Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 10

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 10

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 10: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 10. Abin ya dame shi matu?a, ko ya kira numberta bata ?auka, yau kwana uku bata…

3,364 words

Abin ya dame shi matu?a, ko ya kira numberta bata ?auka, yau kwana uku bata zuwa school, ya shiga damuwa matu?a, ya rasa ina zai sanya ransa, abubuwa sun ha?e mashi, ga shi idan ya kira number Jaish bata shi ga, yana cikin tashin hankali a kan hakan! Sannan ga wani tashin hankalin da ya faru a Dubai wanda Rizwan ya sanar da shi ya ce kada ya gayawa kowa dan suna iya ka bakin ?o?arinsu dan su shawo kan matsalar, sannan yanzu ga shi baya samun damar ganin sanyin idaniyarsa bare ta rage mashi ra?a?in da yake ji, har zazza?i sai da ta kama shi, a halin yanzu ya fi shiga damuwa sosai a kan Jaish, shi ne a ransa, ?o?ari yake yi ya ?an samu lafiya ya ji kwarin jikinsa sai ya bi bayansa, dama ?asar England ya ce mashi zai je, so yasan hotel ?in da ya sauka ma, dan da ya sau?a ya tura mashi sa?on a kan ya sau?a lafiya da sauran bayanai, coz yanzu yana son ne jikinsa ya ?an warware daga damuwar da suka yi mashi yawa sai ya bi bayansa ya je ya gani shin aiki ne ta yi mashi yawa har ya kashe wayarsa ne ko kuma dai wani abin ne ya faru?.

A safiyar yau ma sai da King ya tambaye shi ina Jaish? Da ya rasa me zai ce mashi sai ya ce ya tafi ?asar Brazil wajensu uncle Jahiz yau da safen, ya rasa amsar da zai basu ne yasa ya ce masu haka, dan kullum idan suka tambaye shi sai ya ce masu bai dawo office da wuri bane, ya yi dare shiyasa yana dawowa ya kwanta, da sassafe kuma ya sake fita saboda aiki ta yi mashi yawa, kullum amsa ?aya shiyasa yau ya canza amsar.

Sosai King ya yi fa?a a kan ya za'ayi ya yi yafiya ba tare da ya sanar da su ba? Idan wani abin ya je ya farufa? Allah ya tsare!. Sai hakuri Jawad ?in ya rin?a bashi, ya yi ?o?arin kiran number Jaish ?in amma bata shi ga, sai ya yi tunanin ko dai yana cikin jirgi bai sauka bane yasa wayar bata shiga ba, da haka dai ya samu suka rabu da King ?in.

Yana barin part ?in King ya kira number uncle Jahiz ?in nasu, wato ?an autan Akka kenan kaninsu King. Yana kiransa bai ?oye mashi komai ba ya sanar da shi gaskiya, sannan ya ?aura da cewa King zai kirasu dan ya tabbatar da cewa Jaish yana tare da su, idan ya kirasu dan Allah su amsa da e, idan ba haka ba sun san halin King sarai. Da yake uncle ?in nasu ma irin uncle Abbas ne, yana kaunarsu sosai kuma ya iya goya masu baya, sai ya yarda a kan e lallai za'ayi yadda suke so, amma Jawad ?in ya yi saurin nemo in da Jaish ?in yake, cikin raunin zuciya ya amsa da tabbas zai yi duk yadda zai yi ya dira a ?asar England gobe ko jibi domin ya duba shi, idan ba haka ba za'a samu matsala, da haka dai suka bar zancen suka shiga hirar duniya.

Suna tsaka da yin hiran ne Momma ta kira numbersa, sallama ya yi wa uncle ?in nasu ta hanyar sanar da shi cewa Momma na kiransa bari ya ?auka, okey ya amsa mashi kafin su yi sallama ya ?auki kiran nata.

"Jawad ka sameni a parlourna yanzu". Shi ne abin da ta fa?a. Cikin sanyin murya ya amsa mata da okey ga shi nan zuwa.

Katse kiran ta yi shi kuma ya nufi part ?in nata. Zazza?i sosai yake ji a jikinsa, da alama shakuwarsa da Jaish yasa yake yi mashi ciwon wahalar da ya shiga, kun san idan mutun biyu suka sha?u, in ma mata da miji ne ko ?an uwa, in dai shakuwarsu ta kai sha?uwa zaku ga ko basa tare idan ?aya ya shiga wahala ko tashin hankali sai kuga shi kuma ?ayan ya kamu da wani ciwo, ba dai ciwo mai tsanani can can bane, amma sai ku ga yana ta fama da ciwo, daga ya ce kansa na ciwo, sai ya ce zazza?i, mutuwar jiki, ko zafin jiki, haka zai yi ta fama da rashin kwarin jiki har sai randa wancan ya fito daga cikin matsalar da ya shiga, ana samun irin haka sosai a cikin al'umma. So shi dai ga shi yana yi wa Jaish jinya ba tare da ya sani ba.

A parlournta ya iskota zaune cikin kwalliya irin na hamsha?an gimbiyoyi, da alama ma wajen King zata je, dan kwalliyar ta musamman ce.

Saman carpet ya zauna ta kusa da ita kafin ya ?aga mata gaisuwa cikin girmamawa. Amsa mashi ta yi fuska ba yabo ba fallasa, sannan ta ?aura da cewa. "Jawad ina Jaish? Yau kwanansa hu?u kenan ban sanya shi a idanu na ba, kuma sanin kanka ne baya ta?a yin kwana guda cur ba tare da ya zo in da nake ba, na kira numbersa bata shiga, na je part ?insa daren jiya misalin karfe 1 ban samesa ba, ?akin nasa ma ya nuna mun alamar kamar ya kwana biyu babu mutun a ciki, saboda curtains na windows and balconynsa duk sun nuna alamar an kwana biyu ba'a ta?asu ba, kuyangun da suke gyara ?akin nasa basa ta?a wajen, meyake faruwa? Ina ya tafi?".

Wani irin yawu mai wuyar wuce ma?ogwaronsa ya ha?iye da kyar, sannan ya ?an ?ago da kallonsa izuwa kanta. Ya rasa me zai ce mata, yasanta da kaifin ?wa?walwa, sannan ita ta renesu shi da Jaish ?in, yana yi mata karya zata ganosu, ta yi masu farin sani, ko da sunan wasa ya yi mata magana ba dai'dai ba tana ganewa cikin ?an sakani bare da gaske, to yanzu ya zai yi da ita? King ya fita sauki, shi bai cika tsawwalawa sosai ba, ko ya gane ba gaskiya ka fa?a mashi ba yana kawar da kai sai ya yi bincike da kansa, ita kuma sai ta tirkeka ka fa?i gaskiyar da bakinka.

"Shirun da ka yi mun Jawad ya tabbatar mun da abin da zuciyata take raya mun, tun jiya bani da kwanciyar hankali, ina jin fa?uwar gaba da fargaba kamar wani abin ya samar mun ?aya daga cikinku, duk na kira ?an uwanka a waya suna lafiya, kai kuma muna tare da kai a nan, shi ka?ai ne ban samu damar yin magana da shi ba, kuma shi ka?ai ne idan na tuna shi nake jin fa?uwar gabana ya tsananta, ka gaya mun gaskiya me yake faruwa?".

Wani irin nisawa ya yi wadda da ka jita kasan yana cikin mawuyacin hali, muryarsa har wani ?an sarkewa ta yi, ?an gyaran muryar ya yi kafin ya ce. "Momma babu abin da ya samu Jaish, In Sha Allah yana cikin aminci tare da kariyar Ubangiji, tafiya ya yi izuwa ?asar Brazil wajensu uncle Jahiz........"

Bai ?arisa maganar ba saboda wani irin kallo da ta wurga mashi yasa ya shanye sauran maganar tasa. "Jawad ka manta cewa da Mommarka kake magana ne? Sam babu kamshin gaskiya a maganarka, fa?a mun gaskiyar dai ina sauraro".

Ha?i?a sai da ya ji kirjinsa ya bada dum dum, dama yasan halinta sarai, ba zaka mata karya kuma kasha lafiya ba, sai ta kamoka, bashi da za?in da ya wuce ita dai ya gaya mata gaskiya ko dan ta tayasu da addu'a idan ma wani abin ne ya samu ?an uwan nasa.

Ya sha madarar mamakin ganin fuskarta bai sauya ba duk da ya gaya mata gaskiyar halin da ake ciki, shiru ya yi yana tunanin ko dai dama tasan gaskiya ne? Ko dai gwadasa kawai ta yi?.

Katse mashi tunanin nasa ta yi da cewa. "Kana mamaki ya aka yi ban shiga damuwa ba duk da na ji abin da yake faruwa ko?".

Da sauri ya gy?a mata kai alamar e. "Dama nasan dole wani abin ya sa?a, domin kai da Jaish tamkar ?an biyu kuke, tun kuna yara idan ?aya ya yi rashin lafita da safe to ?ayan zai kwanta nasa ciwon da yamma, tun jiya da naga yanayinka na fahimci kana taya Jaish ciwo ne, ka dawo wani sukuku da kai, kai da kanka baka san me yake damunka ba, hakan ce ma yasa na bi?i ganin Jaish ?in dan na tabbatar da abin da yake damunka, shin ciwon gaskiya ce ko dai ciwon sha?uwa ce? Yanzu na tabbatar, coz ban yi mamaki ba, kuma ban ji cewa Jaish ya aikata ba dai'dai ba, a jikina ina jin ba lafiya yake ba, amma koma menene ni ban haifi rago ba, jarumta a jininmu take, a ko'ina yake ina da ya?inin da izinin Allah zai fidda kansa, dan babu rago a zuri'armu, bamu san komai ba sai jarumta, dan haka kai ma ka warware ka taya shi da addu'a, Allah kuma yasa ya cinma burinsa a kan abin da ya je nema, zan yi mashi addu'a, sannan bana son ka gayawa kowa wannan magana, dan sanin kankane a gidan ba kowace magana ake yinta da mutane ba, wani lokaci is better ka ha?iye magana a cikinka sai ya fi maka sauki, ko daddynku kada ka gaya mashi, dan zai shiga damuwa, and lastly ka gaya mun gaskiya duk da ni kai'na ban yarda da abin da zuciyata ta gaya mun ba, amma zanso in ji gaskiya daga bakinka".

Dakatawa da yin maganar ta yi tana kallon face ?insa. Tattare nutsuwarsa waje guda sosai ya yi, dan ya ji ta ?auko wani maganan na daban.

"Ka fa?a mun gaskiya kai ka shiga ?akin Jannat kwana uku da suka wuce?". Tana magana tana kara kura mashi idanun, dan ta kalli yanayin da fuskarsa zata yi.

Zaro idanu ya yi kafin ya ce. "Momma ina zuwa ?akin Jannat, amma kwana uku da suka wuce ban shiga ba, kwana hu?u da suka wuce dai na shiga da daddare sosai wuraren karfi 12 haka, har daddy ya zo ya samemu a tare na ?uya a cikin toilet, bayan haka kuma babu wani abin".

Tabbas ta yarda da maganarsa, tasan gaskiya ya fa?a, dama kuma tasan ba zai aikata wannan ?anyen aikin ba, ta san halin ?a?an nata sosai, amma sai ta ce. "Me kake zuwa yi a ?akin nata a irin wannan lokacin haka?".

?an kame kame ya fara yi mata yana faman sunkuyar da kai.

"Yau kuma ka dawo Jaish ne da kake ?oye mun fuska? Yaushe kunya ta ratsa jinin jikinka kai ma? Jaish ma ina ganin rashin kunya ce take damunsa da idan ya zo yake ?oye mun fuska yake wani sunkuyar da kai, ashe ko dai hakance tun da gashi kai ma ka fara ?oye fuska".

?an ?a?alo murmushi ya yi kafin ya ce........

??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????

????RAWANIN ?? ZALINCI ????

????????????????

FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????

?????????? 23/9/2024.....??????

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????

??STEP TWO....??????

E___________9

?an ?a?alo murmushi ya yi kafin ya ce. "Kai our Momma, bafa kunyarki nake ji ba, abin da zan gaya maki ?in ne yasa na fara jin kunyarki a yanzu".

"Mmmmmm to dai fa?i na ji menene? Me yake kaika wajen ?ata da tsakar dare haka?".

"Kai Momma addu'a nake zuwa yi mata fa, daga nan sai mu ?an yi hira ka?an haka, bafa dayawa ba, kuma a hiran dukka karatu nake koya mata". Ya fa?a yana ?ago da kallonsa izuwa kanta.

Wani irin kallo da take binshi da shi mai nufin ni zaka yi wa karya ne yasa shi sakin siririn murmushi tare da ?an dafa kafafunta kafin ya ce. "Kai our Momma, to zan fa?a maki gaskiyar".

"Oya go ahead". Ta fa?a tana kara kallon face nasa da kyau, while shi ma kallonta yake yi.

"Magana ta gaskiya zan gaya maki, dan ko zan ?oyewa kowa ban da ke our Momma, zance ta gaskiya son Jannat nake yi kuma ina fatan ta zama matata, amma da alama bata sona, dan yau kwana uku kenan tana guduna ba tare da ta tsaya ko kallonta na yi ba, taki tsayawa ko tambayarta me nayi mata take gudu na ma taki, ban san me yake faruwa ba, ban san laifin da na yi mata ba, amma a baya tana nuna mun kauna, kwana hu?u da suka wuce ma da na je ?akinta da daddaren lokacin da zan koma nawa part ?in sam bata so hakan ba, ta so na zauna mu yi ta hira har wayewan gari, duk da bata fito ta gaya mun hakan ba ni naga hakan a cikin kwayar idanunta, amma haka dai na danne na koma part ?in na, na rasa me yasa yanzu take guduna, sam bata sonna, ban kuma san laifin da na yi mata ba, please Momma ki tayani da addu'a, wlh ina kaunar Jannat sosai". Ya kai karshen maganar cikin wata iriyar raunanniyar murya.

Saboda kaifin ?wa?walwa irin nata nan take ta gane lallai lallai akwai mai son shiga tsananinsu a cikin gidan nan, tabbas akwai mai son rabasu, to wanenen? Ta tambayi kanta, sai dai abin da bata gane ba a nan shi ne meyasa Chuchu take gudun Jawad ?in tun da ba shi ya shiga ?akin ya yi ?o?arin keta mata mutunci ba? Dole wani abin ya sa?a, dole akwai wata makar?ashiya da basu san menene bane.

Shiru ta yi tana tunanin ta gaya mashi gaskiyar abin da ya faru domin ya yi ?o?arin yi wa Chuchun bayani yadda zai shawo kanta ne? Ko dai ta yi shiru sai ta gama bincikenta?.

Voice ?insa ne ya katse mata tunanin da take yi ta hanyar cewa. "Momma please ki tayani da addu'a, wlh ina kaunar Jannat sosai, yau tsawon kwana uku kenan ban sanyata a cikin idanuna ba, ki taimakeni na ganta, idan ba haka ba zan iya cutuwa". Cikin raunin murya tamkar zai saka mata kuka ya yi maganar.

Ajiyar zuciya ta sauke tare da fara magana. "Eyeee wato Jawad sam baka kunyata ko? Kai tsaye kake gabatar mun da yadda kake kaunar ?ata ko? Ba irin jin kunyar surukai da ake yin nan?".

Kamar zai sa mata kuka ya ce. "Momma please ki daina fa?in hakan mana, ni ban yarda ba, ke mahaifiyar miji kike bana mata ba, ki bar batun surukuwar nan, mummy ce zata zama surkuwa, ni yanzu please Our Momma a samo min mafita, in dai ba so kike yau na ki cin abinci na zauna nan nayi ta yi maki kuka ba to a ha?a ni da Jannat ?ita, Kila ma Momma ke kika ?oye mun ita saboda kina son na gaya maki me yake tsakaninmu, to dai na fa?a maki surukarki ce, dan Allah a ha?ani da ita ko na minti biyar ne".

Dan siririn murmushi ta saki kafin kuma ta sake ?aure fuska sosai kamar bata ta?a yin dariya ba, a tsanake ta fara bashi labarin abin da yake faruwa dukka, bata ?oye mashi komai ba, dalilin da yasa Chuchu take gudunsa duk ta gaya mashi da abin da ta ganewa idanunta, daga karshe ta rufe mashi da cewa lallai lallai ya kula sosai, sannan ya kara tsananta addu'a, yanzu haka Chuchun tana part ?in Aunty MieMie, ya je ya sameta shi yasan ta yadda zai shawo kanta, kada ya yi ?asa a gwiwa, ya jajirce sosai zai yi nasara.

Sosai ya shiga tsananin ?acin rai da jin anyi ?o?arin yi mata fya?e ne, jikinsa har wani tsuma yake yi, bai damu da cewa zarginsa take yi a kan hakan ba, damuwarsa a yanzu shi ne ya gane wanda ya yi mata hakan domin ya hukuntasa, uncle Taheer ?anin mama baya ?asar, ya tafi wajen iyayensa dan sada zumunci bare ya ce ko shi ne ya yi mata hakan, Jaish ma baya nan, kuma koda yana nan ma ko giyar wake ya sha ba zai aikata hakan ba, a mazan gidan dai shi ka?ai ya saura a gidan. Tashin sense!!

Ganin alamar ransa ya ?aci sosai ne yasa ta fara rarrashinsa tare da ?ara mashi kwarin gwiwa. Ina ai yanzu duk maganar da take yi ma bata shiga kunnuwansa, ya yi nisan kiwo wajen tunanin mafitar yadda zai kama wanda ya yi mata wannan aikin, fa?i yake yi a cikin zuciyarsa wlh idan ya kama wannan mutumin koma wanenen sai dai uwarsa ta haifi wani.

Tsabar ya afka kogin tunani da tsananin ?acin rai bai ma san time ?in da ya mi?e ya nufi hanyar fita ba, ko sallama bai yi wa Mommar ba, da alama ma ya mance cawa a wajenta yake, kawai ya nufi waje. Har ta bu?i baki zata kira sunansa sai kuma ta fasa, saboda ta lura baya tare da ita, ko ta kirasa ba lallai ya jita ba, dan haka sai ta bishi da kallo tare da fatan nasara.

Yana fita kai tsaye wajen Aunty MieMie ya nufa, zuciyarsa na tafarfasa sosai, tsikar jikinsa har tashi yake yi.

Tsabar ya shiga damuwa ko sallama bai yi ba ya afka cikin parlourn, babu kowa shiru, da yake already ya san in da zai sameta a part ?in idan ta shigo sai ya nufi stair case kai tsaye.

Sama ya haura, kai tsaye ya nufi wani katafaren luxurious bedroom wanda yake zaton zai sameta a ciki. Babu ko sallama ya tura kofar ya afka ciki.

Tana kwance a saman gado, bata jima da gama yin waya da Rizwan ba, da ga ita sai kayan barci, da alama a part ?in ta kwana, har yanzu kayan barcin jiya ne a jikinta, bata yi wanka ta canza ba, haka zalika bata fito ta ci abinci ba, tana kwance shiru tana fuskantar celling ?in ?akin. A tunanin Aunty MieMie ma barci take yi shiyasa bata zo ta ce mata ta tashi ta yi breakfast.

Jin motsin mutun yasa ta sauko da kallonta izuwa bakin kofar room ?in, a tunaninta ma Aunty MieMie ce. Tana sauke idanunta a kanshi ta wani irin zabura tare da mi?e zaune a dubu, nan take ta yi ?asa da kallonta tare da fara ?an kame kame, tsabar razana har kerma jikinta ya fara yi.

Tura kofar room ?in ya yi ya rufe, sannan ya tako a hankali ya nufo in da take.

Kara tsorata ta yi da ganin ya tura kofar kuma ya tunkaro ta, muryarta na karma yana sarkewa ta fara fa?in. "Yah Jawad dan Allah ka yi hakuri, na shiga ukuna, Momma, mummy kuzo ku ceceni, Aunty MieMie kizo Yah Jawad zai kashe ni, dan Allah Yah Jawad idan wani laifin ma na ya yi maka ka yi hakuri, wlh ba zan sake ba, dan girman Allah........." Ka sa ?arisa maganar ta yi dan ganin ya zauna a saman bedside drawer tare da zuba mata idanu, tana magana muryarta na sarkewa, ga shi ta datse idanu gam tare da sanya hannunta ta tare fuskar tata duk wai dan kada ya ta?ata.

Jin ya zauna a kusa da ita ba tare da ya ta?ata ko ya yi mata magana bane yasa ta ?an bu?e idonta guda ?aya a hankali dan ta saci kallonsa. Ganin yana zaune shiru ya kura mata idanu ne yasa ta mai da idon nata ta rufe tare da fara yin tunanin to ko dai ya zo bata hakuri ne? In kuwa haka ne wlh ba zata saurare shi ba, kuma ba zata sake jin maganarsa ba, daga yau ta dai'na kula shi.

Shiru shiru almost 10 mins bai ce da ita uppan ba, da ta gaji da datse idanun nata ne sai ta bu?esu tana kallon ?asa, taki yarda ta ?ago su yi ido hu?u, tunane tunane kala kala ne a ranta.

"Jannat". Ya ambaci sunanta a wani irin low voice sosai. Kin amsawa ta yi kuma taki ?ago kai, ko ?an motsawa ma bata yi ba tamkar ba ita ya kira ba.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Yanzu Jannat ko wata aka ce maki na shiga ?akinta da nufin na keta mutuncinta zaki yarda?".

Still bata motsaba kuma bata amsa ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull