L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 80
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 80: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 80. Murmushi me qarfi ya qwacewa nanay,ta danyi qasa da…
3,375 words
Murmushi me qarfi ya qwacewa nanay,ta danyi qasa da kanta tana karantar tsoron cikin sosai daga idanunta. Sake matsowa kusa da ita tayi ta kuma sake kamo hannayenta tana karantar yadda take buqatar a nutsar mata da zuciya da bayanin da zata gamsu.
"Eh....ke din".
"Amma nanay.....banji ciwo ba" Tayi maganan da yanayin dake nuna sakalcinta a fili.
"Duk wanda yake da ciki sai yaji wani ciwo ne na daban?....sannan baki lura da yadda kikejin gajiya ba.....zaben abinci?,rashin son wani qamshi ko wari da sauransu?,duka wannan ba ciwo bane?" Nanay tayi maganan tana duban tsakiyar qwayar idanunta. Shuru akhnan din tayi,wani irin shuru da ya nuna zurfin nazarinta sosai.
Murmushi nanay tayi,ta miqa hannu ta shafi gefan fuskar akhnan din a nutse.
"Nima na taba zama sabuwar amarya"
"Kuma na taba daukar ciki" Ta fada tana murmushi,maganan ta yiwa akhnan nauyi da yawa,tayi qasa da kanta tana jin kamar zata narke. Ashe dai duk yadda ta dauki nanay a matsayin uwa....akwai wani abu da ba lallai ya sauya ba. Surukuta.....bata sauyawa,koda wannan matar zata uwa gareka.
"Uwa tana gane wasu abubuwa kafin a gaya mata."
"Mijinki....akhnan,akwai wata boyayyar soyayyar da yake miki wadda ni kaina basan da ita ba. Tunda muka zauna a nan idanunsa yana kanki sau ba adadi.....yana kula da dukka motsinki,shi kansa jikinsa ya fara sanin abin da ke tare da ke kafin hankalinsa ya gane." Kunya ta sake narkar da ita,ta sakeyin qasa da kanta sosai.
"Akhnan" Nanay ta kira sunanta a tausashe.
"Allah ya baki wata ni'ima me girma"Hawayen farin ciki suka fara taruwa a idanun Nanay.
"Zaki zama uwa idan Allah yaso"
"Ni kuma zan zama kaka" Ta qarasa fadan maganan da wani feeling sosai cikin ranta tana jin kamar ta hadiye akhnan.
A wannan karon akhnan ta sauke idanunta kan cikinta. Har yanzu tana jin abun kamar almara,kamar zuciyarta na gaya mata ba zata yarda gaba daya ba. Amma wani abu a zuciyarta ya fara canzawa. A hankali.....A hankali. Kamar tana fara fahimtar cewa rayuwarta ta shiga sabon babi ne.
Wani irin farinciki ya mamaye zuciyar haisam dake tsaye a bakin qofa yana kallonsu,yana kallon komai,sai ya sauke hannuwansa qasa a hankali yana jin shima qwalla tana cika masa idanuwa.
Baisan girman karamci irin na Allah iya adadinsa ba. Banda shi.....ba wanda zai maka haka. Ya maka baiwa ya sake qara maka da wata.
★★Wani hukunci ta yankewa kanta na koyon komai da komai a sanda duka haisam baya kusa. Cikin awannin da tasan zaije ya dawo. Ta yanke hukuncin zama cikakkiyar matar auren da zata bawa miji kulawa,ta kuma kula da yaran da zata haifa a gaba.
Ko kusa ko alama bata bari yasan da wannan shirin ba. A hankali kuma a boye take koyon komai. Saboda a yanzun....ta sani bata da komai....bata da wani abu da zata bawa haisam bayan wannan kulawar,bayan ta iya komai da yakeso yake kuma buqata.
Ta sani.....babban kuskure take aikatawa,saboda yadda haisam din idan yana gida koda daukan cup baya barinta tayi,hakanan idan zai fita sai ya tabbatar da dukka hadimanta biyar dinnan dama baba hannatou daya dauko mata ita daga Niamey tana kusa da ita.
