L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 71
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 71: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 71. Yanason soyayya da matuqar qurewar da tun kafin yayi…
3,341 words
Yanason soyayya da matuqar qurewar da tun kafin yayi aure yakejin zai iya haqura da komai idan matarsa bata iya ba.....amma banda soyayya. Soyayya ta gaske.....bawai intimacy ba.....ba kwanciyar auren kawai da rungume rungume ba. Soyayya me dafa zuciya.....wadda ana iya rayuwa da abokin rayuwa da kowacce naqasa da sai samu. Saboda ZUCIYAR ta dahu da soyayyar...... ZUCIYAR kuma ita akeso.
"Me yasa?" Ta tambayeshi a nutse. Kasa daurewa yayi,sai dayakai hannunsa ya shafi gefan fuskarta.
"Because I’m taking my wife somewhere.”
"Where?" Ta sake tambaya.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 127* ___________________________ *_Amintaccen gurin siyayya_*
*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*
*_BONONZA DA PROMO akai akai_*
*dukka sai a HUGUMA CLOSET*
*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*
*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*
*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*
*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________
"Madeena" Ya furta kalmar na fita daga anihin zuciyarsa da wani irin nauyi da kimar gurin dake qaruwa a ruhinsa kowacce rana.
"Madeena" Ta fada itama idanunta a lumshe...... Karon farko da garin ya tsaye mata a rai da wata irin tarin soyayya.....shine tafiyar da sukayi shida ita. Sanda ta gane girma da matsayin gurin. A yanzu sake dawo mata garin yakeyi da wata doki kaman bata taba zuwa ba.
"Eh can.....kina buqatar qarin nutsuwa,ni kuma......" Ya bude idanunsa sosai yana kullesu da nata.
"…need to thank Allah for returning you to me whole.” wani irin taushi ya cika zuciyarta. Wani irin laushi sanyi qauna da soyayya. Sai taji kaman ya mata albishir na zuwa wani guri da bata taba zuwa ba.
★★Tana zaune daga bakin gadon,cikin wata nutsuwa,sanye royal abaya two in one data fidda sigar kanta da kuma jinin izzar dake jikinta. Wani irin kwantaccen kyau irin na asalin buzuwa. Saidai ita duka ba wannan take kalla ba.
Haisam.....haisam dinta dake sanya da wata sassalkar throbe saqar qasar oman. Ta masa kyau,wani irin kwantaccen kyau me daukan hankali. Shi take kalla.....da wannan kyan nasa da wani lokaci yake sanyawa taji ta raina kanta da kanta idan har ta kalleshi.
Links din hannunsa yake sanyawa a hankali,zara zaran eyelashes dinnan nasa sunwa idanunsa rumfa. Saita miqe a nutse,ya daga kansa zuwa gareta sanda yaji alamun tafiyarta yana sauke mata tattausan murmushi.
Links din ta karba,ta fara saka masa a hankali,ya sauke wani tattausan murmushi yana jin dadin yadda tayi masan cikin kulawa. Idanunsa akan kyakkyawar innocent fuskar nan tata da tayi kusa dashi sosai. Ya miqa yatsansa a hankali ya aza saman tiny lips dinta dake tsananin burgeshi. Zagayasu ya fara yi da yatsan nasa,yana jin sulbinsu da taushinsu. Tadan motsa bakin kadan saboda wani irin yanayi yammm da yake saukar mata.
"Ka duba kanka?" Ta tambaya da yanayin kulawa,saidai bata d'aga kanta ta kalleshi ba. Idanunsa ya fidda gaba daya alamun neman qarin bayani.
"Tun safe kake pretending kana lafiya,amma zuciyarka bugawa take" Ta qarasa fadi bayan ta gama saka masa,ta kuma goye hannuwanta a qirji tana kallonsa,kyansa yana son bugar da ita.
Yatsansa daya ya miqa ya kalaci hancinta. Ta tafi dashi ainun,duk da ba ma'abocin kallon mata bane shi.....amma yasan matarsa ta musamman ce.
"Kina iya jinta yadda take bugawa yanzu?" Ya tambaya yana lumshe idanunsa da wannan murmushin dake qara masa kyau.
Idanunta tayi rolling.....blue eyes dinnan dake tafi da nutsuwarsa.
"Eh.....ba yanzu ba....ko yaushe ina iya jin yadda zuciyarka take bugawa". Taku biyu ya qara ta hade tazarar dake tsakaninsu,ta bude lallausan tafin hannuta ta dorashi saman qirjinsa.
" Wannan gurin.....wannan muhallin....mallakata ce.....ta har abada.....zaka bani ni kadai?,zaka qyale gurin ya zamana baquncin soyayyata kadai ya taba karba?.....zaka ci gaba da mallaka min nan din har abada ni kadai?" Ta furta muryarta a sanyaye tana dora kanta saman qirjinsa.
Murmushi ne kawai ke fita daga samam fuskarsa. Wani kalan murmushi da yaji zuciyarsa tana narkewa. A hakan da suke tsaye.....shima bugun zuciyarta yakeji,bugun zuciyar daya zamana cike da kishinsa.
Fargaba taci gaba da mamayarta jin yayi shuru,amma sai taji tausasan hannuwansa yana dagata daga qirjinsa. Ya bude idanunsa sosai yana kullesu cikin nata.
"Khadeeja" Ya fada yana motsa labbansa da suka bata sha'awa har suka sanyata rufe idanunta da kuma budesu.
"Na'am". Kai ya girgiza.
"Wallahi......bazan taba iya adalci tsakaninki da wata mace ba......ta yaya nasan ni rago ne?,bani da kalar wannan jarumtar zan bawa wata mace baquncin wannan gurin?. Gurin da ke kika fara budeshi sannan kece ta qarshe?. Kinsan yadda Allah ya jarabceni da sonki har kike tunanin zan iya naso wata macen kuwa?" Ya fada dukkanin idanuwansa da kalamansa suna fadin gaskiyar abinda ke cikin zuciyarsa.
Kai ya sake girgizawa.
"A cikin tarihin duniya.....banajin akwai namijin daya jarabtu da soyayyar wata d'iya mace.....irin yadda na jarabtu da taki khadeeja" Ya fada yana aza hannunsa saman qirjinsa,idanunsa sun lumshe kansu da budewa.
Wani irin yanayi me sanyi.....wani irin yanayi me taushi taji yana ratsata. Ta bude idanunta a kansa har sau uku tana rufewa. Sai taji ta rasa a wacce duniya take?,ta buda bakinta a hankali zata sake magana,amma sai ya aza yatsansa akan lips dinta.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Chapter closed please......wannan hirar batayimin ba.....muje ki rakani" Ya fada yana kama tsintsiyar hannunta.
"Morsa......tasan sa khadeejanta zasu hadu kuwa?" Yayi tambayar wa akhnan sanda take tayashi saka bisht dinsa tana zagayawa ta bayansa tana gyara masa kafadun. Abinda ya sanyashi yaji kansa ya wani qara kumbura kenan. Tana treating nashi sometimes kamar wani sarki. Murmushi ya subucewa kyakkyawar fuskar akhnan.
"Bata sani ba.....ta dauka kawai ordinary khadeeja ce zatazo" Murmushin gefan baki yayi a hankali
"She’s going to cry.”
"Both of them fa" Akhnan ta fadi tana sakin siririyar dariyar da taso shagaltar dashi,har baisan sanda ya saka hannu ya dawo da ita gabansa ba yana riqe da qugunta. Yayi missing dinta....kewa ta sosai,amma yaja jiki saboda yanaso taji a ranta she's ready......yanaso taji a ranta itama tanason mu'amalar......yanason kuma ya gane adadin matsayinsa a zuciyarta.....ya kuma gani....sannan ya gane din gaba daya.
"And you.....you'll cry too?" Ya tambayeta bayan zubawa juna idanu da sukayi na wasu sakanni suna kallon junansu cike da shauqi.
"I’m stronger than all of you.” ta fada idanunta suna rage girma a hankali da wani irin shauqinsa dake fusgarta.
Tun daga saman kansa har tafin qafafunsa yaji wani abu ya yarfa masa. Sai ya sassauta riqon daya mata kadan,ya kuma sunkuyo saitin fuskarta sosai har tana jin wannan numfashin nasa me qamshin gaske dake fita zuwa saman fatar fuskarta.
