Kenza eBookz

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 63

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 63

L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 63: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 63. "Gate up" Ya furta a nutse sanda ya iso gabanta.…

3,367 words

"Gate up" Ya furta a nutse sanda ya iso gabanta. Idanunta ta lumshe tare da budesu gaba daya. Fushi ya kamata tayi dashi,haushinsa ya kamata taji......yaji ya kamata ta masa......amma ta kasa. Duk sanda zai kalleta da wadannan idanun.....duk sanda zai tsaya a gabanta duk sai taji kwarjininsa ya mamayeta. Tana jin yana kakkarya zuciyarta da kallonsa kawai ba tare da yakai ga yin magana ba.....hakanan ta samu kanta da d'ora hannunta cikin nasa sanda ya miqa mata tattausan tafin hannunsa.

Bata ankara ba ta jita lullube cikin faffadan qirjin nan nasa.....wannan faffadan qirjin daya zame mata wata mafaka ta samun nutsuwa da duk duniya bata jin akwai wani guri da zata samu shigen wannan nutsuwar. Wannan faddadan qirjin dake cike da tausayi rahama da kuma jin qai. Wannan faffadan qirjin dake cike da hikima yake lullube da jarumar zuciyar da kullum idanunta ke kalla da wani irin alfahari.

Ajiyar zuciya taji ya sauke har sau uku,kaman akwai wani abu a boye dake damunsa. Ya lumshe idanunsa yana jin yadda wannan dumin nata dake bashi comfort yake ratsa gabbansa a hankali yana tayar masa da wannan feeling din da yakai wani saqo ya binneshi da zummar adanashi zuwa wani lokaci.

Sai daya tabbatar ya aike ma da zuciyarta nutsuwar da zata isheta na awannin,sannan ya janyeta yana motsa wadannan labban nasa da take matuqar so.

"Get dressed" Ya fada yana rarraba kallonsa tsakanin blue eyes dinta da suka rame kadan.

"Ina zamu?" Ta tambaya tana motsa tiny lips dinta daya gaza jurewa,sai daya matsa da bakinsa yakai musu sumbata kadan.

"Zaki gani" Ya fada yana riqe tsintsiyar hannunta softly.

Kai tsaye ya bulla da ita bedroom din da suka zabi kwana a ciki tun ranar da suka sauka a agadez din. Yace dai ta shirya,amma ja tayi ta tsaya,tana kallonsa ya bude bangaren daya adana mata kyawawan hijaban da aka dinkasu da wani irin dinki me aji da tsadajjen yadikan da ko sunansu bata sani ba. Ya ciro wani dark coffee ya wareshi,ya sanyata mata,sai ya juyata zuwa fuskar madubi yana daure mata igiyar hijabin,fuskarta da tasa dukka suka bayyana,ya zube mata qwayar idanunsa yana kallon fuskartata yana jin wani abu me qarfi a kanta yana ratsashi,tun daga fatarsa har zuwa jini da b'argonsa.

Ya ci gaba da daure igiyar hijabin a hankali kamar wani abu mai daraja da yake tsoron ya b'aci. Itama sai ta kasa d'auke idanunta daga reflection d'insu cikin mirror d'in.

Yadda yake tsaye a bayanta… yadda dogayen yatsunsa suke gyara hijabin nata da nutsuwa......komai nasa yana saka zuciyarta bugawa da wani irin nauyi.

Daya kammala bai matsa baya,sai yaci gaba da tsaiwa kusa da ita.....ba kusa kawai ba.....wata irin kusa da har jikinsa yana gogar nata,idanunsa cikin nata ta cikin mirror din.

"You look dangerous.” Ta d'an had'e gira saboda yadda ya fad'i kalmar cikin low voice d'in nan nasa wadda ta tilasta tsigar jikinta zubawa. Kamar dai zuciyar da gangar jikin sunason mantawa da yanayin da take ciki,kamar dai suna gaya mata MUNA KEWARSA.

"Dangerous?" Ta fada da wata murya kamar meyin rad'a. Sai ya d'an sunkuyar da kansa kusa da kunnennata.

"Mm" Ya fada yana sauke wani irin nannauyan numfashi. Ya sake maida idanunsa kan fuskarta ta cikin madubin ba tare daya d'aga kansa ba.

"Beautiful enough to make a sane man forget himself.” wani abu me sanyi taji yana bin dukka sassan jikinta,sai ta kauda idanunta daga mirror d'in saboda kallon nasa ya fara kassara mata qafafu.

"Kana yawan fad'in abubuwan da suke rikita mutum.” wani lallausan murmushi ya saki,qaramin murmushin dake nuna zallar miskilancin dake b'oye a bayan izzarsa.

