L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 77
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 77: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 77. Ta matso kusa da shi,a hankali ta kamo hannunsa cikin…
3,366 words
Ta matso kusa da shi,a hankali ta kamo hannunsa cikin nata. Ba wai saboda ta san abin da zata ce ba. Sai saboda suddenly… bata son ya tsaya shi kadai cikin wannan silence din.
"Shikenan.” ta furta tana lumshe ido kad'an
“Komai ya wuce…” sanda ya rigata sake magana muryarsa ta yi qasa sosai.
“Komai ya qare.” ta sake fadi itama.
Kalmar ta tsaya a tsakaninsu cikin nauyi....ba wai yana magana akan Mammina kadai ba. Yana magana akan rikice-rikicen da suka bi su a bayan rayuwarsu.
Akhnan ta kalleshi cikin nutsuwa,sai ta ga abin da bai taba furtawa ba.
Ya gaji.....ba da komai ba,sai da abinda dukka ya shafi mammina.
A hankali ta matso kusa da shi.
“Haisam…” kama fuskarta yayi cikin tafukan hannayensa ya sauke goshinsa a kanta na second guda. Sai ya rufe idonsa yana furta
“I just want peace now.”
Wani irin tausayi mai nauyi ya cika zuciyar Akhnan. Saboda ta gane,mutumin da duniya ke gani a matsayin untouchable… a wannan daren, yana neman gida ne kawai. Wannan gidan kuwa itace.....jikinta ne......kulawarta ce,batayi qasa a gwiwa ba ta soma bashi wannan gidan,tana mantar dashi komai da zafafan 'yan aike.
Sai daya tabbatar da baccinta yayi nisa sannan ya miqe ya koma ga wayarsa,yana budewa hoton wasiqar yana fadowa email dinsa. Ya zauna a hankali ta yadda motsinsa bazai tasheta ba ya soma karantawa.
Haisam
Na tsane ka. Wataqila wannan shine abu na qarshe da zaka taba ji daga gareni,amma bana son tafiya ba tare da ka san cewa kai ne mutum na farko da ya sa na ji tsoron kaina.
Ka rushe komai.
Ba saboda ka qi sona ba…ko na kasa samun goyon bayanka ba, sai saboda ka kalli raina da burikana kamar basu da wani muhimmanci.
A rayuwata ban saba da rashin samun abin da nake so ba. Amma a kanka!. Ka bani abu mafi muni fiye da wofantarwa da rashin nasara,wannan shine. Wulakanci. Ka sanya mutane suna kallona da tausayi. Ka tozarta alfarmata,ka kashe mafarkin dana shekara sama da arba'in ina ginawa tun quruciyata. Ni. Mammina. Ban iya rayuwa cikin wannan ba. Ban juri qasqanci ko rayuwa qasan kowa ba Daukaka na sani,jagoranci ne dabi'ata. Tunda dukka na rasasu....na fi son na bace da in tsaya ina jiran a yanke min hukunci kamar wata mara daraja. Ka ci nasara, Haisam. Ka kare matarka. Ka kare sunanka. Ka kare duniyarka. Ka kare ahalin matarka.....tabbas na sara maka da wannan namijin qoqarin.....na yaba maka,na kuma taya akhnan murnar samun namijin duniya irinka Amma kada ka taba tunanin baka lalata tawa rayuwar ba....kaine ka lalatata,kaine silar mutuwata. Zan tafi barzahu qiyayyarka a raina.....data akhnan da dukkanin jinin safeena Mammina.
"Subhanallah" Ya maimaita har sau uku yana lumshe idanunsa. A hankali ya motsa labbansa.
"Ba shakka abinda Allah ya fada a qur'ani gaskiya ne. Wanda Allah ya shiryar shine shiryayye.....duk wanda kuma Allah ya batar ba wanda zai shiryar dashi. Yaga wannan ayar a zahiri kan mammina,sai ya shiga ya goge saqon gaba daya,don baida wani amfani a gurinsa.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 140* ________________________ *_Amintaccen gurin siyayya_*
*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*
*_BONONZA DA PROMO akai akai_*
*dukka sai a HUGUMA CLOSET*
*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*
*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*
*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*
*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ________________________
A kwanakin da suka yi a Amangiri, Akhnan ta fara fahimtar wani bangare na Haisam da duniya bazata taba gani ba. Sai ita kadai,sai ita daya ita khadeeja muhammad hammud.
