Nayi nadama book 1 complete - Chapter 9
Nayi nadama book 1 complete Chapter 9: Nayi nadama book 1 complete Chapter 9. Kashe gari Tun da safe Aysha ke kuka wuy wuy da hawaye da suka kasa tsayuwa…
3,353 words
Kashe gari Tun da safe Aysha ke kuka wuy wuy da hawaye da suka kasa tsayuwa Saka makon bayanin da Abba ya mata Na tafiyarta tare da Hamma Yusuf din Kuka take sosai tana pita parlorn Abban nata kitchen ta nufa Ummi dake qoqarin hada musu breakfast ta fito da sauri gami da kama hannuta cikin tausaya mata da cikar takaici Dan Sam Ummi bata son abin da zai taba mata autar tannan Daki ta wuce da ita kan gado ta zauna gamida jawota Cikin kuka ita kuma ta zame ta zuba guiwowinta a kasa ta kifa kanta kan cinyar umminta cikin tsananin kuka tace Shi kenan Ummi nikam Na shiga ukuna Ummina cikin Neman alfarma tacigaba da cewa Dan Allah Ummi Ku gafarceni Na tuba kumin afuwa dan son Annabinmu Dan Allah kar kubari ace tare zamu tafi da Hamma Yusuf wlh tsoronshi nakeji Ummi zai kashe miki nifa Haka tai ta kuka tana surutai Ummi ta dago fuskarta tace kalleni nan Aysha Na miki alqawari Indai Na isa Da Hamma ku To insha Allah bazai cutar da keba Kisa ido kigani ni nasan iya koki da dokokin da zan bashi a kanki Haka dai tai ta bata baki da kontar matada hankali Dama tuni an qarisa mata shirinta
Ahmad kuma da Adam tun da sukayi sallan asuba suka taho gida Dan yiwa biyayensu rakiya zuwa airport Suna tare a farfajiyar yar gidan bayan an gama dura jakukkunansu a but
Cikin nitsuwa Yusuf yaje gaban baba bello ya Dan duqa gamida cire hular kansa cikin sanyin murya
yace toh baba zan tafi fatan Allah ya qaddara saduwarmu kan alkhairi ya Dan yi shiru kadan ya Dan kuma dago kanshi cikin rawan murya yace Ku gafarceni baba in akwai abin da Na muku cikin rashin Sani
A hankali baba bello ya dafa kanshi cikin son Dan Dan uwanbnashi yace baka mana komai ba Yusuf Allah ya maka albarka Yusuf mu iyayenku xuqatanmu baza su iya yin fushi da kuba duk da kaso ka boye min tafiyar Amman ya zama dole nasan duk woni motsinaka shiyasa tun jiya Na sanar da kai munSan da batun tafiyar taka Dan kar da safe ka shirya ka tafi ba tare da ka nemi afuwar iyayenka da sanya albarkan suba Allah yayima albarka Hannun shi ya Sara kan hannu baba bello da ke cikin sumar kanshi yace Amin ya rabbi
A hankali ya taka yaje Gaba mahaifinshi Cikin biyeyya ya duqa gaban shi ya dago ya kalli ma haifin nashi yace Abba ka gafarceni ka San yamin albarka ko zan samu sauqi cikin rayuwata Ya kuma Dan duqar da kanshi Yagi gaba da cewa yau zan tafi ina mana fatan saduwa cikin alkhairi
Kai Abban ya jinjina yace ba komai Yusuf Allah ya muku albarka baki dayanku da kai da yan uwanka INA maka fatan alkhairi cikin karatun ka Amin yace cikin jin dadi Haka yaje gaban Nenne ita ta samai albarka A gaban Ummi ya tsaya cikin mmk ganin tana riqe da hannun Aysha ita kuma sai kuka take fuskarnan duk tayi jazur da ita Ba tare da ya qara kallon inda Ayshan takeba yace toh Ummi ni kam zan tafi sai kuma Allah ya gaddara saduwarmu Toh Allah ya kaiku lfy ya kuma dawo daku lfy Amin yace cikin rashin gane me zancen Ummi yake nufi Allah ya kaimu lfy to shi da waye kenan Cikin ransa kuma yace toh me ruwanka kai da zaka bar musu qasar Cikin Dan sassarfa ya qarisa gun Adam rungume juna sukayi cikin qaunar juna Adam ya Dan kai bakinshi dai2 kunneshi cikin sanyin jiki yace Zamuyi missing dinka biyaye A hankali yace insha Allah kamar yau zan dawo muci gaba da rayuwar mu mu 3 dinmu Har yanxu suna ruqqume da juna cikin jadda dawa Yusuf ya Dan bubbugi bayan Adam yace Adam nabar amanar Ahmad dinmu a hannuka Dan Allah ka kukan mana dashi ka Samar mai farinciki insha Allah nima inna isa zan aiwatar da aikin ummra zan roqi mahaliccinmu da ya cikawa Dan uwanmu farin cikinsa Cikin qarfin hali Adam yace Na karbi wannan amanar A haka ya sakeshi tare suka nufi gun da Ahmad din yake tsaye yana jingine da jikin mota Anuty Sadiya Na gefebshi wanda yanxu kenan isowarta
Ya Isa gaban shi kenan Abba ya iso riqe da hannu Aysha cikin muryar umurni ya kamo hannu Yusuf din ya damqa mai annum Aysha cikin nasa ya hada ya rumtsesu Cikin mmk ya dago ya zubawa Abba Ido cikin Ido sukayi Cikin kaduwa ya bude baki zaiyi mgn Da sauri Abba ya dakatar dashi dacewa Bana son jin komai daga gareka Yusuf a yanxu haka umurni nake baka kai tsaye ka kama hannun matarka tare zaku tafi wannan umurnine kuma kab mun gama yanke wannan hukuncin
Cikin razani da kidima ya maida dubanshi kan baba bello da alamun tabbaya Kai ya jinjina mai cikin alamun yes umurnine Ummi ya kuma kallah cikin daure fuska tamai nuni da amanace
Cikin tsananin bugawar qirji ya maida dubanshi ga Ahmad dake gaban shi da ya zama tamkar an dasashi Girjinshi ke duka 3 3 a take zufa ta fara keti mai tabbas yasan da tfyar Yusuf Amman baiyi tunanin za a hadashi da Aysha ba Cikin sauri ya dawo kanshi ya kalli fuskar Aysha Ido cikin Ido sukayi cikin wata iriyar narkekkiyar murya ta saki kuka mai tsuma xuciyar mai sauraro Kuka take tana wayyo ya Ahmad dina shike nan kun rabani da ya Ahmad dina Cikin azama ta fizge hannuta daga cikin hannu Yusuf din da ya zama tamkar ruwan ya cinyeshi Da qarfin ta fada qirjin Ahmad din ta Sa hannuta ta qaqumishi ta mannashi da qirjinta tamkar zasu chige cikin juna Gaba daya shiki kam ya zama tamkar takarda jinshi yake a tsakiya shi ba sama ba shi ba qasaba tabbas badan a jingine yake da jikin motoba da tuni sun kai qasa Bugun zuciyarsa kuwa tamkar zata balla girjinsa ta fito woje qoqol warsa ko gaba daya ta cushe mai ji yake kamar zai zauce Allah sarki Ahmad damo sarkin haquri A hakan yayi murmushin qarfin hali yasa hannushi ya dagota cikin ciccijewar voice yace Aysha ai tafi ya ba mutuwa bace koba Dade ko banjima zaki damo ki samemu Kuma muma zamuna kawo muku ziyara Ita dai kuka take harkamar zata shide Hannuta ya kamo ya miqawa Yusuf cikin qarfin hali da juriya yayi Dan murmushi yace Biyaye ko zaka iya riqe wannan amanar da zan baka cikin takun jarumta ya matso gareshi yace Yusuf bazan taba gane kana so naba sai ka tayani son abinda nakeso fiye da kaina Dry ya danyi kuma cikin dacin rayuwa yace INA nufin Aysha kuma INA nufin so Na Dan uwanta ka Cikin mmk Yusuf ya zuba mai I do shi tunda suke da Ahmad bai taba kiran shi da woni sunan da ya wuce biyayeba Amman yau ya kirashi da yusuf kenan yana nufin amanar dai yake bashi da gsk
Da qarfi ya jawoshi ya fada jikin shi runqume juna sukayi kamar zasu shige jikin juna Cikin rada yace Ahmad nayima alqawari zan dawoma da farin cikinka Cikin juya kai yace Na yarda Amman in kasa Aysha farin ciki ne koda INA cikin qabarina zanyi farin ciki biyaye am Da sauri cikin razani😱 Yusuf yasa hannu ya rufe mai baki cikin firgici ya rinqa ja da baya yana fadin a a A a kam Ahmad zamu rayuwa tare kuma Zamu mutum tare
Shiko Ahmad Abba ne yazo ya jashi sukayi cikin gida yana juyawa yana kallon Yusuf dinncikin sanyi ya daga mai hannu tare da furta mai zanyi kewarka Dan uwana Usman ko da Rabi,u gaba daya jikin su yayi sanyi Abdul ka mai saurin kuka tuni yake ta sharbar kuka
Baba bello da Adam ne kadai suka yi masu rekeyi Basu dawoba har saida jirginsu ya tashi
Allah sarki Ahmad ko ya rayuwa zata kasan CE mai ne ? Abinda masu karatu suka rinqa kirana suna tabbaya ta kenan ko ya Yusuf zai yi da amanar da aka bashi ? Duk dai am soshinku Na gaba kunbiyoni dai a hankali
Fatan alkhairi ga dukkan daukacin alummar musulmai Inai mana barka da jumma,a
Dan jin ra ayinku masu karatu qofar a bude take da shawarwarinku ina alfahari daku
By garkuwan Fulani [4/9, 2:25 PM] +234 909 785 3276: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 NAYI NADAMA MI,WASMITI.. page 4⃣9⃣to5⃣0⃣ Na Aysha Ali Garkuwa 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Maryam kam tun ran dasu Hamma Yusuf suka zo musu ziyara Suka fita tare da ya Ahmad har yau bata kuma sashi a idonta ba Haka kuwa rayuwa ke tafiyar musu kullum dare Ahmad zaiyi ta kukan zuci da zantuka cikin tsananin quncin rayuwa Haka kuwa sukaci gaba da rayuwa
Sai dai al,amarin Na yau din ya firgita Maryam sosai Misalin Garfe 8:30 Pm Maryam Na cikin kitchen tana Dan tafasa indomi Dan tunda gari ya waye batasa komai a bakinta ba
Daga cikin kitchen din taji sautin da ta saba ji matuqar dare yayi Cikin fargaba da tausayawa Dan uwan nata Ta fito ta nufu qofar dakinshi A hankali ta zame a baking qofar
Cikin fitar hayyaci take jin zantukan da ya Ahmad din yakeyi Cikin kuka yake ta nanata innalillahi wa,inna ilaahi raji,un Cikin muryar kuka sosai kamar yaro Yake cewa ya Ubungijina ka kawo min mafita Allah Na ka dubeni da idon Rahama rabbi ka bani ikon cinye wannan jarrabawar da ka jarab ceni da ita yaci gaba da fadin Woyyo Allah Wayyo yar uwata Aysha ko cikin wanne hali zaki kasance Allah sarki Dan uwana biyaye Na kamin adalci ka luranmi da burin raina Ki gafarceni Yar uwata Na cutar da zuciyarki
Cikin tsananin kuka yaci gaba da cewa Ya Allah menayi gareka ka hukuntani da wannan baqin cikin rayuwa ya ugaban gijina kowa Na cikin farin ciki sai ni zuciyata ke suyuwa
Ya Allah ka jibanci lamuranna
Kukan da yakeyi ya sata kuka sosai tun tanayi qasa 2 cikin sheshsheqa har kukan yaci qarfin ta ya kufce mata
Can cikin kukan tajishi cikin rawar murya yana Astaqafirillah Astaqafirilah Haka yayi ta Nana tawa har zuwa woni Dan lokaci can kuma tajishi cikin kuka mai tsananin da alamar toshewar numfashi Yana fadin ya Allah kai kaso ka ganni a haka ya ubangijina kai kafini sanin matsala ta ya Allah ka karemin imanina ya Allah ka kawo min sauqi tako wacce hanya Cikin Jan numfashi yace koda ajalinane matuqar dai shine waraka ga rayuwata Allah ka bani Sa,ar tafiya kawai Ya Allah ka gafar tamin kura kuraina Allah ka bani ikon sauqi haqqin matata maryama da ya rataya a wuyana Yana cikin haka Wani irin tari mai garfi ya sarqa fe mai wuya
Trin yake yana fadin ase dama bazan rayu dakeba Aysha Ayyah yar uwata ko zaki gafar tamin nan kuma tari ya rufeshi mgnar ta tsaya sai tarin da yakeyi cikin jin daukewar numfashi ya rinqa zagaya cikin dakin kamar mai yin dawafi
Cikin tsananin kuka da firgita da fitar hankali Maryam ta zame a baking qofar ta konta kuka takeyi sosai Kukan takeyi irin kukan da Dan Adam zai iya suma da kaji kukan kasan bata cikin hayyacinta Qofar take bugawa da qarfin cikin rawar murya Take ta kwada mai kira tana Ya Ahmad Zo ka bude min qofar ya Ahmad Ka budemin wayyo Allah Na Dan uwana wayyo Abba Na wayyo Nenne na
kuka take sosai tana buge buge kamar ta bebbiya tana ya Ahmad ka bude dan Allah kazo ka budemin qofar
Cikin rike cewar ya rinqa salati yana lalabu qofar Dan Sam idonshi bai gani da gyar yake furta
Ina kike Maryama ban gankiba Na rasa qofar Ita dai kukan takeyi tana buga qofar da iya qarfin ta Da gyar ya samu ya lalubo qofar ya bude Yana budewa yaji ta
konce a qasa tanata kuka mai qona zuciya
Da sauri ya durqusa guywa bibbiyu hannushi ya Sa ya kamata Yana fadin Maryama kiyi shiru kiyi haquri zo ki fadamin waya taba min ke ita dai kukan take da cure cure tana tuttureshi gashi da iya qarfin ta take kukan a nata tunanin tanayi da qarfine Dan a kawo mata dauki
Da gyar ya tattaro iya sauran qarfin shi ya matseta a cikin qirjinshi Amman Sam ta kasa tsaida kukan nata Cikin tausayi yace maryama ban so cutar dakeba ya yar uwata idan laifin nawa ne kimin afuwa banson Na mutum da nauyin cutar da ke a zuciyata kanta ya qara mannawa kan qahon xuciyarsa cikin karaya yace Maryama kiji bugun xuciya tako maryama ba zanyi tsawon rayuwa ba shiyasa gwara Na nemi gafararki Zancenshn ya qara ingizata ta qara rushewa da kuka tana qamqameshi cikin tsoro tana fadin bazaka mutuba ya Ahmad insha Allahu zamu rayuwa tare mu mutum tare ya Ahmad in ka mutum nima zan mutum Ganin ta rude sai surutai takeyi duk yayi iya yinshi ta kasa barin kukan Shiyasa cikin Hikima Ya tallabo Fuskarta Cikin tausayawa Kansu da Kansu ya tsurawa bakinta Ido yadda take kuka baji ba gani A hankali qoqolwarsa ta rinqa bashi umurni