"Liar" Ya fada qasa qasa yana qaramar dariya. Sakin numfashi tayi cikin jin kunya,sannan ta tureshi baya a hankali da hannunta dukka biyun,amma ko gezau bai motsa ba ballantana ya matsa. Yana murmushi,idanunsa yana kanta,deep and soft.
"You’ll stay with Safiyya and Falaak?” ta gyada kai a nutse.
"We'll receive her here" Kai ya gyada a hankali yana zare jikinsa,taku biyu baya sannan ya juya a hankali.
"Watch morsa safiyya carefully.....she may collapse from shock" Murmushi tayi har cikin ranta tana jin dadin yadda yake treating duk wani ahalin sultane.
"You sound worried.”
" Yes....I'm " Ya fada yana dawowa gabanta ya tsaya,ya bata lite kiss a goshinta,wanda har cikin jininta taji dumin lips dinsa.
"Everything beautiful scares you first.” ta fada tana zura hannunta cikin nasa.
"But somehow…” “…you still bring it into people’s lives.” Wani irin kallo ya mata......deep enough da ya sa zuciyarta bugawa. Sai ya kamo hannunta. Ya sumbaci bayan tafinta gently.
"Pray for today"
"I already did" Sai ya juya zai fita,don ya fahimci idan suna tare ita dashi basa gane muhimmanci komai sai kawunansu.....basa kuma gane yadda lokaci yake gudu sai sunyi da gaske.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
Amma kafin ya kai qofa,khnan ta sake kiransa da wani irin laushi a muryarta.
“Haisam.” Ya tsaya sannan ya waigo,sai ta zuba masa ido cikin wani irin softness.
“Thank you…” ta dan dakata.
“For bringing families back together.” shuru Na second biyu,kamar maganar ta tab'a wani very deep part a zuciyarsa. Sai ya gyada kansa a kadan yana duban blue eyes dinta dake jansa zuwa gareta.
“See you soon, habibti.” ya furta da wannan husky voice din nasa,sannan ya fita ya barta da bugun zuciya mai laushi,da wani kalan murmushi a lips dinta,tare da jin cewa yau… zata shaida wata rana da baza’a taba mantawa da ita ba,sai taji kewa ta kamata....kewar mamminta. Inama ace tana raye?....inama ace harda ita za'ayi wannan kyakkyawan reunion din?.
"Allahummagfir laha" Ta fada a hankali. Tun daga ranar data tsinceshi yana yiwa wasu lecture akan muhimmancin yiwa iyayen da suka rasu addu'a......bata sake bari rana ta fito ta fadi ba tare data saka a addu'arta ba.
★Koda kai baqo ne.....koda kuma kai din bakasan komai ba daga yanayin convoy na motocin dake bin kwalta cikin nutsuwa zuwa ainihin agadez palace zakasan cewa wasu mutane ne na musamman. Wasu baqi ne masu cike da daraja da kuma alfarma suka iso qasar agadez din.
A daidai wannan lokacin morsa safiyya ke yafa mayafinta,abu na qarshe cikin adonta na yau. A shirye tsaf falaak ta turo qofa,ta dora idanunta a kanta a hankali tana kallonta. Tayi haske sosai da wani irin yanayi data tabbatar na shigar yaron ciki ne.
Wani abu guda daya dake sanyata yawan sakin murmushi kenan,tana sake hamdala ga ubangiji dake daidaita komai cikin qaramin lokaci. A yanzun.....wannan fatanne cikin idanunta da zuciyarta......wannan burinne a ranta taga akhnan tana sauyawa irin haka,sauyin da zai tabbatar da shigar ciki a tare da ita. A ranar idan har ta tabbata......batasan wanne irin yanayi na farinciki zata shiga ba.
Tana yatsina fuska ta qaraso.
"Momma.....kin dade yau,suna kusa da titinnan fa?". Abun hannunta ta dauka tana sakawa. Abun hannun da kullum zata sakashi yana tuna mata da khadeeja ne da safeena. Ta sare zuwa yanzu da dukkan buri da fatan haduwarsu a gaba....saidai bata sani ba ko sai a rayuwa ta gaba?.
"Bansan me ya sakani wannan nauyin ba falaak......yau fargaba naketa fama da ita."
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 128* __________________________ https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0
*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*
*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*
*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*
*_Assalamu alaikum my loyal people_*
*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*
*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*
*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*
*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*
*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*
*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*
*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*
*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*
*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee* ___________________________
"Hmmm.....kin saka zancan ahmad dai a ranki....kin nunawa sultane kaman yadda yace kinfison d'anki a kanshi" Ta fada tana dariya. Dariyar itama momma tayi tana takawa zuwa hanyar waje falaak ta bita.
Bawai bataso ahmad yaci gaba da sarautar agadez bane kaman yadda sultane suka yanke da haisam......aah gani take kaman yayi quruciya da yawa.....a qalla a barshi ya cika shekara ko talatinne zuwa da biyar. Amma a qarshe ita kanta taga ba wani zabin sama da wannan,don haka sai kawai ta bisu da addu'a.
Daidai sanda take fitowa akhnan ta shigo cikin rakiyar hadimanta. Tayi kyau cikin wani tsadajjiyar atamfa exclusive wine colour da ratsin peach me haske. Wadda wuyanta da hannuwanta duka aka yiwa wani sirfani. Dan siriri ne na alfarma daga mafi tsadar zare. Tea boubou ce data zama kaman oversized a jikinta. Amma ko daga iya yadda dankwalin ya zauna mata a kanta.....sai tayi wani sirrintaccen kyau me jan hankali.
A saman kanta kuma saman daurin kanta na ture kaga tsiya ta dora mayafinta,saita fita a matar aure da wani irin aura me jan hankali.
Kaman yadda ta saba yanzu.....kanta tsaye ta isa jikin morsa safiyya ta rungumeta......itama saita rungumeta sosai tana jin wani farinciki yana mamayarta,kafin kuma ta zame a hankali tana gaidata,ta amsa mata tana riqo hannayenta,sannan ta riqeta suka fara takawa waje,daidai sanda hayaniya kadan ta qaru cikin gidan da motsin manyan qofofin gidan guards da securities.
Sanda motocin suka tsaya cak a muhallin tsaiwar motoci na gidan....gurin ya cika da securities da guards na Ethiopia dana agadez gaba daya.....siririyar busar sarauta na tashi cikin wani yanayi da ba hayaniya a ciki....haka kawai sai morsa safiyya ta samu kanta da qarin faduwar gaba.
Idanunta akan motocin sanda mutanen ciki suka fara fitowa,taga haisam ya fito,ya kuma zagaya side din motar daya fita a ciki zai bude,tabbacin mmamarsa ce a gurin,daidai sanda armelle ta qaraso tana mata magana akan kammala shirya dakin cin abincin,sai ta dauke idanunta tana maidawa ga armelle.
"Sannunku da qoqari.....hakan yayi,kowa yana iya tafiya tunda an kammala k....." Ta qarasa maganan tana maida idanunta inda haisam ya fita dazu. Saidai kuma ta gaza qarasawa,saboda abinda idanunta ke gane mata.
Wata razanniyar almara da Zuciyarta ba zata taba yarda da ita ba,don ta tabbatar idanunta ne suka yaudareta. Wata almara da taso tafi komai daga mata Hankali.
Khadeejanta take gani,tana magana da wannan nutsuwar tata tunta quruciya,da wasu shekaru na girma,idanunta akan haisam..
Idanu ta zuba sosai,saidai fa suna sake matsowa tana sake ganin khadeeja dinta muraran a gabanta.
"Itace.....Allah ita ce" Ta fada a fili ba tare data sani ba.....dukka ilahirin jikinta yana rawa,abinda ya sanya akhnan kama hannunta a nutse tana son bata nutsuwa,daidai sanda nanay ke janye idanunta daga haisam,wanda da alama wani bayani yake mata suka sauka akan morsa safiyya.
Cak ta tsaya tana kallonta. Ta sani yaronta baya qarya....haisam a tsahon shekarun data rauneshi,tun daga quruciya zuwa girma ba zatace ga sanda ta kamashi da laifin qarya ba,amma kuma sai yanzu take sake tabbatar da maganarsa a zahiri.
"Sadiyeee" Nanay ta faurta da murya me rawa.
"Itace.....ta kirani da sunan da iya su biyu kadai suke kirana dashi" Ta fada a fili. Idanun morsa safiyya ne ya cika da hawaye,ta soma takawa da sassarfa tana fadin.
"…Khadduu?” sunan saka nanay itama kasa jiran qarasowar morsa safiyya,saita soma takawa da nata hanzarin don ta cimmata.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
A tsakiya suka hade ita da ita,suka yiwa junansu wata wawar runguma da saur kadan su zube qasa,saida hadimai suka lullubesu daga idanun mutane akhnan da falaak harma da haisam suka tsaya a gefansu.
"Khadduu.....khadduu" Shine kawai abinda morsa safiyya ke maimaitawa tana jin kamar cikin mafarkanta take.
"Sadiyeeee.....'yar uwata" Nanay ta furta da qyar saboda kalan kukan dake neman shaqeta. Sake rungume juna sukayi sosai,kamar masu tsoron idan suka saki juna d'aya zai bace ya sake barin dan uwansa. Suka raunana zuciyar kowa dake gurin,musamman sultane dake gefe tsaye shida motii da motarsu sai yanzu ta ida qarasowa. Falaak ta fara qwalla,saiga akhnan tana hawaye har suna fita a idanunta. Tana hango wannan tatacciyar soyayyar ta 'yan uwantaka har ina?. Inda ace mamminta tana nan yaya zai wannann kyakkyawar haduwar zata kasance?.
Idanunta suka fada kan haisam,sai a sannan ta lura bai damu da kowa ba....ba wanda yake kalla a gurin sai ita,ita kadaice idanunsa suke kansa.
Ido daya ya kanne mata yana hade yatsunsa biyu,ya mata maga da ido da yatsun ba tare da yace komai ba.
"Kinyi kyau sosai.....karki kuka....zaki bata wannan fuskar".
" Wannan mutumin" Ta fada cikin ranta tana gayyato jarumta. Batasan a wanne layi zata sakashi ba....a komai ya qware,komai kuma ya iya,ya isar mata da saqon soyayya cikin salo,ba tare da kowa dake zagaye dasu ya fahimta ba.
Saida sultane da motii sukayi magana aka samu daidaituwar yanayin,suka fara takawa ciki hannuwansu cikin na juna,idanunsu cike da mamaki da qaunar junansu.
"Kin tsufa.....girma yazo"nanay tace da morsa safiyya cikin murmushin da zai gaya maka akwai abinda ta tuna zamanin suna tare ta fadi haka.
"Ke kuma har yanxu kina kuka idan kika tsorata" Dukkansu suka yi dariya cikin hawaye.
Kasa jurewa morsa safiyya tayi,ta waiwaya tana duban haisam.
"Kai ka dawomin da ita?ya akayi baka manta labarin khadduu dina ba saida ka dawomin da ita?" Tace da haisam dake musu gadi daga bayansu. Dariya kadan nanay ta sake cikin nishadi,duk da hawaye ne fal idanunta.
"Danki ne fa......dankine da baki sani ba" Cak morsa safiyya ta dakata da tafiyar,ta juya gaba daya tana kallon haisam
"La'ilaha illalllahu......muhammad?" Kasa qarasa magana tayi,har saida muryar sultane ta bayyana.
"Idan safiyya ta gagara ci gaba da tafiya....to a nemo abun daukarta mana" Maganan ya bawa kusan kowa dariya a gurin. Anaani rumaisa noorah da khansaa gaba dayansu suna jinsu cikin wata sabuwar duniya,gasu a baquwar qasar da basu taba zuwanta ba.
Wani irin zama ne akayishi cikin qawataccen parlor din na alfarma. Parlor ne da kusan sai manya manyan baqin sultane ko baqin da suka shafi cikin gidan ake saukarsu a ciki.
Zama ne me tsayawa a zukata.....cike da farinciki da walwala. Dariya da murmushi na gasken gaske ba fake ba,wani irin nutsuwa me cike da sukuni da kuma walwala. Karbar baqin zuwa yanzu ya wuce hawaye da runguma kawai......ya kuma wuce zaman tattauna abubuwan da suka faru da sake bude tarihi tsakanin nanay da morsa safiyya,ya zarce ga zaman cin abinci na bai d'aya.
Ba zancan surukuta a gurin nauyi ko jin kunya,motii nanay morsa safiyya da sultane sunaji a jikinsu dukkaninsu nasu ne.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 129*