Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 11
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 11: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 11. Cigaba ya yi da cewa. "Jannat kenan da gaske zaki yarda da cewa zan iya shiga…
3,276 words
Cigaba ya yi da cewa. "Jannat kenan da gaske zaki yarda da cewa zan iya shiga ?akin wata ma ba ke ba?".
Har yanzu dai shiru bata amsa ba. "Shirunki ya nuna mun cewa kin yarda kenan ni ne?". A wannan karon kai ta gya?a mashi alamar yes she's agreed!.
?an zaro idanu ya yi tare da bayyanar mamaki a face ?insa. Hannayensa ya kai ya ri?o nata cikin nasa. Wani irin zabura ta yi tare da yin baya a ?ari tana ?o?arin kwace hannayen nata. Bai saketa ba sai ma ?ara ?an?ame ?an hannayen nata ya yi, ?asa ?asa kaman mai ra?a ya furta. "Jannat menene hujjarki na cewa tabbas ni na shiga ?akinki? Ki gaya mun! Idan na ji hujjar taki na kuma gamsu da ita zan kar?i laifin da bani na aikata na, zan yarda da cewa ni na aikata".
In a low voice sosai ta fara magana kamar wadda aka sanya dole. "Wlh Yah Jawad kai ne! Kai ne ka shigo mun ?aki, face ?inka ne, jikinka ne, komai nake n........." Bata iya kai karshen maganar ba sakamakon sauke kallonta da ta yi a kan hannayensa dake ri?e da nata. ?an zaro idanu ta yi tare da juyar da nata hannayen ta ri?o nasa, kurawa hannun nasa idanu sosai ta yi, har da ?an ?agosu tana kara dubawa da kyau, duk bata gamsu ba sai da ta fara jujjuya hannun nasa.
Kura mata idanu ya yi yana binta da kallon mamaki, abin ya ?an ?aure mashi kai. "Lafiyarki kuwa Jannat?". Ya fa?a tare da zame hannayen nasa daga ri?on da ta yi masu.
Da sauri ta ?ago da kanta ha?e da kallonta izuwa garesa, a ?an ru?e ta furta. "Yah Jawad ina tabon cizon da na yi maka na fasa maka fatan hannu? Izuwa yanzu wlh wannan cizon ba zai yiwu ace ya warke ba, dan na fasa fatar wajen har ta yi jini, ko da jinin ya tsaya da zuba ba zai yiwu a ce babu tabo ba". Tsabar ta ru?e har ta kare maganar tana kallon cikin kwayar idanunsa, yau ba sunkuyar da kai, da alama bata san ido cikin ido suke kallon juna ba saboda ru?u.
"Jannat ni babu wanda ya cijeni bare tabo ya zauna, a yaushe aka yi hakan? Yaushe kika cijeni?".
Still har lokacin tana kallon cikin tsakiyar kwayar idanunsa, mamaki ne ya kara bayyana a saman fuskarta, ta kara shiga ru?ani ta furta. "Ranar da ka shigo ?akin nawa ne ina ?o?arin kwatar kai'na na cijeka har na fasa maka fatar hannunka, wlh kuma ya yi jini sosai".
Wani irin sanyi ya ji ta ratsa shi, Allah ba azzalumin bawansa bane, ga shi cikin sauki ya kawo mashi mafita ta yadda zai wanke kansa, Allahu Akbar, gaskiya ne Ubangiji baya barci, kai ko gyangya?i baya yi bare barci, Allahu Akbar, Allahu Akbar. Ya fa?a a cikin zuciyarsa.
Mi?ewa tsaye ya yi tare da fuskarta gabas, ya zube gwiwowinsa a ?aya ya gabatar da sujjudur shukur tare da mi?a ?inbin godiya ga Ubangiji. Bayan ya mi?e ya koma ya zauna, cikin hanzari ya ri?o hannayenta a cikin nasa, cikin tsantsan farinciki tare da murmushi a saman face ?insa ya furta. "Allahu Akbar my Jannat, Ubangiji ya wankeni daga zargin da kike yi mun, na gaya maki ba ni na shiga ?akinki ba, jannat ko ?ar wani can da ban ba zan iya keta mata mutunci ba bare ke da kike kanwata, jinina, farincikina, wannan ke kin sani ba tarbiyar gidan nan bane".
?an sakin jiki ta yi da shi ka?an, izuwa yanzu ta fara yarda da cewa e ba shi bane, amma kuma da yake shi she?an munafuki baya son yaga ana zaman lafiya sai ya rin?a zuga zuciyarta yana sanya mata wasi wasi a kan idan ba shi bane to wanene? Ga kamanninsu ?aya, komai nasu iri ?aya ne da wanda ya shigo ?akin.
"Yah Jawad amma idan ba kai bane ya aka yi komai naku kai da wancan ?in iri ?aya? Na kasa yarda da hakan wlh".
?ara matsowa ya yi dab da ita, har lokacin tana kallon cikin idanunsa, mamaki da al'ajabin abin yasa ta kasa kawar da kallonta daga kansa, ta kasa iya tunano ko abu guda ?aya da ya banbanta Jawad ?in da wanda ya shigo ?akinta, babban tambayar da yake cikin zuciyarta ma shi ne, idan ba shi bane to wanenen? Ita dai tasan shi ba twin's bane bare ta ce ko ?an uwansa ne.
"Tunanin me kike yi kuma Jannat?".
?ar razana ta yi tare da ?an kyafta idanunta ka?an, ta sake kura mashi ido tana kallonsa. A hankali ta zame hannunta ?aya daga ri?on da ya yi mata ta kai hannun nata saman kumatunsa, ta dage ne tana son nemo banbancin dake tsakanin shi da wancan, tun da dai taga babu tabon cizon da ta yi wa wancan a hannunsa.
Zuba mata idanu ya yi yana kallonta, shafa kumatun nasa ta fara yi har izuwa saman lallausan sajensa, ita kanta da ta?a fatarsa a yanzu sai ta ji yana da banbanci da na wancan, wancan fatarsa tauri gareta kamar jikin samudawa, shi kuma Yah Jawad jikinsa da laushi sosai. Sam bai yi ?o?arin katseta ba, ya zuba mata idanu yana kallon yadda take ta shafa mashi kumatu har izuwa hannunsa.
Shiru ta lulu?a duniyar tunani, nan take kuma ta ji kanta na sara mata, ta gaza gane me yake shirin faruwa da ita ne, wani irin jiri ne ya fara ?o?arin ?ibarta, kanta ya kulle ruf.
Sarai ya lura da ta shiga halin ru?ani sosai, hakan yasa ya ?an jawota jikinsa, murya ?asa ?asa sosai ya ce. "Baki yi addu'ar barci lokacin da zaki kwanta ranar ba ko?".
Kai kawai ta gya?a mashi alamar e. Cikin nutsuwa ya yi mata fa?a a kan wasa da addu'a, sannan ya bata labarin da Momma ta bashi na abin da ya gani, daga karshe ya rufe mata da cewa ta zage da yin addu'a sosai, kada ta kuskura ta yi wasa da addu'a, idan ba haka ba wlh akwai babbar matsala sosai.
Kasa iya amsa mashi ta yi, ta kwanta a jikinsa shiru, izuwa yanzu ta yarda ba shi bane ya shiga ?akin nata, saboda ta gano ko fatar jikinsa da wancan ma ba ?aya ba ne, ga ba tabon cizon da ta yi mashi. Tsoro da ru?a ne ya ?ara kamata yasa ta ?ara shigewa jikinsa, yau ta shiga uku taga Yah Jawad guda biyu take fa?a a ranta......... Ni kam na ce ai dama dole ki tsorata, irin wannan ru?ani haka? Mutun ?aya ya zama biyu, kin ma yi ?o?ari da baki suma ba bayan jin wannan labarin.
Turo kofar da Aunty MieMie ta yi ne yasa shi saurin kai kallonsa wajen. ?an zaro idanu ta yi tana kallonsu, hararar wasa ya wurga mata lafin ya ce. "Ya da shigowa ?akin mutane ba neman izninsu?".
Dakuwa ta ware yatsunta biyar ta watsa mashi da hannu kafin ta ce. "Me kazo yi a nan? Kazo kana tsara yar mutane ko? To zo ka wuce".
Da sauri Chuchun ta yi ?o?arin barin jikin nasa jin voice ?in Auntyn tasu. ?an?ameta ya yi ya hanata barin jikin nasa. Cikin zolaya ya furta. "Aunty MieMie gaskiya zaki takura mun, yanzu me kika zo yi a nan?".
"Zo ka fita nace ko na kira Akka, ke kuma Chuchu zo ki wuce ki yi breakfast ki yi wanka, uncle Dr yana zuwa ya dubaki, dan ina son gobe ki je school".
Dawo da kallonsa kan face ?inta ya yi tare da fa?in. "Dama baki da lafita ne yasa 3 days baki zuwa school?".
?oye fuska ta yi a kirjinsa dan kada Aunty MieMie ta ganta, ?asa ?asa ta ce lafiyarta lou, zuwa ne bata son yi yasa ta ce masu bata da lafiya.
"Kus kus ?in me kuke yi?". Cewar Aunty MieMie.
"Kash Aunty MieMie wai ba zaki barmu mu ?an zanta ba, ina ruwanki tsakanin yaya da kanwa, ni ki tafi zata zo". Ya fa?a yana juyo da kallonsa a kanta. "Babu in da zanje, zo ka wuce ka tafi ko na kira Akka, ke kuma zo nan ki je ki yi breakfast". Tana magana tana wurga mashi harara, saboda su abokan wasa ne sosai.
Raba jikinsu ya yi, ya ri?o hannunta tare da sauko da ita daga saman gadon. "Zo mu tafi kada ta kira mana wannan masifaffiyar tsohuwar ta ji?a mun aiki. Ya yi maganar tare da nufar kofar fita hannunsu cikin na juna.
"Tun da ba zaki barni na yi hira da farincikina ba ai sai mu tafi tare ko?". Ya fa?a bayan ya zo ra?awa ta gefenta zai wuce.
Harara ta bishi da shi tana fa?in. "Oho dai kaje dai, ko na kira wayar Akka".
"Ni Aunty MieMie ki daina kiran sunan tsohuwar nan, kina sanya na ji kai na na sara mun". Ya karesa zancen nasa a waje, saboda yana tafiya ne bai dakata ba.
Juyawa ta yi ta bi bayansa tana zolayarsa a kan Akka ce maganinsa, kuma sai ta sanar da ita yana tare mata jika a lungu ya kalailameta da kalamai.
Duk zancen da suke yi suna ta raha tare da tsokanar juna sam Chuchu bata a tare da su, ta afka duniyar tunanin ya aka yi aka samu mai kama da Yah Jawad a gidan nan? Wannan abin ya tsaya mata a rai matu?a. Sam bata san lokacin da suka isa saman dining table ?in ba, ta lulu?a duniyar tunani, sai da ta ji spoon na abinci yana ta?a lips ?inta ne ta farga ashe sun iso wajen cin abincin har ma ya zuba masu ya fara bata a baki.
?ago idanu ta yi sai saman fuskarsa, wani irin fa?uwar gaba ta ji ya ziyarce, lokaci guda ta fara jin sauyin yanayi a cikin zuciyarta a kansa, taga ya kara yi mata kyau sosai. Bu?e baki ta yi ta fara kar?ar abincin, ita kam Aunty MieMie ta kama kanta abinta ta basu wuri.
A can cikin babban family part kuwa, sai shiryawa Auta take yi tana tsantsara kwalliya mai kyau cikin Turkey gown brown color mai matu?ar kyau, ya ji duwatsu sosai a jikinsa, sai kyalli yake yi, kun san yanda kayansu yake ai, daga ta sama ya yi dai'dai da jikinsu, ya bi shape ?insu, daga wajen kugunsu zuwa ?asa kuma a bu?e a bage kamar umbrella. Kayan yana da kyau sosai, yana ?ara fito masu da ainahin kyansu.
Tamkar wadda zata je wani wajen mai muhimmanci, sosai ta tsara kwalliya, ta ?aure gashin kanta kashi biyu, ta kuma kitsa bakin gashin tare da ?aure karshen jellar gashin da roba saboda tsantsin gashin zai sanya kitson nata ya warware, ta saki jelar a saman shoulder ?inta sun zubo mata har saman ciki. Ba karya kam ta ha?u iya ha?uwa, ta ?auko wani malesian cap mai tsadar gaske ta sanya a kan nata, sai ta ?ara kyau sosai. Flat smooth shoe ta sanya a kafafunta, wanda ko tana taka ?asa ba zaka ji tafiyarta ba.
A hankali ta fito waje, kai tsaye ta hau elevator ta yi kasa mai gaba?aya, sai sauri take zubawa tana yi tana waige waige kamar wata maras gaskiya. Kai tsaye wannan wajen hutawa na musamman ?in na mussan dake cikin family part ?in ta nufa, wajen wasu kyawawan tsuntsaye dake cikin keji ta nufa a hanzarce. Tsuntsaye masu matu?ar kyau da ?aukar hankali ne suke birjik a wajen, a kallah kejunansu sun kai guda 20 a wajen, tsuntsaye ne different types and colos.
Kai tsaye wajen wasu fararen tattabaru ta nufa, guda biyu ta damko bayan ta bu?e kejin, ta ri?osu da kyau a hannunta, suna ta faman ?o?arin kwacewa su tashi sama, amma ta ri?e su gam dan kada su gudun.
Da sauri ta nufi waje, har da ?age doguwar rigarta dake sharar ?asa saboda sauri. Wani hanya da ya ra?a da wajen da ake gabatar da gasar tsaren doki duk sati ta nufa, a hanzarce take tafiya kamar zata kifa, tana yi tana waigawa bayanta dan taga shin akwai wanda ya ganta ne? Sai la?ewa take yi a duk lokacin da taga wani warriors ya zo zai gifta, da alama bata ?ullo gaskiya ba.
Wasu jiga jigan warriors ne suke gadin gate ?in in da ta dosa ?in.
Maya?a biyu ne a wajen, sun ji horarwar yaki sosai, commander Zafar ya yi aiki a jikkunansu wajen basu horo mai lafiya, sun ginu tamkar wasu dakuna, ga fa?in kirji da baya kamar na zaki, ganinsu da ido kawai sai sun tsorata ka, suna tsaitsaye cikin kayan ya?insu, ?aya daga cikinsu yana sanye da hular yakinsu a kansa, ?ayan kuma ya cire shi, sai hira suke yi da junansu, dukkaninsu larabawa ne tas tas da su, ga kyau sosai da bakar gashi ha?i da saje.
Suna ganinta tun bata iso wajen ba suka tinkarota da sauri. ?ara ?aga kafa ta yi wajen yin sauri, dan bata son su tareta a hanya, ta fi son ta isa in da suke. A kusa da bakin gate ?in suka ha?u. Cikin girmamawa ?aya daga cikinsu ya ce. "Barkanki ranki ya da?e, shin kina da bu?atar wani abin ne?".
Shiru ta ?anyi tana tunanin abin da zata ce masu, dan wlh yau ko zasu yi yaya sai ta je gonar ?awisun daddynsu, so take yi ta je ta gani kuma ta ?auki hutona da su, sai dai kash saurinta yasa ta manta ma bata ?auko wayar da zata ?auki hoton da shi ba, kuma har izuwa yanzu bata tuna cewa babu waya a hannunta ba.
King Zuhair ya hanasu kusantar gonar ba tare da shi bane saboda sanin halinsu, basu ta?a shiga cikin gonar ba, ita kuma Auta ta ?aukarwa kanta alkawarin sai ta shiga taga me a ciki, akwai mugayen namun dawa sosai a ciki, akwai kuma dabbobi masu ban sha'awa sosai a ciki, irin su ?awisu akwai su dayawa kala daban daban, su kuma ba'a cikin keji suke ba, an sakesu suna yawo a wajen, akwai su jimmina, su kifaye kala kala na gida dana waje wa?an da suke cikin wani ha?a??en glass mai matu?ar ?aukar hankali, an zuba masu ruwa sai shawagi suke yi abinsu, akwai tsuntsaye kala kala, ga su dila, Zomo, bushiya, a manyan dabbobi da aka killacesu a cikin keji akwai su zakuna, damisai, kuraye, da dai sauransu, duk wasu dawakai da King yake hawa suna cikin wajen an kewaye masu nasu ?angaren daban ana kula da su sosai, akwai dai tarin abubuwa dayawa a ciki, wasu suna cikin keji, wasu kuma an sakesu suna ta shawagi a cikin katafaren filin tsakiyar wajen.
To ita bata san saboda ha?arin da yake a ciki bane yasa King ya hana su ko tinkarar wajen, ta ?auka baya son ta yi hoto da su ?awisan ne kawai, shiyasa ta saci hanya ta zo ba tare da sanin kowa ba.
Ganin ta yi masu shiru ne yasa suka sake tambayarta cikin girmamawa a kan ko dai tana bu?atar wani abin ne?.
?ago idanun ta yi ta zuba masu kallo, cikin dabara ta saki tattabara ?aya ya tashi sama, kukan gulma ta sanya masu a kan lallai su kamo mata tattabararta kafin nan su zo ta gaya masu abin da take bu?ata a wajensu. Mutun ?aya ne ya yi saurin bin bayan tattarabar da ta tashi sama ta bi ta wajen tseren dawakai da suke gudanarwa a cikin masarautar duk sati.
?ayan warriors ?in kuma sai ya hau bata hakuri yana fa?in za'a kamo mata shi ta yi shiru. Sake fakar idanunsa ta yi ta saki ?ayar tattabarar ma, kara fashewa da kuka ta yi mai sauti tana fa?in ?ayar ma ta sake guduwa lallai lallai ya kamo mata abinta. Sanin ita wacece da kuma girman kaunar da ake mata a gaba?aya fa?in kingdom ?in yasa ya bi tattarabar da gudu yana mai gaya mata zai kamo mata amma dan Allah ta yi shiru.
Ai kuwa suna barin wajen ta yi saurin ?arisawa wajen gate ?in. ?o?arin tura gate ?in ta yi dan ta bu?e, amma ta ?asa saboda karfi da nauyi irin ta kofar, kamar zata rushe da kuka ta sanya dukkanin karfinta tana turawa.
Ko gezau kofar bata yi ba, bakin ciki kamar ta ha?iyi zuciya, sai waigowa take yi tana kallon bayanta dan taga ko suna dawowa. Ta yi iya yinta kofar ko motsawa bata yi ba, tamkar dasata aka yi, fara bin jikin kofar da kallo ta yi, can ta hango wajen key ?in datse kofar, ashe a rufe take, sai dai tsawonta ba zai kai ta iya ta?a wajen key ?in ba, dan kofar tana da tsawo kuma key ?in a sama yake. Ciccikowa da kwallah idanunta ya yi dan haushi, kamar ta ?aura hannu a kai ta zunduma ihu.
Juyawa ta yi cikin sanyin jiki, har zata nufi hanyar komawa kuma sai wani dabara ya fa?o mata, da sauri ta juyo tare da janyo kujerun da warriors ?in suke zama a wajen ta kawo shi wajen saitin key ?in, takawa ta yi ta haye dan ta ?ara tsawo. Ta kuma yi sa'a tsawonta ya kai wajen makullin, da sauri ya kama key ?in dake manne a wajen ta hau mur?a shi, tana yi tana waigo bayanta.
Tana bu?e key ?in ta hau tura kofar, Da kyar ta iya bu?esa, a hanzarce ta afka ciki, tana shiga ta datse kofar da wasu keys da suke ta ciki, a kallah key zasu kai uku a jikin kofar ta ciki, sai ta sanya ?aya wai dan kada idan warriors ?in suka dawo su zo su fitar da ita, yau ta ci alwashin sai ta kewaye cikin wajen gaba?aya duk girmansa, waje ne fa mai matu?ar girma sosai, amma wai sai ta kewaye dukka.
Tafiya ta fara yi a cikin wajen tana kallon halittun dake wajen, wasu halittun su bata dariya, wasu su bata tsoro, wasu kuma su sanyata afkawa kogin mamaki. Sai da ta iso wajen wasu ?anana ?ananan fararen zomaye wa?an da suka so su yi kama da wolf ?inta ne ta tsaya, nan ta fara neman wayar da take tunanin ta ?auko shi dan ta yi hoto, sam babu wayan a jikinta, kuka ne kawai bata yi ba, amma ta ji haushin manta wayar, ta so ?aukar zomayen hoto.
Wucesu ta yi ta cigaba da tafiya ba tare da tasan in da ta nufa ba, kwatsam ba zato ba tsammani ta ganta a gaban bushiya, da gudu ya yi kanta yana son kama kafarta ya gwaguya, kun san halinsa dama, ga iya sake kifiya.
Ai kuwa watsawa ta yi a guje tare da sanya hannu ta toshe bakinta dan kada ta yi ihu wani ya jiyota. Garin gudunwa bushiya ta je ta fa?a cikin dawakan da ba'a ?aure suke ba, ai kuwa watsewa gaba?aya dawakan suka yi a guje, wasu suka yi kanta, a haukace ta zunduma ihu tare da fara ?o?arin cetar ranta.
To bari dai muga zata iya cetan ran nata kuwa? Ga shi da iya ?o?ari irin nata har da rufe kofar da key, ko taya ma za'a shigo a kawo mata ?auki idan an ji ihun nata ma kenan? To ni dai bari na le?a ?asar DARK WORLD mu gani, wata kila kafin mu dawo dawakan nan sun gama take Gimbiya Zunaira ta yi laushi tilis tun da bata jin magana.......??
DARK WORLD????????
Yar karar azaba ta saki kafin ta furta. "Am so so sorry sir". Slowly aka sakar mata hannun nata, wani irin haki take saki tamkar wadda ta yi gudu ta ?oshi, kamar wadda ake horar da cikin kashi da ?argon jikinta, har wani gumi take ha?awa kamar ba lafiya ba, abin da abin mamaki, yadda kuka san azabtar da ita ake yi, har sauyawa kalar idanunta ya yi izuwa jan kala.