dashi,baqon qamshin da tunda suke sai yau ta fara jinsa a tattare dashi.
Sauyin qamshin ne yaja hankalinta. A nutse ta daga kanta daga amsa messages na falaak da takeyi ta zube kallonta a kansa. Ya mata kyau....wani irin sassanyan kyau,ko don bata saba ganinsa cikin qananun kaya haka bane?. Data tuna a gaban wa take kuma saita sauke kanta da sauri.
"You're staring"
"Ban kalla ba" Ta amsa da sauri,wata tattausar dariya ya sake.
"Another lie". Kai ta dauke tana sake jin nauyinsa,yayin da shi kuma ya aza idanunsa akan gurin.
Wani irin luxury setup ne.....da warmlight ne a gurin me kwantar da zuciya.
" Wow......ma sha Allah" Ya fada yana qarasawa. An ajiye pillows masu laushi qananu qananu wadanda yafi jin dadin zama a cikinsu yaci abinci duk sanda ya gaji irin haka.
"Waye ya baki satar amsa?" Ya tambayeta kai tsaye bayan ya zauna yana dubanta murmushi yana qin barin fuskarsa.
Yadda taga ya yaba kawai ya sanyata jin wani irin dadi. Take zuciyarta taji tana mararin ci gaba da ganin wannan yabawar.....wannan jin dadin saman fuskarsa.
"Komai da komai......ya kamata na koya" Taji zuciyarta tana sake qarfafarta.
Tayi qoqarin serving nasa.....zata sake zubawa a wani plate din ya janye,ya saka musu spoon biyu a dukka plate din.
"Oya....bismillah" Ya fada yana tattare hannun rigarsa gami da janye nasa spoon din gefe.