Kenza eBookz

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 78

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 78

L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 78: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 78. Yana gina mata tsaro da wani irin aminci ne,da rayuwar…

3,375 words

Yana gina mata tsaro da wani irin aminci ne,da rayuwar da bata taba mafarkin zata samu ba.

Ta bude baki zatayi magana,Amma sai ya hana mata wannan damar, ya sanya hannuwansa gaba daya ya daga ta cak ya rungumeta a qirjinsa yana cewa.

"Ki huta haka nan,zan amsa kowacce tambaya taki bayan kin huta" Wani guri taga yana nufa da ita, sun wuce wani dogon guri me kama da hallway wanda ya qunshi wasu irin luxury bedrooms ba daya ba ba biyu ba. Ya zabi daya daga ciki ya tsaya a gaban qofar, tayi magana cikin harshen turanci tana nuna fahimtar waye tsaye a wajen, ta kammala scanning nasa ta bude musu suka shige.

"Welcome to my world" Ya furta yana direta tsakiyar bedroom din data jita tun bayan shigowarta tana fita daga duniyarta zuwa wata duniyar ta daban.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Gaba yayi zuwa wata qofa kawai ya barta, duk yadda taso ta maze kuma ta kasa, sai data saki idanunta sosai tayi kalle. Kalle yadda ya kamata. Ta sauke ajiyar zuciya a hankali, sai ta samu kanta da furta.

"Alhamdulillah" Don a yanzun bata da sauran abinda zata yiwa Allah Idan ba godiya ba. Ya bata sama da yadda ta tsara..... Me yafi wannan ni'ima da dadi ga ubangijinka?.

Ruwan wanka ya hada musu,kaman kuma yadda ya tsara wankansu a tare Tun a wancan ranar ba abinda ya sauya wannan tsarin. Tare suke wanka, ba wanka kawai ba komai da komai ma. Har wani lokaci tana tunanin,ya zaiyi Idan aiki ko tafiya ta sameshi ba tare da ita ba?. Duk da shi kawai take tunawa tana mantawa da kanta,wanda tasan zata fishi jigata tabbas a yanzu Idan wani abu da zai sanya suyi nesa da juna Idan ya taso.

Idanu ya zuba mata ganin yadda taqi cin komai cikin abincin da aka shirya a gabanta.

"Habibty" Ya Kirata da wannan muryar tasa da sautin ke ratsata a duk sanda zai kirata. Idanunta ta daga a kansa, Shima ya mata nuni da taci wani abun.

Fuskarta ta bata, ita kwata kwata ba abinda yayi mata, batasan yaushe ta canza ta koma haka ba. Tana jin cewa Tana son cin abubuwa da yawa, amma komai Idan an kawo sai taji ya fita daga kanta. Har tausayinsa takeji sometimes, sai taga Kamar tana bashi fatigue ne kawai.

"Nanay nakeson gani please" Ta fada da shagwabar nan tata. Numfashi ya sauke a nutse, yana jiye spoon din hannunsa idanunsa cikin nata.

"Please.....kada kace a'ah" Ta furta tana hade hannayenta guri daya. Kaman bazai magana ba, sai a hankali ya furta.

"Okay" Da wani sauti can ciki.

"Ya Salam" Ta fada can qasa,simplicity dinsa yana burgeta sosai.

"Na gode yarima na" Yadda ta fadi maganan ya sanyashi sakin murmushi me qaramin sauti.

"Ni ba wannan cin hancin nakeso a bani ba, already na sani yarima ne ni...... Cin hancina...... Na dare nakeso. A wannan sabuwar duniya,DAGA NI SAI KE" Ya qarasa fadi idanunsa suna narkewa cikin nata.

"Baka da damuwa" Ta fadi da wani irin confidence tana rolling idanunta, abinda ya kusa zautar dashi, ya sanyashi miqewa yana ture plate din abincinsa.

"Let's go" Dariya sosai ta saki har tana duqawa saman table din, sai ya koma baya a nutse ya tsaya yana crossing hannayensa a qirjinsa,sannan yayi crossing legs dinsa yana qare mata kallo.

"Ni kike wa dariya giiftii? " Ya fada da softness dinsannan yana nuna kansa da yatsarsa.

"D'okin is too much my prince" Idanunsa ya lumshe yana budesu, sai ya sauke hannayen nasa da qafafunsu qasa, ya soma takawa zuwa gareta.

"Okay..... Lemme show you irin d'okin da nake" Tana zullo tana komai haka ya dagata cak ya wuce bedroom din da ita.

Sai daya goge mata duk wata hadda ta kanta tas. Ya jefata wata duniya data sanya ta dinga leqen fuskarsa bayan wani dan gajeran bacci yayi awon gaba dashi.

Ta miqa hannu a hankali ta saka dan yatsanta qwaya daya tana maida sumarsa data kwanto gaban goshinsa zuwa baya. Ya mata wani irin kyau,kamanninsa sosai dab da ita. Allah ya sani,bata taba ganin namiji me wani irin kwantaccen kyau irin nasa ba. Komai nasa me kyau ne,komai nasa me wani irin sanyi ne da daukan hankali.

Ta dan matsa kusa da shi kadan. Idonta ya sake tsaiwa a kansa.

Wani lokaci har yanzu bata yarda cewa wannan mutumin… wanda mutane ke tsoro saboda kwarjininsa ba.....wanda wanzuwarsa kawai ke sa mutane su yi shiru…. Shine mutumin da yake jan blanket ya lullubeta idan taji sanyi. Shike hada shimfidata da ita. Shike gauraya numfashinsa da nata numfashin.

Ta bi fuskar tasa da kallo a hankali. Dogayen lashes dinsa, dogon hancinsa, kwantaccen sajen dake qasan habarsa.....hannunsa da yake kusa da nata,sai murmushi mai laushi ya bayyana a fuskarta ba tare da ta shirya ba.

Ta sauke ajiyar zuciya a hankali tana janye yatsanta. Caraf taji an kama yatsan an riqe, sannan a hankali ya bude idanunsa ya zubesu fes saman fuskarta.

Ba abinda yake tunawa sai duniyar data jefashi a dazun,wata duniya da yake fatan har abada ta zama mallakinsa shi da ita.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 142* _________________________ https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0

*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*

*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*

*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*

*_Assalamu alaikum my loyal people_*

*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*

*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*

*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*

*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*

*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*

*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*

*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*

*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*

*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee* __________________________

"How long have you been staring at me?” ya fada da muryar bacci,wata nannauyar murya me ratsa zuciya sosai idanunsa suna lumshewa,Adams Apple dinsa yana sama da qasa Kamar me hadiyar wani abu.

"Ban.... " Ta fadi tana zaro idanunta saboda ya shammaceta.

"You’re a terrible liar.” Ya fada da wannan nannauyar muryar tasa idanunsa a kan razanannun idanun nata. Ta masa wani irin kyau, musamman sanda ya fadi hakan, ya kuma sanyata kauda Kai gefe kunya tana cikata, sai ya jawota sosai softly cikin jikinsa sanda take amsa masa.

"Na dauka bacci kakeyi"

"I was" Ya amsa mata a taqaice yana kissing dogon wuyanta gami da sake mannata a jikinsa.

"Then why did you wake up?” ta fada a shagwabe tana turn baki gaba.

A hankali wani lazy smile ya bayyana a gefen bakinsa, ya gyara mata kwanciya sosai yana shaqar qamshin hair mist dinta

"I felt you..... Shi yasa na farka"wani shuru ya ratsa tsakaninsu,tana qoqarin qidddige yawan adadin soyayyar da yake mata,wadda takai har cikin baccinsa ma yana iya feeling presence dinta.

"Tell me" Ya sake fada da wata sirrintacciyar muryar data kasance tata ce ita kadai. Ita kadai kejin wannan sautin....... Wannan muryar da wannan amon.

Ta lumshe idanunta tana jin yadda muryar ke saukar mata da kasala a kowacce gaba ta jikinta.

“I was thinking…” sai ta dakata

“…you look peaceful when you sleep.”ta qarasa fada tana sauke idanunta da wani irin sanyi akan fuskarsa. Kallon yaji yana ratsa shi a hankali,kamar wanda aka mannawa qanqara a qirjinsa. Shuru, wannan shurun dai ya sake ratsawa ta tsakaninsu, kaman bazaice komai ba, sai kuma ya dora hannunsa a hankali yana rarraba dogayen eye lashes dinta. Ya motsa labbansa a hankali da wata irin kasala.

