L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 79
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 79: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 79. *_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki…
3,345 words
*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*
*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*
*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa ameen* __________________________
"Ina ya tsaya shi muhammad din?" Nanay ta tambaya tana zama sosai saman shimfidartata,saidai tana sauke maganan muryarsa ta bayyana.
"Yaya za'ayi ki ganni nanay.......gani nan a tsaye kusan minti nawa.....amma nanay wai baki ganni ba tambayata ma akeyi" Ya fada da wani yanayi daya sanya rumaisa sakin boyayyar dariya. Murmushi nanay ta saki,tasan kishinsa da yadda bayaso a shiga tsakanin soyayyarta da shi.
"To qaraso mana" Ta fada tana daga masa hannu. Kafada ya maqale yana komawa wani kalan tausayi.
"Alqawari nanay......nima na cancanci a marabceni" Murmushi tayi ta kauda kai.
"Ka shigo muhammad" Ta furta,sai ya tsugunna ya zame takalman qafafuwansa sannan ya sanyo qafar tasa a hankali yana shigowa.
"Shikenan......tawa ta qare,Allah sarki ni" Ya fada da muryar tausayi wadda dukkansu sai data saka suka kusa fashewa da dariya,harsa akhnan da kadan kadan takejin yaren oromo,amma zamanta dashi tana fahimtar abubuwa sosai,maidawa ce saidai da qananun jimloli kuma.
Ga mamakinta kanshi tsaye ya wuce saman abun sallar nanay din,ya qarasa zuwa gabanta ya zauna sosai yana tanqwashe qafafu.
Hannunta ya kama cikin nasa,yana duban idanunta cikin kulawa da qauna ya fara gaidata.
"Fatan kun dawo lafiya....."
"Alhamdulillah nanay,ina fatan na same ki lafiya"
"Lafiya qalau muhammad...." Ta fadi daidai sanda ya riqe hannunta yayi kissing bayan hannun nata.
"Ma sha Allah" Ta fada itama tana dora hannunta saman nasa.
Satar kallonsa akhnan keyi,mamakinsa yana saukar mata. Mutumin da kullum yake tafiya da cikakken iko da nutsuwa... wanda ko manyan mutane ke gyara zamansu idan ya shigo waje... yanzu yana zaune a gaban Nanay kamar qaramin yaro.
"Amma muhammad me yasa baku zauna ta huta ba?.....nace da kaina zan shigo ko?,dazun muka gama magana da motii" Nanay ta tambayeshi tana kallonsa cikin zallar kulawa.
Tunanin akhnan ya yanke sanda ya zame ya kwanta,yana dora kansa saman cinyar nanay din,ya gyara kwanciyarsa sosai fuskarsa tana nuna kalar nutsuwar daya samu.
"Gata nan nanay....ita ta takura lallai sai tazo ta ganki" Ya qarasa maganan yana sanya idanunsa cikin na akhnan wadda mamaki ya sanyata daskarewa a gurin.
Hannu nanay ta dora saman lallausan gashinsa
"Laifinka ne......me zaisa ka bari tayi wahala.....halanma kaine ka matsa sai kun fito" Ta fada tana duban akhnan.
"Wayyo ni" Ya fada a tausashe.
"Nanay.....giiftii ta fara shiga tsakanin mu" Ya fada a narke yana maida idanunsa ga akhnan,akhnan din data narke a gurin tana kallonsa.
Wannan ne haisam?. Wannan ne mutumin da idan ya shiga daki mutane ke gyara zamansu. Wannan ne mutumin da ko murmushi yake yi sai ya zama kamar ni'ima ga wasu. Amma yanzu...yana kwance kan cinyar Nanay kamar qaramin yaro da ya dawo gida bayan doguwar tafiya.
Ido daya ya kashe mata,saita janye idanunta a hankali tana kallon qasa.
A gurinta kawai da gurin nanay take iya ganin wannan siffar.....wannan kamannin.....da wannan haisam din. Mutum biyu ne kawai DUNIYARSA a rayuwa.....mutum biyu kawai ke iya ganin wannan side din nasa.....mutum biyu kadai,ita da nanay.
