Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 14

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 14

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 14: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 14. To a takaice a haka aka raba maman Zainab da Hauwa, bayan kamar sati biyu…

3,241 words

To a takaice a haka aka raba maman Zainab da Hauwa, bayan kamar sati biyu suka sake jonewa, sai dai basu bari an gane suna tare ba, suna kawancen ne kawai daga islamiya sai school, a cikin unguwa basu ta?a nuna kamar sun san juna, ko sannu basu yi wa juna. A haka suka cigaba da yin rayuwa har lokacin da aka zo neman auren Hauwa, wani bakano da ya zo biki a garin Kaduna, a unguwar su Maman Zainab ?in za'a ?auki amaryar a kaita Kano, so Hauwa tana cikin kawayen amarya, a nan dai suka ha?u da mijin nata har ta kawo shi gida, aka yi abin da za'ayi, a lokacin mijin nata yana ji da ?an dukiyarsa dai'dai gwargwado, shiyasa ta yarda ta amince ta aure shi ya tafi da ita Kano, amma a lokacin sun kammala secondary sai dai babu abin da Hauwa kam ta iya in ba satar amsar ?a'?an jama'a ba, dama ita fa ba karatu take zuwa ba, yawon neman samari take fita ato, ku?in makarantar ma daman yayan mamanta yake biya mata ba bappan nata da ya ri?eta ba, shi yaransa ai basa makaranta, Hauwar ce kawai ta shiga makaranta a cikinsu.

In short bayan aure Hauwa da kamar wata biyar baban Zainab ya zo wajen wani abokinsa a Kaduna, a hanya suka ha?u da maman Zainab ta je wajen kanwar mamarta tana dawowa, ta tsaya a bakin hanya zata nemi abin hawa dan ta dawo gida, a nan ya ganta, sai dai bai tare ta a hanya ba, ya bi bayanta shi da abokin nasa, abokin nasa yana da mota, so basu yi mata magana ba ta hau abin hawa suka bi bayanta har sai da ta shiga gida.

Da ta shiga gida sai suka yi sallama da babanta, Sadiq baya nan lokacin sai Hajiyarsu ta sanya katuwar hijabi ta fito, a takaice suka fa?i abin da ya kawo su, ganin irin abin da suka yi yasa Hajiyar tasu ta fahimci lallai lallai baban Zainab yana da hankali da kuma ilimi, kuma ya cancanci a bashi aure, saboda alama ya nuna shi ba wasa ya zo yi ba, da wasa ne ba zai nemi gidansu ko iyayenta ba, ita kai tsaye zai tara, amma ya biyota gida, bayan ya biyota gidan ma bai dakatar da ita ba ya nemi ganin babanta, lallai ba shakka yana da hankali sosai. Hakan yasa ta ce mashi ya yi hakuri ya dawo gobe, dama a ranar zai koma Kano, ai kuwa ya ce ina kwana Kaduna ta kara kama shi, kun san kanawa da son fararen mata (??) ya kuwa ce dole ya jira amsar Hajiyarsu.

Ita kuwa ta ce mashi haka ne dan tana son su yi maganar da ?a?an nata barema Sadiq da yake da hankali sosai, ?aramin yaro ne a lokacin amma akwai hankalin manya sosai kamar wan da ya girma a cikin dattijawa.

In takaice maku labari wannan shi ne sanadiyar aure baban Zainab da maman Zainab bayan anyi bincike da komai da komai. Baban Zainab ya sha jigila tsakanin Kano da Kaduna yana zuwa hira.

Lokacin da aka yi auren su maman Haidar kamar su cinyeta saboda so, ko kwatancen haske fata suke yi a magana to da nata fatar suke kwatantawa, suna bala'in sonta barema Hajiyarsu da ta ?auketa kamar ?arta, suna zaman lafiya da kaunar juna ha?e da girmama juna, ganin mutuncin juna.

Rana tsaka kawai Maman Zainab da jaju?owa kanta wahala ta nemo number Hauwa ta hannun wata kawarsu ta Islamiya, ta kirata ta sanar da ita ai ita ma a Kano ta yi aure, yadda kuka san Hauwa ta shanye mata kurwa.

