Kenza eBookz

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 82

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 82

L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 82: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 82. Akhnan ta zauna gefen window tana kallon hasken Agadez…

3,375 words

Akhnan ta zauna gefen window tana kallon hasken Agadez da suke wucewa.

Tun fitowarsu daga masarautar bata sake cewa komai ba. Bata kalli Haisam ba. Bata tambaye shi komai ba. Shi kuma ya barta,saboda ya san wannan shirun nata.

Har yanzu ba abinda ya sauya sultane,har yanzu goyon bayan haisam yakeyi akan komai. Kaman baiyi kewarta ba kanshi tsaye yace mata tabi mijinta.

"Akhnan." Ya kirata bayan ya tabbatar bazai jure shirunta ba. Bata amsa ba,sai kawai ta ci gaba da kallon waje.

Wani dan murmushi marar qarfi ya bayyana a fuskarsa.

"Habibti." Ya sake kiranta dai bai gaji ba.

Har yanzu babu amsa,sai ya mayar da kallonsa gabansa.

"Good,at least now I know you're angry." A wannan karon ta juya ta kalle shi.

"Ka sani kenan."

"Mm." Kasa cewa komai tayi saboda qwallar data sake cika mata ido,sai ta sake mayar da kanta gefe. Shirun motar ya sake komawa kamar da.

Har suka isa gida,ya zagaya ya bude mata ta fito,maimakon ta jirashi saita fara takawa ciki tana tura qatoton cikinta gaba,ita a lallai fushi takeyi.

Stairs ta nufa kai tsaye,abinda a yanzun indai ya kama zata hau din yana riqe da ita ne,hakanan idan zata sauko shike zame mata madogara.

Amma kafin ta kai matakalar farko.

"Zauna." Muryar Haisam ta dakatar da ita.

Sai ta juya,ya nuna mata kujerar falon.

"Please." Ya qarashe fada a nutse.

Ta lura da yadda ya fadi kalmar,ba umarni ba ne wannan karon. Sai ta tsinci kanta da dawowa ta zauna a hankali.

Gabanta ya matso shima ya zauna sosai. Na wasu seconds yana kallonta ne kawai,kamar yana neman hanyar da zai fara.

Ita dince ce ta fara magana muryarta na rawa.

"Yanzu zan iya sanin me yasa ka taso ni daga wajen su Sultane kamar yarinya?" Hawayenta suka tsaya dab da idanunta.

Numfashi ya sauke a hankali.

"Saboda kina daukar kanki kamar baki da ciki." Nan take ta yi shiru,wannan ya bashi dama yaci gaba.

"Kin yi tafiya daga wata qasa." Ya daga yatsa daya.

"Kin isa gida." Sai ya daga na biyu.

"Kin qi hutawa." Na uku.

"Kin je masarauta." Na huɗu.

"Kuma kin zagaya rabin wurin." Akhnan ta sauke idanunta a hankali tana jin nauyinsa. Yana da wani irin kawaici,yana da wani irin haquri,amma batasan me yasa take saurin hasala haka ba. Ta sani,ba qarya yake yi ba.

Jingina yayi da kujerarsa. A karo na farko muryarsa ta yi laushi sosai fiye da kima.

"Do you know why I'm worried?"Ta girgiza kai a hankali,sai ya dan yi shiru kafin ya ce

"Because there are only ten days left." Akhnan ta dago kai da sauri.

"What?"

"Ten days."Ya maimaita.

"Kwana goma kacal." Ya sake fadi.

Ta kafe shi da idanu kamar bata fahimtar yaren French

"Kwana goma zuwa me?"Sai ya kalleta kai tsaye.

"Kwana goma zuwa ranar haihuwar yaranmu."

Wani irin shuru parlor din yayi,sai ta ji zuciyarta na bugawa

"Me?" Ta tambaya da tsoro a muryarta.

Haisam ya dan matsa kusa da ita.

"Likitoci sun riga sun tsara ranar haihuwar,saboda yanayin da suke ganin ya fi dacewa da ke da jariran" Ido ta zuba masa da tsoro sosai.

"Kuma baka gaya min ba?" Wani dan murmushi mai laushi ya bayyana a fuskarsa.