Cikin sanyi ya manna bikinshi da nata Da dabara ya samu ya zira harshenshi cikin bakinta A hankali yaji jikinshi Ya fara sakewa tako ina yaji kamar ana watsa mai ruwan zafi a take idanshi ya fara canzawa Cikin zafin nama ya samu ya cabko harshenta ya rinqa tsotsan harshen cikin wani yanayi ya fara sarrafata Itako gaba daya jikin ta ya Debi bari da firgici jin irin karatun da yayan nata yake qoqarin biya mata nanda nan ta fara tureshi cikin tsoro da son zaro bakinta daga nashi Amman Ina ta kasa
A hankali ya zare bakinshi daga Nata ya nufi kan gado ya zube sai faman maida numfashi da mishi yake tayi
Da hamzarita ta sake miqewa a karo Na 3 ta samu ta miqe din bata fadiba ta nufi kan gadon Zama tayi a gefen kanshi tana Ya Ahmad tashi mu tafi asbiti Hannushi yasa ya kamata ya kontar da ita a gefenshi cikin Rada yace maryama bani haqqina ko zan samu sauqin zogin da nakeji Zuba mai indo kawai tayi tana zubda qollah😭 A hankali ya ronqofo kanta cikin hikima ya zare rigar jikin ta ya rinqa sauqe mata salo kala kala
A hankali naji sautin kuka guda biyu Na tashi Ita kuka take Na tunanin irin shirin da Aysha take yiwa derennan ga ya Ahmad din ase abin zai canza ya dawo gareta Shiko kuka yake yana ya Allah ka zama sheidana Na sauqi haqqin maryama da ya rataya a wuyana rabbi ka bani ladan biyeyya da nayiwa iyayena
Bayan sun gama dawowa haiyacinsu Ya tashi ya hada mata ruwan zafi ta Dan gasa jikinta tayi wonka ta fito ta kinga gefen shi
shima wonkan yaje yayi gamida yin alwala yazo yayi ta nafilfili Sai da akayi kiran salah ya tasheta shi kuma ya nufi masallaci
Bayan ya dawo daga masallacin ya samu bata nan Cikin mutuwar jiki ya konta Zuciyarsa Na bugawa a ranshi yaji bai yiwa maryama tashi Adalciba a fili yace da Aysha ce da bazan mata hakab da zan bataba kulawa t sosai
Da gwarin guywa ya nufi dakinta tun da tazo gidan bai taba shi gaba sai yau Sosai yayi mmkin ganin ta konce hawayen Na bin fuskarta da sauri ya qarasa gunta cikin Dan kula ya tallabota ya daurata kan cinyarsa Maryama ni nasaki kuka ko ki gafar ceni kar kijamin Allah ya isa Kai ta rinqa juyawa tana zubda qollah😭 cikin sanyin murya tace ya Ahmad ba kamin komai ba kuma ko kamin ma Na yafe Toh meyasa saki Kuka Kaine ya Ahmad Da sauri yace kuma kince ban mki komai ba Ehh bani kake yiwaba Toh me NAYI gayamin yake yar wuta Na baki haquri
Cikin kuka tace ya Ahmad meyasa bazaka Sa haquri a rankaba ya Ahmad ka ruqwumi qaddara mana ka dena azabtar da zuciyarka da ta maso yanka da halin da kake ciki
Cikin cije lebe yace maryama ba yin kaina bane bani da yadda zanyi
Cikin kula tace ayyah ya Ahmad duk da nasan ba sona kakeyiba Amman zan roqeka alfarma ka daina rufe qofar ka gareni Da sauri ya katseta da cewa waya CE miki ban sonki kin tabajin inda Dan uwa yaqi yar uwarsa Cikin kukan tace Ya za ayi in yarda kana sona Cikin qarfin hali da qoqarin ganin ya fatan ta mata yace zo zonannki gani Bakinshi ya hade dannata ya rinqa tsotsar harshenta sai da yaji tayi nuqui ya zare bakinshi ya dan nunata yace Maryama zabin Allah kece zabin da Allah ya min kuma bazanngi zabin mahaliccina ba cikin Dan jin sanyi tayi ajiyar hrt tace I love U so much my dear Broz Me 2 Yace mata gamida fita ya nufi dakinsa Kai tsaye toilet ya nufa Dan amai yakeji mai bala,in zafi yake jin yana tuqarsa daga qahon zuciyarshi Sosai yaketa kakari ga wani zazzabi mai zafi da ya rufeshi a take
Cikin tsinkewar zuciya da frigata da tsantsar azaba ya zubawa a man da yake kwara wan ido 😳
By garkuwan Fulani [4/9, 2:25 PM] +234 909 785 3276: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 NAYI NADAMA MI, WASMITI page5⃣1⃣to5⃣3⃣ Aysha Ali Garkuwa 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Jini ne guda2 baqiqqirin dashi aman yayi sosai Cikin wahala da dimuwa ya koma cikin dakin kan gadon shi ya fada Cikin maida numfashi a hawale cikin tausa yawa kanshi yake qoqe qollahr😭da ta cicciko mai ido A ranshi yake tunanin wannan karo Na biyu kenan yana aman jininnan ran da Maryam ta tare da yau kuma
Cikin tunanin da azabar da yakejin baccin wahala ya saceshi Dan wannan lkcin ya kasance kamar shine dare a gareshi daran kuma yakan zame mai tamkar rana da wuta a cikin zuciyarsa
Tin daga wannan rana Maryam take shigewa rayuwar Ahmad sosai Dan qoqarin qanin ta debe mai kewa ta Dan kawar mai da matsalolinshi Ba laifi kuma iya dai dai gorgodo ya sake Yana boye damu warshi Dan ganin Maryama manshi Na shiga ciki. Damu sosai Sai dai banan gizo ke saqanba Ase a hankali ciwon zuciya ya gama raraka qarkuwar jikin Ahmad
Wata rana da aman ya sashi a agaba Dole ya shirya cikin sirri yaje hospital gojin forko da akayi aka gano zuciyar Sa ta samu mugun raunin dr Jabir ne ya kalleshi cikin kula da tausa yawa yace Ahmad dole sai anma dashen zuciya
Kai ya sunkuyar cikin siyayar da qollah😭 ya Dan kuma daqowa yace Dan Allah doctor ina Neman alfarmanka plx wannan mgn ta zama sirri tsakani Na da kai karka gayawa Abba Na Cikin mmk Dr yace Ahmad me kake nufi zaka boye musu abinda ke damunka ne shin sai ciwon ya kasheka ne kakeson su Sani Ko nufinka bazaka nemi mgni ba Na gayama dole ayi dashen zuciya kuma mu anan ba,ayi dole zamu fidda kai India ne Dan acan muke da qorarrun likitocin zuciya
Zan nemi mgn Dr kuma zan fidda kaina India a bincikeni in takama ajene ma Na tabbatar zaka tsaya min a mddin Abba Na Toh meya baka son shi din ya Sani ?
Sabida zai cutu nikuma ban son abinda zai cutarmin dashi In yaji shima zai iya kamuwa da ciwon Na tabbatar Abba zaisamu matsala matuqar yaji cutar dake jikina kaima da kanka kasan rayuwara ta azgara ai shiyasa nafi son sai nasamu sauqi Ko kuma sabanin n hakan inyaso a gaya mai daga baya
Cikin sanyin jiki Dr yace haba dai Ahmad aishi cuta ba mutuwa bane zafin ciwo bai kawo qarshen numfashi Haka dai yai ta kontar mai da hankali Cikin wota 2 suka kammala shirye shiryen tfyar cikin sirri ba Tate da kowa ya saniba
Kullum Yusuf sai ya kira Ahmad da Adam dama wannan Al,adarsu kenan ko basa tare sai sun Kirayi juna da safe Dan jin lfyar juna da dare suyi sai da safe
Sosai Ahmad ke qarfin halinsa kan baya son kowa ya gane ciwon dake tare dashi Lkta da dama in yaje gida yakan zauna yasa Nenne shi a gaba yana tuna wanne irin hali zata shiga ran da babu shi sautari in yaji haka yakan fita kawai ya komai part dinsu da a yanxu ya zama nasu Usman yai ta kuka