Hamadar wajen ta kasance da wata irin cikin nutsuwa da kuma wani irin yanayi me kwantar da hankali… a karon farko a rayuwarta,shiru bai tsoratar da ita ba. A karon farko ta fahimci ma'anar shiru.... A karon farko ta gane shiru wani abu ne dake bada alamu na nutsuwa cikakkiya tare da shi.
Ta kalli yadda yake lura da qananan abubuwa game da ita ba tare da tayi magana ba. Yadda yake rage muryarsa idan zai mata magana. Yadda yake cire duk wani abu da zai dame ta kafin ma ta furta,tare da cika mata komai da take so take muradi kafin ma takai ga furtawa.
Kuma duk da ikon da yake da shi… a wajen, bai yi kama da mutumin da duniya ke tsoro ba,sai wani mutum da duniya take girmamawa matuqar girmamawa.
A idanunsa take ganin mutum mai gajiya da yake neman wajen hutawa a tare da matar da yake so.
A wasu dararen,Akhnan kan tsaya tana kallon desert lights tana tunanin yadda rayuwarta ta sauya.
Cikin lokaci kadan daya wuce ta taba jin tsoron duniyar haisam.
Tsoron irin ikonsa.....tsoron izzarsa da irin girman da yake da shi a idanun duniya.....daga qarshe ta soma tsoron soyayyar da zata iya cinye mutum gaba daya,saboda girmanta da fadinta.
Amma a Amangiri… ta fara jin wani abu daban. SAFETY. Ba saboda wajen ba,sai saboda shi. Ya bata wani irin aminci cikin rayuwarta. Ya bata tabbaci.......sannan kuma ya bata yaqini na har abada.
Ko lokacin da jikinta ya fara canzawa, canzawar da ta sani da gaske ne yana sauyawar. Lokacin da tsoro ya fara shiga zuciyarta,haisam bai matsa mata ba. Bai tambayi abin da bata shirya furtawa ba. Bai tilasta mata fuskantar gaskiyar da take gudu daga gare ta ba.
Sai dai ya tsaya kusa da ita cikin nutsuwa… kamar yana gaya mata cewa ko menene zai zo, bazata dauke shi ita kadai ba.
Kuma a cikin shirun hamadar da babu kowa sai su biyu…Akhnan ta fara gane cewa wata soyayyar bata zuwa da hayaniya. Wata soyayyar tana zuwa ne da kulawa da nutsuwa, hannun da baya sakinka idan kina tsoro, da kuma mutumin da yake maida duniya gaba daya ta yi shiru saboda ke.
Private jet dinsu ya bar hamadar Amangiri ne da sassafe.
Idanun akhnan kafe daga qasa. A qasan golden desert din na qara nisa a hankali.
Amma duk da tafiyar,akhnan har yanzu tana kallon wajen ta window kamar bata son barin peace din da suka samu a can ita da haisam din.
Yana zaune kusa da ita. Suit dinsa dark charcoal. Ta kalli hannunsa a hankali,agogon hannunsa na kyalli under soft cabin lights. Wannan royal calm dinsa ya dawo yanzu.
Phones. Business calls. Security updates,kamar da zarar sun bar Amangiri duniya ta sake tunawa da shi. Wannan ya sake gaya mata da gaske ya manta da kowa dake duniya sanda suna Amangiri. Da gaske ya bar mata dukka duniyarsa ne da lokacinsa gaba daya. Ya sadaukar mata da komai da komai ita daya!.
Sai dai ta lura duk tsakiyar calls din,idanunsa na komawa kanta lokaci zuwa lokaci. Always checking. Always aware of her.
“You’re back to being busy.” ta fada softly cikin salon tsokana.
Wani lallausan murmushi ya saki yana sauke wayar dake riqe a hannunsa.
“I was always busy.”
“I just ignored the world for you.” wani laushi zuciyarta tayi, ta lumshe idanunta a hankali. Kowacce magana Idan zaiyi sake bata proof yakeyi na yadda yake qaunarta. Kowacce magana proof ne na yadda soyayyar ta take da zurfi a zuciyarsa.
Da wannan kallon yake dubanta, da wadannan idanun nasa masu matuqar kwarjini. Idanun nan da har yanzu nauyi suke mata.
"Zo nan" Ya fada softly yana miqa mata hannunsa. Ka fada ta maqale tana narke idanunta cikin nasa. Jikinsa ya mutu murus da kalar kallon da take masa.
"Ayimin izini ranki ya dade na qaraso idan ba zaki samu tasowa ba" ya sake fada yana karya wuya kamar wani marayan da ya rasa uwa da uba gaba daya.
