Kenza eBookz

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 69

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 69

L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 69: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 69. “…domin ki cinye iyalina?." Wani irin shuru nauyi ban…

3,374 words

“…domin ki cinye iyalina?." Wani irin shuru nauyi ban tsoro da kuma ban mamaki ya cika gurin. Kowa ya kasa motsi,kowa ya gaza takawa daga inda yake,kowa ganin komai yake kaman shirin film ko cikin labaran hikaya. Wai matacce ya dawo.....ya kuma dawo a daidai gab'ar daya kamata dama ace ya dawo din. Ya dawo a sanda agadez ke dab da nutsewa. Ta cikin wannan shurun sautin kuka ke fita. Ta cikin wannan shurun sautin kukan mutane da dama ke fita. Banda falaak,falaak din data daskare tun sanda sultane ya shigo.....take zaune a gurin kamar wani gunki,kuma dai har yanzun a zaune take,amma amma unconscious. Idanunta da kunnuwa ne kawai suke aiki a jikinta.....banda wannan......ba wani abu dake aiki tattare da ita.

Sake takawa yayi zuwa gabanta,idanunsa dauke da wani zuzzurfan kallo. Ba irin kallon mata da miji ba.....ba irin kallon dake dauke da taushi qauna ko bege ba.....aah....

Kallo ne da wanda akaci amana yakewa wanda yaci amanar tasa. Kallo ne irin na wanda soyayya ta juye masa zuwa zazzafar qiyayya.

"Kinyi mamakin dawowata ko?" Ya fada yana sake jin wata matsananciyar qiyayyarta tana hudashi.

"Ka saurareni!" Ta qwato kalaman da qyar tana jin yadda harshenta da maqoshinta gaba daya suka bushe,ba wani digon yawu,tana ji kuma a ranta da zuciyarta cewa.....komai bazai tafi a haka ba.....komai zai daidaita. Hargitsin na wani d'an lokaci ne kawai.

"Shuru!" Ya fada cikin daka tsawar data sanya kowa sunkuyar da kansa cikin ladabi bawai iya mammina kawai ba. Sabon abune wanda basu taba ganin irinsa ba. Sultane yayi magana da hadimai da irin sigar nan bama ballantana kuma matarsa.....matar tasa ma kuma GIWA.

"AKHNAN!" Ya kira sunanta a kausashe.

"Yarinyace da aka rasa uwarta" Sai muryarsa ta karye.

"Na dorata a hannunki"

"Amma maimakon ki zame mata mafaka......sai kika mayar da rayuwarta filin yaqinki" Motsawa baya kadan mammina tayi,komai yana gwada mata duk abinda ke faruwar nan da gaske ne yake faruwar.

"Kin rabata da danginta....."

".....kin cusa mata qiyayya"

"Kinci amanar gidan nan" Ya dakata yana jan numfashi da qyar idanunsa suna sauya launi.

".....amma abinda yafi karyani....."

".....ashe duk tsahon shekarun nan jiran mutuwata kike ki tarwatsa iyalina....ki tarwatsa ahalina.....ki shafe komai nawa daga duniya".

" Wallahi ina sonka" Ta fada tana girgiza kai,tana jin kamar kwanyarta na shirin fara aiki ba daidai ba.

Ji yayi kaman ta dauki guduma ta doka masa a tsakiyar kansa.

"Kina dai son nasara.....kinason nasararki,kuma kin shirya yinta ta kowacce hanya. Kansa ya dauke,don baya qaunar ganinta ko yaya,ya waiwaya ga tarin guard din dake tsaye.

"Ku saki Ahmed.....ku fitomin da safiyyatah!.....sannan ku tabbatar.....duk wanda aka tsare bisa zalunci a sakeshi bisa yardar yarima haisam" Ya fada maganan da wani amo.

"Kinsan me yasa ban bayyana tun farko ba?" Ya sake juyawa gareta sanda guard din ke fita da sassarfa don cika umarnin adalin sarkinsu.

"Saboda inaso naga iya duhun da zuciyarki ke dashi.....a kwanciyar da nayi da sunan ciwo.....ba ciwo bane.....hutu ne da haisam ya yanke bawa gangar jikina.....na huta,na karanci wasu abubuwa da xirga zirgar mulki.....kula da jama'an dake wuyana......da makircin masu makirci da idanuwana basa iya gani....."

".....ina kwance.....amma ina iyaji.....ina kwance amma ina gani......naji!.....na gani....tun daga sanda kika fara saka guba cikin fankoki da ac da pillow din da zan dora kaina a kai......daga sannan haisam ya fara shirin yadda zan mutu a idanun duniya kafin ki sakani nayi mutuwar gaske." Wani irin shock ya sake shigan kowa. Mamakin wannan idea ta yarima sheikh muhammad haisam yana sake shigarsu.

"Nasan wacece ke zaituna......gudajjiyar me laifi daga Ethiopia......wadda ta biyo safeena......ta biyo dukiyar ajani.....wadda ta shigo ahalina.....saidai wani abu daya...." Ya fada yana hadiye yawu da qyar.

"Shi Allah......adalin sarki ne.....ya hanani sanin wacece ke......bayan inacan ina damuwa don baki haihu ba.....ashe ya hanani....bani kadai ba.....ya hanaki haihuwa da dukkan mazan da kika aura saboda bamu da haqqinki......saboda ke din GUBA ce.....saboda baki cancanci zama UWA BA!"

"Ba hukuncin agadez kawai ke jiranki ba,.....zaki isa Ethiopia......zaki kuma amsa nasu tuhumar qarqashin jagoranci da binciken sheikh muhammad haisam"

"Haisam kuma?" Ta fada tana dauke idanunta daga kan handcuffs din da ake maqala mata. Da farki kafin ya kira sunan haisam.....sanda ake maqala mata ankwar.....tana dubanta ne.....tana jin cewa itace mafi girman tozarci a gareta......amma yanzun da yake shaida mata cewa.....zata fuskanci tuhuma daga wajen hukumomin Ethiopia.....kuma qarqashin sheikh haisam......sai taji wannan tozarcin yafi na maqala mata handcuffs din sau dubun dubata.

Bai amsa mata ba.....amma yaga meye cikin idanunta. Nadama yakeso ya gani me zurfi,duk da hakan bazai qaresu da komai ba shi da ita.....amma sai yake hangen akasin hakan daga idanunta. Kansa ya sake daukewa,sai ya waiwaya ga al'ummar dake gurin.

"Ba ita kadai ba.....duk wanda ya taimaka wajen qulla dukkanin wannan sharrin......to xa'a bincikeshi shima". Ya juya yana nuna mammina da yatsarsa.

"Amma ita......ta rasa matsayinta da komanta a wannan masarauta daga yau!". Daidai sanda guard din suka fara janta. Wani irin fusga me cike da rashin girmamawa.

"Muhammad!!!......don Allah!!!.....ka tsaya ka saurareni!!!,sharrin maqiya ne.......abinda kazo yanzun ka tarar yana faruwa!....."

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Abinda ke faruwa yanzu?.....wansa ya faru a baya fa?.......ko alfashar da kikaso yi da hadiminki da kika saka aka qulle da sunan d'an tawaye saboda bai baki had'in kai ba shima yansu ya faru?!!!......zaituna!.....Ki kirani da matsayina.....ba da sunan mijin da kikaci amana ba....sunana na gaske yabar bakinki da bashi da tsarki!." Ya fadi yana jin zuciyarsa kamar zata tsinke daga qirjinsa ta fado.

Dif wuta ta daukewa mammina.....bama ita kadai ba.....kowa dake gurin.

"Ka yafemin" Ta fada wani irin kukan baqincikin tona mata asiri da rashin mafita da bata hango ba ya qwace mata.

Idanunsa ya lumshe yana jin jininsa kamar gashi yana hawa. Ya lumshesu na second daya yana jin kamar ya binne wadancan shekarun gaba daya.

"Da ace laifin a iya kaina ni kadai yake......"

".....wataqila na iya yafewa" Sai ya bude idanunsa da suka sauya zuwa kalar ja,wani yanayi daba wanda ya taba ganin sultane a cikinsa. Wani yanayi daya sanya kowa sadda kansa qasa.