Haba Hauwa kam bata yi ?asa a gwiwa ba wajen kar?ar address ta ce gobe gata nan zuwa. Wannan shi ne musabbabin sake ha?uwarsu a Kano, suka cigaba da kawance, Hajiyarsu maman Zainab bata sani ba, Sadiq bakinciki ta isheshi kamar ya kashe Hauwa, amma haka ya danne, kuma bai gayawa Hajiyar tasu ba, dan shi tun ainahi ba mutun ne mai fa?ar duk abin da ya gani ba, baya son gutsiri tsomi, yana da kawar da kai a kan abubuwa ba komai yake nacewa ba.

Lokacin da baban Zainab ya sanya Sadiq ?in a school daga nan ne Hauwa ta fara jin wani iri a ranta, dan kuwa mijinta ko naira baya bawa kannenta, zasu taso daga Kaduna su zo wajenta ko ku?in motar komawa baya basu, ta yi mashi ?orafi har ta gaji ta hakura.

Baban Zainab tun da suka yi aure da maman Zainab arzikinsa sai kara bun?asa yake yi, da farko ?aramin makaranta ya sanya Sadiq, daga baya ya ?auko Haidar ya ha?asu.

Bayan an haifi Khadija da Zainab ya canza masu Sadiq ?in makaranta zuwa ta ?a?an masu ku?i, nan fa Hauwa hankalinta ya tashi, abinku da mai kwa?ayi, mai hali baya fasawa, ga maman Zainab da iya bata labarin abin kyautatawa da baban Zainab yake yi masu sannan yake turawa Hajiyarsu ma Kaduna. Hauwa zuciya ta yi bakinkirin kamar gawayi saboda haushi ita ba'ayi mata mai kyau ma bare ayi wa danginta. Ita kuwa maman Zainab tana gaya mata wai dan ta tayata murna ta samu miji na gari, bata san hasada take yi mata ba.

A haka dai suka cigaba da tafiya, Hauwa fa taga ba zata iya jurewa ba hasada zai kasheta, nan ta bazama ta fara nemanwa kanta mafita, to a wannan ga?ar ne ta ha?u da wata kawar banza ta jefata bin bokaye, farkon abin da ta fara yi ta mallake mijinta ta rufewa danginsa baki a kanta. Tana mallakesa ta fara kwasan ku?insa ta shiga harkar dillanci, duk tana rame tana bushe, Maman Zainab kuwa ko'ina a cike ?ul ?ul gwanin sha'awa.

Bayan ta kwashi ku?insa ta bi sahun dillalai sai ta sake kwasan dubu ?ari biyu nasa ta koma wajen boka dan a shiga tsakanin maman Zainab da dangin mijinta da mijin nata gaba?aya, a lokacin asirin ya ki kama baban Zainab, sai dai su maman Haidar, ta raba maman Zainab ?in da dangin mijin nata, su maman Haidar suka dawo basu kaunarta, su da a baya kamar su cinyeta saboda so, amma suka zama basu kaunar ganinta sam sam, aka rasa daga ina matsalar take, ashe Hauwa ce ta hassasa komai. Wannan shi ne farkon shiga matsalar maman Zainab kenan a rayuwarta, amma ta cigaba da hakuri har duk abin da ya faru ya faru.

A takaice kenan abubuwan da suka faru a baya, nasan zaku fahimta duk da in short na baku labarin, idan zaku lura a rubutuna ban cika tsawaita bada labarin baya ba, zan dai yi maku yadda zaku fahimta, amma bana son dogon labari a kan abin da ya wuce, ayi wanda ake yi a yanzu, dan ban son ?ata lokaci. Coz yanzu nasan kun fahimci labarin maman Zainab ko?.