"Zo nan kinji" Nanay ta fada tana miqawa akhnan hannu.
A kunyace ta miqe tana matsowa gaban nanay din,wannan ya sake bata daman sake qarewa akhnan kallo sosai. Ta sauya....komai nata ya sauya,komai nata kuma yana bada wata alama ta daban. Amma ba wanda yace mata komai a cikinsu,wataqila kunya sukeji.....wataqila akwai sanda suka ajiye don sanar mata. Zata jira wannan lokacin,duk da bata da cikakken tabbaci.
Cikin jikin ta zaunar da akhnan din,sai ya daga kansa a hankali yana dubansu,a badini zuciyarsa na masa wani fari da haske,yana kallon duniyoyinsa guda buyu,yana kallon farincikinsa.....aljannarsa da kuma rayuwarsa a fuskokinsu.
Amma kuma a zahiri sai ya hade rai kadan.
"Nanay....."
"Haisam" Ta fada tana tsaidashi. Bayason kowa a gurin idan suna tare,ta sani,amma yanzun tana jin akhnan ta riga ta shiga wani bangare na rayuwarsu dukkaninsu.
Kafin tace komai rumaisa data fice ta basu guri ta turo qofar.
"Nanay.....an shirya table din"
"Gani nan" Ta amsa mata,sai rumaisa ta juya ta koma,don sun saba kebewar Captain din nasu da nanay dinsa ba wanda ya isa ya shiga,sai yanzu da akhnan ta zama ta ukunsu.
Tana riqe da hannunsu suka isa dining din. Katafaren dining din da aka shiryawa kalolin abinci,ba masu yawa sosai ba,daidai yadda zai nuna alfarmar wanda zai zauna cin abincin.
Yana shirin jawa nanay kujera don ta zauna akhnan ta rigashi. Yadan fiddo idanu cikin subutar baki ya furta.
"Easy mana....karki qara" Zuciyarsa nadan bugawa kadan. Gani yake kaman mistake qarami zai iya taba abinda akhnan din ke dauke dashi,abinda har yanzu akhnan din bata amince akwaishi ba.
Dukkaninsu ita da nanay din suka kalleshi,idanun akhnan fal da tambaya,yayin da nanay kuma abun ya sake sa mata gamsuwa da zarginta,amma saita dauke kai kaman bata fahimci komai ba. Shima basarwa yayi yana shafa sumar kansa,ya matsa a hankali ya jawa akhnan tata kujerar,ta zauna,sannan yaja tasa opposite tasu shima ya zauna.
Biyu daga cikin bayinta ne suka matso suka fara serving nasu,akhnan tana jin hirarsa da nanay din kadan kadan. Bata saka musu baki ba,duk da yadda nanay ke sakata a hirar. Yanayin mu'amalarsa da nanay na burgeta,har wani lokaci takan rasa tantancewa dawa yafi shaquwa?. Nanay din ko motii. Abu daya ta barwa ranta,shaquwa ce sosai tsakaninsa da nanay,da motii kuma wasu sirrikane yakeyi dashi wanda qirji da zuciyar uwa ba zasu iya dauka ba,dole lallai sai uban.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Fitowar noorah da Aareef ya sake sanyawa ta kuma jin dadin zaman. Tanason yarinyar sosai,tana da wani irin hankali me ban mamaki. Ta yarda ba banza ba haisam ke sonta shima. Tana murmushi take tsokanarta bayan ta gaidata.
"Hoton me dame aka dauko mana a wannan satin?" Murmushi ta saki tana ciro camera dinta da bata rabo da ita.
"Na sake siyan wasu sabbin tsuntsayen wajen halyjesheru ventures giiftii 704 666 5338....har da dawisu guda hudu.....kin gani" Ta fada tana miqa mata camera din. Daidai nan rumaisa da Aanani suka shigo,suka samu guri suka zauna suna jan plate suma,tana jin nanay tana mitar sai suqi cin abinci sai taxo cin nata,ta saki murmushi family din na sake burgeta.
Tana murmushi tana duba hotunan,sai ta sake girmama lamarin ubangiji. Wasu irin kyawawan tattabaru da kaji,ga wasu irin dawisu harda parrot ma,ita sun mata kyau sosai,ta daga ido tana duban haisam. Girarsa ya dage mata,sai itama ta dage masa tata girar,ya juya ga noorah a nutse.
"Auta,a saka mana order.....a zaba mata masu kyau" Murmushi noorah ta saki,wannan murmushin dake qarawa yarinyar kyau.
"Amma obbo.....zan dora ribata fa" Murmushi ya saki
"Riba halal ce auta,ki qara ko nawa kikeso" Suka saki dariya gaba daya.
Duk cikinsu bayan shi itace ta biyu dake da neman na kanta sosai,shi yasa yake qara qarfafa mata gwiwa,yanayin abubuwanta zaka dauka ba daga gidan sarauta me girma irin wannan ta fito ba. Ga qananun shekaru amma haka take koyon kasuwancin dabbobin.
Dauke da babban tray ta shigo gurin,ko sau daya akhnan bata yarda ta kalleta ba. Haka kawai batason koda ganin fuskar yarinyar. Ta qaraso tana tafiya a hankali zuciyarta tana wani irin matsewa a qirjinta.
Tsakiyarsu ta ajiye tray din coffee din,saidai,ta ware cup biyu kadai. Nanay ta zubawa ta ajiye a gabanta,sannan ta sake zubawa a dayan.
Sai data saci kallon akhnan din,sannan ta sanya qaramin tray a qasan mug din. Ta matsa daura dashi tana lanqwashe murya.
"Gashi obbo" Ta qarasa fada tana ajiye masa a gabanshi.
Hannu yasa ya janyeshi gefe idanunsa na sauka kan fuskar akhnan.
"Daukeshi daga kusa da nan.....na nanay is okay" Ya fadiwa saamee ba tare daya kalli fuskarta ba.
Ta lumshe idanunta a hankali tana budesu saboda tuni qamshin ya buwayi hancinta da wani irin yanayi me daga hankali. Kaf qamshin nan da yakeyi wani abu na daban yake zame mata yana sake hautsina mata ciki.
"Are you okay?" Ya fada muryarsa can qasa da wani irin kulawa. Kai ta daga masa a hankali tana qoqarin qaqaro murmushi,sai ya dora hannunsa a hankali saman bayan hannunta idanunsa cikin nata.
Gabanta yayi wani mummunan faduwa. Wani abu ya sauka a hankali yana mamayar zuciyarta. Kulawarsa.....kulawar da yake bata ta tsaye mata a rai da wani irin matsanancin kishi.
"Me yasa batason qamshin coffee.....me yasa?" Ta tambayi kanta. Tantancewa takeso tayi,tana son sanin dalili,sai ta dauki wani mug din ta cikashi taf ta tura gabanta.
"Ga naki" Ta furta idanunta akan akhnan.
Iskar data shaqa ta shiga sosai cikin cikinta,ta soma hautsina mata duk wata nutsuwarta da walwalarta,take ta tattara wani irin amai cikin qasa da second biyar ta soma yunqurin turo mata shi waje.
Yunqurin aman da sautinsa ya daga haisam daga mazauninsa cikin qiftawar idanun da baisan zai iya hakan ba sai yanzu. Sai akan akhnan din.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 144*
"Me ya faru?....giiftii....I'm sorry.....sorry please" Shine kalman da yaketa maimaitawa kawai da wani irin rudadden yanayi.
Kaman aman na jiransa ne ya isa gabanta,gaba daya ya soma fitowa ba tare da wani jiran komai ba. Kai tsaye ta soma wankeshi tana wanke kyakkyawan jubah din jikinsa. Dukkaninsu hankulansu yayo kanta,nanay ta tashi itama daga mazauninta ta iso gaban akhnan din tana qoqarin riqeta,saidai kuma me abun ya rigata,tuni haisam ya sanyata a jikinsa yana jin yadda jikinta dukka ke girgiza saboda qarfin aman.
Damuwarta na yadda zata kauce masa ne kada ta batashi. Tanata qoqarin kauce masa amma sake sakata yakeyi a jikinsa yana tare aman.
"Sannu.....I'm sorry" Shine kawai abinda yake fadi. Ya rikice gaba daya saboda ganin yadda farar fuskarta ta soma zama jajaja saboda azabar yunqurin.
Matsanancin bugawar da zuciyarta keyi,da tashin da hankalinta yayi na fahimtar abinda akhnan ke dauke dashi yafi komai daga mata hankali sama da irin hukuncin da zata fuskanta daga gareshi. Ta tattara dukkan wadannan yanayin,tashin hankali da bala'e'en kishin da takeji ta cinyesu gaba daya da wani irin yanayi me rad'adi tana takowa zuwa gefansu,tana kuma amfani da dukka wani sign na tashin hankali da takeji tana juyeshi akam dukka damuwa da yanayin akhnan ne.
Aareef noorah rumaisa da Aanani dukkaninsu sunyi carko carko daga gefanta. Har zuwa sanda ta kammala aman.
Sannu kawai nanay ke jera mata,kamar ta sauke ciwon daga kanta ta dawo dashi mata jikin. Ta kasa tantance cikin biyun wanne zatayi?. Jimamin wahalar da akhnan din tasha yanzu?,ko kuma murnar qara samun tabbatuwar zarginta?. Tana hango fuskar motii ne kawai,yadda zaiji da wannan albishir din. Tanaso ta zama ta farko da zata fara gaya masa wannan kafin kowa ya fadi masa.
Idanunta akan haisam,yadda hankalinsa ke a jagule sanda rumaisa ta kawo roba yana gyarawa akhnan jikinta.
Matsowa saamee tayi,cikin wannan kulawar da qarqashinta abubuwa ne masu yawa tana miqa hannu zata karba robar da aka kawowa haisam din.
"Bari na qarasa mata obbo....kaje ka gyara jikinka". Sau daya tak! Ya daga kai ya aje mata wani irin kallo,take taji dukka 'ya'yan hanjinta sun girgiza. Ta rufawa kanta asiri a hankali ta taka tana ja baya ta basu sararin gurin.
Tas ya gyara mata jikinta,ya zare tasa cloak throbe din da ita kadai ta baci ya miqawa rumaisa dukka ya tattara ta fita dasu don bawa hadimai su gyara.
Shi ya riqeta da kyau sanda take maida numfashi suna sauka zuwa parlor suna barin dining area din da tuni bayi sun fara aikin tsaftaceshi.
Nanay na biye dasu,banda jera mata sannu ba abinda takeyi,har ya zaunar da ita saman sofa,ya tsaya daga gefanta yana ware hannun jubah dinsa daya nade a dazun.
"Wata nawa ne?" Nanay dake zaune dab da akhnan din ta fada bayan ta gama qarewa faratanta da tafin hannunta kallo.
Dif sukayi ita da haisam din,sai kuma ya juya a hankali yana duban akhnan din. Itama shi take kalla,don bata fahimci komai a maganan nanay ba.
Kamar ta tamabayeta,sai kuma haka kawai taji nauyin tambayar nanay din me take tambaya?.
"La'ilaha ilallahu muhammadurrasulillahi.....muhammad nace wata nawa ne?,kada dai kacemin bakasan komai akai ba ballantana watanninsa?,yawo kawai kuka dinga yi baka kaita an duba lafiyarta ba?" Nanay ta fada tana tafa hannu sannan ta kama haba idanunta akan haisam din da yayi tsaye ya rasa ma daga inda zai debowa nanay bayanin. Kunyarta da nauyin ta kuma suna sake danneshi,uwa uba kuma shi baisan me yadda akhnan din kanta zata fahimta ba.
Idanun nasa ya janye a hankali,ya sake maidawa ga akhnan yana jin wani nauyi yana sake nutsar dashi yana jin nanay naci gaba da mita.
"Nace wata nawa ne muhammad?" Ta sake tambayarsa. Kamar ayau an cire mata duk wani shamaki tsakaninta dashi.
"Banda sakalci,ka sakata a gaba kuna yawonku abinku,baka damu da sanin lafiyarta ba?. In banda zamani ina ake haka?"
