L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 76
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 76: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 76. "Are you okay?" Shuru tayi,dafe da mararta da taji ta…
3,375 words
"Are you okay?" Shuru tayi,dafe da mararta da taji ta karta saboda yunqurin aman da tayi,tana jin wani abu daya dunqule mata yana sauka a hankali.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Zama yayi sosai,ya jata jikinsa yana bata comfort yadda zataji dadin zaman sosai. Har ya lura tayi relax,sannan cikin nutsuwa ya tambayeta.
"Bakya jin dadi giiftii" Ya fada kai tsaye maganan nasa kaman tana bata tabbaci ne bawai tambaya bace. Bata musa ba,ta daga masa kai a hankali. Tsarin rayuwarsu da suka soma aza kansu akai shine. Ba boye boyen komai a tsakaninsu.
"Since when?" Ya sake tambaya. Ta kalleshi idanunta suna rusunawa.
"Ban san yaushe ba" Ta fada a narke. Shuru yayi yana ci gaba da kallonta,kamar yana qoqarin hada wani abu a kanta.
"We’ll see a doctor when we get back.” ya bata tabbaci yana gyara mata zama sosai a jikinsa,ransa yana masa ba dadi.
Ta yi kokarin murmushi kadan.
“Doctor? Haisam,it’s not that serious fa." Bai amsa nan take ba,sai ya zare hular kanshi da yakan saka duk sanda zaiyi sallah,fara qal da ita ya ajiye gefe,idanunsa har yanzu a kanta.
“You almost threw up because of coffee.....then black tea shima?"
“Ban yi amai ba.” ta fada a shagwabe,don ita zancan zuwa asibitine sam sam bataso. Don qilan azo kan lamari na allura babbar abokiyar adawar tata kenan.
“Almost.” ya fada sa accent dinnan nasa na yaren French dake narka mata zuciya. Ta ja blanket kadan tana kau da ido.
“Maybe saboda flight ne fa.”
“Maybe.” ya furta shima,saidai yadda ya fada din ya nuna bai yarda ba sam. Ya zameta a hankali yana sauka don qarasa shigo da abinda zasu buqata.
Shiru ya sake ratsa suite din. Sai qarar desert wind daga can wajen glass walls.
Akhnan ta lumshe ido na wasu seconds. Jikinta na jin wani irin nauyi da wani baqon yanayi. Sai ta ji gadon ya motsa. Ta sake bude ido,hisam ya zauna kusa da ita sosai,har tana jin dumin jikinsa.
“Come here.” ya fada yana wara mata hannuwansa gaba daya,da alama isowarta kawai yake buqata.
“Haisamm" Ta kira a shagwabe.
“Akhnan.” shima ya kirata da muryarsa low sosai. Ta matsa kusa da shi a hankali,zancan zuwa asibiti ne bataso,shi takeso ya janye.
Nan take ya janyota jikinsa a tausashe,hannunsa daya yana bayan kanta ya tallafeta sosai yana mata wani zuzzurfan kallo.
Cikin mintuna qalilan wanna feelings din me nauyi ya fara tasiri da zagayawa a gangar jikinsu. Suka fara mantar da junansu komai,sai wannan soyayyar....wannan qaunar... Sai muhammad da khadeeja din kawai.
Wani abu game da yadda yake handling dinta tonight ya bambanta da kowanne lokaci. Extra kulawa kamar tana da wani abu fragile da bai kamata ya karye ba a jikinta. Hakan sai yazo mata da wani sabon salo,wani sabon salo da ya sake tafiya da imaninta da tunaninta. Sai taji kaman ba haisam din ba....kamar an sake sauyashi gaba daya. Ya sake mamaye zuciyarta da tunaninta. Wani iri halitta ne da ba'a taba yin irinsa ba cikin rayuwarta,kullum cikin shayar da ita mamaki yake game da komai daya shafeta.
Bai barta ba,sai daya tabbatar shi da ita dukka sun kashe wutar data taso musu. Yanayin ya masa dadi matuqa da gaske,don ya fahimci kamar yanayinta ya sake canzawa gaba daya itama,kamar wata daban aka sauya masa. Ya samu kansa da zuba mata idanu bayan sun fito daga wanka,ya hanata saka komai sai towel din jikinta,yace a haka yakeso ya ganta.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 138* _________________________ https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0
*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*
*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*
*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*
*_Assalamu alaikum my loyal people_*
*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*
*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*
*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*
*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*
*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*
*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*
*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*
*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*
*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa ameen* ____________________________
Ta dago ido tana kallonsa.
“Why are you looking at me like that?” Ya dan shafa gefen kumatunta da thumb dinsa.
“I’m thinking.”
“Dangerous.”
A hankali wani siririn murmushi ya bayyana a gefen bakinsa.
“You’re funny when you’re sleepy.”
Ta so ta bashi amsa… amma sai ta tsaya saboda wani abu da ta sake ji can qasan mararta. Numfashinta ya canza kadan,idanunsa suka sauka kanta.
“What happened?” ya tambaya yana jawota cikin jikinsa.
“Nothing.”
“Akhnan.”
Ta dafe cikinta lightly ba tare da ta sani ba,sai ta gane abin da tayin ta soma motsa yatsunta.
A hankali idanunsa ya sauka kan hannunta. Daga hannun… zuwa fuskarta yabi da kallo.
“Haisam…” ta kirashi tana sauke hannun ganin wani zuzzurfan kallo da yake mata,bai amsa ba amma yaci gaba da kallonta,kamar akwai tunanin da ya fado masa
“When was your last period?” ya tambaya yana tsaida dubansa tsakanin idanuwanta.
Tambayar tasa ta sauka a tsakaninsu kamar wani abu mai nauyi.
Akhnan ta kafe shi da ido na wasu seconds bata iya magana ba.
“Haisam….."
“When?” ya sake tambaya yana jin kamar ya kurma ihun kabbara tun kafin yaji amsar da zata bashi. Muryarsa har yanzu calm ce. Amma akwai intensity a cikinta.
Ta kau da kai a hankali.
“I don’t remember exactly.” Ya cigaba da kallonta. Kamar ya riga ya fahimci cewa tana son ta tuna.....amma tana avoiding answer din.
Kasa nutsuwa tayi......a hankali ta mike daga jikinsa,bai hanata tashi ba,yana kallonta ta isa side table inda wayarta take.
Yatsunta suka bude calendar din cikin sauri kadan. Sai ta tsaya,numfashinta ya dauke na second guda.
Haisam bai motsa ba. Bai tambayeta me ta gani ba,yana kallon fuskarta kawai.
Ta sake duba dates din,gyara tsaiwarta ta sakeyi tana kallon calendar din wayarta kamar numbers din sun rikide mata.
Yatsunta suka tsaya kan screen din.
One month. Then another. Numfashinta ya dan canza.
A hankali ta sake dawowa tayi counting. Daga Madina......daga tafiyoyinsu......daga lokacin da rayuwarta ta cakuda data haisam,sai wani abu ya fado mata.
Tun bayan saninshi.....tun bayan daren farko da ya fara shiga rayuwarta gaba daya......ta daina ganin period dinta. Zata iya tunawa.......period dinta na qarshe ta yishi ne kafin ya cakuda rayuwarsa da tata. A ranar data gama......a ranar ta zama tashi.....a ranar ta amsa sunan mace cikakkiya.
Zuciyarta ta bugu da karfi,bata taba mayar da hankali sosai ba sai a yanxun daya tambayeta,saboda rayuwarta tun daga lokacin ta juye da tarin abubuwa.
tashin hankali......canjin rayuwa......tafiye tafiyensu da emotions. Yanayi na sabon aure. Haisam din kansa,komai yazo mata lokaci guda,har bata tsaya ta lura da kwanaki ba,sai yanzu.
Yanzun da yake tambayarta. Yanzun da jikinta yake acting strange.
Ta sake duba dates din......again.....again. Kamar zata samu wata answer dabam idan ta kara kallo.
Da kanta ta gaji,a hankali ta zauna gefen bed din.
“Haisam…” Muryarta ta canza. Shi kuma tun kafin ta karasa magana… ya fahimci akwai fargaba a tattare da ita.
Ya karaso gare ta a hankali
“What is it?” Ta dago idonta. A karo na farko akwai real panic a idanunta
“I… I don’t think I remember the last time."
Idonsa bai bar fuskarta ba.
“When exactly?” ta girgiza kai a hankali
“I don’t know.”Sai ta hadiye yawu,tana tsoro sosai.
“Everything became messy after you."Ta dafe kanta kadan.
“Na dauka saboda stress ne…travel… hormones…” ta fada muryarta na kara raguwa.
“But now I can’t even tell when it stopped.”
Wani irin shuru mai nauyi ya cika suite.