To maganar da zan yi a nan shi ne, abin da ma yasa na kawo tarihin maman Zainab a nan shi ne dan na baku darasi mai girma, ku sani ita uwa ba'a bijire umarninta matu?ar bai sa?awa Allah ba, uwa ta wuci wasa, ta wuci tunanin mutun, duk lokacin da kika bijire maganar iyayenki to ko bajima ko ba da?e sai kinga ba dai'dai ba, mahaifiyarki ba zata ta?a hanaki yin abu haka kawai dan ra'ayin kanta ba, saboda duk duniya babu wanda ya kaita kaunar taga farincikin ?a?anta, dan haka duk abin da zata haneki da shi ki daure ki hakura, gaba zaki gane illar abin da yasa ta hanaki wannan abin, abin da babba ya hango yaro ko ya hau rimi ba zai hango ba, to dan Allah idan mama ta ce abari a bari ?in shi ne yafi. Da maman Zainab ta rabu da Hauwa tun lokacin da mamarta ta umarceta da duk abin da ya faru da ita bai faru ba, amma taki wai ita a dole tana da wayo ta yi wa mama wayo suna ?awance da Hauwa a ?oye. Ta manta da cewa zata iya yi wa mama wayo amma ba'a yi wa Allah wayo, Allah ba abin wasa ba ne! Wane ?an adam ya ce zai yi wa Allah wayo! Daga ?arshe dai rashin jin maganar mahaifiya ya jefata duk cikin wannan bala'in da ta shiga, yanzu ga shi tana danasani maras amfani!!.......... My people's mu gyara halalenmu, mu bi iyayenmu sau da kafa dan samun ribatuwar duniya da lahira, wani lokaci ki na ?aukar maganar mamarki ai karamar magana ce ba wata babba ba bari ki shareta kawai, wlh babu karamar kalma a maganar uwa, duk abin da zai fita daga bakinta babbar kalmace da garinku ya yi ka?an ya ?auketa idan za'a mai da kalmar dutse, dan haka ki lura da komai ?an?antar maganar mama kada ki yi wasa da shi, dan kuwa maganar mahaifiya yana bin bawa har tsufa, Mama ta wuci wasa, ina fa?a ina karawa, a kula sosai. Kun dai ga maman Zainab dai ta bijire maganar Mama ta kare a prison tare da tarin uban danasani maras amfani! Allah ka kiyashemu yin danasani, Allah kasa mufi karfin zu?atanku. Yanzu mu koma kan labarinmu, dan gidansu Zainab akwai tarin darusan rayuwa sosai, kuma duk abin da yake faruwa a cikin gidan abu ne wanda yake faruwa a cikinmu sosai da sosai, labarin kamar true life story nake jinsa a rai'na, fata na dai ?an uwana mata zaku ?auki darasi domin gyara, wa?an da irin haka ya faru da su sai dai muce Allah ya kiyaye gaba, wa?an da kuma bai faru da su ba sai ku ?auki alluran rigakafi daga rayuwar maman Zainab, a rashin jinta ta cuci harda rayuwar ?a?anta gaba?aya!. Ni yanzu damuwata ma ko ina Khadija?......????

STORY????

Sadiq dai shi yake jinyar Zainab a hospital, yarinyar ba um bare um'um, shiru, sai wa?an nan dara daran idanun nata da suka kara girma saboda rama take bin mutun da su

(Amanar Jehan, Leesharh, Ummu Sudais, Maman Sultan, Sumayya, Daughter in low, Adama, babyn Oumma, Oumu Amjad, Zubaida Abdullahi, Zaituna, Shafa'atu Adam, Princess, Meerah, Maryamcy, wlh sunan ma ba zasu ?irgu na, da dai sauranku dukka yau ku tashi kai'na da ruwan commenters, kamar yadda na sanyaku hawaye a page ?in nan ni kuma ku sanyani dariya na gaya maku?? maman Sultan Allah ya ji?an Sweetie na gaya maki?????? Maltina mai sanyi yana jirana????)

??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????

??RAWANIN ?? ZALINCI ????

????????????????

FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????

?????????? 30/9/2024.....??????

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????

??STEP TWO....??????

Sadiq dai shi yake jinyar Zainab a hospital, yarinyar ba um bare um'um, shiru, sai wa?an nan dara daran idanun nata da suka kara girma saboda uban rama take bin mutun da su..................., kome Sadiq zai ce mata sai dai ta bishi da ido kawai, duk ta rame ta zama abin tausayi, kamar ba Zeezeen babanta ba, ta yi wani haske fau kamar bata da jini a jikinta.

Ita ka?ai tasan ra?a?in da yake cikin zuciyarta ?ar tahali?ar nan, azabar da ta yi mata yawa ne ma ya hanata bu?e baki, ta ci kuka har hawayen sun dai'na zuba izuwa yanzu, babban damuwarta shi ne ina Khadija? Ina ta tafi? Yau kwana arba'in da wani abu babu ita babu labarinta, a wani hali take ciki? Wannan shi babban abin da ya fi damunta, gara mata iyayenta ta rigada tasan babanta ya rasu, ya tafi in da ba'a dawowa, yanzu ba zata sake ganinsa ba, wlh har gizo sautin muryarsa yake yi mata a cikin kunne yana fa?in Zeezeena zan kawo maki lemu mai zaki sosai, Zeezeena yau kam lemun nan dukka naki ne ke ka?ai kada ki bawa mamanki ko ?aya, Zeezeena mu je kasuwa ki za?i duk kalar abayar da kikeso kala biyar mu dawo.

