Kenza eBookz

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 68

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 68

L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 68: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 68. A yau tana ji a ranta zata rasa komai. Tana ji a ranta…

3,270 words

A yau tana ji a ranta zata rasa komai. Tana ji a ranta yau mammina zata gama da ita kaman yadda taso. Hannunta na rawa kad'an yayin da take qoqarin gyara bracelet d'inta. Wannan bracelet din na azurfa wanda ke maqale da adon lu'u lu'u a jiki.......wannan bracelet din me girman matsayi da daraja wanda aka bata daga Ethiopia randa ta saka qafafunta cikin masarautar.

Saidai amma ta kasa rufewa. A hankali hannayensa masu taushi suka karba gently,yana tsaye daga bayanta,irin tsaiwar data bada wani irin kusanci na sosai a tsakaninsu.

Ba tare da magana ba,ba kuma yare da yace komai ba,ya d'auki bracelet d'in. Ya rufe mata shi a hankali. Kamar wanda yake handling glass.

Ita dashi dukkaninsu suka fito tarwai ta mirror din,ya nuna su tare. Shi cikin all black royal attire. Perfectly tailored dake nuna zallar sanin darja da mutuncin ado da iya sanya sutura. Agogon silver dinsa ya zauna sosai saman lallausar fatarsa. Azurfa qwaya daya data sanshi da ita tsakiyar hannunsa dake da adon wani dutse na lu'u lu'u dakesheqi yana sauya colors. Aura d'in nan tasa mai had'a......power.....danger da calmness.

Ta d'ago idanunta ta kalleshi ta cikin madubin,tun safe zuciyarta a matse take. Ahmad yana prison......morsa safiyya tana tsare.....a yau kuma.......yau ita mammina keson hukuntawa cikin bainar jama'a. Ta sake nutsar da idanunta a kansa. Ba wani alamun tsoro fargaba ko d'ar saman fuskarsa. Sai wata irin sassanyan nutsuwa a tare dashi. Har yana da karsashi da kuzarin tsokanarta a dazun.

“…Ya kamata mu tafi.” ta hada kalaman a nutse labbanta suna motsawa da wani yanayi daya masa kyau sosai. Idanunsa ya zare a hankali daga kanta,sai ya ci gaba gyara cuff ɗin hannunsa calmly,kamar baya cikin gaggawa ko kad'an

“Not yet.” Ta haɗe gira kadan tana motsa fuskarta. Wannan halin nasa.....wannan dabi'ar ta sanya komai da kowa su jirasu....kaman a wannan gurin bata dace ba.

“Haisam…” ta kirashi da wannan sound din nata.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

“Everyone is waiting.” Sai ya d'ago idanunsa sosai yana sanyasu cikin nata.

“Let them wait.” ya amsa da wata nutsuwa. Wani irin bugun zuciya ta ji,saboda yadda yake calm yau. Too calm.

"me yasa ba zamu tafi ba?" Ta tambaya. Tanason suje akan lokaci ne,saboda kada mammina ta tsammaci tsoro ko rashin gaskiya tattare dasu.

Kyawawan idanunsa ya lumshe sannan ya budesu a kanta gaba daya.....kyawawan fararen idanun nan da a yau taga kamar sun qara haske.

"Because timing matters". Ta matsa kusa da shi sosai.

“You’re scaring me again......tsoro kake ban.....tsoro nake ji har cikin jikina". Shuru kawai yayi,sai ya zuba mata ido na wasu seconds. Kamar yana kallon wani abu mai daraja sosai sosai.....kamar yana qiyasce tsadarta da darajarta ga rayuwarsa. A hankali ya d'aga hannu ya gyara gefen hijab dinta da ya dan zame. Wannan dabi'ar tasa dai,kaffa kaffa da komai nata.

“Look at me.” Ta daga idanunta gare shi,sai ya riqe hab'arta a tausashe.

“What do you see?” sai ta dan rikice,idanunsa suna mata kaifi da yawa.

“…You.” Wani lallausan murmushi ya tab'a lips d'insa a taqaice.

“No.” sai ya sake takowa shima yana hade tazarar dake tsakaninsu.

“tsoro kike ji.”

“And I need you to stop.” sai ta runtse idanunta kad'an......saboda gaskiya ne. Tana jin tsoro,da gaske ne. Da gaske ne,ya karanta cikin zuciyarta ta idanunta kamar yadda ya saba.

“rusheni takeson yi.” ta furta muryarta tana rawa.

“She already destroyed everyone around me…” Sai Haisam ya girgiza kansa a hankali.

“Listen to me carefully.” sai yayi qasa da muryarsa kamar wani sirri ne a tsakanin shi da ita.

“No one destroys you while I breath" Zuciyarta ta buga da qarfi,saboda yadda ya fadi kalaman dab da kunnuwanta. Ya kamo fuskarta dab da tashi sosai har numfashinsu na had'uwa

"Kin tsira daga abubuwa da yawa.....abubuwa masu yawan gaske.....abubywan da suka fi wannan muni da girma....."

“You survived betrayal.”

“You survived grief.”

“And today" Ya furta tana kulle idanunsa cikin nata.

“…you survive the truth.”

Idanunta ta lumshe a nutse,tana jin yadda kalamansa suma samu gurbi me kyau cikin zuciyarta......tana jin yadda kalamansa suke bata qwarin gwiwa.

“What does that mean?” Sai ya yi shiru......a hankali ya d'ora goshinsa a nata.

“It means…” cikin muryar rad'a

“…by tonight, nobody will ever make you bow your head in this palace again."

Hawaye suka cika idanunta,saboda yadda yake magana kamar ya riga yaga gobenta. Yadda yake bata tabbacin tsaro da aminci. Sai ta kamo gaban rigarsa a tausashe,zuciyarta da muryarta suna rawa.

“What if I break today?. Idanunsa ne sukayi wani irin duhu,kamar kalmar ta taba wani sashe me girma ma zuciyarsa

“Then break in my hands." Ya furta da Fuskarta cikin tasa,hancinsu yana gogar na juna,yana riqe da qugunta sosai cikin hannuwansa.

“Not alone.” ya qarasa fadi muryarsa na fita da wani irin nauyi. Wani irin numfashi ta sauke,tana jin ruhinta.....jarumtarta da dukka nasararta ta ta'allaqa dashi. Sake riqeta yayi sosai cikin jikinsa,da sautin nan na rad'a dake ruguza kowacce garkuwa ta jikinta.

“And when we walk into that courtyard…” ya fadi a nutse.

“I don’t want fear in your eyes.” Sai ya d'an sunkuya kadan zuwa saitin tiny lips dinta.

“I want them to see the wife of Haisam.” ya qarasa fadi da wani yanayi da taji kamar qafafunta ba zasu iya daukarta ba.

Wani irin d'umi ya ratsa zuciyarta. Sai ya miqa mata hannunsa.

“Ready?” Ta kalli hannun nasa. Then ta daga idanunta gare shi. Still tana jin wani tsoro.....saidai jarumtar daya bata ta mamaye wannan tsoron da wani irin qarfin gaske.

A hankali ta sa hannunta cikin nasa.

“…Ready.” Sai Haisam ya dan matse hannunta. Kuma a karon farko yau,wani abu kamar relief ya bayyana a idanunsa.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 123 A* __________________________ *_Amintaccen gurin siyayya_*

*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*

*_BONONZA DA PROMO akai akai_*

*dukka sai a HUGUMA CLOSET*

*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*

*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*

*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*

*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________

Cikin qasa da minti daya kaf guards nasa da security dinsa suka zagaye kotun,da wani irin salo da qwarewar aiki,wanda ba lallai kai da kake gurin ma ka fahimci su waye zagaye daku ba. Bada uniform ba ballanta ka ganesu,saidai kwanya da horaswar da suka samu daga yarima muhammad haisam kadai abar kallo ce. Sun riga da sun tabbatar da tsaron gurin,kuma suna cikin shirin kota kwana......su dakatar kosu afkawa duk wanda yayi yunqurin yin wani abu na ba daidai ba.....ko duk wanda yake shirin cutar da yarimansu ko matarsa akhnan.

Wani irin kiran hankalin mutane sukayi sanda suke takawa cikin chamber din. Kamar wadanda aka gayyata walimar girmamawa.....ba wadanda aka gayyata don hukunci ko tuhuma ba. Bada kalma sukaja hankalin kowa ba ko daya.....bada wani sauti ba.....aah....zallar kwarjinin sheikh muhammad haisam dake haskawa da wani irin qyalli cikin idanun duk wanda ke iya ganinsa. Sanda yake takowa hannunsa a bayyane cikin na matarsa.....gimbiya akhnan muhammad hammud...... Riqon daya mata....kamar yana gayawa kowa cewa. A shirya yake yayi komai saboda ita,....a shirye yake ya bada fansar rai da rayuwarsa.....a shirye yake kuma yayi fito na fito da duk wanda ya qalubalanceta.

Mammina dake zaune daga garinta ta gani.....taga komai.....ta kuma fahimci komai. Ta dinga qoqarin saisaita kanta,don daga kallo daya tak daya mata yaso birkita tsarinta da tunaninta na yau.

"Wannan idanuwan ibraheem ne" Ta fadawa kanta tana qoqarin controlling kanta.

Bai tsaya gaban kowa ba....bai magana da kowa ba har sai daya isa mazaunin da aka tanada masa shi da akhnan. Ya riga ya tabbatar da tsaronsa. Don haka kai tsaye ya dorata saman kujerar cikin girmamawa,shi kuma ya koma bayanta ya tsaya kamar wani badakkare daya shirya bada rayuwarsa saboda qasarsa da al'ummarsa. Wata irin tsaiwa dake nuna mutuntawa da bada cikakkiyar kariya.....wata tsaiwa data tsayewa mammina cikin idanu da zuciya.

Mammina din ce ta miq tsaye cikin,cikin shigar nan tata da kowacce daqiqa take nuna izzar mulkin da ake tattalinta kowacce rana. Ta d'aga kanta da isa. A yau,tana jin kamar finally ta mallaki komai ta kuma mallaki kowa.

"Wannan masarauta tana zargin khadeeja muhammad hammud da karya dokokin masarauta masu tarin yawa....ko a yanzun da taqi amsa kiran masarauta a sanda ta kirata alama ce ta raini da tozarci.....kafin sannan......ana zarginta da laifukan hada kai masu cin amanar rawani da masarauta gaba daya......" Sai ta dakata tana duban fuskar akhnan don son tantance meye akai.

TSORO take buri da muradi gani......amma ga tarin mamakinta shine.....irin shigen nutsuwar da take ganinta akan fuskar safiyya......irin tarin nutsuwar da take gani game da haisam,itace a yanzu take gani akan fuskar akhnan din. Ba digon tsoro ko gigita sam akan fuskarta. Ta sauke idanunta tana ci gaba da karantawa,tare da bawa kanta tabbaci. Ba yadda za'ayi taji hukuncinta na gaba ba tare da sun gigita ba su duka.

“Bisa ga dokokin masarauta…” murya na fita cikin courtyard din.

“…duk wanda ya had'a kansa da masu cin amanar masarauta...."

“…ba shi da gurbi a gidan nan.” Akhnan ta runtse idanunta,zuciyarta na bugawa da wani irin ciwo. Ita ake nufi za'a barranta?......ita ake nufi za'a kora daga da'ira da ikon mahaifinta?. Mahaifarta....inda cibiyarta ke a binne?. Muhallin da duk duniya bata da kamanshi?. Ba'a tsada ko alatu ba.....aah.....GIDA wani abune na daban da ba kowanne muhalli ke iya maye gurbinsa ba. Hannun haisam ta matse a hankali,sai shima ya matse nata cikin nasa da wani irin taushi,saidai bai motsa ba,bai kuma barta ta motsa ba kwata kwata,idanunsa kafe kan mammina.

"Ba yanzu ba.....yi haquri.....sauran 'yan mintuna" Ya fada yana matsa device din kunnensa muryarsa can qasa. Da yake baya ta bashi,ta dauka da ita yake,saita sake aro nutsuwa ta azawa kanta tana sauraren komai da bugawar zuciya.

“Daga yau…” ta fada tana nuna akhnan kai tsaye da yatsarta.

“…an cire ta daga duk wani iko da alaqa da masarautar Agadez!.” Hayaniya......wata irin hayaniya ce ta tashi. Falaak ta fashe da kuka......falaak din dake zaune cikin ciwon data rasa musabbabinsa. Tana jin kamar duniya takewa bankwana.....tana jin kamar kwanakinta sun qare a duniya.

Wani hukunci ne da yazo musu da girma da nauyi. Qananun qus qus har a sashen dattawa ta fara tashi. Saidai kuma.....kowa tsoro ne fal idanu da zuciyarsa. Kowa baya da iko na cewa komai.....kowa baya da iko na daga harshensa ko hasashensa akan maganan. Hannu mammina ta daga.....abinda ya sanya duk wani cecekuce dakatawa,shuru kama anyi ruwa an dauke.

“Kuma idan ta qi bin umarni…” ta fada da izza tozarci da gadara.

“…za’a kaita prison kamar sauran ‘yan tawayesu." Nan take guards suka soma matsowa kusa da inda akhnan ke zaune. D'an motsawa kawai haisam yayi ya saka guards tsayawa da wani yanayi na shakka da tsoro a fuskarsu.

Mammina ta lura da hakan,Idanunta suka hadu da nasa.

“Ko kai ma zaka tsaya gaban dokar masarauta?” ta masa tambayar tana jin a daidai wannan lokacin tafi sha'awar maganarsa akan shurunsa. Wannan shurun.....wannan shurun dake razanata da hanata bacci a dukka darare. Ta tuna shi alsaamit ne.....alsaamit kuwa da shurun aka sanshi.....saidai shurunsa kuma hadari ne. Tasha qiyasta da wanne hadari shurunsa zaizo muta?. Duk da tana jin ta shirya......ta shirya ta kowacce fuska ta wanne bangare da yake tunanin zai iya zuwa mata.

Shuru gaba daya gurin yayi.......tamkar kowa na jiran amsar Haisam.

Ya d'aga idanunsa a hankali zuwa fuskarta. Bataga digon FUSHI BA a ciki....wani abu daban ta gani. Wani abu da yafi fushi tasiri.....wani abu da yafi fushi razanarwa.

“Dokar masarauta?” ya tambaya irin tambayar nan ta kai tsaye......irin tambayar nan ta titsiye.

“Ko son ranki?” wata hayaniya ce ta sake tashi. Wani tasiri ta ji a cikin jininta.....tasirin QASQANCI da wannan kalmar da haisam din ya jefeta da ita. Ba wanda ya taba dubanta ya gaya mata wata kalma da bata amintar da ranta ba da muradinta saishi......shine mutum na farko.....kuma tunda har yayi wannan gangancin.....to tabbas zata tabbatar daya zama mutum na qarshe.....zatabar tarihi a kansa.....tarihin daba wanda zaiyi marmarin kwatantawa.

“Ka manta wa kake magana da shi?."

“A’a.” ya amsa mata kai tsaye kuma a taqaice.

“Ke ce kika manta iyakarki.” ya amsa mata yana duban tsakiyar idanunta.

Dukkanin tarin qasqanci taji yana nuqurqusarta. Ta sauke idanunta a nutse akan Akhnan,duk da zuciyarta ba digo na nutsuwa kwata kwata. Tayi niyyar barin Akhnan ta nesanta kanta da agadez.....don ta samu daman salwantar da rayuwarta.....amma a yanzun....ba zata yi hakan salin alin ba.

Ya kirata da RED LINE din da ba'a qetarewa nasa......amma ita a yanzun zata qetare shi. Zata taka ta kuma turmurmusa wannan line din.....idan yaso taga mene zai aikata.

"Lokaci yayi" Ya fada da wani faffadan murmushi.....murmushin da ba mammina kawai ba.....harma wanda yake nesa ya gani. Ta dauka da ita yake magana haka kai tsaye....lokacin me?,murmushin me yake?,abinda ya tunxurata kenan ta buda bakinta a tunzure.

"Ku kamata!" Ta bada umarnin a hargitse sannan kuma a tsawace da sautin daya isa kunnen harna nesa ma.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Saidai kuma......taku d'aya tak sukayi aka ji karar sanda yana bugun qarfen bene daga bayan mutane na ciki dana waje.

Sau daya. Sau biyu. Sau uku

Kaf courtyard ya dauki shuru. A hankali.....da wani irin yanayi jama'a suka fara matsawa gefe. Guards suka juya. Dattawa suka miqe tsaye cikin firgici da wata irin dimautacciyar d'imuwa

"BAZAI YUWU BA!" Wani dattijo ya furta kafatanin ilahirin jikinsa yana rawa kamar mazari.

Qara bugun sandar ya sake bayarwa. Tak… Tak… Tak…

Daga cikin taron mutanen.......wani dogon mutum cikin farar babbar alkyabba ya fara qarasowa. A hankali,da takun da kowa a Agadez ya sanshi.

Mammina ta hade gira tana duban mutumim.

"Wanne me tsaurin idanun ne wannan.....da zai keto tsakiyar mutane sannan ya iso nan ina tsaka da yanke hukunci?....ko kaima kazo hanani kai khadeeja muhammad hammud prison dinne?.....shin kazo dakatar da nine kamar yadda wancan malamin d'an gidan ibraheem yake yaudarar kansa da ganin zai iya?" Ta fada tana nuna haisam dake tsaye,tana jin kuma dole ta sake tsaurarawa. Dole ta saka tsoronta a zuciyar kowa.

Da wani irin nutsuwa ya janye hular alkyabbar dake kansa. Gaba daya courtyard din ta daskare na wasu sakanni. Jinin dake yawo a jikkunan mutane da dama dake gurin ya nemi tsayawa cak. Wasu suka ja baya cikin tsoro. Wasu kuma suka durqusa suna jin kamar girman wannan almarar yafi qarfinsu......yafi qarfin abinda zasu iya jurewa.

“SULTANE…”

“…Sultane?!”

“ALLAHU AKBAR!!!" Wasu muryoyin dake da sauran dakiyar zuciya suka rude da fada duk da akwai burbushin tsoro a tare dasu.

Sultane ne......a raye......a tsaye......yana kuma duban mammin kai tsaye.....kamar ita kadai ce dan adam me numfashi a gurin.

Da wani irin gigicewa da madaukakin tsoro taja baya. Gane gane ta fara yi ko jifa akayi mata?. Sultane ne dai.....sultane take gani,a raye.....a tsaye a gabanta cikin qoshin lafiya. Sultane dai da aka masa wanka a gabansu.....sultane dai da aka hada cikin likkafani......sultane dai da aka binne yau kwana daya daya kwana kusan talatin da takwas?.

“…A’a.” mammina ta furta tana girgiza kai a rude gami da kallon hagunta da damanta waiko wani zai taimaka ya tasheta daga mummunan mafarkinta.

"BAPPIIIIIIII!!!!" sunan da Akhnan keta qoqarin fada tun dazu.....sunan data furta shi a zuciyarta yafi sau d'ari.....ta kasa fada a fili amma a yanzu ya subuce ya fito daga bakinta.

Har a yanzun......da yaji fitar sautin d'iyarsa.....diyarsa mafi soyuwa a garesa.....sosai dab da shi ta cikin kunnensa.......har yanzu sultane bai kalli kowa sai Mammina. Only Mammina!!!.

Yana jin sanda Akhnan ta fada jikinsa da wani irin qarfin da sai da yasa dukka hannuwansa ya tallafeta a jikinsa,still idanunsa akan mammina.

"Bappppp....." Saita kasa qarasawa idanunta kafe a kanshi. Numfashinta ya katse daga qirjinta......abinda ya sanya haisam saukowa daga gurin. Da wani irin sassarfa.....da wani irin zafin nama yana karbeta daga hannun sultane yana kiran sunanta a jejjere.

Sakar masa ita yayi.....a hankali.....a tausashe.....da wani irin amincin daya tabbatar zai daidaita numfashinta a qirjinta....da yaqini da duka amannar data hanashi jin D'ar ko d'aya da suman da Akhnan ta tafi.

Ba yaune karon farko data fara suma a hannunsa ba.....amma a yau din,sai yakejin kamar suman ya banbanta dana kullum. Sai yakejin wannan suman data tafi ta tafi kenan.

"Akhnaaann" Ya sake kiran ta da gaske yana girgiza fuskarta a tafin hannunsa.

Cak ya dauketa yana adanata a qirjinsa,sannan ya fara takawa da sassarfa yana fita da ita daga courtyard din,guards dinsa suna buda masa hanya kafin ya iso gurin,yayin da sultane ke tsaye gaban mammina.....ko na second daya ya gaza dauke idanunsa a kanta.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 123* ___________________________ https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0

*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*

*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*

*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*

*_Assalamu alaikum my loyal people_*

*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*

*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*

*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*

*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*

*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*

*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*

*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*

*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*

*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee* ___________________________

“Kin gama?” sultane ya fada da nutsuwa da wani ciwo cikin muryarsa.

Soma girgiza kai ta farayi a gigice,wata maqurar gigicewa da bata taba yinta ba kaf rayuwarta. Karon farko ta rasa kalmomin da zatayi amfani dasu kaf rayuwarta don ta kare kanta.

“Na baki shekaru maay kyau.....” muryarsa ta fita da nauyi

“Na baki suna da kika riqa kike amfani dashi cikin izza da alfahari"

“Na baki amana da nake zaton ko bayan raina ba zakici ba,ba zaki tozartar da ita ba.” Sai ya dan matsa kusa da ita.

“Amma kina jiran mutuwata ne kawai ashe?." Ya fada idanunsa suna yin wani irin duhu.

Readers Also Read

More by Huguma