Kenza eBookz

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 56

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 56

L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 56: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 56. Basu aisa kawai ba.....hatta da akhnan kanta ya sake…

3,350 words

Basu aisa kawai ba.....hatta da akhnan kanta ya sake kwanceta fitar da sukayi. Guraren da suke kashe kudade masu yawa.....guraren da suke kula da shigarsu a yau sun shiga sun fito ba tare da sunsan sun kashe komai ba. Batasan girma da kimar da yake dasu haka ba cikin qasar.....wanda iya card dinta kawai ake kalla a duk inda sukaje din sai taga an ninka girmamawar da ake bata.

luxury malls.....rooftop lounges......waterfront restaurants......designer stores.....amma duk inda suka shiga da zarar Akhnan ta nuna card din. Staffs nasu suna sauya attitude instantly.....still kuma ana kaisu VIP sections a kowanne guri da zasuje din.

Daidai da boutique din da sukaje private collection room aka kaisu.

"Wow" Kawai shehnaz ta fada. Kaman yau ta fara sani ko ganin luxury,sai takejin kanta yana sake girma da fadi.

"Sheikh dinnan....wannan sheikh din naki ya wuce duk zatonmu.....me yasa ya boye kansa haka?,anya ba yana sane bane kuwa?,anya ba wani babban dalili kuwa?" Shehnaz ta fada tana fidda idanunta waje sosai.

"Kudi ne da mutumin nan irin na films"

"......ba kudi kawai ba shehnaz....influence" Aisa ta fadi itama abun yana tsumata.

Tambayar qarshe da suka mata bayan sun koma gida. Shehnaz ta rutsata.

"Don Allah biftu mana.....wannan fa ba sheikh dinnan bane na agadez.....ki gaya mana waye haisam?" Tana daure zaren igiyar rigar baccinta ne sanda shehnaz take mata tambayar,kanta cunkushe da tunani,saita samu saman sofa bed ta zauna tana dubansu da blue eyes dinta.

"Mijina" Ta furta kai tsaye don bata da amsar data wuce wannan.

"Akhnan" Aisa ta fadi tana sake samu tabbacin wani abu game da abinda yake faruwa yanzun haka a sahel couture.

".....barta mana aisa.....bafa wannan muka tambaya ba" Ta fada tana fiddowa akhnan ido waje,abinda ya tilastawa akhnan din murmusawa. Idan wannan tambayar ce....itama har yanzu neman cikakkiyar amsarta takeyi

"Kinga yadda mutane suke rusuna masa kuwa?" Aisa ta fada fuskarta dauke da tarin tambayoyi da kuma murmushi.

"Ke bakiga yadda ake sauya komai saboda sunansa kawai ba?" Shehnaz ta fada tana rungume da hannayenta. Komai burgeta yake.....amma mamakin da suke shiga yafi qarfin kwatance.

"Ni kaina ban gama fahimtar hakan ba....ni kaina a rude nake har yanzu" Ta fadawa kanta da kanta ba tare data bari sunji ba.

Security alert na qofar suite dinne ya kada,alamun akwai wani kusa da qofar. Hirarsu ta katse da tarin tambayoyinsu,suka maida dubansu ga akhnan.

"Bari na duba" Ta fada softly tana miqewa gami da zura flip flops dinta.

"Dawo ki dauki wayarki,don idan mijinki ne babu lallai ya barki ki dawo" Aisa ta fada tana dariya shehnaz tana tayata.

Tsaiwa tayi cak,sannan ta waiwayo tana watsa musu harara.

"Banason sharri.....be dawo bama ballantana kuce shi dinne".

" Zamu gani.....idanuwan sheikh na rantse da Allah cike suke da giyar qaunarki....kowanne motsinki akan idanun security dinki,wanda na tabbatar suna aikinsu ne da qaqqarfan gargadinsa na su kula dake".

Bata waiwayowa ba ta biyewa zancan shehnaz,saidai har cikin ranta tana jin saukar kalamanta,ta kuma ga hakan itama,ta yarda dari bisa dari,amma idan tace zaya biyewa shehnaz ne to zasu kwana suna musu.

A hankali ta murda qofar tana budeta. Zuciya daya.....ruhi daya dake rayuwa cikin gangar jiki guda daya suka bayyanawa juna.

