Kenza eBookz

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 65

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 65

L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 65: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 65. Da idanu kawai take kallon Akhnan,tana jin zuciyarta…

3,344 words

Da idanu kawai take kallon Akhnan,tana jin zuciyarta tana bushewa. Sai yau idanun Akhnan suka fara budewa tarwai kenan take kallon ainihin siffa da kamannin matar?,abinda yake yawo kenan cikin kan falaak wadda kanta ke kwance saman cinyar hairaan dake share hawaye tun dazun ta kasa ma magana.

A fusace ta miqe,ta gaji,tana buqatar yiwa mammina wadannan tambayoyin kai tsaye. Tana buqatar ganinta ido da ido,taji meye manufarta......meye matsayarta?,meye dalilinta na hargitsawa da dagula duk wani abu me kyau da sultane ya bari. Tarihi....Kyakkyawan mulki da kyakkyawar mu'amala.

Basu dakatar da ita ba.....hakanan kan hanya ba wanda ya dakatar da ita. Har haisam dake takowa zuwa bangarensu don bai shigo ba tun sanda zaman ya tashi,shima baga ganshi ba,idanunta ya riga ya rufe. Shima bai tsaidata ba,duk da baisan inda ta nufa ba,sai da yaga tana dosar shiyyar private chamber d'in Mammina.

Da idanu yakewa guard din dake hanya umarni,haka suka dinga matsa mata salin alin ba tare da cikas ko kallonta ba. Guard's din da mammina din ke ganin ta gama mallakarsu da dukka ayyukansu.

Qofar ta bud'e da qarfi. Mammina dake zaune cikin nutsuwa da annashuwa da wani golden cup a hannunta ta daga idanunta tana kallon Akhnan din,ba tare data motsa ba.....saidai can qasan ranta tana tambayar kanta abinda ya kawo yarinyar. Ba ita take tsammanin gani ba.....haisam taketa lissafin sanda zai tattaki ya sameta don nemawa mutanensa sassauci.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 117* __________________________ ✨ AMINTACCEN GURIN SIYAN THRIFT ABAYAS ✨ Ingantattun Thrift Abayas masu kyau da tsari akan farashi mai sauƙi da araha. Muna kawo sababbin kaya akai-akai tare da rangwame na musamman. 🤍 Dukka sai a MK ABAYA BOUTIQUE 🤍 Duniyar Thrift Abayas masu kyau, masu tsari, da salo iri-iri domin kowane lokaci da kowane irin event. Abayas masu inganci, masu salo, masu araha, kuma na zamani ga mata masu son ƙawata kamanninsu cikin kamala da kamun kai. Karki bari a ba ki labari... Leƙo ki ga yadda MK ABAYA BOUTIQUE kullum ke cike da kyawawan Thrift Abayas akan farashi mai kama da kyauta. 'YAN SARI, 'YAN REPOSTING, DA MASU SIYA DON AMFANIN KANSU... DUKA INA MUKU MARABA! 🤝🤍 📱 WhatsApp: 07064399623 📞 Call: 08036027448 🔗 Join our Wholesalers Group: https://chat.whatsapp.com/JBg80RmA47v7GoqvWdgLJT?s=cl&p=a&mlu=3 _________________________

“Me yasa?!” ta jefawa mammina tambayar tana kallon qwayar idanunta da wani irin zuzzurfan kallo da bata taba ganin irinsa cikin idanun Akhnan din ba.

“MEYASA kike mana haka?!” sai mammina ta d'ago idanunta a hankali.

“Ki rage murya.” ta fada cikin nuna isa da taqama.

“morsa safiyya fa?,me ta miki?" hawaye suka gangaro mata.

“Ahmad fa?,shima me ya miki?" Ta fadi tana samun tabbacin akwai dalilinta na shirya musu haka.

Takawa ta sakeyi,ta qarasa kusa da ita tana jin zuciyarta tana tsatstsagewar,fushi da kokwanto suna rinjayarta.

“Ke ce kika raineni…” sai muryarta ta fara karyewa.

“Ke ce kika bani kulawa…”

“Me ya sauya yanzu?!”

Shuruuuuuu......mammina ta zuba mata ido na wasu seconds. Sannan ta saki dariya. Not warm laughter. Wata baqar dariya da tayi qaramar amsa kuwwa cikin dakin,wata dariya data kusa fasa zuciya da kwanyar Akhnan.