Tunda take....ko a tarihi bata taba ji ko ganin inda ake lelen ciki irin nata ba. Ta sani tabbas banda tsaurara tsaro akan fitar maganan cikin da haisam ya yanke ya zama abune daya faru cikin sirri saboda sharrin ido da baki.....tayi imani da yanzun haka anacan ana shagali na kwana da kwanaki akan cikin.
Don gaba daya sunyo kabbara akansa. Tsakanin nanay motii dasu oga Anaani batasan waye yafi qaunar wannan d'an tayin dake kwance a mararta ba. A cire ta oga kwata kwata haisam.....nashi abun baya da misali dana kowa a cikin su,don tabbas inda yana da hali,daidai da numfashi ma cewa zaiyi zaiyi mata shi.
Batasan tana da kunya har haka ba.....sai sanda morsa safiyya ta kirata tana mata sannu da jiki. A maganganun morsa safiyya ta tabbatar nanay ba zata iya boye wannan farincikin ba....ba zata iya qin gayawa 'yar uwarta ba. Sanda sultane ya kirata zai mata sannu da jiki a wani lokaci da jikinta yayi weak,haisam ya dage lallai sai an saka mata drip saboda tafijin qwarin jikinta,kashe wayar tayi. Kunya ta dinga ji,ba zata iya magana da sultane ba,bayan ya fita sanin komai da akayi aka samu cikin.
Ta dora idanunta akan haisam dake zaune a gefanta yana yanka mata fruit,sai ya dage mata girarsa dukka biyun,daya daga cikin alamun tsokanarsa kenan idan yaso.
"Bakaji kunya ba?" Ta tambaya da muryarta da tayi laushi saboda wahalar da tasha jiya.
"Name?" Ya fadi yana kashe mata ido daya.
"Haisammm mana" Ta fada a karye.
"Wash Allah na" Ya fadi shima yana lumshe idanunsa gami da dora tafin hannunsa a qirjinsa.
"Har yau.....ba abinda ya canza....har yau ina bala'in son naji sunana abakinki" Yana sauke maganan yana jifansa da pillow. Saurin fushinta ya motsa,wani abu ya tsaye mata a wuya. Haisam ya rainata,ta lura kallon yarinya qarama cancan yake mata. Idan tana magana serious shikam bai taba bata muhimmanci ba.
"Bakajin kunyar bappi na.....kasan me kayimin na samu ciki,amma har zaka iya gaya masa ina da cikin?" Ta fada hawaye na silmiyo mata.
Dariya taso qwace masa,amma yasan bai isa yinta a wannan lokacin ba. Maganan gaskiya ya rasa wanne kalan sakalci yake damun akhnan din.
Ita ba 'yar fari ba....ita ba auta ba. Duk da wani bangaren ana iya kiranta da auta din,tunda itace ta qarshe a wajen mamminta. Komai ya ajiye ya isa inda take,ya tsugunna saman qafafunsa yahau aikin lallashi da share mata hawaye. Saboda ya sani......indai nanay tazo ta samesu a hakan....bame qwatarsa sai Allah. Laifin duniya duka nasa ne.
Nanay.....ba wai tana son akhnan bane kawai. A'a....yanzu tana kallonta ne da idanun uwa.....suruka....kuma mahaifiyar babban jikanta na farko.
Akhnan ta fara jin kamar Nanay tana zaune ne a gidansu,saboda kullum sai ta kira. Safe.....rana....dare.
"Kinci abinci?" "Me kika ci?" "Me yake damunki?" "Me kikeso yanzu?" "Ina fata haisam bai takuraki ba" "Akwai abinda kike buqata?" "Me kikeyi yanzu?" "Qarfe nawa kikayi bacci?" "Basu katse miki bacci ba ko?"
Wadannan tambayoyin dama tarin wasu ya sanya haisam ke kame kansa kafin sunanshi ya shigo list na 'yan tuhuma.
Shi kansa bai tsira ba,wani lokaci shi take kira ba akhnan ba. Akwai randa yayi wani mistake ranar ya gane a yanzun baida wata faada a gurin nanay. Akhnan da abinda ke cikinta sun karbe gurbin.
"Muhammad" Yana tsaka da aiki a sannan a office dinsa dake jimma.
"Na'am nanay"
"Taci?"
"Me taci?" Ya tambaya saboda kanshi ya buga da tarin gyare gyare da sukeyi a kamfani,da kuma settling ayyukan akhnan na sahel couture dana maison akhnan daya hadawa kansa gaba daya.
"Dama na sani....baka tambayeta ba....anya muhammad kana kula da ita yadda ya dace kuwa?"
"Nanay...." Ya kirata don bada uzuri amma ta katseshi.
"Ka kirani idan ka isa gida" Sai ta katse wayar abinta.
"...I failed an inspection." Ya fadi a fili yana dafe kanshi.
Bayan kwana biyu kuma sai ga motoci sun iso gidan cike da kayan abinci.
Fresh fruits,honey da traditional foods da yawanci masu juna biyu suke ci. Komai carefully selected,kana kalla kasan da takatsantsan aka shirya komai.
Da kanta ta sauko ta duba cartons din cikin mamaki.
"Waye ya turo wannan?"
Birra tayi murmushi tana dubanta.
"Nanay." Sai Akhnan ta dafe goshinta tana dariya.
Jiya suka gama wannan case din da haisam. Yanata complain. Duk kulawar da yake bata shi ya lura ma kamar nanay ta rainata. Kamar ma baya yin komai,yau ga aiken kayan abinci da fruit bayan duka stores dinsu na gidan ba wanda ba ajiyayyen kayan abincin da zai shekara biyu su da dukka hadiman gidan suna amfani dashi komai yawansu.
"Allah ya barmin nanay na" Ta fada tana murmushi,ta sake matsawa tana kuma buda kwalayen.
Har ma da notes,small notes a takaddan da handwriting din nanay dake nuna rubutunta ne.
"Ki ci wannan da safe."
"Kar ki bari yunwa ta same ki."
"Ki huta sosai.". Saita dauki takardar a hannunta tana komawa ciki da ita.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 146*
★Da wani yammaci.....daya daga cikin yammacin da haisam yake addis ababa. Yaje can headquarter dinsu zaiyi supervision na wani aiki da aka tura wasu daga nan office dinsu under na'urorin da suke communicating.
Yawanci idan zaije addis ababa din ta private jet yake tafiya ya kuma dawo,baya ma shiga kuma sai idan wani abu ya taso,don haka duka duka awanni uku zuwa hudu yakeyi.
Yaso yaje da akhnan din.....amma baisan ya akayi yayi subutar baki yana sallama da nanay din tace kul kada ya soma daukar mata diya,shi din dai sai ya dawo.
Hakanan ya haqura din,amma duk bayan wasu mintuna sai taga kiranshi ko tex dinsa.
Tashinta a bacci kenan da yammacin,tayi sallah ta sake watsa ruwa saboda yanzun wani irin jin zafi ne da ita. Ta shirya cikin wata cotton gown data sauke har qasa ta rufe mata qafafunta. Wani material ne olive green me taushi da rashin nauyi. Ta kame gashinta da wani band,hakan ya bawa gashin nata daman sauka a gadon bayan ta yana lilo. Dan matashin cikinta daya soma bayyana tun a wata uku ya dago rigar kadan. Tayi wani irin kyau irin na masu farkon shigar ciki.
Ta sauko downstairs da wayarta a hannu tana murmushi bayan ta gama duba saqon haisam.
"Giiftii.....my princess.....bana gane aikin nan sam....anya bazan musu shirme ba?,the silent one bazai samu suspension ba kuwa?,nanay taqi fahimta.....ke aljihuna ce....na gaba gaba" Maganan ya sakata dariya da nishadi sosai,da wannan a fuskarta ta qarasa saukowa.
Buhaina da bushira ne kawai a parlour din,suna turareshi da sassanyan qamshin nan na shuwa incense and more,daya daga cikin qamshin da har yanzu bata daina so ba.....basa damunta kuma (+234 704 229 3387 tasted and trusted,zaki godemin sosai).
Da girmamawar nan da qauna dake tsakaninsu da uwar dakin nasu suke mata barka da saukowa. Ta amsa musu itama da kulawa. A ranta tana jin kamar lokaci yayi da suma ya dace ta aurar dasu,koda kuwa zasuci gaba da rayuwa da ita ne.