Yarima haisam ne......sanye cikin dark gray din silk pajamas masu gajeran hannu da dogon wando. Sassnyar iskar dake yawo cikin Atlantis the royal tana kada daddadan turaren nasa kamar yadda take kada sassalkar sumarsa dake kwance saman kansa. Da alama ya dawo tun dazun,kuma har yayi wanka sannan ya sauya kayanshi ba tare data sani ba.

Ta qifta idanunta har sau biyu a kansa saboda yadda ya mata wani irin sassanyan kyau cikin hasken fitilun alfarma da suka qawata ginin gaba daya.

Baiko barta tayi tunani na biyu ba,ya saka hannunsa dukka biyun ya dagata cak kamar ya samu baby doll,ya rungumeta sosai cikin qirjinsa sannan ya juya ba tare daya damu da rufe qofar suite din ba.

"Ka saukeni please,zan iya tafiya da qafafuna"

"No need.......indai ina tare dake ba buqatar sai qafafunki suna aiki,tawa ta ishemu" Ta motsa zata sake magana,sai bai bata wannan damar ba,ya hade bakinsu guri daya yana takawa da ita sannu a hankali har suka isa suite din nasu.

Ta dauka zai sauketa ne ta taka da qafafunta tunda sun shiga ciki....amma akasin hakan ci gaba yayi da tafiya da ita,bai kuma sauketa a ko ina ba sai cikin bedroom din da a yanzun suke sharing shi da ita. Ya kulle duka sauran bedroom din guda biyu ya hana mata maqullin.

Saman lallausan gadon ya direta sannan yayi mata rumfa. Da wani irin zafi zafi yake aike mata da saqo.....wasu irin saqonni da suka soma bin jininta cikin mintuna qalilan.

A yau....bar mata bakinta yayi a bude,baiyi yunqurin komai na rufe mata shi ba,saidai da kanta.....a karan kanta ta kasa kiran sunan kowa.....ta kuma kasa tabuka komai saboda yadda saqon ke shigarta da wani irin tasiri me gigita tunani.

Sai daya kaita wata duniya me nisan gaske.....sai daya kaita qololuwa sannan ya zame jikinsa a hankali yana sauke wani irin numfashi.

Shuru ne ya ratsa tsakaninsu,wani irin shuruuuu daya shige har cikin kawunansu. Ya runtse idanunsa sosai yana riqe tsintsiyar hannunta da wani irin qarfi da sai da taji riqon har cikin qashinta,a kasalance ta furta.

"Wayyo Allah" Mirginawa yayi yana maidata cikin jikinsa da kyau yana matseta sosai wannan karan har sai data saki qarar me dan qarfi.

"I'm sorry....." Ya fada dukka jikinsa yana rawa.

"Me yasa zaki tafi ki barni?......me yasa zaki barni a kango?,me yasa zaki sanya na dauki alqawarin da zai wahalar dani?" Ya fadi yana kamo fuskarta ya hade da tasa yana sauke wani irin wahalallen numfashi,gumin da yake tsatsafowa daga kowanne sashe na jikinsa yana ratsa fatarta wadda tuni ya kauda komai da zai zame masa shamaki daga nutsewar fatarta cikin nasa.

"I'm sorry......kayi haquri" Ta fada softly tana motsa labbanta da wani yanayi daya tilasta masa kama lips din nata ya tsotsa da kyau. A hankali ya zame bakin nasa daga nata,ya sake riqe fuskarta sosai a tausashe

"Ke tawa ce......ni kadai giiftii.....ba zanyi sharing dinki da kowa ba" Ya fada yana zamewa daga jikinta. A karo na biyu ya sake saka hannu ya dauketa cak,ba tare daya damu daba komai a jikinta ba,ya kuma wuce kai tsaye da ita zuwa bathroom,tana qanqameshi saboda nauyin hakan da takeji,saidai batasan hakan da takeyi sake kunnoshi kawai tayi ba.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 100*

*_THE REVEALS_*

Wani shiryayye kuma lafiyayyen grand opening ne da labarin yinsa ya zagaya duniya gaba daya. Wani bikin bude kamfani da yasha banban da saura......bikin daya tara manya manyan shuwagabannin larabawa masu yawan gaske. Al'umma daga kowanne sassa na duniya.....bikin kuma da aka shirya gabatar dashi da daddare sab'anin rana.

Da wannan amintaccen hasken na qasar dubai,wanda ya zame mata kamar wani ado daya sake banbantanta da kowacce qasa a duniya. Kamar duk duniya sunfi kowa sanin martabar haske da qyale qyale na rayuwa.

Qarfe bakwai na daren.....sanda wasu irin golden light suke walqiya cikin babban dakin taron sabo dal dake wata shiyya daban na kamfanin. Manyan glass windows da na building din gaba daya an qawatashi da wasu irin fitilu gold color.....flowers masu tsada cakude da daddadan qamshin turare mafi tsada da girman daraja daga gurin larabawa wato oud. Tako ina qamshin sa ne me dadi yake tashi,qamshin da zai gaya maka da gaske bikin bude kamfanin turare ne.

Daga gefansa take zaune....cikin Rolls Royce din da a yau da kansa yake driving dinta ba tare daya buqaci driver ba.

Wani irin kyau yayi mata,wani irin kyau dake fusgar idanu da hankulan kowanne mutum.

Kanta ta dauke a nutse tana maidowa kansa. Ya jima a waje yana gaya mata gashinan dawowa.....ya jima da fita yana gaya mata zaizo da kansa ya kaita,har ta fidda rai,tana kuma kallo su shehnaz da aisa sukabi su maleek da falaak da suma sukace mata sunzo ganin bikinne. Ta danyi mamaki,idan shehnaz da aisa fan din brand dinne.....batasan maleek da falaak a wannan harkar ba.

Tanata juya wayarta tana kallon yadda lokaci yaketa gudu,idanunta sunata tara hawaye tana hanasu xubowa sanda ya shigo. Wayace a kunnensa yaketa amsawa,yayi cak yana zuba mata idanu kafin ya ware mata hannuwansa,ta taso kaman hakan take jira ta fada ya rufeta a qirjinsa. Still bai daina amsa wayar ba wadda da larabci yake duk maganan da yake,wannan ya sanya bata iya gane abinda yake fada.

Wayar dai bata qare ba,don yana ajiyewa wani kiran zai shigo,a haka ya taimaka mata ta fara shirya kanta cikin wata baqar laffaya da aka yiwa adon gold stones.

Sai daya taimaka mata ta gama nade jikinta tsaf sannan ya saki wayar tayi gefe.

"Ya salammmm.....zan iya?" Ya fada yana motsa maqoshinsa a hankali. Idanu ta fidda waje tana dubansa,gabanta yana faduwa,kada dai yace an fasa zuwa....indai hakane batasan wanne irin kuka zatayi ba

"Ina kishinki.....na rantse da Allah,inajin kamar kishinki zai iya kasheni......" Ya fada idanunsa suna lumshewa can qasa da wani irin emotion cakude da kishi.

".....idan wani ya kalleki biftu.....koda sau daya ne......inajin kamar na shafeshi yabar duniya.....inajin kamar kowanne namiji yabar duniyar nan.....ya barmin duniyata dake kawai a ciki" Ya qarasa fada yana mata wani kyakkyawan riqo cikin jikinsa kamar zai hadiyeta.

Saidai taji nasa kishin baikai nata ba.....nasa kishin kaman salam ne akan nata sanda ya fito cikin shigar wata irin suite da hannunta bai taba kaiwa kan fabric irin nata ba.

Har ji tayi kaman bata iya shaqar numfashinta da kyau,duk yadda takeso suje gurin,sai taji kamar tace masa su fasa.

"Yadai?" Ya fada sanda yaga yanayin fuskarta yana sauyawa. Kanta ta kwantar a hankali hannun kujerar.

"Zasu kalleka......."

"......dukkansu maza ne.....maza suke komawa a idanuna......wallahil azeem biftu" Ya fada yana kama tafin hannunta yana murzawa a hankali.

"Mu tafi?" Ya fadi bayan ya dauke idanunsa daketa haske. Kirane yaketa shigowa ba qaqqautawa wani yana bin wani.

"Muje....kiranka akeyi" Ta fada tana sauke idanunta akan wayar da taqi daina haske.

"Zan iya dakatar da komai saboda ke.....har sai kin amince kin gamsu mu tafi din" Ya fada yana daukar wayar. Cikin idanunta yaga kaman tana suspecting wani abu.....don haka ya haska mata fuskar wayar da sunan OMAR keta yawo akan screen din.

"Bayajin magana.....tunda suka hadu su shidan.....zasu cinye miki ni" Ya fada yana langwabe mata kaman yadda ya saba. Taji kunya ta kamata,ta saka hanny ta rufe fuskarta. Ta sani ya fahimci abinda yake mata yawo cikin rai,shi yasa ya goge mata wannan shakkar ta hanyar nuna mata me kiran.

"Indai ina kusa.....bazan dagawa kowa qafa a kanka ba".

"Ya ilaheeee..... Maimaita don Allah" Ya fada kamar muryar wanda yasha giya ya bugu. Cak ya tsaida komai,wannan kalmar kawai ta hanashi tada motar har sai data maimaita don kada su makara

"Da gaske nake....zan fito na fito da duk wada keda shirin matsa ma zaman lafiyarka"

"Oh my goodness!!" Ya fada yana riqe tafin hannunta cikin fuskarsa.

Ko yanzun da suke gaban building din,tana ankare da yadda security suka zagaye motar. Shi kuma ya zuba mata idanu.

Hannunta ya sake riqewa sosai yana murzawa a hankali,yana jin santsin fatarta da laushinta suna ratsashi.

"Anya zan iya?" Ya fadi ba tare da yasan maganan ta fito a fili ba. Kallonsa tayi,kallon dake alamta masa taji,sai ya sauke wani numfashi me nauyi yana sake kwantar da kansa saman tafin hannunta.

"Kimin alqawari don Allah.....inajin kamar na hanaki shiga.....amma bazan iya ba" Idanunta ta lumshe,a yadda ta kwadaitu da son shiga gurin,ba zataji dadi ba.....amma idan hakan ya yanke,zata jure.

"Fadi"

"Ba zaki kalli kowa ba"

"Zan zama makauniya na awanni duk don saboda kai" Baisan sanda ya raba shingen dake tsakaninsu ba.....ya mata wata kyakkyawar runguma ta mintuna

"Allah yayi miki albarka" Ya fada yana sakinta a hankali. Daga jiya zuwa yau kawai sake rikita masa lissafi takeyi,nan gaba idan ya gama horonsa yana hangota a matsayi best romantic wife.

Da kansa ya zagaya ya bude mata,ta sanyo qafafunta waje. Ga mamakinta duk security din sun watse,batasan kuma me ya watsasu ba.

Tanata ganin tahowar wasu mutane masu baqaqen kaya amma sai taga sun waske basu qaraso gurinsu ba,ko sun koma da baya,bata fahimci komai ba suka fara wucewa ciki,inda ta fahimci an fara gudanar da taron.

"Wannan opening din yana da girma sosai" Ta fada a hankali gurin yana qayatar da ita.

"Uhmm" Kawai ya fada a hankali da yanayinsa da taga yana komawa wani boss sosai a idanunta,kwarjinin nan da kamalarsa sai taga tana sake hauhawa.

Sake kallon giant black backdrop din hall din tayi. Sai idanunta suka tsaya cak. *MAISON AKHNAN* sunan ya bayyana baro baro. Idanunta tadan lumshe a nutse

"Akhnan?" Ta maimaita sunan kamar ba nata ba,saita waiwaya tana kallonsa.

Ido suka hada,dan siririn murmushi na gefan baki yayi sannan yaci gaba da takawa hannunta cikin nasa.

"Irin sunana?" Ta sake fada a fili saboda gaza boye mamakinta da tayi.

"Does it?". Bata amsa masa ba,sai tunaninta ya cilla kawai coincidence ne.....ko wani family name ne....ko branding style kawai.

Shigowarsu hall din ya danyi shuru.....Mc din dake magana yadan dakata kadan,kamar kuma wanda aka bawa umarni sai kawai yaci gaba da maganan da yakeyi. Cikin shakka da kokwanto taga suna nufar VIP section na baqi bisa jagorancin wani security guda daya dake sanye da baqaqen kaya idanunsa toshe da baqin glass. Har suka zauna bai saki hannunta ba,kamar yasan hakan ya taimaka mata qwarai wajen iya takawa har zuwa mazaunin data cika da mamakin wanne iko ne dasu da zasu zauna a nan?. Abu na biyu idanun da ta gani a kansu ba zata iya qirgasu ba......su suka sake daburtata....girma da tsaruwar gurin.....uwa uba yadda dukka hankula suke sake daukuwa a kansu tun bayan shigowarsu,sai takejin kamar wannan shine karon farko data fara shiga taro irin wannan. Daga gefansu kadan ta hangi su shehnaz......Anaani....rumaisa....balqess harda hansaaa. Daga can bangaren kuma su khadeem dasu amjad,saidai sunfi kusa da haisam akan inda take zaune din. Ta sake jin mamaki yana saukar mata. Dukkaninsu a VIP?.

Wata nutsuwa ta ziyarci gurin,kamar an musu wahayi,a hankali me gabatarwa ya sake bayyana da magana cikin nutsatsen turancinsa.

"Tonight, we are not merely celebrating a fragrance company…” babban screen ya haska daga bayansa. Bottle design na turarukan masu matuqar kyau suka soma bayyana.

Cak akhnan ta tsaya tana tattara hankalinta akan bottle din. Wadannan turarukan data sansu.....tasha amfani dasu,bayan wasu lokuta kuma sukayita bacewa daga kasuwa daya bayan daya.

Canzawa screen din yaci gaba dayi yana nuna mayan turarukan da duniya ke magana a kansu,wanda dukkaninsu daga ainihin brand dinta ne na amana.....company din da tafiso,turarukan da sukafi kowanne karbuwa a duniya,luxury collection din da ko ina ake magana a kansu,guraren iko sarauta da manyan attajirai.

"Wadannan brands din....." Ta waiwaya cikin magana rad'a rad'a tana gaya masa,sai kuma ta dakata saboda yanayin fuskarsa da taga ya sauya. Ya zama wani cikakken boss. Wannan kwarjinin yana sake mamaye fuskarsa. Wannan din sheikh muhammad haisam take gani. Idanunsa akan stage ya amsa mata.

"Yes" Ba tare daya waiwayo ba.

Kafin ta sake cewa komai muryar host din ya sake cika dakin taron.

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 101* ________________________ *_Amintaccen gurin siyayya_*

*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*

*_BONONZA DA PROMO akai akai_*

*dukka sai a HUGUMA CLOSET*

*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*

*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*

*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*

*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX __________________________

"The man behind one of the most exclusive fragrance empires in the Middle East…” sai ya dakata sauran maganan yana amsa kuwwa cikin dakin taron.

"......the founder of Maison akhnan" Sunanta ya sake amsa kuwwa cikin dakin abinda ya sanya gabanta bugawa.

"PRINCE HAISAM MOTII ABA JIFAR".

Gaba daya hall din ya karade da tafi da sowa da yabo,abubuwan da suka cakude gaba daya suka cushe kwanya da tunanin akhnan na wucin gadi,suka kuma dagula duk wani lissafi da take zaton tana dashi.

Sunan da host din ya kira ke sake amsa kuwwa cikin kanta,ta waiwaya a hankali sanda take hangoshi.....sanda Business elites suke miqewa cikin girmamawa,sanda tarin cameras ke juyawa kansa.

"Bayason camera a kaina....wannan dalilin ya sanya ya dan banbanta gurin zamana da nasa?.....inde haka ne da gaske shine....." Kasa qarasawa tayi saboda wani abu da taji yana sauka saman zuciyarta a hankali.

Tana kallonsa sanda ya miqe,Kamar wanda wannan ikon ba sabon abu bane gare shi. Wani irin pure power without noise a tare dashi.

Dole ta gabanta zai wuce,tana kallon yadda ya rage wannan ginshirar tasa sanda ya iso gabanta,ya rusuna kadan.

"You looked surprise?" Ya tambaya cikin salon tsokana,saidai ita a wannan matakin,ba tsokanar takeji cikin kanta ba,wani abu daban takeji daya girmi tsokanarsa.

"You...." Ta fada da qyar,murmushi ya mata kadan yayi kaman yana gyara cuff dinsa saboda yawan cameras din dake saitinsa.

"I'm sorry,I thought you would recognize the scents eventually.”

"All these perfumes?....you're the owner?" Ta fada softly ta yadda shi kadai zai iya ji,saboda tanason wanke zargin mafarki takeyi daga ranta

"For years...." Ya dakata kadan

"And now....."

".....your name is on the door".

Sai taji jikinta ya yi sanyi.Ba saboda kudin kawai ba.Ba saboda empire din ba. Sai saboda ya boye mata girmansa. Ya sanya sunanta a saman abin da yake alfahari da shi. Kuma bai taba amfani da dukiyar wajen nuna iko a kanta ba. Bai taba qoqarin gwada mata shi wani bane.....saidai ikon ya nuna kansa da kansa a tattare dashi. A iya nan kawai.....yasha banban da tarin mazan da sukasota,sukaso ta kasance mallakinsu.

Kowa yana zuwa don nuna mata kansa.....a sanda shi boye mata kansa yake. Sanda ya kama ta fara saninsa kuma.....ikonsa ne ke magana bawai shi ba.

Hannunsa ya miqa mata calmly.....yana jin kishinta.....amma yanaso ya cika mata wannan burin daya gani rubuce cikin qwayar idanunta.

"Come with me giiftii....."

"......You should stand beside the owner tonight."

Dukka gwiwoyinta suka sakeyin sanyi,bata da wannan qwarin gwiwar.....bata da wannan power din da zata iya tsaiwa kusa dashi a idanun duniya. Tana jin batakai ba....matsayinta baikai ba,komai nata baikai ba,sai tayi qasa da kanta.

"Na gode da wannan karramawar.....amma...."

"Is okay....ba buqatar jin dalili,zabinki ne....zan cika miki shi" Sai yaci gaba da takawa yana wucewa zuwa stage din a hankali.

"Tashin hankali" Omar.....shi kadai kalmar ta iya fita daga bakinsa,amma dukkaninsu hudun daskarewa kawai sukayi kowa ya gaza cewa komai.

Sautinsa kadai ya sanya kowa shiga cikin nutsuwa. Wannan muryar wannan husky voice din da kishinta ya cika zuciyar akhnan ta fara tashi cikin mic din daya karade ko ina.

Ya tsaya a tsakiyar stage din cikin nutsuwarsa ta al’ada. Power dinsa baya buqatar hayaniya. Silence kadai ya isa ya sa mutane su saurare shi. Wannan sunan THE SILENCE ONE.....ya matuqar dacewa dashi sama da duk yadda za'a kwatanta.

Tarihin gwagwarmayarsa da kafa kamfaninsa na farko....a hankali har zuwa yanzu inda qoqarinsa ya tsaya.

Ba mutanen dake zaune kawai a gurin ba.....hatta ita saida tarihin yaja hankalinta. An interesting story da yake dauke da wasu darussa kala kala. Nasara daya bayan daya.....jajircewa.....karbar qaramin matsayi ba tare da duba daga irin gidan daya fito ba,kawo yau yanzun nan da yake amsa sunan WANI.

"Before tonight ends......" Muryarsa ta sake ratsa tsakanin maganganun mutane ta kuma wanzar da wani irin shuru daya haifu lokaci guda.

"......there is one more thing" Sake daukan shuru hall din yayi.

Da wani irin nutsuwa ya sauke idanunsa akan akhnan din.

"Maison Akhnan was never built for business alone.” tsaiwa cak tayi itama da nata idanun cikin nasa,tana jin wani abu yana zagaya duniyarsa da tata.

"Some names carry value…” ya dakata yana ajiye numfashi.

“…and some names carry peace.” sai ya sakeyin shuru na second biyu muryarsa tana bada wani echo cikin hall din. Ya sake dauke idanunsa zuwa kan manyan mutanen dake gabansa.

"“Hers carried both.” ya furta kalmar yana maida idanunsa gaba daya a kanta.

Idanun nata ta lumshe a hankali tana jin wani irin yanayi. Nauyinsa.....qauna.....soyayya da tarin girmamawar da take ganin bata cacanceta ba.

Readers Also Read

More by Huguma