Akhnan din ta tsaya cak,saboda bata tab'a jin dariya haka daga gareta ba.

“Sauyawa?” ta jefawa Akhnan tambayar,tana mata wani qasqantaccen kallo still dariyarta kuma bata tsaya ba.

“Akhnan…” ta kira sunanta,sai ta ajiye cup d'in hannunta a hankali.

“Kin rayu cikin qarya ne shekaru da yawa.” ta fada idanunta kai tsaye cikin nata tana zurfafa kallonta a kanta.

“…Me?” Akhnan ta fada tana jin tunaninta yana girgiza.

Miqewa mammina tayi a hankali,ta qaraso kusa da ita. Idanunta cike da wani irin tsohon qunci......kwadayin d'aukar fansa da tsumammen rashin imani.

“Kin tab'a tambayar kanki…” sai tayi qasa da muryarta.

“…me yasa na d'auke ki bayan mutuwar uwarki?”. Da Akhnan zata iya tabbas data girgiza mata kai alamun aah.....amma saita zabi ci gaba da kallonta kawai.

"Banyi saboda Allah ba.....saboda ni ban iya abu bati siddan ba....ban kuma iya abu na jira Allah ya biyani ba,nafi ganewa duka d'auka,nayi a take.....na samu sakamakon alfanun a take" Sai ta dakata tana sauke numfashi.

“sannan banyi ba saboda wani INA SONKI BA.....ban taba sonki ba Akhnan,koda na qasa da second daya!" Akhnan ta ji wani abu ya tsaya mata a qirji da wani irin nauyi kaman tana shirin faduwa,har sai data dafe wani table.

“…Mammina?” ta kira sunanta muryarta na fita da qyar tana rawa kaman mejin sanyi.

Sai Mammina ta matso kusa sosai.

“Na raineki ne…” ta fada idanunta suna sake qanqancewa da wani irin duhu.

“…saboda in tunasar da ita ta taba qwace a duniya......saboda a sanda take kwance a kabarinta ta tuna akwai wadda ta taba qwacewa abu duniya.....na raineki ne don na dauki fansa.....na aura miki dan uwanki almaz.....ahmad a yanzu bayan na saceshi da quruciyarsa.......na raineki ne don ko sanda tana ramin kabarinta kada ta huta......ko sanda tana ramin kabarinta ta d'an d'ani baqincikin da bazata iya tarewa 'ya'yanta ba......shi yasa na raineki da qiyayayar safiyya,don kada ta zama silar tsiranki” ta dakata tana maida numfashi. Wadannan maganganun data dade da binnesu tana binta da murmushin fake qauna,tana jin a yau ta shirya furzar mata dasu kafin takai rayuwarta mahallaka. Kamar zararriya haka akhnan ta zaro ido,tana jin kamar kowacce gaba dake jikinta ba'a jikin nata take ba. Tana jin kamar hauka ta fara kwanyarta ta samu damuwa shi yasa take rattabo mata wadannan bayanan.

“Uwarki.” ta fada da d'aci sosai a muryarta da bai boyu ba

“itace mace ta farko da wasu 'ya'ya maza har biyu suka sota kafin ni......ajani.....sannan kuma sultane.....ita kadai ta kafamin wannan tarihin da har na mutu bazai goge ba!."

Wani irin sanyi ya ratsa Akhnan. Qafafuwanta suka kasa motsi tana fatan wani ya tasheta a wannan mafarkin.

"Guraben da nake muradin mallaka......ita ta qwacesu ta mallakesu.” ta fada da muryar dake nuna tsohon ciwo.....tsohon miki ya tashi.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

“ta bashi 'ya'ya......ba d'aya ba.....ba biyu ba kafin na bashi koda rabin mutum....ke koda b'ari ne......sannan safiyya tazo ta sake laftamin wani ciwon ta hanyar bashi falaak?.” Akhnan ta soma girgiza kai,wasu iri hawaye da basu da misali.....hawayen da baka isa kayi controlling d'insu ba suka soma mata ambaliya.

“A'ah…” ta fada tana girgiza kai,tana jin kanta bazai d'auki wannan abun ba,kamar zaiyi tsawa.

"Eh!" Mammina ta fada da qarfi ta yadda zai isa kunnuwanta da kyau. Burinta ta qara hargitsewa ta yadda hakan zai sanadin haukacewarta gaba daya

“NA TSANETA!.” Sai ta sunkuyar da kanta kusa da Akhnan.

