L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 58
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 58: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 58. "......i just honored my wife" Cak numfashinta ya…
3,372 words
"......i just honored my wife" Cak numfashinta ya dakata na wucin gadi. Kalmar MY WIFE din tana sauka saman zuciyarta da wani irin nauyi da kuma kima me yawan gaske.
"A cikin wadannan....." Ya sake fada da wata nutsuwa cikin kalamansa da maganarsa.....ya fada din kuma yana maida idanunsa kan takardun dake gefan.
"None of this is bigger than your value to me" Me zatayi?,bata sani ba itama,sai kawai ta dora hannunta saman bakinta tana fidda idanunta waje. Zuciyarta na wani mahaukacin bugawa tana neman rasa control dinta.
"You look shocked" Ya furta yana murmushi gami da lumshe idanunsa. Yadda ta zare dukkan blue eyes dinnan a kusa dashi haka,sai yaga ta masa wani mugun kyau.
Wani raunannen murmushi daya taho hade da kuka tayi
"...Because nobody has ever treated me like this before.....sai sultane.......sultane kawai".
Kansa ya jinjina a hankali,yana jin cewa koda bai ture sultane ba.....ba shakka shine zai zama mutum na biyu da zaici gaba da girmama rayuwarta har haka.
Wani irin taushi da tausayi take gani nata a idanunsa,amma har yanzun tana jin kamar bata samu amsarta ba,akwai abinda takeso ta sadaukar.....akwai abinda takeso ta saka masa dashi,ta tattara dukka dauriyarta ta sake cewa.
"Me kakeso daga gareni?"
Girarsa ya sake dage mata yana dubanta.
"Me kike nufi?" Ya mata wannan kwarjinin daya saba mata,saita sauke kanta a hankali. A yau ta quduri aniyar masa wani abu sabo.....wani abu da zai tambayi kansa AKHNAN ce?. Saita miqa tafin hannunta a hankali tana shigar dashi cikin nasa tafin hannun. Idanunsa ya sauke a hankali yana kallo. Yadda ta hade tafukan hannunsu guri guda,yatsunta suka samu cikakken gurbi cikin nasa yatsun kamar tare aka haliccesu. Wani irin feeling ya ratsashi sanda ta matse yatsun nasu gam cikin na juna.
"Ka bani girmamawa...." Ta fada muryarta tana rawa.
"Ka bani kulawa......"
".....sannan ka bani abubuwan da ban taba tsammani ba" Sai ta danyi murmushi me ciwo kadan.
".....to ni kuma?"
".....me zan saka maka dashi?".
Shuru dakin ya sake dauka.....wani irin shuru da bai bar komai ba sai dubai light dake walqiya ta sakanin curtains na dakin da skyline view din dake bude.
Haisam ya zuba mata idanu quietly. Wani irin kallo mai nauyi. Kamar yana kallon abu mai daraja da baya son ya subuce masa.
"You already give me more than you realize.” ya furta da muryar rad'a. Kai ta girgiza da sauri
" Aah....."
".....wayo ne wannan......ban kuma yarda ba" Ta fada da wata shagwaba data kusa narkar dashi ya sulale yabi kujerar.
Komawa yayi baya ya jingina da fuskar kujerar yana neman tallafinta.
"You really want to know?” ya tambaya da low voice dinsa. Kai ta gyada a hankali da baby face dinnan nata dake jin rigima sosai. Sai ya danyi shuru,kafin muryarsa ta sauya,Lower and softer.
"When I come back tired…” idanunsa still a cikin nata idanun
"…look at me the way you’re looking at me now.” sai numfashinta yadan tsaya,saboda yadda ta kulle idanunsa cikin nata.
"When the world becomes loud…” ya saki wani miskilin murmushi daya qara masa kyan da taji kaman zai kasheta.
"…be the place my mind rests.”. Hawaye kawai taji sun cika idanunta. Saboda yadda yake magana,ba kamar mai neman abu daga gareta ba. Kamar mutum ne da ya samu nutsuwa a wajenta ta har abada.
Dawowa yayi ya zauna sosai yana hade gap din dake tsakaninsu.
"And......" Kalmar ta sakata sake.maida qwayar idanunta cikin nasa.
".....love me honestly....." Ya qare da fadin
"......that's all".
Wani nauyi me dadi zuciyarta tayi mata. Wata irin soyayya ce ke mamayar kowanne sashe na jikinta.
" Haisamm" Ta kirashi da sound da kuma sunan data lura yana qaunar ji daga bakinta.
"Yes ma'am" Ya fada yana kasa jurewa sai daya cusa yatsunsa tsakiyar cinyoyinta biyu yana shimfide tafin hannunsa a kansu gami da sarqe idanunsa cikin nata.
"“I think… you’re spoiling me.” ta qwato kalmar da qyar saboda yadda ya soma yamutsa fatar cinyarta a hankali da wani irin yanayi me tada tsigar jiki.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Good......“That was the intention.” ya fada yana sake nutsa jikinsa a nata idanunsa na sauka kan towel din daya soma zamewa daga qirjinta.
Maida idonsa yayi fuskarta,still staring at her kamar babu wani abu a duniya da yake son kalla fiye da ita a wannan lokacin.
"Khadeejah nah" Ya kirata da wani sound dake nuna zallar mallaka. Sake kusanta kanshi yayi da ita,abinda ya saka zuciyarta bugawa sosai fiye da dazu,saboda yadda suke musayar numfashi da qamshin jikinsu shi da ita.
"Akwai abinda nakeso ki fada....." Shuru kadan
"Look at me when you say it......kice kina sona khadeejah" Sosai kunya ta rufeta,tana jin kamar ba zata iya ba. Sai ya dan langab'ar da kansa kad'an. Wancan soft needy side dinnasa yana fitowa.
"Yes you can" Ya fada yana dago habarta zuwa fuskarsa sosai
"I want all your attention on me.” ya furta da wani laushi daya sanyata sake kallon idanunsa ba tare data shirya ba.
"Good.....then say it" Ya fada da muryar rad'a sautinsa yana dakushewa kaman yadda mutumin da zaiyi rada yake magana.
"With your eyes on mine.” ya sake fada da rad'ar dai.
Numfashinta ya fara rawa,saboda yadda yake kallonta kamar kalmar zata zama abu mafi muhimmanci da ya tab'a ji.
"I......" Saita kasa qarasawa,hannunsa dayan yasa ya shafi gefan fuskarta yana sake maida mata gashinta gadon bayanta.
"Take your time" Ya fadi idanunsa suna lumshe kansu da budewa.
Ta hadiye wani abu a maqoshinta,kafin daga bisani ta tattara dukka qwarin gwiwarta,ta kuma sanya idanunta cikin nasa.
"I love you....."
".....ina sonka haisam" Ta fada tana rarrabe kalaman.
Wani abu ya sauka a zuciyarsa a hankali da wani irin sanyi,duk expression din fuskarsa ya sauya. Wani deep softness ya bayyana a idanunsa,kamar mutumin da ya ji wani abu da zuciyarsa ta dad'e tana jira jinsa tsahon shekaru.
Ya rufe idanunsa na sakanni kad'an,kafin ya jingina goshinsa da nata.
"…Again." Ya fada da muryar rad'a data zarta can qasan maqoshinsa.
"I love you"
"Again" Ya sake fada da wani strong emotions
"I love you"
"Again" Ya kuma buqata.
"I love you" Ta sake maimaita masa.
"Again" Ya kuma cewa yana jin wata irin yunwa tajin kalmar daga bakinta.
"I love you" Ta furta zuciyarta na karyewa da wata irin matsananciyar soyayyarsa.
"Again" Ya sake fada jikinsa yana daukan wani yanayi daya sanya ya fara rawa kamar me jin sanyi.
"I love you" Ta sake maimaitawa itama tana jin kamar tana rasa control dinta.
"Again....please khadeejah" Tata juriyar ta soma yin rauni,saita aza tafukan hannayenta saman nasa da yake riqe da fuskarta.
"I....love you haisam"
"Again" Ya sake fada yana zabura gami da daukarta cak daga saman cinyarsa zuwa saman gado.
"I love you" Ta sake fada tana lumshe idanunta. Zuciyarta tana wani irin bugawa......sannnan tana sake cika da fargaba.
Tana jinsa.....sanda ya soma haukace mata. Tana jinsa sanda yake bata haquri.
"Yau...zan sake karya alqawarin nanay.....yau bazan iya jira ba biftuu.....bazan iya jira ba my healer.....saikin bani maganin nan.....bazan iya cika alqawarin nan ba yau" Riqeshi tayi sosai,labbanta suna rawa.....amma itama yau tana jin ta shirya fattatakar wannan tsoron.
"Na mallaka maka...kaina......komai nawa....naka ne. Daga yau....ko zan mutu bazan sake hanaka ba.....kayi duk iya yadda kakeso" Tayi maganan da tarin jarumta tana qoqarin binne wannan tsoron.
"Na gode....thank you" Da sauran godiya a yaren oromo da French batasan adadin sau nawa ya furta ba.
Wata irin duniya suka cilla ita dashi.....wata irin duniya dake gusar da hankalin dukka me hankali,sannan ta gusar da nutsuwar wanda yake tutiyar shime nutsuwa ne. Duniyar da ba'a gane komai cikin ta sai abokin tafiyarka zuwa wannan duniyar.
Ta lafe kawai cikin qirjinsa kunya na fattatakar ta. Mamaki kuma yana kusan kasheta. Ya akayi komai yazo da sauqi ba kaman wancan lokacin ba?. Wanne tsatsuba da sihiri ya mata daya sanya ta fita daga saitinta tayita sauka daga kan layukan da sai yanzu take tuna komai?.
Wata irin nutsuwa ce ta mamaye dakin,sai wannan hasken na dubai skyline dake ratsowa da glass din dakin.
Fuskarta na boye cikin qirjinsa,hannayensa suna zagaye da ita kamar wanda baya buqatar ko iska ta raba tsakaninsu.
A nutse ya sumbaci saman kanta.
"You okay?" Ya fada softly,kanta ta gyada kadan ba tare data daga fuskarta ba daga ni'imtaccen qirjin da takejin duk duniya ba inda yakai mata nan nutsuwa. Murmushi ya saki kadan,yana dan mintsinar mata kumatu. Yar qaramar qara ta saki,ya sake sakin murmushi,kunyar nan tana burgeshi matuqa. Yau din rana ce ta musamman,rana ce ta daban data miqa masa dukkan komai,yayi yadda yakeso....har yaso ya wuce gona da iri,shi kansa yasan hakan.
"Still shy?" Ya fada cikin nutsuwa yana leqen fuskarta. Sake boyewa tayi sosai tana murmushi me cike da kunya.
"Don't look at me" Matseta yayi kadan cikin jikinsa yana sakin siririyar dariya cike da nishadi
"Too late" Ya furta da tsokana a sound dinsa.
"......I've been looking at you all night" Wani siririn kukan shagwaba ta sakar masa tana sake narke masa,shi kuma ya lalace da tarairayarta da lallashinta bilhaqqi da gaske.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 104* _________________________ *_SHUWA INCENSE AND MORE_*
😊 *_kai daga jin sunan basai an gaya maka ba_*
*_kai daga jin sunan basai ka tambaya ko tsaya tunanin maganar me ake ba_*
*_MAGANA CE TA GIDAN QAMSHI_*
*BAFA GAMA GARIN QAMSHIN DA KIKA SABA JI BA HAJJAJU*
*KINA QONA TURARE YANA QAURI*
*KINA SAKA KHUMRA TANA BIN SHANUN SARKI*
*WANNAN DIN TURARE NE DAKE DAWWAMA A DAKI DA JIKI.....DA SALON QAMSHIN DAKE MANTAR DA ZUCIYA DUK WANI B'ACIN RAI*
*TASTED AND TRUSTED👌👌👌100% HAJJAJU*
*NA DABANNE A CIKIN NA DABAN*🙌🏽🙌🏽
*idan akazo kan SHUWA INCENSE an tashi magana*
*idan ma kinsan baki shirya jan magana ba a duniyar qamshi to kisha zamanki hajajju*
*_zaku iya magana da ita kai tsaye ta wannan number wayar_* +234 704 229 3387 ___________________________
*W A S H E G A R I*
Tana zaune daga bakin skyline view din,sanye da wata cotton gown me dogon hannu,budaddiya me zuwa hade da wani irin tattasau mayafi. Gabanta cup ne dake dauke da coffee wanda ke fidda tururi a hankali. Fuskarta tayi wani irin fresh,tayi kyau,tana jin gajiyar taron da wadda haisam din ya hada mata daren jiya tana sauka daga jikinta a hankali.
Saidai kuma can qasan zuciyarta.....can cikin ruhinta sam ta rasa walwalar data dauka zata tashi da ita.
A cikin jikinsa jiya tayi mafarki,mafarkin daya razanata matuqa. Taron jama'a anata kuka,sultane yana tsaye a tsakiyarsu sanye da fararen kaya yana lallashin kowa.
Shi ya riqeta a jikinsa sosai harta samu nutsuwa,ya karanta mata addu'ar da akeyi idan akayi mummunan mafarki ta maimaita,ya hanata ta gaya masa me ta gani saboda haka sunna ta koyar,saidai ya sanyata ta shiga toilet ta sake alwala ta dawo ta canza side din data kwanta dazun kamar yadda annabi ya koyar.
Yanzun mafarkinne ke mata yawo cikin kai. Ya lura da yanayinta,shi yasa yau ko suite din nasu bai bude ba. Ya hana kowa ganinta,shiketa hidima da ita har mamaki da nauyinsa yana kamata.
"Kaman ba wannan sheikh muhammad haisam din na duk duniya ba". Ko coffee din dake gabanta yanzu shi ya hada mata,ya kawota nan wani guri na musamman me kama da farfajiya daga gaban benan nasu ta zauna tana hangen gine gine qananu daga qasa. Taga saqon falaak kan sun wuce ita da maleek,bata zaton su shehnaz sun wuce don jirgin yamma kamar zasu bi.
"Hello princess" Taji ya fada da muryar nan tasa da take mutuwar so. Idanunta ta dauke daga inda take kalla da zummar dubansa,amma kunyar daren jiya ta hanata,saita buge da sauke idanunta akan wayarta,sanda yaja kujerar dake opposite din tata ya zauna.
Girarsa ya dage mata dukka biyun dake nuna alamun tambaya. Kai ta girgiza masa a hankali tana sauke qwayar idanunta,
"Ina zuwa" Yace yana miqewa a nutse.
Cikin nutsuwa ya shiga dakin,ya jawo locker din da yayi ajiyar tun a jiya,yana jiran lokacin daya dace ya sake mallaka mata ita a matsayin kyauta. Saidai kuma yana kai hannunsa wayarsa ta dauki qara. Fasawa dauko qaramin akwatin yayi.....yayi taku biyu baya yana kallon wayar dake saman bedside.
"Ahmad?" Ya furta sunan kamar wanda yake mamakin ganin kiran nasa. A nutse ya taka ya koma ya dauki wayar,sannan ya zauna saman sofa bed din,idanunsa akan wayar tana nuna masa lokaci na qarshe da sukayi waya da ahmad din. Ajiya ne,sanda yake kan hanyar dawowa ya dauki akhnan zuwa taron.
Sunyi maganan jikin sultane da yake sake tsanani,ya kuma aike da likita na musamman qwararre da zaici gaba da bashi kulawa,yace da ahmad din.
"Idan sati daya ya wuce babu sauyi.....inajin zan laluba qasar da zata iya kula dashi a fita dashi can" Wannan shine plan dinsu na qarshe kuma maganarsu ta qarshe da ahmad din.
Sallama ita yake fara yi a duk wayar da zai amsa....saidai a yau sallamar tasa ta tsaya cak ba tare daya iya qarasata ba sanda muryar ahmad ta mamaye kunnensa.
Muryar dake cike da wani irin nauyi da rauni dake nuna tazararsa da sakin kuka kadanne.
"Sultane ya rasu.....sultane ya mutu" Shine saqon da ahmad ke fada masa da wata irin muryar dake cike da kakkarwa da saarewa.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shine kalmar data fita daga bakinsa yana jin wani abu yana hargitsewa cikin kansa. Baisan waye ya kashe kiran ba.....shi ko ahmad din,yadai kalli wayar yaga ahmad baya kan layi.
A hankali wayarta dake gabanta ta dauki ruri,abinda ya maido da hankalinta kenan kan wayar. Idanunta suka sauka akan sunan dake yawo saman screen din.
"Mammina?" Ta furta sunan kamar wadda bata taba ganin sunan a rayuwarta ba sai yau,
Tasha kiranta.....amma sanda suka isa Ethiopia,tarin miscal dinta na kwana da kwanaki wanda bata tana biba. Amma a yau,hakanan taji tana muradin daga kiran.
Ta daga kiran sanda take hango haisam daga can qarshen balcony din yana takowa da dan nisa kadan a tsakaninsu,duk da a nesa yake amma hankalinsa yana kanta. Ta danna kore.....koren da dannashi ya juye mata zuwa jaa.
"Yanzu kinji dadin rayuwarki akhnan?......" Kalmar data fara fitowa kenam daga muryar mammina.....kalmar da akhnan din ta jita da wani irin nauyi ba tare da taji komai daga bakinta ba.
"Me?" Ta jefawa mammina tambayar haka kawai tana jin zuciyarta na wani irin bugawa kamar zata rikito daga qirjinta. Shuru ne na second daya....shuru na second dayan da akhnan ta jishi kamar yana daidai da shirun shekara dubu.
"Babanki ya mutu akhnan.....sultane ya mutu!" Ta fadi da wani irin qarfi a muryar ta,qarfin da zai gaya maka da anihin zuciyarta yake fita.
A karon farko da maganan ta dinga gutsirewa tana shiga kanta a hankali......tana samun mazaunai iri daban daban cikin kanta tanason zama tare da son isar da saqon inda ya dace yaje.
"Karya ne" Amsar data samu kenan daga zuciyarta,amsar da taji tafi gamsuwa da ita,ta kuma zabi tayi aiki da ita.
"Me kika ce?"
"Nace gatanki ya fadi.....ba sultane....sultane ya mutu!" Ta sake maimaita mata kai tsaye.
"....sultane ya mutu a sanda kike can yawo a dubai,kina shaqatawa da more rayuwarki ba tare da kin damu kizo kiga jikinsa da lafiyarsa ba.....sultane ya mutu sanda kika zabi miji....kika zabi yawon duniya akan ganinsa....qasa qasa"
"Aah mammina!" Akhnan ta fada a tsawace tana jin yadda zuciyarta ke bugawa kwanyarta kamar zata haukace.
Wata siririyar dariyar raini ce ta fito daga gefan mammina.
"Yanzu kika tuna kina da uba?.....ki dawo kiga gawarsa idan har kina da sauran mutunci da qauna tsakaninku" Sai mammina din ta fashe da kukan da yabar sautin cikin kunnuwan akhnan.
Zare wayar tayi a kunnenta,dukkanin ilahirin jikinta yana bari. Number ahmad take nema,shi kadai takeson kira don taji ta bakinsa.....ta bakinsa takeson tabbatarwa,sai taji kawai an zare wayar daga hannunta.
Haisam ne tsaye a gabanta,wanda batasan yaushe ya iso ba,batasan yaushe ya qaraso ba,amma tana hada idanu dashi abinda ta gani cikin qwayar idanunsa sai taji kamar yana ce mata.
"Da gaske sultane ya mutu"
"Haisam.....abbana......abbana ko?" Ta fada tanason samun amsarta ta idanunsa.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Bayaso taji ko taga komai daga gareshi. Bai taba rasa iyayensa ba.....amma ya sani duk wanda zai gaya maka wannan labarin ba zaka taba manta fuskarsa sunansa da muryarsa ba.
Da gaske mammina ta isa ta amsa sunan MAQIYIYAR SAFEENA.....tunda ta zabi kaf fadin agadez ta zama ta farko da zata gayawa akhnan din babban rashi da faduwar babbban bango daga rayuwarta?.
"Bappi na....haisam bappi na" Ta sake fada tana jijjiga hannun haisam dake tsaye kamar wanda tunaninsa ya tsaya gaba daya da aiki.
"Bappi...." Ta fada da wata murya data tsayewa haisam cak a zuciya da kunnuwansa.
Qarfafar kansa yayi ya taka a nutse yana hade tazarar dake tsakaninsu,ya rungumeta sosai cikin jikinsa zuciyarsa na wani irin bugawa,ya riqe kanta sosai a tsakiyar qirjinsa.
Wani irin gigitaccen kuka ta saki,iya bugun da zuciyarsa takeyi ya isa ya amsa mata tambayarta,iya shurunsa ya isa ya gaya mata ya sani....an gaya masa bappi ya mutu,saita sanya hannunta da suke rawa gaba daya ta cukuikuye rigarsa.
"Haisam......bappina.....bappi na ya mutu" Ta sake maimaitawa da madaukakin sauti.
Cak numfashinta ya dauke daga gangar jikinta,dukka wani qarfi ko garkuwa ta jikinta ta soma kakkaryewa.....qafafunta suka lanqwashe suka gaza daukarta saboda tsaiwar numfashi da kuma wani abu me kama da ficewar ruhi daga gangar jikinta.
A razane ya mata wani irin kyakkyawan ruqo cikin jikinsa yadda ba zata fadi ba. Karon farko da wani abu ya sanya gabansa faduwa......wani tsoro kadan ya shigeshi,yadda jikinta gaba daya da tafukan hannayenta sukayi wani irin sanyi.
Fuskarta ya riqe da sauri cikin hannunsa,girgizata yakeyi sosai muryarsa tana sauyawa completely.
"Babe" Ya fada muryarsa tana rawa. Wani rauni yana bayyana sosai cikin muryarsa sosai,kamar wanda yake hangen zai rasata shima adan qanqanin lokaci irin wannan
"Akhnan" Ya sake kiranta yana tattaba fuskarta sosai,saidai ba wani alamun motsi sam a tattare da ita.
Da wani irin sauri ya sureta gaba daya,ya soma komawa da ita ciki. Ya tsaya hannunsa yana rawa ya kira security service.
"Call the doctor......now!" Ya fada da wani irin murya da tayi amsa kuwa a dukka sassan suite din.
Yama manta yana da wani training gaba daya akan irin taimakon gaggawar.....ya manta kansa......ya kuma manta wayeshi.
Gaba daya suite din ya shiga motsawa,su shehnaz aisa dake kuka,da sauran ma'aikatan dake sauri saurin hada mata abinda zai taimakawa numfashinta. Idanunsa dukka suna kanta,ko sau daya bai daukesu daga kanta ba,yana ganin kamar idan yayi hakan zai waiwayo ne ya tsinci gawarta.
Tana jikinsa....har zuwa sanda likitar ta kammala bata dukkan taimakon da zata bata din.
"Zata tashi in sha Allah" Haka kawai yakejin kamar bata fadi gaskiya ba,haka kawai yakejin kamar ba tashi zatayi ba. Komai ya kwance masa,ji yakeyi kaman ba gangar jikinsa bace a jikinsa.
A tausashe ya gyara mata zama cikin jikinsa. Bakinsa saitin kunnenta ya kirata.
"Khadeejah.......my princess" Sai muryarsa ta sake karyewa
"Wake up" Ya fada kamar wanda yake roqonta akan ta bude idanunta. Ganin idanunta a rufe sake karya masa duk wani qwarin gwiwa yake,ganin idanunta a rufe yana sawa yaji kaman duk duniya ta kulle masa qofofinta gaba daya.
Karon farko cikin lokaci mai tsawo tsoro ya bayyana sarai a idanunsa,wani abu guda daya daba wanda zaice ya taba gani tattare dashi.
Shafa kanta yayi,muryarsa na rawa cike da damuwa.
"I'm here....." Sai muryarsa ta sake rauni cikin yanayi na roqo da magiya.
"Akhnaann". Kamar taji kiran,kamar sunanta daya ambata yakai har cikin qwaqwalwarta da zuciyarta dake shirin tsaiwa da aiki,saita motsa yatsunta sannan idanunta suka fara motsawa suna yunqurin bude kansu.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*