L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 66
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 66: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 66. Sai ya riqe hannunta cikin nasa. Ba kamar yadda yake yi…
3,357 words
Sai ya riqe hannunta cikin nasa. Ba kamar yadda yake yi kullum ba. A yau.....riqon nasa ya sake zama na musamman. Tamkar yana gayawa duniya da ita dashi kansa cewa. NINE GARKUWARTA NA HAR ABADA.
Ita dinma Ta kasa sakin hannunsa ko da sau d'aya. Kamar idan ta sake shi,zata sake fad'uwa ne....faduwar da ba ranar sake tashinta.
Da kansa haisam ya bud'e kofar. Ya jima da tsaida da kima dakatar da wata hidima duka data shafi akhnan din. Komai......kusan komai dasu birra ke mata shi yakeyi yanzun. Yayi tasa yayi nata. Takanji nauyinsa idan ta ganshi kitchen......yana dafa mata tea ko madara. Batasan wanne baiwa Allaj ya mata ba.....wacce irin nau'in kyauta Allah ya mata daya bata irin wannan LU'U LU'U da yafi komai tsada cikin nau'in kadara. Billionaire irin wannan......ita diyar muhammad hammud tayi sanadin shigarsa kitchen yana mata hidima?. Mutumin da idan yaso inda kuma yana da ra'ayi.....cook kowanne iri ne zai iya hiring ya kawoshi kawai don ya masa girki.
Yana lura da hakan,akwai kuma sanda ya rutsata da narkakkun idanun nan nasa,ya sanyata a tsakiya yana tareta da hannunsa ta hanyar dafe cabinet din kitchen din da hannuwansa.
"Kin dauka da wasa ne......idan nace miki ina karantaki ta idanunki?" Kai take qoqarin kawarwa saboda yadda kwarjinin nan nasa ke bugunta.
"A duniya babu wanda yakai muhammadurrasulillah daraja......duk duniya sun shaida haka ne?" Ya fada yana d'age girarsa. Kai ta gyada a hankali.
"Amna yana tsayawa a gidansa,ya taya matansa hidima". Maganan ta sauka a kunnenta da wani irin ma'ana da cikakken nutsuwa. Daga ranar.....daga lokacin wani girmansa ya sake ninkuwa a ranta da idanunta. Ko a labari.....ta jima bataga mutum me matsayi irin nasa ba,amma kuma bai dauki kansa a bakin komai ba.
Ya shigar da ita ciki yana kaffa kaffa da ita. Dakin yayi duhu mai laushi,nutsuwa.......da wata irin kwanciyar rai a cikinsa.
Ya sake matsawa ciki,sai ya cire alkyabbarsa ya aje gefe. Ya juya gareta. Har yanzu tana tsaye kusa da qofa kamar bata san me zatayi ba. Kyawawan farare kuma blue eyes dinnan jajur da alamun kuka.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 119* ________________________ ✨ AMINTACCEN GURIN SIYAN THRIFT ABAYAS ✨ Ingantattun Thrift Abayas masu kyau da tsari akan farashi mai sauƙi da araha. Muna kawo sababbin kaya akai-akai tare da rangwame na musamman. 🤍 Dukka sai a MK ABAYA BOUTIQUE 🤍 Duniyar Thrift Abayas masu kyau, masu tsari, da salo iri-iri domin kowane lokaci da kowane irin event. Abayas masu inganci, masu salo, masu araha, kuma na zamani ga mata masu son ƙawata kamanninsu cikin kamala da kamun kai. Karki bari a ba ki labari... Leƙo ki ga yadda MK ABAYA BOUTIQUE kullum ke cike da kyawawan Thrift Abayas akan farashi mai kama da kyauta. 'YAN SARI, 'YAN REPOSTING, DA MASU SIYA DON AMFANIN KANSU... DUKA INA MUKU MARABA! 🤝🤍 📱 WhatsApp: 07064399623 📞 Call: 08036027448 🔗 Join our Wholesalers Group: https://chat.whatsapp.com/JBg80RmA47v7GoqvWdgLJT?s=cl&p=a&mlu=3 __________________________
A hankali ya qaraso kusa da ita. Ya dago hannunsa ya sake gyara mata hijab din daya dan zame cikin kulawa.
“Kin ci wani abu yau?” Ta girgiza kai.
“Bani jin zan iya…”
“Zaki iya.” ya amsata calmly
“Ko kad'an ne.” sai ta sauke idanunta.
“Bana jin cin komai yanzu…” Sai ya d'an yi shiru yana kallonta da wani irin taushi mai nauyi a idanunsa
“Then borrow my strength tonight.” Ta d'ago idanunta gare shi a hankali.
“Har sai naki ya dawo." Ya furta yana lumshe idanunsa gami da budesu a cikin nata.
Wannan kalaman nasa,suka sake karyata. Yana da wasu irin kalamai....a idanunsa da harshensa wasu irin dafi ne da ba wanda zai gane sai wadda ta jarabtu dashi......sai wanda yake tare dashi. Tarin hikimar zance me laushi da nutsuwa.....wanda ke iya sanyaka ko ya hanaka abinda duk kayi niyyar yi.
Sai ya ja ta zuwa sofa gently ya zaunar da ita. Ruwa ya miqe ya dauko da kansa,ya dawo ya tsugunna gabanta yana zuba ruwan da kansa. Ta bishi da kallo......yana sake shiga zuciyarta da wani irin qarfi da shi kansa bai sani ba.
"Madalla da miji na gari" Ta fada tana sake jin kamar zuciyarta zata karye sanda ta tuna sultane shine tsanin samun wannan lu'u lu'un me tsada a gareta. Wanda ya yarda yayi kuka tare da ita.....suyi dariya tare. Wanda ya yarda ya tsaya a gefanta ba tare daya durqushe ko ya tsuguna ba.
"Take it" Ya fada yana miqa mata tambulan na glass cike da ruwan idanunsa masu sanyin nan cikin nata.
Ya jira har ta sha kad'an. Ya karba ya ajiye,sai taga ya jawo plate din abinci da bata lura da sanda ya zubashi ba. Kai ta langabe sai shima ya mata yadda ya saba,yadda yakewa nanay dinsa,dole ta sauke nata makamin duk da ranta baya so. Cikin nutsuwa har ta ci spoon uku. Cikin bata kulawa kamar yana kula da abu mai rauni da zai iya karyewa.
Shi ya tsaya tayi wanka.....shi ya tsaya ta sauya kaya,ta zauna gefen gadon cikin shiru......shurun da ya dauketa ya cillata wata duniyar tunani da mamakin da har yanzu bai saketa ba. . Kamar zuciyarta ta gaji da kuka haka takeji. A nutse haisam ya zauna kusa da ita,sanye da lausasan pyjamas da kyansu ya sake fitowa saboda daddadan qamshin nan nasa dake kadawa. Qamshin kuwa yayi nasarar isa zuwa ga hancinta kai tsaye,ya kuma aike mata da wannan nutsuwar da ya saba aje mata a dukka sassan jikinta.
Na d'an lokaci babu wanda yayi magana,sai shuru daya wanzu tsakaninsu,suka barwa zukatansu saqe saqensu.
Sai ya d'ago hannu ya kamo nata da wani irin taushi da nutsuwa. Ya miqa dogayen yatsunnan nasa yana shafa bayan tafin hannunta a hankali.
Numfashinta taki yayi nauyi......taji ya soma saukar mata da wata irin tsumammiyar kasala a dukka gangar jikinta. Tadan saci kallonsa,idanunsa suka d'an gutsira mata wani abu daban.
"Kinga d'a namiji.....bashi da haquri a fagen mu'amalar aure......musammanidan yana samun dukkan yadda yakeso....kuma idan har ya d'an d'ana yaju yadda abun yake......bazanji kunyarki ba.....zan fada miki.....mijinki da dukkan yaqini zai iya kasancewa a wannan sahun" Ta tuna wata magana da nanay ta taba gaya mata,wadda sai da taji inama ace qasa ta tsage ta shige?.
“Ki kwanta.” muryarsa ta sauka a kunnenta softly. Idanunta ta bude a hankali,ba wannan maganan ta dauka zataji daga bakinsa ba,akwa abubuwa masu nauyi danqare data hanga cikin idanun nasa......amma me yasa ya zabi gaya mata iya wannan?,koda ba zata magance masa da komai ba.
kai ta girgiza kai kad'an,tana jin tausayinsa yana saukar mata a hankali. Yayi kawaici.....ya kauda kai akan komai......bayan tasan can qasan ransa yana da buqatuwa zuwa gareta.....wacce irin sadaukarwa ce wannan?.
“Idan na rufe idona…” muryarta tayi rauni,tana jin zata fada masa ne don shi kadai ya rage mata a duniya.
“…zan sake jin muryarta.” Wani irin abu ya motsa a zuciyar Haisam me ciwo,sai ya matsa kusa da ita kad'an. Ya d'ago hannunsa ya shafi gefen kanta.
“To kada ki yi yaqi da tunanin.” ya fadi calmly
“Kiyi tunaninki gwargwadon yadda zai ishi kwanyarki ta bari ya wuce.” sai ya dakata yana kallon fuskarta da kullum kwanan duniya sai yaga abinda ya burgeshi.....sai yaga abinda ya masa kyau.
“And every time it hurts…” ya saka hannu yana share wani sabon hawaye
“…look at me.” Sai ya ja ta jikinsa a hankali. Da wani irin rauni ta kwantar da kanta a kafad'arsa shi kuma yana riqe da ita cikin nutsuwa.
Mutsuka tafin hannunta yaci gaba dayi,ta daidai gurin da yake da connection da idanuwa da sanya bacci. Batasan me yakeyi ba,tasan dai tana jin dadin wadannan tafukan hannayen cikin nata. Sannu a hankali kasala ta fara saukar mata,idanunta suka fara nauyi.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Kwanta" Ya fada yana gyara mata pillow. Ba musu ta kwanta,yaja mata comforter yana lullubeta sosai. Idanunta a lumshe sanda yake shafeta da addu'a. Taja numfashi sosai,tana jin yadda hannuwansa suka yita son sauya akala da tsaiwa a wasu gurare da yawa a jikinta,abinda ya haifar mata da kasala kenan,ya kuma so tayar mata da nata tsumin daya tsuma mata a ranarsu ta qarshe a dubai.
Ta dauka zai fita ne yayi uzurinsa bayan ya gama mata addu'ar.....amma maimakon haka sai taga ya jawo abin sallarsa bakin gadon ya zauna akai kamar wanda aka bawa gadinta. Bai matsa mata da magana ko yawan kallo ba.....ya bata space sosai yana raba hankalinsa tsakaninta da littafin hannunsa.
A haka ya zauna da ita tsawon dare. Yana shafa kanta lokaci zuwa lokaci. Yana duba yanayin baccinta. Yana gyara mata gashi idan ya rufe mata fuska. Yana lallashinta idan hawaye suka sake kufce mata. Kamar duk aikinsa na daren nan guda d'aya ne....... Tabbatar da cewa Akhnan bata ji ita kad'ai bace a duniya ba!
*_Nima a nan nace MADALLAH DA MIJI NA GARI IRIN HAISAM_*
★★★Tun bayan kalaman mammina zuciyar Akhnan ta kasa samun sukuni.
Duk sanda ta rufe idonta,sai ta ji muryarta tana dawo mata kamar a sannan take fada.
“Ban tab'a kallonki a matsayin d'iya ba…”
Amma abin da ya fi kashe mata zuciya ba wannan kadai bane. A’a. Yanzu ta fara tuna yadda aka rabata da morsa safiyya tun tana yarinya. Yadda aka sanya aka kuma maidata me tsananin yi mata rashin kunya. Yadda aka cusa mata qarya shekaru masu yawan gaske,ta kuma girma cikin wannan qaryar.
D'aya bayan daya abubuwan da suka faru a shekarun suka fara dawowa mata. Tana qin zuwa sashenta. Tana jin haushinta ba tare da dalili ba.
Yadda mammina ke nuna mata Safiyya a matsayin barazana a fakaice cikin hikima da dabara bawai kai tsaye ba. Yanzu kuma.... wadda aka hanata ta qaunata… ita ce ke prison saboda qarya makirci da tuggu?.
Wannan tunanin ya soma cin Akhnan daga ciki. Ta kasa cin abinci yadda ya kamata. Ta kasa bacci. Takai koda haisam yana kusa da ita......zuciyarta na ci gaba da nauyi.
A safiyar ranar,daya tsareta da wadannan narkakkun idanuwan saman dining table,inda suke zaune daga shi sai ita. Ya zuba mata komai yana cin nasa a hankali yana monitoring dinta da d'aurarriyar fuska. Tun kalaman farko da yace.
"Kina cutar dani da rashin cin abincin nan......kinaso mu rusa rayuwarmu ne gaba daya?". Bai sake cewa komai ba,saidai da wannan qwarewar tasa yake tilasta mata cin abincin ta hanyar sarrafata da idanunsa.
Batajin taste din komai,kaman yadda komai baya mata dadi. Morsa safiyya kawai take burin gani,wanda a yau tana jin ba zata tsallake yau din bata ganta ba.
"Zanje wajen momma" Ta fada muryarta a qasa.
Haisam dake gyara cufflinks d'insa bayan ya gama shanye nasa tea din ya dago idanunsa gareta. Ya lura da yadda muryarta take rawa.
"Akhnan" Ya kira sunanta na asali,maimakon giiftii....my princess....my healer da yafi kiranta a yanzu.
“A’a.” ta fada da sauri tana girgiza kai,saboda ji tayi kaman yana shirin cewa ba zataje bane.
“Ba zan iya zama a nan ba.”
“She’s alone because of me.” ajiyar zuciya me nauyi haisam ya saki,sai yaja kujerarsa sosai yana d'an matsawa kusa da ita.
“Ba saboda ke bane.” ya fada yana bata assurance da idanunsa.
“Da ban yarda da Mammina ba tun farko…” hawaye na taruwa mata
“Da ban dinga cutar da momma ba…” Sai ta dafe kanta ta taji yana sara mata.
“Ya Allah......Allah…” Ta fada sautin yana komawa can cikinta.
“Yaya zan kalleta yanzu…” a hankali haisam ya kama hannunta a tausashe,ya kuma game da nasa tafin hannun yana bata therapy dinnan dake nutsar mata da d'imautar zuciya.
“She knows who poisoned your mind." Yayi maganan da faransanci,kalamansa a jejjere kaman wanda ya shiryasu kafin ya fadesu.
“She never blamed you.” Sai ta girgiza kai,tana jin kamar ba haka ba.
“nice abar zargi.....ni kaina ina zargin kaina da kaina.” shuru yayi,baisan ta yadda zai cire mata wannan ba kuma,baisan ta yadda zai gamsar da ita ta daina zargin kanta ba,ya kuma tabbatar inde ba morsa safiyya ce ta fada da bakinta ba ba zata aminta da hakan ba.
"Ka barni naje.....i.need to see her" Hannunsa dayan ya sake azawa saman nasu yana damqewa sosai.
"And if this is exactly what Mammina wants?.....ta fada,kece next target nata.....ko ba haka tace ba?"
"Ban damu ba......ban damu ba haisam a yanzu......abinda na sani kawai morsa safiyya......she's alone" Sai muryarta ta karye.
"…and I left her alone for years.” ta qarasa fada hawaye yana gangaro mata.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 120* _________________________ https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0
*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*
*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*
*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*
*_Assalamu alaikum my loyal people_*
*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*
*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*
*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*
*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*
*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*
*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*
*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*
*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*
*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee* _________________________
Wani irin zafi na fitar hawayenta ya ratsa haisam.....Saboda ya san,wannan guilt d'in ne zai fi kashe ta akan komai. Yatsansa ya santa yana dauke mata hawayen.
" You're not your childhood mistakes......you were manipulated"
"Amma ai i still hurt her" Ta fada sabbin hawaye suna zuba a fuskarta.
"And now she’s in prison while I’m here…”
Jawota yayi jikinsa ya rungumeta a nutse,yana shafa bayanta a hankali gami da maimaita fadin.
"Hasbunallahu wani'imal wakeel" A hankali ta kama da bakinta tana maimaitawa
Sallamar birra da wata irin murya me cakude da tsoro yaja hankalinsu. Sai data shigo sannan suka lura,ba muryarta kadai ke rawa ba.....dukka ilahirin jikinta ne yake rawar.
"Jami'an tsaro ne......sunce gurin gimbiya sukazo" Ta fada jikinta yana rawa gaba daya. Tunda take a agadez bata taba ganin masifar data sanyata jin kamar ta gudu ba irin wannan lokacin.
"Kije kice zamu fito yanzu" Haisam ya fada calmly,da wannan nutsuwar tasa dai data zame masa tambari,tamkar babu wani abu da aka gaya masa me daga hankali.
Juyawa yayi ga akhnan,sai yaga ta zuba masa idanu. Tashin hankali ne kwance cikin idanunta tana dubansa,amma ga mamakinta sai ya sauke mata tattausan murmushin nan nasa.
"Me kike tsoro?,koma meye karkiji tsoro muddin haisam yana tare dake.....no one is taking you anywhere idanma abinda sukazoyi kenan.....not while I'm standing".
Hannunsa ya miqa a nutse,ya dauki hijab din daya cire mata dazun da hannunsa ya ajiye gefansa sanda zasuci abincin,yana dan tsokanarta sanda ya zare mata hijabin
"Komai ma an tattare an hanamin......wannan beautiful gorgeous face and body dinma hiding mani shi ake?" Murmushi ya bata a sannan,wani sassanyan murmushi mara kuzari ko kadan.
A yanzunma.....da kansa ya dagata,ya kuma saka mata shi ya daure mata igiyar,sannan ya riqe hannunta softly suna takowa a hankali zuwa bakin qofa.
Dab da bakin qofar suka tsaya,ya soma karanta addu'ar fita a gida ba tare daya kalleta ko yace komai da ita ba. A hankali ta kama itama har suka kammala tare,suka sanya qafafuwansu zuwa waje a tare kuma lokaci daya da bismillah.
Taka qwallewar tana tsakiyar qwayar idanunsu haka fitowar tasa ta kasance musu dukkaninsu gaba dayansu. Su bashi suka buqaci gani ba.....akhnan ce.
A nutse yake binsu da kallo,jami'ai ne saidai kuma shima nashu guards din sun zagayesu cikin shirin kota kwana.
Wannan yaqin ba nasu bane,baya kuma fatan sanya kowa a cikinsu,don haka da idanu kawai ya musu umarni suka janye suna bacewa daga gurin.
D'aya daga cikin jami'an ya matso,don tafiyar wadancan mutanen sai sukejin ya zame musu wata babbar dama da zasu aiwatar da aikin yadda akeso.
"Gimbiya akhnan......an buqaci ki biyomu". Maganar tasa ta tsaya cikin iska tana yawo. Akhnan ta tsaya cak tana dubansu,jikinta yayi wani irin sanyi. Ta fahimta.....sai yanzu ta sake fahimta.......ita ma ta shiga jerin wad'anda Mammina take son rushewa.
Sai ta ji yatsun Haisam sun qara matse nata a hankali. Gargadi ne......wani kakkausan gargadi da zaiso ace sun fahimta tunda wuri......tun lokaci bai qure musu ba.
Haisam bai kalli jami’in nan take ba. Idanunsa na kan Akhnan. Yana kallon yadda numfashinta ya rikice. Yadda tsoro ya soma shiga idanunta. Sai ya d'an matsa gabanta kad'an bayan ya saki hannunta. Nan take ya koma GARKUWA.....nan take ya shimfida katanga tsakanin ganinta dasu.
Wadannan idanun......idanun nan dake cike da wani shimfidadden kwarjini ya daga a kansu,take dukkaninsu sukasha jinin jikinsu......kowanne kuma yanayin da yakeji a jikinsa da zuciyarsa ya sauya. Ya musu kwarjini.....me yawan gaske. Basusan waye ba.....baqin haya ne,shigarsu gidan na farko kenan akan aiki na musamman da ogansu yace zasuyi cikin agadez. Ta zabi dauko bare na waje.....saboda tasan duk cikin agadez babu wanda zai iya tunkarar wannan aikin haka kai tsaye ba tare da tsoro ko shakka ba.
Bausan waye ba.....amma kallon Haisam yanzu ba irin wanda suka saba gani bane.
“Wa ya aiko ku?” ya fada da wata irin nutsuwa dake gauraye da fushi. Saida jami'in ya hadiyi yawu sannan yace.
"Giwa ce.....giwa mammina ce ta bada umarni......"
"Naji!" Haisam ya yankeshi ba tare daya barshi ya ajiye bayanin ba,duk da ba dabi'arsa bace hakan.
Wani irin shuru ya ratsa gurin. Sai Haisam ya d'an karkatar da kansa. Nasa salon aikin dake cikin jini ya motsa,ya soma karantar yanayinsu shigarsu dama nutsuwarsu,irin qwaqwafin nan na masu binciken qwaqwaf da suka saba.
Idanunsa suka sauka kan takardar dake hannun jami’in.
“Da wace hujja?” ya tambayeshi yana zare idanunsa daga kan takardar.
Jami’in ya soma rikicewa kad'an,don har cikin hanjinsa yakejin kallon
“Ana zarginta da.... ”
“Na ce ba!…” haisam ya datseshi da kakkaifar muryar nan tasa.
“Da wace hujja?” ya sake maimaitawa yana zube musu idanunsa yana binsu da kallo daya bayan daya.
Guards d'in suka soma kallon juna. Saboda ba su tab'a jin mutum irin Haisam ba. yana magana haka kamar ba kamu sukazo yi ba akan laifin da ake tuhumarsu dashi.
Takardar hannunsa jami'in ha miqa yana rawar murya,yana jin kamar bazai iya ci gaba da tsaiwa a gurin ba.
“Royal order ne…” Haisam bai karb'a ba ma. Sai ya kalli seal d'in kawai sannan yayi murmushi kad'an. Wani irin murmushi mai razanar da zuciya.
“She’s getting bold.” ya fad'a muryarsa can qasa.
A hankali Akhnan ta d'ago idanunta tana saukesu a kansa.Ta fara jin wani abu daban a yanayinsa. DANGER!!!.....shigen wanda ta gani a sanda TAMIM yayi nufin keta iyakarta.
Barin inda yake tsaye yayi,yayi taku biyu gaba.....takun daya sanya guards d'in saurin jaa baya,tamkar sun hangi zaki ya tunkarosu. Da wani irin kallo yake binsu,yana jin naman zuciyarsa yana motsi.