"And you keep doing things that make me say them.” ya fada yana narke mata da wannan sakalcin nasa daya kwana biyu bai gwada mata ba.

Lips dinta ta hade dukka ta tura cikin bakinta don tana qoqarin hana kanta yin dariya. Sai ya d'aga hannu ya gyara d'an gashin daya kwanta kusa da goshinta yana maidashi sosai cikin hijabin. Yatsunsa suka d'an shafi fatarta lightly. Idanunsa ya lumshe saboda wani saqo da hakan ya aike gabbansa suna gaya masa kamar kusancin ya masa yawa.

"Haisammm" Ta kirashi da wannan sunan.....ta kirashi da wannan yanayin da yake qishirwar ji a tattare da ita

"Me yasa kake kallona haka?" Ta tambaya don da gaske yana narkar mata da zuciya ne kawai,a yanayin da takejin duka irin wannan abubuwan dole tayi nisa dasu,don har yanzu tana jin rashin sultane a tattare da ita. Sai ya bud'e idanunsa slowly ya sake had'a su da nata a mirror din da wani irin intensity.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 113* _________________________ *_SHUWA INCENSE AND MORE_*

😊 *_kai daga jin sunan basai an gaya maka ba_*

*_kai daga jin sunan basai ka tambaya ko tsaya tunanin maganar me ake ba_*

*_MAGANA CE TA GIDAN QAMSHI_*

*BAFA GAMA GARIN QAMSHIN DA KIKA SABA JI BA HAJJAJU*

*KINA QONA TURARE YANA QAURI*

*KINA SAKA KHUMRA TANA BIN SHANUN SARKI*

*WANNAN DIN TURARE NE DAKE DAWWAMA A DAKI DA JIKI.....DA SALON QAMSHIN DAKE MANTAR DA ZUCIYA DUK WANI B'ACIN RAI*

*TASTED AND TRUSTED👌👌👌100% HAJJAJU*

*NA DABANNE A CIKIN NA DABAN*🙌🏽🙌🏽

*idan akazo kan SHUWA INCENSE an tashi magana*

*idan ma kinsan baki shirya jan magana ba a duniyar qamshi to kisha zamanki hajajju*

*_zaku iya magana da ita kai tsaye ta wannan number wayar_* +234 704 229 3387 __________________________

"Because every time I look at you…” sai ya sake sassauta muryarsa sosai tana yin can qasa.

"..…I feel like Allah spent extra time creating you.” da qyar ta iya qwatar numfashinta ta kuma saukeshi a hankali saboda yadda ya sanya zuciyarta na bugawa da wani irin qarfi.

Juyowa yayi da ita a tausashe da wani irin sanyi tana fuskantarsa sosai har suna musayar numfashi. Kallon da yake mata yanzu sanyayar mata da kowacce gaba yakeyi da wani tarin sonshi da qaunarsa.

"Sannan.....wannan hijab din....." Ya furta hana mutsuka yatsunsa saman kafadarta da wani irin softness kaman yadda tantance sulb'in yadin.

"...…is already testing my patience.” wata irin kunya ce ta taso ta lullubeta,ta kuma fahimci sarai abinda yake nufi.....amma sai takejin zai mata nauyi. A irin wannan lokaci?,a masarautar?.

" Haisaammm" Ta kirashi da wannan sound din da wannan yanayin. Sai kawai ya langabar mata da kansa kamar wani innocent man.

"What?" Ya fada a narke yana sauke mata murmushi. Boye fuskarta tayi cikin qirjinsa tana jin wani sanyi da sassauci yana saukar mata. Ba shakka MIJI NA GARI duniya ne.....a kowanne rashi da mace zatayi....kowanne irin maraici da zata fuskanta,muddin akwai miji na gari....komai zata fuskanceshi da wani irin sauqi da sassauci.

"Muje kiga abinda na kawo" Ya fada yana janyeta daga jikinsa yana saka mata takalmanta.

Hannunsa cikin nata.....ba tare da damuwa da mutanen da suke wucewa ba dama me kallonsu. Cike da wannan kulawar da tattalin suke takawa. Yana mata hira kadan kadan da ta sake dauke hankalinta,sai gasu a babbar bargar dawakai na gidan.

A nan dawakanta suke.....da dukkan wasu dokuna da sultane keji dasu. Dokuna masu tsadar gaske da wasunsu ma kyauta ce ake bashi daga sarakai na qasashe daban daban.

Zuciyarta taso ta karye,amma daya dafa kafadarta ya juyo da ita tana fuskantarsa idanunta cikin nasa sai wani abu ya sassauta daga zuciyarta.

"Kin shirya?" Ya tambaya da kulawa. Kai ta gyada masa a nutse duk da yadda zuciyarta ke bugawa kadan kadan,saboda gurin ya tuna mata abubuwa masu yawan gaske game da sultane. Tun daga quruciyarta zuwa girmanta da rabuwarta da gidan dalilin aure.

Hannu ya sanya da kansa ya bude mata,saboda cikin gidan sam baya yawo da guards dinsa. Musamman idan har tare yake da ita,tana mamakin yadda yake kaffa kaffa da ita.

Suna sanya qafa wata kyakkyawar Arabian mare ta fito(macen doki ingarma na musamman,irin wanda su kansu masu dawakin sunsan na dabanne).

Idanu akhnan ta waro waje wani numfashin mamaki yana qwace mata.

"Ma sha Allah....tabarakallah" Ta fada da sautin daya sanyashi waiwayawa ya kalleta. Abubuwa da yawa.....dabi'u da yawa nata sun fara sauyawa zuwa na koyarwar musulunci sosai. A baya zata ce wow ko wani abu makamancin haka....amma a yanzun kalaman bakinta sun sauya ba tare data sani ba.

Zame hannunta tayi daga nasa tana isa gaban dokin da wani irin d'oki. A hankali tayi d'age saboda tsahon dokin,ta dora hannunta saman wuyanta tana shafawa a hankali. Kamar tasan waye a gabanta sai itama dokin ta sunkuyar da kanta.

Hannunsa nade a qirjinsa yana monitoring irin walwala da farincikin daya gani cikin idanunta,wadanda suka bace bat daga randa rasuwar sultane ga shiga kunnenta. Iya wannan kawai ya isheshi nasa farincikin shima. Waiwayowa tayi tana kallonsa.

"Ina ka samu irin wannan dokin?" Ta fada da murmushi,saidai bayan maganan ta fito sai taji tambayar ta mata banbarakwai bayan kwanyarta ta dawo mata da hoton WANENE HAISAM din.

Da tarin sauqin kan nan nasa sai ya saki murmushi,ya sauke hannuwansa yana takowa cikin nutsuwa inda take tsaye.

Hannunsa ya d'ora saman dokin yana tayata shafashi a nutse

"You still remember that race?” ya fada yana saka idanunsa a nata.

"No" Ta fada a hankali tana dubansa itama da blue eyes dinta dake wani shining ta siririn hasken almurun. Taku uku ya qara,ya kama hannunta suna matsawa daga gefan dokin kadan,ya sanya hannuwansa dukka yana riqe da qugunta suna musayar numfashi a tsakaninsu.

"Kin manta?.....You chased me for months after that.”

Numfashinta ta riqe a hankali,hippodrome yana dawo mata fes a kanta kamar yanzun komai yake faruwa.

Wannan qwararren mahayin daya fara sanya mata tsorom tsere na farko a duniya....boyayyar fuskar nan.....wadannan idanun da su kadai suka bayyana kansu.....sai faduwarta ta farko rashin nasarar farko cikin rayuwarta.

"Kaine?" Ta fada da wani irin excitement a fuskarta tana waro idanunta gaba daya waje.

"You were the rider at Hippodrome?” ta sake maimaitawa da alamun dake nuna ta dade tana zargi dama.

Qasa yayi da kansa kadan,murmushi yana qwace masa.

"The one who stole your trophy.” ya fada da wannam ginshirar tasa. Idanu ta zuba masa cikin tuhuma

"You let me spend all those years looking for you?!” dariya ce ta subuce masa....karon farko da taji nutsatsen sautin dariyarsa tunda take dashi,sai kuma abun ya mugun qayatar da ita ta sake zuba masa idanu sosai tana kallon yadda yau dariya ba murmushi ba suka masa kyau.

"You looked angry enough to stab me if you found me wallahi." Ya amsa mata yana ci gaba da dariyanshi harda dan janye kafadarsa baya kaman da gaske tsoronta yakeji.

Hannunta ta dunqule,tadan kaiwa qirjinsa duka tana danne dariyarta data tuna yadda ta zama frustrated sosai a sannan sabodashi.....saboda abinda yayi mata.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Haisammm" Ta kira sunansa kamar me magiyar ya daina mata dariya. Qugunta ya sake kamowa yana matsowa da ita,saita sake dukansa kamar me son turashi baya.

"You should’ve seen your face when you lost.” ido ta sake zarowa waje.

"I never lose!"

"You did that day...." Ya fada cikin salon tsokana yana sake matsowa jikinta.

"....to me" Ya qarasa fada da calmness.