“lokacin data mutu…”

“ban so mata mutuwa ba a sannan......naso ta qare rayuwarta tana raye amma tana kallon yadda rayuwar d'iyarta take d'ai d'aicewa....bansan ma ya akayi rayuwarki ta tsaya a haka ba!....bansan waye ya tsaya miki ba!….” ta fada da qaraji kaman zata yage maqogoronta.

"Allah" Amsar da zaiso bata kenan.....amma ya zabi yaci gaba da tsaiwa behind the curtains and doors indai batayi yunqurin taba mata lafiya ba.

Akhnan ta ja baya da sauri kamar an mareta numfashinta ya rikice,kalaman sun mata nauyi da yawa.

“me kike cewa?....kinsan me kike cewa?."

Mammina kai tsaye da kallon nan tsirararsa ta zuba mata idanu .

"Ke ba 'yata bace!.....har abada!"

"Ke alama ce kawai ta tozarcin safeena a gareni!"

Akhnan ta soma girgiza kai cikin kuka. Gaba daya tana jin an dawo da quruciyarta yanzu tana rushewa daya bayan daya. Kowacce runguma?,kowacce nuna qauna?,kowacce kulawa?,kowanne murmushi?,kowacce soyayya fake ce?!.....jabu ce?!.....ba gaskiya bace?!.

“kinyimin qarya.....”

“ta shekaru da dama...…”

"Qwarai.....kuma na tsallake ba" Ta fada da iszgili a muryarta. Sai ta juya baya a hankali

"Soyayya ba ita ke tafi da masarauta ba........power ce!" Ta fada tana watsa mata wani kallo.

"Kina zaton soyayyar malamin can zata kubutar dake.....kina tsammanin d'an gidan ibraheem zai zame miki garkuwa?" Ta tambaya wata dariya na bayyana saman fuskarta.

"Kina ganin kin tsallake duk shirina a kanki?,.....ba zaki tsira ba Akhnan.....baki da gata a yanzu....baki da wanda ya tsaya miki.....sai yadda naga daman juya akalar rayuwarki".

Hannayensa ya dunqule,yana qoqarin hana kansa afkawa chamber din,da qyar ya dawo da control dinsa.

Akhnan tayi wata irin tsaiwa a wurin kamar wadda aka cirewa numfashi,wani irin ringing Kunnuwanta sukeyi kamar masu shirin kurumcewa. Zuciyarta na bugawa kamar wadda ke shirin kamuwa da ciwon zuciya.

“Kin san me yafi bani dariya?” ta tambayeta ba tare da ta juyo ba

“Yadda kika dinga kallona da idon soyayya shekaru.” kalaman suka fita da sautin qaramar dariya a muryar mammina din.

*_wai wai wai.😭😂.....lallai.....mara kunya yaji dadinsa. Ya Allah ka rabamu da makantar zuci.....kasa mufi qarfin zukatanmu_*

*_muje zuwa dai....saimun warware zaren duka in sha Allah_*😭😭

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 118* __________________________ ✨ AMINTACCEN GURIN SIYAN THRIFT ABAYAS ✨ Ingantattun Thrift Abayas masu kyau da tsari akan farashi mai sauƙi da araha. Muna kawo sababbin kaya akai-akai tare da rangwame na musamman. 🤍 Dukka sai a MK ABAYA BOUTIQUE 🤍 Duniyar Thrift Abayas masu kyau, masu tsari, da salo iri-iri domin kowane lokaci da kowane irin event. Abayas masu inganci, masu salo, masu araha, kuma na zamani ga mata masu son ƙawata kamanninsu cikin kamala da kamun kai. Karki bari a ba ki labari... Leƙo ki ga yadda MK ABAYA BOUTIQUE kullum ke cike da kyawawan Thrift Abayas akan farashi mai kama da kyauta. 'YAN SARI, 'YAN REPOSTING, DA MASU SIYA DON AMFANIN KANSU... DUKA INA MUKU MARABA! 🤝🤍 📱 WhatsApp: 07064399623 📞 Call: 08036027448 🔗 Join our Wholesalers Group: https://chat.whatsapp.com/JBg80RmA47v7GoqvWdgLJT?s=cl&p=a&mlu=3 ___________________________

Girgiza kai akhnan tayi,wasu irin zafafan hawaye suna wanke mata fuska

“Don Allah kiyi shiru…” ta fada cikin karyewa. Ji take kaman zatayi hauka.....kaman kwanyarta tana damulewa a duk kalma daya da zata fito daga bakin mammina.

"Abinda yake sake bani dariya shine......yadda kika dinga gudu zuwa jikina a duk sanda wani ya b'ata miki rai ko ya miki ba daidai ba....." Cak kalaman mammina suka tsaya cikin iska.....komai na quruciyarta yana dawo mata ana mata kamar wadda aka kunnawa faifan rayuwarta. Daga kai tayi ta sake kallonta.....tamkar ba itace wannan matar data tab'a rainonta ba?. Tamkar ba itace wannan matar data kira UWA ba.

"Ashe baki taba sona ba?" Ta fada tana zubawa mamminan idanu,tsantsar karaya suna nunawa cikin idanun nan nata da ruwan hawaye yake kwarara.

Murmushi tayi,irin murmushinnan me sanyi wanda yafi mari ciwo

"Na gaya miki ai....amma inajin kina buqatar maimaici ne.....so ko?.....kinsan me ake kira soyayya a fada?"

"Rauni" Ta qarasa maganarta.

"Amma kina rungumeni....kina cemin d'iyata" Akhnan ta furta cikin fitar hayyaci tare da jin komai yana zame mata kamar mafarki ko wasan kwaikwayo.

Juyowa tayi tana kallonta sosai,Idanunta babu taushi ko kad'an

“Ko kina tunanin rungumar da nake miki na gaskiya ne?” sai ta saki wata dariya me ciwo

“Duk lokacin da na kalleki…”

“…ina ganin fuskar uwarki." Riqe qirjinta akhnan tayi,numfashinta na sarqewa.

"Ki tsaya.....don Allah ki tsaya" Ta fada tana fatan ta tsaya din,tana fatan kuma ya zama mafarkinne. Saidai ko alaman ta tsaya ba tare data amayar ta tsiyayar da dukka magangun bakinta batayi ba.

"Uwarki ta samu abinda nakeso......wato sultane...."

"Tsahon shekarunnan yana bauta mata saboda sanyi da taushin halinta.....tsahon kuma shekarun da suka biyo bayan mutuwarta din ya gagara mantawa da ita duk da tarin kyautatawata a gareta,safiyya taxo ta sake lullube wannan gurbin da nake harin samu....."

"Na tsani yadda yake kallonta....." Ta fada muryarta na cracking.

"Na tsani yadda ya kasa mantata" Ta sake fada wannan zallar wutar qiyayyar na nunawa qarara cikin idanunta. Sake takowa tayi gabanta.

"Da Gaske na girmar dake.....saidai ki tuna,kowanne halin kirki nawa qwara d'aya.....yaqine ga mataccen jikin safeena".

Wani irin baya akhnan taja,tana jin yadda quruciyarta ke rugurgujewa a gabanta. Mammina ta gyara mata gashi sau ba adadi.....ta rungumeta sanda tana kuka.....ta tsaya mata a gurare masu tarin yawa.....mafi girma ta kirata da D'IYATA.....duka wannan FAKE NE?!.....qarya ce?.

"Ya zama dole a kanki ki godemin.....don na barki da ranki ba kaman yadda na salwantar da wasu ba.....na barki kin rayu cikin daular mulkin mahaifinki......ba kaman yadda na hana 'yan uwanki zama cikin tasu daular ba.....ahmad d'an sultane da safeena......da kuma d'an AJANI jinjirin da bashi da suna" Sai ta fara takawa da wani irin taku dake nuna zallar rashin imani a tare da ita

"Ke wace irin macace?" Akhnan ta fada a tsawace tana jin yadda take sake tarwatsewa a gaban mammina. Murmushi ta sake mata tana duban fuskarta.

"Mace me son nasara......abinda ya hanani cinyeku tunda wuri.....shine sultane.....yanzu kuma babu shi.....ba wanda ya isa ya dakatar dani daga dukkan shiri na....."

"Daga yau.....kada ki sake kallona a matsayi uwa!" Ta fada tana takawa zuwa qofar da zata fiddata a gurin.

"Saboda nima ban taba kallonki a matsayin d'iya ba......sannan....." Sai ta dakata.

".....ki shirya.....kece plan dina na qarshe.....ba kuma wanda ya isa ya kareki" Tana kaiwa nan ta bude qofar ta shige tana maidata ta kulle.

Yana jin takunta......yana jin takun wucewarta......amma baima kalleta ba,saboda dukka hankalinsa yana kan kowanne fitar numfashin akhnan da komawarsa. Qirjinsa na masa wani irin ciwo,yana jin kamar bazai dauka ba.....kaman iya abinda zai iya dauka kenan. Akhnan red line dinsa......wanda tabbas idan mammina ta sake ta qetarashi,komai zai sake muni sama da munin da yake dashi a yanzu.

Kasa motsi akhnan tayi,kamar jikinta ya manta yadda ake numfashi. Kamar qafafuwanta sun daina daukar nauyi.

“Mijina ya kasance nata kafin na zama komai…”

“Murmushin da nake miki yaqi ne…”

“Na rainaki ne saboda kina tuna min ita…” Kalaman suna ta maimaituwa cikin kanta. Idanunta suka soma rawa. Kwanyarta ta kasa karbar abinda taji,sai numfashinta ya fara qoqarin rikicewa.

"Aah.....aah....aah" Haka ta fada a jajjere tana dora hannunta akan bakinta wai ko zata iya hana kanta zubda hawaye. Gaba daya qirjinta taji yana mata ciwo,kamar an tsaga an ciro wata tsoka daga muhallinta.

Sai ta juya da sauri ta fito daga chamber d'in. Cikin takunta na tangal-tangal,kamar wadda tasha wani abun maye ta bugu. Hawayenta kawai sauka suke ba qaqqautawa. Cikin tsoro hadiman suke matsawa suna sauke idanunsu qasa daga kallon matar sheikh muhammad haisam din. A yanayinta kawai basu tab'a ganin rauni a tattare da ita ba irin na yau.

Ta kai qarshen corridor din da qyar,sai qafafuwanta suka kasa daukarta. Ta dafe bango da qarfi. Numfashinta na rawa.

A lokacin ne yake sake takowa zuwa gareta,cikin sassarfa da karsashi da tarin kuzarin nan nasa wanda a yau yakejin kamar ya zarta kullum,kamar jinin da zuciyarsa ke bugawa zuwa ga gangar jikinsa na yau ba irin na ko yaushe bane.

Qamshin nan nasa shi ya gaya mata shine ya iso gabanta. Ta d'ago idanunta tana dubanshi......suna hada idanu sai wani sabon kuka mai ciwo ya kubce mata.

“Haisam…” ta fada da wannan sautin da yakeso,saidai a yau wannan muryar ba irin wadda yake da muradin ji bace.

Bata iya jira ya risketa a inda take tsaye ba,ta soma takawa zuwa gare shi da sauri. Kamar mutum mai neman mafaka.

Kafin ta isa din qafafuwanta suka sake tangal-tangal da ita.

Tareta haisam yayi da sauri. Ya mata kyakkyawan riqo kafin ta kai ga fad'uwa. Da qarfi ta kama rigarsa ta riqe sosai cikin hannunta,yanayi riqon daya zame masa ma'auni na girman zafi da rad'ad'in da takeji a zuciyarta.

"Tayimin qarya......tasa na qare girmana tana yaudarata". Kallon fuskarta haisam yayi.....kumburarrun idanunta....rikicewar numfashinta kawai sai suke neman d'auke tasa nutsuwar. Ya sake matse haqoransa yana qara tilastawa kansa controlling abinda yakeji din.

"Me tace miki?" Ya tambaya cikin sanyin murya kaman baiji komai ba. Jikinsa ta shige sosai......dukka jikinta yana rawa. Daya bayan daya ta gaya masa.....sak yadda mammina ta fada baiji ta mañta ko ta rage abu ko qwara daya ba.

“Ashe duk shekarun nan…” ta fada ko ina a jikinta yana rawa.

“…ni ba d'iya bace a wajenta…” .

Hannunsa ya dago,ya riqe bayan kanta a tausashe. Ya jawota jikinsa sosai kamar yana qoqarin tattara dukkan b'angarorin zuciyarta da suka tarwatse.

“Ki kalle ni.” ya furta da wata sirrintacciyar murya me taushi. Sai ta d'ago idanunta cikin hawaye kamar yadda ya buqata.