Duk in ta motsa baiwar Allah sai ta ji sautin muryarsa yana dakar dodan kunnenta, ta rasa ina zata sanya ranta, hakan ne ya jawo mata ciwon kirji, kirjin nata yana tsananta gudun bugu fiye da yadda yake yi saboda tashin hankali. Mamanta kuma ta rigada tasan tana prison, kuma izuwa yanzu ba'a bawa kowa damar zuwa ganinta ba, kome dalilinsu oho? Case ?in ma kamar akwai ?ullalliya a ?asa. So tasan maman nata ba lallai ta sake sanyata a idanunta ba tun da ?aurin rai da rai ne, idanunta sun kasa dai'na ganin face ?in maman nata ta lokacin da babansu yake tsokanarta yake cewa ya fita kyau hasken fata kawai zata gwada mashi, ta kafe ita kuma a kan lallai ta fishi, har yanzu Zainab tana ganin face ?in maman tata a idonta cikin wannan yanayin, sai kuma idan tana murmushi babansu ya kawo mata abin da take so.

Wa?an nan abubuwa suna neman zautar mata da ?wa?walwa, in da Allah ya taimaketa dai bata magana, da tana magana kam da anji sambatu kala kala, sai dai fa da alama bata cikin hayyacinta sam sam, dan kuwa irin kallon da take yi wa Sadiq abin da mamaki, in ta kafe shi da ido bata ko kyaftawa har sai idan shi yaga kallon ya yi yawa sai ya matsa daga saitin idanun nata, haka kuma zata sake binsa da kallo. Idan ya bata kankana ko lemu haka zata zubawa lemun idanu ta yi ta kallo kamar wadda taga abin da bata ta?a gani ba.

Tun abin bai dame shi sosai ba yanzu har ya fara ?aga mashi hankali sosai da sosai, bawan Allahn sai tausar zuciyarsa yake yi a kan ya yi hakuri zata ji sauki. Duk hakuri da dauriya irin nasa sai da ya zubarwa da Zainab kwallah, ba dan shi namiji bane kuma yana da tawakkali wlh da shi ma ya zube a gadon asibiti irin wannan tsananin tashin hankali, ba ?ar uwa, sannan ba Khadija! Zainab na asibiti! Babu babansu ya iyali ya lilliahi, lokacin guda gidan farinciki ya ruguje ya koma na bakinciki. Har yau ya gagara iya gayawa mahaifiyarsa abin da yake faruwa, kullum idan ta kirasa a waya ta ce ina maman Zainab tana kiranta wayar bata shiga, sai ya yi mata karyar wayar ce ta lallace, in ta ce ya ha?asu a waya sai ya ce yana kasuwa, last week kam ma sai ce mata ya yi ai baban Zainab da maman Zainab ?in sun yi tafiya zuwa wajen wasu ?an uwan baban Zainab dake jihar Bauchi.

Sam bata yarda da maganarsa ba hakan yasa tasa ayi mata bincike ba tare da saninsa ba, dan tana ji a jikinta ba lafiya ba, uwa kenan, babu kamarki a duniya!!.

A ?angaren neman Khadijan kuwa, Sadiq ?in ya je station ya fi a kirga, zuwansa na ?arshen nan ma sai ce mashi wanda case ?in yake hannunsa ya yi cewa ai ?asar waje aka fita da Khadija, bata Nigeria, a ranar da aka ?auketa a ranar aka bar ?asar nan da ita, dan haka suna cigaba da binciken wace ?asa aka tafi da ita, ya je ya yi ta tayasu da addu'a kawai.

A lokacin ji ya yi tamkar zai ha?iyi zuciya ya mutu, ga shi Zainab bata magana bare ya tambayeta ko akwai abin da ta sani dan gane da Khadija ko zai iya samun damar yin hasashen su waye suka ?auketa, ya kashe ku?i tun yana lissafi har ya dai'na, ya shiga damuwa na wuce misali, ko abinci bashi da lokacin ci bare wanka, da kyar yake samu ya yi wanka a rana sau ?aya, da farko hotel ya kama, daga baya ya ha?a kayansa ya koma tsohon ?akinsu a tsohon gidansu Khadija ya zauna, bige kwa?on kofar gidan ya yi ya sayi sabo ya saka. Haidar kuwa sai Allah ka?ai yasan a wace duniya yake yanzu, dan baya garin Kano gana?aya.

A ?angaren Hauwa mai bakar kafa kuwa, sai shirye shiryen ta yadda zata fara kwasan dukiyar gaba?aya ta gudu take yi, tana ta ?ara ingizata su Maman Haidar tana hure masu kunne.

_____________________________????

DUBAI??

A hankali ya yi ?asa da kallonsa izuwa kan kafafun nasa.

Kwata kwata Leesharh bata cikin hayyacinta saboda marin da ya wanke mata fuska da shi, tana can tana ganin jiri, sai ?o?arin fa?uwa ?asa take yi, sam kunnuwanta sun daina jiyo mata sautin komai.

Kasancewar wajen babu wadataccen haske yasa bai iya gane menene ya same shi a kafafunsa ba, ya dai ji ra?a?in zafi ta ziyarcesa kawai.

?o?arin gano me ya same shi a kafafun nasa ya fara yi ta hanyar sanya hannu a aljihunsa zai ciro wayarsa dan ya kunna light ?in ta. Dai'dai lokacin Sharifat ta iso wajen, idan baku mance ba dama ta biyo bayan Leesharh ?in. Ganinsu a tsaye cirko cirko yasa ta ja binki ita ma tana fa?in. "Leesharh meyasa kika tafi kika barni bayan nace ki jirani?".

Ina ai Leesharh bata iya jinta, kunnuwanta sun do?e. "Leesharh lafiya kike kuwa?". Ta sake jefa mata tambayata tare da kwalalo idanunta da kyau dan ta samu damar ganin Leesharh ?im da kyau. Shi kuwa Obaid sai ?o?arin kunna wayarsa ta ya yi switch off ?inta a wajen walima yake yi.

"Obaid meyake faruwa? Me ya ha?aka da Leesharh?" Ta tambaya tare da dawo da kallonta a kansa. A dai'dai wannan lokacin kuma Leesharh ?in ta fara dawowa cikin hayyacinta. Addu'a ta fara yi a cikin zuciyarta Allah ya ku?utar da ita daga hannunsu, zuciyarta tamkar zai fasa kirjinta ya fito waje saboda tsorata na halin da ta shiga.

"Leesharh meya ha?aki da Obaid?". Ta yi maganar tare da dawowa kusa da ita ta ?an ri?onta. Ganin tana dafe da kumatu ne yasa ta sake cewa. "Marinki ya yi ne?". Wannan magana da ta yi a kan kunnen Guyson da ya iso wajen a yanzu ta yi shi, sai sauri yake zubawa zai je wajen Ramish kafin ya fita, bai san cewa already Ramish ya jima da fita ba, wannan stair case da Leesharh ta tsaya a kusa da shi ?azun da Sharifat ta ce ta jirata a bakin part ?in nasu hanyar sirrinsu ce na fita part ?insu ta kofar baya ba tare da elevator ba kenan, ta nan Ramish ?in ya fita, da alama ba kowa yake son ya san da fitarsa ba, dama kuma already kun san shi baya yarda da kowa, fitarsa ta wannan kofa hanya yasa suka samu sa?ani da Guyson dake shirin komawa ?asar Tunisia, da Abu Abdussalam ya ki yarda ya barsa ya koma, amma da King Zuhair ya matsa mashi sai ya hakura zai mayar mashi da shi, dan fa ya ri?ewa King yara dayawa yaki bashi, kowanne ya ce yana so, shi ka?ai ya tattaresu dukka.

"Obaid yanzu sake marin yarinyar nan ka yi? Wai me ta yi maka ne? Meyasa baka sonta? Kafa san wannan hannun naku kai da Omaid kamar na a'dawa yake ga shegen zafi, kun kar?i horo iya horo da ake bawa manyan mutane, kuzo kuna gwada marin ?ar tahalika da bata yi maku komai ba?". Cewar Guyson.

Shi duk abin da suke fa?a ma ba ta kansu yake ba, burinsa wayarsa ta karisa kunnuwa ya ga ?afarsa me ya taka take yi mashi zafi.

Sharifat ce ta amsawa Guyson ?in da cewa. "Dama Yah Guyson ya ta?a marinta ne na ji kace ya sake marinta?". "Kwarai Sharifat, ?azun ya mareta a wajen grass carpet dake kusa da hall".

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull