L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 60
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 60: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 60. Wani irin shuru me gauraye da mamaki ya sake cika…
3,375 words
Wani irin shuru me gauraye da mamaki ya sake cika gurin. Wasu na kallon haisam din,sunaso suga reaction nasa.....saidai ko daya.....ba abinda ya sauyashi,ba abinda ya sauya wannan calmness din nasa......wannan nutsuwar da haibarsa ko daya ba abinda ya canza a tattare dashi.
Nauyi taji qirjinta ya sakeyi.....me yake damun mamminan?. Kwanyarta ta dauko kalamanta.na jiya a kanta ta hada da abinda ya faru yanzu. Attack ne.....attacking haisam din take?. Kai tsaye ta soma takawa don isa gaban mamminan.....don ta tuna mata me take cewa,don kuma ta sake tuna mata da mijin waye dama waye take magana a kanshi. Taku biyu tak tayi taji ya riqo hannunta cikin nasa,saidai hakan bai sanya ta waiwaya ba,bai kuma hanata duban idanun mammina din ba wani bacin rai yana wanke mata fuska.
"Shi d'in mijina ne...." Muryarta ta fito da wani irin qarfi da iko,sannan ta waiwaya tana duban idanunshi.
"Sannan mutumin daya tsaya dani tun daga sakannin da aka bani labarin mutuwar mahaifina da wani irin salo da ba jin qai ko tausayi a cikinsa....." Takai qarshen maganan wasu hawaye na kubce mata. Ta dauke idanunta tana sake maidawa kan fuskar mammina.
"Ya tsaya dani fiye da wasu jinin sultane din....fiye da makusantansa".
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 107* _________________________ *_SHUWA INCENSE AND MORE_*
😊 *_kai daga jin sunan basai an gaya maka ba_*
*_kai daga jin sunan basai ka tambaya ko tsaya tunanin maganar me ake ba_*
*_MAGANA CE TA GIDAN QAMSHI_*
*BAFA GAMA GARIN QAMSHIN DA KIKA SABA JI BA HAJJAJU*
*KINA QONA TURARE YANA QAURI*
*KINA SAKA KHUMRA TANA BIN SHANUN SARKI*
*WANNAN DIN TURARE NE DAKE DAWWAMA A DAKI DA JIKI.....DA SALON QAMSHIN DAKE MANTAR DA ZUCIYA DUK WANI B'ACIN RAI*
*TASTED AND TRUSTED👌👌👌100% HAJJAJU*
*NA DABANNE A CIKIN NA DABAN*🙌🏽🙌🏽
*idan akazo kan SHUWA INCENSE an tashi magana*
*idan ma kinsan baki shirya jan magana ba a duniyar qamshi to kisha zamanki hajajju*
*_zaku iya magana da ita kai tsaye ta wannan number wayar_* +234 704 229 3387 ________________________
Zallar mamaki kawai ya sauya idanun mammina,ya kuma daskarar da wasu a gurin. Sabon abune ko ace abinda take idanu basu taba gani ba,a gurin wani mutum gama gari ma ya maida mata magana gatsal haka kai tsaye yana duban qwayar idanunta.....ballanta kuma ace ya faru tsakaninta da akhnan?.
"Kin manta kina magana da waye?"
"Ba manta ba......ina sane.....a cikin hayyacina nake.....abu guda daya na sani shine....bazan bari a rainamin mijina ba.....domin shine gatana.....shi sultane yace nabi.....shi sultane yace na yiwa biyayya......na girmamashi,kuma zan aikata hakan.....bakin raina" . Idanuwanta gaba daya taji kaman zasu fado,wani irin daskararren mamaki ya mamayeta.
Ita mammina?,ita akhnan yau ke iya maidawa magana akan sheikh din?. Ita mammina ita akhnan ke iya sa'insa da ita?,a gaban mutane adadin da batasan yawansu ba?.
Da hannunsa dake cikin nata ya jawota baya a tausashe. Bayaso.....bayaso ita da kanta ta tsaya tana qalubalantar matar.
"Basai kin kareni ba" Ya fada a tausashe,tausayinta qaunarta da kimarta suna daduwa a idanunsa. Ta yarda.....ta amince fa fuskaceta saboda shi. Duk da batasan wacece ita ba.....batasan tarin zalunci da gurgunta rayuwarsu da tayi ba a a binne cikin qasa.
Idanunta dake jiqe da hawaye ta daga ta kalleshi.
"Mijina ne kai.....bazan kuma bar kowa ya wulaqantaka ko ya tozartaka ba".
"Ina dogarai?.....kuzo ku fitarmin dashi daga nan!" Mammina din ta fada da qarfin muryar data isa har inda suke tsaye suna bawa gurin tsaro da kula da zirga zirgar masu shige da ficen zuwa gaisuwa.
Cikin mitunan qalilan suka iso gurin,ta sake maimaitawa.
"Na zare masa izinin shigowa gidan nan kwata kwata daga yau.....ku fiddashi daga gidan nan". Baiko motsa ba,haka ya matsa hannun akhnan daya fuskanci tana shirin magana.
Duk wanda ya kalleshi sau daya cikinsu sai ya sadda kansa qasa.
"Allah ya taimakeka....Allah ya qara maka lafiya" Abinda akwai suke fadi kenan suna sadda kansu qasa.
"Bai kamata ba....surukin sultane ne fa?" Nannnie dake zaune ta fada,wadda tashin hankali ya sanya jikinta dukka ya kama rawa.
"Rufemin baki.....kibar gurin nan......kema daga yau rumfar nan zamanta ya haramta a gurinki.....don baki da gadon sultane,ko kina tunanin bamusan uba kawai kuka hada shi ba!" Ta fada a tsawace.
"Koma ki zauna" Haisam.yace da nanay yana takowa cikin kamewa da haiba. Idanu suka sake komawa kanshi,jikinta na rawa ta koma ta zauna tana duban haisam da ya kawo akhnan gefanta ya zaunar da ita,sai ya miqe tsaye yana zube hannayensa a aljihun black silk jubah dinsa.
"Ku koma bakin aikinku" Yace da hadiman,wada kamar walqiya suka soma juyawa suna barin gurin.
"Duk taku daya idan kuka qara ba tare da kunyi aikin danace muku ba.....a bakin aikinku,sunanku korarru" Ta fada cike da zallar mamaki tana dunansu.
Ta dauka zasu dakata da tafiyar,ta dauka zasu dawo su nemi gafararta,amma sai taga ba wanda ya juyo sunci gaba da takawa.
"Allah ya gafartawa sultane" Ya fada yana duban nannie
"Ameen" Ta amsa hankalinta yana sake tashi da abinda ke faruwa cikin gidan tun kafin a fidda gawar sultane daga gidan
"Allah yasa ya huta.....ki zauna a nan tare dasu.....idan kin gaji ko kina buqatar ganina ki kirani,duk inda nake zanzo,karkiyi kuka.....kada kiyi hayaniya....ki huta sosai....zuciyarki ta samu nutsuwa" Ya fada calmly idanunsa akan akhnan din kamar ba kowa a gurin,kamar ita daya ce me rai a gurin.
Kanta ta gyada a hankali tana dubansa,tana kallonsa ya taka a nutse yana ficewa daga gurin.
"Ba abinda zai sauyata......yanzu za'a fara wasan" Ya furta qasa qasa suna jerawa da abdii da shigowarsa masarautar kenan. Kai tsaye babbar rumfar da ake karbar gaisuwa abdii ya masa jagora,ya hana duk wani security da guard dinsa shigowa cikin gidan.
"Me ya faru da manyan falukan baqi na gidan da ake zaman makoki a wajen rumfuna?" Yayi tambayar yana duban maher.
"Giwa ta hana,ta hana kowa rab'ar sashen.....muqullin kowanne sashe da d'akuna yana hannunta. Banda dakin ajiyar sultane,maqullin naji tana nema yau tunda sassafe". Kai haisam kawai ya gyada,ba tare da yace komai ba,saboda suna dab da isa rumfar,kuma yaga tasowar wazeer da wasu manyan mutane na qasar agadez din.
★ Daren gaba daya garin AGADEZ ya sakeyin shuru,sai iska me dauke da sanyin sahara dake kadawa .
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Cikin sashen ya yanke sauka,sashen dake cikin gidan wanda kafin isowarsa ya zamana a gyare cikin control,komai a kintse yake akan tsarin da sukasan yanason ya kasance,bisa jagorancin maher da abdii,wadanda suna daga cikin wadanda basu bar agadez ba ko bayan ya tafi.
Shuru akhnan ta sakeyi,tana kwance lamo,tun bayan dawowarsu daga rumfar zaman makoki.
Kuka ya gajiyar da ita,zuciyarta kuma ta yi nauyi fiye da yadda zata iya d'auka.
Haisam na can tare da mutane da tarin baqi,gaba daya zaman makokin bayan isowarsa sai ya zamana kamar kowa shi yake jira. Shi yake tsaye akan baqi da sauran masu zuwa gaisuwa,don sam ahmad bashi da wannan qwarin gwiwar ko kadan. Duk da irin jarumatar da haisam din ke roqe hannunsa yana gwada masa,amma ya gaza jurewa,ya gaza tsaiwa kaman yadda ya kamata ya tsaya din. Minti daya zaka ganshi zaune.....minti daya zaka nemeshi ka rasa,ya shiga ciki don yayi kuka,sannan ya share hawayen ya sake dawowa cikin jama'a.
Ta sake juyar da kanta wani sashen,kowa fuskarsa a galabaice take da tashin hankali,ba wani me sukuni cikakke,amma bata hangi wannan abun ko qanqani ba a kan fuskar mammina.
"Me ya sameta ne haka?,meye a zuciyarta?" Ta maimaita tambayar karo na babu adadi. Baqi kawai take karba cikin nuna izza da mulki,duk wasu siffofi da doka dame takaba ya kamata ta kiyaye a musulunce babu ko daya tattare da ita.
Hira da zantukan dake tashi a rumfarta sam ba zaka hada dana rumfar morsa ba,wadda ta cika da shuru da nutsuwa,sai qur'anai da ake rabawa me juzu'i juzu'i ana sauka ana sake juyawa wata.
Nannie......hairan.....shehnaz.....aisa take hango fuskokinsu,banda ta morsa safiyya da kamanninta suka sauya saboda kuka. Bata hangi koda digo daya a fuskar mammina kalan alhinin da take gani ba. Ama ture ta falaak wadda tun la'asar mummunan zazzabi ya mata mugun kaye,har sai da maleek ya shigo gidan da kansa ya sanya aka saka mata ruwa,ya dauketa zuwa wani sashen daban da aka basu shi da ita,duk da yana da gida a waje,amma shima ya zabi zama a nan saboda ta zama kusa da morsa,shima ya zamana kusa da abokinsa.
"Wannan ba tsari bane.....komai na gidan nan a yanzu na magada ne.....bai kamata a dinga bawa baqi daman wanzar da abubuwa ba. Na kwana uku kawai zasu zauna.....a tashesu a bani.maqullan sassan" Haka ta zaunar da sarkin gida tana gaya masa cikin mutane.
"Aah?" Akhnan ta furta a hankali tana jin kanta kamar zai tsage. Ta dauko maganganun mammina randa ta kirata gatsal ta gaya mata ubanta ya mutu. Ta sake dauko maganganunta na dazu,ta dauko wadannan tana hadasu guri daya.
Kai ta fara girgizawa sanda zuciyarta ta fara raya mata wani abu.
"Aah.....bazai yuwu ba" Ta fada tana miqewa ta zauna sosai,sai a sannan hannunta ya dunguri black tea din da haisam ya hada mata kafin ya sake fita sallar isha'in da har yanzu bai dawo ba,yace kafin ya dawo ta tabbatar ta shanyeshi.
Qofar aka murda a hankali cikin nutsuwa,wanda tun kafin ya bayyana ma ta fahimci waye da qamshin nan nasa.
Ya sauke ajiyar zuciya yana yabawa qoqarin abdii. Nan din ba hayaniyar waje sam....sai soft gold light. Ba wani motsi da zai iya janye maka hankali. Sai tsantsar safety da zakajishi har jikinka.
Ninkin masu tsaro ne suke zagaye da sassan,har abun yadanso daure mata kai,amma koda ta tuna a yanzu wayeshi?sai tayi shuru kawai.
Da sallama ya shigo,da sassanyan sautin nan nasa da a yau yakejin ya gaji da yin magana gaba daya,yana jin kamar duka kalaman bakinsa sun qare.
Tun asali mutum ne shi da bayason koda musu ballantana wani abu daban,amma yau shi da wazeer da manyan dattawa masu yanke hukunci a masarautar sun qarar da awanni suna duba yiwuwar dora ahmad a gobe a kujerar sultane.
"Shine daidai....abinda ya dace kenan,a rantsar dashi a gobe,tabbas zai iya,yayi riqon qwarya mun gani,wani jinkirin kuma nashi da fa'ida". Da wannan maganar aka rufe kowa ya sanya hannu,saidai acan idanun wasu yana hangen wani abu da zuciyarsa bata gamsu ba,cikin jikinsa yakejin
"Akwai wani abu....tabbas akwai 'yan wata jam'iyyar daban a cikinsu" Saidai a matsayinsa na qwararren me binciken bin qwaqwaf,koda yatsa bai nunawa kowa komai ba. Abu daya ya sani.....duk wani jini na sultane a yanzu yana jin yana wuyansa.....duk wani ahali na sultane a yanzun yana jin alhakinsa yana wuyansa. Lafiyarsu,tsaronsu da kariyarsu....shi kuma zaiyi bakin rai bakin fama,sai inda qarfinsa ya qare.
Amsa masa sallamar tayi blue eyes dinta a kansa. Wani zaki take hanga yana takawa da qafafunsa bawai yarima haisam tsura ba. Jarumta takejin labari.....amma a tsaiwar da dukka maganarsa JARUMTAR take gani da kanta tana wakiltarshi.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 108* ________________________ https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0
*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*
*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*
*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*
*_Assalamu alaikum my loyal people_*
*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*
*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*
*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*
*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*
*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*
*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*
*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*
*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*
*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee* __________________________
Takowa yaci gaba dayi,saidai idanunsa suna kan tray din daya hada mata komai. Ya tsaya cak daga gaban tray din yana kallonsa yana kuma cire agogonsa quietly. Kunyarsa da nauyinsa taji ya kamata,sai ta danyi qasa da kanta,amma ga mamakinta komai baice mata ba. Ya gama cire agogon,ya zare thobe din jikinsa,ya rage raga shi sai fara qal din singlet wadda ke fidda lallausan qamshin nan nasa,sai wani wando baqi three quarter daya haska fatarsa sosai.
Sunkuyawa yayi ya dauki tray din gaba days ya fice dashi,minti goma kacal ya dawo da wasu kayan shirye a sama. Kunyarsa da nauyinsa ya sanya ta sake sadda kanta qasa.
"Waane mutum?,waane aikinsa?" Kamar ita?,ita kesa young billionaire prince din aiki?,aikinma irin na kitchen?,hidima da ita?. A dazu ya dafa mata baqin shayi......a yanzun kuma bai gaji ba,ya sake dafa shayin ya hado da wata irin nau'in madara.
Gefanta ya ajiye shima ya zauna a nutse,sai a sannan ya kulle idanunta cikin nasa.
“Come.” ya fada da muryarsa me laushi can qasa. Bata musa ba,ta miqe a nutse tana takowa inda yake,tana jin kamar iska zata kadar da ita. Kanta sarawa kawai yakeyi,ba abinda kuma ya shiga cikinta tsahon wunin.
Ta dauka zai ajeta a gefansa ne,sai ya azata saman cinyarsa,ya mata kyakkyawan masauki,ya kuma yi mata kyakkyawan riqo yadda zataji dadin zama.
"Bude bakin" Ya fada yana saka spoon cikin madarar. Ba yadda ta iya ta bude dan qaramin bakinta dake dauke da siraran labba,ya fara saka mata madarar a baki tana karba a hankali.
D'aci kawai take mata a baki,basuyi nisa ba ta girgiza masa kai.
"Na qoshi" Ta fada a hankali hawaye suna cika mata idanu. Bata dauka idan sultane ya mutu zata iya sake rayuwa koda na second daya ba,yau gashi yana iya shan madara a ranar da zaiyi kwana na biyu cikin kabari,albarkacin miji na gari daya zaba mata.
Baice mata komai ba ya maida ya ajiye,ya dauki black tea din.
"Bismillah"
"Bazan iya ba.....na qoshi" Ta sake fada hawayen suna sauko mata. Shuru yayi,saidai yadan b'ata fuska kadan,abinda taji sam bataji dadinsa ba,sai ta bude masa bakin ya soma zuba mata a hankali. Koda tace ta qoshi,sai yadan sake mata murmushi.
"Thanks" Ya fada kamar shi ta ciwa abincin ba cikinta ba.
“You need rest.” ya fada yana goge mata gumin daya tsatstsafo ta goshinta saboda yadda dumin madarar da maganin gajiyar me kama da black tea ya soma ratsata.
Miqewa yayi tsam yana tasar da ita tsaye,ya kama zip na rigar baccinta zai zuge,saita dora hannunta saman nasa tadan riqe.
Wani murmushi kadan ya saki,idanunsa cikin nata yana girgiza kai.
"Zan rage miki ita ne saboda kiji dadin bacci sosai.....bazan miki komai ba....in fact bazan iya komai ba.... Just hutawa kawai nakeso kiyi" Sake masa hannun tayi a hankali,tana jinsa ya zuge rigar tsaf,sannan ya dauko mata wata cotton vest da wani skirt mara nauyi iyakar gwiwa ta saka.
Har saman gadon ya rakata ta kwanta,yaja mata duvet sosai sannan ya tsugunna ya mata lite kiss.
“Haisam" Ta kira sunansa a hankali sanda yake shirin sauka daga gadon.
"My princess" Ya fada yana tura hannunsa ta qasan duvet din ya riqe hannunta sosai cikin nasa.
“Everything feels empty.” ta qarasa fada muryarta yana rawa. A tausashe ya matsa hannunta
“Look at me.” A hankali ta d'ago idanunta.
“You’ve cried enough for tonigh" Yayi maganar yana sanya daya tafin hannun nasa a gefan fuskarta a tausashe.
“…I keep hearing her words.” ta fada hawayen dake idanunta suna gangarowa.
Ya gane sarai,tana nufin Mammina. Sai idanunsa suka d'an yi duhu,yana sake jin wani abu me kaifi game da matar......yana sake jin qasa da sati biyu idan bai sanya matar ta karbi hukuncinta ba shi ba d'an babansa bane. Ta kawo geji.....kuma a yanzun ba idanun duk wani wanda zai sanya ya daga mata qafa saboda shi.
Qafafunsa ya daga yana haurawa saman gadon,sai ya kwanta sosai a gabanta suna sharing pillow. Wannan ya bashi daman musayar numfashi tsakaninsa da ita. Wannan ya bashi daman jin bugun zuciyarta sosai,abinda yake gaya masa cewa zuciyarta har yanzu bata gama nutsuwa ba.....bata gama haqura ba,sai ya sarqafe yatsunsa da nata guri daya.
“She wanted to hurt you.” ya fada da calm voice,yana ganin ya kamata ya sake buda mata tunaninta akan matar.
“Don’t give her victory by breaking yourself.”
Sai ta lumshe ido a h a hankali,sannan ta bude tana dunan qwayar idanunsa.
“I miss him.” sai Haisam ya rufe idanunsa briefly yana jin ciwo da rad'ad'in zubar hawayen nan nata da yaqici yaqi cinyewa da gasken gaske. Kissing goshinta ya sakeyi,ya dora hannunsa saman kanta yana shafa dogon gashinta a hankali da sigar lallashi.
“I know.” cikin muryar rad'a ya maimaita.
“I know, babe......kiyi haquri....komai zaizo ya wuce.....kuma komai yayi farko yana da qarshe".
Kalamansa sun zauna mata sosai cikin ranta,saita cusa kanta sosai da fuskarta cikin qirjinsa. Gurin da takejin bata da sauran gida duk duniya irinsa. Gurin da takejin bata da wata mafaka me daraja irinsa.....gurin da takeji shi dayane yake bata nutsuwa sama da komai duk duniya.
Shuru ya sake ratsa dakin,sai ya miqa hannunsa ya dauki bedside lamp dinsa. Karatun qur'ani ya kunna,da sautinsa da qira'arsa dake.nade cikin fitilar,ya daidaita sautin yadda bazai damu me bacci ba ya ajiye ya kwanta kusa da ita cikin nutsuwa,hannunta cikin nasa,kamar yana tsaron duk wani ciwo ko cutarwa da zai iya isa gareta.
Nutsuwa da wani tarin kwanciyar hankali suka soma mamayarta,ta sauke wata ajiyar zuciya me hade da sheshsheqa,kaman yadda yaron daya gaji da kuka keyi cikin qirjin mamansa a sanda ta lallasheshi.
Bacci yana qoqarin fusgarta,yana qoqarin dauketa daga wannan duniyar zuwa wata taji sautinsa can qasa sosai kusa da goshinta.
“No one will hurt you while I’m here.”
Sai daya tabbatar ta nutsu ta kuma yi nisa a baccin sannan ya zare jikinsa hankali.
A nutse ya wuce bathroom,yayi wanka yayi steaming jikinsa sosai,yana jin duk wata gajiyarsa tana wartsakewa. Yanaso yayi bacci amma bazaiyuwu ya kwanta ba. Bawai don bayason baccin ba.....aah,sai saboda yana jin cewa bacci bai kamashi ba a agadez.
Cikin qatar thobe ya shirya black silk. Ya zama dole ya saka black din,saboda yanason ya dinga sajewa da duhun guri idan yaso haka. Hirami ya nada baqi saman kansa,ya masa wani dauri kaman na dankwali. Baiyi shigar don ado ba.....amma idan ka kalleshi sai kaga ya maka wani irin kyau me daukan hankali.
Coffee kawai ya iyasha,sai gasashen naman da baifi yanka hudu ba. Yana tsaye yana sipping coffee din yana kallonta,tayi relaxing sosai dukka jikinta ya saki tana fidda numfashi a hankali.
Saita masa wani irin kyau,fuskarta tayi fayau,alamun kukan da tasha sosai yana sake bayyana a fuskarta.
Tsaiwa yayi gabanta sosai,ya karanta addu'o'i ya shafa mata,sannan ya sake karanta wasu ya tofa gabas da yamma....kudu da arewa,ya sake rage mata hasken dakin,ya sanya takalmansa masu laushi dake boye sautin taku ya juya yana barin dakin.
Sai daya tsaya yayi addu'o'i sosai,bayan wadanda suka wuni a bakinsa yana yi duk zaman wunin da sukayi din,sannan ya saka qafarsa a hankali yana fita.