L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 81
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 81: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 81. Sannu a hankali akhnan ta fara shiga wasu daga cikin…
3,370 words
Sannu a hankali akhnan ta fara shiga wasu daga cikin ayyukan kamfanoninsu daga gida. Ba wani dogon stress ko aiki me wahala ba. Saboda Haisam ya hana ta wahala sam sam.
Tana bibiyar reports,tana ba da ra'ayinta akan abubuwan da suka shafi gudanarwa,tana shiga online meetings idan tana da kuzari.
Da wani yammaci suna zaune a library na gidansu.
Takardu ne a gaban haisam,akhnan kuma laptop.
Yayi nisa qwarai cikin lissafin ribar da sahel couture ke kawowa,wata irin riba me ban mamaki cikin watanni kadan da ci gaba da gudanar da kamfanin wanda akhnan ke jagoranta daga gida.
Da tare suke aikin,sai yace ya bata break,ta zauna tayi relax kawai na wasu mintuna. Sai data huta sannan ya kalleta.
"Time up" Ya fadi yana dubanta,sai ta dage girarta tana murmushi. Sai da yaga taci gaba sannan ya maida hankalinsa ga takardun da yake lissafin.
Haka kawai cikin jikinsa yakejin idanunta,sai ya dago kai a nutse yana dubanta. Tarar da ita yayi ba ta aikin,ba kuma karatu takeyi ba. Bata komai,kawai ta tattara dukka idanunta da nutsuwarta a kansa,kallonsa kawai take yi,zara zaran eyelashes dinsa dake motsawa a hankali saman takardun suna sake sanyawa tanaji yana sake burgeta.
"Me?" Ya tambaya a hankali.
"Nothing." Ta fadi murmushi yana subuce mata a hankali
"Akhnan." Ya kirata da sautin dake nuni da kada ki sake kiyimin qarya.
"Ina tunanin..." Ta yi murmushi.
"...yadda yaranmu zasu yi." Sai ya tsaya cak,takardun da ke hannunsa suka rasa muhimmanci na dan lokaci.
Ajjiyesu yayi a hankali yana fuskantar inda maganarta ta dosa.
"Akhnan" Ya sake kiranta a tausashe.
"Kina tunanin......inda za'a bani zabin qwace komai dana mallaka.....a barmin ke da yaran da zaki haifamin.....bazan zabi zama matalauci daya mallaki kyakkyawar gimbiya da yaran da suka haifa ba?" Maganan ta sauka a zuciyarta da kunnenta da wani irin laushi daya tilasta mata lumshe idanunta gami da budesu.
"Naji tsoro....." Ya bude idanunsa duka yana dubanta.
"Naji tsoro sanda na fahimci zuciyata ta fara sonka a sanda kai ko kallo ban isheka ba. Naji tsoro sanda na fahimci na fada tarkon qaunarka. Naji tsoron rasa kimata.....darajata da martabata. Ashe abinda ban sani ba,wannan soyayyar....wannan son shine silar da zai fidda rayuwata daga duhu zuwa haske.....wannan son shine zai mallaka min LU'U LU'UN dake gabana.....LU'U LU'UN da nake shirin tattakeshi da qafata ba tare dana gane shi bane". Ta cikin idanunta kadai ya fahimci dukkanin gaskiyarta. Ta cikin idanunta kawai ya fahimci gaskiyarta kenan take fada daga zuciyarta. Sai kawai ya ture kujerarsa baya,ya miqe a hankali yana takowa.
Idanu ta fidda kadan murmushi yana subuce mata.
"Me?,ina zaka?" Ta tambaya tana sake fidda blue eyes dinnan nata da suka sake girma.
"I've missed your warmth..." Ya furta a hankali yayin da ya yi mata rumfa da hannayensa a saman kujerar da take zaune. Idanunsa suka sauka kan nata da wani irin yanayi me sanyi.
"Let me stay here for a moment." Ya fada sanda yake mata rumfa saman kujerar da take zaune akai.
"Haisammm" Ta fada da wannan yanayin da yakeso.
"Akhnan" Shima ya furta da wata sirrintacciyar murya yana sake hade tazarar dake tsakaninsu.
"Aikin....." Bai bari ta qarasa ba,ya toshe mata bakinta da nasa.
