L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 72
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 72: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 72. Saidai duk a wannan zaman....a wannan yanayin idanun…
3,352 words
Saidai duk a wannan zaman....a wannan yanayin idanun akhnan lokaci lokaci yana fadawa kan dan matashin saurayin da batasan waye ba,wanda a qalla zaiyi sa'an hairaan ya girme mata sosai ko ba'a fada ba.....amma tana ganin kamannin mamminta a tattare dashi..
"Da jinjirin safeena daya bata fa" Maganan da yaja hankalin morsa safiyya,hannuwanta na rawa take riqe da Muhammad. Zaman cin abincin da bai yuwu ba,sai koke koke ya koma sabo.
Akhnan jin Zuciyarta takeyi tana sake nisa da tsanar mammina sanda motii ya gama cikakken bayani shima muhammad ya dora da nasa,kafin motii ya sake karba.
"Wannan zuciyar dukiyar ajani din.....ta muhammad ce....yamin wasiyyar ya barwa duk abinda safeena zata haifa,saboda yasan bai zarce kason daya zama haramun ka kyautar ba...kuma kaman yasan zai zamana baida kaso a dukiyarsa......muhammad yaqi karba.....yace na riqa masa.....ko na bawa obbo dinsa,shi kam yanzu neman ilimi zai tafi,kuma in sha Allah sati me zuwa zai wuce madeena can zaiyi dukkanin karatunsa,haisam ya gama masa komai lokacin tafiya kawai ya rage ".
Data daga idanunta tana kallon haisam.....ba miji kawai ya gani ba. UBA ta gani.....wata KADARA ta gani me tsananin tsada da daraja. Wani LU'U LU'U da mallakarsa sai me tsananin sa'a. Ta sake maimaitawa kanta tambayar.
"Wanne abun arziqi na taba yiwa Allah a duniya ya mallakamin wannan LU'U LU'UN?" tayi tambayar a hankali qasan ranta tana kallon shehnaz da tayi joining dinsu.
Bata manta ba......a safiyar yau ya mata abinda ta kasa riqe kukanta. Ta samu labari dama daga birra.....kaf kayan da mammina ta dinga saidawa tana gwanjonsu ya maidosu. Secretly ya sanya mutanensa suka dinga shiga suna siyan kayan da farashin da yafi kowanne tsada da daraja. Komai ya maidashi a muhallinsa,kamar ba'a taba ba. Kwatsam sai ga takardar kamfaninta a hannunsa.
Sahel couture.....kamfanin da mammina ta d'ai d'aita shi da mummunar sata......tare da hadin bakin ma'aikatan bogin data zuba a kowanne reshe na kamfanin,sannan kuma ta aza alhakin hakan akan aisa qarara. Ba kunyar nannie ba komai......taso ta mata tozarci,saidai bayan haisam ya maidata kamfanin bisa murde hukuncin mammina,ya dora aisa a wasu hanyoyi da dabarun da sai da suka gano daga inda komai ya fara. Ya barta taci gaba da rusa kamfanin har zuwa sanda tayi gwanjonsa. Ya ninka kudin ya kuma siya ta hannun jabeer ba tare da tasan waye ba.
Saidai kuma.....a yanzun da takardun saheel couture yake dawowa hannunta da sunan mallakinta a karo na biyu.....ba sahel couture take gani ba. Wani gingimemen kamfani take gani,wanda yake da qarfin jarin da zai iya gogayya da sauran kamfanunuwan qasar waje. Sun mallaki komai nasu na qashin kansu,ba buqatar zuba hannun jari daga kowa.
Sahel couture din daya zama wani na duniya gaba daya....ya fara qoqarin gina reshe a dubai,kusa da kamfanin turaren daya mallaka mata. Kamfanin turaren da har yanzu ta gasgata yarda ya zama nata. Saboda duk sanda suka zauna ita dashi......yanaso ya qarasa handling komai na kamfanin.....ya buda mata komai a matsayinta na CEO....mamallakiyar kamfanin sai ta kasa qarasa zaman dashi.
Kudaden da take gani yana lissafi kawai akai suna gigitata tare da gaya mata anya reality ake magana?.
Bai wani yarda ta masa godiya ko daya ba.....hasalima ya b'uge da tsokanarta ne. Tayi kuka sosai tana tuna ranakun baya data rainashi.
A yanxun kuma da yake dawo mata da danginta daya bayan d'aya. Yake dawo mata da ahalinta.... Ruhinta farincikinta dukka tattare da ita saita rasa dame ya dace ta saka masa?.
"Ya dawo mata da morsa safiyya.....jajirtacciyar uwar dataso rasawa.....ahmad.....ga muhammad da kwata kwata duniyarta batasan dashi ba sai yanzu. Ya qara kusanto mata da nanay....amintacciyar mahaifiyarta.....ya sake qara mata yawan 'yan uwa ta hanyar hada nasabarta dasu Anaani.....rumaisa.....noorah.....Aareef.....hussam.....balqees da khansaaa duka.
Idan ta juya ta kalli Ahmad......ta kalli muhammad..... Sai taji wani abu me laushi da nauyi saman zuciyarta.
Ashe dai itama tana da gata?,ashe 'yar gata ce itama sama da qasa,yayyen nan maza da take ganin wasu dasu.....ashe dai itama tana dasu?.
Wata qauna lokaci guda irin ta 'yan uwantaka ta soma tasiri tsakaninsu,amma duk da haka sai taga kamar falaak ma ta fita murna da d'oki. Don ita din,bata da saurin sabo,uwa uba wannan dabi'ar miskilancin har yanxu bata barta ba.
Daga baya mazan motii sultane ahmad muhammad hussam Aareef da haisam suka wuce sukabar iya matan. Su dai su akhnan suna zaune suna kallon ikon Allah. Lokaci lokaci sai nanay ko morsa su kalli juna,su saki murmushi,kosu riqe hannun juna. Sun manta dasu dake gurinma kwata kwata.
Sabuwar 'yan uwantaka....tsohuwar soyayya,dangantar zuci ta fara motsawa. Hirarsu suke suna tuna baya,suna tuna daa....amma kuma idan suka tuna da safeena ako wanne gurbi saisun tsaya sun zubda hawaye.
Anaani da noorah da kuma hasnaa sun wuce sashe na musamman dake manne dana nanay na baqi na musamman,amma rumaisa ta wuce kitchen inda 'yan aikin morsa safiyya ke qoqarin sake dora wani abun,duka cikin nuna girmamawa da karramawa ga baqin nasu.
Yadda suke tuna safeena da yawan kukan da taga sunayi ya sake karya mata zuciya. Sai kawai ta miqe. Bata gaji da ganinsu haka a tare ba.......tana jin kamar mamminta itace ta ukunsu,tana tare dasu a sannan,don haka saita yanke bin rumaisa kitchen.
Wani abu daya data lura dashi.....mulkinsu ko sarauta da yawan dukiya da iyayensu dasu kansu suka mallaka bata sanya sun rasa kansu cikin masu jin izza ko girman kai ba. Tana mamaki zamanta a Ethiopia yadda zata samu rumaisa a kitchen,duk da tarin hadimai dake qarqashinta wadanda aka ajiyesu kawai donsu hidimta mata.
Ko yanzu data shiga,ta sameta ita da me aikin morsa safiyya guda daya......wadda asalinta 'yar oromo ce. Tana hada wani abinci rumaisa na gefanta tana kalla suna hira.
Yadda taga rumaisa ta zage tana tayata hadawa,kawai saita samu kanta da sha'awar zama kamar haka. Falaak ta iya komai.....itama dai kamar su rumaisa din,ita aka baro a baya. Morsa safiyya ta taba fadi,duk daba da ita take ba,amma a sannan ta riqe abun,hartana jin zafinta tana ganin da ita take. Fada takewa falaak a wani yammaci datayi kuskuren hada mata wani abincin gargajiya na abzinawa.
"Macen da bata iya girki ba ta rako mata duniya ne. Koda mahaifinta waye......samun hanya ko qofar zuciyar d'a namiji.....tana ga cikinsa,wato abincinsa."
Burinta a yanzun daya ne tak!....ta zama cikakkiyar macen da zata hidimtawa mijinta ba....ba wadda bayi zasuyi hidima da ita sannan suyi da mijinta ba. Sai ta samu kanta dayin tattaki tana harhada plates din da aka gama amfani dasu.
Daga me aikin har rumaisa sunso hanata amma taqi. Suka dinga juyawa time to time suna kallonta,har me aikin ta gama tabar musu kitchen din,saiga Aanani tana santin agadez,harta sauya kayanta zuwa na lounge wear,masu kyan gaske da taushi irin wanda safiyya huguma ke kawosu,saqar qasar china da kaloli masu kyan gaske. 08187255862.
A sannan akhnan din ta nade hannun rigarta,dankwalinta ya zame tana son koyon yadda ake kwaba wani abincin fulawa. Rumaisa tana ta dariya,saidai kuma tana mamakin yadda lokaci daya ta canza.
"Wallahi ni kam ba ruwana.....idan obbo yazo ya tarar kin manta dashi".
"She already did" Wannan muryar tasa me taushi da nauyi ta bayyana.
Cikin shakkarsa suka waiwayo,kowacce tana kallonsa tana qoqarin kama kanta,yayin dashi kuma dukka idanunsa suke kan akhnan.
Muryar ta isa ga kowanne sashe na jikinta,sanda ta waiwayo kuma mamaki ya cikata. Yana sanye da All black pyjama da suka fidda sirrin kyansa. Wato a yau ya amsa cikakken sunan d'an morsa safiyya,shi yasa kanshi tsaye yake takowa har kitchen dinta?. Ba kunya.......ba nauyi?.....ba iso?.
"Allah ya fara kishi.....bari na gudu" Rumaisa ta fada can qasa tana radawa akhnan,saita tsame hannunta daga kwabin,ta isa famfon sink kafin ya qaraso ta wanke hannayenta ta lalubi qofa.
"Tsayani mana yaa rumaisa" Anaani ta fada itama da wannam tsoron nasa da rashin son wargin da suka sanshi da shi tana bin bayan rumaisa din salin alin.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 130*
Wani irin emotion ne,dake fusgar zuciya da gangar jiki zuwa ga 'yar uwarta......zuwa ga d'aya b'arin nata.....zuwa ga abinda zuciyar da gangar jikin sukeso. Tana ta kwab'a fulawar.....taqi kuma juyowa gareshi,saidai dukkanin gangar jikinta... Dukkanin wani bugu na zuciyarta.... Duk wani sashe dake gangar jikinta jiran isowarsa yakeyi.
Shima kamar ita.... Idanunsa duka yana kanta,yana takawa da wani nannuyan yanayi na kewa,kamar ya shekara bai ganta ba. Saidai shi din yana qoqarin karantarta ne,tun daga tsaiwarta,ya zubawa bayanta idanu sosai. Idonsa ya lumshe yana fidda wani siririn numfashi. Boubou ce a jikinta,gashin nan nata me tsaho da santsi yasauka har kusa da mazaunanta,mazaunan da duk da cewa cikin sakakkiyar sutura suke......amma hakan bai hana bayyanarsu da bayyanar shape dinsu ba da tudunsu. Ya hadiye yawu a hankali yana jin wani irin mahaukacin kishinta. A tausashe ya isa bayanta yana karantar yadda ta qagu ya iso garetan,amma wannan izzar tata tana hanata nunawa. Baiga laifinta ba.....bazai kuma rabata da izzarta ba,don izzar na daya daga cikin abinda ya dauki hankalinsa da ita,yake kuma kan daukar hankalin nasa.(koda kun dade da miji.....ki zama me kamun kai da izza,bawai izza na girman kai wajen kyautata masa da biyayya ba.....aah....izza na kamun kai da nutsuwa,ba baragada......ki zauna kin b'andashe cinya da jiki,waike an zama d'aya,kai a wargatse ba kintsi,da wata bulalliyar rigarki wai ta zaman gida ce,tafi dadin sawa bata da nauyi. Ki zauna da daurin qirji koda datti wai ai wanka zaki shiga yanxu. Kai a tsaitsaye sai kice wai kitso kiketaso kije kin kasa.......please ki zama me aji,harshi kansa mijin yasan ke me aji ce,bawai yammatansu na waje ne kadai zasu zama hakan ba. Sometimes ma fa daidai da kiranki idan yayi kina iya ja masa aji,phone call,kina gani kidan basar ko sai ta kusa tsinkewa da sauransu,normally maza irin wannan attitude din yana jan hankalinsu sosai. Ba always available ba. Ya fita kullum kina hanyar kiransa,baisan ya kiraki ba. Wataran ki kama kanki,ki barshi ya kiraki da kansa mana,ire iren wadannan suna da alfanu sosai,amma hakan kada ya hanaki yi masa biyayya kyautata masa da faranta masa.......amma ki koyi jan class koda time to time ne).
Cikin faffadan qirjinsa ya adanata yana mannewa da bayanta,ya sanya hannuwansa yana lanqwaso hannuwanta sake cikin flour din ba tare daya damu zata bata masa jiki ba,ya aza kansa saman kafadarta yana sauke mata wani irin numfashi me nauyi.
"Haisammm manaaa" Ta fada a shagwabe tana qoqarin zame hannunta don kada ta b'atashi. Sai ya sake mata hannun,amma kuma ya musu kyakkyawan masauki saman qirjinta yana musu kyakkyawan riqon daya sanya jikinta duka ya hau rawa.
"I’m jealous of anyone who makes you forget I exist.” ya fada da wani yanayi cikin muryarsa yana lumshe idonsa,har yanzu kansa yana kafadarta.
"Come" Ya fada da wani irin energy yana sakinta,sannna yasa dukka hannuwansa biyu ya juyo da kafadunta tana facing nasa,sai kuma ya sake boyeta cikin jikinsa yana mata kyakkyawar runguma.
"Mmnnn"
"Mnnn" Yake fada yana sansansa kowanne lungu da saqo na jikinta dake bada wani kalar qamshi na daban. Wuyanta.....tsakanin dukiyar fulaninta.....cikin gashinta.......qasan hannunta......har fuskarta. Dariya.....itace ta qwace mata,dariyar da bata shiryawa ba. Don tana tsaye ne a tsorace,tana tsoron kada wani wanda zasuji kunyarsa ya shigo ya samesu a haka,amma shikam ta lura very comfortable yake abinsa.
"Fuskata ma qamshin take?" Ta tambayeshi tana ware ido sanda ya hade fuskokin nasu guri guda.
"Ko ina my wife.....ko ina da ina.....ba qamshi kawai ba....wani sulbi jikinki yakeyi.....kaman nanay ta canza miki soap ko?" Ya fada da muryar rada yana manne hancinsa saman nata. Kai ta daga a hankali. Yana noticing nata sosai,ko yaya wani abu ya sauya tattare da ita. Yana noticing cikin qauna da kulawa.
"Wanne ne?,ya sunansa?" Ya fada yana cusa kansa cikin wuyanta yana sake jin laushi da dumin fatar gurin,gami da sassanyan qamshin da take fiddawa na cakudaddu kuma hadaddun turarukan shuwa incense and more(+234 704 229 3387) Wadanda zuwa yanzu suka fara guda jikinta sosai,kabbasarta kuma suka mannewa duk kayan da zata d'aga(iya wuya kina mace?,karki rabu da kabbasa)🫶🏽.
"Sabulun......Mg's special soap (0806 2991549)......complete package ne na gyaran jiki......morsa safiyya tasa aka kawomin daga nigeria" Ta bashi details din muryarta a rarrabe saboda yadda dumin numfashinsa yake saukar mata da kasala.
"A sake kawowa......dukka packages din.....fatarki......ta sake santsi......don Allah......" Ya kasa qarasa fada,sai wani wawan riqo daya mata yana matseta da kyau cikin jikinsa.
"Haisammmm"
"Say it again.......giiftii" Ya fada sunan yana ratsa kwanyarshi. Da gaske yake.....bayaso ta sauya masa suna......da gaske yake mata da yace sunan na masa tasiri. Idan ta kirashi da sunan,sai yaji kaman duk duniya ba wada ya kaishi sa'ar suna.
"Please mana" Ta fada tana qoqarin tureshi a jikinta.
"Kowa fa zai iya shigowa" Ta fada tana ture kanshi da gaske. Baya kadan yaja......ya kuma daga fuskarsa daga saman qirjinta daya cusa kai yana duban tsakiyar qwayar idanunta.
Kallo daya tak ta masa ta kasa ci gaba. Ta janye idanunta da sauri gabanta yana faduwa. Wani irin kallo daya aje mata....wani irin sauyawa da kalar idanunsa sukayi ya sakata taji kaman zata birkice.
"Don't do it again" Ya fada da muryar gargad'i
"Haka kawai suka riqemin mata.....right?.... Nisa'ukum harsul lakum fa'atu harsakum anna shi'itum.... Matanku gonankinku ne......saina kasa zuwa ma gonata?. At any time?......idan sun gani.....next time su dinga turamin ke da wuri" Ya fada yana sake jawota cikin jikinsa da wani irin zafin nama.
Sau biyu tana jin motsi ana kuma fita.....ta riga ta saddaqar akwai wadanda suka shigo.....kuma suka gansu a haka,dole ta saddaqar ta kuma sake masa jikinta kawai.
Sai da yayi mai isarsa.......sai daya rage zafi sosai.....har tana jin yadda yake sauke numfashi a wahalce sannan yaja da baya. Kitchen cabinet din kawai ya dafe da hannuwansa yana sauke wahalallen numfashi,idanunsa akanta sanda take sulalewa zuwa saman kujerun island din kitchen din,saboda yadda taji qafafunta ba zasu iya daukarta ba.
Ya jima a haka kafin ya isa gaban freezer,ya bude ya ciro ruwan gora me sanyi,fari qal dashi har yana zufa ya balle!murfin ya kafa kai yana kwankwada.
Sai daya shanyeshi tas ya cilla roban cikin dustbin yana aje idanunsa a kanta. Abinda bata taba gani ba.....shan ruwan sanyi a tattare dashi. Ya zuba mata idanu a inda take cure tana qoqarin daidaita numfashinta.
"Come" Ya sake fada da laushi sosai a muryarsa yana miqa mata hannuwansa. Da wani irin kasala da kunya take takowa gabansa,ya zuba mata dukkanin idanunsa yana kallon salon tafiyar me burgewa. Irin tafiyar da a gurinta kadai yake ganinta.....irin tafiyar da tasha banban da tarin mata. Izza.....da qasaita da wani irin yauqi a tattare da ita,da wani yanayi me jan hankali d'a namiji.
Jikinsa ya sake riqeta da kyau,saidai a yanzun yabar qaramar tazara tsakaninsu,yadda zaifi jin dadin kallon cute face dinta.
"Karki sake yin nisa dani please.....bazan iya jurewa irin wadannan dogayen awannin ba tare da ke ba". Idanunta ta lumshe,kalamansa suna sake dilmiyar da ita sosai.
" Haisammm" Ta kirashi kaman yadda tasan yana so.
"Awanni kadan ne fa" Ta fada softly tana duban cikin qwayar idanunsa. Sai daya rusunar da idanunsa sosai a kanta sannan ya amsa mata.
"To you....awanni kadanne" Ya fada yana matsa hannunta cikin taushi.
"Amma ni.....daidai suke da wasu darare da yininka masu tsahon gaske" Murmushi me taushi daya sanya dukkan kyawunta fitowa ta saki.
"You're dramatic malam"
"No.....I'm attached to you" Ta sauke idanunta cikin kunya. Sai ya daga habarta gently. Ya tilasta mata kallonsa.
“Look at me.” ya fada da taushi. Ta dago idanunta gare shi. Zuciyarta ta sake bugawa saboda yadda yake kallonta da narkakkun idanun nan nasa masu nauyin gaske kamar wanda ya shekara yana nemanta ba tare daya ganta ba. Ya motsa labbansa.....wadannan kyawawan labban nasa masu taushin da bata iya mancewa da presence dinsu akan nata labban.
“When you laugh somewhere else…”
“…I want to hear it.”
“When you smile…”
“…I want it facing me.”
“And when you disappear for hours.....”
“…the palace stops feeling right.” kasa magana akhnan tayi har na wasu sakanni. Gaskiyar dukka kalamansa take gani a cikin idanunsa. Hannunta ta dauka ta dora tafin hannun nata a saman qirjinsa.
“You really missed me that much?” ta furta da muryar rada,kamar bataso kowa yaji kalaman bakinta saishi.
Qasaitaccen murmushin nan nasa na gefan baki ya saki a hankali.
“I always miss you more than I should.” Kitchen d'in ya yi shiru,sai numfashinsu kawai. Sai ya jawota gently zuwa jikinsa. Ya rungumeta tightly.
“Promise me something.” ya fada yana tura yatsunsa cikin gashinta daya tsone masa idanu me santsi sosai.
“What?” akhnan ta tambaya. Sai ya rufe idanunsa na sakanni kafin ya budesu.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 131*
“Ko duniya ta cika dake da mutane da farin ciki…”
“…ki dinga dawowa gareni.”
“Always.” ya qarasa fada yana lowering voice nashi sosai. Hawaye masu sanyi suka taru a idanunta. Yadda yake mata magana sake dulmiyata yakeyin cikin matsananciyar qaunar da bata da suna. Yana kuma sake karya mata duk wani qarfi da ta mallaka a z uciyarta da gangar jikinta. Sai ta gyada kai a hankali.
“I’ll always come back to you.” ta sake fada da wannan muryar me sanyi da rashin hayaniya.
Goshinta ya sumbata da wani irin taushi. Wani irin relief ya sauka a idanunsa.
“Good.”
“Because I don’t think my heart knows how to survive your absence anymore.” cusa kanta tayi a qirjinsa,ya riqeta yana murmushi wani boyayyen murmushi,sannan ya soma takawa da ita ta qofar baya suna ficewa.
★Jet dinsu ya bar sararin Agadez ne cikin dare.
Kasan hamadar na nisa a qarqashinsu.......yayin da city lights ke raguwa a hankali.
A cikin private cabin din,komai na sauke da luxury mai nutsuwa,wanda suke qarawa akhnan jin wata sabuwar rayuwa tattare da haisam din.
Duk sanda ta daga idanunta mutum biyu take gani. Wannan malamin da duniya ta sanshi a malami.....malami kawai makarancin alqur'ani masanin litattatafai......amma kuma a yanzu haka a gabanta......wata fuska tasa da mutane da yawa basu sani ba.....boyayyen billionaire..... Mamallakin madafun iko da kadarori. Baya ga turare.....da boyayyen harkar gold dinsa da ba kowa yasan da ita ba,sai mutane masu tarin muhimmanci cikin rayuwarsa kamar ita.
Wasu irin warm gold lights......soft leather seats da qamshin oud mai laushi ke tashi,wani yanayi sak irin na mutanen da suka saba da rayuwar kudi da iko.
Batasan me yasa bata gajiya da kallonsa ba.. ..d'an gayu ne gasken gaske,ita kanta ta shaida hakan. Har wani lokaci tana ganin kar yazo ya wucema gayunta,wani lokaci tana canza shiga ko kaya saboda ya dace da nasa class da gayun.
Ta dauke idanunta a kansa, har yanzu jikinta na jin gajiyar duk abubuwan da suka faru a Agadez. Amma duk da haka,zuciyarta tana samun wani irin peace saboda mutumin dake gabanta.
Yana zaune opposite d'inta. Laptop dinsa a bud'e. Yana amsa Messages da email dake da yawa kan wayarsa,wadanda bai samu daman dubasu ba. Wani lokaci kuma idanunsa suna kan laptop din nasa yana amsan business updates.
Har a sararin samaniya rayuwarsa ci gaba take da tafiya.
Amma duk da hakan......duk da wannan busy din na rayuwarsa duk bayan few minutes sai idanunsa sun dawo kanta. Always checking. Always aware of her.
Wani murmushi ya qwace ma akhnan a hankali,data tuna yadda ya satota shigen abinda ya faru a wancan tafiyar tasu.
“Ka ma manta ka yi wa Nanay sallama?.” ta fada da tsokana cikin muryarta tana son ganin reaction dinsa. Sai ya d'aga idanunsa daga screen d'in. Wani murmushi daya tsaya iya labbansa ya bayyana yana dubanta da narkakkun idanunsa.
“I was in a hurry.” ya furta da nutsuwar nan tasa,muryarsa da wani irin laushi. Idanunta tayi rolling,wadannan blue eyes din da fitilar gurin ta qara musu wani irin kyau.
“Hurry for what?” Sai ya rufe laptop din da wani irin slow,ya zuba mata ido da wani irin zurfaffan kallo.
“To take you away from everyone.” Zuciyarta ta yi wani irin bugawa da wani irin laushi,ta sauke idanunta a nutse tana sakin murmushi.
Ya ilaheee.....bazai dai qyaleta ba,duk da yadda ta zurma da yawa saiya sanya qilan zuciyarta bugawa saboda kalamansa da soyayyarshi.
Ya miqa mata hannu. Ta sa nata cikin nasa. Kamar abinda yake jira kenan Immediately jawota zuwa seat din kusa dashi.
“You’ve shared yourself with too many people these past days.” ya fadi da muryar rada kaman yadda ya saba mata magana yanzun.