Haisam ya tsaya yana kallonta
“Look at me.” ya fada yanata qoqarin qunshe dariyar data kusa minti goma tanason murqusheshi. Ta dago ido kamar yadda ya buqata.
“Are you scared?” Tambayar tasa ta karya wani abu a kirjinta,saboda kafin wannan second din....bata ma fahimci tana tsoro ba.
“A little.” Idonsa ya rusuna kadan.
“For what?” ta hadiye wani abu. Tasan ana mutuwa....mutuwa akeyi sosai idan an samu ciki,tana iya tuna staffs dinta mata kusan uku da dukka suka mutu gurin haihuwa,bayan haka batasan komai game ea daukan ciki da haihuwa ba. Sai kunyar yadda zata kalli duniya da wannan abun dake turowa gaba. Duk wanda ya kalla kenan sai yasan me tayi ita da haisam?.
“…I don’t know.” kawai ta zabi ta amsa masa da hakan.
Shuru ya sake shiga tsakaninsu. Sai ya kai hannu ya cire wayar daga hannunta ya ajiye a hankali.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
“No more thinking tonight.”
“Haisam”
“If it’s nothing, we’ll know.”
“And if it’s not nothing?” A karon farko tun farkon daren… wani abu mai laushi sosai ya bayyana a kallonsa.
Sai ya matsa kusa da ita har tana jin saukar numfashinsa.
“Then,” ya fada cikin kasa-kasa da murya.
“I guess the desert just became our witness first.”
Cikin jikinsa ya sanyata,ya rufesu iya qugu,ya bude wannan glass din ta yadda zasu samu daman ganin desert din sosai dama taurarin dake lullube da sararin samaniya.
A nutse ya fara magana akan abubuwan dake gurin da Muryar nan tasa da tafiso.
Taurarin wajen......yadda hamada ke yin shiru da dare.......yadda yake son wajen saboda babu hayaniya.
Akhnan ta gane abin da yake yi,yana kokarin cireta daga wannan tsoron ne ba tare daya matsa mata ba,Just… quiet protection.
Taji wannan amincin har cikin zuciyarta,sai ta jingina da kafadarsa a hankali. Haisam ya sumbaci saman kanta a tausashe,Idonsa kuwa suna kallon desert darkness.
Wani farinciki yakeji a zuciyarsa. Haka kawai yakejin yaqinin cewa zai wahala idan qwallonsa bata shiga raga ba. Indai hakanne tabbas yana cikin mazaje dake da sa'a. Yanason 'ya'ya sosai....ba daya ko biyu ba,yara masu yawa,da khadeejansa kawai kuma yakeson ya tarasu.
Amma idan Akhnan tana bukatar lokaci kafin ta iya kallon gaskiyar.....zai jira har sai wannan lokacin yayi.
Tun daga ranar yake wani kaffa kaffa da ita,kaffa kaffan da batasan dalili ba. Ya qara ninka yawan kulawarsa a kanta,Komai bayaso tayi. Ko fita sukayi tattaki cikin saharar....tafiya kadan take gajiya,sai ya zamana yana lissafe da sanda take gajiya din. Da sunkai wannan gejin zai tsaya ta huta.
Abinda kawai ta yarda dashi bata da lafiya,normal rashin lafiya. Inda zaka tambayeta kawai zatace rashin kuzari ne yake damunta. Sannan kuma tana yawan gajiya,uwa uba yanzun ba Komai takeso ba.... Ta zama me zabe zaben abinci,da launikan qamshi daban daban. Amma wannan qamshin nasa.....har yanzu ba abinda ya girgizashi a zuciyarta.
Yaso ma suyi using the sam perfume,amma ta girgiza kai tana lumshe idanunta.
"A jikinka kadai nake buqatar jinsa......zanci gaba da jinsa a gurinka kai kadai" Ya saki lallausan murmushi yana yin qasa da idanunsa.
★★★Kwanakinsu a amangiri resort wasu irin kwanaki ne da bazasu taba gogewa daga memories dinta ba. Bata taba ganin guri me tarin nutsuwa a duniya irin gurin ba. Zaka rantse da Allah ku kadai kuke rayuwa,don duk kwanakinsu a gurin sau biyu kawai ta taba ganin wasu couples. Kowa rayuwarsa yakeyi cikin suit dinsa.
*MORNING POOL*
Waya dasu rumaisa ne ya kaita gurin a safiyar.....mutanen da kulli yaumin saisun kirata sun tambayeta yaushe zata dawo jimma,don already sun baro agadez. Agadez din data musu dadi kaman ba zasu koma gida ba,saidai kuma an qulla babbar alaqa tsakanin sarki ahmad da rumaisa. Don tana kyautata zaton abune da bazai dauki dogon lokaci bama. Hakanan Aanani,sun dinke da muhammad. Da farko dabara ya mata akan ta zama malamarsa,yana zuwa daukan karatu,sannu a hankali sai taga karatun da yake zuwa dauka nasa ya zarta nata,ashe zuwa karatun nasa akwai manufa.
Ba ya wannan abun ya tsaya ba......Aisa da shehnaz........duka rumaisa ta fara qyasa mata. Khadeem dama da tuni ya nuna ra'ayinsa akan aisa. An riga an gama magana. Hakanan shehnaz,wadda dama anata kai ruwa rana tsakanin mahaifansa. Mamarsa shehnaz takeso,babansa kuma ya zaba mata wata,daga qarshe sultane ya yanke ya haqura gaba daya kawai zaifi kwanciyar hankali. Ana yin hakan mutallab ya sako kai..... Ba sabo ko shaquwa tsakaninsu.......amma kunya da nauyin haisam ya sanya ta bashi dama. Sai a sannan ta gane ashe sakiyar da ba ruwa takeso ta yiwa kanta.
Sunata mata nuqu nuqu,ita kuma tace ba zatace komai ba sai sun fito sun gaya mata da kansu. Sannan zata wankesu tass ta rama tsiyar da suka mata,duk da tuni taji zancan har a bakin haisam. Kar tasan kar ne,sunsan halinta,saita rama duk wata tsiya da suka tabayi mata.
A nutse take takawa a gurin,desert sunlight na shiga glass walls da infinity privaate pool din villa din nasu dake gabanta suna haske mata idanu.
Koda ta gama wayan zama tayi a nan,a bakin ruwan tana shaqar daddadar iskar saharar dake tuna mata da agadez. Ta baro haisam a ciki yana amsa waya shima.
Ta danyi nisa kadan cikin tunanin rayuwa. A hankali taga inuwarsa tsaye a bayanta daga poolside.
Takowa yayi yana dawowa ta gefanta,inda zaifi ganinta sosai. Ya zube lumsassun idanunsa da kullum ta kallesu abu daya suke gaya mata.
"Ina buqatarki.....na har abada a cikin rayuwata" Yana sanye da baqin trouser da tshirt me laushi me gajeran hannu,itama baqa. Ta zauna masa sosai a jiki da wani kwantaccen kyau. Tunda sukazo gurin bashi da wata sutura sai irin wadannan kayan. Three quarter short ko long trouser da sauransu.
Kallonta yake tana sake kwanciya saman ransa. A kwaakin wani glowing take qara yi,abinda ke qarfafa zarginsa a kanta kenan. Duk da har yanzu taqi bada hankalinta da gangan bare ta fahimci abinda ke gabanta. Zai qyaleta,har sai sanda komai ya mata ba zata. Dariya me laushi takan qwace masa a duk sanda ya hango ranar.....ranar da zatayi realising tana dauke da baby. Yana iya nasa qoqarin gurin bata kulawa da kariyar daya dace ace ta samu.
“You keep staring.” ta fada tana tura baki gaba kadan.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 139* __________________________ *_Amintaccen gurin siyayya_*
*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*
*_BONONZA DA PROMO akai akai_*
*dukka sai a HUGUMA CLOSET*
*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*
*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*
*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*
*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX __________________________
“You keep giving me reasons to." Ya amsa mata calmly yana sunkuyowa kanta kadan.
Hannu ta saka a cikin ruwan wanda ta tsoma qafafunta a ciki,ta debo kadan a hannunta ta dan watsa masa.
Sai ya tsaya still,then slowly ya cire agogon hannunsa.
Akhnan ta zaro ido da sauri
“Haisamm" Da wannan muryatata da kullum zata kirashin kashe masa jiki takeyi.
Saidai it's too late daga sanda ta kirashin,don tuni ya shiga pool din straight toward her. Calm.....focused.....dangerously.....attractive
Ta soma ja da baya tana dariya da wannan sautin nata dake shagaltar dashi.
“No.....don’t start.” ta fada tana qoqarin zame qafafunta don ta samu ta gudu.
“You started it.” ya fada da low voice dinnan nashi me zurfi.
Ya samu nasarar kamo hannunta gently,ya kuma jawota cikin ruwan,sannan ya sake matso da ita cikin jikinsa. Close enough da zataji numfashinsa.
“You’re happy here.” ya fada yana kallon blue eyes dinta daya cika da tsoro,da digo digon ruwa daya barbazu saman fatarta me santsi da sheqi,wadda sabulun Mg's skin product ya sake karbarta sosai.(806 299 1549).
Ta kalleshi da wani zuzzurfan kallo sannan ta gyada kanta.
“I’m happy anywhere…”
“…you let me rest.”. Wani irin softness ya bayyana a idanunsa,sai ya dora goshinsa a nata.
“Then rest with me forever.”
Kai tsaye bedroom suka koma bayan gama wankan,saidai suna shiga wayarsa nata ruri tana maimaitawa,sai ya taka zuwa gaban madubi ya dauki wayar.
"Omar" Ya furta a fili yana zama saman sofa ya daga kiran ya sakata a hands free gami da yin cikakkiyar sallamar nan tasa.
“Omar.” ya kira ssunansa Shiru,sai muryar Omar ta fito qasa qasa da wani canji a cikin ta
“Haisam…”ya kirashi da wani yanayi,nan take idanun Haisam suka dan sauya. Dukkaninsu suna iya gane yanayin junansu su shidan daga muryar 'yan uwansu.
“What happened?” daga daya bangaren......numfashin Omar ya fito a hankali kafin ya amsa.
“Mammina ta mutu.” maganan ya maqale cikin iska yana yawo. Akhnan da ke gefen gadon ta d'aga kanta kamar me ciwon wuya.
Haisam bai motsa ba. Ko qyafta idanunsa baiyu ba na wasu seconds.
“Sun same ta a daki ta rataye kanta.”
“Ta bar letter.” omar ya sake fada
"Ta rubutata da manja na abincinta da tsinke."
Wani irin shiru ya cika suite din har Akhnan ta fara jin zuciyarta na bugawa.
A hankali Haisam ya juya baya ga glass wall din.
“Omar.” kafin yace komai omar yaci gaba da bayani.
“She didn’t wait for trial.”
“Ta ce bazata jure humiliation ba,ba zata juri qasqanci a idanun maqiya ba"
Haisam ya rufe idonsa na second guda. Ba wai saboda shock kadai ba......sai saboda ya san Mammina......ya san pride dinta. Ya san yadda take kallon duniya. Baya ga haka.....girman nauyin data daukawa kanta,bata tsaya an sauke mata shi ba tun a duniya.....bata tsaya an rage mata nauyinsa ba.....ta sake daukar wani gangamemen nauyin,nauyinma cikin haqqin Allah me gaba daya.
Har yanzu haisam ya gaza cewa komai,tsigar jikinsa kawai ke tashi. Ba don komai ba.....sai don hasaso nauye nauye daki daki dake rataye a wuyan mammina. An yankewa tamim dama dukkan wanda aka kama da laifin kisa hukuncin kisa. Masu cin amanar qasa kuma an musu nasu hukuncin daidai dasu. An saki yalwa bayan an horata,an kuma koreta kwata kwata daga masarautar agadez ba ita ba rayuwa a cikin ta har abada.
Omar ya sake magana cikin gajiya.
“The letter is mostly for you.” A hankali yatsun Haisam suka matse kan wayar,ya sani....zata rina....zata aikata. Ya sani duk duniya haushinta a kansa ne,koda ta mutu salin alin....zuciyarta zata tafi lahira ne da burin daukan fansa a kansa.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Akhnan ta mike tsaye ta kasa zama jin zancan letter da kuma sunan haisam. Tana kallonsa. Something about his face changed. Ba tsoro ba.......ba tashin hankali ba. Sai wani heavy stillness.
“I’ll call you back.”Ya kashe wayar a hankali,sai ya rubuta masa gajeran saqo akan yayi scanning paper din ya aiko masa da saqon.
A yanzu bayason duk abinda akhnan zataji da zai sanya ko yaya ta kwana ba cikin farinciki ba. Ya gaji hakanan,bayaso taji komai idan ba alkhairi ba. Sunan mammina da case dinta wani abune daya kamata ace an rufe babinsa har abada. Zai roqa mata rahama da sassauci gurin Allah,amma baya ga haka,baida wani power akan lamarinta,wannan tsakaninta da ubangijinta ne.
“Haisam…” Bai amsa ba nan take. Sai ya ajiye wayar a hankali kan table.