Murmushi ne ya subuce mata, ta karyar da wuya itama tana kallonsa. Tana kallon mutumin da dukka rayuwarta da numfashinta suka dogara dashi. Sai ta miqe, da wata irin nutsuwa,da wani irin taku da tasan yana janye hankalinsa. Da wani irin yanayi da takejinta a sama. Tana jinta kamar tafi kowacce mace sa'ar miji da dacewa.
Kyakkyawan masauki ya mata cikin jikinsa,yana matseta da kyau a jikin nasa. Ya sauke wata sassanya kuma siririyarr ajiyar zuciya yana cewa.
"duk sanda nake neman gida......ba wani gida sama da nan" ya fada yana nuna saman qirjinta,inda mafi yawan lokuta a nan yake kwantar da kansa idan zai mata runguma irin wannan. Hannuwanta duka biyun ta saka itama tana zagayeshi gami da rungumeshi tsam cikin jikinta. T sauke itama ajiyar zuciyar tana bashi daman sakewa a jikinta. Lokuta da yawa bata iya magana,bata iya cewa komai idan ya soma dafa zuciyarta da lausasan kalamansa irin haka.
Lokacin da suka isa jimma sama ta fara duhu kadan da alamar samun saukan ruwan sama kowannw lokaci daga sannan.
Jimma ta yi green sosai saboda wadataccen ruwan sama da tsirrai suka samu. Gari ne da yake da wani irin yanayi me kyau tun asali,wadatar shuke shuke da qoramu dake sanya garin kasancewa cikin koren yanayi,sosai suke da yawaitar tsirrai,tsaunika masu kyau dake qarawa garin kyau,bishiyoyi dake dashe a tituna da Street na anguwanni. Wani iska mw sanyi garin yake bayarwa,ga qamshin qasa mai sanyi dake alamta saukar ruwa.
Convoy mai tsawo ne yake jiransu outside private airstrip.
Black luxury SUVs,royal security.
Mutanensu ne cikin girmamawa da Karramawa.
Zuwa yanzu ta gama fahimta ta kuma fara sabawa da ganin komai tattare dashi......amma kowanne lokaci tana sake fahimtar haisam ba ordinary bane.
Soyayyar mutanensa a kansa tana da girman data isa ka gane cewa,bawai.....sun sonsa bawai don yarimansu bane. Suna sonsa bawai don ya mallaki dukiya bane. Aah,kalar soyayyar da suke masa.....soyayya ce da zakasan cewa tausayi da kulawa da kyautatawa sune jigon ginata.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
A nutse giiftii akhnan ta sauka daga motar tana kallon surroundings din sans motocinsu ke daukan hanyar gida. Wannan bangaren Jimma din da suke nufa ba irin city din da ta sani bane. A hankali ta waiwayo gare shi tana dubanshi.
"ina zamu je?" ta furta kai tsaye,don ita nanay takeso ta gani,ta masu taje ta ganta. Har cikinranta da zuciyarta takejin tayi missing dattijuwar sosai. Sosai take jinta a ranta tamkar mahaifiyarta. Ko ba komai......ko ba alaqa ai ta haifa mata jarumin maza,daya tamkar da Million.
Siririn murmushi ya bayyana a lips dinsa. Wancan murmushin nasa nan da yake nuna ya san wani abu ita bata sani baa
“Home.” ya amsa mata a taqaice.
"wanne gida......banga nanay ba.....haisam mana" ta furta a shagwabe tana kyabe fuska. Murmushi ya kuma saki,yana lumshe idanunsa gami da budesu duka lokaci guda. Har jijiyoyinsa yake jinta idan ta kirayi sunanshin nan. Baisan sai yaushe ba,bausan sai yushe zai daina jin dadin sunanshi idan ta kira ba.... Ba lokaci,baya jin akwai zuwan wannan lokacin.
Sai ya gyada kai kawai yace.
“Mhm.”
“The one I built for you....Ba wani guda bayanshi akhnan" Ya fada yana lumshe idanunsa Akan fuskarta. Zuciyarta ta motsa a hankali. Yau itama zata shiga gidanta kenan Kamar kowacce cikakkiyar mace?.
Idanunta ta maida a hankali kan hanya sanda motocinsu suka fara hawa wani private mountain road. Fog mai laushi na zagaye da bishiyoyin gurin.
Tun daga tsarin hanyar da titin tasan cewa wata unguwa ce...... Wani guri ne na musamman da yasha banban da kowacce hanya.... Kowanne titi da kowacce unguwa. Tsarinsa na dabanne kuma na musamman. Tun daga nutsuwa da shirun titunan. Kwaltar da aka malale titin dashi,dama fitilun dake jere tare da shukokin da suka yiwa titin rumfa.
A hankali suka fada wani street daban na cikin unguwa, Wanda duka duka tafiyarsu bata haura mintuna goma ba zuwa sha biyar suka soma qoqarin tsaiwa gaban wata villa.
Idanunta ta daga a hankali,kyawawan idanunta nan da suka qara girma da haske tana saukesu saman Villa din da yake a gaban ta din,daidai sanda motocinsu suka fara motsawa a hankali suna shigewa ciki bayan tafkeken gate din gidan ya bude Kansa da kansa automatically ba tare da kowa ya isa gabanshi ko ya tabashi ba.
Ba kawai gida bane. Masterpiece ne. Modern royal architecture. Huge glass walls. Dark stone exterior. Soft warm lights. Gidan ya zauna cikin mountains kamar wata boyayyar masarauta da aka killaceta daga ganin idanuwa.
Water features na gudu softly a gefe. Dogayen bishiyoyi sun kewaye compound din. Everything private. Everything expensive.
Wani irin laushi jikinta yayi,taji wani irin nauyi yana ratsata. Wanna irin gida ne wannan kenan?. Wacce irin ginanniyar masarauta ce?. Me yasa komai nata yakan sanyashi ya zama na daban?,me yasa ko yaushe yake zabar mata surprise akan komai?.
Da wannan halin nasa na basarwa.... Yayi abinda ya kamata ya kalleka..... Yayi abinda ya dace ya tsaya ya tayaka dauka girman mamakin abun,Amma sai yayi burus Kamar baisan komai akai ba.
Tafin hannunsa ya bata sanda kowanne guard da security na gidan suka janye suka kuma juya baya don bawa matar oga daman fitowa. Idanunshi ta sake kalla,har yanzu bai yarda ya kalleta ba, Amma tana iya ganin kyakkyawan murmushi can qasa boye qasan idanunsa. Ta janye nata idanun tana dora masa nata hannun kawai saman nasa ba tare da tace komai ba.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 141* ___________________________ *_Amintaccen gurin siyayya_*
*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*
*_BONONZA DA PROMO akai akai_*
*dukka sai a HUGUMA CLOSET*
*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*
*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*
*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*
*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX __________________________
Cikin girmamawa ma'aikata da hadimai na gidan ke miqa musu gaisuwa,cikin girmamawa da sunkuyar da Kai. Wani irin ban girma da har yanzu yake saukar da mamaki a zuciyar akhnan. Da kulawa Kamar ba wannan hamshaqin yariman billionaire din ba yake amsawa. Yana riqe da hannunsa cikin nata Kamar wanda za'a qwacewa ita Idan baiyi hakan ba.
Tare suka ratsa cikin gidan,har suka kai deluxe entrance na gidan. Wata irin qofa da akhnan ta kasa gane kanta kwata kwata,sai idanu da take binta dashi. Yadan sunkuyo kadan zuwa fuskarta.
"Kiyi addu'a" Ya fada a nutse,ta lumshe idonta tana sauke ajiyar zuciya. Komai matsayinka a rayuwa akwai na gaba dakai. Da gaske ne baba ma da babansa, tabbas rayuwa ta gaji irin wannan abubuwan.
A nutse yake Karan to mata addu'o'in tana maimaitawa, ya sake riqe hannunta cikin nasa suka sanya qafafuwansu bakunansu dauke da bismillah.
A cikin jikinsa ya sanyata, suka fara zagaya gidan ita dashi yana mata bayanin kowanne sashe dalla dalla.
Ta kasa magana,sai bin ko Ina kawai da takeyi da kallo. Duka yadda taga ginin daga waje, ta ciki ya zarta hakan. Wata aljanna ce kawai ya Samar da ita tun daga nan gidan duniya.
“Haisam…” ta kirashi tana dubansa bayan daya Kira sunanta tana tsaye cikin dakin Yara. Wani irin daki da aka masa wani tsari na musamman, tsari me daukan hankalin da duk uwa zataso ace mallakin abinda zata Haifa ne. Komai an saka a dakin, ba wani abu da za'a buqata sai sanda za'a haifi abinda aka tanadi gurin saboda shi.
“You like it?” ya tambayeta, yana tsaye da wannan tsaiwar tasa irin ta giant din maza. Hannunsa zube cikin aljihun wandonsa ya rusunar da narkakkun idanuwa nan nasa a kanta.
Ta kasa magana ma kwata kwata, Idan ta bude baki zatayi magana sai taji muryarta tana rawa. A hankali ta fusgo kalmar
“You built this?”Sai ya gyada kai.
“For year” Ta kasa magana kawai tana lissafa kwanakin zuwansa agadez. Shekara ta farko daya fara saninta. Shekarar daya fara hada idanu da ita. Shekarar daya fara jin cewa yana sonta a rayuwarsa.
"A wannan shekarar kenan ya fara gina gidan saboda ita? " Ta yiwa kanta tambayar tana daga idanunta tana zubesu a kansa.
Yanzu take sake realizing.....tun kafin abubuwa su kai yadda zasu fara magana da juna.....tun kafin ta fahimci yadda yake sonta.....already yana gina mata future cikin wannan shirun daya zama tambarinsa.
"Amma wannan dakin...... Bani da ciki haisam" Tayi maganan tana narke murya. Murmushi ya saki,wani qaramin murmushi me dauke da tarin ma'anoni. Baisan ya mata suke idan suka samu ciki ba, Amma shikam lamarin akhnan dariya yake bashi. Har yau har gobe taqi believing abinda takeji,bayan ita kanta shaida ce da yadda abubuwanta keta canzawa. Ita kanta shaida ce Akan yadda komai nata yake tafiya ba'a daidai ba, ba'a kuma yadda ta sanshi ba.
"I know" Kawai yace mata, yana qoqarin adana dariyarsa.
Taku biyu ya iso gabanta,ya sake sanya hannunsa yana lalubo hannunta cikin nasa, ya hade tafin hannunsa da nata, sannan ya fara takawa da ita a hankali suna fita a dakin.
Juyawa take tana kallon komai cikin disbelief.
Ta tsaya tsakiyar living area din da suka sake bullowa. akwai elegant staircase,saidi amma ba sama yake hawa ba. Qasa yake sauka,underground. Ta sake maida idanunta kansa da mamaki.
“What’s down there?” ta zabi ta bayyana qauyancinta kawai akan tayi shurun.
Haisam ya zuba mata ido,siririn murmushi yana subucewa daga labbansa. Tana burgeshi, bata da girma kan nuna batasan abu ko bata ganeshi ba. Zata tambaya ne Kai tsaye kawai, ya danganta da yadda ka dauki abun.
“Come see.” ya kamo hannunta gently.
Sauka suka fara yi tare,step by step.
Wasu irin soft hidden lights na cikin stairs din na haska ko Ina, har saman qafafunsu da suke takawa da wata irin cikakkiyar nutsuwa.
Akhnan na jin zuciyarta na bugawa saboda gidan already ya wuce imagination dinta.
"To me zai sake boyewa a qasa?" Ta tambayi kanta da kanta can qasan zuciyarta.
Ko ba'a fada mata ba stair case din ta musamman ce. Kana takawa kana jin wani sanyi da taushi qasan tafin qafarka. Suna sauka suna nutsawa zuwa qasan wani yanayi me dadi yana lullube gangar jikinka. Wani haske.... Wani tattausan oud scent me dadin shaqa.
Da suka isa qarshe sai ta tsaya cak.
Gaba daya underground level din kamar secret luxury world ne.
Private indoor lounge,glass ceiling sections,soft waterfall wall,library,cinema room ga kuma hidden relaxation spaces haka suka dinga zagayawa daki daki.
Kamar wajen da mutum zai boye daga duniya ya samu sukuni ya manta da komai. Sai a sannan ta sake gasgatawa,ta sake yadda dashi. Da gaske bayason hayaniya. Da gaske shi din mutum ne da baison dogon zance ko kuma hayaniya ko kadan. Tasha jin su rumaisa suna gulmarsa,amma yau ta samu tabbaci da kalan ginin gidan qasan da yayi.
Ta juya gare shi cikin mamaki sosai,sai ya sake bata hannunsa suna sake takawa ciki.
Da suka shiga ciki,even the silence felt luxurious.
Huge open spaces. Warm lighting,minimalist elegance....Oud scent mai laushi.
Kowane detail din wajen carefully planned ne. Da wannan nutsuwar tasa..... Tsarin nasa da ita aka gina wajen..... Da ita aka gina komai na gurin.
“This doesn’t even look real. " Kaman bazai magana ba, kaman bazai motsa ba kafin ya tako a tausashe ya qaraso kusa da ita sosai. Kusan da take iya jin saukar numfashinsa a hankali.
“It’s real.” yadan dakata da tarin nutsuwarnan tasa.
“And it’s yours too.” wani irin shuru ya gilma,akhnan ta ji zuciyarta na yin wani irin laushi,saboda duk inda yake kai ta.....bawai wajen nuna kudi kawai yake kai ta ba,a'ah...