L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 75
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 75: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 75. Da motar ta shiga cikin doguwar hanyar hamadar garin…
3,366 words
Da motar ta shiga cikin doguwar hanyar hamadar garin utah....sai khnan ta fara jin wani irin shiru da bata taba ji ba.Ba hayaniyar gari. Ba mutane. Sai duwatsu masu girma da hasken faduwar rana da yake lullube komai da gold color.
Mamakinta ya gaza boyuwa sanda ta fara hango wata ginanniyar duniya a gabansu. Cikin sahara?....cikin duwatsu?.
Sai a hankali AMANGIRI RESORT ya fara bayyana daga cikin duwatsun hamadar…
Akhnan batasan sanda ta mike ta zauna sosai ba akan seat dinta.
“…Subhanallah.” Bata ma san lokacin da kalmar ta fita daga bakinta ba.
Wajen bai yi kama da hotel ba. Ya yi kama da wani boyayyiyar masarauta ce da aka sassaka daga cikin duwatsun hamada.
Concrete mai launin ruwan kasa. Glass walls masu nuna desert view,water reflections,fire pits,minimalist luxury mai tsada sosai.
Komai a wajen idan ka kalla kasan ba qaramin guri bane....ba kuma gama garin guri bane da kowa da kowa ke iya zuwa ba.
Haisam yana kallonta fiye da wajen,yana monitoring na reaction dinta sosai. Burinsa gurin ya burgeta kaman yadda yake burge kowa,burinsa gurin yayi mata,duk kuwa da cewa ya riga yaga alamun hakan a fuskarta.
Akhnan ta fito daga motar a hankali tana kallon wajen kamar mafarki.....kamar almara,komai a wajen tana dubansa daya bayan daya. Bata taba ganin guri irin wannan ba. An qirqiri komai cikin duwatsu da sahara?. Wanne irin guri ne wannan?.
“Haisam…”
“Hmm?”
“Mutane suna rayuwa a nan gaske?” Ya dan sunkuyar da kansa kusa da kunnenta.
“Only a few can afford to.” ta yarda da maganansa dari bisa dari sanda suke shiga ciki,staff dinsu suna nan nan dasu cikin kulawa. Tsarinsu da yadda suke tafiyar da baqi kawai ya isa ya gaya maka lallai sun saba karbar manyan baqi,kuma manyan mutane a kowanne sashe na duniya.
Ta tsaya cak tana kallon suit dinsu bayan an shigar musu da luggage dinsu,an kuma samar da sauran duka abinda haisam yace a kawo din,banda coffee da sukace yanzu zasu kawo,oromian coffee dinnan nasa.
Duka suite din kamar private palace ne,kaman kowanne guri da zaiyi masauki a duniya.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
floor to ceiling glass walls,private heated pool,outdoor fire lounge,desert-view,bathtub,giant king bed mai white linen,soft hidden lights,private spa section,dressing room da ya fi wasu apartments girma,duk sai daya ja hannunta a hankali da wani irin kulawa don ya tabbatar komai yayi mata yadda takeso.
Amma abin da ya fi girgiza Akhnan…...shirun wajen. Kamar duniya ta tsaya musu cak,ba wanda kuma ya rage a cikin ta,daga ita saishi.
Ta juya a hankali tana kallon Haisam.
“Ka taba kawo wata mace nan?” ta masa tambayar tana jinjina yadda yasan kowanne guri daya dace da ma'aurata....ba'a iya qasarsa kawai ba....a qasashen duniya daban daban.
Idonsa ya tsaya a kanta na wasu seconds. Kishi.....ya fada qasan ransa,dariya yakeso yayi,amma yasan idan yayin zai jawa kansa jagwal,shi da yake buqatar dare mafi tarihi a amangiri din.....ba iya wannan daren ba.....ya shirya musu yadda zasu lalace sosai shi da ita a gurin,sai kawai ya fuske
“No.”
“Da gaske?” ta sake tambaya. Ya lumshe idanunsa,sai a yanzu ya yarda da kalar rigimar mata.
“Ban kawo kowa cikin duniyata haka ba.” ya fada yana cire agogonsa yana ajiye wa a hankali.
Idanunta ta zuba masa tana jin tarin qaunarsa a ranta. Royal billionaire aura dinsa ya kara fitowa,calm,untouchable,dangerously composed.
Ya taka zuwa glass wall din yana kallon desert sunset,yana sake girmama iko da buwayar ubangiji,yadda launin sama ke sauyawa a duka lokaci irin wannan.
Sai ya juyo gare ta.
“But you…”Ya tsaya kadan.
“You belong here.” idanunta ta lumshe a hankali,tana jin yadda yake sake shigar da ita wata sabuwar duniyar da batasan da ita ba,wani sabon lainin soyayyarsa dake taso mata kaman zai hallakata.
"Ko a map.....babu gurin nan.....ko map ya kasa tattara gurin nan a cikinsa......haka nakeso na mallaki nutsuwarki.....zuciyarki da dukka lokacinki a wannan sabuwar duniyar" Ya furta da sautinsa me zurfi....wannan husky voice din da idan yana mata magana takeji kamar ya tabbata yana hira da ita har abada.
Knocking din da akayi ya katse musu komai,wannan shurun....da kallon da yakewa cute face dinta yana jin duniyarsa duka ta tattaru a wajen.
Ta bude idanunta tana sake saukewa a kansa sanda yake dawowa ciki,hannunsa dauke da tray me azabar kyau,wani irin Royal tray da aka shirya asalin oromian coffee dinsa da baya rabo dashi a ko ina.
"Kai" Ta fada da sauri tana dora hannunta saman hancinta sansa tururin coffee din ya isketa har inda take sanda ya ajiye tray din ya soma zubawa don ya fara dumama cikinsa.
"What?" Ya dago kai yana tambayarta da lumsassun idanunsa.
"Wanne irin coffee ne wannan?"
"Me ya faru?" Ya tambayeta yana duban mug din daya cika da coffee din da tun kafin yakai gasha yawunsa ya fara tsinkewa saboda yadda ya dahu sosai.
Kanta ta girgiza tana kallon mug din da yake shirin kaiwa bakinsa.
"Wannan kamar ba coffee dinka bane" Kadan yayi sipping,sannna ya saukeshi idanunsa cikin nata.
"Shine.....ba abinda ya rabasu dana jimma" Taku biyu ta matsa baya tana yamutse fuskarta.
"Dadi kakeji?....dadi yake maka?" Yadan tsaya da mamakin ganin kamar hankalinta yadan tashi,sai kuma ya dage mata girarsa duka biyun alamun yes. Kai ta girgiza ta juya,ganin tana neman hanyar fita ya kirata a tausashe.
"Hey.....giiftii" Ta waiwayo a hankali tana jin iskar dakin kamar ya sauya mata. Da girarsa da idanunsa ya tambayeta,saita tura baki gaba.
"Ni tunda ka shigo dashi naji iskar dakin ta canza". Idanunsa ya zaro waje,yana mamaki don shikam baiji komai ba. Yayi shuru irin na wanda ke nazari.
"Okay" Kawai yace da ita,sai ya fara tattare tray din kawai,ya dauka yana zuwa ya wuceta a tausashe yana fadin.
"Stay in your room,coffee ne yazo ya sameki,shine zai fita ya baki guri" Ya fadi da kulawa sosai cikin muryarsa.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 136* ___________________________ *_Amintaccen gurin siyayya_*
*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*
*_BONONZA DA PROMO akai akai_*
*dukka sai a HUGUMA CLOSET*
*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*
*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*
*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*
*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________
Idanunta ta lumshe duka sanda ya kammala fita daga dakin da coffee din.
"What a simple man" Ta fada a hankali muryarta qasan maqoshinta. Batasan me yasa yake da sauqin kai har haka ba,da fari idan ka kalleshi.....zaka dauka zaiyi taurin kai.....zaiyi wuyar sha'ani.....kuma bazaiyi dadin mu'amala ba. Amma kuma sai ka mu'amalanceshi......sai kasha tarin mamaki.
Mu'amalarsa da ita ya sanyata ta sake komawa bitar tarihin ma'aiki da mu'amalarsa da iyalansa,sai a nan ta fahimci tsantsar aiki da ilimi ne yake aikinshi a gurin.
Komai yana qoqari wajen ganin ya kwantanta yadda annabi ya koyar. Taushinsa.....rahamarsa da tausayawa iyali. Yadda yakan tsokani matansa a gurare......tayasu hidima dama yi musu hidimar gaba daya. Sai taji yana sake burgeta,sai taji yana sake shiga ranta,sai taji a duniya tafi kowacce diya mace dacewa da abokin rayuwa na gari.
Taji wani tausayinsa kadan ya taba zuciyar ta,sarki ne shi a gaban duniya......wani abun girmamawa da cika umarninsa.....amma a gida.....a gabanta,yana maida kansa kamar bawa saboda taji dadi.
Ta taka zuwa babban glass door din dake corner din dakin tana tsayawa. Batasan me yahau kanta ba,amma dai ita taji qamshin coffee din ya mata strong da yawa.
Ta sauke idanunta zuwa ga hasken waje dake shigowa,wanda ke nuna yadda rana ke bankwana da duniya. Gurin ya mata ya mata ya mata,har batasan yadda zata misalta ba. Yasan ko ina.....ko ina me kyau.....kowanne guri da zai bawa mace mamaki ya tsaya a zuciyarta. Ta dora hannunta saman glass din tana sakin murmushi tana kallon Huge glass walls. Soft lights. Warm neutral colors masu daukan hankali dake gurin. Ta tuna sanda suke shigowa private villa din nasu. A cikin duwatsu take,a cikin duwatsu aka ginata.
A nutse ya tura qofar dakin yana shigowa bayan ya kammala shanye coffee dinsa. Yayi tsaye daga bakin qofar yana qare mata kallo. Duk sanda zai kalleta.....wata tauraruwa yake gani,ba khadeeja ba.....ba akhnan ba....ba biftu ba.....ba giiftii dinsa ba.
Ya sauke hannuwansa yana takowa cike da nutsuwa. Batasan ya shigo ba,sai duminsa taji a bayanta,ya jawota yana rungumeta ta baya,ya dora habarsa akan kafadarta yana tayata kallon villas din dake gine cikin duwatsun amangiri din ta glass din.
"This place doesn’t look real…” ta furta a hankali kamar me rada. Sauke idanunsa yayi yana kallon yatsunta daya shimfidesu cikin tafin hannunsa. Ba gurin ke masa kyau ba. Itace take masa,ita take haska gurin cikin idanunsa. Baya mantawa,zuwansu na qarshe da 'yan shidansa.......baiji wannan nishadin ba....baiji burgewar gurin a idanunsa kamar yanzu ba.
"It's....."
"......But you look better.” ya fada yana sumbatar dogon wuyanta da wani irin laushi. Tsigar jikinta taji ta zuba,tadan motsa kadan tana murmushin kunya
"You flirt too much these days.” sai ya manneta a jikinsa da kyau kamar zai narke a jikin nata su zama abu guda.
"I’m making up for lost time......ke dince....." Sai ya kasa qarasawa,idanunsa suna lumshewa gami da bude kansu. Yana tuna darare masu yawa data dinga fiddashi daga saitinsa.
".....bansan me zance ba" Ya fada jikinsa na wani irin laushi. Ya karantar da ita karatuttuka masu nauyi a madeena,ta kuma dauka da kyau. Yadda take sarrafashi abun yana kwance masa kai,har sama da yadda ya dauka zata iya..... Harda sabbin darasissikan da bashi ya bata ba. Ta bude hannunta da kyau,ta karbeshi da kalan rayuwar da yakeso,ta sakar masa ragamar kanta da kanta,tana kuma tayashi sarrafa komai yadda zai qayatar dashi.
Da yace mata baya buqatar komai daga gurinta sai SOYAYYA QAUNA KULAWA DA LOKACINTA. Ta dauki dukkan wannan abun daya fada da muhimmanci. Yace mata bayason ra wahalar da kanta gurin neman hanyar da zata mallakeshi......saboda a mallakensa yake indai a kanta ne. Ya gama mallakuwa already,tun ranar farko daya aza idanunsa a kanta. Tayi dariya ranan sosai.
"Amma.....fada mukeyi fa haisamm......bakaso mu hadu ko a hanya.....baka kallona.....ka dauka banyi noticing bane?" Ya lumshe idanunsa kana ya budesu yana murmushi.
"Na sani.....bazan kuma manta ba......ina kishin mazan daketa zuwa ganinki da sunan aure ne........ina tsoron mu dinga haduwa kina kallon cikin idanuna,saboda banaso ki gane komai a lokacin. Ina tsoron naci gaba da ji da ganin mazan dake zuwa gurinki,kada naje nayi loosing control dina saboda kishi......" Sai ya dakata.
".....akhnan" Ya kirata da yanayin daya tilasta mata maida hankali kansa.
".....ina da kishi......ina tsananin kishinki akhnan......billahi zan iya rasa raina a kan kishinki....." Sai ya tsaya yana maida numfashi,kamar wani abu me nauyi ya taba ransa.
"Zan iya yarda nayi sharing ko na rasa komai nawa......amma bazan iya daukan hakan a kanki ba"
"Taka ce ni......takace ni har abada......" Ta fada tana shigewa qirjinsa.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Daga ranar da na fahimci kaine kayimin ALFARMA.....ba nice na maka ba....daga ranan na yarda kaine kalan mijin da zan rayu dashi har abada". Ya riqeta sosai a lokacin yana sakin murmushi. Ya tuna....,ta riqe kalmanne sanda morsa safiyya ke warware mata sauran abinda bata sani ba game da aurensu.
"Har abada ke mai ALFARMA ce.....kuma har abada ke kikamin ALFARMA bani na miki ba" Ta motsa labbanta zatayi magana,ya dora yatsansa akan lips dinta yana kashe maganan.
A yanzu da suke tsaye gaban glass din,sai ya saka hannu ya juyo da ita. Kallon kallo suka yiwa junansu,ya motsa lips dinsa a nutse.
"Do you know how many nights I imagined this?”
" No chaos "
"No danger"
"Just having you somewhere peaceful.” kasa magana tayi,sai hawaye da taji sun cika mata idanu. Wacce irin qauna yake mata haka?.
Kanta kawai ta dora saman qirjinsa tana sauke numfashi
" We survived a lot" Sai ya rungumeta cikin jikinsa tightly kamar har yanzu yana tsoron rasata.
"Yes"
"But I’d survive it all again if it leads me here with you.” yadan sassauta riqon da yayi mata ya bata lite kiss a goshinta.
Sakin daya mata sai taji kaman an saki wani abu daga jikinta ta rage nauyi. Tadan tafi baya kadan tayi tangadi. Ya riqeta da sauri yana duban idanunta.
"you okay?" Ya tambaya yana duban ta. Bata sani ba.....itama batasan me yasa taji wannan dan qaramin dizziness din ba. Batason yadda qaramin abu a kanta yake sanyashi damuwa haka,ko yaushe dan adam kan iya jin canji a jikinsa,bai kamata nata ya dameshi ba. Ta tsaya sosai akan qafafunta tana son nuna masa normal takeji.
"I'm fine"
"Akhnan" Ya kira sunanta har yanzu yana riqe da hannunta cikin nasa. Muryarsa low ce,calm,amma akwai warning a ciki,irin muryar mutumin da baya son a boye masa abu. Tadan kauda kanta tana jin damuwarta tana damunsa da yawa.
"May be I'm just tired" Ta amsa masa.
Idonsa ya tsaya a kanta na wasu seconds kafin ya kama tsintsiyar hannunta zuwa bakin gadon ya zaunar da ita.
"Okay......ya kamata ki wanka ko qarfin jikinki zai dawo.....right?" Kai ta gyada a hankali,ya sake mata murmushi,ya juya yana takawa zuwa bathroom wanda tasan ruwan wanka zai hada mata.
Kaman ko yaushe tare sukayi wankan,ya kuma tayata ta shirya. Bai fasa tayata ba har yanzu,duk da ta iya yanzu abubuwa da yawa da bata iya yiwa kanta a baya. Yace yanzun shine amininta.....shine abu mafi kusanci da ita. No more BB's dinta. Birra barratu bara'atu bushira.
Sallan magariba sukayi,sannan suka wuce private dining dinsu da suke da option biyu. Daya a cikin suite din nasu,dayan kuma a waje,inda zai basu daman ganin desert din sosai da duwatsun dake gurin. A waje ya zabi suyi dinner din,gurin ya mata wani irin kyau,haske tako ina me daukan hankali,wata irin nutsuwa da zaka dauka daga kai sai wanda kukaje gurin kuke rayuwa,sai kuma masu muku hidiman da komai idan suka kawo suka tafi shikenan.
Iskar da yanayin gurin suna mata dadi sosai. Yadda ta sake ma kawai ya gaya mata gurin na musamman ne. Ya barta ta saka kayan da takeso,very lite. Hakanan da kansa yace mata tabar gashinta haka,basai ya saka komai ba banda 'yar siririyar bandana. Ya matsa kusa da ita yana shaqar qamshin hair mist din muryarsa tana rarrabewa da yanayin da ita kadai ke fahimtar meke faruwa dashi.
"Inaso na kalli gashinki.....iska tana kadashi....from left to right" Murmushi ya qwace mata. Wato kowanne namiji da irinsa.....kuma kowa da abinda yake burgeshi daban,abinda nanay ta gaya mata kenan rannan. Ba uwa kadai bace.....ba uwar miji kawai bace.....aah. Ita din malamarta ce.....ta zamantakewa da rayuwa gaba daya. Idan suka fara waya saidai haisam ya koma gefe,har yanzu kuma ya kasa gane dame dame ake fada akan doguwar wayar da akeyi tsakanin nanay da akhnan. Wani lokaci dariya yake bata bayan sun gama wayar,saboda sai yayi wani shuru kamar maraya yana narke mata ido.
Akwai randa ya gaji da jira,ya rasa yadda zai calling attention akhnan towards him. Yana da wani irin kishi na gaske a kanta. Da gaske bayason ta raba lokacin ta da kowa saishi. Sai ya saki siririyar qara wai coffee ya zube masa a qafa. Da kanta nanay tace subhanallah cikin rudewa tace.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 137* ___________________________ *_Amintaccen gurin siyayya_*
*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*
*_BONONZA DA PROMO akai akai_*
*dukka sai a HUGUMA CLOSET*
*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*
*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*
*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*
*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX __________________________
"Jeki duba shi.....Allah yasa ba serious bane" Ita tasan ba wani coffee,kawai sharrinsa ne. Mutumin da ruwan da yake wanka dashi har tururi yake?,sannan idan ya tashi shan coffee din har mamakin yadda bayajin zafinsa take..
Tayi hasashenta daidai kuwa,don tana zuwa ya cafketa ya matseta a jikinsa.
"Haka kawai.....saiki dinga raba min lokutana" Bai ma bata daman fadin komai ba ya shiga yin abinda yafi ganewa,a nan yabar coffee din nasa ya huce ya gantale,qarshe sai masu shara da gyara musu gurinne suka zubda shi.
Kwata kwata saita rasa d'an d'ano a bakinta. Yayi juyin duniya taci wani abun amma duk abinda ta saka a bakinta a gurin sau daya biyu sai taji bai mata ba.
Ya dakata da cin nasa abincin,ya kafeta da idanun nan nasa.
Ya dafa bayan hannunta da yatsunsa,duminsu ya ratsata.
“You barely ate.”
“Bana jin yunwa ne.”ta amsa masa.
“Coffee upset your stomach.” Ba tambaya yayi ba,observation ne a muryarsa.
Ta yi shiru,don bata da tabbacin amsar da zata bashi. Kusan kwana biyu saura su baro madeena taji komai baya burgeta.
"Is okay" Ya fada yana ciro wayarsa. Kira yayi cikin harshen turanci na sakanni,sannan ya katse,sai taga yana rubutu. Batasan dame dame ya rubuta ba,taga dai ya aika ya sake ajiye wayar a gefansa,yaci gaba da cin abincin saidai still idanunsa suna kanta yana observing nata.
Saqo ya shigo,ya dauki wayar ya duba,sai ya miqe a nutse yana ajiyeta,ya taka yana fita a gurin. Ta bishi da kallo,yau tana sake tantance tsahonsa. Giant ne sosai ta yadda duka duka kanta yake tsayawa cikin qirjinsa,yayi wani kyau abinsa yau cikin wata tshirt da wandon da iyakarsa qasan qaurinsa.
Daga nesa ta hangoshi dauke da babban tray niqi niqi.
Bata taba daina mamaki idan ta ganshi yana hidima da ita. Ya qaraso gabanta ya ajiye tray din,sannan a nutse ya fara bude komai da yake ciki.
Bayan ya kammala budewar sai yaja ya tsaya yana dubanta. Itama duka abincin take bi da kallo. Ya kusa kala goma,na qasa daban daban.
"Ki duba wanda zaki iya ci na zuba miki.....idan duka basuyi ba sai a sake zabo wasu guda goman your royal highness" Ya fada yana dora tafin hannunsa a qirjinsa gami da rusuna mata kaman yana gaban boss dinsa.
Dariya ya bata sosai,ta aza hannunta abaki tana rufe dariyarta. Daya bayan daya ta soma gwadawa,saidai duk cikin goman abu daya ne ya mata. Iya hakanma ya masa dadi,ya tsareta har sai da taci,saidai tana kammalawa wata irin kasala ta rufeta,dole suka koma daki,ya tayata tayi shirin bacci.
Tana shiryawar yana mata fadanci. Ta gane sarai me yake nufi,can qasan ranta take masa dariya,baisan itama a cikin yanayin take ba. Kwana biyun nan har tsoron kanta takeyi. Kada fa ya zamana ya horata sama da yadda zai iya riqeta?. Sai take ganin kamar ma taso ta fishi zaqewa da kwadayin harkar,amma ko daya ba zata bari ya gane hakan ba,wannan dalilin ya sanya koda ta gama shiryawa saita haye gadon abinta tana basarwa.
Fita yayi,ba jimawa ya shigo hannunsa da mug. Black tea dinsa ne,bai nema coffee ba wannan karon don kada ya sake takura mata ko ya bata mode dinta.
Idanunsa a kanta,ya qaraso a hankali saman bedside drawer ya zauna. Ta daga kanta a hankali tana ruban kyakkyawar fuskarsa. Magana zatayi.....amma tururin black tea din ya bugeta,ya qarasa can cikin cikinta ya hatsinashi. Wani yunquri tayi kaman me shirin yin amai,abinda ya sakashi miqewa da hanzari,har cup din yana shirin subucewa daga hannunsa,ya samu ya ajiyeshi saman bedside din yana haurowa saman gadon da sauri yana tambayarta.