"Ha'intata kayi....you cheated" Ta fada tana narke idanunta a kansa.

"Mm..." Ya fadi yana kulle idanunsa cikin nata.

"How?" Ya tambaya da innocent tone.

"Ka boye fuskarka ne ai"

"....inda kin ganni a wannan ranar gimbiya....." Sai ya dakata da salon sabuwar tsokana.

"Definitely you wouldn’t have focused on the race.” sai ta kasa magana. Saboda yadda yake kallonta yanzu,kamar ya san adadin tasirinsa a kanta completely.

"The eyes...."

"I know those eyes" Ta fada da muryar rad'a. Matsowa ya sakeyi sosai kusa da ita,har tana jin dumin numfashinsa dake fita gauraye da qamshinsa.

"Kin gane ni ta idanuwa na?" Ta gyada kai a hankali.

"They irritated me first.”

"Then they stayed in my head". Wani abu mai qarfi ya wuce cikin idanunsa,sannan ya zarce zuwa zuciyarsa. Tana sake bud'a masa wani rufaffen sirri na zuciyarta.....rufaffen sirrin da ba wanda ya sani a yau....sai yaji tana sake lalata zuciyarsa.

"Good" Ya fada yana lumshe idanunsa da budesu.

"Good?" Ta tambayeshi tana hade girarta.

Murmushi ya sake kubce masa. Ya daga hannu yana shafan gefan fuskarta a tausashe. Ya masa....hakan ya masa,yana sake sanin cewa baiyi kuskure ba da irin zurfin da soyayyarta ya bari ta masa,tun daga ranar farko....tun a ranar datace ta kasa mance idanunsa,shi ya kasa mance komai nata ne....tun daga wancan ranar yake kokawa da komai da zai tuna masa da ita don ya fuskanci aikinsa....ashe qaddararsu tana kulle ne a guri daya.

"I hated the thought that another man’s face might stay in your memory longer than mine.” ya furta yana jin tsananin kishinta cakude da matsananciyar soyayyarta suna gware a zuciyarsa. Hannunta ta d'ora saman nasa hannun,tana sake nutsa idanunta cikin nasa,tana sake karantar zurfin son da yake mata.

Saidai hayaniya qaqqarfan sauti kuka da haniniyar dawakai ta ratso da katse musu wannan daddadan yanayin.

Dukkaninsu suka waiwaya cikin mamaki suna duban daya qofar,sannan a tare suka taka zuwa bangaren.

Wani irin yanayi na zallar mamaki ya bayyana saman fuskar Akhnan. Dawakai ake fitarwa.....dawakai kuma na sultane ma ana loda su cikin wata mota da suke hangowa daga can inda suke tsaye. Dawakan sultane masu tsada da daraja.....wasu dawakan ma baya hawansu tsabar sabo kawai ana kiwonsu ne ana kula da lafiyarsu gami da fiddasu lokaci lokaci sdon su motsa jikinsu.

"No!" Ta fada da madaukakin sauti ba tare data shirya ba sanda ta hangi mammina na bada umarni gami da magana da ma'aikatan dake fita dasu.

"Ku kula da fararen can.....suna da tsada sosai.....wanda yafi biyan kudi me yawa a sallama masa" Maganarta ta kawo har nan inda suke tsaye.

Da wani irin shock ta juya tana kallon haisam

"Sai dasu take.....dawakan bappi.....abun debe kewarsa" Idanunsa ya lumshe ya kuma budesu lokaci daya yana duban Akhnan din.

Yadda yayin sai zuciyarta ta gaya mata bazaiyi komai ba akai ba.....bazai dauki mataki ba,don haka ta qwace hannunta cikin ba zata ta taka zuwa gaban ma'aikatan.

"Wadannan dokunan bappi ne....yanason dokunansa!!" Ta fada a tsawace kaman fushin yanason fiddata a saiti.

"Ranki ya dade kiyi haquri.....umarni aka bamu na fidda duk wani abu me daraja daga gidan nan a yau dinnan". Sai a sannan mammina ta lura dasu......da wani irin taku me cike da izgili take matsowa gurin.

Bata taba jin ta rainashi ba irin yanzu.....ashe damisar kwali ce shi?,kwarjinin daga nesa ne kawai?,zaton duk da take zai zame mata cikas ashe ba haka bane?. Tanadin data masa duk taji yana zuba,na meye ma zata tsiyayar da energy dinta akan wanda bai isa ya dakatar da ita da komai ba?,bayan saura kadan aikinta ya kammala?,saura kadan ta cika dukka burikanta?. Idan wannan dad'adden burin ya cika sai taji dashi daga baya,kwana daya ne tak ta gama dashi.