★Watanni sun yi nisa. Cikin Akhnan ya kai girman da ko juyawa a bacci sai ta yi tunani kafin ta motsa.
Wani yanayin da ita kanta yake bata tsoro,saidai tana dannewa ne kawai saboda yadda hankalin haisam gaba daya ya tattara a kanta.
Karfe biyu na dare,gidan gaba daya ya yi shiru. Wani irin shuru me nutsuwa. Ba abinda kake ji sai sautin motsin security da suke kwana aikinsu cikin gidan kafin safiya wasu su canjesu.
A hankali ta farka. Wani irin yunwa ce ta tashe ta daga baccin daya dauketa tun dazu,batasan ma ya akayi haisam ya maidota daki ba. Wani irin nauyin bacci takeyi,ta kwanta da wayarta a hannu tana lissafa EDD dinta. Sati shida ne ya mata saura a yadda scanning da calendar yake nuna mata.
Ta yunqura tayi qoqarin tashi ba tare da ta tashi haisam ba.
A hankali ta zame daga jikinsa,bataso ta farkar dashi,bataso ta hanashi baccinsa,saboda yini yake yana ayyuka biyu. Tata hidimar,da kuma hidimar kamfani. Duk da wani lokaci yana rikida ya koma dan binciken sirri boyayyen aikinsa da duniya batasan dashi ba.
Saidai amma kafin qafarta ta taba qasa,muryarsa ta fito daga dim light din dakin.
"Ina za ki?" Tadan firgita kadan,saboda yadda tayi takatsantsan gurin tashi batayi zaton zai ji barinta jikinsa haka da wuri ba. Ta yi rolling eyes dinta tana sauke numfashi a hankali.
"Ina jin yunwa." Maganan ta sanya ya bude idanunsa gaba daya a hankali. Sai yaji kaman shine sila. A dazun sai data tabbatar ta gama kaishi duniyar da yakeso kafin su koma parlor inda a nan bacci ya dauketa,sai shine ya dauketa cancakat ita da cikin,yana takawa da takatsantsan saboda yadda ta ninka nauyinta. Sai a sannan ya sake kallonta da kyau,tausayinta yana ratsashi a hankali. Cikin bai mata muni ba.....amma kuma komai na halittarta ya canza. Ya sani,tana jin jiki koda bata fada ba,tsabar juriya ce irin tata da bai taba zata tana da ita ba,musamman idan ya tuna first night dinsu,sai gashi tana shirin bashi mamaki.
Wannan ya sanya yayi booking medical team qasa uku,duk inda ta fada kota kama zasuje. Bai gaya mata Cs bane,saboda bayaso hankalinta ya daga kafin lokacin. Baya so hankalinta ya tashi ko kadan,ko a jiya da sukayi waya da likitocin yana jiran date ne kawai na randa zasu cire mata cikin. Yanaso ya ganta ta huta hakanan,yanaso ta koma akhnan dinnan daya sani.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 148*
Bude idanunsa yayi gaba daya a wannan karon.
"Yanzu kika fara jin yunwar?"
"Eh." Ta amsa masa a shagwabe.
"Karfe biyu na dare,me yasa baki tasheni ba?" Ya fada yana miqewa zaune sanye da fari qal din wandon pyjamas
"Ni ba agogo ya tashe ni ba." Ta fada tana narai narai da idanu ta cikin hasken fitilar daya kunna ta gefan gado. Sai ya yi dariya kadan,ya kama kumatunta ya danja a tausashe
"Me kike so acici?" Ya tambayeta
"Ban sani ba." Ta fada qwallar nason gangaro mata.
"Wonderful." Ya fadi yana sanya yatsansa ya dauke mata qwallar kafin takai ga zubowa. Lips dinsa ya dora saman goshinta,yayi kissing nata softly,sai yaci gaba da barin lips din nasa saman nan yana sauke mata lallausan numfashinsa a nutse saman goshinta.
Wani irin nutsuwa hakan ya saukar mata,bai janye ba sai daya tabbatar zuciyarta ta sassauta.
"I'm sorry.....kiyi haquri,Allah yana tare dake,kowacce rana qwaya daya tal tarin lada kike samu,double lada saboda yara biyu ne a jikinki.....ke din 'yar aljanna ce in sha Allah". Maganan ya sake sanyawa zuciyarta tayi wani irin taushi,ya miqe ya kama hannunta a nutse yana sauko da ita daga saman gadon.
Minti goma bayan haka,akhnan na zaune a kitchen island. Blanket ne a kafadunta wanda haisam ya lulluba mata don taji dadin zaman,da kuma sanyi sanyin daren da akayi ruwa a cikinsa dake ratso kitchen din.
Haisam kuwa,wanda manyan kamfanoni ke jiransa safe,yana tsaye yana binciken fridge. Kai ba zaka ce shine wannan zakin ba.....wannan malamin.....wannan attajirin.....wannan yariman da number dinsa ke kadawa cikin manyan diyan jinin sarauta da duniya ke alfahari dasu.
"Fruit?" Ya waiwayo yana tambayarta gami da d'age girarsa sama.
"A'a." Ta fadi da shagwaba tana bubbuga qafafunta a qasa. Sai ya maida kansa ga fridge din yana ci gaba da bincikawa.
Sake waiwayowa yayi yana dubanta da fararen idanunsa.
"Yogurt?"
"A'a." Ta sake amsa masa tana maqale kafadarta.
"Soup?" Ya sake tambaya bayan ya sake bincikawa.
"A'a."
"Akhnan." Ya fada yana miqewa tsaye daga tsugunnon da yayi yana waiwayowa dukka gareta. Dariya ta fara yi,wata boyayyar dariyar da haisam yake iya ganeta nan da nan duk da boyetan da take qoqarin yi.
"Ban sani ba ne." Ta fada tana langabar da kai cikin yin kalar abun tausayi.
"Two babies woke me up for this." Ya fada da muryar tausayi shima,sai ya ci gaba da bincike cikin fridge din.
A qarshe ya fahimci ta shirya wahalar dashi ne,don haka bai sake tambaya ba ya shiga hada mata wasu abubuwa.
"Bismillah" Ya fada yana dora mata saman island din,sannan yaja kujera ya zauna opposite nata.
Yatsina fuska kadan tayi,ta saka spoon cikin bowl din.
Ta saka na farko a bakinta,ta tauna,sai ta tsaya.
"Hmm." Ya daga kansa yana dubanta sosai.
"What?"
"This." Ta nuna plate din.
"This is exactly what I wanted." Sai ya tsaya kawai yana kallonta.
"You just said you didn't know what you wanted."
"Ban sani ba sai da na gani." Ta fada tana sake kai loma bakinta hankali kwance tana lumshe idanunta.
Ya kalli ceiling kamar yana neman taimakon Allah. Sai wata irin dariya ta subuce mata,ta dara sosai har fararen jerarrun haqoranta suna fitowa reras.
Kai kawai ya girgiza,yaci gaba da kallonta tana cin abinta hankali kwance har ta kammala. Ta gyara zamanta sosai cikin dabara kaman yadda ta saba tana kallonsa.
"Sorry." Ta fada tana kama kunnuwanta.
"For what?" Ya tambaya yana dage dukka girarsa biyun.
"For waking you." Sai ya kalleta,sannan ya sauke idanunsa kan cikinta.
"If you wake me ten times a night..." Ya tsaya da wannan nutsuwar tasa.
"...and it means you and my children are okay..." Ya girgiza kai
"I'll get up all ten times." Shuru tayi,zuciyarta na narkewa,sai ya matsa kusa da ita,ya gyara mata blanket din da ke kafadarta.
"Now finish that."
"Na koshi."
"Akhnan." Ya kirata da wannan yanayin me nauyi.
"Haisam." Itama ta kirashi,kamar kowannensu iyayensa sun saka musu wannan sunan ne saboda dan uwansa. Ba gurin wanda suke jin dadin sunayen sai a bakin daya daga cikinsu.
"One more bite." Ya fada yana daga yatsansa guda daya
Sai ta yi dariya. Saboda yanzu ta gane wani abu.
Tun da cikin ya girma......ba nanay kadai suke takurawa ba....haisam ma ya shiga qungiyar kula da ita da cikakken lokacinsa.
Tana motsawa saqo yana shigowa wayarta,haisam yabi wayar da kallo sanda take dauka. Kaman zai hanata sai kuma ya qyaleya,taci abinci,yanzun nan idan 'yan rigimar suka motsa saita narke masa hannun agogo ya koma baya.
Idanunta dukka ta fidda waje tana kallon haisam bayan ta janye idanunta daga kan wayar. Tana jin kamar tayi ihu ne,amma kuma tasan dare ne.
"Falaak my prince.....falaak ta sauka......ta samu baby girl.....maleek ya zama daddy before you" Ba haihuwar bace ta burgeshi. Yadda take maganan idanunta da suka sake girma da haske a waje. Yadda excitement dinta ya nuna,sai yaji kawai yana dokin zuwan ranar da zata riqe nata babies din.
"Next week sunan falaak.....next week bikin shehnaz......aisa....rumaisa da Aanani. Yaa muhammad.....ya ahmad......the whole next week is for us". Shikam kallonta yake kawai yana zaune,ya nannade hannunsa a qirjinsa.
Mamakinta kawai yake,bata ko jin nauyin abinda ke jikinta take tunanin bukukuwa da suna. Yana jinta tun jiya take lissafa events events,wanda bayajin ko daya zai barta. Bazaima yarda da zamanta ciki wannan hayaniyar bikin ba sam sam.
"Come,let's go to bed my princess" Sai taji ya dagata cak tana tsaka da surutunta.
"Malamina.." Ta kirashi da sunan da take kiransa a wasu lokutan.
"Sleep babe" Ya fada muryarsa can qasa.
"Na sani.....amma banji kace komai ba"
"Sai da safe" Ya fada da yanayin daya tabbatar mata bacci yakeso tayi. Bata musu dashi,bata iyawa sam,sai bata sake cewa komai ba,ta maida idanunta ta kulle,har bacci yayi awon gaba da ita.
Sanda yaji tai relax sosai ya tabbatar masa bacci ne,sai ya zare jikinsa a hankali ya dauki wayarsa yana sauka zuwa parlor din qasa.
Dr farrah ya fara contacting,yasan yanzu haka tana asibitinta,ma'abociyar night duty ce,yasan zai wahala ace tayi bacci a sannan.
Sun jima sosai suna tattaunawa da ita,tayi connecting kiran da sauran teams din. A qarshe suka yanke shawarar ajiye kwanaki goma a gaba don cirewa akhnan jariran,don dukkaninsu girma da nauyin cikin yana basu mamaki,suna zuba ido suga wanne irin manyan babies haka zata haifa?. Dalilin da ya sake jan hankalinsu kenan ma wajen cire yaran,kada garin bata dama ya zame mata matsala.
Washegari kallonta kawai yake,yana jin kamar ya mata wani kuskure ko ba daidai ba. Itakam shirye shiryenta kawai takeyi. Yana jinsu sanda rumaisa tazo gurinta wadda surukuta takeyi yanzu kawai da akhnan din,duk da girma suke bawa juna sosai,saboda kowacce tana matsayin mata ga yayan daya.
★★★
*_AGADEZ & ETHIOPIA_*
Wani gagarumin shirin bikin aure ne ke motsawa tsakanin qasashen guda biyu. Bikin auren da tuntuni sati biyu kafin zuwan lokacin hotuna da short short videos na kayan auren kowacce ya karade social media. Harma wadanda ba 'yan qasashen ba suna tambayar yaushe ne bikin?,'yan wacce qasa ce da sauran su.
A yadda aka tsara....za'a faro bikin daga agadez dinne. Za'a dauro auren shehnaz da aisa,sai a daukosu a taho dasu jimma,sannan a nan a daura auren rumaisa da Anani,su karbi su shehnaz.....a basu su rumaisa da Anaani kuma.
Saukar safe prince sheikh muhammad haisam aba jifar da gimbiyarsa khadeeja sultane muhammad hammud sukayi a private jet dinsu cikin filin sauka da tashin jiragen sama dake agadez. Kai tsaye kuma motocin alfarma,cikin royal convoy dinnan nasa masu daukan hankali suka daukesu daga airport din zuwa personal home dinshi.
Narke masa idanu akhnan tayi,rabonta da agadez tunda aka kammala case din mammina. Ta qagauta taga babyn falaak,ta qagauta taga sultane....ahmad....morsa safiyya da yanzun take kallonta kamar mamminta,da wasu kamannin mammin nata da sai yanzu take ganinsu tattare da morsa din.
"Na dauka masarauta zamu wuce" Ta fada tana dubansa,don tun kafin motar ta fita daga airport ma,zuciyarta tana can. Amma lokacin da ta lura convoy din ya kama hanyar personal residence din haisam...sai taji ta kasa shuru.
Bai ma dago daga tablet din hannunsa ba ya amsa kai tsaye a taqaice
"A'a." Sai ta hade gira.
"A'a?" Ta maimaita. Sai a sannan ya dago idanunsa gare ta.
"Kin yi tafiyar sa'o'i da yawa."
"Haisam..."ta kirashi a narke.
"Akhnan." Shima ya kirata kama yadda suka saba idan akwai sabanin ra'ayi.
Sai ya gyara zamansa ya katse ta cikin nutsuwa.
"Wannan ba maganarki bane."
Ta san muryar nan,muryar da ke nufin ya riga ya yanke hukunci,sai ta jingina da kujerar motar tana hura hanci.
"Ni ban gaji ba." Wani dan murmushi ya bayyana a fuskarsa.
"Good." Ya fada kawai. Ta dan gyara zamanta.
"Ashe zamu iya zuwa kenan."
"No." Ya sake amsawa a taqaice. Halinnan ya motsa,na masu tsohon cikin da kusan haushin kowa sukeji. Ta watsa masa wani kallo me kama da harara a fakaice,shi kuwa ya ci gaba da kallon tablet dinsa kamar babu abin da ya faru.
Kaman zata saki kuka taji,batason wannan salon nasa.....wani irin salo ne da idan ya yanke abu duk tsaurin idanunka baka iya masa musu. Yana da wani irin kwarjini da badai ka kalli tsabar idonsa ka gaya masa wani abu ko ka musa masa ba.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 149*
Bayan sun isa gida haisam ya tilasta mata cin abinci da hutawa,har sai da ta yi bacci na awa uku.
Tana ta farkawa kuwa toilet kawai ta shiga ta wanke fuskarta,ta bulla wani daki ta dauki ruww,bata ma kammala shanyewa ba ta soma lalubensa.
Ta same shi a office din nan nasa na cikin gida.
Da cikakkiyar sallama ta shiga,ya daga kansa daga wata takarda ya amsa mata yana qare mata kallo. Yadda cikin ke rinjayarta kullum bashi tausayi takeyi,amma ita din kafiyarta da irin jarumtarta na sake burgeshi wani lokaci.
Zama tayi saman sofa,har sai daya miqe da zummar kamata amma taka qarasa zama.
"Haisam." Ya dago kai.
"Mm?"
"Na huta."
Ya kalleta na wasu seconds bayan ya koma ya zauna. Sai ya rufe file din da yake dubawa.
"Good."
"Yanzu zamu iya zuwa." Ta fadi tana marairaice masa. Ya san ba zata daina ba,ba zata daina roqonsa ba. Sai ya girgiza kai.
"One hour." Idanunta suka soma tara qwalla.
"Da gaske?"
"One hour." Ya maimaita.
"Ita zaki ki dawo." Ta gyada kai da sauri. Ta fahimci idan ba haka tace masa ba,tsaf zaice ba zata ko ina ba sai gobe. Ita kanta ta san ba zata yi biyayya a yau ba.
Sosai masarauta ta cika da farin cikin ganinta. Komai ya koma daidai cikin wani irin yanayi da kowa bai taba zaton faruwarsa ba. Wani irin mulki ne qarqashim jagorancin ahmad,wanda yake cike da hikima irin ta sultane da zamananci irin na ahmad din,da kuma shawarwari daga haisam. Mulkin sai ya zama wani iri,kuma na musamman,har yaso yafi na sultane dadi.
Me jego falaak na manne da ita. Morsa afiyya ta qi sakinta,kallon akhnan din kawai takeyi tana godewa Allah daya sanya komai yayi farko yana da qarshe.
Sultane kuwa ya kasa boye murnarsa shima da zuwan shalelensa. Don ma kunya ta hanata sakewa dashi.
Yarinyar falaak tubarkalla,qatuwa fara tas kamar ba daga cikin falaak ta fito ba saboda girma. Ta dade a hannunta ta hanawa kowa ita,har tanajin kamar ta bude idanu taga nata yaran. Sai a sannan taji itama mace takeson haifa,don ita sam basu tsaya tambayar wanne gender bane,haisam din yace kowanne Allah ya bashi yana so,yana maraba dasu.
Kaf ta manta dukka sharuddan daya sanya mata na zama ta huta da taqaita zirga zirga,bayan ya amince ya qara mata wasu awannin biyun akan awa dayar farko.
Sai data kusa zagaya rabin masarautar,inda duk ta dade bata shiga ba. Ta shiga wani sashe,ta fita wani.
Ta je wajen dawakai,dawakanta da tayi kewa,duk da haisam ya siya mata wasu daga qasashe daban daban,amma akwai sabo da kewa me yawa tsakaninta da wadannan. Ta je wajen lambuna,sun jima a ciki ita falaak suna tuna abubuwa da yawa da suka faru a gurin,ciki harda zuwan samarin dake neman aurenta,da ganinta da haisam a guraren na farko.
A jikinsa yake jin bata zauna ba yadda yace mata. Da yamma yana cikin meeting da shugabannin tsaro na gidan,daya daga cikin jami'an tsaronsa ya qaraso.
"Your Highness." Haisam ya dago kai.
"Yes?"
"Sun bada tabbacin bata zauna ta huta ba" Sai ya ajiye biron hannunsa.
"How long?"
"Tunda kuka iso" A hankali Haisam ya lumshe idanunsa. Kwana goma kacal suka rage. Kwana goma zata kwanta a fedeta,amma ta kasa bawa jikinta wannan nutsuwar tun yanzu?.
Sallah ta koma yi sashen haisam dake cikin gidan,tana tura bedroom din yana tsaye ya kammala alwala shima zai wuce masallaci.
Tun kallon farko ta gane yana fushi. Irin fushin shiru din nan nasa.
"Me kuma nayi?" Ta tambaya da salon kama kai irin na wanda yasan yayi laifi.
Ya juya a hankali. "Kin huta?" Ta dan yi murmushi tanason boye laifinta.
"Eh."
"Really?" Yadda ya fadi kalmar ya sa murmushinta ya dan ragu.
"Haisam..." Ta kirashi ganin yana neman qureta da wannan narkakkun idanun nasa masu tsananin kwarjini.
"Kin zagaye masarauta yau son ranki." Shuru kawai tayi,cikin ranta tana gayawa kanta ashe an kai masa rahoto?. Wanne irin damuwa haka yayi da lamuranta?.
Ta dan kau da kai. "Ba wani abu bane me yawa fa."
"Kina da tsohon ciki." Muryarsa ta yi qasa da wami nauyi a cikinta.
"Kuma kin yi tafiya me yawan da bai kamata kiyi ba right?" Ta yi shiru,shi kuma ya sake zuba mata idanun nan nasa masu girma da haske.
A hankali ya qaraso kusa da ita.
"Ba zaki kwana a nan ba." Ta daga kai da sauri,ta dauka zai barta ne ganin har ya sake qara wasu awannin. Ta saki jiki zaman gidan ya mata dadi sosai.
"Please" Ta fada tana tara hawaye.
"Zamu tafi gida tare"
"Haisam!"ta kirashi
"No."Ya katse ta.
"Bana son gardama akan wannan."Ta kasa yarda.
"Falaak fa....."
"Zata ganki gobe."
"Sultane...."
"Zaki zo gobe." Dukkaninsu sukayi shuru sannan ya qara da wani irin sanyin murya mai cike da damuwa
"Amma yau gida zaki tafi,shine kwanciyar hankalina da nutsuwata." Akhnan ta lura da wani abu a idanunsa. Ba iko bane. Ba tilastawa ba,kaman tsoro ne. Irin tsoron da yake boyewa tun watanni da cikin ta ya fara wani irin girma. Tsoron wani abu ya same ta ko jaririn. Batasan me yasa sam baida jarumta akan komai daya shafeta ba. Rago ne shi sosai ta wannan bangaren ba kadan ba. Sai kawai ta sauke numfashi. Ta san cewa a wannan karon....ba zata ci wannan musun ba.
Motar ta bar masarautar cikin shiru. Irin shirunan mai nauyi da ke nufin akwai wanda yake fushi.