Nida patient dina book two by mrs isham - Chapter 18
Nida patient dina book two by mrs isham Chapter 18: Nida patient dina book two by mrs isham Chapter 18. Godiya sukayi wa Allah jin daddadar labari biyu a…
3,924 words
Godiya sukayi wa Allah jin daddadar labari biyu a lokaci daya,ga labarin tana tafiya tafito daga hantsari ga kuma labarin cikin da take dashi kuma alhamdulillah abinda ke cikin na lafiya , sujjada Mr azaad yayi yana godewa Allah , mika mishi hannu doctor yayi ya ce " congratulations natayaka murna sosai" dayan hannunshi Mr azaad yasa a aljihun wandonshi daduk riga da wandon sun ɓaci da jini yafito da key din motar da sukazo dashi sabuwar Benz yau yafara amfani da ita daze kawo fanan asibiti ya ce " ga goron albirshir dinka dakamin " karban key din doctor yayi murna kamar ya kashe shi yama rasa ina zesa ranshi godiya kawai yake kwararawa Mr azaad, kowa awajan nan yana cikin farin ciki dangane da abinda sukaji doctor yafada yanzu jira sukeyi afito da fanan din , se anan ne suka samu nutsuwar gaisawa , Abba ne yakalli Mr azaad ya ce " azaad Yakamata kaje gida kayi wanka ka canza kayan nan kaga yanda yabaci da jini " " no abba bazan tafi yanzu ba se anfito da wifey" yafada yana zama , gaba daya tausayinshi ne yakamasu, saboda yana fuskantar kalubale musamman ma idan fanan ta tafi , se bayan 20mint aka fito da fanan dake kwance tana sanye da rigar asibiti kanta daure da bandeji hannunta an daura mata ruwa , fuskanta yayi fayau za'a kaita resting room mikewa Mr azaad yayi yabi bayansu zuwa room din, jawo kujera yayi ya ajiye agaban gadon nata , yarike hannunta yana kallon fuskanta murya adashe ya ce " am sorry wifey! kiyafemin laifina ne wannan" jakadiya abashiyya dake kallonsu ta dafa kafadarshi dagowa ya kalleta murmushi tayi mishi kafin ta ce " azaad wannan dalilin ne yasa nace kuyi gaggawan dawuwa gida saboda badan fanan ta tashi ba to wannan abun akan shayida ze faru , daga nan kuma zata rasa yaran dake cikin cikinta idan hakan yafaru Allah ne kaɗai yasan halin da shayida zata shiga, sarauniyarmu akoda yaushe ita tana taimako, abinda yafaru yau Allah yariga da ya rubuta haka daga kai har shayida kudena bawa kanku laifi " idonshi yayi ja sosai girgiza mata kai yayi kafin ya ce" abashiyya amma yanda tarasa jini sosai nayi tunanin zaace ana bukatar jini amma ga shi da ikon Allah ta dawo hayyacinta " abashiyya ta ce" eh tabbas tarasa jini sosai amma kasani sarauniya ba kamar sauran mutane ba ce , nan da anjuma zata farka gobe kuma zasu sallameku " sosai abashiyya tadinga kwantarwa Mr azaad hankali haryaji wani ɗan damuwar dake damunshi yadan ragu suna cikin tattaunawa, su ummi duk suka shigo ciki har a lokacin abashiyya na tare da Mr azaad amma babu wanda yake kallonta se shi kadai kawai,duk zama sukayi ummi tazauna agefen gadon fanan ummi ta ce " yaseer kadauki son kuje gida yayi wanka " " to ummi" yafada yarike hannun Mr azaad tashi Mr azaad yayi badan yaso ba , bayaso yayi nisa da ita fita sukayi shida yaseer din duk bayanshi sukabi da kallo ganin yanda yake tafiya cikin sanyin yanayi .
Ahanzarce yayi wanka yashirya yafito yasamu yaseer afalo ya ce " dude mutafi nagama " riko hannunshi yaseer yayi ya zaunar da shi ya ce " dude calm down please ka kwantar da hankalinka fanan yanzu na cikin koshin lafiya, yanzu ka tsaya ka sa wani abu a cikinka " ajiyar zuciya Mr azaad yasauke ya ce " banida lokacin wani cin abinci yanzu kawai mutafi karka ɓata min rai" yanda yaga ya haƙiƙice sesun tafi yasa cikin sauri ya shiga kitchen ya dauko mishi yogurt yabashi ya ce " dude ɗan Allah kayi hakuri kasha wannan se mu tafi kaga kai kanka yanzu baka cikin yanayi me kyau kamar fah zaka fadi " ganin yaseer baze barshi su tafi ahaka bane yasa ya karbi yogurt din yabude yakafa abakinshi seda yashanye tas yayi cilli da goran sannan ya ce " yanzu zamu iya tafiya ?" Yar murmushin yaseer yayi at least yasamu Mr azaad yasa wani abu a cikinshi ya ce " to muje " gaba Mr azaad yayi yabarshi abaya saukowa sukayi dede zasu fita a falon ya hangi maryam rakube abayan kujera , " keeee" yafurta yana tsaye yariƙe kugu yaseer kuma na gefenashi yanason ganin wayake ƙira fitowa tayi daga lungu kujerun jikinta na rawa ta ce " naaam" watsa mata harara yayi ya ce " karki yarda in dawo gidan nan in sameki " yana gama fadin haka yafice kare mata kallo yaseer yayi fuskanshi adan hade yabi bayan Mr azaad motar suka shiga yaseer yafara driving hankalinshi nakan titi ya ce " dude wancan yarinyar daga ina ? wallahi kallo daya na mata naji hankalina be kwanta da itaba, kamar wata mara gaskiya" kwantar da kanshi Mr azaad yayi akan seat din motar ya ce " nima haka dazun bayan dawuwarmu naganta agidan kallo daya na mata naji na tsaneta , banason ganinta jikina na bani kamar akwai abinda yakawota gidanmu " dukan siterin motar yaseer yayi ya ce" exactly wallahi dude dole abinciki yarinyar nan kasan yanzu duniya ba yarda ,bakowa ne zaka yarda dashi ba daga baya seka taimaki mutum yazo ya cutar dakai " sake maimaita maganar yaseer Mr azaad yakeyi acikin ranshi se yanzu ne ma yafara zargin wannan yarinyar tabbas akwai abinda yakawota gidan, zarginta yafara abisa abinda yafaru da fanan tuna maganar abashiyya yayi na kancewa abin akan anty shayida yaso faruwa sekuma fanan taje amaimakonta tabbas akwai wani abinda ba dede ba , haka yadinga tunani har suka iso asibitin, shiga cikin resting room din sukayi suka samu abba da baba basa nan , da sallama dauke abakinsu suka shigo mikewa Amira tayi ta bashi kujeran gaban gadon fanan zama yayi yariƙe hannunta yana kallon fuskanta, mama kam kunya ne ya kamata se kawar da kanta gefe takeyi saboda rike hannun fanan da Mr azaad yayi,ummi ta lura da haka murmushi tayi aranta ta ce " kunyan fanan ashe ga do tayi " karban wayarta tayi ahannun zeenat dake zaune waje daya tayi tagumi tazubawa fanan ido , kiran layin gida ummi tayi abu me aiki tadauka sanar da ita tayi girki sukawo itada driver asibiti tayi sannan ta katse kiran.
Kiran sallah la'asar akayi mazan suka tafi masallaci matan kuma sukayi acikin dakin bayan sun idar suka zauna a lokacin mazan duk sun dawo . Kusan atare anty firdausi tadawo hannunta rike da katon basket na abinci daddyn junior kuma na rike da junior haka abu me aiki itama hannunta rike da basket din abinci gaishesu abu me aiki tayi tana tambayar yame jiki suka bata amsa da sauki sannan ta zauna .
Kowa sa mishi abinci akayi yanaci amma banda mama da Mr azaad dake zaune yana rike da hannun fanan. Bayan kamar awa daya lokacin har biyar yayi hannunta dake cikin nashine yaji yana motsawa maida hankalinshi yayi kan hannun yaga yana motsi , ahankali tafara ware idanunta da tajisu sunyi mata nauyi kamar ba nata ba hasken dataci karo da shine yasa tamaida idon ta rufe sake jarraba bude su tayi nan tafara gani dishi_dishi , akan kyakkyawar fuskar Mr azaad tafara bude idonta da shima itadin yake kallo murmushi yamata itama tamayar mishi tana kokarin mikewa rungumeta yayi ajikinshi sannan yazaunar da ita , ya sa hannu yashafa gashinta ya ce " alhamdulillah wifey thank god you're awake" yagama magana yana manna mata kiss agoshinta , ganin ta farka ne yasa sukayi hamdala suna godewa Allah rike hannunta ummi tayi ta ce " my feena ya jikin naki ?" Muryanta da dan karfi saboda ta tashi taji jikinta da karfi kamar babu abinda yake damunta sedan ciwon kai kadan ta ce " da sauki sosai ummina " haka suka dinga mata ya jiki hairah da zeenat Amira duk dawuwa kusa da ita sukayi suka zauna kallon mama fanan tayi ta ce" mamaana " murmushi kawai mama tayi ta ce" na'am fanan ya jikin naki ?" " Dasauki mama " motsa hannunta dake cikin na Mr azaad tayi amma yaƙi sakinta shi babu ruwan shi bedamu da mutanen da suke cikin dakin ba . Hairah ce ta kalli zeenat ta ce" anty zeenat ina ya hafiz ?" Kafin zeenat tayi magana ma areef ya rigata da" hafiz na makaranta yanzu hakama maybe ko sun tashi kokuma sun kusa tashi " jin ya'yan nata na makaranta yasa bata sake cewa komai ba.
Kamar ba mara lafiya ba haka ta sake anata hira da ita duk sunyi farin ciki da ganin condition din nata is not critical, shide Mr azaad ƙala bece ba se aikin kallon yanda fanan take hira yakeyi yana jin dadi aranshi ɗan dawani abu yasameta besan yazeyi da ranshi ba .
Se yamma liris hafiz yadawo gida driver nayin packing yafita rike da school bag dinshi da laptop yashiga cikin main falo babu kowa gidan shuru beyi tunanin babu kowa ba yawuce part dinsu yashiga bedroom dinshi ya ajiye school bag din da laptop akan table yashiga toilet wanka yayi yafito yashirya yadau wayarshi acikin locker dan inze tafi makaranta ajiyeta yakeyi dukda makarantarsu makarantar masu kudine yara suna abinda suka gadama amma shi barin waya yakeyi agida saboda karatu ne yakaishi beze yi abinda wa'yanda suka taimaki rayuwarshi zasuji ba dadi ba. Part din ummi yashiga ze gaisheta yayi ta sallama a bedroom yaji shuru ba amsa se ya dawo main falo kawai yazauna yana danna waya , motsi yafaraji abayan kujera beyi tunanin komai ba yatashi ya leka bayan kujeran ganin mutum yayi tana zaune ta rakube mamaki ne yakama hafiz dan yasan shide be santa ba amma daga ina take to ya ce " sannunki" kallonshi Maryam tayi ta ce " inayini " be bata amsa ba se tambayar ta dayayi " me kikeyi anan ?" Inda_inda ta fara " uhmm ina zaune ne " "okay to kifito abayan kujera wani inya ganki ahaka zeyi tunanin bakida gaskiya ne " yafada yakoma inda yake yazauna besake bin ta kanta ba yaci gaba da danna wayarshi.
Alamun mutum yaji tsaye akanshi hakan yasa yaɗago kai , kallonta yayi tsaye akanshi tana kallonshi haɗe fuska hafiz yayi dan ta bashi haushi ya ce" ke meye haka zaki tsayamin akai bakisan babu kyau ba " wani irin munafikin murmushi maryam tayi batace mishi komai ba , kuma bata tashi mishi akai ba ganin hakane yasa yatashi akan kujeran dayake ya koma wani yaci gaba da abinda yake yi sake tsayawa tayi akanshi , kallonta kawai yayi bece komai ba yadauki wayarshi yabar falon yahaura upstairs kamar daga sama yaganta agabanshi ja da baya yayi ɗan yadan tsorata saboda yasan afalo yabarta maida kallonshi yayi fallon yaga tana nan a inda yabarta sannan yakalli wacce take gabanshi addu'a yafarayi acikin zuciyarshi kafin ya ce " meye kike bukata awajena ? Meya kawoki wannan gida?" Murmushi tayi mishi kafin ta ce " abinda nake buƙata awajanka shine ranka , abinda yakawo gidan nan kuma shine kashe duk wani wanda yake cikin wannan ahalin " duk adan tsorace hafiz yake amma afusace ya ce " Allah baze taba baki nasara ba , kuma nima bazan bar hakan yafaru ba sede koke koni! Koki kasheni ko ni in kasheki" dariyar bosawa tayi harda rike ciki ganin yanda yake da karfin hali kyasta yatsunta tayi nan take kayan jikinta da ita kanta ta sauya, fara ce sol tana sanye da bakaken kaya ,matsetsen riga da wando baƙi jikin riga da wandon akwai chains , ga uban hills shima baƙi , gashin kanta brown color ne curly bakinta yasha baƙin janbaki , shiganta da komai nata na yan America ne , ja baya yakeyi tana biye dashi ta ce " zamu gani yau kaiɗin jarumine ko kuma ragone " juyawa hafiz yayi yana neman abinda ze buga mata mopper ya hango yadauko ya buga mata akanta nan take mopper ya karye sake ja da baya hafiz yayi ya ce " to ke din wacece ? meye mugun nufin ki akan mu?" Hannunta ta mika nan take yayi tsayi tashaƙo wuyar hafiz ta dagashi sama kafin ta ce" okay tunda abinda kake so ka ji kafin ka mutu , sunana Jessica kelvin " tana fadar haka ta kara shaƙe mishi wuya sannan taje can saman upstairs tana shirin wurgoshi ƙasa, kallon ƙasa hafiz yayi yaga irin mugun nisa dayake dashi da ƙasa yasan tabbas ta wurgoshi mutuwa zeyi hakan yasa muryarshi da baya fita sosai saboda shaƙeshin datayi ya ce " hairahhhhhhhhhh" dariya tayi ta ce " itakuma wacece haka shin kana ganin zata ceceka ne ?" .
Suna zaune suna hira lokacin su Abba da baba ma sun dawo suna cikin dakin , zuruf sukaga hairah ta mike jikinta ne yadau rawa , ko wannensu da al ajabi akan fuskokinsu suke kallonta, zubewa tayi aƙasa jikinta na ci gaba da rawa mikewa dukkansu sukayi suna tambayarta meya faruwa amma ba ta basu amsa ba ya Usman yasa hannu yadagota yazaunar da ita akan gadon fanan yana mata magana " hairah meyake damunki ?" hawaye takeyi jikinta na tsuma , fanan ce ta ce" kowa yanda yi shuru na wasu lokuta " mikawa hairah hannunta tayi duka biyu , daura hannayen hairah tayi da nata hannun lokaci daya jikinta yadena rawan dakyar ta iya cewa " yayana ! Zata kashemin yayana " fanan ta ce "ki fadamin meye kike kallo " ta ce " na naganta itadin makira ce kuma mara imani " sake matse hannun fanan tayi ta cigaba da magana " ta shaƙe yaya hafiz zata wurgoshi ƙasa daga upstairs" jin abinda tafada ya tsorata su de yanzu suka tuna da babu kowa agidan dasauri fanan ta ce " su waye agidan bayan hafiz din sannan akan waye kike magana?" Hairah ta ce " babu kowa agidan securites ne dasuke cikin compound babu wanda yasan abinda yake faruwa , yayana kuma ita da shine acikin falo yanzu haka tana gab da wurgoshi ƙasa" tana gama fadin haka Abba dasauri yazaro wayarshi yakira number securites din gidan nan take suka daga yasanar dasu abinda yake faruwa , kusan su ashirin suka shiga cikin falon lokacin da Jessica ta gansu dariyar mugunta tayi sannan ta ajiye hafiz a ƙasa shafa wuyanshi yayi yana tari ganin tana gangarawa downstairs ne yasa yafara rarrafawa yasulale yashiga part din Mr azaad daga nan ya bullo ta garden sannan yafito compound baba me gadi ne kaɗai se driver suka rage acikin gidan dakyar ya iya kwalawa driver kira suka shiga motar yace mishi yakaishi gun ummi da gudu driver yafisgi motar .
Gangarowa ƙasa Jessica tayi ta tsaya a tsakiyarsu wani daga cikinsu ne yafara tunkaronta duka daya ta mishi yazube aƙasa yasuma , dukansu takeyi baji ba gani kaff dinsu kaff seda ta sumar dasu da muguwar duka , sannan ta fito compound tunda baba me gadi yaganta yaji tabashi tsoro tunkafin ta ce yabude mata kofa yabude . fita tayi tana kallon titin daya kasu gida uku nan take tagano hanyar da su hafiz sukafi ,gudu tafarayi tana ɓacewa kamar walkiya tana bin bayansu .
Hairah dake rike da hannun fanan tana kallon duk abinda ke faruwa a falon ta ce " dukkansu tamusu duka sannan ta sumar dasu , yayana kuma yanzu haka yashigo asibitin nan tana binshi abaya " tana karishe maganar da takeyi tasake hannun fanan, ta mike tsaye , tana magana da hafiz dake gudun ceton ranshi domin har cikin asibitin ta biyoshi mutane se kallonta sukeyi kamar sun samu tv , yana gudu itakuma tana tafiya cikin kwanciyar hankali.
Gudu yakeyi yana hakki yana jin kwantaccen da hairah takeyi mishi can yace " hairah naga wasu kofofi gudu biyu wanne zanshiga wanne ne kuke ciki ga ta nan abayana" tsayawa hairah tayi abakin kofa ta ce " na farko zaka shigo yaya " sude al'amarin ya matuƙar girgizasu tunani suka farayi suna tambayar kansu shin hafiz da hairah sudin su waye ?.
Da karfin gaske ya turo kofar yarungume hairah dake tsaye abakin kofa, fashewa tayi da kuka tana " yayana " suna a haka Jessica tashigo dakin ja da baya sukayi dagudu hairah taje ta buya abayan mama shikuma hafiz ya boye a bayan Mr azaad harde hannunta tayi akirjinta tana kallonsu kamar yanda suma ita suke kallo seyanzu suka gane ashe Maryam din da Abba yatsinto ce innalillahi wainna ilaijiraji unnn lallai duniya babu yadda aciki se ka taimaki mutum yazo ya cuceka shisaka yanzu taimako yayi karanci , zuciyar Abba se kuna yakeyi yana kallon Maryam yama kasa magana amma har cikin ranshi beyi danasanin taimaka mata da yayi ba domin shi tsakani da Allah yataimaka mata , kallon Mr azaad tayi ta ce " ka turo yaron bayanka ko kuma ta sanadiyyar shi kowa na dakin nan ya rasa rayuwarshi , mugun kallo fanan da Mr azaad suke watsa mata, ganin beze miko mata shi bane yasa taje gaban Mr azaad din tasa hannu zata jawoshi Mr azaad yakai mata damka a wuya sannan ya dagata sama ya hade kanta da jikin bangon dakin ta zube aƙasa, daman haushinta yakeji domin yanzu yasake tabbatarwa Ita ce nan ummul aba isin abinda yafaru da fanan tana kokarin mikewa daga bugun datasha Mr azaad ya taka ruwan cikinta so yakeyi kawai yaga ta mutu ko hakan ze rage mishi raradin abinda yakeji , sa hannu yayi ya sake damko gashin kanta , ɓacewa tayi ta dawo bayanshi ta ce " kana tunanin zaka gwada min kai jarumine hahaaa" tafada tana dariya nuna anty shayida ta yi da hairah da hafiz ta ce " dake , dake dakuma kai duk sena kasheku ayau din nan " a tsorace anty shayida ta je taboye akusa da Abba . Baba ne ya ce " baiwar Allah menene hadinki damu ? wani laifin mukayi miki ne ?" Abba ya kalli baba yace " ni ne nan nakawota gida da niyar taimaka mata ashe annoba nadauko bansaniba" Maida kallonta kan baba tayi ta ce " babu abinda kukayi mini nidin yar saƙoce nazo gudanar da abinda aka aiko nine " ummi ta ce " to waye ya aiko ki wajen mu " fanan da ranta yayi matuƙar ɓaci ne ta ce " yi shuru ummina kar wanda yasake ce mata ƙala yanzu zatayi da nasanin zuwa aikan da aka mata " tana magana tana zuro ƙafafuwan ta kasa mikewa tayi tsaye tana bin Jessica da kallo dama tun farkon ganin da ta mata taji tsanarta lokaci daya ashe akwai dalilin haka, tunkaro fanan tayi tana kallonta daga sama har kasa cikin shakiyanci ta ce" oho nagane wato ke ce sarauniya? Amma yanaga bakiyi kama da sarauniyar da kowa yake shakka ba yanda ake labarin ki se naga ba haka kike ba , kinmin kama da matsoraciya sede balaifi kinada kyau kam, dukda bake nazo kashewa ba wancar me cikin nazo kashewa sekuma kema kina da ciki sekiyi kokarin taimaka mata ta hanyar zuwa a madadin ta , hakanma ba laifi tunda kema kinada cikin " tayi magana tana kallon anty shayida dake bayan Abba ,murmushi fanan tayi ta ce" kwantar da hankali, ai gane asali ba daga fuska take ba se angwada ake ganewa . shin kinason ganin asalina? amma fa kisani in kika gani ba lallai ba kici gaba da rayuwa ba " cewar fanan da idonta yakoma kalar fari tayi magana tana damkar wuyan Jessica kokarin kwatar kanta Jessica tafara tana fisge_fisge amma takasa kwatar kanta a hannun fanan, matso da fuskanta fanan tayi daff dana Jessica,sannan ta zaro idonta da suka koma fari tass babu digon baƙi aciki , hasken cikin idonta ne yafara shiga cikin idon Jessica nan take tafara konewa ta ciki ihu tafarayi . Fanan ta ce" nasan zaki bawa wa'yanda suka aiko ki labari inkun hadu a lahira " tana gama fadin haka tasake Jessica ta fadi ƙasa nan take jikinta yafara karkarwa kamar wacce aka jonawa shocking jikinta nafitar da hayaƙi me tururi haka tadingayi har ta koma kwarangwal daga nan kuma takoma toka tabace.
Dukkansu ajiyar zuciya suka sauke ganin sun rabu da ita , jinjina mata zeenat dake ɓoye abayan mama tayi ta ce " aikin ki na kyau anty fanan" hararanta fanan tayi ta ce " kema naki nakyau saboda kin iya ɓuya kam " dariya sukayi .
Kallon hafiz fanan tayi ta ce " lallai hafiz kaiɗin jarumine kayi na mijin kokari " hafiz da se yanzu hankalin shi yakwanta ganin fanan ta gabama da Jessica yayi murmushi kawai yaje bayan mama yariko hannun hairah suka zauna akusa da ya usman ya ce" fatan babu abinda yake damunki " kai ta gyada mishi sannan ta kwantar da kanta akan kafadarshi , sude yanzu tunda sun samu sun rabu da Jessica damuwar su susan su hairah sudin menene suke dauke dashi koɗe karya sukayi musu adangane da asalinsu.
Babane ya ce " hafiz shin ya akayi kuke iya magana da junanku batare da waya ba kuma hairah take iya ganinka aduk inda kake ? " Ajiyar zuciya hairah da hafiz suka sauke atare domin sun san dama dole sesunyi zargin wani abu , hafiz ya ce " mahaifinmu yakasance babban wanzami ne dake taimako sosai kuma yana bada magani , yana aiki da aljanu to tun muna yara wata rana yadawo gida da daddare muna bacci yasa mamanmu ta tashemu , zama mukayi agabanshi ya ce " hafiz ga hairah kanwarka ce ko bayan ranmu nasan zaka iya kula da ita " sannan ya yafito da wasu abubuwa acikin leda wanda nida hairah bamu san meye aciki ba, sunce ledar yayi nan take mukaga wasu abubuwa guda uku biyu masu zubi da kunne daya kuma kamar ido , miƙa min kunnen yayi yace in rike shi da karfi sannan yabawa hairah ido da hannu ya ce itama tarike, bamufi mintuna 30 da rikewa ba muka nemi abubuwan mukarasa domin ji mukayi babu su ahannun namu ashe cikin jikinmu yashige , se babanmu yace mana wannan abinda yabamu shine zezama garkuwa garemu duk nisar duniyar damuke zamu iya magana da junanmu sannan hairah zata na kallona inde wani mugun abu ze faru ne kaɗai hakan ze kasance, tundaga wannan lokacin in waninmu yana cikin hatsari mukan iya jiyowa har musamu wa'yanda zasu taimaka , wannan shine " shuru sukayi suna jinjina wannan lamarin ta wani bangaren za'a iya cewa hakan ze taimakawa yaran amma ta tawani bangaren hakan tsubbu ne tunda bawai dashi aka haife su ba rana tsaka yasaka musu shi ajikinsu , abba ne ya ce" Allah yajikansu da rahama " suka amsa da ameen.
Washe gari doctors din ganin jikin fanan da sauki sosai yasa ya rubuta mata sallama , sungama kimtsawa mazan suke jira su shigo su tafi wa'yanda suka kwana da fanan ummi ce se anty shayida , su mama tun jiya bayan mangrib suka koma gida zeenat kuma Abba ne yacewa Mr azaad da fawwaz su maida su gida , Mr azaad da yaseer suka shigo cikin asibitin ga securites suna binsu abayana rike da manyan kwalaye yaɗuwa yayi da doctor din yabashi result din fanan, shiga cikin resting room din sukayi suka bar securites din suna rabawa majinyata da kuma nurses din asibitin kudi kamar yanda Mr azaad ya sanar da su , duk wani wanda yake cikin asibitin seda yasamu dubu dari dari , haka suka dinga kwararowa Mr azaad da family shi adduo'i , saboda awannan lokacin kafi karfin abinda zakaci arana daya ma ka godewa Allah gashi yau sun samu wani bawan Allah yaraba musu kyautar dubu ɗari _ɗari babu abinda zasu gode masa dashi sama da addu'a.