L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 59
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 59: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 59. *SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
3,361 words
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 105* ___________________________ https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0
*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*
*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*
*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*
*_Assalamu alaikum my loyal people_*
*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*
*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*
*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*
*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*
*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*
*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*
*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*
*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*
*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee* ___________________________
Sosai ya sake riqeta cikin jikinsa yana sake jera kiran sunanta,idanunsa a kanta.
"Alhamdulillah" Ya fada sanda numfashinta ya tsaya,saidai kuma cike da rauni. Ta ware idanunta fes a kansa,wadannan blue eyes din da suka sake wani irin haske dake birkice da tsoro da fargaba.
"Alhamdulillah" Ya fada yana taba qirjinta yanason jin yanayin bugun numfashinta.
A hankali komai ya dawo mata,tamkar mutumin da ya farka daga wani mummunan mafarki bayan dogon lokaci.
"Bappi...." Ta furta a raunane hawaye suna sake wanke mata fuska.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.....Allahumma ajirni fi musibati,wa'aklifny khairan minha" Ya soma maimaitawa a hankali,ba tare daya kula da kukanta ba.....ba tare daya tsaidata ba....ba kuma tare daya hanata yin komai ba. Ya hade yatsunta cikin nasa yana bata support a hankali da wani yanayi da yake kama da yanason dora harshenta da zuciyarta a ambaton Allah.
A hankali bakinta ya kama innalillahi din,taci gaba da maimaitawa tare dashi ba qaqqautawa.
Bai motsata ba,bai hanata kukanta ba bai kuma tasheta zaune ba,ya barta a jikinsa sunaci gaba da maimaitawa istirja'in a tare. A haka ta soma jin wannan dutsen me nauyi da qarfi daya tokare mata numfashin yana narkewa yana buda mata 'yar siririyar hanyar da zata iya zama.....siririyar hanyar da zata iya numfasawa adadin kwanakin da takeji sun rage mata.
"Da gaske kenan.....bappi na ya mutu?,sultane ya mutu?" Ta fada kanta kwance saman qirjinsa,hannunta na riqe da rigarsa kamar tana tsoron duniya gaba daya.
Shi kansa zuciyarsa tana nauyi da ganin halin da take ciki.
Muryarsa ta zama calm,soft,cike da nutsuwa. Sai yadan shafa kanta a hankali.
"Akhnan" Ya kirata yana qoqarin danne nauyin yasa zuciyar.
"Ki saurareni" Ba zata iya amsa masa ba......amma kunnuwanta shi suke saurare. Fatanta daya yace mata abinda taji kawai ba daidai bane,fatanta kawai tace masa sultane bai mutu ba yana raye.
"Mutuwa wajibi ce akan kowa" Sai ya dakata a tausashe.
"Kuma babu wani rai da Allah ya halitta wanda bazai d'an d'ani mutuwa ba"
Hannunsa ya sanya yana dago fuskarta daga qirjinsa,yana bin hawayen dake sake ambaliya suna wanke mata fuska da kallo. Yatsansa ya sanya yana dauke mata su.
"Nasan akwai ciwo"
"Musamman mutum ya rasa wanda zuciyarsa take qauna" Sai ya danyi qasa da kansa yana kallonta.
"But akhnan"
"Qaddarar Allah bata tabayin kuskure" Ta lumshe idanunta da qarfi saboda zafin da ke zuciyarta.
"Amma na barshi.....shima kuma ya tafi ba tare da mun yiwa juna bankwana ba" Ta fadi tana jin zuciyarta kamar zata tsage.
Hannunta ya riqe cikin nasa a tausashe,yana matsawa a hankali cikin nuna rarrashi.
"Kada ki azabtar da zuciyarki da abinda baya hannunki.”
" Allah ya fimu sonshi.....kuma wataran muma zamu bishi,zamuje inda yaje" Sake matse hannunta yayi da salon bata qwarin gwiwa.
"Ki tuna...."
"....Duk addu’ar da zaki yi masa yanzu zata isa gare shi.” kai take gyadawa a hankali,duk da ta kasa magana sai hawaye kawai dake zuba.
"......Kuma idan ya kasance uba nagari gare ki…” ya saki siririn murmushin da bashi da alaqa da farinciki.
"Then the greatest gift da zaki masa yanzu…”
"…shine ki ci gaba da zama d'iyar da zai yi alfahari da ita.” kai ta sake jijjigawa da qarfi,sai wani kukan ya sake qwace mata. Wannan karon....kuka ne dake sauke mata gami da rage mata nauyin zuciya.
Jawota jikinsa yayi a tausashe yana bata kyakkyawar runguma.
"Kiyi haquri saboda Allah"
"Ki karbi qaddara saboda Allah" Shuru ya sake ratsawa tana jin yadda maganganunsa ke samun muhalli me kyau cikin zuciyarta suna kuma saukar mata da nutsuwa kadan kadan.
"Duniya gaba dayanta tafiya ce akhnan...."
"Wata rana muma zamu koma ga Allah" Ya sanya idanunsa cikin nata a tausashe.
"So while we are still here…” ya jijjiga kansa.
"…let us hold onto faith.”.
Maganganunsa wadansu taskoki ne masu tsada a tare da ita,wasu taskoki ne masu nauyin da idan aunasu za'ayi cikin ma'auni zasu rinjayi komai dake kanta.
Wani irin tauhidi....imani......haquri da karbar qaddara ta gaskiya ta saukar mata. Da taimakon kalmomin nan guda biyu....masu nauyi da tsada da ya maidasu suka zama abun saurarenta daga sanda aka fara shirya private jet dinsu na tafiya agadez har aka kammala.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Da kuma
"La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimeen" Daga baya ya surka mata da.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel". A dukkan awannin.....awanni masu tsananin gaske a cikin rayuwarta.....awanni mafiya jirkicewa rudewa da fuskantar ibtila'in da bata taba ganin makamancinsa ba.....hannunsa yana cikin nata. Idan har ya zameshi ko ya sakeshi to sallah zasuyi shi da ita.
Bai bari su shehnaz sun ganta da wuri ba sai bayan wasu awanni. Batasan yadda yasha kansu ba.....amma dukkanunsu sunyi qoqarin zama cikin nutsuwarsu,saidai ba wadda idanunta ya dakata daga zubda hawaye.
Ba shakka sultane uba ne.....ubane har uba game uba da mara ubanma. Bai taba nuna banbanci gazawa ko kasawa ba tsananinsa da akhnan da kuma falaak ba.
Sai zuwa dare sannan private jet din ya samu daman tashi dasu.
Shuru ne ya sake wanzuwa cikin jet din,sai sautin engine mai laushi da kuma dim golden lights dake cikin cabin.
Tana zaune kusa da window ne kawai,amma idanunta basa kallon komai. Ko daga nesa kana iya ganin yadda idanunta suka kumbura da kuka,kukan da haisam yace tayi idan tanaso.....amma karta fadi karta bari zuciyarta ko bakinta su furta abinda Allah bai yarda dashi ba.
Tun bayan tashinsu daga Dubai,bata iya zama lafiya ba. Zuciyarta wani zugi take mata,fargabar da batasan ta meye ba tana sake mamayeta.
Kowanne minti zuciyarta tana tuna Sultane ne.....kalaman Mammina .......da kuma yadda bata yi bankwana da mahaifinta ba.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Haisam kuwa yana zaune kusa da ita. Ba aiki ba kuma danna waya kwata kwata,gaba daya attention d'insa yana kanta. Kowannd motsi idanunsa suna kanta,yana jin yadda tausayinta ke narkar da zuciyarsa.
A yau duk wani tausayi nata da yakeji a baya.....sai yaji ya ninka kansa ninkin baninkin,tausayin daya sake narkewa da wata mahaukaciyar soyayyarta da baisan qarfinta yakai haka ba sai yanzu.
A hankali sai ya lura hannayenta suna rawa kad'an. Ya motsa a hankali ya dauki gorar ruwan dakr gabasa ya tsiyaya a cup ya miqa mata
“Drink something.” ya fada idanunsa cikin nata a tausashe. Ta girgiza kai cikin karaya.
“Bana so…” Sai ya matsa kusa da ita kad'an.
“You haven’t eaten either.” ya fada da kulawa sosai,bai jira amsarta ba ya d'ora
“Your body needs strength.”
Ta lumshe ido tana qoqarin hana sabon kukan fitowa. Bata jin a wannan yanayin da take ciki,banda iska akwai wani abu da zai samu daman wucewa ta maqoshinta.
Sai kawai ya cire belt d'insa ya matsa kusa sosai,kafin ya jawota jikinsa cikin tausasawa.
“Come here.” Ba musu ta kwanta a jikinsa. Bango take buqata a yanzu,majinginar damiwarta. Ta lumshe idanu cikin gajiya da ciwon da zuciyarta take mata. Sai ya rufe ta da soft cashmere blanket,hannunsa na shafa bayanta a hankali cikin kwantar da zuciyar dake cike da firgici
“Sleep a little.” ya fada kaman me lallashin jaririn goye,yayi kissing nata a hankali
“I’m here" Ya sake fada yana matsa kafadarta cikin bata assurance.
Tafiyar awa biyar zuwa shida tsakanin dubai zuwa agadez. Duk lokacin da ta farka cikin kuka sai ta sameshi still a gefanta,still yana riqe da hannunta.....sannan still calm Kamar baya son ta ji tana ita kad'ai. Bayason yaga wannan kewar.....wannan kadaicin cikin idanunta. Inda yana da dama.....inda ya isa tabbas da zai kauda mata wannan quncin da taketa fama dashi,wannan quncin da take kokawa dashi.
*A G A D E Z*
*Mano Dayak International Airport*
Gaba daya yanayi da atmosphere ya bambanta tsakanin Dubai da agadez.
A idanunta sai taga sararin samaniya tamkar ya dusashe.
Iskar hamada na busowa a hankali,kunnuwanta suka jiye mata wani irin shuru da agadez din tayi.
Daga can nesa tana iya jin sautin karatun qur’ani daga masallatai mabanbanta mallaki qasar agadez din daga kowanne sashe nata.
Motocin masarautar agadez ne sun cika wajen. Hadimai bayi da masu tsaro. Royal convoy sosai duk saboda taronta.
Amma duk fuska d'aya,yanayi daya zaka gani saman fuskar kowa da zaka kalla a gurin.
A hankali take takowa matattakalar tana saukowa,da wani irin kasala da mutuwar jiki cakude da matsewar da zuciyarta takeyi. Tazo step din qarshe saita tsaya cak zuciyarta na wani irin bugawa.
Karo na farko kenan.....karon farko da ta dawo Agadez ba tare da jin wanzuwar mahaifinta cikin qasar ba. Karon farko data shigo agadez taga ta mata baqi.....ta mata duhu. Wata agadez da a yanzu ba sultane a cikinta....sultane din da zuwa yanzu yayi kwana d'aya cikin qabarinsa. Wata agadez daban take gani cikin idanunta ba wadda ta saba gani ba.
Hannuta ya riqe yana sake matsawa softly cikin yanayin bata qwarin gwiwa.
"La haula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem....Allahumma ajirni fi musibati,wa'klifni khairan minha" Ya fada cikin taushi. Hawayen nan dai da suka kasa yanke mata,sune suka ciccika idanunta,ta motsa labbanta a hankali tana maimaitawa tare dashi,saita fara takawa suna nufar motar dake bude tana jiran isowarsu.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 106* __________________________ *_Amintaccen gurin siyayya_*
*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*
*_BONONZA DA PROMO akai akai_*
*dukka sai a HUGUMA CLOSET*
*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*
*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*
*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*
*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________
Hatta da titunan agadez sai data dinga ganinsu wayam,shuru kuma empty. Kamar suma suna kewar sultane ne. Abu daya data lura dashi,.....masu sana'o'i kamar gurarensu duka a kulle yake. Ta lumshe idanunta tana jan iska tana faran qirjinta ya bude ya kuma rage nauyi. Qila suma suna kewarsa ne.....qila suna tayasu jajen rasashi da sukayi.
Sanda suka isa gidan sai ta hangi Ahmad,falaak.....morsa safiyya da nannie,suna tsaye daga nesa. Zuciyarta ta karye da wani yanayi me nauyi sanda take kallon fuskar morsa safiyya. Komai sai yake dawo mata a sannan,hirarrakinsu da nanay.....labarin data bata game da rayuwarsu su ukun. Da gaske ne......uwarta ce ita ta haqiqa.....ashe da gaske ne itace mace mafi kusanci da ita duk duniya....ashe da gaske bata da sama da ita.
Ta manta mijinta ya rasu......ta taso ta tattako don kawai ta tareta,don kawai ta tallafi rauninta.....don kawai ta raba wannan baqincikin da tashin hankalin da ita. Duk yadda momma takejin tana da qwarin gwiwa sai taji ashe ba haka abun yake ba sanda idanunta suka sauka akan Akhnan. Kallo daya suka yiwa juna da ita kowa ya karanci dan uwansa bai taba fuskanta da shiga tashin hankali kwatankwacin wannan ba. Rauni ya mamaye morsa safiyya,sai ta saka gefan mayafinta tana lullube fuskarta da wani sabon hawaye ya balle mata.
Ahmad ne ya fara takowa gareta da sauri. Ta kalli cikin idanunsa.....sunyi wani irin jaaa sosai. Kamar wanda ya rasa baccinsa na wata da watanni.
“Akhnan…” ya kira sunansa hannunsa yana rawa amma yana qoqarin bawa kansa wannan jarumtar da tun jiya daya tabbatar ya rasa sultane ta soma kwaranyewa. Kamar jira takeyi,ta soma takawa tana isa gareshi da sassarfa,sai ya rungumeta sosai yana qoqarin danne tasa zuciyar.
“bappi ya tafi…” ta fada da rikitacciyar muryar kuka.
Falaak ma idanunta cike da hawaye ta tako da sauri,sai ta rungume Akhnan daga gefe.
"Komai ya faru cikin sauri.....komai ya faru cikin irin taqaitaccen lokaci,mun rasa bappi dinmu" Ta sake rushewa da kuka tana riqeta.
Kowa kasa magana yayi,kowa zuciyarsa ta raunana.
Kasa magana morsa safiyyan itama tayi,kallonsu kawai takeyi da idanun da suka gaji da kuka. Tana jin komai kamar almara,tana kallon komai kamar a mafarki. Yau ba sultane......yau ta rasa sultane,daga ita sai 'ya'yanta,daga ita sai abinda suka haifa ita da safeena.
Da qyar ta tattaro qwarin gwiwarta,ta taka wajensu a nutse tana rungumesu dukka a jikinta.
"Allah ya baku haquri,ku yaiwata karanta hasbunallahu wa ni'imal wakeel".
Akhnan ta duqushewa tayi a jikinta tana kuka kamar qaramar yarinya.
Haisam danunsa ya lumshe yana jin zuciyarsa na masa wani irin zugi. Yana jin kamar bazai jura ba.....kamar bazai jurewa ganinta haka ba. Yana jin wani rauni da bai taba jin irinsa tattare dashi ba,komai girman tashin hankali masifa ko qalubalen da zai fuskanta.
"Itace rauni na" Ya gayawa kansa a hankali yana sake bude idanun nasa ya zubesu akan Akhnan din.
"Haisam" Morsa safiyya ta kirashi tana dubansa.
"Kamata muje ciki" Ta fadi ahmad yana riqe falaak wadda zazzabi ya rufeta ruf a gurin.
Kamar qafafunta ba zasu taku ba,amma haka ya riqeta cikin jikinsa ya bata dukkan support har suka isa ciki.
Babban guri ne da aka ware saboda masu shigowa su yiwa matan sultane din gaisuwa. Shiyya biyu ne,na morsa safiyya sai bangaren mammina,rumfarta da jama'arta da suke opposite da daya bangaren da morsa safiyya ke zama.
Guri daya ne....amma a kallon farko da idanunka zaka gane akwai banbance babance me yawa a shiyyoyin biyu da suke opposite da juna.
Tana zaune.....kamar ko yaushe....kamar kullum......kamar yau din ba wata rana bace data banbanta da sauran ranakun da sukeyi cikin rayuwarsu ba.....kamar bata amsa sunan MAI TAKABA BA.....kamar ba abinda ya hadata da wannan sunan.
Suturarta me nuna ado da iko......mutane zagaye da ita da shimfidun alfarma,manya filalluka masu taushi da manyan warmers na alfarma da fulasai na ruwan zafi da kuma ruwan tea. Wayarta na riqe a hannunta,amma sanda suke shigowa saita dauke idanunta zuwa kansu. Kamar an gaya mata ne.....eh.....gaya matan akayi,tafisu......tafisun dake zaune daga hannun damanta,sai tabar komai,tabar duk abinda takeyi tana zube idanunta a kansu.
Wadannan mutanen..... Wadannan rayukan da a yanzu sune target dinta. A dunqule guri daya,a cure guri guda. Yadda take kallonsu a hade guri guda dinnan.....haka takeso so samu ta gama dasu rana guda,ta shafe babinsu.....ta mantar da al'ummar agadez labarinsu.
Bata yarda me sa'a bace ita.....bata aminta tana cikin matan da sukayi sa'ar zuwa duniya ba sai da aka wayi gari da mutuwar sultane.
"Wannan wacce irin sa'a ce haka?" Ta tambayi kanta tana qyalqyalewa da dariyar da har tafisu sai data daga kai ta kalleta.
"Qyaleni na daara tafisu.....kinga laifina?,Allah yana sona......ya kalli tsakiya zuciyata ya hutashesheni daga qoqarin daukan ransa da nake tayi amma a banza. Sun saka tsaro me tsanani.....sun saka likitoci duka don su sashi yaci gaba da rayuwa,ashe gawa suke jira......wannan itace damata.....wannan itace damar da nake jira.....kowa sai.ya shiga uku.....saina jefa masarautar agadez cikin uquba da masifa.....wanda ya bini ne kawai.....wanda yayi biyayya ne kawai zai tsira" Ta fada tana girgiza qafarta cikin jin isa da qasaitarta tana cika. Banda bata sha'awar hawa kujerar sultane.....tafi qaunar juya me mulki daga nesa,tabbas tun a asubahin ranar zata kira kanta SARKIN AGADEZ.
Ta dauke idanunta daga kan falaak kenan don duban fuskar akhnan,sai idanunta sukayi kuskuren fadawa kan fuskar haisam. Idanunta ta lumshe sannan ta budesu. Idan tace gabanta bai fadi ba tayi qarya.....idan tace zuciyarta bata tsinke ba ta shimfida qarya. Kyakkyawan dan sauri......mallakar qabilar oromo....wannan kyan nasa irin na ubansa ibraheem......ibraheem din da taso mutuwar so amma ya kwashi qasa ya watsa mata a ido......ibraheem din da shine namiji guda daya da taso ta d'and'ana amma ya nuna yafi qarfinta fintinkau.....ibraheem din da har yau har gobe tana muradinsa......amma ta yarda da yace yafi qarfinta har gaban abada...... Ashe wannan dalilin ne yasa take jin wani abu na daban bayan kwarjini duk sanda ta kalli fuskar haisam?. Inama ace ta san haka tunda wuri.....inama ace tasan jinin ibraheem ne.....lallai da ko ranta zata bayar saita bayar wajen hada jiki da haisam din,koda na dare daya ne ta kuma aikewa Ibraheem saqo har masarautarsa. Bata samu cikakkiyar fansa daga ibraheem ba.....banda KHALEED data kashe masa. First born dinsa daya fara haifa kafin haisam din.
Ko a yanzun da idanunta suka sauka kan haisam,saida taji wannan yanayin. Kyansa shi da ubansa me kashe zuciya ne sosai.....amma kuma a yanzun......haisam din babban abokin gaba ne....
"Na gode daka kawomin kanka da kanka cikin sauqi......ka gajartamin wahala,basai na gama da yaqin nan ba naje nayi na Ethiopia ba" Ta fada idanunta cikin nasa.
Kamar ya karanci komai.....kamar ya karanci abinda take fada,sai ya murmusa kadan yana zare idanunsa daga nata.
"Murmushi?" Ta tambayi kanta tana sauke idanunta qasa.
"The silent one.......alsaamit" Ta tunawa kanta da title dinsa. Duk sanda yayi murmushi akwai akwai matsala.....duk sanda yayi murmushi tabbas akwai wani abu me qarfi.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Zan fara rusa duka qwarin gwiwarka daga ranar farko daka shigo agadez" Ta fadawa kanta sannan ta ajiye wayarta tana miqewa.
Sai shuru ya ratsa gurin,ganin yadda ta miqe afujajan. “Ya tsaya!.” ta fada cikin bada umarni tana nuna haisam dake takowa da cikakkiyar nutsuwarsa.
Idanu kowa ya zubawa mammina din,kafin a hankali wasu idanuwan suka koma kan haisam cikin mamaki. Mamakin da kusan zuciyoyinsu ke maimaita maganan mammina tare da kokwanton da haisam din take kuwa?. Akhnan ta maida idanunta data dauke daga kan haisam zuwa fuskar mammina din tanason tantance akan wa take magana?.
“Shi ba jinin Sultane bane.” ta sake furtawa kai tsaye tana ware idanuta a kansa da sauran manyan mutane dake gurin da suka zuba mata ido.
“Bashi da abin yi a cikin rumfar zaman makokin gidan nan.” ta fadi wannan karon tana haqiqancewa cikin d'aga sauti da son tozartarwa.
Kallon kallo mutane suka fara yiwa junansu,mamaki yana kashe kowa. Ba wanda baisan waye haisam a gurin sultane ba....ba cikin agadez daya rayu dasu na watanni masu tsaho ba,suka amfana da abubuwa da yawa nasa ba.....aah har niger gaba daya. Wasu cikin mamaki. Wasu cikin tashin hankali suke kallon mammina din da wani tarin mamaki,wannan raini ne a bayyane,kuma ga surukin Sultane din?,wanda ya daukeshi a matsayin dan cikinsa halak malak.
Akhnan ta tsaya cak,kafin idanunta suka sauya a hankali da wani irin ciwon bacin rai daya cika cikinsu.
Me mammina keyi haka?,hankalinta daya?,ko kuma duka da rikitar mutuwar sultane ya taba kwanyarta?. Wannan ya sanya tayi yunqurin dawo da ita hayyacinta.
“…Mammina.” ta kirata tana dubanta don tabbatar da zarginta. Da sauri ta dagawa Akhnan din hannu tana dakatar da ita.
“Zaman makokin nan na iyali ne.....bana baqi ba" Ta fada tana tsaurara harshenta.