"Kaima kazo ne ka kwashi rabonka ka tarar an rigaka ko?. Allah sarki.....duk da ibraheem nada dukiya sosai ta gasken gaske.....amma banajin d'ansa zaiyi qoshin da abun wani zai gaza burgeshi". Cak maganan ta masa tsaiwar mashi cikin kunnuwansa.

" Karka yarda kome zatayi ya tunzuraka inde akaran kanka ne da mu iyayenka.....kome zata furta" Ya tuna maganan motii dashi ta qarshe. Hannunsa ya dunqule da qarfi yana cije haqoransa yana qoqarin controlling kansa.

"Mammina!.....kinsan irin kuskuren da kikeyi?.....me kike shirin aikatawa......kayan bappi?....dukiyarsa.....alamar mulkinsa?" Sheqeqe ta kalli akhnan dake magana kaman zata shide.

"Kayan mamaci?....me zamuyi da kayan mamaci?,shi kansa qasa yanzun ta fara cin namansa bare abinda ya mallaka.....dole mu share tarihinsa" Ta fada kalmarta ta qarshe tana fita da murya qasa qasa.

Yaga meye a idanun akhnan a sannan......yasan kuma makamin da mammina keson amfani dashi kenan ta fiddata daga hayyacinta. Tayi abinda bai dace ba a idanun mutane,don haka taku uku kawai ya isa gaban matarsa,ya kuma kamota ya sanyata cikin jikinsa ya rungume ba tare da shakka ko kunyar kowa ba,ma'aikatan wadanda suka juya da sssarfa suka fice,ko kuma mammina da tayi mutuwar tsaye tana dubansa da wani mahaukacin qiyayya da takejin kamar ta sanya musu wuta a take a gurin.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 114* ________________________ *_Amintaccen gurin siyayya_*

*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*

*_BONONZA DA PROMO akai akai_*

*dukka sai a HUGUMA CLOSET*

*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*

*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*

*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*

*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX __________________________

Cikin kunnuwanta yake rad'a mata wasu abubuwa,wasu irin kalamai masu saukar da wani irin sanyi ga zuciya. Kalaman da suka sassauta mata zuciya ta dinga sauke ajiyar zuciya shi kuma yana sanya yatsunsa yana dauke mata hawayen.

"Kina sonsu ne gaba daya?" Ya mata tambayar ba tare data zaci haka daga gareshi ba. Jiqaqqun idanunta ta daga ta kalleshi.

"You're buying them back?" Ta fada da dusashiyar murya. Wannan murmushin dake da hatsari yayi.

"Would you rather strangers keep pieces of your father?” wani lafiyayyen murmushi ne ya qwace mata,ta riqeshi qam qam cikin jikinta idanunta suna tara sabbin hawaye. Godiya takeson masa amma batasan ta wacce hanya ba.....ta kasa magana gaba daya,sautin mammina ya sake ratsasu.

"Da wanne arziqin zaka iya siyan dawakai masu tarin daraja irin wannan?,da albashin kudin bincike?,zamu gani" Saita taka tana daga murya.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Kowanne d'aya inaso a ninka farashinsa ga duk wanda zai siya". Idanu suka hada da akhnan,abinda ya gani a idanunta suka sanya tausayinta ya kusa narkar dashi. Kamar tana tuhumar kanta.....me yasa ta zama uwa a gareta?,kamar tana tambayar kanta ya akayi ta shigo ahalinsu?,kaman kuma tana tuhumar me yasa sultane ya aureta?. Kai ya jinjina mata yana mata wani kyakkyawan riqo,kafin ya dagata cak ya rabata da qasa yana rungumeta a jikinsa. Murya can qasa.....ya kuma kulle idanunta cikin nasa yana hanata kallon kowa ya soma mata wata magana qasa qasa,wadda ta sanyata kwantar da kanta cikin qirjinsa tayi luf.

Wani mugun tsaki mammina taja tana binsu da mummunan kallo. Ba abinda zai hanata tsinke wannan igiyar soyayyar. Tasan ibraheem.....kome akace yaronsa zaiyi akan matarsa na sadaukarwa ba zatayi mamaki ba.

"Aikin banza.....ka dauka kudin wadannan dokunan kamar kudin siyan littafi ne?". Sautin ya isa kunnensa,amma ya hana akhnan taji da zaqaqan kalaman da yake karanto mata har tana jin duk wani bacin ranta yana kwaranyewa.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 115* ___________________________ https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0

*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*

*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*

*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*

*_Assalamu alaikum my loyal people_*

*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*

*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*

*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*

*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*

*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*

Readers Also Read

More by Huguma