"That’s because my heart rests when you’re near me.” wani irin abu ke sake sauka a zuciyarta, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa..... Saboda shi kadai. Sai ya sake zuba mata ido cikin sleepy softness din nan tana sake yi masa kyau.

"You watch me like you’re scared I’ll disappear.” ya fada yana lakace mata hanci.

"You disappeared once already.” ta fadi tana cizon fatar qirjinsa a tausashe.

"Ouchch" Ya fada Kamar da gaske yaji zafin cizon, sai suka saki dariya ita dashi gaba daya lokaci guda.

Sanda suka gama shiryawa ji yayi kaman yace su fasa zuwa gurin nanay din. Ya dinga qare mata kallo,tun daga siffa har zuwa takunta.

Ya ware mata hannunsa yana sauke mata lallausan murmushi. Batayi qasa a gwiwa ba ta qaraso ta shige ciki, tayi luf abinta tana sauraren bugun zuciyarsa.

Sai da suka kusa minti goma a tsaye a haka ba tare da yace mata komai ba,sannan ya janye ta a hankali yana kissing goshinta.

Wannan yanayin ba wani sabon abu bane a wajen ta. Ta riga ta saba da hakan,sometimes yakan zabi gaya mata abinda yakeji a kanta ta hanyar runguma,sanyata cikin jikinsa da bata daman sauraron bugun zuciyarsa sama da magana da baki.

Sanda suke takawa a farfajiyar gidan, riqe da hannuwan juna. Kai me karatu inda zaka hangensu a sannan zasuyi matuqar burgeka. Yariman Jimma da sarauniyar agadez. Wani iri perfect match ne da yake bawa kowa mamaki. Ba iya mutanen waje ba. Daidai da ma'aikatan cikin gidan wani lokaci suna labewa satar kallonsu.

Kamar ko yaushe,ya bude mata motor da kanshi, sannan ya zagaya daya bangaren shima ya shiga. Motor ta fara motsawa tana barin gidan. Idanunta akan farfajiyar gidan, komai tana ganinsa da wani irin yanayi me matuqar jan hankali, komai na gidan burgeta yakeyi,hakanan komai din sai yake mata kamar dama can ita ta zauna ta tsara yadda komai zai kasance a cikin gidan nata.

Sanda suke shiga masarautar Jimma,abinda yafi bata mamaki basu sanar da zuwansu ba, amma kafin su wuce gate na farko har kowa ya ankara da isowar yarima haisam. Suna ta cikin motar ne basu kai ga fitowa ba,amma wani girma dukka hadimai da al'ummar masarautar ke bawa motar kanta bama su ba. Kowanne shinge da zasu wuce kafin sukai ga qarasowa ake budeshi da wani irin yanayi me cike da girmamawa.

Shi ya sake bude mata motar, ya zagayo ya riqe hannunta yana fiddo da ita, sannan suka fara takawa zuwa cikin gidan yana amsa gaisuwar bayi da hadimai da wani irin yanayi dake nuna asalin izza da sarautar dake yawo a jininsa.

Faluka bayan faluka suka dinga ratsawa shida ita. Tako Ina gaisuwa ce cikin girmamawa suke karbarta shi da Akhnan din.

Sanda suke isa sitting room na qarshe da zai sadasu da inda nanay tafi zama,a daidai lokacin take shigowa itama ta daya qofar da ahalin gidanne kawai suke using wannan qofar, Kamar yadda yake akwai kebantattun gurare da iyasu dinne kawai ke da access da gurin.

Ganin farko data musu taji wata matsananciyar faduwar gaba ta saukar mata. Wani irin kyau suka mata me daukan hankali. Kwarjininsu,da kalar matching din da sukayi da juna abune da idanu ba zasu iya kaucewa a kansu ba.

Har tayi taku daya baya,amma wata zuciyar me cike da kishi ta bata shawarar dawowa. Ba musu ta tako a hankali zuwa gabansu.

"Barka da shigowa obbo" Ta fadi da wani yanayi na girmamawa sosai cikin muryarta,da kuma nuna kulawa. Yanayin daya tafi a hankali,kai tsaye kuma ya sauka a zuciyar akhnan.

"Yauwa" Ya fada a taqaice idanunsa suna kan hanya. Ta dan saci kallon akhnan. Ko yaya tana so tayi abinda zata qona mata rai,tanaso ko yaya ta motsa wannan izzar tata.

"Kamar nanay tasan zakazo,tace na hada mata coffee me yawa na kawo mata" Ta fada da murmushi a fuskarta tana dubansa. Abun yadan masa banbarakwai,amma hankalinsa sam baya ta gurin,sai ya waiwaya yana duban akhnan din.

"Mu qarasa?" Kai ta gyada masa a nutse,sai ya sake ware hannayensa yana sarqesu da nata kamar wanda akace za'a qwacewa ita.

Akan idanunta yayi hakan,bata sare ba ta murmusa kadan.

"Idan ba damuwa na maka iso,kaman ta zauna zaman addu'a" Ta fada da girmamawa,amma yadda tayi gaba ba tare data damu da miqa wannan girmamawar ba yaja hankalinsa.

"Saamee" Ya kirata kai tsaye. Har cikin ranta taji saukar sunan,wani abu me sanyi ya lullubeta,don ta manta yaushe ne na qarshe da taji ya kira sunanta. A ladabce ta waigo tana amsawa.

"Wannan ya zama karo na qarshe da zakiga matata ki wuceta ba tare da kin gaidata ba.....ina fata baki manta hukuncin dake kan duk wanda ya aikata hakan ba". Wani irin qasqanci zallarsa taji yana mamayarta. Wannan maganar tasa tana daidai da tuni daya mata gami da maidata asalinta na DIYAR BAYI. kenan....hakan na nufin ba'a canzawa tuwo suna?. Hakan na nufin ita ba diyar kowan kowa bace har yanzu ba abinda ya shafe wannan?.

"In sha Allah" Ta fada a sanyaye,sannan ta waiwaya sashen akhnan.

"Barka da isowa"

"Na gode" Akhnan din ta amsa still ba tare daya dubi sashenta ba.

Wani abune ya mata tsaye a zuciyarta,wasu irin dabi'u take karanta tattare da saame wadanda suke bata haske kan inda ta nufa.

"Ba buqatar kiranta....zan qarasa da kaina" Akhnan tace da saamee sanda take shirin isa ga nanay ta sanar mata isowarsu. Saita tsaya cak tana jin kamar an sace mata gwiwa,sannan taja baya a hankali sanda akhnan ke tattakawa riqe da hannun haisam ba tare data sakeshi ba.

Dole taja gefe ta basu hanya,sannan ta koma da baya a hankali tana barin gurin.

Suna shiga ta zame hannunta daga nasa,saita ja baya kadan tana duban idanunsa. Haka kawai ta samu kanta ta watsa masa harara.

"Ban yarda kowa ya shiga tsakanina da sultane ba.....wai har don saboda inason ganin mahaifina sai anmin iso.....haka yake game da nanay. Ban gayyaci kowa gurin neman iso kan ganin mamana ba" Ta qarasa fada tana sake miqa masa wata hararar sannan ta fara takawa. call

"Tun wuri ka gaya mata. Bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane....idan da wani tunani da take dashi a kanka,ka gaya mata ta daina,tun kafin ta shiga inda ba zata iya fitowa ba" Ta dan matsa kusa da shi, idanunta cike da kishin da take qoqarin boyewa.

"Tana kirawa kanta tashin hankalin da mutane duniya duka basu isa mana sulhu ba"

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"ni khadeeja muhammad hammud ba sa'ar kowa bace". Wani lallausan murmushi ne yake fita ta gefan bakinsa,idanunsa zube fes a kanta. Idan tana nuna kishinsa irin haka,shi kadai yasan yadda abun ke burgeshi,shi kadai yasan yadda abun ke masa dadi. Hararsa ta qara yi,yanayin daya sanya idanunta suka masa kyau.

"Kaima kada ka sakemin wannan murmushin"

"Which smile?" Ya tambaya cikin nutsuwa kuma kai tsaye still yana kallonta.

"Wanda yake nuna jin dadin abinda nake fada" Ta sake fadi wannan karon harda murguda masa wannan qaramin bakin nata. Dariya ta kusan subuce masa,yadda ta koma me tsiwa sosai cikin lokaci kadan. Wannan tsiwar da yake hange daga nesa.....yau gata kusa dashi ana gwada masa.

"You're jealous" Ya fada murmushinsa yana qara fadada. A hankali ta bude bakinta don ta musanta,amma saita kasa hakan,ta kauda kanta gefe tana tura baki gaba.

"Duk yadda ka dauka" Sai ta fara takawa zuwa ciki.

"Akhnan." Ya kirata yana jin yadda idanunsa suke narkewa a kanta. Ba tare da ta juyo ba ta amsa.

"Me kuma?"

"Kin makara." Ta hade gira.

"Makaran me?" Ya jingina da bangon dake kusa dashi yana kallonta

"Da wannan kishin." A hankali ya qara da fadin.

"Da kin zo shekaru da suka wuce,da kin samu abin kishi." Sai ya girgiza kai.

"Yanzu kuwa..." Ya dakata na dan sakanni.

"Babu wanda nake gani sai ke." Akhnan ta ji yadda zuciyarta ta yi wata irin bugawa,amma duk da haka ta qi ba shi nasarar gani a fuskarta. Sai kawai ta sake jefa masa harara,wacce a wannan karon ta fi kama da murmushi fiye da fada,ta kuma juya abinta tana shigewa zuwa ga nanay.

Cikin nutsuwa ta yiwa nanay cikakkiyar sallama,nanay din dake saman abun sallah rumaisa a gabanta da alama magana suke ta amsa tana d'aga kanta zuwa ga akhnan din.

Wani faffadan murmushi me cike da qauna da soyayya ya kubcewa nanay din.

"Giiftii.....fitowa kikayi?,haisam bai gaya miki zanzo da kaina na ganku ba?" Nanay ta fada cikin kulawa tana duban akhnan da tarin soyayyar da irinta takewa mahaifiyarta safeena.

Qasa akhnan din tayi da kanta,tana jin wata matsananciyar kunyar nanay da bata taba jin irinta ba. Haka kawai takejin all over her body nanay na ganin komai. Komai da sukeyi ita da haisam din,dama yadda haisam din ya lalatata a kwanakin nan. Ashe haka surukutar take?,take tambayar kanta sanda takejin ba zata iya hada idanu da nanay ba sanda nanay din ta miqe da kanta tana marabtarta.

"Maraba da diyata" Nanay ta furta tana budewa akhnan hannuwanta don ta rungumeta.

Idanun nanay din a kanta sanda take takowa,mamaki kadan yana kama nanay din da yadda akhnan din ta wani bude lokaci guda tsakanin tafiyarsu da dawowarsu. Ta sauya gaba daya kamar sai a yanzunne mijinta ya santa diya mace.

Wani abu ya d'arsu a zuciyar nanay din sanda take rungume akhnan a jikinta.

"Barka da warhaka nanay" Ta fada tana rusunawa cikin jikin nata. Riqeta tayi sosai a jikinta.

"Banason ganin wanna surukutar cikin idanunki giiftii.....ke din kamar rumaisa kike ko Aanani,matsayinki ma a zahiri ya d'ara wannan" Ta fada tana dagata daga jikinta gami da mata mazauni saman shimfidarta data tashi a kai. Rumaisa na zagayowa tana zama gefan akhnan din gami da leqen fuskarta sosai. Ita kanta mamakin sauyawar giiftii din tasu takeyi,wani ajiyayyen kyau tayi me matuqar daukan hankali duk da tarin kyan nan nata.

"Giiftiin Captain.....kina kallon madubi kuwa?,anya captain sheikh zaici gaba da barinki fita koda tare zaku fita din?" Ta tambaya da gaskiya cikin muryarta.

Ture hannunta kadan akhnan tayi cikin jin kunya tana mata nuni da nanay da idanu. Nanay din da tayi kaman bata ji ba,saidai zuciyarta tayi nisa a wani tunani.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 143* ________________________ https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0

*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*

*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*

*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*

*_Assalamu alaikum my loyal people_*

*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*

*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*

*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*

*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*

*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*

*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*

Readers Also Read

More by Huguma