L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 61
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 61: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 61. Tun daga babban corridor ya tsaya,yana nazarin guards…
3,354 words
Tun daga babban corridor ya tsaya,yana nazarin guards din dake kula da gurin. Qaramin murmushi ya saki,dama ya sani,ya sani kowanne lokaci zaa canza asalin tsaffin guard na gurin. Yasan hakan zata faru,saidai ya riga ya shiryawa faruwar hakan dama.
Ta gefansu ya soma wucewa yana karantar fuskokinsu. Ta wani b'angaren kai tsaye zai iya cewa mutanen mammina ne,saidai hakan bai canza komai ba.
Da girmamawa suke gaidashi,duk wanda ya aza idanunsa akanshi sai kwarjininsa ya sanyashi sunkuyar da kai yana miqo gaisuwa.
"She moved quickly" Ya furta qasan zuciyarsa,zuciyar tasa kuma ta masa sanyi. Yana jin wani qarin qarfin gwiwa da qarin tabbaci.....nasararsa da sauqi zatazo,wataqila ita da kanta zata zame musu tsani zuwa ga nasarar tasa.
Ci gaba yayi da nazartar komai,yana kuma taking note akai. A hankali har ya isa treasury wing(baitul mali).
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Cikin hikima yake karantar gurin. Komai ya canza...komai tsakanin jiya zuwa daren yau. Sabbin lockers.....qarin masu tsaro da dukkaninsu suka kasance sabbin fuska ne,hatta da seal din gurin an canzashi gaba daya.
Daya daga cikin masu tsaron ya zubawa wadannan idanun nasa masu cike da kwarjini bayan ya gaidashi,ya lura kaman shi aka dorawa shugabancin dukka guards din dake gurin.
A jikinsa yakejin ba dan asalin qabilar Tuareg bane....a yanayinsa yaji dan qasarsa ne Ethiopian,saidai komai nasa kamar ya juye kadan daga asalin qabilarsa.
"Ranka ya dade.....giwa ce ta bada umarni" Ya fada kaman ya tambayeshi.
Baice komai ba,yadai sake kallon qofar na second daya sannan ya wuce abinsa. Wanda a kallon second dayan ya gama karantar wanne irin qarfe aka sarrafa aka saka tsaron qofar.
Cikin qwarewa da sanin sirrantattun hanyoyi na gidan ya wuce kai tsaye zuwa chamber na sultane da yake kaman office a gurinsa. Badon yana tsoro ko akwai wanda zai hanashi isa gurin ba......aah,ko daya. Hasalima kusan tari jama'arsu ne a hanyoyin da suka birkida suka zana jama'ar mammina cikin rashin saninta. Saidai a komai sirri yana da dadi. A komai kuma akwai kad'ar da hankula koda hankulan amintattun daka yarda dasu ne,da wannan salon....da wannan strategy din da yawa ya cimma nasarar ayyukansa.
Gurine dake dauke da muhimman takardu.....muhimmam abubuwa masu yawan gaske. Can qasa ya lura da haske,hasken dake gaya masa akwai wani ta ciki.
"At this hour?" Ya fada a hankali ba don yana mamaki ba. Yasan daga yanzu zuwa kowanne lokaci komai me faruwa ne.
Cikin inuwar duhun ya dinga takawa da wani irin qwarewa,har ya isa bangaren daya lura hasken yafi yawa ta nan. Ba lallai ya iya jin abinda ake fadi ta ciki ba,baya hangowa baisan kuma waye a ciki ba still saboda yanayin tsaro na ginin,don haka ya matsa ya maqala wani abu a jikin glass din,wanda aikinsa shine zuqo magana daga nesa. Ya sake dasa wani abun,sai ya dago hannunsa dake daure da wani abu kaman agogo me dan fadin fuska. Yana dannashi ya kawo haske,ya kuma nuna kalmar connected.
Kai tsaye hoton mammina ya bayyana tarwai saman abun. Ba ita kadai ba..... Ita da wasu mutane ne da baisan kosu waye ba har sai daya matso da fuskar agogon sosai sannan.
Fuskarsu ya fara bi da kallo daya bayan daya,ya sansu a ido....yasan 'yan cikin masarautar ne....amma kuma bazaice ga irin zurfin matsayin kowa ba. Takardu ne da files baja baja bila adadin saman table din,wasu a rufe,wasu a bude.
"Kana gani?" Haisam ya fada qasa qasa yana taba abun kunnensa. Motsin da yaji shi ya tabbatar masa ana gani din,saiya gyara abun muryar kunnensa dayan ya soma saurarensu.
"Ahmad zaisa hannu.....ko yanaso ko bayaso kafin rana ta fito a safiyar gobe" Ta fada tana caccaka yatsanta a saman takardun cikin nuna tabbaci da tilashi.
"Amma fa.....wannan kaman ba dabara bace me sauqi.....saboda jama'a suna tare dashi,suna yinsa ko don mahaifinsa".
"Ina ruwana?......inaso zuwa gobe ku basu dalilin da zasu tsaneshi!" Ta furta muryarta cike da son kanta da kuma gaggawa a al'amarinta.
"Kuma ku fara nemo duk wanda yake tsoma baki cikin umarnina......ban damu ba koda kurkukun da muke dashi zai cika mu aro na maqota" Ta sake fada da zafi zafinta.
Cutting komai yayi,don iya haka kawai ya isheshi hujjar wannan ranar.....iya wannan ya isheshi tsanin farko.
"Kina gaggawa zaituna....kina gaggawa......da alama komai da wuri zai qare" Ya fada can qasan ransa sanda yake komawa sassansa a hankali.
Qarar da yaji kadan daga Device din kunnensa ya sanya ya taba kunnen.
"Akwai motsin daya dace muyi?,ko akwai abinda ya dace mu dakatar?" Suka tambaya daga can bangaren.
"Noo" Ya fada sanda yake murda handle na qofar.
"Let her make the mistake publicly.” ya fada sanda ya tura qofar ya sanya qafafunsa.
" Abu daya nakeso......adadin mutanen da ta kulle daga jiya zuwa yau dinnan......sannan....duk yadda zaku bada cin hanci ku bayar ta hikima,banason kowa ya wahala,bawa ko d'a.....me muqami ko farar hula".
"Done!" Ya fada daga bangarensa,muryarsa na nuna yadda yake enjoying aikin da gaske kaman yadda ogansa kuma ubangidansa haisam din ya karantar dashi ya samu horo kuma daga gareshi.
Ya koma ya samu dakin yadda ha barshi,ba wani abu daya sauya. Ya qarasa gabanta kaman me sake bincikar lafiyarta. Bacci take sosai har yanzu,irin baccin da yakeso tayi.
Tausayinta ya sake kame zuciyarsa. Baccinta take da nutsuwa da cikakken tunanin shi ne kad'ai safety d'inta,alhali entire palace already entering silent war
*_TURQASHI........me karatu?.....akace garin tone tone ko?,kaza take tono wuqar yanka kanta.....muje zuwa mu gani dai. NASARAR ko FADUWA.....wannan shine YAQIN TSAKANIN QARYA DA GASKIYA_*
*_WANNAN SHINE BIGIREN DA RAYUWA KE JUYAWA AKHNAN BAYA.....BA AKHNAN KAWAI BA.....DUKA JININ SULTANE MUHAMAMMAD HAMMUD.... WANNAN SHINE LOKACIN DA MAMMINA KE BURI A RAYUWARTA_*
*ZAMUJI KUMA ZAMU GANI IN SHA ALLAH*
*Hugumanku ce*
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 109* ________________________ *_Amintaccen gurin siyayya_*
*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*
*_BONONZA DA PROMO akai akai_*
*dukka sai a HUGUMA CLOSET*
*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*
*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*
*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*
*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX __________________________
*_W A S H E G A R I_*
Washegarin da tazo a cikin ranar juma'a. Juma'ar da take babbar rana me dumbin daraja ga dukka musulmi.
Safiyar da agadez ta wayeta da wani irin nauyi daga zukatan al'umma da dama da har yanzu sukejin mutuwar kamar yanzu yanzu aka yita. Ba kuma ga iyalan sultane din kawai ba......ga dukka al'ummar agadez din gaba daya.
Tun daga daren jiya zuwa safiyar yau din,duka fadar Masarautar agadez cikin shirye shiryen nadin sabon sultane suke. Sannu a hankali har sanda a wannin suka cika,baqi kuma suka fara isowa suna wucewa babban hall da ake nad'i a duk sanda yanayi irin wannan ya faru.
Manyan masu ruwa da tsaki ne cikin hall din,manyan malamai da masu fada aji cikin agadez,manyan hakimai da dukka dattawan azbin.
Taro ne daya amsa suna taro,saidai duk wanda gurin.....duk wanda zaka gani ba farinciki bane ya kawoshi gurin ba.
Motsa hannunta akhnan tayi wanda yake cikin na haisam,hannun da ko sau daya bai taba sakinsa daga cikin nasa.....hannun da gake riqe dashi bayan kowanne minti don qarfafarta a duk sanda take shirin rikicewa......don bata tabbaci a duk sanda takejin bata da wani sauran tabbaci. Yanzun ma matsa hannun nata yayi,a hankali kuma ya furta.
"I'm here" Kaman wanda yake tuna mata tana cikin kulawa da kariya. A hankali ya sauke idanunsa a kanta,sannan yabi inda take kalla da idanunsa.
Ahmad ne,wanda yake tsaye cikin shiga ta sarakuna,sarakunan abzin irin shigar da sultane yakeyi.
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali,wani irin tausayinta yana saukar masa. Bashi da nutsuwa ko kadan,sama da yadda bata da ita. Bayason ganin irin abinda yake gani a idanuntan nan. Rashin nutsuwa,tashin hankali,qin cin abinci,bacci ma ya tabbatar banda yana tsaye akai ba zata yishi ba.
"Sai yaushe?,sai yaushe zaki haqura?" Ya tambayi kansa yana jin qirjinsa yana nauyi da damuwarta.
Idanunta ta sake lumshewa tana jin sanda aka fara karatun wasu daga cikin dokokin masarautawa ahmad don rantsar dashi.
"Bappi zai alfahari dashi.......tabbas zai alfahari dashi" Ya furta tana motsa labbanta a hankali.
"In sha Allah.....in sha Allah" Ya fada yana sake riqe hannunta a tausashe idanunsa akan ahmad din. Jini baya qarya,koda anso batar dashi,koda kuma anso tozartashi. Yana tsaye ana shirin rantsar dashi......gaba daya ya juye sultane zam. Ya lumshe idanunsa a hankali yana budesu wasu abubuwa suna sake nauyi a zuciyarsa.
Muryar wanda keda alhakin jaddadawa sarki dokokin masarauta ya fara tashi,wanda dagashi sai karbar shahadar rantsuwa.
"Bisa ga tsarin masarautar azbin......"
“…idan babu wani cikas, Yarima Ahmad shine zai hau kujerar mahaifinsa.”. Gaba daya hall din ya dauki shuru,shurun da akan samu bisa al'ada idan dukkan wanda ke da ruwa da tsakin zaben dorawa ko nad'i ya amince da hakan.
Idanu morsa safiyya ta lumshe tana kiran sunayen Allah a zuciyarta. Tana sake jaddada girman zatin Allah.......tana kuma sake tsoro zuwa ga hukunci da iya sarrafa al'amura na ubangiji. An dauke ahmad tsahon shekaru tun yana yaro. Wanda tasan ba don komai bane babban dalilin sai gudun zuwan wannan rana ga abokan adawa. Yau ga ranar da ake gudun tazo. Yau ga abunda ba'aso zai tabbata......yau ga qaddarar da ake qoqarin gogeta zata wanzu.
Cikin abinda ba gaza minti daya ba sautin taku ya fara cika hall din. Wani taku me nauyi daya dauki hankulan duk wanda yake gurin suka kuma waiwaya zuwa babbar qofar shigowa gurin.
Mammina ce mutum ta farko data fara shigowa,cikin black royal tufafi dake bayyana ikon da take neman daukakawa. Daga bayanta kuwa bayine da hadimai masu kula da tsaro na sasannin sultane......'yan sanda harda sojoji a cikinsu.
Tsakiyar hall din ta iso,idanunta a bude tarwai
"A dakatar da wannan nadin!" Ta furta da madaukakiyar murya tamkar ba macen dake cikin takaba ba. Ta maida idanunta kan jami'an tsaro sannan ta aza akan ahmad dake tsaye.
"Hajiya zaituna" Muryar wazeer ta fada a rude tana dubanta.
"Dakata!......." Ta fada cikin fusata tana daga masa hannu.
".......Ba za’a dora wanda ake tuhuma da kashe Sultane akan kujerarsa ba!.” a hankali haisam ya lumshe idanunsa sannan ya budesu tar kan fuskar mammina. Yanaso ya gane a wanne jinsi zai sanyata?,yanaso ya fahimci mutum ce ita ko wata halittar dabbar ta daban?.
Wani irin girgiza ilahirin hall din yayi,dukkan wasu manyan fada dake gurin suka soma kallon kallo cike da zallar mamaki,qananun surutai suka fara tashi kadan kadan.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Nannie take fada a birkice idanunta dukka a waje. Rawa kawai ilahirin jikinta yake,mammina take kalla,kwanyarta a yanzun tana komawa shekaru talatin baya. So take ta dauko maga wacece wannan mamminan?,....wannan mamminan da suka qyamaci aurenta?.....wannan mamminan da magabatansu suka hana sultane aurenta.....wannan mamminan da ita kanta asali bata sonta.....amma kirkinta ya rinjayeta.....ya rinjayesu gaba daya suka manta da duk wani qishin qishin din bincike a kanta. Maida dubanta tayi ga morsa safiyya,idanunta a lumshe suke tamkar batason taga kowa da komai dake faruwa a gurin,saidai can qasan zuciyarta
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Astagfirullah" Take fadi a hankali tana maimaitawa.
Daya daga cikin dattawan masu zartawa ya dakatar da yamutsewar gurin,ya miqe yana duban mammina din.
"A dakata jama'a.......a saurara"
"Ku kamashi!" Ta furta gaba gadi kai tsaye.
"Me kike fada?,kin rasa hankalinki ne?" Ahmad ya furta yana takawa gabanta. Dukkanin idanunsa a bude suke tarwai,kamanninsa yana son komawa na wannan almaz din data raina a baya. Murmushi ta saki a nutse tana dubansa.
"Koda ka qaraso gurina.....ba abinda zaka iyayimin...." Ta fada tana jin zafin yadda daren jiya duka ta sanya a nemo mata shi,su bugar dashi da kayan mayen daya daina sha,ya sanya mata hannu a wadannan takardun sannan a yau ya tashi cikin maye a gaban kowa,saidai sama ko qasa ba ahmad din ba dalilinsa,abinda ya sanya ta qarfafa zarginta akan lallai akwai wanda ya sanar masa da wani abun,wanda babu wanda tafi maida hankalinta a kanshi irin HAISAM ALSAAMIT.
"......ko kunsan tsohon mashayi aka dauko a matsayin yaron sarkinku!" Wani irin hautsinewa gurin ya sakeyi
"Ku kamashi!" Ta sake fada saboda duk qaruwar minti daya tana jin kamar delay take jawo mata. Tanaso kafin sultane ya cika kwanaki bakwai a kabarinsa ita ta gama nata aikin. Tanaso kwanakin bakwai din suzo daidai da sanda zata gama hargitsa masarautar kuma ta tashi.daga wannan duniyar data dade qulle a cikinta. Ba wata duniya data taba dadewa haka zaune a cikinta tana jiran wani abu irin wannan duniyar.
"Ba zamu bari ku kamashi haka kai tsaye ba" Daya daga cikin dattawan ya fada.
".....akwai hujjojin da suka bayyana qarara suka kuma nuna yarima ahmad yana da hannu a mutuwar marigayi sultane" Wani d'an tittirnan mutum dauke da kaya irin na lawyers da tarin files a hannunsa ya matso gaba yana fadi gami da soma bude wani babban file cikin files din hannunsa.
"Wacce hujja kuma?" Morsa safiyya ta furta cikin ba zata tana bude idanunta tarwai a kansu. Idanu mammina ta aza mata......tanaso ko sau daya,ko sau daya wannan fuskar......wannan halittar RAZANI TSORO da FIRGICI ya nuna saman fuskarta. Saidai har a yanzun da take shirin fara yiwa iyalinta d'auki d'ai d'ai ba wannan alamun a tattare da ita.
"Rahotannin masu tsaro guda biyu..." Ya sake fada mutumin yana daidaita takardun hannunsa.
"An samu tabbacin cewa,a daren da sultane ya rasu,kaine mutum na qarshe daga shiga gurinsa,ka kuma fito da mintuna masu qarancin tazara Allah yayi masa rasuwa" Kallon kallo aka fara yi,kafin mutumin ya dora.
"Kuma masu tsaron sashen sultane guda biyu,mafi kusa da dakunansu sun shaida cewa.....sunji sabani tsakaninku kwanaki kafin mutuwarsa"
"Wannan qarya ce!" Ahmad ya fada cikin fusata yana motsawa kaman zai kaiwa me karanto bayanan duka.
"Ka nutsu.....nan fa ba mashaya bace" Mammina ta fada tana sakin murmushi.
"Tabbas haka ne" Muryar hadimin ta ratsa gurin yana matsowa tsakiya. Mahadi.....daya daga cikin mafi kusanci kuma amintattun da aka yarda sukai kusa da dakunan sultane.
"Naji sultane yana cewa bazai yarda da wasu abubuwan da yarima Ahmad yakeso ba......shi kuma yana fadin babu wanda ya isa ya masa shamaki da tsarikansa da abinda yakeso" Ya fada da yanayin da ba tsoro ko shakka a tattare dashi.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" Akhnan ta fada a hankali tana lumshe idanunta,tana jin kamar bugun zuciyarta zai dakata daga aiki. Hannunsa ya sake matsewa cikin nata zuciyarsa na bugawa sosai. Yana kallon yadda matar ta shirya qarya ha'inci yaudara da cin amana,takeso ta gamsar da kowa cikin salo me burgewa. Koda dukka jikinsa kunne ne......ba yadda za'ayi ya amince ahmad zai iya kashe sultane.....to ta yaya ma?,yaron da sultane din kawai ya sani?,shine duniyarsa?,shine kadai ya rage masa?.
"An kuma samu wannan" Mutumin yaci gaba da rattabo bayanai yana matsowa kusa.
"Menene?" Daya daga cikin dattawan ya fada.
"Guba ce......gubar da aka sameta a sassan yarima ahmad,bayan an samu ragowar irinta a matse matsin gadon sultane" Shock kowa ya shiga,wasu suka waiwaya suna kallon ahmad din,ciki harda akhnan da falaak.
Ba don sun yarda ba.....sai don yadda hujjojin sukayi hatsari da yawa....yadda hujjojin zasu iya shigar da shakka da kokwanto a zuciyar al'ummar agadez.
"Ahmad?....ahmad fa" Akhnan ta fada ita da kanta wannan karon tana matse hannun haisam a nata.
"Masarautar azbin tana da dokoki!!!" Mammina ta fada tana dukan table din dake kusa da ita. Shuru ya sake wanzuwa......ta juya tana karbar wata tsohuwar takarda daga hannun daya daga cikin masanan doka na masarautar.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 110*
".....Doka ta goma sha bakwai....."
“…ta bayyana cewa......duk magajin da ake zargi da hannu cikin mutuwar Sultane......”
“…za’a dakatar da nadinsa har sai an gama bincike.”
Wani irin shuru hall din ya dauka......shurun da kowa ke da tabbaci akan dokar. Kowa ya sani,haka dokar take a rubuce,kuma har yau har kwanan gobe ba abinda ya sauyata akanta masarautar take aiki.
"Kuma idan zargin ya shafi cin amanar jini…” ta fada tana dora idanunta akan ahmad dake tsaye dukka jinin jikinsa a daskare.
"…masarauta na da ikon tsare wanda ake zargi ba tare da jiran nadin sarauta ba.”
"Qwarai kuwa....haka yake a rubuce cikin doka" Daya daga zaune cikin dattawan fada ya fada saboda tsegungumi da suka fara tashi gurin. Doka haka yake a rubuce......amma kuma zukatan wasu basu kwanta da ita ba.
"Wannan ba tsari bane......bai kamata ba.....abune da hankali bazai dauka ba" Wazeer ya fada yana dubanta,jikinsa yana rawa saboda tashin hankali ga shekaru,idanunsa akan mammina. Waiwayowa tayi ta kalleshi,ta dade tana jin haushin mutumin,ta dade tana zarginsa akan hana ma ruwanta gudu sosai,tsakaninta da sultane ko kuma cikin fadar,yanzu ya jefa kansa cikin issue din da asali babu shi a tsarin
"Duk wanda zai hana a kama Ahmad......tabbas zai shiga sahun wadanda za'a iya tuhuma da hadin bakinsa......ku kama WAZEER......sannan ku kama Ahmad ku tsaresu dukkaninsu". Ta fada tana jin wata power.
Fara tattaki sukayi da wani irin energy,kamar wadanda zasu kama wani zaki.
"Aah.....bazai yuwu ba!" Falaak data kasa jurewa ta miqe tana fada dukka jikinta yana rawa.
Tsam morsa safiyya ta miqe.....ta damqe hannunta falaak cikin nata tana zaunar da ita.
"Ki nutsu falaak.....ki nutsu....me laifi shike tsoron kamu.....kamun Allah kawai muke shakka,don duk wani kamu na duniya ya biyo bayan na sarkin sarakuna!!!" Morsa safiyya tayi maganan da dakakkiyar muryarta da ba tsoro ko shakka a ciki.
"Ahmad jinin safeena ne.....jinin safeena ba tsoro a cikinsa.....jinin safeena halastaccen jini ne da ba abinda ya isa ya batashi ko ya gurbatashi......tana tsarkakakkiyar haihuwar da ba wanda ya isa ya taba wannan nasabar!!" Ta sake fada da muryarta data amsa a kowanne sashe na hall din. Saqonta yakai.....saqonta ya isa zuwa duk inda takeso ya isa. Ahmad da mammina,mamminan da ambatar suna safeena yaje ya mata tsaiwar mashi a zuciya.
"Dole na haramta kiran wannan sunan a gidan nan.....dole na shafeta har a bakinsu" Ahmad kuma maganganun sun sake daukan hankalinsa zuwa ga morsa dinne.
"Haisam......" Akhnan da bata fahimtar komai ta fada tana matse hannunsa da qarfi. Ahmad kawai take gani.....kuma ahmad ne kawai bataso a tafi dashi yanzu......wannan kawai shine matsalarta ba komai da ake tattaunawa ba.
"Pleeeaseee" Ta furta tana juyowa gareshi,fitar kalmar ya hade da fitar hawayen idanunta. Shi kadai ne take da hope.....shi kadai ne take da fatan yana magana komai zai canza.
Idanunsa ya daga a hankali ya zubewa ahmad su. Wani irin kallon kallo a tsakaninsu na tsahon wasu sakanni.
"The investigation should continue......and the low should proceed". Ji tayi kaman ya sanya hannu ya zabga mata mari.
" What?" Ta fada a gigice kunnuwanta suna kasa yarda da abinda taji. Kai ya gyada mata a hankali ba tare daya kalli cikin idanunta ba,don bazai iya kallon idanun nata ba.
"Idan har shi bame laifi bane.....gaskiya zata wankeshi" Ya fada Kai tsaye da wannan tarin nutsuwar tasa.
Yayi maganan ne idanunsa akan mammina.....yayin data sakar masa wani murmushi. Murmushin da zuciyarta ke yaudararta tana gaya mata ta fara nasara.....kuma itace da nasara har abada. Taku suka sakeyi guard din don isa gareshi dauke da handcuff.
"Ku dakata!" Morsa safiyya ta furta cikin wani irin zafi.