“Abinda mugun mutum ya kasa bayarwa…” ya furta yana share mata hawaye

“…ba yana nufin baki cancanci shi bane.” wasu sabbin hawayen ne suka sake bin kuncinta bayan wadanda ya share mata.

Kamar wuta haka yake jin d'igarsu har cikin tsakiyar zuciyarsa.

"Kinjini?" Ya fada yana tattaro fuskarta a tsakiyar tafukan hannayensa.

"Rashin soyayyarta......" Ya fada da muryar rad'a.

"Ba laifinki bane" Sake riqe hannayensa tayi sosai tana girgiza kai hawayen sun kasa controlling kansu suma.

"Na yarda da ita.....na qaunaceta" Wani kallo me taushi ya bayyana a idanunsa.

"And that says more about your heart…”

"Than hers........" Ya qarasa fadi yana jin yadda numfashinta ke a rikice kamar zuciyarta ta kasa d'aukar nauyin gaskiyar da taji.

Da wani irin taushi ya mata muhalli me kyau a qirjinsa,ya kuma lullubeta da dogayen hannayensa,ya mata rumfa ruf ta yadda ta bace gaba daya a faffadan qirjinsa. Yana jinta,tana son sakeyin magana,sai ya lumshe idanunsa yana furta.

"Shshshsh..... Ki bari numfashinki ya daidaita tukunna"

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Qara mannewa tayi cikin jikinsa,tana sauke wani irin kuka me nauyin gaske. Hannunsa saman kanta yana shafawa a hankali har zuwa gadon bayanta. Idanunsa suna runtse,yana jin yadda bugun zuciyarsa ke sake motsawa da wani irin nauyin gaske.

"Bansan me yasa yakemin zafi ba......ya kamata na tsaneta yanzu" Ta fada muryarta na sarqewa da kukan.

"Ki tsaneta......ki tsaneta gwargwadon yadda zaki iya.......is allowed" Ya furta da wani taushi a muryarsa,idanunsa har yanzu a kulle. Ya fahimci ciwon da take ciki,mutum mafi kusa da ita tun tana yarinya...... ashe duk shekaru yana rayuwa da qarya......me yafi wannan ciwo?.

"Zakiji ciwo giiftii.....zakiji ciwo sosai....."

"......Mutum mai zuciya mai tsabta idan aka cuce shi…”

"...…ciwon yakan zurfafa.” Ta girgiza kai tana kuka a hankali.

“Na kira ta uwa…” Sai ya share hawayen gefen fuskarta da babban yatsansa yana dubanta a nutse.

“Kuma kin yi hakan da zuciya d'aya ba.” ya sake karkatar da kansa yana kallonta cikin idanunta

“Kar ki ji kunyar hakan.” sai ta sauke idanunta qasa.

“Amma ni wawiya ce…” tayi maganan muryarta tana rawa.

Yatsunsa ya sanya,ya dago habarta a nutse yana jin kalmar data gayawa kanta da kanta ta masa ciwo.

“Kada ki sake fad'ar haka.” yadan kausasa muryarsa.

“Kin ji ni?” Ta kalleshi cikin rawar ido irin na wanda ke qoqarin dakatar da hawaye.

“Mai yaudara ne yake da laifi.” ya fada yana cusa tafin hannunsa cikin nata.

“Ba wanda ya bada gaskiyarsa ba.” hawaye ya sake gangaro mata ta dukkanin idanunta biyun. Sai ya jawota jikinsa yana matseta sosai da wani irin dumi da taushi daya mamaye ilahirin jikinta.

Ya bari ta yi kukanta. Bai hanata ba. Saboda ya san: 👉 wasu ciwukan hawaye kad'ains suke iya rage su.

Na wasu seconds corridor d'in ya yi shiru. Sai sautin kukanta kad'ai,da bugun zuciyar Haisam da yake ji har kunnuwansa.

Ya bata tazara da ratar mintuna kafin ya motsa a hankali,ya d'an sunkuya kusa da kunnenta.

“Mu tafi?.” ya tambaya kamar me mata rad'a. Sai taji zuciyarta ta harba tana skipping na wasu sakanni daga aikinta.

“Ba zan barki a nan ba.” ya bata tabbaci yana sake gyara mata hijabinta daya sake fdda wannan marainiyar fuskartata.

Readers Also Read

More by Huguma