"Amma kin cutar da marayi.....ba daya ba ba biyu ba.....uku!.....dukka jinina.....akhnan.....mahmud.....da jinjirin ajani......kinso hada haramtaccen aure a tsakanin jini daya......saboda SAFEENA KAWAI?". Mummunar kaduwa ta sakeyi.....dukka wannan.....dama sauran sirrikanta......haisam ya sani?,haisam ya gaya masa?.

"Ka yafemim....bazai sake faruwa ba.....ka dakatar dasu mu fahimci juna.....zan gyara kura kuraina.....zan gyara komai" Ta fada tana jin wata masifa da bala'i suna tsarga mata. Daga waje.....ta hangi tarin 'yan jaridu kafe da cameras da takardu abubuwan rubutu da abubuwan nadar sauti.....ta tabbatar kuma jiran fiddo da ita kawai suke.....kaman yadda kura ke jiran shigowar nama dakinta.

Murmushi me ciwo.....shine abinda ya subucewa sultane....irin ciwon da wanda ke nesa ma sai daya hangoshi. Mamakin rashin kunyar mammina.....mamakin qarfin halinta.

"Matata?" Ya tambaya kaman yana tantama. Ya daga idanunsa yana kallon dattawan da kyau.

"A cikinku.....a nan na tabbatar akwai wadanda suka shaida daurin aurena da zaituna shekarun da suka wuce......to a yanzun a gabanku inaso ku shaida....." Sai ya kalli magatakarda.

"Dakai da mataimakanka.....dukkaninku ku ukun ku rubuta.....ni muhammad hammud........sultane na agadez......na saki matata......"

"Sultaaannne!!!......don Allah!!!!" Ta fada tana turjewa guard din sanda suke dab da fita kuma take jiyo kalaman bakinsa.

Abu na qarshe da zai mata da yafi komai ciwo cikin abinda yayi ko yace kenan......ya rabata da aurensa....auren daya bata kariya......ya bata garkuwa......ya bata abubuwa da yawa da bata isa ta mallakeshi ba. Koda da amsa sunan MATARSA kawai wata alfarma da martaba ce a tattare da ita.

"......na saki matata zaituna saki daya"

".......ya isa sultane.....don Allah!!!" Ta fada tana hada hannayenta biyu guri daya daga inda take tsaye.

"Na saketa saki biyu"

"Na roqeka sultane don Allah!!!" Ta sake fada da mahaukacin sautin daba wanda ya taba jinsa a tattare da ita.

"Na saketa saki uku!" Ya qarasa fada da wani sauti da amon daya ratsa gurin,shuru kuma ya maye gurbinsa.

"Ku ninke ku bata dukkanin takardun uku ta fita dasu......don wannan ce fitarta ta qarshe a gidan nan......" Ya fada cikin umarni.

Sauri sauri suka ninke.....suka kuma miqawa guard din suka karbar mata.

"A tabbatar a yau.....basai gobe ba.....an kwashe komai daya danganci zeenatu anbar gidan nan dashi" Yayi magana ta qarshe yana fita ta qofar baya,qaramar qofar daya shigo a dazu.

Waiwayawa tayi tana duban tafisu. Ta yaya zata bari a tafi da ita haka a qasqance ba tare da tafisu ba?. Ta rasa kowa amma ba zata rasata ba....a duk inda zata fuskanci hukunci tasan zata taimaketa.

"Tafisu.....tana daya daga cin...."

"Karki kuskura ki qarasa" Tafisun ta fada tana dagawa mammina yatsa,abinda ya kusan sumar da ita kenan da wani irin d'an banzan mamaki.

"Kin dauka nima shashace maciyar amana irinki?. Aduk shekarun da muka dauka....kin dauka ina aiki a qarashinki ne?,ina aiki saboda ke ne?" Ta mata tambayar data sanya mammina taji jinin jikinta yana qafewa.

Kai ta girgiza tana dubanta idanunta fal da hawaye.

"Ni 'yar halak ce.....ina zaune dake ne saboda AKHNAN......bazan taba manta halascin safeena a gareni ba...." Ta fadi muryarta tana katsewa da wani irin kuka me cin rai.

"Mutuniyar kirki kenan...baiwar Allah....Allah ya rahmsheta" Sautikan mutane daban daban na yabon safeena ya dinga shiga kunneta. Da qarfi ta runtse idanunta,tana fatan ta daina jin wadannan muryoyin masu yabon safeena a gabanta.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 124* __________________________ *_Amintaccen gurin siyayya_*

*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*

*_BONONZA DA PROMO akai akai_*

*dukka sai a HUGUMA CLOSET*

*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*

*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*

*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*

*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ____________________________

"Na rayu ne saboda na bawa d'iyar safeena kariya daga dukka sharukanki....duk plan dinki da nake baki shawara....kin dauka ina baki shawarar ne saboda amfanin kanki?. Ko kadan,shawarata ina bayar da ita ne daidai da fitar gimbiya akhnan. Daidai da tafiye tafiye da nake yawan yi na kasuwanci.....ba kasuwanci nake zuwa ba.....ina zuwa ne takakkiya karbowa gimbiya akhnan tsari,rubutu magunguna da nake sanyawa a ruwan wankanta dana shanta,tun zamanin uwar hadima birra......har ita birra din ta gaji mahaifiyarta" . Kai tsaye sultane yake gyada kai,don kusan yasan komai,haisam kuma ya sake buda masa komai daga mutuwar da yayi yaje ya dawo,mutuwar da zai iya cewa ta kusan masa daidai da zuwansa lahira da dawowarsa. Daqyar yakai wadannan kwanakin,da qyar yayi surviving bai bayyana ba,saboda ya kasa taunawa......ya kasa hadiye abubuwan da idanunsa ke gane masa sam sam.

"Tir dake...tir da halinki.....tir da daqiqiyar qwaqwalwarki.....na dade ina fargabar kada ki ganoni a shawarwarina......amma da yake makauniyar daqiqiya ce ke,wadda idanunta suka rufe a zalinci da daukan fansa,sai kika gaza gane komai" Idanunta ta runtse tana jin yadda ake yankar naman zuciyarta. Ita giwa......ita qanqantacciyar baiwa irin tafisu ke yankawa magana haka son ranta a bainar jama'a. Ta bude idanunta ta watsasu saman fuskar tafisu. Tana jin inama sultane ya mata lamuni,ya maidata ikonta koda na minti daya ne don kawai ta nunawa tafisu kurenta?. Saidai inaaaa....bakin alqalami ya riga ya bushe. Don takawa sultane yayi yana fita daga gurin gaba daya ma.

Kamar kowa yana jira ya fitane,surutai na la'anta da Allah wadai suka fara tashi akan mammina dake tsaye a qofar qarshe tana kallon taku da ficewar sultane.

"Ashe da bata zama ajalinsa ba,shi shine yake shirin zama ajalinta?" Ta tambayi kanta tana binsa da kallo,tsinuwar al'umma tana bin kunnuwanta zuwa kwanyarta,tsinuwa da la'anta mafi girma,wanda sai taji ta gwammace ta tunkari tambayoyin 'yan jarida akan jin tsinuwar talakawanta.....mutanen da suke rayuwa bisa umarninta da alfarmarta a baya.

Ita. Sarauniyar da take bada umarni. Yanzu ana riqeta kamar mai laifi.

Guards na Ethiopia na tsaye a gefenta. Ba girmamawa,ba tsoron nan nata da take gani a idanunsu.....ba ban girman nan wanda ke tattare da iko,aikinsu kawai suke kaman yadda suke serving kowanne me laifi.

Babbar gate na masarautar suka nufa. Tafiyar da take jin kamar kowanne step na cire mata shekaru ne daga jikinta. Daya daga cikun guard ya tura qofar ya budeta,take kuwa

Flashes. Cameras. Hayaniyar ‘yan jarida suka cika mata idanuwa da kunnuwa.

Ta sake fidda idanunta tana mamakin cikar gurin. International press har da na qasarta Ethiopia da reporters dinsu kaca kaca......royal media.....da tarin mutanen da take tunanin ta wuce musu.....ta tsere musu yau gasu gata.

Ko ba'a gaya mata ba,yanayin 'yan jaridar dake tsaye a gurin na qasashe daban daban dake zagaye da yankin sahel kawai ya gaya mata shiryayyen abu ne.....wannna abun....an shirya faruwarsa dama a yau din,bawai shi ya shirya kansa ba.

"Ranki ya dade......da gaske ne cewa kin boye asalin identity dinki na asalin qasarki ta Ethiopia?"

"Da gaske ne kin kubuta daga Ethiopia da sunan daba naki ba?"

"Ranki ya dade.....me zakice game da zargin da ake miki wanda yake da alaqa da rayuwarki ta baya?" Kai kawai take girgizawa. Ba zargin ba.....ba mutanen ba ...tarin hasken cameras din dake shige mata idanu,yana kuma sake tabbatar mata da adadin yawan tulin 'yan jaridar dake gurin.

"Sources claim your Agadez identity papers were false documents.”

“Were you living under a fabricated royal identity all these years?” tambayoyi biyun da suka sake dimautata. Ta soma numfashi da qarfi. Saboda yanzu,abinda take tsoro fiye da prison ya same ta........public humiliation.

Mutanen da take rainawa,take mulka,take tsoratarwa......yanzu suna kallonta cikin handcuffs,ana kuma tambayarta irin tambayar da akewa criminal sak!.

Sai a yanzu ta fahimta.....shurunsa.....shurunsa da gaske hadari ne me girman gaske.....shurunsa yana gina rushewarta ne a hankali,cikin wani irin salo da bai buqaci gagggawa ba kwata kwata. Shurunsa!....da tasan yana da wannan ikon......tabbas data saka qaimi da kima sama da yadda ta saka a baya. Shurunsa!....inda tasan hakane.....da ta sanyashi ya zama me yawan motsi....me yawan magana a komai.

"Are the accusations true?!” dan jaridan ya sake tambayarta da faransanci.

"Did you manipulate the Agadez throne?!”

"Do you regret what you did to the royal family?!”. Tambaya ta qarshe......tambayar qarshe data sanyata daga kai ta kalli dan jaridar

"NADAMA" Kalma daya me dauke da haruffa shidda da ko bayan ranta batajin zata yarda ta rabi gawarta.....ballantana yanzun.....yanzun da har a sanda take tsaye a raye take. Ita kuwa ya za'ayi ta bari haisam yaga NADAMA a idanunta?. Ta FADI kenan fa?,shi kuma yaci nasara?. Janta da guards din sukayi zuwa gaba tare da datse 'yan jaridar da suka dauki hotunansu iya son ransu a mabanbantan yanayi shine ya katse tunanin ta,hotunan da suka zame mata abun tsoro.....hotunan da bata da tabbacin ina da ina zasu tsaya?.

*H A I S A M*

Cikin jikinsa yakejin wani yanayi na tashin hankali.......yana jin kamar a duniya bai taba jin tashin hankali irin wannan ba......irin yadda yaga akhnan shimfide a hannunsa cikin dogon suma.....dogon suman daya dinga jin kamar mutuwa zaiyi.....kamar binta zaiyi shima.

Ya manta duk wani taimakon gaggawa daya iya.....da wanda aka koya masa na yadda zai kula da me yanayi irin wannan......kawai neman tallafin likita ta daban yake.

Hannuwa da idanuwansa a kanta,sanda likitar ta gama bata duk taimakon daya dace.

"Tana buqatar hutu da nutsuwa" Abinda tace masa kenan a taqaice. Idanunsa ya lumshe yana jin bayananta. Sai yaji kaman yayi tsuntsuwa shi da ita yaga sun bar agadez din.

"Zata huta.... Lallai akhnan zata huta,alqawarin fansar raine wannan" Ya fada can qasan maqoshinsa ba tare da kowa yaji abinda ya fada din ba.

Duk yaqin da yayi.....duk plan din daya gina.....bai taba tsoron rasa komai ba kamar yadda yake tsoron rasa numfashin akhnan.

A hankali ya dora goshinsa saman nata,ya runtse idanunsa tightly.

"Don't do this to me" Ya fada da wani irin rauni ganin ta dara mintunan da likitar tace mata zata farka. Muryarsa a wani irin karye. Kamar ba shine wanda ke tunkarar muggan masu laifi ba,ya kamesu daya bayan daya ba tare da tsoro ko shakka ba. Yau gashi a zube gaban mace.....cikin wani irin tarin rauni da tsoron rasata. Baisan baida juriya ba sai yanzu a kanta....baisan rago bane shi sai yanzu.

"You scared me" Ya fada yana motsa wadannan labban nasa.

"You weren’t supposed to carry this much pain.” ya fadi yana maida mata gashin kanta daya taba gefan fuskarta bayanta.

"Not all at once" Ya qarasa fada muryarsa tana sakeyin laushi

"I should’ve prepared you better.” ya fadi da zargin kansa cikin muryarsa. Sai ya sauke kansa kad'an.

Karo na farko!.....karo ma farko bayan dogin lokaci ya bari gajiyarsa ta bayyana.

".....but i was selfish" Ya gayawa kansa yana jin dukkan tuhumar da zuciyarsa take masa daidai ne.

"Ki yafemin......i just wanted it to end.” ya furta yana dora labbansa saman bayan hannunta.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Kamar taji wannan connection din......kamar taji wannan dumin.....kamar taji wannan lallausan labban da basa gajiya da narkar mata da zuciya da lausasan kalamai saita motsa yatsun nata. Daidai inda ya ajiye lips dinsa. Ta motsa kadan tana bude idanunta.

Fes ta zubesu akan fuskarsa,komai yana dawo mata sabo daya bayan daya.

Shi din dai......haisam dindai.....always him. Shi ta fara gani.....shi idanunta suka fara gani kafin kowa.

"Haisamm" Ta kirashi da sunansa....sunansa din da sai yanzu ya soma sonsa tsahon lokaci....sunan da sai data fara furtashi sannan ya fara jin dadinsa.....sai da labbanta suka fara fidda sautinsa sannan ya gane yana daya daga cikin abubuwan da yakeso ashe a tattare dashi.

"I'm here giiftii" Ya fada yana kamo fuskarta cikin tafukan hannayensa yana sanya idanunsa cikin nata. Yana kallon yadda numfashinta ya sauka. Ya sauka da wani irin relief.

"I'm right here biftu" Ya sake fada ta sigar ra'da. Kallonsa itama take,tana qyaftawa a hankali,sai ruwan hawaye suka fara cika mata idanu.

"Bappi.......he's alive" Idanunsa ya lumshe yana jin yadda take karya masa zuciya.

"Yes giiftii"

"......he's alive" Ya qarasa fada da taushi a muryarsa.

Kuka sosai ta saki amma mara sauti,sai hawayenta......d'aya yana bin daya.

"Ka sani.....na tabbatar ka san hakan tsahon wannan lokacin". Sake riqeta yayi sosai,yana sunkuyowa fuskarta da kyau.

"“I needed to bring him back safely.” sai ya qarasa fadin.

"And I needed Mammina exposed completely.” da wata irin murya cikin kunnenta,kamar ita daya kawai yakeso taji abinda yake fadi din.

"Na dauka da gaske ya mutu.....na dauka mun binneshi"

"I know.....i know habibti"

Ta rufe idanunta tana kuka da wani irin rauni da taushi. Sai kawai ya kwanta kusa da ita kawai ba tare da ya matsa mata ba. Just enough for her to feel him there. Zuciyarsa na wani sake raunana,yana jin kamar baida kalaman da zai wanke kanshi a gurinta.

"Sleep.....ki barci....ki huta.....everything is over now" Ya fada yana bata comfort sosai da duvet ta kowanne angle yadda zata jita safe yadda ya kamata.

Shuru me hade da zubar hawayenta ya cakuda guri daya,bai matsa daga gurin ba,bai kuma daina jin yadda zuciyarta ke sauka ba a hankali.

"Did you ever think I’d hate you for hiding it?” ta furta a hankali. Qasa ya danyi da kansa.....kalmar tana masa nauyi.....amma hakan bai hana boyayyen murmushi subuce masa ba,bai motsa ba koda yatsansa kuwa,sai tausasan labbansa daya motsa a hankali.

"Yes" Amsar ta fita da dukkan gaskiyarsa.

"And I was ready to live with that…” ya sake fadi.

"…as long as you survived this.” ya fada da wata tarin nutsuwa data sanyayar da jikinta.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

Readers Also Read

More by Huguma