"Nanay tazo" Buhaina ta fada da murmushi,don suna matuqar son zuwan matar gidan. Badai mutunci da karamci ba. Da dan mamaki ta daga idanunta daga amsar da take kan bawa haisam din idanunta a waje.
"Yaushe?,tana ina?"
"Yanzu ne,bata jima na,tana kitchen"
"Kitchen kuma?" Ta tambaya da mamaki,sai kawai ta fara takawa da kanta zuwa kitchen din ba tare data jirasu ba.
Tun daga nesa ta hangota cikin cook ma gidan tana duba abinda ake dafawa.
"Me yasa suka saka spice haka?" Ta fadi tana d'an d'ana wani fried chicken da suka kammala.
Cook din ta tsaya cak tana rusunawa.
"Ban dauka ba'a buqatarsa ba ranki ya dade" Kai nanay ta girgiza
"Kunsan ba ita kadai bace.....ba za ku dafa kamar yadda kuka saba ba,a daina using nashi kwata kwata,yayi strong da yawa" Ta qarasa maganan cikin jikinta kamar tana jin isowar akhnan ta maida idanunta can.
Ajiye abun hannunta tayi ta tako tana marabtar akhnan din. Cikin kunya ta zame mata shirin gaidata amma saita rungumeta tana tambayar lafiyarta.
Tare suka baro kitchen din,nanay na mata tambayoyi game da lafiyarta. Sai data duba komai nata,tare suka zauna zaman cin abinci,wanda sai da suka zauna din sannan taji qarar da wayarta takeyi. Koda ta duba haisam ne. Ya tara mata messages da miscal saboda jinta shuru suna tsaka da magana,sai kawai tabi kiran.
Bugu daya ya dauka kaman daman jiran kiran yake daga gareta.
"I can't wait my princess,on my way,nan da fifty minutes zan qaraso" Tadan fidda idanunta tana mamaki,kafin ta sauke wayar sanda ta jishi ya yanke kiran.
Ga mamakinta,adadin wadannan mintunan su ya dauka taji shigowarsa shida guard dinsa. Ta lumshe ido a hankali sannan ta bude tana jin kamar wani sashe na jikinta ke dawowa gareta.
Sanda ya shigo nanay ta tayar da sallah bata parlor din. Ya bude hannayensa yana dubanta gami da jiran isowarta jikinsa kamar yadda suka saba. Sai ta noqe kafada,wannan ya sanyashi jefo qafafunsa da sassarfa yana fadin.
"Ba lokaci my princess......bazan iya jiran wannan jan ajin naki ba yau" Ya qaraso kusa da ita ya sanya dukka hannayensa yana shirin dagata
"Nanay" Ta fada da sauri tana zaro idanu waje,daidai sanda nanay din ke fitowa,sai yaja da baya yana shafa sassalkar sumarsa idanunsa a qasa.
Da wannan dabi'artata ta ta gani amma kaman bata gani ba ta zauna. Ya zauna qasanta yana gaidata cike da kulawa.
Su danyi hira kadan kafin ya miqe yana duban akhnan din.
"Ku jirani na fito sai muci abincin tare nanay idan ba damuwa" Ya fada idanunsa akan akhnan.
"Na kusa tafiya....amma idan baka zauna ba zaka sameni" Ta fadi tana duban agogon hannunta.
"Okay.....yanzun in sha Allah" Ya fadi idanunsa da fatansa dukka akan akhnan. So yake ta taso.....so yake ta biyoshi. Yanason yaji dumin jikinta,yana so ya aza hannunsa saman cikinta yaji tudin ajiyarsa. Yanaso ya shanshanata,ya shanshana qamshin nan nata. Yayi missing nata ba dan kadan ba.....yayi kewarta kaman ya dauki wasu kwanaki ba tare da ita ba. Amma har ya soma takawa zuwa ciki akhnan batayi niyyar wannan ba.
Koda ya shiga dakin sai ya kasa komai,ya cire socks dinsa da cufflinks dinsa,amma duka sai ya jefar. Yaji sam bashi da wani energy. Ya tako a hankali yana komawa bakin qofar dakin ya bude a hankali ya tsaya ta inda zai iya ganinta. Hankalinta kwance a gaban nanay,ya saki qofar ya koma da baya yana sauke numfashi. Daga ita har nanay kaman suna mantawa dashi idan suna tare,ya rasa wanne irin wariyar launin fata suke masa haka.
Sake takawa yayi ya koma bakin qofar,wannan karon kai tsaye ya kirata.
"Akhnan"
"Na'am" Ta amsa tana waiwayowa,suka hada idanu amma sai ta basar. Duk da tana jin kewarsa itama,duk da tanason zuwa gareshi,amma kunyar nanay takeji
"Ina kika ajiyemin kayan nan da na bari a gefan bedside" Da farko ta shiga tunanin wadanne kaya?,amma daga bisani data dago maganan da kuma yadda ya zuba mata ido sai dariya ta kusa zuwar mata.
"Suna inda ka ajiye....."
"Giiftii" Nanay ta kira sunanta.
"Na'am"
"Tashi kije gurin mijinki" Ta fada a nutse don ta fahimci komai ita. Sai data dan dakata kadan,sannan ta miqe a kunyace tana takawa zuwa dakin.
"Ki kula da kanki" Nanay ta fada a hankali,kalmar data saka akhnan ta kusa nutsewa a gurin.
Tasan yana kusa....amma bata dauka yana kusa da qofa haka ba,sai ji tayi ya jawota a tausashe cikin jikinsa.
Juyo da ita yayi suna fuskantar juna,idanunsa sunyi wani irin laushi cakude da gajiya da wani irin shauqinta da kewarta. Ya motsa labbansa a hankali da zummar yin magana.....amma saita hana masa wannan damar ta hanyar hade bakunansu guri daya.
Wani irin fitinannen kiss take ajiye masa wanda ya qarasa cakuda hankalinsa gaba daya,ya sake ingizashi wata duniya data sanya ya gaza komai,har sai daya dauketa cancankat dinta ya maidata saman bed din.
Zazzafar maraba ya samu da wata irin tarba ta musamman data sanyashi jin kamar sannan komai yake wakana bayan kammaluwar lamarin. Baisan kowacce mace a duniya ba sai ita....a kanta ya fara sanin me ake kira da wannan abun....amma shi kansa ya tabbatar yayi imani ita din ta musamman ce. Ya sani ba shakka samun irinta cikin mata kadanne.
Tasa hannu kaman zata tsone masa idanu saboda yadda yake faman qare mata wani narkakken kallo sanda kawunansu ke saman pillow daya suna huce gajiya.
"Nanay tayi kuskuren fahimta......ina jinta tana cewa ki kula da kanki.....batasan yaronta ba,Allah sarki,yanzu ya zama salihi......diyarta ita ce fitinanniyar" Yadda yayi maganan dole ya bata dariya. Ta cusa kanta cikin pillow tana qyalqyalawa.
Ita kanta da farko abun yayita bata tsoro,har ta kaita ga yin binciken dalilan dake sawa buqatar mace ta qaru. A cikin jerin sawun taga harda pregnancy saboda sauyawar hormones,hauhawar wasu daga ciki.
"Shikenan.....yallabai yarimana ayi haquri,yanzu dai kada na takurawa ya sheikh,ya kamata na tafi hutu koda na sati biyu ne....."
"Wallahi baki isa ba...." Ya furta yana cafkota sanda take qoqarin sauka daga gadon ba tare daya bari ta gama furta abinda zata fadi ba.
Dariya sosai ta saki,saboda yadda yayi wata sufa yana kamota. Sai shima daga baya abun ya sanyashi sakin tattausan murmushi me qaramin sauti.
"Wannan tsarin shine daidai na.....ta yaya zakimin qauro?" Ya fada yana matseta cikin jikinsa.
*_BAYAN WATA BIYAR_*💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 147*
Sannu a hankali kwanaki ke juyawa suka bada wadannan watannin. Watannin da suka maida cikin akhnan ya zamana wata takwas daidai da wasu 'yan kwanaki.
Cikin 'yan biyu ne kaman yadda scanning ya nuna musu,amma yayi wani irin girma daya sanya haisam ya sake maidawa gami da tattara dukka hankalinsa a kanta.
Komai kusan da wahala yake zuwa mata.....amma duk da wannan wahalar abubuwan sai suke juye mata da sauqi saboda kasancewar jajirtaccen namiji a gefanta. Uwa uba kuma taimakon amintattunta irinsu birra,wanda numfashi ne kawai basu da ikon suyi mata,amma komai da take buqata saidai idan bata nuna hakan ba.
Yayin da cikin ke qara girma wata bayan wata,cikin zuciyar Haisam ma wani abu ke sake canzawa.
Ba soyayyarsa ga Akhnan ce kawai ke qaruwa ba......Aah,wani irin girmamawa yake mata ta musamman. Tattalinta da tattalin dukka al'amuranta.
Musamman da aka wayi gari akhnan din ta zama cikakkiyar mace a gareshi.
Bata damu da nauyin da take dauke dashi ba......bata damu da irin matsayin da Allah ya bata ba. Bata kuma damu da gidan data fito ba.....shi MUHAMMAD HAISAM shi dinne kawai a gabanta. Ta yaya zata faranta masa?. Ta yaya zata kula dashi?. Musamman data fara fahimtar irin yawan matan da zuciyoyinsu ke yawo a kansa. Yawan matan da burinsu a ko yaushe shine yadda zasu mallakeshi da komai nasa.
Tun daga rainon cikin ta sake jin wata sabuwar soyayya da qaunar mahaifiyarta. Tun a sannan ta sake ganin kimar morsa safiyya....nanay....dama duk wata uwa da zata bude ido ta ganta rungume da yaronta.
Ta shiga wani sabon yanayi gaba daya. Wasu kwanaki tana cike da kuzari. Wasu kwanaki kuma tana gajiya da qananun lalure lalure.
Amma duk da hakan,ta zabi ta zama jarumar uwa. Ta zabi ta zama jajirtacciyar mata me tsananin kulawa da mijinta da komai daya shafeshi.
A irin wadannan lokutan haisam ya koyi abu guda daya. Biye mata da kuma lallashinta cikin kowanne yanayi.
Ta zama wata mafadaciya me saurin fushin da babu dalili,takan iya sanya masa kuka haka siddan ba tare da yasan yayi komai ba. Duk lokacin da ta ce
"Ban san me yasa nake kuka ba." Sai kawai ya jawota jikinsa.
"To ki yi kukanki.....yi kukanki yadda zaiyi miki"
"Ba ma san dalili ba fa." Takan maimaita fada wani lokaci cike da tsoron kanta da kanta na yadda komai da komai da yadda yanayinta yake sauyawa.
"Ba lallai sai kin sani ba." Zai sake amsa mata da kulawa a tausashe. Hakanan sai ya zauna yana lallashinta,tsadaddun lokutansa duka ya sarayar mata har sai ta gama.
A gefe guda kuma duk wasu harkokinsu basu fasa garawa ba. Kamfanonin su na ci gaba da bunqasa.....kasuwancin na wani irin habaka daya bawa haisam mamaki cikin watannin.
Sau daya ya taba jin wani yana fadin,wani lokaci wani arziqin silar aure Allah yake sake bude maka shi. Baisan adadin abinda ke shiga account dinsa ba kullum rana. Sabbin yarjejeniyoyi na shiga. Sabbin cinikayya na budewa.
Sau tari ana iya samun Haisam a babban conference room yana tattaunawa da manyan shugabanni. Yana yanke shawarar da zata iya motsa miliyoyin daloli.
Amma a tsakiyar meeting wayarsa zata yi haske,message daga giiftii dinsa zai shigo. Ko yaya ya fita suna tare akan waya. Tun tana cewa ya maida hankalinsa kan ayyukansa idan ya fita harma ta daina ta biye masa. Haka kawai tsakiyar meeting yana iya daukan break,kowa sai ya jira,yakan shiga rest room ya zauna ya kira takanas don yaji muryarta da lafiyan yaranshi. Yaran da tun kafin suzo duniya batasan irin soyayya da mutane da dama ke gwada musu ba.
Duk muhimmancin meeting idanunsa basa gaza sauka kan message dinta. Murmushi yakan bayyana a gefen lips dinsa.
Abin da ma'aikatansa suka daina mamaki da gani,wannan murmushin da idan ka ganshi saman fuskarsa to tabbas yana da alaqa da princess dinsa.
Su kansu yanzu sun sani......CEO dinsu ya zama mutum daban idan maganar matarsa ta shiga.