"Na yi qoqarin hakan." Sai ta tuna.....sau nawa yake son yin wata magana ya fasa. Sau nawa yake kallonta ya yi shiru.

Ya kamo hannunta,yatsunsa suka rufe nata gaba daya.

"Kin kasance kina gudun maganar cikin tun farko giiftii." Yayi dan shuru.

"Ban so na matsa miki ba." Idanunta suka cika da wani irin yanayi. Ba tsoro zalla ba.....ba fushi ba.....sai mamaki da yanzun yafi rinjaye.

Kwana goma.....kwana goma kacal?. Kwana goma sai ta zama uwa?.....

A karon farko ita ce ta matse hannun haisam,muryarta can qasa sosai.

"Haisam..."

"Mm?"

"Tsoro nake ji." Sai ya dan yi murmushi,irin murmushin da yake yi idan yana son kwantar mata da hankali.

Ya dago hannunta ya sumbaci bayan tafin,sannan ya ce a hankali

"Good."sai ta hade gira.

"Good?"

"Because I'm scared too." Akhnan ta zuba masa ido.

Da wuya Haisam ya taba yarda yana tsoron wani abu,yau gashi saboda ita taga tsoro qarara a idanunsa.

Kallonsa ya sauka kan cikinta,sannan ya dawo kanta.

"But we'll do it together......in sha Allah".

A wannan karon,akhnan ba ta sake tunanin masarauta ba dama kowa da kowa,sai kwanaki goma da suka rage kafin rayuwarsu ta canza har abada.

*_To masu tafiya suna saiku shirya,ku bada list kafin a gama diban adadin 'yan tafiya_*🤒🤒

Nidai na gama nade kayana zanyi gaba,saikun iso.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 150*

*_The Day Three Princes Arrived_*

*A Kingdom Reborn*

Cikin wani irin yanayi aka kammala dukka bakukuwan. Wani irin biki daya barwa akhnan wani kebantaccen nishadi duk da irin yanayin da take ciki. Ya kuma taimaka wajen dauke mata hankali dan kadan daga tunanin kwanaki goman da suke tunkarota.

Tare suka wuce da amare,shehnaz da aisa,wadanda daga kowacce tabi mijinta inda zasu zauna,daga can kuma kowacce zasu wuce guraren da sukafi yawan zama guraren ayyukansu a qasashe da garuruwa daban daban.

★★Safiyar ranar ta zama ta daban kuma ta musamman a gurin dukkanin ahalin motii ibraheem aba jifar,da kuma ahalin sultane muhammad hammud. Safiya ce da dukkanin ahalin biyu ke sanya ran yin idanu biyu da jikokin farko na masarautun.....wadanda zasu sama cikakkun jikoki zalla na jikin motii da sultane.

Daga cikin lafiyayyen amenity na asibitin. Giiftii khadeeja muhammad hammud ce,zaune gefan gadon asibitin da aka gyarashi da kyau tun da sassafe da wani irin lallausan fari qal din duvet. Sanye take da silk white robe,wadda tabi jikinta ta kuma fidda dogon cikinta dake gaba wanda sai data tallafeshi da pillow saboda yada take jin yana rinjayarta. Dogon gashinta a nannade a cure a qeyarta da yanayin daya sanya tsayinsa dukka ya bace gaba daya saboda gammo da akayi mata dashi. Hatta da dakin ya sani,yau din wani abu ne na musamman ke shirin faruwa. Saboda kebantaccen daki ne da iyalan motii aba jifar kawai ke kwanciya a cikinsa. Ba dakin kawai ba.....ward ne musamman dan madaidaici da aka ware saboda royal blood na gidan motii aba jifar.

Tun daren jiya hannunta yake saman cikinta. Cikin daya kasance tare da ita tsahon wata takwas da kwanaki,cikin da ya canza rayuwarta..... A yau zasu rabu,ba rabuwar baqinciki ba,tana sanya ran zama ta alkhairi da farinciki. Yadda aka jarrabi haisam da son cikin ya sanya take ganin tata qwalamar akan son yaran batakai ko ina ba.

Ranar asibitin ya cika da tsaro gaba daya,kamar shugaban qasa ke kwance a ciki. Ranan komai na asibitin ya shaida masu abu da abinsu ne suke cikinsa. Dukkan floor din maternity wing an killaceshi.

A hankali qofar bathroom ta bude,haisam ne ke takowa a hankali,gashin kansa dana girarsa,harma da gargasar hannunsa duka jiqe da ruwa.

Batasan sau nawa yayi alwala yayi sallah ba daga daren jiya zuwa yanzu. Ta maida idanunta a nutse cikin nasa idanun. Wadannan manyan idanun masu haske,amma a yau sun canza launi kadan,sun kuma rusuna sosai,alamun dake sake bata tabbacin baiyi cikakken bacci ba jiya,bayan ita ya tilasta mata yin baccin duk da bata shirya hakan ba. Dauke idanunsa yayi,ta tabbatar yana son boye mata rashin baccinsa dama karayar da tunda take dashi bata taba ganinta cikin qwayar idanunsa ba irin yau. Tun daren jiya bai zauna ba......batasan ya fita damuwa ba sai yanzu. A kwana taran baya kallon kanta take tana sake mamakin yadda take tsoro take karaya.....amma haisam nan da nan yake maida mata wannan energy din. Batasan ya boye komai bane ya kuma danne sai yanzu,yanzun da mintuna kadan suka rage a shiga da ita Cs din.

"Haisam." Ta kirashi da yanayin da tasan yafi so. Sai ya waigo kamar yana jiran kiranta.

"Ka zauna." Ta fada tana jin tausayinsa yana narkar da zuciyarta. Iya wannan kawai ya sanyata dagewa da addu'an Allah yabar masa ita da yaran duka a raye.

"Ina zaune tun dazun ai"

"A'a." Ta girgiza kai tana sakar masa murmushi.

"Kana sintiri dai yarima na" Karon farko a ranar dan murmushi ya bayyana a fuskarsa.

"You're enjoying this." Ya tambaya yana dage mata girarsa duka biyun.

"A little." Ta fada tana kashe masa ido daya still da murmushi a fuskarta.

"Good." Ya fada yana warware hannun shirt dinsa daya nade saboda alwala. Ta dan bishi da kallo,yau shigarsa ma,irin shigar da ba kasafai ya fiya fita da iya bane. Farar t-shirt ce qal da baqin trouser daya haska har saman dogayen yatsun qafafunsa. Ya mata wani irin kyau,sai takejin kamar a qara mata lokaci tare dashi tayita kallonsa.

Qarasowa yayi ya durqusa a gabanta. Ya dora hannunsa kan cikinta. A hankali ya motsa labbansa,bayan ya matso dasu kusa da tsinin cikin.

"Behave yourselves today." Wata tattausar dariya ta saki

"Wa kake wa magana?" Ta fada idanunta a bude tana kallon wannan calm face din nashi.

"My sons." Ya bata amsa da calmness dinsa da baya taba barin jikinsa komai girman tashin hankali.

"Who said they're boys?" Ta fadi tana bata fuska,don ita har ga Allah baby girls tafi sha'awa. Tunda ta dora idanunta akan baby falaak da taci sunan morsa safiyya suke kiranta da sultana,taji duk duniya baby girl takeso.

"Ku bani ita don Allah" Tace da maleek a daren sunan daya samu shigowa ganinsu. Murmushin nan nasa me harba jinin sarauta a jikinsa yayi,ya kalli falaak kawai.

"Idan ta baki nima na bayar" Saita falaak ta fidda ido waje tana dariya.

"Zai hadamu fada ne kawai giiftii". Haisam da yake can gefe yana amsa waya ya jisu,bai amsa mata ba sai da suke tattaki suna komawa sashensu.

"Abinnan fa da kikace zaki kira sultane ki gaya masa anyi shi akayi aka samu yarinyar nan....banda anyi hakan da falaak din taki tana nan zaune ita daya ba sultana din.......amma yanzu duk bayan kince zaa kashe miki sisinki kuma an mata gata da baby kice su baki?" Kunya ta kamata,wata irin kunya me nauyi data tuna wautarta a wancan ranar. Allah ya taimaketa daya taka mata birki,da da wanne ido zata dinga kallon sultane a yanzu?.

"Eh....amma har yanzu abinnan dai kasan abun jin kunya ne ko?"

"Eh.....duk da hakan kuma baki fasa tashi na jiya kince saina miki ba ko" Qaramin ihun kunya ta saki tana cusa kanta a qirjinsa data tuna da dabarun da aka samu akayi saboda yadda tsaho da tudun cikinta ke hana komai.

"Allah ya tabbatarmin dake a haka ko kin haihu" Taji yana fada qasa qasa cikin nishadi.

"They are." Amsar haisam ta maido da tunaninta kansa.

"And if they're not?" Ta fada tana turo baki gaba.

"They are." Ya sake maimaitawa kyawawan idanunsa suna lumshewa gami da budewa.

Kukan shagwaba ta sakar masa,ya miqe yana sakin siririn murmushi gami da fara cire mata dan kunnen dake kunnenta.

"Fadata ai ba fadan Allah bane ko?" Sai daya fadi hakan sannan ya samu sauqi.

Shi ya shiryata tsaf cikin kayan daya kamata ta kasance a cikinsa.

Wani irin shiru ne ya mamaye private wing din asibitin. Ba shiru irin na rashin mutane ba. A'a.....shirun da ke zuwa kafin wani babban al'amari.

A cikin waiting parlor din dukkaninsu suka dakata,don haka ba wanda akhnan tasan da zuwansa. Basason su kasance tare da ita tunda wuri haka,saboda karsu kaya mata zuciya,shi yasa ta dauka daga ita sai haisam dinne kawai a gurin.

kowa na qoqarin boye damuwarsa. Daga bangaren kujerun dama nanay ce,zayne riqe da tasbaha. Labbanta na motsi da addu'ar da bata saketa ba tun daga ranar da haisam ya gaya mata Cs din akhnan. Morsa Safiyya na zaune kusa da ita,Idanunta na kan qofar da akhnan zata fito. Ta kasa tantance wanne matsayi take kai,gaba daya ma sai taji kaman addu'ar na shirin qwace mata. Sultane yaso ta zauna gida saboda falaak,amma ita kanta falaak din sai da akayi da gaske sannan ta zauna din.

Daga daya bangaren sultane dinne,zaune yake cikin nutsuwa,amma duk wanda ya san shi zai gane cewa yau zuciyarsa ba cikin nutsuwar da yake nunawa take ba.

Hussam na kusa dashi shi da Aareef,sau noorah dake zaune gefan morsa safiyya.

A nutse akhnan da haisam suka fito daga dakin,magana yake gaya mata qasa qasa wadda ba wanda yasan me yake gaya mata sai ita dashi.

Cikin doguwar farar rigar asibitin take takowa,hannunta cikin na haisam din.

Mamaki ya saukar mata ganin dukkaninsu a zaune a gurin,ba tare da sanin isowar kowa a cikinsu ba. Ta bude ido da baki dukka tana takowa,sai dukkaninsu suka hutar da ita ta hanyar tasowa suka risketa. Gaidasu taketa qoqarin yi,amma sukam ba wannan bane a gabansu. Yadda cikin ya qara qasa yadda take takawa da qyar kowa ke tausayawa. Addu'a ce kawai ke tashi a gurin,ta wani tana shiga cikin na wani,haisam na tsaye daga baya yana amsawa daya bayan daya.

A lokacin ne kuma nurse ta iso da wheelchair.

"Madam, we're ready." Ta janyo wheelchair din kusa da akhnan din.

Kallonta akhnan din tayi,sai kuma ta kalli wheelchair din. Ta girgiza kai a hankali.

"No." Ta fada a sanyaye. Murmushi nurse din tayi,tana zaton ba ta ji ba ne.

"It's okay. We'll take you comfortably." Ta fada cikin girmamawa.

Kai akhnan ta sake girgizawa.

"Ba zan hau ba." Ta maimaita mata wannan karon da yaren oromo yadda zata fi fahimta.

Mamaki ya kama nurse din,ta dan rusuna sannan tace

"But......"

"I can walk." Ta dakatar da ita ta hanyar qarasa mata bayanin.

A nutse ta janye dubanta,sai idanunta suka koma kan haisam.

"Ina son muyi tafiyar tare." Ta furta a sanyaye idanunta cikin nasa.

Wata irin nutsuwa ta ratsa fuskar haisam,kamar ya fahimci abin da take nufi. Ba maganar tafiya ba ce kawai. A'a.....tafiya ce ta qarshe da zasuyi kafin su zama iyaye ita dashi.

Ya matse hannunta a hankali yana sake nutsa idanunsa cikin nata.

"Are you sure?" Ta gyada kai.

"Very sure." Ta amasa masa tana qoqarin maye gurbin tsoronta da murmushin.

Sai ya dan sunkuyar da kansa da yanayi na girmamawa tamkar yana magana da motii.

"Then we'll walk." Ta bata tabbaci tare da wani confidence na daban.

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 151*

A nutse nanay ta share hawayen da suka cika idanunta. Wata irin qauna take gani wadda take kafa kanta da kanta,take kuma kafa tarihi,koda ba'a gaya maka ba idan ka gani kasan cewa sun manta da kowa,sun manta da komai sai kawunansu.

"Allah Ya tsare ku." Nanay ta fada a fili. A hankali akhnan ta qarasa gare ta,ta saka hannuwanta suka ta rungume nanay din,rungumar da batayi yadda taso ba saboda cikin gabanta.

Rungumar da ta sa Nanay ta qara riqeta,kamar ba ta son sakinta.kamar rumaisa ko Aaani ne zasu shiga dakin tiyatar. A yadda takeji a yanzun,batajin idan su dinne ma zataji hakan.

"Ki dawo min lafiya diyata." Nanay ta fada cikin rawar murya

"In sha Allah." Ta amsawa nanay da jarumta sosai a muryarta.

Sai ta matsa wajen morsa Safiyya,morsa safiyyan da ta riga ta fara kuka tuni. Ta kasa jurewa,idan har wani ke rubuta qaddarar wani,zatacw bata taba hango akhnan din zata iya daukar ciki me girma irin wannan dake jikinta ba a yanzu.

"Sannu da qoqari biftu....sannu da ibada." Akhnan ta yi dariya kadan cikin jin nauyi.

"Ni kuma bana son kina kuka." Qoqarin shanye kukan tayi ta janye jikinta kadan tana son bawa kanta qwarin gwiwa.

"Ki dawo da kishiyoyina ko masu gidana lafiya qalau"

"Ana gudun kishiya kuma kina nemanta momma" Akhnan tadan tsokaneta kadan.

"Eh,to wadannan su kam ya zanyi dasu?." Ta fada tana qarasa goge fuskarta.

Duk suka yi dariya. Ko da cikin damuwa ne,amma hakan ya sake rage musu tension.

Daga nan ta juya zuwa ga Sultane,na dan lokaci suka tsaya suna kallon juna ita dashi. Wannan qaunar ta daban dake tsakaninsu kana iya ganinta cikin idanunsu.

Sultane ya daga hannunsa ya dora shi saman kanta.

"Allah ya sanya albarka a abinda zaki samu biftu.....Ki dawo mana da farin ciki in sha Allah"

Qwalla taji ta taru a idanunta,aai ta gyada kai kawai.

Ba ta yarda ta yi magana ba,saboda ta san idan ta yi hawaye ne zasu zubo. Kuma ta yiwa haisam alqawari ba zatayi kuka a gabansu ba. Koda zatayi kukan,zata yishi ne a jikinsa.....a kafadarsa.....a gabansa shi kadai.

Juyawa tayi tana maida hannunta cikin na haisam. Ba wheelchair. Ba gaggawa. Kawai su biyu. Miji da mata. Masu tafiya zuwa lokacin da zai canza rayuwarsu har abada.

Corridor din yayi tsawo,amma babu wanda ya yi magana na wasu daqiqu tsakanin ita ko shi.

Ita ta fara matsawa sosai kusa da shi.

"Haisam."

"Na'am." Ya amsa mata yana qoqarin kore damuwa.

"Kar ka firgita idan na firgita." Ta fada a sanyaye. Sai ya yi murmushi kadan,wancan murmushin da ita kadai take iya fitowa da shi saman fuskarsa.

"Too late." Ya furta ba tare daya kalli fuskarta ba. Murmushi me sauti kadan tayi.

"Kana tsoro ne?"

"A lot." A yau ya bata amsa kai tsaye ba wani kwana kwana.

Ta dago kai ta kalle shi tana jin amsar tasa har cikin zuciyarta. Mutumin da yayi hannun riga da tsoro......amma a yau yana bata tabbacin tsoro kai tsaye daga bakinsa.

"Ni kuma bana tsoro." Ta furta kai tsaye.

"I know." Ya amsa a wannan karon yana maido dubansa kan fuskarta.

"Why?" Ta tambaya taba rungume hannunsa sosai,sai ya tsaya na dan lokaci daga tafiyar da sukeyi ya kalleta da kallon da ya saba yi mata tun farkon soyayyarsu.

"Because you're stronger than all of us." A wannan karon,hawaye suka cika idanunta. Kafin ta samu damar amsawa suka isa qofar theatre din.

Ta dauka zai tsaya ne kaman yadda kowa keyi daga waje,amma sai taga suna shiga tare dashi. Wani irin sanyi da farinciki ya mamayeta. Bata fahimci yana gurin za'ayi aikin ba sai da taga sun bashi medical gown yana sakawa.

Ta lumshe ido tana kallonsa sanda yake daure rigar a jikinsa. Ta masa kyau.....sosai,wani irin kyau daya haska har cikin qwayar idanunsa.

Hannunsa cikin nata suka mata anesthesia suka kwantar da ita,sai suka ajiye masa kujera kusa da kanta ya zauna idanunsa cikin nata. Shi da ita dukka suna jin maganganun likitocin da zasu mata aiki wadanda dukansu mata ne,sai anesthesiologist namiji da wani guda daya daban da bazaizo kusa da ita ba.

Ko sau daya bai bari idanunta sun huta daga kallonsa ba.....tana jin sanda aka soma yaga fatar cikinta cikin nutsuwa da takatsantsan. Ta daga idanunta tana kallonsa sosai.

"You look pale."

"I don't." Ya fada da murmushinsa dinnan me taushi yana juya kansa kadan.

"You do." Ta maimaita masa tana son yin dariya.

"Focus on yourself." Ya fada yana dan lakuce mata hanci da yatsansa. Murmushi ta sauke

"Allah you are scared."

"I'm not......giifii mana" Ya fada yana dan yamutsa fuska yadda take masa idan ya dameta da tsokana.

Likitar ta yi dariya,don duk maganan da suke tana jinsu. Komai nashi asali burgeta yakeyi,a yanzun da taga mu'amalarsa ta zahiri da matarsa sai abun yake sake burgeta qwarai. Ta girme masa nesa ba kusa ba,amma tana yabawa halayensa sosai.

"Your husband is definitely scared." Itama ta sanya musu baki.

A karo na farko akhnan ta ga ya kasa musantawa.

"Can everyone stop discussing me?" Ya fada yana basarwa sosai,abinda ya bawa kowa na dakin dariya,dariyar kuma ta cika dakin.....ta rage mata tsoro.

"Hold my hand tighter" Akhnan ta fada da muryar rada. Idanunsa cikin nata ya sauke mata wani murmushi me laushi,ya kuma sake matse hannun nata cikin nasa. Abinda ya lura,yadda yake qoqarin bata aminci.....itama dake kwance cikin irin wannan yanayin qoqarin bashi nutsuwa takeyi.

Lokaci ya ci gaba da tafiya a hankali,yana debo mata memories din rayuwarsu ta baya. Wani tayi murmushin kunya wani ta musanta kadan ba hayaniya ko motsi me qarfi. Doctors suna aikinsu,komai na tafiya yadda aka tsara.

"Remember madeena?" Ta dan yi mamaki.

"Yanzu?" Saboda bata dauka labaransa zasuyi tsaho haka ba,kwata kwata ya hana tunaninta komawa kan Cs din da ake mata a yanzu haka,yanata daukarta yana cillata wasu duniyoyi.

"Yes." Ya amsa mata,sai ta yi dariya a hankali.

"Me yasa?" Ta sake tambayarsa,ya dan yi shiru kafin ya ce

"Saboda a lokacin ne na fara gane....." Sai ya dakata kaman yana ja mata rai,ya saba mata irin haka idan yana bata labari,sai suyita rigima.

"Gane me?" Ta tambaya da zumudi

Idanunsa suka sauka a kanta da wani laushi.

Readers Also Read

More by Huguma