Wannan karon dariya ce ta kusa kubucewa daga bakin haisam,saboda gaba daya wadda ake maganar a kanta ma tana zaune tana kallonsu cikin mamaki,kamar ba a kanta ita ake magana ba.
Akhnan ta waiga daga nanay zuwa Haisam,sai kuma ta saukar da kanta qasa tunaninta yana kullewa.
"Zan sake tambayarka a karo na qarshe" Ta fada fuskarta na nuna serious.
Yanzu kam dariyar gaba daya ta mutu a fuskar haisam. Ya zauna sosai cikin kujera. Kamar dalibin da malaminsa ya tsare.
"Ban sani ba.....Allah ban sani ba nanay" Yayi maganar yana lumshe idanunsa gami da budesu lokaci guda.
Tunda yake bai taba ganin abinda nanay ta yiwa serious haka ba. Fada takeyi da gaske,har sai daya koma a hankali ya zauna.
"Nanay" Ya kira sunanta a tausahe. Harara ta balla masa.
"Me?" Kaman zaiyi dariya amma ya danne,zaiso yaga yadda zata ganar da akhnan abinda yake tare da ita.
"Ba laifi na bane...."
"To na waye?" Ta tari numfashinsa hannunta cikin na akhnan din. Ya zare hannunsa daga kan hannuwansu dake harde,ta riqeta sosai kamar wanda ya yiwa akhnan din wani mummunan abu.
"Itace...."
"Ni?" Akhnan ta tambaya cike da mamaki tana fidda idanu. Me tayi yau haka da haisam ya zabi bayyana laifinta da kuskurenta qarara?. Kaman ba shine ke bata kariya a dukkan muhalli ko gurbi ba?.
"Eh ke..taqi yarda.....taqi fahimtar abinda ke faruwa da jikinta". Idanu sosai akhnan ta sake fiddawa,kafin kuma a hankali su koma daidai saboda ruwan hawayen da suka tara na karyewar zuciya.
Shuru ya ratsa dakin,kowa da abinda yake kai kawo cikin ransa.
A hankali nanay ta sauke kallonta kan akhnan. Ba mamaki bane.....kowacce mace takan tafka nata kalan shirmen da quruciyar yayin cikin fari. Wani abune da kusan yake shammatar kowacce mace,don haka nata kalan shirmen cikin fari kenan. Yadda tayi tsuru tsuru kama me laifi ya sanya nanay kusan sakin murmushi,amma saita maze,ta maida dubanta ga haisam.
"Bamu guri.....zamuyi magana" Tsam ya miqe ba tare daya musa ba. Hakan ya masa,qilan tunda nanay ce ta tsaya ta saurara ta kuma fahimta. Shima ta rage masa aiki,amma yadda yasan ta koyi rikici da rigima a kwanakin nan tabbas yau saidai ya shiryawa tarar kowanne rikici nata.
Yana sanya qafarsa waje ya tuna abinda saamee tayi dazu,take dan annurin fuskarsa ya bace,ya kuma sauya akalarsa daga sitting room da yayi niyyar zama ya jirasu,ya nufi hanyar dakunan baccinsu.
Da farko sanda saqon kiran ya iski saame ta tsorata,ta fara hasashen girman laifin abinda tayi da hukuncinta. Sanannen abu ba,ba wanda zai taso cikin gidan yace baya gane umarni daga gurin yarima haisam,da idanu kawai ba tare da aiki ko magana ba. Ya mata maganan.....amma son gane komai ya sanyata batayi aiki da ita ba,wanda wannan kawai laifi ne me zaman kansa.
To amma a hankali sai taji tsoron yana gushewa sanda aka gaya mata shi daya ne,a wani qaramin guri da sukan zauna susha iska.
Samun kanta tayi da matsawa ta qara turare,ta sauya hijabin jikinta da mayafi yalwatacce. Ko ba komai.....koda fada zaiyi mata,zataso ya ganta da kyawun nan nata.
Duk wani confidence data dauko ya kwaranye sanda ta soma hangen bayansa. Yana tsaye ya bada baya,amma gaba daya kwarjininsa ya cika gurin,kamar yadda qamshinsa ke sauya yanayin gurin da wani irin yanayi me dadin gaske.
