Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 13

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 13

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 13: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 13. "Ayya gajin Bappanmu kin ga ina jin tsoron aljaninnan, dan Allah ki fito, wlh…

3,203 words

"Ayya gajin Bappanmu kin ga ina jin tsoron aljaninnan, dan Allah ki fito, wlh ba zan iya shigowa ba, ki zo kinji ko? Idan muka je kiwo gobe zan ciro maki kanya".

Kin fitowa ta yi, ta kafe sai Mahnoor ?in ta shigo in dai tana son su je. Tana surutu tana ?an murgu?a baki, gashin idanunta kam ba'a magana, suna tsaitsaye zara zara dasu na rashin kunya.

Cigaba da yi mata magiya daga waje ta yi, amma ta ki fir, sai cigaba da mulmulawa bawan Allah kumatun nasa take yi. Ai kuwa kamar daga sama ba zato ba tsammani kwatsam ya wani irin zaro idanu waje, ga idanun nasa sun yi jajir tamkar wadda aka watsawa barkono a cikinsu.

Subhanallah wani irin ihu da Mahreen ta zunduma mai sautin toshe jin mutun, ta yi wani mahaukacin razana, dan bata yi excepting zai bu?e idanunsa ba, sam bata kawo hakan a ranta ba. A dubu ?ari ta mi?e ta fasa waje tana ihu.

Ai kuwa tun da ta zunduma ihu farko Mahnoor ta arta waje a guje, dan a tunaninta aljanin ne ya tashi ya kama Mahreen ?in yasa take ihu, a maimakon ta shiga ciki ta kai kama agaji idan ma hakan ne, ina ai sai ta yi ta kanta a ?ari, dama kamar a kan kaya take, tana jin tak ta arta waje a dubu abinta.

Haba wa hajiya Mahreen ana firowa sai kofar gida, ihu take har da cire takalma da ?an'kwalin kamar su ne suka sanya Jaish ya bu?e idanu, yau har da karanta suratul fatiha a cikin ihun nata. Bata zame ko'ina ba sai gidan kakansu Ar?o, duk ta zubar da takalma and ?an'kwali a hanya.

Can ta isko Mahnoor har ta isa gidan sarkin tsoro, tuni har ma ta shige cikin ?akin kakarta mace tana kuka da hawayenta duk da ita bata ga abin da Mahreen ta gani ba, ihu kawai ta ji amma har da kukanta. Kakar su dake cikin madafa bata san da zuwan Mahnoor ba dan ita bata yi ihu ba sai hawaye gudowa kawai ta yi, sai da Mahreen ta shigo a haukace tana ihu ne duk wata halitta mai rai dage gidan har da magensu sai da suka fito, manyan mata an shigo waje ai dole a fito a tarbeta, Mahreen manyan ?asa.

Mata uku ne a cikin gidan, so bukkoki hu?u ne da na Malam Ar?o biyar kenan a cikin gidan. Harta Ar?o sai da ya fito a hanzarce jin irin ihun da ta afko masu cikin gida da shi.

Da sauri kakarta ta yi ?o?arin kamata tana kiran sunanta, ina kin basu ha?in kai wajen ri?ota da suke yi ta yi, fa?i take. "Hande mi woni, ina Nennenmu? Ashe da gaske ne aljani Bappa ya kawo gida, wlh aljani ne idonsa ba irin na mutane bane, kamar wuta idanunsa suke, na shiga uku, ga idanunsa wlh sun kai ukun na Adda Mahnoor a girma, kato kato da su, yau kam mutuwa zan yi na kalli idanun aljani".

Sai ?o?arin nutsar da ita suke, amma ina yadda kuka san iska haka take yawo a sama dan sun rirriketa, sai ta ?age kafa sama tana wuwwuntsiyasu tana ihun ina Nenne.

Nennen nasu dake tsaka da barci ne ta tsinkayo muryar ?ar tata a cikin kunnenta, a hanzarce ta zabura ta taso ta fito, kusan a tare suka fito da ainahin Kakansu Mahreen ?in.

Matan Ar?o uku ne, so biyun da suka tari Mahreen ?in suna ?o?arin rarrashinta kishiyoyin kakar tasu ce, ita kuma ainahin wadda ta haifi Nennen tana ban?aki lokacin da Mahreen ?in ta afko masu, so yanzu fitowarta kuma a tare da Nennen kenan.

Kanta suka yi a tare da gudu kakar tata ta ainahi tana fa?in. "Cikinku wace shegiya ce ta dakar mun jika?".

Sake Mahreen ?in suka yi, ai kuwa a guje ta yi wajen Nenne tana ihu. Ar?o na ?o?arin yin magana ?ayar matar wadda ake kira da Diddi ce ta rigasa da cewa. "Ai babu shegiya a cikin gidan nan ko kin manta ne? Ko wacce da ubanta".

"To rasa kunya ?erar tanka, wacece ta dakar mun jika na ce?". Cewar kakan Mahreen da suke kira da gwaggo.

Sa kai ?ayar matar da suke kira da Inna ta yi ta wuce izuwa nata ?akin abinta, bata tofa ko uppan ba, da alama bata son hayaniya.

Su kuwa suka tsaya kace nace, gwaggo ta zage sai ta ji uban waye ya dakar mata jika.

Inna na shiga ?akinta ta ci karo da Mahnoor a zaune tana ta kuka, dan ba karya ta tsorata. A hanzarce ta ?ariso wajenta. "Mahnoor lafiya me ya faru?".

Tana ganinta ta yi maza ta mi?e ta fa?a jikinta tare da kara sautin kukanta. "Mahnoor ki gaya mun me ya faru mana? Meyasameki?".

?asa yin magana ta yi tana cigaba da yin kukanta. Nasan zaku yi mamakin ganin Mahreen ta nufi wajen gwaggo ita kuma Mahnoor ta nufi ?akin Inna ko? To barin baku ka?an daga labarinsu dan ku fahimci ina muka dosa. Mahnoor Inna ce kakarta a gidan, ita ta haifi mahaifiyarta, ita kuma Mahreen gwaggo ce kakarta ita ta haifi Nennenta.

Mahaifiyar Mahnoor bata gidan Bappa kwairaga, Inna ?a?anta biyu rak a duniya, daga mahaifiyar Mahnoor mai suna Halima, sai kuma kaninta Ibrahim. Bappa kwairaga mahaifiyar Mahnoor ya fara aura, ita ce matarsa ta farko, Nenne kawarta ce da aka maye mashi gurbin mahaifiyar Mahnoor da ita bayan ya rasata, ?a?an kishiyoyi suke da Mahaifiyar Mahnoor da Nenne, kuma kunga gidan Ar?on ba zaman lafiya suke yi ba, akwai kishi a tsakaninsu, lokacin da Bappa ya rasa mahaifiyar Mahnoor Mahnoor ?in tana yarinya bata wuci 2 years ba, shiyasa Ar?o ya bashi auren Nenne dan ta ri?e Mahnoor ?in tunda ?ar ?ar uwarta ce, suna ganin zata kula da ita sosai.

Hakan kuma aka yi, da farko Nenne ta ri?e ta sosai da sosai, tamkar ?ar cikinta, har ta haifi Mahreen, ta ha?asu ta ri?e da amana, sai dai kash mahaifiyarta ta canza mata tunani daga baya, a in da suka fara sakawa ?inbin uban tulin dabbobin bappa ido, daga nan ta fara sanyata ta fara juya ri?on amanar da take yi wa Mahnoor izuwa nanzalinci, duk lokacin da Inna ta yi wa gwaggo ba daidai ba, sai gwaggo ta ce da Nenne ta azabtar da Mahnoor, ta hakan suke cusawa Inna bakinciki, dan Mahnoor ita ce ka?ai jikarta, ita take kallah ta tuna ?arta, bappa kwairaga kuma yaki bata Mahnoor ?in ta ri?e, wai shi ma yana tuna mahaifiyarta a duk lokacin da ya ?aga idanu ya kalleta, so ba zai iya rabuwa da it ba.

Sannan su gwaggo suna bakincikin irin kauna da bappa yake nunawa Mahnoor ?in dan maraicin rashin uwa, sai ya zamana yana kula da ita sosai fiye da kansa, kuma yana ?o?ari dannewa fa baya nuna banbanci a tsakaninsu da Mahreen, amma saboda shegen makirci irin na gwaggo ta zuga Nenne wai Bappa ya fi kaunar Mahnoor a kan Mahreen, hakan yasa ta kara tsananta wahalar da Mahnoor ?in.

Duk kuma wannan abin da yake faruwa Bappa ko Ar?o ba wanda ya sani a cikinsu, bappa bai san ana wahalar mashi da ?iya ba, kuma bata ta?a gaya mashi ba baiwar Allah, idan ya yi tafiya har talla Nenne take ?aura mata, amma da ya dawo zata dai'na ta nuna tana kaunarta ma a gaban idanunsa.

Ita kuma Mahreen da kuke ganin nan, rikici suke yi da Nenne, saboda ita tana kaunar ?ar uwarta, tana sonta fiye da tunaninku, ba ruwanta da zancen su ?a?an kishiyoyi ne, babu wannan a ranta, kuma kullum Nennen nata tana gaya mata ba ?aya suke da Mahnoor ba, Mahnoor ?ar kishiyarta ce dan haka dole ta tayata kishi, ita kuwa ta ce ba dai ubansu ?aya ba? Ai tun da ubansu ?aya ita kam ba ruwanta da wani banbanci uwa, koma yaya ne Mahnoor ?ar uwata ce.

Idan Nenne tasa Mahnoor aiki to fa ko zata mutu sai Mahreen ta tayata, bata yarda ta barta ta yi ita ka?ai, duk fa?ar da Nenne zata yi mata zata ce wlh ita sai ta taya ?ar uwarta, tun Nenne tana fa?a har ta hakura, dan ta lura Mahreen zata tona mata asiri wajen bappa idan ta matsa.

Wannan dalilin yasa Mahreen ?in take cewa bata son Nennen ta dawo gidan, dan tana wahalar da Mahnoor, ita kuma bata son hakan, shiyasa ta ce kada Nennen ta dawo, ita fa Mahreen wlh sam bata son zalinci, bata son abin da zai ta?a mata Mahnoor ?inta, ?ar uwarta ?aya tilo a duniya. Bata bin bayan rashin gaskiya! Ga iya kwatar ?ancinta abinta, ko ba karfi akwai baki, da bakinta zata ?aure mutun har igiya ya saura!!.

Wannan a takaice yadda suke kenan, fatan kun gane?.

Lallashinta sosai Inna ta yi har barci ya ?auketa a kwance a saman cinyar Inna ba tare da ta gaya mata dalilin yin kukanta ba. Ita kuwa Mahreen da kakarta gwaggo ta jata suka yi ?aki bayan sun gama masifar tasu Ar?o ya fice ha basu waje dan yasan sun saba. Da kyar suka iya lallashin Mahreeh ta yi shiru, ai kuwa tana yin shiru ta yo waje sai wajen ?ar uwarta Mahnoor a ?akin Inna, suna kiranta tana ce masu tana zuwa bari ta dubo Mahnoor, ?akin Inna ta shige abinta.

Ko da ta zo Mahnoor ta yi barci har ma Inna ta kwantar da ita a saman gado ta fita waje dan cigaba da aikace aikacenta. Ita ma tana shigowa ta kwanta kusa da ?ar uwar tata tana fuskantar saman zanar bukkar kamar mai tunanin wani abin.

A can ?angaren Jaish kuwa, bayan ya bu?e idanu da Mahreen ta tsorata ta guda sai ya sake mayar da idanun nasa ya rufe, da alama baya cikin hayyacinsa sosai sosai, dan da alama bai ma san in da yake ba, ya rufe idanu ya kwanta shiru har barci mai nauyin gaske ta ?aukesa. Bappa kuma a lokacin ya fita zuwa wajen wani abokinsa likitan gargajiya irinsa dan ya ?auko shi ya zo ya yi nashi gwaje gwajen ko Allah zai sa Jaish ?in ya farfa?o, shi ya yi iya ka yinsa tun safe shiru, shi ne ya ce bari ya jarraba kiran ?ayan dattijon likitan, dama su uku ne kawai likitocin gargajiya a kauyen, to ?aya ya rasu, kuma shi ne babbansu dama, yanzu sun rage su biyu ne kawai likitocin kauyen.

Da yake wajen yana da ?an nisa sai da ya sha tafiya kafin ya isa wajen, sai gab da mangariba suka ?ariso shi da likitan. Har lokacin barci Jaish yake zubawa.

Sun sha madarar mamakin ganin yana numfashi, kun san dama already bappa ya barosa baya numfashi, bama su da tabbacin yana raye ko ya mutu. Da sauri bappan ya yi yo waje dan ya tambayi Mahnoor yaushe wannan bakon ya farka?. Sai dai ko da ya shiga cikin ?akinsu basu nan, mamaki ya fara yi a kan ina suka tafi? Can ya tuna sun ce zasu je wajen Nennensu, tuna hakan yasa ya ce nan suka tafi sai kawai ya fito ya koma nasa ?akin.

Sun yi murna sosai na ganin bakon nasu yana numfashi, dan haka sai suka hau aikin da zasu taimaka wa rayuwarsa shi da likitan abokin nasa.

TO ALLAH YA BAKA LAFIYA OUR PRINCE JAISH.

??????????????????????????????????????

GIDANSU KHADIJAH ????

A takaice dai yau aka yi arba'in na baban Zainab, Maman Zainab dai in short hukuncin ?aurin rai da rai aka yanke mata, a hakan ma dan ta ce bada gangan ta yi hakan ba, amma kotu bata yarda da kalamanta ba, saboda su Hauwa sun fita makirci, sannan kuma su sun ?auki makirin lauya da ya kware wajen take gaskiya a kullum, hakan yasa dole ta hakura ta kar?i kaddararta na ?aurin rai da rai.

Zainab kuwa tana gadon asibiti saboda ciwo, Sadiq ya ?auketa ya kaita asibiti ba tare da sanin su maman Haidar ba, kuma tsabar basu kaunar Allah ko nemanta basu yi ba da suka dawo daga kotu, ko a jikinsu kamar ba ?an mutun ne ya ?ata ba, sai ma tunanin abin da zasu ci suke yi.

Shi kuwa Sadiq ya kaita asibiti ne dan jikin nata ya yi tsanani, kuma tsawon wannan lokaci da ta fara jinya tun rasuwan baban nata babu wanda ya sai mata ko paracetamol a cikin ?an uwan baban nata, Maman Hanif dai bata cikin gidan, dan kuwa kaca kaca suka yi da Maman Haidar shi ne ta wuce gidan mijinta, ita kuwa Maman Haidar taga wajen zama, ta share mazaunanta ta yi zamanta, ko ina gantalallen mijin nata ne kuma ya shiga sai Allah ya san mashi. Ita dai Maman Hanif ta ce wlh abin da baban Zainab ya yi masu a rayuwa bai cancanci irin wannan sakayya daga garesu ba, a halin yanzu addu'a yake da bu?ata ba duk wannan balaja'un da suke ta yi suna up and down within karya and gaskiya ba, shi ne fa Maman Haidar da yake ita ce babba ta hauta da ruwan masifa, ai kuwa a wannan karon bata raga mata ba, ta yi mata wankin babban bargo har da ce mata babbar banza sai girma a shekaru babu girman kwakwalwa, daga karshe ta ce zata ?auki Zainab su wuce da ita gidanta ta je ta yi jinyarta kuma ta cigaba da ri?eta tun da dai ita kam Maman Haidar shashasha ce babu tunani a cikin kanta, to ita dai tana da tunani kuma tasan ya kamata, dan haka zata ri?e Zainab duk da tasan bata da karfi mijinta ma haka, amma ba zata bar bayan baban Zainab ya wala?anta ba, zata san ta yadda zata yi ta kula da Zainab ?in.

Nan fa Maman Haidar ?in ta yi tsalle ta dire ta ce bata ga uban da zai ?auki Zainab da Khadija ya fitar da su daga cikin gidan nan ba, ai ita ce babba, ita ce zata yanke me za'ayi.

Kuma duk borin kunya take yi, dan tana bakin cikin Maman Hanif ?in ta yi mata zagin kare dangi kuma ba halin ta daketa, dan kuwa tsab Maman Hanif zata karye banza ta ajiye, so tana tsoron fara kwatantacewa ma zata mareta, dan a lokacin Maman Hanif ?in ta fusata sosai, komai aka yi mata ba zata kyale ba, coz shi ne take hucewa ta hanyar hanata ?aukar Zainab.

Maman Hanif kuwa, sai a lokacin da ta shiga ?akin Zainab da nufin ta ?auketa ?in ne sai ta ga ba Khadija, ta tambayeta ina Khadija ?in kuma?. Dan su hankalinsu na a kan kotu duk tsawon kwanakin nan, sannan ?an gaisuwa sun cika gidan, bugu da ?ari basa shiga in da su Zainab ?in suke, suna ta fama da jama'a. Hajiyarsu da izuwa yanzu ta gama nadama da danasani, ko uppan bata iya furtawa, banda kuka ba abin da take yi, Maman Hanif ?in ce ke zama kusa da ita tana rarrashinta, time to time Hauwa na zama kusa da ita dan makirci, so maman Hanif abubuwa sun taru sun mata yawa shiyasa bata farga Khadija bata gidan ba, ita kuwa maman Haidar dama can bata nemesu ba bare ta san Khadija bata nan, tana can tana gantali a tsakanin police station and court ita da Hauwa! Yanzu Hauwa kawarta ce, Allah sarki ta rigada ta shanyeta.

Ko da maman Hanif ?in ta tambayi Zainab ina Khadija ta yi?. Zainab baiwar Allah ta kasa iya yin magana, ciwo ya ci karfinta, zama kusa da ita Maman Hanif ?in ta yi tana ?o?arin lalla?ata ta gaya mata ina Khadija, a wannan lokacin ne Maman Haidar ta biyo bayanta tana bala'i a kan bata ga uban da ya isa ya ?auki Khadija daga wannan gidan ba.

Da maman Hanif fa taga ba iya masu da balai'n nan zata yi ba sai ta kama kanta, ta bawa Zainab hakuri tare da gaya mata cewa wlh tana kaunarsu har cikin ranta, kawai ba yadda zata yi ne da balai'n dangin nan nasu, dan haka Zainab ta kula da kanta ta cigaba da addu'a, idan Khadija ta dawo ma ta gaya mata hakan, dan a tunaninta Khadija ?in ta fita sayan wani abin ne.

A takaice dai wannan shi ne abin da ya faru a kwanakin baya kafin kwana arba'in da rasuwar bbn Zainab ?in.

One thing da ban sanar da ku a nan ba shi ne, mu koma baya mu ?auki farkon labarin A'isha wato maman Zee. Maman Zainab and Hauwa they're very very close friend. Unguwa guda suka taso, makarantarsu ?aya, islamiya ma ?aya, coz ita Hauwa tun suna ?an'mata mayyar ku?i ce, a hanyar islamiya idan suna dawowa duk namijin da ya ?an yi masu wasa irin matasan unguwa haka sai Hauwa ta ce ayya wane ?an saya mun gya?a dafaffa ko wani abin makamancin haka, idan zai saya sai ya saya tare da Maman Zainab, ita bata kar?a, dan mamarta ta hanata.

So a haka suke rayuwa, mayyar kwa?ayi ce ga rokon bala'i, lokacin da Sadiq ya san da hakan dan tana yawan rokonsa, ko abu ta gani a hannunsa sai ta ro?esa, shi ne ya gayawa mamarsu halin Hauwar, gata da yayu?en samari kamar wata ballagaza, Sadiq ya ce wa mamarsu kullum saurayin da zaka ganta da shi na safe daban na yamma daban, kuma dukka yara ne da basu wani isa aure ba, ba iya ri?e mata zasu yi ba, amma sai ta biye masu tana cinye masu ku?i, ga shegen kaifin harshe kamar reza, nare nare zata kalailame ?an mutane da kalaman yaudara ya ?ebi duk ?an cinikin ku?in da yayo a kasuwa ya bata, ta kar?e ta shige gida.

Hajiyarsu Sadiq da ta ji haka ta bincika kuma ta gane hakan sai ta ce da Mmn Zainab maza maza ta kama kanta, ta yi maza ta fita harkar Hauwa dan ba kawar zama bace, duk mace mai kwa?ayi da rokon maza da mata abu to tabbas tana gab da jefa kanta ga halaka, dan kuwa kwa?ayinta zai kaita ya barota.

Da Hauwa ta biyo mata zuwa Islamiya Sadiq da kansa ya kora mata jawabin kada ta sake zuwa gidan, kuma kada ta sake ko ?aga idanu taga maman Zainab, kowa ta yi rayuwarta, ta so ta masa rashin kunya ta zage shi, sai Hajiyarsu ta taka mata birki ta kara mata da bayanin ko sannu kada ya kara ha?ata da maman Zainab basu so, kowacce ta bi nata layin.

Abin ya ba?anta mata rai sosai, already dama ita Hajiyar tasu tasan yaran gidansu Hauwa ba yaran kirki bane, uban nasu ne wato kanin baban Hauwa shi ne mutumin banza maras zuciya da kwa?ayin abin duniya, shi ne ya koyawa yaran kwa?ayi da ro?o yana zaune su ciyar mashi da gida, har tutiya yake yi ya haifi jari, ?iyar arziki su suka ri?e mashi gida. Coz Hajiyarsu tasan da wannan, amma da taga Hauwa na zuwa makaranta har da Islamiya sai ta yi tunanin to kila ita ta fita zakka a cikinsu, ashe kuwa duk kanwar ja ce bata sani ba, shiyasa bata ?ata lokacinta wajen cewa zata yi wa Hauwar nasiha ba kawai ta yanke hukuncin rabata da ?arta, dan tasan duk gidansu haka suke ba kamun kai ga ?an banzar rashin kunya da rena manya, komai girman babba ya yi masu zage shi fes zasu yi babu ruwansu.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull