L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 57
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 57: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 57. Dukkanin hankula sukayi kanta,manyan baqi dama duk…
3,368 words
Dukkanin hankula sukayi kanta,manyan baqi dama duk wanda yake gurin,cameras din dai da bayaso da sauri kowanne ya maida tasa kanta. Wani babban labari ne.....wani babban al'amari ne da ba wata tasha da zataso ya wuceta.
Zazzafar soyayya a bainas nasi,kai tsaye.....daga bakin babban malamin nan na duniya gaba daya....yarima kuma sheikh muhammad haisam aba jifar.
Saidai cikin qasa da minti biyar dukka security din dake gurin suka sanya 'yan press saukar da cameras dinsu,dole kowa ya kasheta ya kuma sauke don samun ci gaba da kallo da idanunsu.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
A gurin....ji yakeyi kaman ita kadai dashi sune suka rage.... Gurin ya masa fili fayau.....ba wanda yake gani sai ita daya tallin tal. wani elegant black document legal director na kamfanin ya miqa masa cikin girmamawa,yasa hannu ya karba yana riqeshi da kyau.
A nutse ya fara saukowa daga stage din,straight zuwa gabanta.
"Haisammm" Bakinta yake furtawa sanda yake takowa zuwa gabanta. Shi daya ya gane sunanshi ta ambata saboda kalmar ta fita ne ba tare da sauti a cikin ta ba. Ya tsaya a gabanta,sannan ya rusuna saman qafafuwansa yana dora nauyinsa akan qafarsa ta dama.
"You once said this scent felt like memory.....uhmmm?" Ya tambayeta yana dage girarsa guda daya sama.
Idanunta ta lumshe.....ya ilahee.....komai da take boyewa,komai da take alkintawa cikin zuciyarta ya sani. Ya akayi?,garin yaya yasan komai game da ita?.
Tafin hannunsa ya bude mata saitin fuskarta. Ta dora idanunta a hankali tana kallon kwalbar dake ciki. Wata irin kwalba ta alfarma da bata taba ganin irin design din ba,wadda ke rubuce da LUNE NOIRE ✨.
Perfume din da tafi so a duniya ba tare da tasan sunansa ba. Luxury exclusive line.
"“You loved it long before you knew who created it.....haka ne?" Ya sake tambayarta wani lafiyayyen murmushi yana fita daga saman fuskarsa. Kasa amsa masa tayi,don gaba daya ya gama qone mata ruwan kai.
".....and now" Ya fada yana gyara tsaiwarsa tsugunnonsa a gabanta Yana qarashe maganan nasa da wnai slow pause
".....it belongs to you" .
".....what?" Ta fada tana fidda idanunta waje da wani razanannen mamaki.
Murmushi ya sake sauke mata.
"The scents" Sai ya dakata.
"The formula" Ya sake dakatawa.
"The ownership rights".
Girgiza kai tayi a hankali kamar bata fahimta ba.
"This is impossible". Ya fahimci rikicewa a tare da ita,sai ya sake rage tazarar dake tsakaninsu,wannan ya sanya security dinsa suka sake rufesu kaman yadda suka musu a dazu,muryarsu ce kawai ke fita.
Qasa yayi da muryarsa sosai,kamar da ita kadai yakeson yayi magana duka taron mutanen.
"No....."
".....Impossible is the effect you have on me.” ya fada da wani salo daya sare dukka sauran karsashinta.
A nutse ya bude folder din. Official signatures. Legal seals. Ownership transfer duka suka bayyana b'aro b'aro. Manyan shanyayyun idanun nan nasa ya daga ya dubeta
"As of tonight...." Sai ya dakata.
"LUNE NOIRE is yours". Wasu irin hawaye taji sun cika mata idanu.....wasu irin hawaye masu dumin gaske.....Ba saboda kudin ba. Sai saboda yadda ya miqa mata wani b'angare na empire dinsa kamar abu mai sauqi.
Ms ta masa?.....me ta mallaka masa?,me ta taba masa data cancanci wannan?. Kasa jurewa tayi.....tambayar ta mata tsaye a wuya,ta ware idanunta da hawaye ya fara jiqe eyelashes dinta.
"Why would you do this for me?” ta furta da wata tattausar murya dake nuna karaya sosai a cikinta.
"Because some things are too personal to sell to the world.” sai ya dakata kadan yana duban qwayar idonta data masa wani irin kyau,blue din ciki yau na dabanne.
".....wannan turaren"
".......ko yaushe yana tunamin dake.....yana tunamin tsada da darajar abinda na mallaka".
Hall din ya sake gaurayewa da qananun sowa. Gani suke kaman wani film suke saurara......duk da basa iya ganinsu,amma maganganunsu sun tsuma kowa. Mamaki ya daskarar da 'yan shidanshi,banda suna iya ganinsa zasuce wani haisam dinne daban.
Akhnan kuwa.....bata jin komai yanzu. Sai shi.......sai kalamansa......sai yadda ya d'ora sunanta a kan abin da duniya ke dauka matsayin luxury empire.
“…Ya bani fiye da dukiya…ya bani matsayi a rayuwarsa" Abinda zuciyarta ke maimaita mata kenan.
*_Wannan farinciki......wannan soyayyar da aka sake tabbatar da ita a gaban idanuwan duniya........wannan walwalar......cikin rashin saninsu......ashe K'ADDARA TANA SHIRIN WARGATSASU A WASHEGARIN WANNAN RANAR......BABBAN TASHIN HANKALIN DA ZAI GIGITA DUNIYARTA....SHIN ZAI ZAME MATA LU'U LU'UN DA HASKENSA ZAI HASKA MATA GABANTA?_*
*_LU'U LU'UN DA HASKENTA ZAI WALQA MATA ABINDA KE DUQUNQUNE CIKIN RAYUWARTA?_*
*_HASKEN WANNAN LU'U LU'UN ZAI ZAME MATA MAGANI?,ZAI MATA RANA?_*
*_muje zuwa da yardar me duka zuwa shafukanmu na gaba_*
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 102* ________________________
*_SHUWA INCENSE AND MORE_*
😊 *_kai daga jin sunan basai an gaya maka ba_*
*_kai daga jin sunan basai ka tambaya ko tsaya tunanin maganar me ake ba_*
*_MAGANA CE TA GIDAN QAMSHI_*
*BAFA GAMA GARIN QAMSHIN DA KIKA SABA JI BA HAJJAJU*
*KINA QONA TURARE YANA QAURI*
*KINA SAKA KHUMRA TANA BIN SHANUN SARKI*
*WANNAN DIN TURARE NE DAKE DAWWAMA A DAKI DA JIKI.....DA SALON QAMSHIN DAKE MANTAR DA ZUCIYA DUK WANI B'ACIN RAI*
*TASTED AND TRUSTED👌👌👌100% HAJJAJU*
*NA DABANNE A CIKIN NA DABAN*🙌🏽🙌🏽
*idan akazo kan SHUWA INCENSE an tashi magana*
*idan ma kinsan baki shirya jan magana ba a duniyar qamshi to kisha zamanki hajajju*
*_zaku iya magana da ita kai tsaye ta wannan number wayar_* +234 704 229 3387 _________________________
D'aya bayan d'aya suke shigowa daya daga cikin empty suite din da ya sanya aka ware saboda su cikin Atlantis the royal hote din.
Omar ne a gaba.....wanda ya zare blazer dinsa ya jefar
"No" Omar ya fada da wani abu cikin muryarsa me nauyi.
"Absolutely no" Ya sake fada yana sauke idanunsa akan haisam wanda ke takowa cikin suite a gajiye rungume da suite dinsa 'yar saman.
Idanunsa ya dauke daga kan omar yana zama saman daya daga cikin sofas din dake zagaye da qawataccen parlor din. Ba omar kawai ba,tunda suka taho duk da a mota daban daban suka taso,kowa cikin tasa motar amma yana lura da irin kallon da suke binsa dashi.
Agogonsa ya fara zarewa kafin ya amsawa omar.
"What now?".
" Wallahi bakai bane" Naseeb ya karba wannan karon da wani expression na mamaki akan fuskarsa.
"This is getting serious fa?" Khadeem ya fada yana yarfa hannunsa shima mamaki kwance akan fuskarsa.
A nutse ya ajiye agogon,ya koma yana sassauta tie dinsa gami da bin kowa da kallo d'aya bayan d'aya.
"I warned you people....." Maleek daya bude wani gwangwanin lemo ya fada yana qoqarin boye dariyarsa,ya zuqi lemon sannan ya qarasa maganan daya fara
".....love humbles men violently" Dariya suka sanya gaba dayansu,suna tafawa a tsakaninsu. Sai a sannan ya jefawa maleek din harara yana dubansa.
"Be quite" Ya fada idanunsa suna lumshewa saboda gaiiya. Bada murya me amo yayi maganan ba,amma a halittarsa ce.....muryarsa tana fusgar hankalin duk wanda yayi magana dashi koda cikin hayaniya ne.
"Haisam" Amjad ya fada yana dawowa gabansa ya zauna yana dubansa sosai....kamar wani me daukan karatu.
"You adjust akhnan's chair today?"
"And you adjust her bracelet?" Khadeem ya fada.
"Ko blinking bakayi.....hala baka sani ba....duk wani motsinta yana under control naka....." Mutallab ya fada yana fidda idanunsa waje.
"......ga wata irin gabatarwa.......ka gabatar da wannan soyayyar a inda ya dace" Naseeb ya fada yana girgixa kai.
"Mu masu aure.......two years ago.....sai naga kaman bamu iya komai ba.....bamusan komai bama ashe" Naseeb ya fada yana watsa hannuwansa fuskarsa tana komawa kalar tausayi.
Murmushi ya subucewa haisam din....wani kalan sassanyan murmushi. Ya juya kansa kadan yana dubansu.
"You people are overreacting" Ya furta softly yana kallon agogon hannunsa. Tun a gurin ya barta da baqi mata bai kuma sake ganinta ba,saidai ya tabbatar tana under security guard,ba wani abu da zai sameta. Har yanzun da suka sashi a gaba da wannan kalar tsiyar tasu ita yake gani. Sanda take karbar baqi mata a matsayinta na matar mamallakin kamfanin.....kuma shugabar sabon kamfanin da ya zama mallakinta a daidai lokacin da kowa baiyi zato ba. Yadda take tafi da komai cikin tsari da nutsuwa,duk da baiyi mamaki cancan ba sai burgeshi da yanayinta ya sakeyi ya kuma sake dilmiyashi a kogin qaunarta.....ko ba komai yasan ta taba zama.shugabar wani kamfanin samar da suturu na alfarma.
"Ko ba overreacting ba?" Omar ya fada mamakin haisam yana sake kasheshi. Har yanzu yana jin komai ne kamar mafarki,har yanxu ya kasa gasgata hakan.
"......hmmmm,this from the man who Once said....." Maida muryarsa yayi wani iri yana qoqarin kwaikwayon muryar haisam.
"Women complicate focus...." Dukkansu sun tuna,magana ce da yake yawan maimaitata.
"And now look at you....." Khadeem ya fada
"Your focus literally wearing laffaya".
Murmushi ne ya subucewa haisam yana sake relaxing cikin sofa din. Maganan lafayar ya sanya ya sake hangota a wancan awannin cikin baqar lafayar data maidata wani yare na daban. Ta Maidata wata mace ta daban da baka isa ka iya cankar qabilarta ba. Ya yarda d'ari bisa d'ari BUZUWA daban take....buzuwar ma irin tasa.....irin tasa d'iyar sultane Muhammad hammud.
Shurun da suka sakeyi suna kallonsa bama baisan sunayi ba.
"No" Omar ya fada yana girgiza kai....omar din da haisam din yafi shayar dashi mamaki akan kowa.
"He's gone wallahi.....he's gone." Ya fada Omar yana yamutsa sumarsa kamar dan wasan qwallon da aka cinyeshi a wasa.
Kusan wasan ya koma tsakanin haisam da omar din,yadda omar din ya gigice yasa suka fahimci shi kadai yasan me ya gani tattare da haisam din aka MATA sama da abinda suka sani. Gaba daya setting room din ya rude da dariya
"Welcome to marriage sheikh haisam" Maleek da shi ya riga yasha ta hudashi ya fada. Dama irin wannan ranar,....irin wannan lokacin yake jira daga haisam din.
"It's not marriage...." Ya amsa calmly yana jin yadda shauqin son ganinta yake ratsashi.
"It's her....." Wani irin ihu suka sanya gaba daya,har omar da zuwa yanzu dariyarsa ke bayyana sosai.
"Finally...." Khadeem ya fada kaman me calling attention dinsu. Shuru dakin ya sake dauka kuwa.
"Now.....explain your self" Murmushi ya sake subuce masa,sai ya miqe ya zauna sosai yana dubansu daya bayan daya.
"I'm not explaining anything".
"Wallahi zakayi kuwa" Mutallab ya fada yana nunashi da yatsa.
"Yes.....ya kamata....don ka fola da yawa billahi.....not just smiling fa.....BRO WAS STARRING" Ya fada yana kaurara muryarsa da buda hannuwansa kaman me shirin kama wani abun.
Wani irin dariya maleek yakeyi sosai,har yana sunkuyawa. Shi ya sani.....yana da falaak a gefansa,ya sani muddin akhnan din jinin falaak ce.....dole haisam ya zauce.....dole ya zauce babu ko makawa.
"He has entered the dangerous stage fa....."
"......the my wife stage" Omar ya qarasa yana sake qoqarin kwaikwayon muryar haisam din again.
"Women are unnecessary emotional responsibilities.” omar ya sake fada da yanayin muryar haisam din.
Ya gama fahimta,kawai sun hadashi a nan ne saboda suyi masa titsiye. Ba wannan yanzu yafi buqata ba. Hutu....hutawa yakeso yayi.....so yake yaji duminta,so yake ya jita a gefansa. A yau yadda jininsa ya tsinke dinnan sosai,ya sani zaisha wahalan bacci....zaisha wahala kafin ya iya dauke mata ido a yau. A kwana biyar din daya qyaleta shi kadai yasan yadda yake surviving.
Miqewa yayi abinsa yana riqe da rigarsa.
"I hate all of you" Ya fada a kasalance yana soma takawa.
"No....you loved one person" Sai suka sake saka dariya.
Khadeem ya nutsu zuwa serious.
"But seriously....." Ya tsaya kaman yana nazari.
"......I’ve never seen you this relaxed around anyone.”. Shuru dakin ya dauka,don dukkaninsu kaman tambayar tana ciki kawunansu ne.
A karon farko,da fidda dukkanin gaskiyarsa.....bawai kare kai ba,ya jingina da bangon da yake daura dashi,idanunsa sun zama soft sosai,ya motsa labbansa da nutsuwar nan tasa.
"She makes noise in my head disappear.” sake shuru dakin yayi. Saboda ko su sun san wannan magana tana da nauyi coming from him.
“You people are witnessing the downfall of a proud man.” maleek ya fada yana satar kallon haisam yana boye dariyarsa.
"Maleeekkkkk"
"Sorry babban yaya.....tuba nake" Maleek ya fada da sauri yana surrender.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Matse qwalla omar ya hau yi,duk da na wasa ne amma yayi calling attention kowa.
"Our emotionally unavailable Sheikh has fallen.......khadeem muna da meeting.....dole mu nemi aure" Dariya ta kaure gaba daya a dakin,haisam ya kaiwa omar cafka saiya zille.....sai kawai ya bude qofar yana fita yana bar musu dakin.
*A K H N A N*
Rudewa......mamaki......da shiga shock sosai su shehnaz sun yishi. Yadda suke juya zancan tun daga fitowarsu bayan kammala komai da sallamar tarin investors din dakeson magana da ita tace sai tayi shawara da mijinta duk tana jinsu.
Itadai abu daya ta sani,da gaske komai ya tashi daga mafarki zuwa gaske. Shin akwai wani sauran abu yanzu daya rage daga haisam wanda bata sanshi ba?.
Wanne irin mutum ne shi me abun mamaki?. Me yasa ya zabi ya boye mata komai?. Me ta bashi a duniya.....me ta mallaka masa data cancanci wannan kyautar?....wannan girmamawar?,.....wannan kambamawar?.
"DAME ZAN SAKA MASA?" Tambayar data rasa amsarta kenan,saidai a hankali maganganun aisa suka zame mata kamar wani tsani.
"Akhnan......baki da masoyi a yanzu sama da sheikh haisam.....ba don ya mallaka miki dukiya ba,saboda soyayyarki a idanunsa daban take da wadda aka saba gani. Baki da wani abu da zaki bashi akhnan a yanxu.....saidai ki soshi.....kici gaba da sonshi......ki riqeshi ki bashi kulawa. Ki kiyaye mutuncinsa....ki faranta masa.....ki sallama masa kanki.....ki miqa masa komai naki. Kin tsinci LU'U LU'U a cikin juji......kina dab da yasar dashi sultane ya cafe miki shi. Kin kalleshi kina mamakin alfanun da wannan abun me datti zaiwa sultane.....ashe shi ya fuskanci lu'u lu'u ne. Sai yanzu daya wanke mikishi tas.....sannan kimarsa ta sake fita" Ta yarda da maganganunsu d'ari bisa d'ari......amma a yanzun abinda ke damunta shine. Ta yaya zata aminta da haisam ta gamsar dashi d'ari bisa d'ari take sonsa. Ta yaya zai fahimci don Allah take sonsa badon dukiya ba?. Ba don abinda ya mallaka mata ba?,ba don shi din a yanzu wani bane?.
Wannan ne ya dameta,bata jima a sassan baqi na residence din ba tabarsu dasu Aanani ta wuce suit dinsu din tace kanta ciwo yake mata.
Wanka tayi wai ko zataji sassauci cikin ranta. Ranar farinciki ce a garesu da dukkan me qaunarsu amma wani karyewar zuciya takeju da wani irin weakness. Haka kawai taji kuka takeson yi,saita koma a hankali ta zauna bakin sofa bed ta soma rera kukan.
Tana tuna komai data masa a baya.....maganganunta.....raininta da izgilinta. Ta yaya zai gamsu da ita cewar da gaske take?,ta yaya zai fahimci komai ya fara kafuwa a zuciyarta tun kafin tasan komai game dashi.
A hankali ya bude suit din nasu da sallama a labbansa kamar yadda ya saba. Duk inda zai shiga,koda ba mutum to zaiyi sallama. Kai tsaye yake takawa yana wucewa cikin dakin yana sake jin shauqin isa gareta kamar ana fusgarsa.
Sanda ya buda qofar.....idanunsa suka sauka a kanta sai yaji wani abu ya tsaya masa cak
"Kuka?" Ya fada a hankali,saidai kuma sautin ya isa kunnuwanta. Share fuskarta ta fara yi da sauri,bataso ya gani,batason wani abu da zai b'ata wannan mode din nasa,batason wani abu da zai ware wannan farincikin da take gani shimfide saman fuskarsa.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 103* _________________________ https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0
*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*
*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*
*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*
*_Assalamu alaikum my loyal people_*
*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*
*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*
*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*
*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*
*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*
*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*
*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*
*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*
*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee* __________________________
"Nothing" Ta fada da wannan jaririyar muryar tata me taushi.
Qofar ya rufe a hankali sannan ya tako cikin nutsuwar nan tasa. Tun kafin ya qaraso,dukkanin kulawarsa da idanunsa suna kanta.
A nutse ya qaraso gabanta,ya kuma tsugunna saman qafafunsa yana riqo hannayenta.
"Me ya saki kuka?" Ya tambaya a tausashe yana bata dukkan kulawarsa da hankalinsa. Da sauri ta girgiza kai,amma hawayen da suka sake zubowa sai suka qaryatata.
Miqewa yayi a tausashe,ya bata hannuwansa dukka ya dagata daga kan sofa din ya maye gurbinta,sannan ita din kuma ya azata saman cinyarsa. Dararewa kadan tayi saboda guntun towel ne kawai daure a jikinta,amma saita lura hankalinsa ma baya gurin. Hannunsa ya miqa ya tattare mata gashinta zuwa gefen kafadarta daya.
"Hey" Ya fadi ganin yadda take qoqarin hanashi kallon qwayar idanunta.
"Talk to me" Ya sake fada da wani irin laushi a muryarsa dake fita can qasa.
Papers din kamfanin dake ajiye saman dressing table din dake gabansu ta kalla,sannan ta dawo da dubanta kansa.
"Me na taba yi maka a rayuwa?" Ta tambayeshi kanta tsaye,blue eyes dinnan nata cike fal da hawaye.
Girarsa yadan hade kadan yana duban fuskarta,amma hakan bai hanata ci gaba da magana ba,don tanajin kamar taso kanta da yawa.
"Wanne irin alkhairi na taba yi maka.......da zan cancanci wannan girman?".
Shuru haisam yayi,kallon da yake mata yanzu ya sauya gaba daya. Wani irin zuzzurfan kallo me cike da taushi .
" Na taba rainaka fa...." Ta fada da rauni sosai a muryarta hawayenta suna sauka saman kuncinta
"......na taba fahimtarka ba daidai ba...." Ta fadi tana sauke idanunta qasa kunyarsa tana cikata.
"Amma kuma kai...." Ta sake fada tana motsa labbanta a hankali.
".....ka bani kuma kana sake bani abubuwan da ban isa nayi mafarkinsu bama".
Idanunsa ya lumshe a hankali sannan ya budesu kamar maganganunta sun taba wani guri me zurfi a zuciyarsa.
Hannunsa dukka ya sanya yana zagayeta ta gefan cikinta,idanunsa sun sake laushi sosai,qamshin jikinta daya cakude da qamshin shower gel dinta har yanzu suna tashi da wani irin sassanyan yanayi dake assasa wani feelings me matuqar qarfi a dukkanin jikinsa.
"Look at me" Ya fada da wani irin laushi. Idanunta ta daga masu jiqe da hawaye,hawayen da suka jiqa dogayen eye lashes dinta suka sanyasu sukayi wara wara tare da nuna ainihin tsahonsu.
Babban yatsantsa ya sanya yana dauke mata hawayen softly,yana yi yana sake qarewa kyakkyawar fatarta kallo me wani irin sulbi sheqi da daukan hankali.
"“You think too little of yourself ko?" Ya fada yana dage mata dukka girarsa. Girar data burgeta ainun yadda take a cike da baqin gashi,gata dab da ita kuma a yau tana kallon yadda Allah ya qera masa ita da kwantaccen gashin da suka kusa hadewa da juna.
"Ba sadaka na baki ba...." Ya fada a nutse