Ta qarasa bayansa ta tsaya tana sallama kanta a qasa. Kamar baiji ba,sai daya dauki wasu sakanni sannan ya amsa qasa qasa,ya taka ba tare daya waiwayo ba ya isa ga wata kujera dake gabansa kadan ya zauna.
Idanunsa ya sauke a kanta a hankali. Karon farko yana jin haushin sonshi da takeyi gaba daya. Besan me yasa ta gaza ganewa ba,baisan me yasa bata fahimci yafi son ya farauci zuciyar da ba ita ta kawo kanta ba.
"Saamee" Ya kirata,sunan da muryar suka tsarga mata.
"Na'am"
"Kinsan hukuncin watsar da umarnin cikin gidan nan....." Ya fada kai tsaye kaman me bata amsar tambayarta bame tambaya ba.
"B....ban..." Ta fara yunqurin yin magana.
"Banyi tunanin....." Ta sake yunqurin fada amma sai ta kasa qarasawa sanda ta tuna ba'ayi masa qarya.
"To ki fara tunani daga yau" Ya furta da wannan nutsuwar tasa da kwarjinin nan dake bugarta.
Tadan daga kanta sannan ta sauke,ta san muryar nan. Muryar da haisam ke amfani da ita idan haqurinsa ya qare.
"Akwai abu daya da nakeso ki fahimta" Ya fada yana dakatawa.
"Kin taso a gidan nan."
"Nanay ta raina ki."
"An ba ki mutunci." Sai ya tsaya.
"Kuma saboda mutuncin nan ne nake magana da ke cikin girmamawa." Zuciyarta taji ta buga da kalmar girmamawar daya ambata. Amma kalmar da ta biyo baya...ita ce ta karya duk wani fata da ya rage mata.
"Daga yau." Ya fada a sarari.
"Idan ni da matata muna wani wuri..."
"Ki bamu guri"
"Me yake nufi?" Ta tambayi kanta da wani irin nauyi da tashin hankali daya saukar mata. Kaman yasan abinda take tambayar kanta din yace.
"Ina nufin....duk inda muka zauna,kibar wajen". Idanunta ta lumshe tana jin tashin hankali. Ta fahimci abinda yakeyi,yana rufe qofa ne. Don wajibi ne dole ne akan kowa cikin masarautar biyayya ga umarninsa muddin yana son ci gaba da zama. Ya rufe ya kulle mata duka sauran wata qofa da take da fata a kanta.
"Kada ki sake shiga tsakanin zamanmu.....kada ki sake kawo wani abu a zamanmu.....kada ki kula da komai daya shafemu a irin wannan zaman...musamman ita,ni zan kula da ita"
Hawaye ne suka zubowa saamee masu wani irin dumi. Ba saboda an yi mata ihu ba. Ba saboda an wulaqanta ta ba. A'ah....saboda ta fahimci saqon sosai sama da yadda take tunanin ma zata fahimta din.
Ya koreta ta ruwan sanyi daga gurin da take da fata,ya koreta daga rayuwar gidan gaba daya a fakaice.
Sai Haisam ya qarasa da kalma daya cikin nutsuwa. Amma mai nauyin da ya isa ya rufe kowace qofa.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 145*
"Ki girmama iyakar da ke tsakanin ki da matata."
"Saboda ba zan sake maimaita wannan maganar ba."
"In sha Allah" Ta fada muryarta tana rawa,sannan ta juya cikin tashin hankali tana komawa ciki.
A wannan karon ta fara zargin kanta. Ta yaya ta bari idanunta suka kulle har take neman zubdawa kanta mutunci da kimarta na diya mace?. Anya wannan hanyar zata bulle mata kuwa?,anya ba zata koma da baya ta maida akalar hankalinta da tunaninta inda ake nemanta ido rufe da dukkan qauna ba?.
(Nidai nace oho....nacin soyayya dai bana diya mace bane wadda tasan ciwon kanta).
*A K H N A N*
"Ciki?...nanay ni?" Ta fada da wani tsoro a muryarta tana fidda idanunta waje tana nuna kanta da yatsanta.